Share this page
sauri tashigo class ɗin. Wata abukiyar karatun Hafsat, Naja'atu ta tambaya tace, ina Hafsat?". Sai Naja'atu tace, "ai Hafsat ta daina zowa school dan tun dawo wa hutu sau biyu ta shigo class,kinga ma exam card ɗinta yanzu haka ita nake jira". Safiyya tace, "bata da lafiya,amma nasan yanzu zata zo,bani card ɗin nabata dan sauran kayan ta ma na hannuna". Ba musu Naja'atu ta bata. Aikuwa tana ƙarɓa da sauri ta fito ta kama hanyar hostel,tana zowa tasumu arun niƙaf tasa afuskar ta ta dake ma ran,ta tashiga class ɗin haɗe da addu'oi Allah kasa kada agane ba Hafsat ce ba. gaban ta na duka uku-uku haka taje ta zauna saman sit ɗin Hafsat batari da tawa kowa magana ba. Ko minti biyu batayi da zama ba aka fara raba Question paper. Ana kawo wa gaban ta,gabanta ya bada dummmm,addu'a takeyi Allah kasa kada ace sai ta ciri niƙaf ɗin da ta sanya..... *To fah Safiyya kin iya ganganci*🤔 *# Vote* *Comment* *Shere* *©SUMY NAIGE.* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~ *SHAFI NA 8📑* *__________📖* Cikin ikon Allah ya aje mata Question paper ya wucewarsa batare da yayi mata magana ba. Aikuwa yana wuce ta ta fara yiwa Allah kirari a zuciyar ta haɗi da godiya a gare shi. Tunda ga lokacin taci gaba da rubuta mata exams har suka kammala ba tare da ta samu wata matsala ba, sai dai gaba ki ɗaya ta dawo hostel da zama dan bata da lokacin komai sai na karatu, kuma tunda ta fara rubuta ma Hafsat jarabawa ba wanda ya gane ba Hafsat bace in ba ƙawar karatun Hafsat ba Naja'atu. Sosai taba Safiyya gudunmuwa wajan ganin tayi ma Hafsat jarabawa, duk da ba department ɗaya suke da Safiyya ba amma tayi ƙoƙari sosai dan gabaki ɗaya ta hana ma kan ta barci ko da yaushe tana library wajan karatu, tayi nata tayi na Hafsat, har Allah ya nuna mata ta gama lafiya sosai tayi rama saboda rashin natsuwa da rashin isashen bacci. Tunani ta farayi lokacin da suka gama exams yadda zata koma gida ba tare da Hafsat ba, dan haka ta yanke shawarar taje gidan sauranyin nata ta gani ko zata ganta,har zata je kuma ta fasa saboda ba ƙaramin baƙin cikin ganin sa takeyi ba dan haka ta yanke shawarar takira ta a waya. Miss call kusan biyar tayi mata amma bata ɗauka ba sai ga na shidda kana ta ɗauka batare da tace komai ba. Safiyya ba tadamu da rashin maganar taba dan haka tace, "kidawo dan ni zan koma gida kuma kin san da naje zasu tambaye ki dan haka gobe zan koma ko ki dawo ko kada ki dawo na dai faɗa miki". Bata ma bari taji me zataceba ta tsinke wayar. Ita ko Hafsat tunda suka sauka ya kama musu hotal bata sake koda leƙo ƙofa ba dan baya barin ta. Kuma yanzu ko lafiya bata isheta ba dan yanzu bata da wani kuzari, ga wata rama da takeyi duk tabi ta bushe kuma tana cin abinci amma kamar bata ci, sosai abun ke bata tsoro dan ita gabaki ɗaya tunda sukayi tafiyar nan bata cikin kwanciyar hankali, abu kaɗan ya isheta kuka. Yau ma kamar kullum suna kwance yana romance ɗin ta son ran shi, sosai yake jin daɗin abunda yake mata, ƙoƙarin shigar ta ya fara amma tana ɗan kaucewa, saboda yanzu ko kaɗan bata son abun da yake mata dan yanzu da ya gama abunda yakeyi da ita sai wani azaftaccin ciwon mara ya taso mata wanda kesa jikin ta kar-karwa lokaci ďaya. Sosai take wahala kuma duk wannan uban ciwon marar dake taso mata ta gagara faɗa masa ya dena amfani da ita ko suje hospital a'a ita baza ta iya faɗa masa ba dan kar ransa ya ɓaci. Duk da tana ƙoƙarin hanashi amma shi bai masan tanayi ba. Ba ɓata lokaci ya afka cikin ta ya fara abunda yake so da ita son ranshi. Aikuwa yana gamawa ya ɗan kwanta dan ya huta yaci gaba da abunda yake yi. Ita ko yana sauka daga kanta, lokaci ɗaya wani abu ya taso mata ƙasan marar ta, tun tana dauriya kar ya gane har abu yazo yafi ƙarfin ta, lokaci ɗaya ta fara fita hayyacin ta, duban sa ya kai gare ta aikuwa lokaci ɗaya ya zabura ya mike zaune haɗi da tambayar ta, "lafiya mike damun ki"?. Ita ko batama san yana yi ba saboda a lokacin bata masan inda kanta yake ba. Abun yaga yafi ƙarfin sa dan haka da sauri ya saka jallabiya ya ɗauke ta domin suje hospital. Cak ya ɗauke ta ya kai mota, rasa asibitin da zai kai ta yayi, dan dare yayi gashi kuma bawani sanin garin yayi ba. Masu gadin hotel ɗin ya tambaya yace su nuna masa hospital mafi kusa? dan matar shi ce ba lafiya haɗi da nuna musu ita a cikin motar. Wani private hospital dake kusa da hotel ɗin suka nuna mai godiya yayi musu kana yaja motar da gudu bai tsaya ko ina ba sai cikin hospital ɗin. Cikin gaggawa Likitoci suka karɓe ta, lokaci ďaya suka fara bata taimako . Sun jima kanta kafin su shawo kan lamarin. Bayan komai ya ɗan lafa kuma ta samu barci dan haka suka fito daga ɗakin da take. Yana ganin sun fito ya fara tambayar su ya jikin nata?. Komai basu ce dashi ba sai babban doctor daga cikin su yace dashi "ka biyo mu office". Komai bai ce dasu ba ya bi bayan su. Bayan sun isa office dukan su suka zauna, kana suka nuna masa kujera domin ya zauna. Bayan ya zauna sai babba daga cikin Likitocin yayi gyaran murya kana yace, "da farko dai munyi nasarar ceto matar ka dan yanzu haka ta samu bacci kuma insha Allahu ina har takiyaye ƙa'idojin da zamu ɗaura ta akai to babu shakka zata samu lafiya sosai da sosai. Sai abu na biyu muna tayaka murnar matar ka na ɗauke da juna biyu har na tsawon wata huɗu....." aikuwa tun Doctor bai kai da ƙarasa maganar ba yace, "what haɗi da faɗin ciki!. Gabaki ɗaya Likitocin kallon shi suka farayi cike da mamaki. Dubin doctor yayi kana yace, "Doctor kun duba da kyau kuwa? dan ni matata bata da ciki gaskiya". Results ďin scanning ďinta dake gaban sa ya bashi yace, "duba kagani". Karɓa yayi ya fara dubawa, abunda yagani ne yayi matuƙar bashi mamaki da tsoro. Yana gama dubawa sai ya ɗago da kansa yana kallan Doctor kana yace, "Doctor na gani kuma na yarda tana da ciki amma ina son a zubar da shi dan ba yanzu zamu haihu ba, ko nawane zan biya kawai a zubar da shi". Tunda ya fara magana gaba ki ɗaya Likitocin suka zuba mishi ido suna kallon shi har ya kai ƙarshen zancen shi. Sai da ya gama kana babba daga cikin Ƙikitocin yace, "kafin na gaya maka komai ina son kasan wani abu ɗaya, lokacin da kake ba matar ka ƙwayoyin hana ɗaukar ciki to kasani sosai sukayi mata illah a mahaifar ta, dan ikon Allah ne yasa wannan cikin ya shiga cikin mahaifar ta har ya zauna ya kai wannan lokacin ba tare da ya zube ba,sosai mukayi mamaki lokacin da muka ga yadda mahaifar ta take dan sanadiyar wannan magani da kake bata mahaifar ta tafara lalacewa sosai, dan ko da wannan cikin ya kai matakin haihuwa to na tabbata bazata iya haihuwa da kanta ba sai ammata aiki, dan haka yanzu idan kace a zubar da cikin to za'ayi ɗayan biyu, dan sanadiyar haka mahaifar ta zata iya lalacewa bazata ƙara ɗaukar ciki ba ko kuma wajan cireshi ta rasa ran ta, kaga ko baza kayi fatar ko ɗaya a cikin waɗan nan su samu matar kaba". Sai da Anwar ya nisa kana ya dube Doctor yace, "Doctor kada kaji komai nasan haka bazata faru ba, kawai a cire shi dan bana son cikin". Gabaki ɗaya Likitoci da ke office ɗin kallon sa sukeyi dan abunda ya faɗane ya basu mamaki. Sai Doctor yace, "banƙi ta taka ba amma sai nayi magana da matar taka idan ta aminta acire to ba komai zamu cire amma idan bata aminta ba to gaskiya ba zamu cire ba saboda aikine mai wuyar gaske?". Sai Anwar yace, "kada ka damu da matata dan nasan zata aminta dan haka kuyi aikin kawai". Sai doctor yace, "a'a sai naji ta bakin ta". Sai Anwar yace, "ba damuwa idan ta farka zaka iyayi mata bayani". Doctor yace, "ba damuwa". Bayan gari ya waye kusan ƙarfe goma Hafsat ta farka, kuma Alhamdlillah dan ta samu sauƙi sosai. Bayan tayi wanka tayi break tasha magani Doctor yazo ya duba ta kuma yaga jikin da sauki dan ba wata matsala yanzu dan haka yace bari yakira sauran Likitocin. Aikuwa yana fita Anwar ya ƙarasu gareta wani kallo ya jefa mata haɗi da yimata ya jiki. Bayan ta ƙarɓa yace, "ni zaki munafur ta, ashe kin san kina da ciki amma kika ƙi sanar dani, to bani kika cuta ba kanki dan ni bazan aureki da ciki ba dan haka tun wuri kisan abunyi". Da sauri ta ɗago da kanta ta kalleshi bakin ta na kar-karwa tace, "wani ciki, wallahi ni banda ciki kuma da'ace inada ciki da kai kanka zaka sani". Wani kallo ya watsa mata haɗi da jefa mata wasu takardu yace, "duba kigani". Jikinta na kar-karwa ta ɗauka ta fara dubawa aikuwa tana gama dubawa ta zabura haɗi da sanya hannu akai tace,"ciki gareni fah!. Wasu hawaye suka fara bin kuncin ta haɗi da durkusawa ƙasa ta fara kuka mai tsoma zuciya. Tsawa ya daka mata haɗi da faɗin tayi shuru zaiyi magana da ita. Hannun ta ta ɗaura kan bakin ta kana tace, "na daina". Yace, "abunda nake so dake idan Likitoci suka tambaye ki kin yarda azubar da cikin kice eh kin yarda, dan idan baki yarda ba to wallahi bazan aureki ba kuma sai dai kije kisamar masa uba amma ba niba". Jikin ta na kar-karwa tace' "na yarda ko ma basu tambayeni ba na yarda kuma kayi hak'uri kada ka fasa aurena please". Har zai sake magana sai ga Likitoci sun shigo ɗakin. Ƙarasawa sukayi gaban gadon da take kwance, bayan sun gaisa sukayi mata ya jiki kana sukayi mata bayanin da sukayi ma Anwar har wanda yayi musu na azubar da ciki. Bayan sun gama yimata bayani sai ɗaya daga cikin su ya dube ta yace, "kin amince azubar da cikin?". Duƙar da kanta ƙasa tayi wasu hawaye masu zafi nabin kunci ta, tunani ta fara idan aka cire shikenan baza ta sake haihuwa ba kenan?ko ta rasa ranta, kuma yace bazai aureni da ciki ba to ya zanyi?. Shurun da sukaji tayi ne yasa suka yi mata magana kallon su tayi da idon ta dasu ka sauya zuwa ja, sosai ta basu tausai dan haka suka ce da ita kin amince?". Sai da ta rufe idon ta kana tace, "a'a ban amince ba". Tun bata kai da rufe bakinta ba Anwar ya daka mata tsawar da tasa ƴan cikin ta kaɗawa. Bai ma damu da Likitocin dake wajan ba yace, "me kika ce? baki amince ba?". Jikinta na kar-karwa tace, "Hayat kayi haƙuri dan Allah ka taimaki rayuwata". Har zaiyi magana sai ɗaya daga cikin Likitocin yace, "Malam bari kaji koda a ce ta aminta azubar da cikin tomu ba zamu zubar ba, dan mu ba aikin mu bane, idan kaga zaku iya zama har ta samu sauƙi to bazamu hanaka ba amma idan kaga baza ku iyaba to zaku iya ƙarawa gaba amma mudai bazamu zubar mata da ciki ba bare ciki har na wata huɗu". . Yace, "ko minti biyar baza muyi anan ba bare har na sa kuɗina taci gaba da kwanciya anan". Kallon ta yayi yace, "ki tashi muje sai kije can ki haifar musu shi dan wallahi kar ma ki soma cewa nawa ne" yana faɗar haka ya kama hanyar fita batare da yaji mi zasu ce dashi ba. Suma Likitocin fita sukayi har sun fita sai ɗaya daga cikin su ya dawo ya sameta sai kuka takeyi kamar ranta zai fita yace, "Shawara zan baki duk yadda yaso kada ki yarda a zubar miki da ciki dan ke zai cutar, shi a kowane lokaci yake son haihuwa zai iya wani aure ya haihu amma ke shikenan baza ki saki haihuwa ba har abada, dan haka ki tashi kije yana jiranki " yana faɗar haka shima yafice daga ɗakin. Sai da tayi kusan minti biyar kana ta tashi ta fara bin bango ta fita a ɗakin har ta kai wurin da motar sa take. Tun bata ƙarasu wajan saba ya fara afka mata wata muguwar harara. Motar ta buɗe ta shiga aikuwa tana shiga yaja motar da ƙarfi kamar zai tashi sama ya fice. Suna isa hotel ɗin ko kallo bata ishe saba ya buɗe motar ya barta ba tare daya kalleta ba. Haka tafito tana tafiya a hakali har ta isa ɗakin da suke. Koda ta shigo yana toilet yana wanka wuri tasamu ta zauna, bata jima da zama ba ya fito yayi kamar bai san da zaman mutum a wurin ba. Har ya gama shirin sa zai fita kana ya dube ta yace, "ki tattara naki da naki dan gobe zamu koma gida kuma wallahi ba zaki sauka gidana ba sai dai kije gidan ubanki" yana faɗin haka yafice warsa batari da ya tsaya yaji mi zata ceba. Yana fita ta fara kuka mai ban tausai, tana cikin kukan ne Safiyya takira ta kuma abunda yasa tak'i magana dan kar taji tana kuka. Haka ya barta har dare batare da ya sake wai-wayar taba. Kuma babbar matsala duk baifi rashin ƙarfin jikin da bata dashi ba kuma ga yunwa ta dame ta dan tun safe rabun ta da abinci gashi yanzu dare yayi kuma har yanzu bai dawo ba. Har barci ya fara ɗaukar ta sai gashi ya dawo, da sauri ta tashi dan a tunanin ta ko zata samu wani abun da zataci koda tea ne tasha. Koda ya shigo sarai ya gan ta amma sai yayi kamar bai ganta ba har yaje toitel yayi wanka yazo ya kwanta, sai ta ƙaraso da sauri gareshi tace, "Hayat dan Allah ka taimakamin da ko ruwan tea ne wallahi yunwa nakeji?" tana faɗa kamar tayi kuka. Kallo ma bata isheshi ba bare tasa ran zai ƙarɓa mata magana. Data ga alamun bazata samuba dan haka ta zo ta kwanta. Bata jima da kwanciya ba ya fara jawota jikin sa yana wasa da ita son rashi, ita ko tunda taga abunda yake son yi da ita ta fara masa kuka tana faɗin, "dan Allah kayi haƙuri ka barni wallahi banda lafiya kuma yunwa nakeji". Yi yayi kamar bai jita ba haka yayi yadda yake so da ita kafin ya barta. Sosai tayi kuka a wannan daren dan iya wahala ta wahala dan har ƙaramin suma sai da tayi, kuma tundaga lokacin bata koma barci ba har gari ya waye....... *#Vote* *Comment* *Shere* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~Wattpad ~Summy M Na'ige~ *SHAFI NA 9📑* *__________📖* Bayan ta idar da sallah asuba tajima kafin ta ta shi sabida ko da ta tashi faɗuwa zatayi dan bata da wani kuzari a jikin ta. Tana kan sallaya ya tashi ya je ya yi wanka kana ya yi sallah, bearkfast yaje ya karɓo musu,yana dawo ya kai duban shi gareta kaifin ya yi mata magana ita tafara gaisheshi ciki da ladabi. bai ma karɓa ba yace, "kizo kiyi bearkfast dan yanzu na keson mu kama hanya kuma idan ki ka tsaya wasa sai na barka". yana faɗa yana antaya mata harara. Ahankali ta tashi kayan da yanuna mata na beark su ta ɗauka ta haɗa tea ta farashi,sosai taci kayan da ya kawo mata,sai da taji ta ƙoshi kana ta tashi taje toilte tayi wanka. tana cikin shiri sai gashi ya fito cikin shirinsa na tafiya,ko kallon ta baiyi ba ya kama hanyar fita. Ɗakin da taga yana ƙoƙarin rufewa yasa da sauri ta ɗauko kayan ta tafito waje ta karasa ya fa mayafin ta. Key ya kai ma masu hotel ɗin kana yazo ya ɓuɗe mota ya shiga itama tashi kana suka kama hanyar garin sokoto. Tafiya sukeyi amma ba wanda yace ma ɗan uwansa komai har sukayi nisa sosai. Wayar Hafsat ce tafara ruri dan haka ta ɗauko ta duba wake kiran ta. Safiyya taga ya bayyana dan haka taja tsaki kana ta ɗauka. Safiyya tace, "Hafsat kina ina wallahi yau zan koma gida kuma kin sa za su dame ni da tambayar ki dan Allah kidawo mutafi tare". Sai da ta kai ƙarshen zancin Hafsta tace, "wai Safiyya ke waci iri ce,nace kirabu dani kinƙi to bazanje gidan ba kije ki faɗa kinji kuma bari kiji kada ki saki kira na sabida ba ajiya ki ka bani ba ehe". tana gayamata haka ta tsinki kiran. Duk abunda takeyi yana kallon ta amma ya yi kamar bai san ta nayi ba. Haka suka cigaba da tafiya har suka shiga garin sokoto. Suna kawowa Flyover ya yi packing ďin motor sa yace, "ki sauka dan ni zan wuce". "Haba Hayat kayi haƙuri muje gidan ka idan na ɗan huta zuwa ajima sai naje gida". Wata tsawa ya daka mata wandda tasa tafice daga motar bata shiyar ba. Har zai tada motar tace,"Hayat bani da kuɗin da zan ƙarasa gida kuma bazan iya ƙarasawa da ƙafa ba gashi kuma dare ya yi". Ko kallon ta bayi ba yaja motar sa ya bar ta tsaye a hanya. Hawayen da kifita a idonta ta goge kana ta ɗau jikar ta tafara tafiya kan ti-ti. Mai napep ta tsayar dashi, ta faɗa masa sunan unguwar da zai kaita. Bai tsaya da ita ko ina ba sai ƙofar gidan su. Fita tayi tace dashi zata shiga ta karɓo masa kuɗi yace to. Sallam tayi ta shigo cikin gidan,aikuwa ƙannin ta najin muryar ta suka fara yimata oyoyo kamar za su kayar da ita gashi ba wani ƙarfin jiki ne da itaba. Da ƙyar tasamu suka sake ta,ita ko Mama tunda taji suna oyoyo ta san ƴar ɗiyar tace ta dawo dan haka da sauri tafito waje sabida ta ganta. Gaban tane ya yi muguwar faɗuwa lokacin da taga Hafsat,dan gabaki daya ta rame tayi fari sosai. Har zata tambaye su Mama sai suka haɗa ido da ita,murmushi Hafsat ta ƙaƙalo tace, "Mama ya nasameku?". Bata karɓa ba dan kallon ta takeyi sosai dan kamar tana son ta karantu wani abu,sai Hafsat ta katsa mata tunani tace, "Mama nafa tsayar da mai napep ban bashi kuɗi ba". Sai Mama tace, "dole na kifeki da ido wannan ubar ramar da fari da kikayi Hafsat, lafiya kike kuwa?". Tace, "Mama bari na sallame mai napep nazo". Tambayar ta kuɗin sa tayi ta faɗa mata sai Mama tabaiwa ƙaninta Ammar ya kai masa. Sai Mama tace, "kinyi tsaye ki ƙaraso daga ciki". Parlour Mama ta shiga ta zauna Mama tace,"Hafsat mike damunki ki ka yi wannan ramar haka?". Sai da ta ƙaƙalo murmushi tace, "Mama wahalar exams ce ta ramar dani" tana faɗa tana yin ƙasa da kanta. Sai Mama tace, "a'a Hafsat da alamu akwai ramar zazzaɓi aciki". Tace, "eh Mama dan jiya ma naje hospital suka rubutumin magani kin gama tagarda maganin" tana faɗan haka tana buɗe zip ɗin jikar ta ta ɗauko mata tagardar maganin da aka rubuta mata a can hospital ɗin da ya kaita dan cewa ya yi tunda bata yarda azubar da cikiba to ko magani ba zai saya ba. Ɗaukowa tayi taba Mama itako Mama takira Marwan tace yaje pharmacy ɗin Baban shi ya karɓo magani. Karɓa yayi yaje itako Mama tace Hafsat ta koma ɗakin ta tayi wanka tayi sallah t azo taci abinci ta sha magani. Tashi tayi taje ɗakin ta, tana shga kafin tayi komai wayar ta ta dauko ta fara kiran Anwar. Kusan missed call biyar tamasa amma bai ɗaga ba daga ƙarshe ma kashe wayar sa yayi gabaki ɗaya. Sai da taji ya kashi wayar kana ta tashi taje tayi wanka tayi sallah magarib da isha'i. Tana idar da sallah Marwan ya shigo ya kawo mata magani da abinci. Bayan ta ci abinci tasha magani ta koma ɗauko waya ta ƙara kira ko ya ɓuɗi?. Amma har yanzu kashe take,tunani tafarayi ko taje gidan sa dan gabaki ɗaya bata da natsuwa dan ita kanta tasan ko tana samun natsuwa sai ta ganshi,kuma tasan Mama baza ta barta tafita ba. Tana cikin wannan tunani barci ya fara ɗaukarta saboda maganin da tasha har da na barci akwai. Ko da babanta ya dawo daga masallaci har barci yayi awongaba da ita dan ko da Mama ta aiki Marwan ya kirata ta yi bacci sai Babanta yace ka da a tasheta abarta sai da safe sai su gaisa. Ko da gari ya waye Mama taje ɗakin ta dan ta kira ta, amma sai ta tarar har yanzu bacci takeyi bata tashi ba, abin ya ba Mama mamaki da taga har rana ta kusa fitowa Hafsat bata tashi ba sabod tasan ba halin taba ne baccin asubah. Tayar da ita ta farayi tana kiran Hafsat tashi kiyi sallah rana tayi, miƙa ta farayi alamun zata tashi Sai ta fara magana cikin muryar bacci tace, " Mama rana ta fara fitowa?". "Eh Ki tashi ga Abbanki can yana jiranki ku gaisa saboda yanzu fita zai yi,Tashi tayi ta nufi toilat Cikin hanzari tayi wanka sannan ta daura Arwala. Ita ko Mama tana ganin ta tashi ta shiga toilat sai ta fice daga dakin Koda tafito bata tarar da Mama ba dan haka ta gabatar da sallah kana ta shirya tafito taje ta gaishe da Abbanta. Da sallama ta shiga parlour,bayan sun ƙarɓa mata ta ƙaraso gaban Abban nata wanda tun shigowar ta yake kallon ta ciki da so da ƙaunar ƴar tasa. Bayan ta gaisheshi ya karɓa kana yace, "Hafsat ashe har ciyo kikayi?Allah ya ƙara sauki kuma kiri ƙa shan magani muga kwana biyu abunda Allah zaiyi". Ya ƙara da faɗin "ya exmas da fatar kun kammala lafiya?". Tace, "eh Abba mungama sai dai muna baran addu'ar samun nasara". Sosai ya yi musu addu'ar samun nasara ita da Safiyya kana ya yi musu sallama yafita wajan aiki. ********* Bayan kwana biyu da dawowar ta tasamu sauƙi sosai dan har cikowa ta farayi ba kamar lokacin da tadawo ba. Kuma tundaga ranar da ya sauke ta bai saki nemanta ba kuma bai saki ɗaukar wayar taba dan ko takira ba zai ɗauka ba shiyasa gabiki ɗaya bata cikin natsuwa dan yanzu burin ta taganta tari dashi dan haka taje tagayawa Mama zataje gidan ƙawar ta ta dubata sabida batada lafiya,da kyar tasamu Mama tabarta amma tace kada tajima. Wanka tayi ta shirya cikin wata koriyar atamfa ɗikin rika da sikt ne sosai suka karɓe ta tayi kyau abunta har ta ɗauko turare tasa jikinta sai ta tuna Mama bazata barta tafitaba idan tasa shi ba, dan haka ta saka shi ajika ta har sai tazo gidan sa haɗi da wani mitsi-tsin gyale. Babban hijab tasaka ajikin ta kana ta fito tanufe ɗakin Mama. Da Sallama tashiga tace, "Mama zan tafi". Kuɗi napep Mama tabata haɗi da ƙara faɗamta karta jima. Karɓa tayi haɗi da faɗi, "bazan jimaba". kana taficewar ta. Tana fita ti-ti ta tsayar da napep,sunan unguwar da zai kata tagaya masa, shiga tayi yaja suka tafi. Basu tsaya ko inaba sai bakin gidan sa. Bayan ta sallame mai napep ta ƙaraso bakin gate ɗin gidan ta fara knocking,bata jima tana knocking ba maigadi ya leƙo yaga wanene?aikuwa yana ganin ta ya yi sauri ya buɗe mata ƙofa haɗi da gaisheta. bayan ta ƙarɓa take tambayar sa ko Anwar nanan?. Yace "eh yana ciki". Part ɗinsa ta ƙarasa , kafin ta isa ga part ɗinsa ta buɗe jikarta ta ɗauko turare tafeshi jikinta dashi kana taciri hijab ta sanya wannan mitsi-tsin gyale wanda dashi da babu duk ɗaya. Ƙofar da zata sadata da falon shi tashiga kai tsaya. Ahankali take tafi har takawo gab dashi yana zaune yana kallon labaru bai masan ta shigo ba. Ƙamshin turarin da ya bige hancin sane yasa ya dago kansa, aikuwa suna haɗa ido dashi ta fara sakar masa murmushi mai ciki da nuna tsan-tsar so da ƙauna. Har yaso ya ƙoreta amma yadda yaga ta ƙara kyau kuma ga ko ina nata ya ciko musammam abunda ya keso wato dukiyar fulani. Irin kallon da yake matane yasa tafara tafiya ɗaya-ɗaya har ta ƙaraso gareshi. Ahankali tazo ta zauna saman cinyarsa haɗi da kai masa kiss abaki tare da faďin,"I miss you so much My Hayat nah". Aikuwa yana jin bakinta cikin nashi lokaci ďaya yaji wata Sha'awa tabi jirumasa bai san lokaci da yafara kissing ďinta ba cikin zafin nama. Hannunsa yasa cikin rikar ta yafara shafar duk wani ilahirin jikin ta,musammam abu son shi sosai yake matsar su itako sai ƙara narke masa takeyi ajiki tana wani nishi ɗaya-ɗaya. Cak ya ɗauke ta ya yi bedroom ɗinshi da ita,kayan jikin ta yacire mata kana yacire nasa romance ɗin ta yafara

Chapter 3 of 13