Share this page
1 / 9
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 👑🗡️ MASARAUTAR KAIZUR 👑 🗡️ ✍️Alƙalamin Nusaiba Ibraheem Rimi (Nusy bee) ❤️ Young talented writers association YOTA ❤️ (Under YOTA'S AMAZING PENS) Marubuciyar 👇 Matar khalees Barrister Hibba Siraɗin uƙuba Ƙaddararmu ce ta zo a haka And now; MASARAUTAR KAIZUR بسم الله الرحمن الرحيم Littafin MASARAUTAR KAIZUR ƙagaggen labari ne,komai da ke cikin littafin nan ƙirƙira ne,kama daga mutane,labari zuwa gari,ko da wani abu ya yi karo da rayuwar wani a zahiri,to a yi min afuwa,a rashin sani ne🙏 GARGAƊI!!! Labarin MASARAUTAR KAIZUR mallakin Nusaiba Ibraheem Rimi (Nusy bee)ne,ban amince a canja labari ko a juya min ta wata fuskar ba sai da izinina Ban amince a karanta min shi a YouTube channel ba sai da izinina SADAUKARWA; Na sadaukar da wannan littafin ga shugaba,ƙawa,kuma ƴar uwa Zainab Shehu Abdullahi (Zee kumurya) alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke bright pens 🥰 Da fatan mun yi Sallah lafiya 🥰 Allah ya karɓi ibadunmu, yasa muna daga cikin ƴantattun bayi a wata mai alfarma 🙏 Daga jiya zuwa yau na samu mutane da yawa da suka yi min tuni,(Nusy bee gobe ne fa😁yau ne da😊 I really appreciate it😍na ji daɗi sosai da kulawarku a gare ni,kuma ina matuƙar godiya, Allah ya bar zumunci 🙏 CHAPTER ONE *TSOKACI* *DAULAR KAIZUR* "Ya'aƙub! ya'aƙub ka tashi!! masarauta babu lafiya,muna cikin masifa da bala'i"da sauri wanda aka kira da ya'aƙub ya ɗago yana kallon mai yi masa magana,a kiɗime ya ce"me yake faruwa ne Zayyad?" "Ba'a ga YARIMA SAHAL ba,ana kyautata zaton sace shi aka yi aka fitar da shi daga masarautar nan,sarki Mu'iz da sarauniya Amna tuntuni sun fito bakin fada,gaba ɗaya kowa hankalinshi a tashe yake" Shiru Ya'aƙub ya yi yana bin Zayyad da kallo cikin kaɗuwa,an sace Yarima Sahal!magajin masarautar Kaizur,wannan wanne kalar ibtila'i ne ya afka musu haka?don tabbas ya san ba'a ci banza ba,don sarki Mu'iz baya yafiya Jiki a matuƙar mace Ya'aƙub ya dubi Zayyad ya ce"to ina su Umayr da Urwa da suke kula da shi?" "Umayr ya tsere,amma an kama Urwa,sai dai yana ta rantsuwa daga shi har Umayr basu da laifi,ba su san yadda hakan ya kasance ba,sarki dai ya ce a wuce da shi da sauran yaranshi a bincike su "Ya'aƙub bai sake magana ba ya miƙe yana gyara zaman tufafinshi,ya nufi hanyar fita daga ɗakin nasu, Zayyad ya biyo shi jiki yana tsuma A bakin fada ya ga jama'a sun taru,a nutse ya ƙarasa cikin mutane kanshi a ƙasa, Kamar yadda ya san al'adar masarautar,idan har Sarki yana magana ba'a kallonshi Bayanan Sarki sun firgita mutane matuƙa,sarki Mu'iz ya juya ya koma cikin fadarshi ba tare da ya saurari uzurin kowa ba, gimbiya Amna da ke tare da shi ta rufa masa baya Cikin saɓulewar jiki kowa ya fara zarewa da ɗaiɗai da ɗaiɗai bisa umarnin babban hadimin Sarki,wanda shima a take ya juya ya bar wajen,mutane suka fara watsewa suna ƙusƙus,kowa yana mamakin dalilin da ya sa aka sace ɗan Sarki Mu'iz, da hanyar da aka bi duk da tsauraran tsaro da ke masarautar Shima Ya'aƙub wucewa sashen su ya yi zuciyarshi cike da fargaba kamar kowa,da tsananin mamakin wanda ya aikata wannan ɗanyen aikin cikin wannan talatainin daren 💫 Da tsananin gudu dawakansu suke keta manyan dazukan masu cike da ababen tsoro da matsananciyar duhuwa,su uku ne, dukkansu sanye suke da baƙaƙen kaya,hatta fuskarsu rufe take da baƙin fuske,ɗaya daga cikinsu ne yake riƙe da wani ɗan ƙaramin buhu wanda da alamu akwai abu mai ɗan girma a ciki Sai daf da asuba suka iso masarautar Jasus,na gabansu,wato wanda yake ɗauke da buhun nan ne ya fara jan linzamin dokinshi don tsayawa,hakan ya sa sauran ma suka tsaya Juyowa ya yi yana kallonsu,cikin dakakkiyar muryarshi irin ta gwarazan mazan fama ya fara magana "Nan da kowanne lokaci daga yanzu asuba zata iya yi,hakan kuma yana nufin fitowar mutanen cikin garin JASUS don yin Sallah,kuma idan muka shiga da wannan kayan ina da tabbacin asirinmu zai iya tonuwa, kun san dai yadda MASARAUTAR KAIZUR take,to masarautar Jasus sun fi mu Su bala'i,don haka za mu yar da shi a nan kawai,akwai muggan namun daji, cikin ɗan lokaci ƙalilan za su iya gamawa da shi,amma ya kuka ce?" Na farkon ya ce"ah!hakan ya yi sosai,babu matsala,mu aiwatar da hakan"babu musu suka jefar da buhun,shugaban yana kallonshi yana murmushi ya ce"to Magaji! Sai na ce sai haɗuwa ta gaba?"ya kaɗa linzamin dokinshi,sauran ma suka kaɗa nasu,suka canja hanya BAYAN SHEKARU ASHIRIN *DAULAR TAYYAR* Tun daga nesa dakarun da ke tsaron babbar ƙofar shiga alƙaryar Tayyar suke jin kaɗe-kaɗe da bushe bushe,wanda hakan alamu ne na nasarar yaƙin da suka fita zuwa gawurtacciyar daular matsafa,kuma azzalumai wato daular BARUDA,inda Sarkin wannan daula,kuma gagarumin matsafi wato SARKI AKAAL yake mulki Tsawon shekaru goma sha ɗaya kenan suna ƙoƙarin yaƙar daular ta Baruda,amma hakan ya gagara, sakamakon tsananin ƙarfi da izza irin ta mayaƙa da matsafa a ƙasar,sun addabi manyan garuruwan da suke maƙwabtaka da su Farin ciki mai yawa ya bayyana a fuskokin dakarun nan,shugabansu,wanda ya kasance mai shela a yayin da mayaƙan suka fita yaƙi,a yayin da jama'ar gari suke dakon jin sautin busa cike da fargaba A yau dai sautin ya bambanta da wanda aka saba ji a duk lokacin da aka fita zuwa gagarumin yaƙi irin wannan, musamman da daular Baruda,a maimakon sautin kukan mikiya da ya saba tashi wanda yake nuni da ba'a yi nasara ba,yau sautin sarewa, wanda yake bayar da tabbacin nasara daga wannan gagarumin yaƙi shine ya tashi Cikin ɗan lokaci ƙanƙani garin ya kaure da sowa da farin ciki, kaɗe-kaɗe da bushe,tuni mata suka fara ɗora girke -girke da harhaɗa ababen sha na alfarma,hatta yara ƙanana cike suke da farin ciki Cikin lokaci ƙalilan mayaƙan da suka dawo daga yaƙin suka ƙaraso,an samu shahidai mutum ashirin da bakwai a cikin mayaƙa dubu uku da suka fita,sannan an samu ribar yaƙi har mutum hamsin da uku,ciki har da gawurtaccen mayaƙi,kuma matsafin nan wato KAZUZI Sanannen abu ne cewa duk wanda ya yi karo da shi sai dai ya amsa sunan gawa, saboda tsananin ƙarfi da tsafi da yake da shi Kazuzi shi kaɗai ya tarwatsa runduna guda da suka tunkari Baruda da yaƙi a lokaci ɗaya,a kowanne lokaci kazuzi a shirye yake don yaƙi,duk girman runduna da ƙarfin mayaƙa ba sa ba shi tsoro,an taɓa ƙarar da rundunar Baruda,amma shi ɗaya ya yi nasarar yaƙin ya gama da rundunar abokan hamayya ya gurfanar da sarkinsu a gaban sarki Akaal Kai tsaye aka gabato da dakarun yaƙi guda hamsin da biyu da aka kama waɗanda aka ɗaure su da wata doguwar igiya ɗaya a bayan ɗaya, jama'ar gari sai ihun murna suke yi,kiɗa da busar da ake yi ta ƙaru,karo na farko kenan a tarihi da aka taɓa cin nasara akan daular Baruda a tsawon ƙarnin, kasancewarta daula mai tsananin ƙarfin jarumai da ƙarfin tsafi Kawunansu a ƙasa suke wucewa, mutanen gari da suka jeru suna kallonsu kowa da abin da yake faɗa cikin farin ciki, dakarun da suka shigar da su suka rufa musu baya,kai tsaye aka nufi ƙofar fadar masarautar Tayaar Daga nan keken doki na alfarma shigo,wanda yake ɗauke da mutane ashirin da bakwai da suka yi shahada a wannan yaƙin,kalamai na nuna tsantsar alhini suka fara tashi daga bakunan mutane,wasu kuma suna ƙarfafa gwiwa da kasancewar sun yi gagarumar nasarar da ba su taɓa yi ba a kowanne yaƙi, ballantana yaƙi a Daular Baruda Ƙaton toron giwar da ya fara shigowa cikin ƙasaita ne ya katse cecekucen mutane,wajen ya yi tsit tamkar ruwa ya cinye ilahirin dubban jama'ar da ke bakin fadar A saman toron giwar an ɗaure wani madaidaicin keji,wanda ake iya ganin mutumin da yake cikin kejin,amma ba'a iya ganin fuskarshi, sakamakon dogon gashin shi da ya sauka har kafaɗarshi,ya zubo ta gaban kanshi ya rufe fuskarshi, kasancewar ya sunkuyar da kanshi, hannayenshi da ƙafafunshi ɗaure suke da wata ƙatuwar sarƙa, irin wadda aka yi amfani da ita aka ɗaure kejin da yake ciki Babu wanda ya ƙara ƙwaƙwƙwaran motsi sai da toron giwar nan ya shige cikin daular Tayaar,daga nan mutane suka fara watsewa ɗaya bayan ɗaya,da yawansu a razane suke duk da tarin nasarar da suka yi, musamman waɗanda suka yi karo da shi suka san wanene ainihin KAZUZI Daga nan kuma kallo ya koma sama, maganganu suka rinƙa tashi na mamakin yadda kazuzi ya yarda ya shigo hannu, inda wasu suke ganin kawai nasara ce daga Allah,wasu kuma suke ganin lamɓo kawai ya yi, hakan wata dabarar yaƙi ce don ya cimma nasara akan abokan gaba, saboda sanannen abu ne a wajen duk wanda ya san wanene kazuzi,baya taɓa yarda a yi nasara akan shi Cikin ɗan ƙankanin lokaci mai shela ya fara yekuwar sanar da al'ummar garin kiran da Sarki yake yiwa ilahirin al'ummar garin bakin fada,don a sallaci shahidan da suka riga mu gidan gaskiya a yaƙin nan,sannan kuma zai yi muhimmiyar sanarwa,da haka kowa ya wuce gida don shirya amsa kiran sarki *DAULAR KAIZUR* Kamar yadda aka saba Rabee'a ne ya ja sallar azahar da aka yi a farkon mukhtarinta,kamar yadda sarki Mu'iz ya ba da umarni,yau gaba ɗaya masarautar a firgice take saboda yadda yanayin da sarki Mu'iz ya tashi da shi, kaɗan daga aikinshi ne ya huce ta hanyar raba wani da ranshi Kai tsaye turakarshi ya wuce bayan an idar da sallar azahar,kallo ɗaya za'a yi masa a gano tsananin tashin hankalin da yake ciki saboda yadda fuskarshi ta kaɗa ta yi jawur Da sallama sarauniya Amna ta shiga turakar, ba tare da ya waigo ya kalle ta ba ya ce"da wani abu ne sarauniya?" Cikin girmamawa ta ce"dama batun abinci ne ya shugabana! An gama haɗawa,a kawo ne?"ba tare da ya kalle ta ba ya ce "ba yanzu ba,za ki iya tafiya"ta sake rissinawa ta ce"ka huta lafiya ya shugaba na"ta miƙe don ficewa daga ɗakin "Ki cewa yarima Zaffar ya shigo,ina son magana da shi"ta tsinkayi muryarshi Sake rissinawa ta yi ta ce"an gama ya shugaba na"sannan ta nufi ficewa daga cikin ƙasaitacciyar turakar A ƙaton katafaren masaukin baƙin da ke cikin gidan ta tarar da Yarima Zaffar da Yarima Jamal a zaune suna jiran fitowarta,ita kam zuwa yanzu ta daina mamakin duk abin da sarki Mu'iz ya yi, yadda yake ganewa a duk lokacin da Yarima Zaffar yake kusa da shi saboda tsananin ƙauna da soyayyar junansu Kallonshi ta yi tana murmushi,ya rissina tana faɗin "Barka da fitowa ya shugaba ta!" "Zaffar! Yanzu mai martaba kuwa ya ce na yi masa magana da kai,ashe dai kana kusa,wannan ƙauna tsakanin ka da mai martaba dabam take" Murmushi yarima Zaffar ya yi, cikin girmamawa ya sake kallonta ya ce"ranki ya daɗe ai tasirin jini ne kawai, kin san an ce jini ya fi ruwa kauri" Sarauniya Amna ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce"haka ne! To yanzu dai ka amsa kira, don kamar ma baya cikin yanayi mai daɗi" "An gama ranki ya daɗe,ki huta lafiya"ya faɗa da girmamawa kamar koda yaushe,sannan ya miƙe ya nufi turakar Sarki Mu'iz Yarima Jamal ya bi shi da kallo cikin takaici,a yayin da sarauniya Amna ta yi tafiyarta ta bar shi a wajen,ya miƙe tsaye cikin ɓacin rai,a ranshi yana jin dole ma ya karɓi kujerar daular kaizur bayan wucewar Sarki Mu'iz zuwa kushewa duk da kasancewar Yarima Zaffar ya girme shi,da wannan tunanin ya bar wajen zuciyarshi cike da baƙin ciki,da muradai kala-kala Sarki Mu'iz ya yi masa iso daga inda yake kishingiɗe a kwance akan ƙawatacciyar kilishin da ke shimfiɗe a tsakar ɗakin, Yarima Zaffar ya ƙaraso ya rissina a gabanshi yana faɗin"Barka da wannan lokaci ya shugaba na" Kallonshi sarki Mu'iz ya yi, lokaci guda ya miƙe tsaye,ya dubi yarima Zaffar ya ce"mu je Yarima!"ba tare da musu ba Yarima Zaffar ya miƙe,kai tsaye suka nufi wata kusurwa a cikin turakar Kamar ba a cikin dakin sarautar ba,wajen da duhu sosai,sarki Mu'iz ya saka hannu ya taɓa wani abu da shi kanshi Yarima Zaffar ɗin bai san da shi ba,take wata ƙofar sirri ta buɗe,sai ga wani madaidaicin ɗaki ya bayyana Ba yau Yarima Zaffar ya saba ganin ɗakin ba,shi yasa ya zama sanannen abu a wajenshi cewa duk lokacin da sarki Mu'iz yake cikin wani yanayi mara daɗi to yana da alaƙa da wannan ɗakin Cikin rauni da sarewa sarki Mu'iz ya dubi ƙanin nashi Yarima Zaffar ya ce "Zaffar! Ban san tsawon wanne lokaci zan ɗauka ina kuka da fargabar inda ɗana SAHAL yake ba Kai shaida ne,tsawon shekaru ashirin kenan da ɓatan shi,amma ban ga wani canji daga taurarin shi ba,sai dai kewarshi da fargabar halin da kujerar kaizur zata shiga idan na bar duniya A kullum ina ganin taurarin Sahal da haske tamkar walƙiya,amma a yau na ga abin da ya kaɗa hanji na" Yarima Zaffar ya kalle shi zuciyarshi cike da fargaba, saboda wannan bayanin da sarki Mu'iz ya ɗauko akwai dalili, cikin fargaba ya ce"menene yake faruwa da Yarima ya shugaba na?" *To jama'a ya kuka ji tafiyar MASARAUTAR KAIZUR?ba mu saba irin wannan tafiyar ba ko? tafiya ta musamman kenan,ku biyo ni kawai!!!* #Nusy_bee 08125952284 👑🗡️ MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑 ✍️Nusy bee ❤️ Young talented writers association YOTA ❤️ (Under YOTA'S AMAZING PENS) Page 2 Cikin jimami sarki Mu'iz ya kaɗa kanshi, lokaci guda kuma ya buɗe wani ɗan ƙaramin abu mai kama da akwati,take wasu taurari guda uku suka bayyana ƴan ƙanana,sai dai sun yi jawur da su Yarima Zaffar ya ɗan bi taurarin da kallo cikin fargaba,idan ya fahimta hakan na nuni da cewa Yarima Sahal yana cikin tsaka mai wuya kenan,to a wanne hali yake ciki?kuma a ina?kuma me ya same shi? A taƙaice ma dai a ina ya rayu tsawon waɗannan shekarun amma suka kasa gano shi duk irin yawon da suka yi? Kallon sarki Mu'iz ya yi wanda ya damuwa ta gama bayyanar masa a fuska, cikin sanyin murya ya ce"to yanzu shugaba na menene abin yi? Ya zamu yi?"sarki Mu'iz ya girgiza kai ya ce"nima bana ce ba,bana son sarauniya ta san da wannan batun,don ban san yadda zata yi ba,kullum ina gaya mata cewa ɗanta lafiya yake,amma a wannan karon ban san yadda zata ɗauki wannan maganar ba" Kai tsaye yarima Zaffar ya ce"kar ka gaya mata ya shugaba na,ina fatan in sha Allahu watan watarana Yarima zai dawo cikin masarauta,har ma ya karɓi ragamar da take jiranshi tsawon shekaru" Sarki Mu'iz ya dafa kafaɗar ƙanin nashi, cikin raunin murya ya ce"ina fata fatan haka ɗan'uwa" Jiki a saɓule suka fito daga cikin ɗakin,sarki Mu'iz ya sake kwanciya a turakar tashi,yayin da Yarima Zaffar ya fice daga turakar cike da jimamin wannan abu *DAULAR TAYAAR* lokaci ƙalilan baya,ƙasa da sa'a guda da aka sallaci gawarwakin waɗanda suka yi shahada a yaƙin da suka fita da daular Baruda,an raka su zuwa gidajen su na gaskiya cikin aminci, zuciyoyin masoya da yan'uwa cike da alhini da jimami,daga nan an dawo fada,don sauraren kiran sarki da jawabin da zai gabatar Ba'a ɗauki lokaci ba sarki IYAAD ya bayyana cikin shigar ta alfarma,fadawanshi da suke tare da shi suka nunawa mutane wajen zama,mutane suka zauna,fada ta yi shiru suna jiran abin da sarki Iyaad zai faɗa Tsawon wasu daƙiƙu ya ɗan yi shiru, kafin ya yi gyaran murya cike da salon izzar mulki,ya yi sallama cikin wani amo mai jan hankali,wanda yake tattare da mazantaka Gana ɗaya fadar aka amsa,cikin nutsuwa da kamala ya fara bayani "To alhamdulillahi! Bayan tsawon lokaci Allah mai kowa mai komai ya cika mana burin mu Kamar yadda muka sani Daular Baruda daula ce da ta ɗauki tsawon lokaci tana rainon azzaluman mayaƙa, waɗanda suke tarwatsa dukkan wani gari da suka gani da aminci Daular Baruda bata tsaya iyaka nan ba,tana yaƙi da Muslunci da musulmai, kusan na ce daula ce da aka yi amfani da zalunci da ƙarfin tsafi aka gina ta don a rusa musulunci To amma da yake Allah shine mai iko a bisa komai a yau ya ba mu iko mun durƙusa daular azzalumai ta Baruda"take ilahirin fadar ta ruɗe da kabbara da muryoyi mabanbanta,wasu har da kukan farin ciki Sarki Iyaad ya cigaba da bayani "bayan mun yi nasarar lalata wannan azzalumar daula,mun yi nasarar hallaka sarkinsu,da sarkin matsafan wannan daula,da duk wani badakare da ake amfani da shi ake cin nasara akan musulunci "take aka sake ruɗewa da kabbara,da ƙananun ƴan maganganu ƙasa-ƙasa da ke cike da farin cikin faɗar ra'ayi,sai da aka nutsa sarki Iyaad ya ɗora da bayaninshi "Nasararmu bata tsaya anan ba,har sai da muka kama babban badakaren da ya mayar da yaƙi tamkar wasa,sadaukin da idan bai ɗauki rai ba baya jin daɗi,jarumin da kisa tamkar maƙon ruwa ne a wajenshi,wanda duk girman runduna bata ba shi tsoro,duk ƙarfin runduna baya razana shi, duk shiri da tumbatsar runduna a ɗan ƙankanin lokaci zai iya tarwatsa shi komai yawanshi,jarumin da yaƙi da ɗaukar rai tamkar wasan yara ne a wajenshi,wato Sadauki KAZUZI!" Ɗif fadar ta yi, tamkar babu wani mai numfashi a cikinta ba don komai ba sai don ambaton sunan kazuzi da sarki Iyaad ya yi, sarki Iyaad bai damu ba ya cigaba da jawabi "Don haka muna cike da murna da farin ciki na wannan Gagarumar nasarar, wadda muka tabbatar da cewa ba wayon mu ko ƙarfin mu bane ya bamu,sai iko da buwayar Ubangijin talikai,muna mai miƙa godiya a gare shi" Gaba ɗaya mutanen fadar suka ruɗe da kabbara,har da waɗanda suka firgita da wanzuwar Kazuzi a cikin Tayaar,sarki Iyaad bai damu ba,ya cigaba da jawabin farin ciki da suke ciki,a ƙarshe ya ƙara da faɗin"muna yi wa iyalan shahidanmu gaisuwa, musamman ma jarumi WALEED,wanda shine ya sauƙaƙa mana hanyar da muka samu nasara akan azzalumi Kazuzi,duk da cewar da kuskure a hakan A ƙarshe ina mai farin cikin sanar da ku cewa za'a yi babbar liyafa ta wannan nasarar da muka yi a bakin fada,zuwa gobe da hantsi,na sallami kowa" Haka taron fada ya tashi,mafi akasarin mutane suna cikin matuƙar farin ciki,yayin da wasu daga cikinsu suke cikin fargaba saboda wanzuwar Kazuzi a cikin Tayaar,wanda sanannen abu ne a wajen jama'ar garin,ba ma su ba,har da maƙwabtansu na yadda yake da haɗari 💫✨ Sarki Iyaad ya dubi wazirinsa da yake zaune kusa da shi,ya ce"waziri! Allah ya yi,mun yi nasara a yaƙin nan da daular Baruda,har ma mun kawar da damuwar da ta addabi gaba ɗayanmu, wato Kazuzi,yanzu ya kuke ganin za'a yi da shi?" Waziri ya ɗago kanshi a nutse, cikin girmamawa ya ce"ya shugaba na babu abin da ya rage sai a sake laƙana masa kalmar shahada,idan bai karɓa ba kawai a kashe shi kamar yadda aka yi wa sauran yan'uwan shi" Sarki Iyaad ya dubi sauran fadawan ya ce"to kun ji,ki me kuke gani?"Sarkin yaƙi ya girgiza kai ya ce"wannan ba mafita ba ce ya shugaba na Abu ne sananne a wajenmu cewa Kazuzi ba zai amshi addini a haka ba,kuma muna buƙatar mutane irin Kazuzi a wannan garin,ni da nake cewa mai zai hana mu ja shi a jiki,mu fahimtar da shi musulunci, idan ya so ba ma sai an yi masa dole ba zai shiga da kanshi?" Sarki ya jinjina kai ya sake mayar da dubanshi ga waziri, kafin ya kai ga magana sarkin fada ya ɗaga hannu,sarki Iyaad ya ba shi damar magana,Sarkin fada ya gyara zama yana duban Sarki Iyaad, cikin girmamawa ya ce"ya shugaba na,da alamu su Sarkin yaƙi sun manta wanene Kazuzi! Sanannen abu ne tabbas ba zai karɓi musulunci ba ko me za'a yi masa,amma kuma ina ganin da kuskure a jan shi a jiki da za'a yi, saboda mu shaida ne,babu abin da jinin Baruda suka tsana kamar musulunci,duk wani wanda ya sha ruwan daular Baruda zai tashi da tsanar Musulmai da burin son ganin bayanmu,mai zai hana a yanke masa hukuncin shi kawai,kar ya yi amfani da yardar da muka yi masa ya cutar da mu?" Girgiza kai sarkin yaƙi ya yi, cikin girmamawa ya ce"ya shugaba na,a dai duba magana ta,ban hana a sakawa kazuzi idanu ba,amma ya kamata a ba shi wata dama, tunda har muka iya kamo shi,abin da babu wata daula da ta taɓa samun wannan kwatankwacin nasarar,idan har ya gwada wata halayya muka ji ba mu yarda ba za mu ɗauki mataki akanshi kawai,amma a matsayin mu na musulmai,sannan manyan babbar masarauta bai kamata a ce mun razana saboda wani bawa da Allah ya ba mu nasara akan shi ba,amma ya kuka ce?" Shiru fadar ta ɗauka,kowa yana nazari,zuwa can waziri ya katse shirun da cewa"to shikenan,a gwada shawarar taku,amma ni ina ganin a saka masa idanu sosai,sannan kuma a tsare shi,a yi duk mai yiwuwa don ganin an karya ƙarfinshi,yadda ba zai iya wani tasiri ba" Sarki Iyaad ya ce"shiyasa muka bayar da umarnin a killace shi, kafin nan sai da muka tabbatar mun raba shi da duk kayan tsafi da surkullenshi" Waziri ya sake rissinawa ya ce"ya shugaba na,an ɗauki matakin da ya dace, ragowar kuma sai mu bar wa Allah " Sarki Iyaad ya ce"hakan ya yi,muna fatan yadda Allah ya ba mu ikon yin wannan jihadin muka yi nasara akan waɗannan azzalumai, Allah ya ba mu iko da nasara akan wannan babban shaiɗanin" Fadawa suka amsa da "Ameen!"daga nan sarki ya rufe taro da addu'a,faɗa ta watse 💫✨ A hankali toron giwar yake zaunawa akan ƙafafunshi bisa umarnin dakarun da suke umartarshi,shugabansu ya kama ƙatuwar sarƙar da aka ɗaure kejin ya fara ƙoƙarin kwancewa cikin dakiya,sauran dakarun suka fara ƙoƙarin taya shi Bayan gama warware ƙatuwar sarƙar tsayawa suka yi cirko-cirko suna kallon juna a ɗan firgice,duk jarumta da taurin zuciyar badakare ya san wanene Kazuzi, yanzu haka ma kallonshi suke yi, wanda shi duk abin da ake yi ko ɗago kai bai yi ba ballantana ya kalli wani,har yanzu kanshi a ƙasa yake,tunda aka shigo da shi cikin birnin Tayaar har yanzu babu wanda ya ga fuskarshi ballantana ya shaida a wanne

Chapter 1 of 9