Share this page
3 / 9
kanka a wata tsiya bayan duk wani alkadari naka ya karye? Ka yi faɗuwar baƙar tasa!daga yadda kake jin kanka a matsayin Sadauki zuwa bawa,bawan ma ƙasƙantacce?har yanzu kana jin kana da wani tasiri?"shiru ta yi tana jan numfashi a fusace,a yayin da ɗakin ya yi shiru kamar ruwa ya cinye su "Na ba ka nan da gobe da za'a sake jin ra'ayinka!ka amsa cewa ka musulunta,ko kuma ni da kaina na raba kanka da gangar jikinka!!! So nake ka ji cewa duk wata ji kima da iko da izza da ka nuna sun rushe, saboda a ƙarshe mace ce ta raba ranka da gangar jikinka!! Ya rage naka ka zaɓi izza ta halaka ka,ko ka saukar da kai,ka ɗauki hakan a matsayin gargaɗi na ƙarshe"tana kai wa nan ta miƙe a fusace tana take ƙafarshi,ta yi waje, suma sauran dakarun suka bi bayan ta Sai da ta fice daga cikin ɗakin Kazuzi ya buɗe lumsassun idanunshi yana bin hanyar da ta bi da kallo,bai taɓa jin zafin maganar da take gaya masa ba ko ya saka ta a rai ta dame shi,asalima tun daga sanda ya rasa wadda yake jin don ita yake rayuwa gaba ɗaya duniyar ta fice masa a rai,amma yana ganin zai yi maganin wannan yarinyar da take damunshi da hayaniya Ita kuwa gimbiya Hayat gargaɗi mai ƙarfi ta yiwa kuyanginta da dakaru akan su kiyayi sanar da mahaifinta abin da ta yi,don tsanar Kazuzi ce dai babu wanda zai iya hana ta yi,kuma muddin tana numfashi sai ta ga bayanshi, shiyasa bata fatan ya amshi musulunci ma Da yamma aka gudanar da gagarumar liyafa ta nasarar wannan gagarumin yaƙi,da addu'ar Allah ya haska zuciyar sadauki Kazuzi shima ya amshi musulunci Kamar yadda sauran dakarun Baruda da aka kama suka yi Ita dai gimbiya Hayat bata halarci taron ba,ta aika a gayawa sarki Iyaad cewa bata jin daɗi *DAULAR KAIZUR* "Barka da wannan lokaci ya shugaba na!" Ɗaga idanu sarki Mu'iz ya yi yana kallon sarauniya Amna da ta duƙar da kai ƙasa tana jiran amsa,a hankali ya furta "Barka da zuwa sarauniyar kaizur" Sauke numfashi ta yi tana gyara zama a gabanshi,daga yadda ya ga fuskarta ya tabbatar da cewa akwai damuwa, cikin kwantar da murya ya ce"da wani abu ne sarauniya?" Jan numfashi ta yi, lokaci guda rauninta ya bayyana, cikin rawar murya ta ce"na yi mafarki da Yariman kaizur ne ranka ya daɗe! Haƙiƙa yarima yana cikin wani hali mai wuyar fassarawa" Gaban sarki Mu'iz ya buga,dama ya yi tunanin hakan zata faru,a duk lokacin da wani mummunan abu zai samu yarima Sahal sai sarauniya ta ji a jikinta ko ta gani a mafarkinta,hakan kuma yana tasiri sosai a gare ta Cikin kwantar da murya ya ce "baya cikin kowanne hali sai alkhairi da izinin Allah Nima na yi mafarki da shi yana cikin kyakykyawan yanayi,har ma ya sanar da ni a tsammaci dawowarshi nan kusa zuwa sarautar shi in sha Allah " Murmushi sarauniya Amna ta yi, hawaye suka cika idanunta, cikin sanyin murya ta ce"kwantar min da hankali kake yi ya shugaba na? Hankalina ba zai iya kwanciya ba har sanda zan ga yarima na ya dawo cikin masarautar nan, ka san yadda nake ji,ina jin zafin cin amanar da aka yi min aka fitar da Yarima daga cikin masarautar nan"zuwa yanzu kuka take yi sosai Dafa kafaɗarta Sarki Mu'iz ya yi, cikin ban baki da lallashi ya fara magana "kowacce rayuwa ta ɗan adam akwai jarrabawa,ki ƙaddara haka tamu jarrabawar take, shekaru ashirin kenan da ɓatan yarima Sahal,a tsawon waɗannan shekarun ban taɓa fitar da rai cewa zai dawo gare ni ba, Na hukunta dukkan masu laifi,na yanke hukuncin kisa ga waɗanda na kama dumu dumu da aikata laifin,amma hakan bai bayyana min yarima ba,dole na bar wa Allah komai,damuwa da tashin hankali babu abin da za su ƙara yi sai dagula lissafi Babu abin da nake tunawa na yi baƙin ciki irin waccan baƙar azzalumar"sarauniya Amna ta ɗago kai a sanyaye ta ce"wacce azzalumar?" "Wadda take amsar hukunci tsawon shekaru ashirin,amma har yanzu babu abin da ya sauya zani" Sauke numfashi sarauniya ta yi,a hankali ta ce"Ni kuma sai nake ganin kamar babu laifinta, saboda dole zata yi raunin da ba zata iya hakan ba" Girgiza kai sarki Mu'iz ya yi, ya ce"ta amsa da bakinta cewa ita ce,amma a yadda na fuskanta akwai waɗanda suka saka ta,su nake so na sani kafin na yanke hukuncin " Gimbiya Amna ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce"fatan nasara ya shugaba na, Allah ya durƙusar da maƙiyanka ya ƙasƙantar da su a gabanka " Sarki Mu'iz ya yi murmushin bayar da ƙwarin gwiwa, sarauniya Amna ta rissina ta ce"na bar ka Lafiya ya shugaba na"daga haka ta miƙe cikin nutsuwarta ta fice daga ɗakin,bayan sarki ya sallame ta *Ga masu sha'awar VIP group an buɗe,ku tuntuɓe ni a number ta gata nan a ƙasa* #Nusy_bee 08125952284 👑🗡️ MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑 ✍️Nusy bee ❤️ Young talented writers association YOTA ❤️ (Under YOTA'S AMAZING PENS) Page 6 Tana daf da sauke takobin a tsakiyar kan Kazuzi,wanda yake zaune kawai ba tare ya yi wani yunƙuri don kare kanshi ba,kuma har yanzu ko kallon sashen da take bai yi ba,kawai ta ji an riƙe hannunta ƙam A hargitse ta juya don ganin wanene ya yi mata wannan shishshigin,da tsananin mamaki da kaɗuwa take kallon mahaifinta sarki Iyaad da fuskarsa take a matuƙar haɗe tamkar hadarin da ya gangamo yake daf da fara zubar da ruwa, ba tare da ya yi magana ba ya fincike ta, bai yi wata-wata ba ya ɗaga hannu da niyyar sauke mata mari,amma ya ji an riƙe masa hannun Da tsananin mamaki ya ɗago yana kallon Kazuzi da ya riƙe masa hannun,ba shi ba ma,duka ilahirin dakarun da kuyangin da ke tsaye kallon Kazuzi suke yi da tsananin mamaki,ya durƙusa a gaban sarki Iyaad yana faɗin "Ka gafarce ni ya shugaba na!mace ce,duk inda mace take ana son a ɗaga mata ƙafa saboda rauninsu"ya faɗa kanshi a ƙasa A hankali sarki Iyaad ya sauke hannunshi,a wani irin fusace Hayat ta ce"ina ruwanka da abin da ya shafe ni da abbana? Me ya kai ka shiga tsakani na da uba na tunda kai ka yi silar barin mahaifiya ta duniya? Kai musiba ne,kuma ibtila'i ga rayuwa ta! menene dalilin da ya sa za ka rinƙa shiga abun da babu ruwan ka?zindiƙi kafiri azzalumi?? menene......" "Hayat!!!"sarki Iyaad ya daka mata tsawa,ta kalle shi da rinannun idanunta,sannan ta sake mayar da hankalinta ga Kazuzi da kanshi yake ƙasa har yanzu,babu alamun ya san abin da take cewa a kan fuskarshi,bata damu ba ta cigaba da faɗin "karo na farko kenan da mahaifina ya ɗaga hannu da zummar duka na, karo na farko kenan da mahaifina ya daka min tsawa,kuma duka a gaban hadimai na!!! Saboda kai,kai dai,na yi maka alƙawarin sai na wulaƙanta rayuwarka,tabbas hakan ba zai tafi a banza ba"tana kai wa nan ta juya ta fice daga ɗakin tana hawaye,hadimanta suka rufa mata baya,sarki Iyaad ya bi ta da kallo yana ɗan murmushi Shima bai sake magana ba ya juya ya fice daga ɗakin,ragowar dakarun da suke tsaye a ɗakin suka bi bayanshi, suka bar Kazuzi a zaune kanshi a ƙasa Kai tsaye ɗakinta ta shige bayan ta kori kuyanginta,ta faɗa kan gadonta tana kuka sosai,bata taɓa jin ta tsani wani mahaluki a rayuwarta ba kwatankwacin yadda take jin tsanar sadauki Kazuzi,kuma alƙawari ta ɗaukarwa kanta tabbas sai ta ga bayanshi Tana ta kuka bata san da shigowar sarki Iyaad ba ma,sai da ya sanya hannu ya ɗago ta,tana kuka sosai,ya zaunar da ita yana magana cikin taushin murya "Allah ya huci zuciyar gimbiyar Tayaar, albarka kuma alfaharin Tayaar,kuma jinin sarki Iyaad,ki yi haƙuri ki daina kukan nan,za muyi magana" Ba tare da ta tanka ba ta kama goge hawayenta,sai da ta goge hawayen sannan ta kalli sarki Iyaad cikin raunin murya ta ce"Abby na tsane shi tsana mafi muni Menene dalilin da ya sa tunda ya shigo cikin Tayaar na daina farin ciki ne? Abby ka yanke masa hukunci, idan ba za ka yanke masa hukunci ba ka kore shi ya bar garin nan,na tsane shi,na tsani ganinshi,bana ƙaunar na tuna cewa akwai wata halitta da ta wanzu a cikin masarautar Tayaar wadda take amsa sunan Kazuzi" Murmushi sosai sarki Iyaad ya yi yana riƙo hannunta,a ranshi yana sake yarda da maganar Kazuzi da yake cewa mata suna da raunin da ya cancanci a ɗaga musu ƙafa saboda shi,ya ce"tashi mu yi magana ƴata" Babu musu ta tashi zaune tana goge idanu,sarki Iyaad ya dube ta sosai ya ce"yanzu wacce shawara gare ki da kike ganin za'a yiwa Kazuzi? Kar ki manta daular Tayaar a duk nahiyar nan babu wani gari wanda yake faɗa da zalunci irin namu, alhamdulillahi kuma muna yin nasara Ba mu kawo Kazuzi cikin daular Tayaar ba sai don mu cusa masa sha'awar musulunci, tunda kamar yadda muka sani musulunci ba'a yin shi da dole,kuma ko da ana yinshi da dole har yanzu Kazuzi bai yi lalacewar da za'a saka shi yin abu da ƙarfi ba Amma ke menene shawararki?" Kallonshi ta yi, cikin raunin murya ta ce "Abby ya nuna baya ra'ayi, meyasa ba za ku ƙyale shi ba?" Murmushi sarki Iyaad ya yi,sannan ya sake dubanta ya ce"kina da labarin Sarkin yaƙi da ya rasu,wato Sadauki Ilyas?" Take fuskarta ta washe da murmushi, idanunta akan shi ta ce"na sanshi, idan ban manta ba da ni da yaya na Yarima Nashwaar ya ɗauke mu a matsayin jikokinsa,yana matuƙar kula da mu a wancan lokacin Na sani shi ma mun rasa shi a wani yaƙin da Tayaar ta gwabza da Baruda "ta ƙarashe fuskarta tana nuna alhini Sarki Iyaad ya ce"to shi wannan bawan Allan da kika sani mahaifina a ribar yaƙi ya samo shi kamar yadda aka samo Kazuzi,babban mayaƙi ne,kuma fitaccen jarumi a daularsu kamar dai Kazuzi,amma da babana sarki Nufail ya yi duk mai yiyuwa sai gashi an samu abin da ba'a yi tunani ba,bayan kasancewarshi Musulmi mai ibada a kowanne lokaci ya kasance shine mai jagorantar yaƙi,kin san menene ya janyo mana nasara a wancan lokacin?"ba tare da ta yi magana ta girgiza kai a hankali Sarki Iyaad ya ce"to jimirin jira ne,don sai da Sarkin yaƙi Ilyas ya shekara bakwai da mu yana bin addinin shi na bautar wuta,a wancan lokacin mahaifina ya fuskanci ƙalubale da dama,ya jure maganganu daga wajen mutane,amma sai gashi rana tsaka burin shi ya cika,sadaukin ya karɓi musulunci,har ma ya ja Sallah a masallaci,shin ni ba kya son na kafa wannan tarihin ne?" Cikin sanyin jiki ta girgiza kai,sarki Iyaad ya ce"to ki ɗauki Kazuzi a matsayin da kike ɗaukar kuyangin ki da dakarun da suke tsaron lafiyarki, yadda kika mayar da su aminanki,masoyanki,makusantanki haka nake so ki mayar da Kazuzi,in sha Allah lokaci yana zuwa da za mu samu nasarar canja masa ra'ayi kamar yadda muka chanjawa sadauki Ilyas" Rissinawa ta yi tana faɗin "fatan nasara mai ɗorewa Abby!" Sarki Iyaad ya yi ɗan murmushi yana faɗin"fatan rayuwa mai albarka da ma'ana yata "daga nan ya juya da niyyar ficewa daga ɗakin Gimbiya Hayat ta bi shi da kallo,ta gamsu da maganarshi,amma tabbas sai ta hukunta Kazuzi ko yaya ne, musamman da ya janyo Abby ɗinta abin alfaharinta ya ɗaga hannu da niyyar marinta *DAULAR KAIZUR* "Ya shugaba ta!mai martaba ne ya ce a yi masa iso" Ɗaga kai gimbiya Amna ta yi tana kallon jakadiya da kanta yake a ƙasa,ta ce"ki yi masa iso Nayyab"Nayyab ta sake rissinawa sannan ta miƙe ta fice daga turakar Bayan ƴan daƙiƙu sarki Mu'iz ya shigo da sallama, sarauniya Amna ta rissinar da kai ta amsa,ya ƙaraso ya zauna kusa da ita, cikin girmamawa ta ce"Barka da zuwa ya shugaba na" "Barkanki da warhaka sarauniyar Kaizur!" "Jakadiya ta ce ayi maka iso" Sauke ajiyar zuciya mai nauyi ya yi cikin damuwa,ta ɗaga kai tana kallonshi,a hankali ya furta"na kasa jurewa ne,dole na taho mu yi magana" "Kan batun yarima Sahal?"ta faɗa a raunane tana kallonshi Shiru ya yi kanshi a ƙasa,ta yi ɗan murmushi mai ciwo tana girgiza kai ta ce"tunda na ji a jikina a kwanannan,na yi mafarkai da yawa,ga yawan faɗuwar gaba na san ɗana ya faɗa mugun hannu,zuwa yanzu na san na rasa Yarima na"zuwa lokacin sosai take kuka Girgiza kai sarki Mu'iz ya yi da sauri,ya ce"wannan hasashe ne kawai sarauniya,ina cikin damuwa ne kawai saboda tsawon lokacin da muka ɗauka muna neman shi amma har yanzu babu labari,na yi duk mai yiyuwa amma babu nasara Yarima Sahal yana raye,shine kawai tabbacin da nake da shi,amma banda haka da tuni na haƙura,komai na bawa muƙaddari ne" Sarauniya Amna ta jinjina kai ta ce"haka ne mai martaba Amma idan da hali ina so mu gana da Munaya, wataƙila mu samu wani haske " Sarki Mu'iz ya girgiza kai ya ce"babu Abin da ganawa da Munaya zata haifar sai damuwa,da alamu waɗanda suka saka ta aikin sun shirya, shiyasa ita ma ta shirya,sam bata tsoron ko da mutuwa, shiyasa bana son abin da zai haɗa ni da ita yanzu" Girgiza kai sarauniya ta yi,ta ce"kar mu yi haka, abu ne na ribar mu,idan yarima Sahal ya salwanta mu ne muka shiga matsala,idan ya bayyana amfanin mu ne,mu je mu tattauna da ita,ina fatan zata yarda ta ba mu ƙarin haske" Girgiza kai sarki Mu'iz ya yi,ya ce"mu je,amma bana jin hakan gaskiya, amma ni na riga na yanke hukunci,ba zata ƙara shekara ɗaya a ɗaure ba,zata baƙunci inda su Umayr da Ya'aƙub suka je"bata yi magana ba sai jinjina kai,sarki Mu'iz ya miƙe tsaye, itama ta miƙe suka fice daga turakar *DAULAR TAYAAR* "Barka da warhaka ya shugaba ta" Kallonshi ta yi sosai, kafin ta fara magana a dake"ribatattun yaƙi da aka kamo daga Baruda,an raba musu wajen aiki ne?" Dakare Amjad ya ce"tukunna dai ya shugaba ta,amma yau in sha Allah za'a raba musu" Sauke ajiyar zuciya ta yi,kai tsaye ta ce"to wannan zindiƙin badakaren,ina so a saka shi cikin jerin masu yi min hidima " A firgice shugaban dakaru Amjad ya kalle ta,a ɗan tsorace ya ce"ranki ya daɗe babu kasada a cikin hakan?" "Umarni na bayar,bana buƙatar a tambaye ni,saura kuma ka kai ni gaba,tashi ka fice,na sallame ka "babu musu shugaban dakaru ya rissina sannan ya miƙe ya fice daga lambun nata cikin zullumi da fargaba Har yanzu sadauki Kazuzi abin tsoro ne, ba'a gama sanin wanene shi ba,ta yaya ita mace mai rauni ta ce wai a saka Kazuzi ya yi mata hidima?shi dai yana ganin da kuskure a hakan Hakan ne ya saka ya yi fatali da umarninta,bai yi ƙasa a gwiwa ba ya samu Sarkin yaƙi da maganar Murmushi sarkin yaƙi ya yi,a ranshi yana fatan abin da yake gani ya tabbata, gimbiya Hayat ta sauƙaƙa musu hanyar jan ra'ayin Kazuzi,don haka ya ce"ka bi abin da ta ce, sauran kuma mu bar wa Allah, in sha Allahu babu wata matsala"dakare Amjad ya rissina sannan ya miƙe ya bar wajen A ranar aka rabawa sababbin bayi wajen aikinsu,ciki har da Kazuzi,da aka tura shi tsaron lafiyar gimbiya Hayat Ta ji daɗi sosai da labari ya iske ta, tana zaune a ƙawataccen lambunta,amintattun kuyanginta sun kewaye ta ta aika ɗaya daga cikin asalin dakarun da suke gadin lambunta cewa ya kira mata Kazuzi Babu jumawa suka ƙaraso,a fizge ta kalle shi sannan ta mayar da kanta gefe ƙirjinta yana bugawa,tsawon lokacin da ta ɗauka tana yi masa tijara bata taɓa ƙare masa kallo ba sai yau Cikakken namiji mai cikar zati,dogo ne sosai,mai ƙirar jiki mai matuƙar kyau,duk da cewa sanye yake cikin kayan bayi amma sai taga sun yi masa kyau tamkar ba bawa ba,sosai ta ga ya yi mata kwarjini tamkar ba bawanta ba,dogon gashinsa da ya ɗaure a tsakiyar kanshi ya sake shi ya zuba gadon bayansa,iska sai kaɗa shi take yi A dalilin haka ta kasa yi masa rashin mutunci da ɗiban albarka da ta shirya,yana zuwa gabanta bai yi wata-wata ba ya zube a ƙasa, kanshi a ƙasa ya ce "Barka da wannan lokaci ya shugaba ta!" Shiru ta yi da farko tana bin shi da kallo, kafin ta yi juriya ta ce"ka iya ladabi kamar gaske,amma ka haɗa ni faɗa da mahaifi na!" Bata yi tsammanin zai ba ta amsa ba,amma ta ji ya ce"ki gafarce ni ya shugaba ta" Da mamaki take kallonshi kafin ta ce"na san zuwa yanzu ka yi nadamar abin da ka yiwa ɗan'uwa na da mahaifiya ta ko?" Ba tare da shakkar komai ba ya ce"Kazuzi baya aikin nadama ya shugaba ta" Da mamaki take bin shi da kallo,su ma kuyangin nata kallonshi suke yi, kafin ta sake dakewa ta ce"anjuma za mu fita yawon shaƙatawa zuwa dajin Lahur,sai ka kasance cikin shiri" Ya sake rissinawa gami da amsawa da faɗin "an gama ya shugaba ta" Cikin ƙosawa ta dube shi ta ce"na sallame ka, za ka iya tafiya" Ya sake rissinawa ya ce"na barki lafiya ya shugaba ta"daga haka ya miƙe tsaye, cikin takunshi na dirarren namiji mai izza ya bar wajen Da yamma ta shirya kamar yadda ta saba lokaci zuwa lokaci,ta yi ado mai kyau,suka shiga keken dokin da suke fita da shi ita da kuyanginta, Kazuzi da wasu dakaru su biyu suka bi bayansu a dawakai zuwa dajin Lahur Hayat tana tsananin son ganin tana yawatawa yadda take so, amma mahaifinta sarki Iyaad bai cika son hakan ba, shiyasa yau da ya yarje mata take cike da farin ciki Daga ita har kuyanginta da ta mayar da su tamkar ƴan uwanta sai shawagi suke yi cikin kwanciyar hankali,sam ba su kula da wata damisa da take fakon gimbiya Hayat ba,sai gani aka yi ta daka tsalle cikin zafin nama ta yi kanta..... (Damisa zata lamushe gimbiya 🥹🥺) Comments da likes suna qaranci sosai☹️ko na tafi Hutu ne 😞 #Nusy_bee 08125952284 👑🗡️ MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑 https://chat.whatsapp.com/Is0HqhjNITL3VZIagV42u7?mode=gi_t ✍️Nusy bee ❤️ Young talented writers association YOTA ❤️ (Under YOTA'S AMAZING PENS) Page 7 Wata firgitacciyar ƙara gimbiya Hayat ta yi a tsorace,kafin ta zame ta zube kasa sumammiya, tuni kuyanginta suka cika dajin da iface-iface, lokaci guda komai ya yi tsit tamkar babu wani mahaluki mai rai a cikin dajin Ba komai bane ya faru face tsalle da Kazuzi ya yi, cikin wani irin tsananin zafin nama ya cafke damisar, ba tare da ɓata lokaci ba ya yi jifa da ita Miƙewa damisar ya yi yana gurnani yana kallon Kazuzi, Kazuzi ma kallonshi yake yi fuskarsa babu yabo babu fallasa,damisar bai bi ta kan Kazuzi ba ya sake nufar inda Hayat take kwance,da wani irin ƙarfi Kazuzi ya sake damƙarshi,ya ja shi da ƙarfi, ba tare da ɓata lokaci ba aka kaure da kokawa tsakanin Kazuzi da damisar, lokaci guda damisar ta farke ɗaurin da aka yiwa ciwon hannunshi na damtse,kuma a take jini ya ɓalle a hannun Kallon hannun ya yi sannan ya sake kallon damisar,yana murmushi ya ce"yanzu hankalinka ya kwanta? To ba abin da kake tunani bane,amma ina gargaɗinka da babbar murya ka fita a harkarta,idan ba haka ba tabbas za kayi nadama"bai rufe bakinsa ba damisar ya sake nufar inda Hayat take kwance da tsananin zafin nama fiye da na baya,wannan karon Kazuzi bai yi wata wata ba,yana damƙar wuyan damisar ya maƙure ta, ba tare da bata lokaci ba ya murɗe mata wuya,bai sake ta ba sai da ya tabbatar bata numfashi sannan ya yi jifa da ita Sai a lokacin hankalin kuyangin da dakarun suka dawo jikunansu, ba tare da ya yiwa kowa magana ba ya wuce inda Hayat take kwance ko motsi bata yi, tamkar babu rai a jikinta,bai yi wata-wata ba ya durƙusa ya ɗaga ta ya saɓa ta a kafaɗa,kai tsaye ya miƙe ya nufi cikin masarauta,sauran jama'ar suka biyo bayansu cikin mamaki da ɗimuwa,babu mai iya magana a cikinsu Kai tsaye masarautar Tayaar suka koma,kafin su isa labari ya iske mutanen fada cewa damisa ta farmaki gimbiyar Tayaar,don haka kai tsaye sarkin dakaru Amjad ya yi musu umarnin su wuce zuwa fada inda sarki yake jiransu, ba tare da ɓata lokaci ba suka nufi can Gaba ɗaya ilahirin fadar kowa yana tsaye a matuƙar razane suna jiran isowarsu,fuskar sarki Iyaad ɗauke da matsanancin tashin hankali da ruɗani,kan Kazuzi a ƙasa,yana zuwa ya kwantar da ita a gaban sarki, kanshi a ƙasa ya ce"ta samu firgici ne shine ta suma,amma babu abin da ya same ta,a gafarce mu idan mun gaza a aikinmu ya shugaba na"yana kai wa nan ya miƙe a hankali ya fice daga fadar *DAULAR KAIZUR* "Amincin Allah ya tabbata a gare ki yake wannan baiwa mai tarin ji da kai" Ɗaga kai ta yi a nutse tana ɗan murmushi,a hankali ta furta "amincin Allah ya tabbata a gare ku ruhin ƙasar kaizur" Ɗan murmushi sarauniya Amna ta yi,sannan ta zauna kusa da Munaya tana kallonta,sarki Mu'iz kuwa bai ce kanzil ba,ya zauna a inda ya saba zama yana kallonsu "Munaya! Tsawon shekaru ashirin kenan kina karɓar hukunci iri-iri, kina fuskantar ƙasƙanci da wulaƙanci, menene dalilin hakan? Saboda ɓatan abin da tun farko kin san ba naki bane, menene dalilin da ya sa ba za ki bayyana shi ba? ke a daina azabtar da jikinki?mu ma zuciyoyinmu su huta da azabtuwa?" Kan Munaya a ƙasa, cikin rissinawa ta ce "gaisuwa gare ku ya shugabanni na,kuma ruhin gari mai albarka kaizur Munaya baiwa ce mai amana,bata taɓa cin amanar wani ba,ko da ace Sarkin kaizur ne Munaya bata salwantar ba,bata da riba a hakan" "Na sani,amma menene dalilin da ya sa kika amsa ke kika fitar da shi daga ɗakinshi?" "Saboda ni na aikata hakan ranki ya daɗe!" Shiru sarauniya Amna ta yi na ɗan lokaci kafin ta ce"to menene dalilin da ya sa kika aikata hakan?" "Saboda soyayya ranki ya daɗe " Sarauniya Amna ta ce"ba dai soyayya ba,an saka ki ne" Shiru Munaya ta yi na ɗan lokaci, kafin ta ce"ba saka ni aka yi ba, amfani aka yi da ni,na gane hakan" Zaro idanu sarauniya Munaya ta yi cikin firgici ta ce"amfani da ke? Wanene ya yi amfani da ke?" Ba tare da bata lokaci ba ta ce"ina son a ba mu waje ranki ya daɗe!" Wani mugun kallo sarauniya ta yi mata ta ce"a cikinmu wa zai ba ki wajen?ni ko Mai martaba?" Kan Munaya a ƙasa ta ce"mai martaba ranki ya daɗe,tunda maganar tamu ce ta mata" A wani irin fusace sarauniya ta saukewa Munaya mari,sannan ta hau faɗa tana faɗin"kina matsayin baiwa ƙasƙantacciya wadda take ƙarƙashin hukunci ko a gaban dubban mutane ba sai an ba ki izini za kiyi magana ba?har kike cewa wai mai martaba ya ba ki waje?" Miƙewa mai martaba ya yi,ya dubi sarauniya ya ce"ku yi magana,dama nima na gaji da jin maganganun tsinanniya irin ta,na gaji da ganin fuskar da ta fi komai muni a idanu na"yana kai wa nan a maganarshi ya juya ya fice daga ɗakin ba tare da ya sake kallon sashen da suke ba Yana fita sarauniya Amna ta watsowa Munaya wani mugun kallo, Munaya ta yi ɗan murmushi, sarauniya ta ce "Ya tafi,me kike so ki ce? Kar dai ki manta ko me kika faɗa zai koma kunnenshi" Munaya ta jinjina kai ta ce"haka ne! Dama game da ɓatan ɗanki yarima Sahal ne"ta ɗaga kai tana kallon sarauniya da ta ƙagu ta ba ta amsa, kafin ta cigaba da magana sarauniya ta ce"me kika sani game da ɓatan nashi?" Munaya ta sake duban sarauniya ta ce"Kamar yadda na gaya miki a baya cewa amfani aka yi da ni to haka ne, Urwa da Umayr da aka kashe akan wannan rigimar duka basu da laifi, ballantana Ya'aƙub da babu abin da ya sani a kai Wasu manya ne a cikin masarautar nan suka sa aka sace Yarima Sahal,ban san niyyar su ta yin hakan ba,amma na fi tunanin saboda mulki ne"ta ƙarashe magana idanunta ƙyar akan sarauniya Amna A wani irin gigice sarauniya Amna ta riƙe hannayen Munaya da suke ɗaure a cikin sarƙa,muryarta tana rawa ta ce"manya a cikin masarautar nan? Su wanene haka?kuma menene dalilin su na yin hakan?" Munaya ta ce"Nima ban sani ba ranki ya daɗe,amma Kamar yadda na faɗa da farko wataƙila shirinsu ne akan kujerar kaizur" Shiru sarauniya Amna ta yi tana kallon Munaya cikin tsananin tashin hankali da ɗimuwa, kafin ta ce"wanene a cikin MASARAUTAR KAIZUR da yake jin zai iya samun mulki muddin ya ga bayan ɗana Sahal?" Shiru suka yi su duka biyun, kafin Amna ta ce"Yarima Zaffar ko Yarima Jamal? Su kaɗai ne masu gadon sarautar wannan birni idan babu sarki Mu'iz Amma ta yaya za su iya cin amanar sarki? musamman ma Yarima Zaffar,ke ma kin san ƙarya kike yi,hakan ba abu ne mai yiwuwa ba" Munaya ta rissina ta ce"nima na san da hakan ya shugaba ta,ban tabbatar

Chapter 3 of 9