da su wanene ba,amma tabbas manya ne a masarautar nan,kuma su ma za su iya gadon masarautar "
Shiru sarauniya Amna ta yi tana jin tana sake shiga ruɗani,a hankali ta ce"tabbas zan yi bincike,zan saka mai martaba ya yi bincike akan duk wani mahaluki da yake da alhakin gadon MASARAUTAR KAIZUR, muddin na samu mutum da hannun shi a ciki tabbas zan ɗauki mataki mafi muni,ke kuma ki jirayi dawowa ta"tana kai wa nan ta miƙe da sassarfa ta fice daga ɗakin, Munaya ta bi ta da kallo tana murmushi wanda ita kaɗai ta san ma'anarshi
*DAULAR TAYAAR*
Yau kwana biyu kenan da faruwar tsautsayi ga gimbiyar Tayaar, wato Hayat, an samu ta farfaɗo,kuma zuwa yanzu zabure-zaburen da take yi ma ta daina
Sai dai tun da aka gaya mata Kazuzi ne ya ɗauko ta tun daga dajin Lahur zuwa gida take jin haushin shi sosai, kwata-kwata bata yaba masa ba na cetar rayuwarta da ya yi, don haka ma ta ƙudurce a ranta sai ta yi masa gargaɗi mai ƙarfi
Kazuzi yana zaune a lambun gimbiya bayan ya kammala aikin da badakare Amjad ya saka shi na gyaran lambun, cikin nutsuwarshi yake ƙarewa ko'ina na lambun kallo,a hankali wani abu da ya shuɗe ya gifta a idanunshi
✨
"Sadaukin sadaukai!tsoro mai ban tsoro!wanda mutuwa take tsoro,takawarka lafiya abin alfaharin Baruda,kai ne sarki ko da ba'a yarda ba"
Ɗaga kai ya yi yana kallonta, murmushi take yi tana wasa da gashin kanta,ya gyara zama yana kallonta,ta ƙaraso ta zauna a kusa da shi tana kallonshi tana murmushi,ya ce"kin fi taurari haske a cikin Baruda,ina roƙon abin bauta mafi haske ya rufe idanun wasu mazan daga ganin wannan haske,sai ni kaɗai,kar wani ya yi min shigar sauri"
Dariya ta yi da sautin muryarta mai daɗi,ta kalle shi tana murmushi ta ce"a tunaninka a kaf ƙasar Baruda birni da ƙauye akwai wanda ya isa ya mallaki Malli?
Ai ko da ace mutuwa ce ta raba mu kowa ya san Malli matar Kazuzi ce abadan,babu wanda ya isa ya mallaki wannan Malli ɗin sai sadauki Kazuzi "
Janyo ta ya yi jikinshi yana murmushi sosai,ya ce"na san da haka nima
Ke ce ƙwarin gwiwa ta a cikin daular Baruda,duk wani farin ciki da walwala ke ce sila
Muddin akwai Malli a gefena bana damuwa, komai na duniya ba komai bane akan Malli
Ki zama ba kya kusa da ni bani da maraba da bawa"
Igiyar tunanin shi ta yanke a daidai nan saboda ruwan da ya ji an watsa masa,ya ɗago da sauri yana kallon Hayat da take kallon shi ranta a tsananin ɓace,cikin hargowa ta fara faɗin
"Shaiɗancin da ka saba a cikin garin naku za kayi min?"
Kallonta kawai yake yi ba tare da ya yi magana ba,ta ƙara fusata sosai, cikin ɓacin rai ta fara masifa tana kai masa duka,amma ko gezau, sai kallonta kawai da yake yi, dakarun da suke tsaron lambun suka taho da gudu don jin ba'asi, idanunta a rufe ta ce"ku kira dakare Amjad!"babu musu wani badakare ya juya don kiran shugaban dakaru
Bayan sun iso ta dubi Amjad idanunta suna kaɗawa ta ce"ku tafi da shi,ku azabtar da shi,har sai ya faɗi dalilin da ya sa ya ƙura min idanu yana kallo na a yayin da nake wanka,kar a ba shi ruwa da abinci sai sau ɗaya a rana,a tabbatar an ɗora shi a SIRAƊIN UƘUBA irin wanda bai taɓa hawa ba tsawon rayuwarsa"shi Kazuzi sai yanzu ma ya ji laifinshi, Amjad ya rissina ya ce"an gama ya shugaba ta,sannan ya finciki Kazuzi, Kazuzi bai yi musu ba ya bi shi suka tafi
Duk da hukuncin da ta saka ayi wa Kazuzi hakan bai saka ta huce ba,cikin tsananin ɓacin rai ta nufi sashenta, kamar yadda ta saba idan ranta yana ɓace sai da ta kori kowa a sashen sannan ta kwanta akan gadonta tana sauke numfashi cikin ɓacin rai
Ta rasa me zata yi wa wannan ƙasƙantaccen bawan ta ji sanyi a ranta,gaba ɗaya ya raina matsayinta,ba ita ba ma,ya raina dukkan wani mai matsayi a Tayaar,amma zata yi duk mai yiwuwa ta yi maganinshi
💫
Da gasken gaske su Amjad suke ganawa Kazuzi azaba iri-iri,kuma ko sau ɗaya bai taɓa yunƙurin kare kanshi ba,hakan ya bawa dakarun mamaki,kuma ya yi musu daɗi, waɗanda suke jin haushinshi suka samu damar rama duk abin da ya yi musu
A cikin kwanaki uku sun yi nasarar galabaitar da Kazuzi irin yadda suke so,sai dai babu alamun rissinawa ko tsoro a tare da shi,kuma sam babu alamun damuwa a kan fuskarsa
A wannan ranar ne gimbiya Hayat ta saka aka fito da shi,kai tsaye aka nufi lambunta da take zaune ita da amintattun kuyanginta kamar yadda suka saba,suna nan a zaune dakare Amjad ya shigo da Kazuzi da taimakon wasu dakarun,suna zuwa suka jefar da shi a gaban gimbiya
Murmushi mai kyau Hayat ta yi tana kallon Kazuzi, kafin ta ce"a kwance masa igiyar"babu musu aka kwance masa igiyar,ta dubi dakarun ta ce"za ku iya tafiya"suka rissina suka juya suka fice daga lambun
Cikin isa Hayat ta kalli Kazuzi ta ce"na san baka yi nadama ba yanzu ma,don da alamu kana da girman kai da ɗaukar kanka wani,bayan kai ɗin ba wata tsiya ba ce illa bawa ƙasƙantacce
Ko babu komai zuwa yanzu ka gane ni ba kalar matan da kake kalla bane lokacin da kana garinku na zalunci,ba zan ce ka daina ba,amma hukunci yanzu aka fara ɗauka a kanka"
Gyara zama ya yi yana yin ƙasa da kai,ya ce"ki gafarce ni ya shugaba ta,ban san me kike magana akai ba,amma a duk lokacin da kike shirin ɗaukar mataki akaina a shirye nake na amsa ya shugaba ta
Amma ina so ki sani cewa,babu wata mace a idanun Kazuzi sai MALLI!duk wata mace koma bayan Malli namiji ne a idanun Kazuzi!!!"
Da tsananin mamaki take kallonshi,da farko kasa magana ta yi, kafin ta ce "har ni?Nima kana nufin namiji ce?"
Kai tsaye ya ce"har ke,ki gafarce ni ya shugaba ta"ya ɗaga kai ya kalle ta ya ce"an sallame ni?zan iya tafiya?"
(Ga masu son VIP group ga number ta nan a ƙasa)
#Nusy_bee
08125952284
👑🗡️ MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Page 8
Hawaye ne suka zubowa gimbiya Hayat,wani irin kuka ya ƙwace mata, tunda take a rayuwa ba'a taɓa ci mata mutunci irin na yau ba, kallonta Kazuzi ya yi,a hankali ya ce "ki gafarce ni ya shugaba ta,ban faɗi hakan don na ɓata miki ba,na faɗa ne don na wanke kaina ban yi tsammanin abin zai yi miki zafi ba
Abin da nake so na fahimtar da ke shine ni ba ma'abocin kula mata bane,mace ɗaya na so a rayuwa ta,kuma a kanta na ɗora dukkan burina,da ban same ta ba shine na cire dukkan buri na akan wata mace,amma idan ba ki gamsu ba za ki iya ɗaukar mataki akaina"
"Tashi ka ba ni waje"ta faɗa a tsawace
Miƙewa ya yi ba tare da ya sake magana ba ya fice daga lambun, ta bi shi da kallo zuciyarta tana yi mata zafi
Ita da kanta ta sani tana cikin mata uku da suka fi kowacce mace kyau a kaf ilahirin ƙasar Tayaar,sai dai sam maza ba sa gabanta,amma yau wani ƙasƙantaccen bawa, kafirin banza yana kiranta da namiji,ita kuwa zata so ta ga wannan Malli ɗin da yake cewa ita kaɗai ce mace a idanunshi,don ta gani da me ta fi ta
Miƙewa ta yi ranta a jagule ta nufi sashenta da yake jikin lambun,a ranta tana ƙara jin tsanar wannan ƙasƙantaccen dan wulaƙancin,a cewarta
*DAULAR KAIZUR*
Cikin wata duhuwar dokar daji yake tafiya,mai cike da ababen tsoro da firgitar da bil adama, sanye yake da wasu baƙaƙen kaya waɗanda ba su bayyanar da komai nashi ba,sai ƙwayar idanunshi da ta bayyana daidai wajen da aka shata a jikin yankin da ya yi amfani da shi ya rufe fuskarshi, tafiya yake nutsuwa da kwanciyar hankali babu alamun tsoro ko firgici a tare da shi
Sam halittu masu ban tsoro da kukan dabbobin da yake arba da su ba su ba shi tsoro ba, cikin nutsuwarshi ya cigaba da tafiya har ya isa wajen wani ƙaton kogo a tsakiyar dajin
Tun daga bakin ƙofar kogon mutum zai gane wannan ba wajen zuwan mutane masu iymani bane, saboda tun daga bakin kogon ake fara cin karo da ƙasusuwa dabam dabam na sassan jikin ɗan adam, ba tare da tunanin komai ba ya danna kai cikin kogon
Halittu masu razanarwa da iface-iface kala-kala na wasu nau'in halittu masu tsananin ban tsoro,amma ko kallo biyu baya yiwa halittun ya miƙe ya cigaba da tafiya har ya kai ƙuryar kogon
Gaban wani dattijo ya rissina kanshi a ƙasa, cikin tsananin girmamawa ya furta "gaisuwa gare ka ya babban matsafi, ishashshen da babu kamarshi,sarkin aljanu da mutane,uban duk wani matsafi, raina fansa ke a gare ka sarkin bokaye lamzur dodo a cikin matsafa"
Tsohon, wanda ya kasance abin tsoro ga duk wanda ya fara arba da shi a kallon farko,idan mutum mai raguwar zuciya ne ganin wannan hatsabibin tsohon ya isa ya halakar da shi saboda tsananin munin siffar halittar shi
Dattijo ne sosai,don a ƙalla zai iya kai wa shekaru ɗari da ashirin,farin gemunshi an raba su gida biyu an kitse su gefe da gefe,an yi musu kwalliya da wasu jajayen duwatsu marasa kyan gani,kanshi ƙwal babu gashi ko ɗaya,sai wasu zane zane da suka canjawa kan kamanni,daga goshinshi akwai wani tambari mai kama da tsayuwar wata,kunnuwanshi sanye suke da wasu ƴan kunnaye marasa kyan gani
Gaban dattijon wuta ce take ci sosai, dattijon bai ba shi amsa ba sai da ya ɗauki wata kaza mai rai a gefenshi ya jefa a cikin wutar,bayan wasu yan daƙiƙu ya ɗago yana kallon shi
"Uban shaiɗanu!ka saɓa alƙawari!
Ba haka muka yi da kai ba"kan uban shaiɗanu a ƙasa ya ce"ina neman afuwa ya shugaba na"
"Amma menene dalilin da ya sa tun da farko ba ka gaya mana ba sai yanzu?"
"Kuskure ne da ɓatan basira ya shugaba na,amma ina neman afuwa"
"Babu afuwa!
Za ka amshi hukuncin ka,ka je,kar ka sake dawowa Sai nan da watanni shida,don haka ka tafi!!"ya ƙarashe da tsawa
Jiki na rawa uban shaiɗanu ya miƙe, ba tare da ya sake magana ba ya fice daga cikin kogon, duk wannan wahalar da ya sha ya zo wajen ba ita ba ce ta dame shi, damuwarshi shine yadda zai samu cikar burin shi cikin sauƙi
Bai ji ko ɗar ba, asalima ba wannan ne karo na farko da ya fara karɓar hukunci daga boka lamzur ba, hukuncin ya ƙare a ɗora daga inda aka tsaya
*DAULAR TAYAAR*
Izuwa yanzu kwata-kwata Hayat ta yi duk mai yiwuwa ta rabu da saka Kazuzi a idanunta saboda har yanzu tana jin zafin maganar da ya gaya mata,ko da a ce zata shiga lambunta Kamar yadda ta saba matukar ta hango shi zata aika masa cewa ya fito tana son shiga,bai taɓa nuna damuwa ba,sai ya fito
Tsawon sati biyu aka ɗauka a haka, kuma har lokacin abin da Kazuzi ya gayawa Hayat yana yi mata zafi,kuma har lokacin tunanin hanyar da zata ɗauki mataki akanshi take yi,amma ta rasa hanyar hakan
Yau tana zaune a lambunta tana shan ƴaƴan itatuwan da wata kuyangarta ta haɗa mata,tana sha tana kalle-kallen tsuntsayen da suke shawagi a cikin lambun tana murmushi
Babu zato babu tsammani tana ɗaga kai ta yi arba da shirgegen kumurcin maciji ya fasa kai yana kallonta, gigicewa ta yi,ta kurma wani uban ihu a firgice,macijin bai yi wata-wata ba ya yi tsalle ya nufi inda take,ta dunƙule a waje ɗaya tana jiran mai afkuwa ta afku,don ta tabbatar kafin dakarun da ke tsaron bakin lambun su kawo mata agaji komai ya faru,gashi yau bata shigo tare da kuyanginta ba,da yake wasu lokutan ta kan yi hakan
Amma sai ta ji shiru macijin bai ƙaraso inda take ba,a tsorace ta ɗago da kanta tana kalle-kalle
Da tsananin mamaki take kallon Kazuzi wanda ya damƙi wuyan macijin da tsananin ƙarfi,a kallo ɗaya da ta yiwa macijin ta ga alamun galabaita saboda shaƙar da Kazuzi ya yi masa,a firgice ta yi kanshi tana faɗin "kar ya kashe ka!ka sake shi!!ba ka da hankali ne?maciji bai san da wani karfinka ba,mutuwa za kayi"
Duk ɓaɓatun da Hayat take yi bai sa Kazuzi ya saki macijin ba,dakarun da suka shigo da gudu suka tsaya suna kallonshi, Amjad ya daka masa tsawa "saki macijin nan!
Ko ba ka ji abin da gimbiya ta ce bane?"
Ko kallonsu bai yi ba, sai kallon macijin da yake yi, cikin nutsatstiyar muryarshi ya ce"ya zama gargaɗi na ƙarshe,kar ka sake"yana kai wa nan ya murɗa wuyan macijin da ƙarfin tsiya,take ya raba kan macijin da gangar jikinshi
A fusace dakare Amjad ya yi kanshi yana masifa, Sarkin yaƙi da ya ƙaraso wajen ya daka masa tsawa,a fusace ya dube shi ya ce "a maimakon yabo da zai samu na ceton ran gimbiya har sau biyu sai ya samu sakamako irin wannan daga gare ka?"
Rissinawa Amjad ya yi,ba don ya so ba ya ce"ka gafarce ni ya shugaba na"daga nan ya juya ya fice daga lambun,sauran dakarun suka bi bayanshi,shima Kazuzi ya ɗauki jikin macijin nan ya bi bayansu
A sanyaye Hayat ta bi Kazuzi da kallo, yaushe ya iso wajen ma har ya ceci rayuwarta duk da wulaƙanci da cin mutunci da take yi masa?
Take idanunta suka kawo ƙwalla, Sarkin yaƙi ya rissina ya ce"ki gafarce ni ya shugaba ta,zamanki a nan akwai haɗari,zai kyautu ki koma sashenki saboda samun aminci"
Babu musu ta wuce ta fara tafiya jiki a sanyaye,dakarun da ke tsaron bakin ƙofar suka raka ta har zuwa sashenta
💫
"Menene matsalarka da macen da take wulaƙanta ka a kowanne lokaci? menene dalilin da ya sa lallai sai ka kare mata hari?
Hakan ya tabbatar min da mazantakar taka ta ƙarya ce tunda ta lalace a wajen ɗaukar wulaƙancin mace"
Kazuzi da ke zaune yana gyara dogon gashin kansa da hannunshi ko ɗagowa bai yi ba ballantana ya dube shi,asalima hankalinshi yana wani wajen, tunaninshi yana wajen abar ƙaunar ruhin shi Malli, wadda da suna tare da yanzu ita ce take yi masa gyaran gashin
"A don haka ina mai jan kunnenka da ka tsaya a iyakarka,babu ruwanka da shiga sabgar yarinyar nan idan ba abu ta saka ka ba,da kana da zuciya da ka daina shishshigi da shiga shirgin ta don ka tsira da mutuncin da ya yi maka saura,idan kuma baka ji ba,duk abin da ya same ka kai ka janyo wa kanka,kafirin banza kawai "
Duk wannan ɓaɓatun da yake yi ko ɗago kai Kazuzi bai yi ba ballantana ya kalle shi,ya cigaba da gyara gashinshi cikin nutsuwa tamkar ba da shi ake ba,sai da ya juya,yana daf da fita ya ji muryar Kazuzi
"Mafi alkhairi a gare ka kar ka sake farmakar ta!"
Dawowa ya yi da baya yana kallonshi,ya kasa gaskata maganar da ya ji daga bakinshi,da ƙyar ya iya faɗin
"Ban ji abin da ka ce ba,ka san girma ya taɓa kunnen"
Ba tare da wata shakka ba Kazuzi ya sake faɗin "ka fita daga harkarta,ya zama karo na ƙarshe da za ka sake farmakar ta
Zuwa yanzu na san ka gane Kazuzi ba kanwar lasa bane, kasancewa ta a cikinku hakan ba yana nufin daidai nake da ku ba, muddin ina numfashi zan gani idan makircinka zai iya taɓa ko da silin gashinta "
Da tsananin mamakin yadda kazuzi ya gano shi ya dube shi, cikin matuƙar tsana ya ce"akwai abin da za ka iya yi akai ne?ka fara zama mai ƙima a cikin masarautar nan tukuna, kafiri zindiƙi kai har kana da zarrar da za ka gaya min wata magana na yarda?"
"Yarda ko rashin yarda wanna ra'ayinka ne
Amma shi Kazuzi baya maimaita magana,bana shakkar na kashe ka a bainar jama'ar ƙasar Tayaar,bana shakkar a kashe ni,idan har kana son ka kuɓuta daga uƙubar Kazuzi to ya kamata ka ɗauke idanu daga kan yarinyar da bata ji ba bata gani ba
Idan kai namiji ne kamar yadda kake jin kanka fitowa za kayi ka gwabza da namiji kamar yadda kake jin kanka,amma idan ka laɓe a bayan tsafi kana nufin cutar da mace hakan zai saka na zargi kai ɗin ba namiji bane,ɗan daudu ne "Kazuzi yana kai wa nan a maganarshi ya miƙe ba tare da ya sake bi ta kanshi ba ya fice daga ɗakin yana ƙarasa ɗaure gashinshi da ya gama gyarawa
Bin shi ya yi da kallo cikin tsananin razani da mamakin wannan abu,bai taɓa tsammanin akwai wani mahaluki da zai iya gano ɗanyen aikinshi a cikin Tayaar ba, dole ya san yadda zai yi ya gama da Wannan hatsabibin mutumin, kafin ya cigaba da yunƙurin kashe gimbiya Hayat, so yake Sarki Iyaad ya ji zafi kwatankwacin wanda ya ji a shekarun baya
💫
A tsawon rayuwar gimbiya Hayat bata taɓa ganin mutumin da har zuciyarta ta yaba da tsananin jarumta da sadaukantakarshi ba irin ta sadauki Kazuzi, jikinta ya yi sanyi sosai,a ranta tana tunanin duk mutumin da zai ceci tsayuwarta irin haka bai dace ta yi masa kallon maƙiyi ba
Na farko ya cece ta daga damisa,na biyu kuma maciji,duk da irin wulaƙanci da cin mutuncin da ta yi masa hakan bai taɓa sakawa ya kasa taimakonta ko girmama ta da bin umarnin ta ba
Tsawon kwanaki biyar da faruwar abin bata da sukuni sai tunanin wannan taimakon da Kazuzi ya yi mata,wata ƙima ta musamman take ganinsa da ita a yanzu
Yau tana zaune da amintacciyar baiwarta Huda,hira suke yi sosai, kafin ta bijiro masa tambaya
"Huda! menene ra'ayinki game da wannan sadaukin da ya ƙi amsar Musulunci?"
Murmushi Huda ta yi, kafin ta ce"wai sadauki Kazuzi?
Jarumin jarumai kenan,ban taɓa ganin jarumin namiji mai zuciyar maza da sadaukantaka irin nashi ba
Har yanzu ina iya tuna yadda ya yi dambe da damisa,kuma ya kashe ta,kwanakin baya kuma cikin wani irin zafin nama ya ƙaraso ya damƙi wuyan maciji,mu da muke bakin lambun ya riga mu shiga har ya kawo miki ɗauki"
Hayat ta ce"duk na ji wannan, menene ra'ayinki game da halayensa?"
Kai tsaye Huda ta ce "mutumin kirki ne ya shugaba ta, yana da tausayi da sanin darajar ɗan Adam,amma sam baya ɗaukar wulaƙanci,kuma hakan ya dace da duk wani ɗan Adam mai daraja kanshi,ko da yake shi Kazuzi bawa ne"
Hayat ta girgiza kai ta ce"duk ba Wannan ba,kin san yadda yake faɗar magana babu girmamawa,hakan ya dace yana a matsayin bawa?nagartaccen mutum zai iya haka kuwa?"
Girgiza kai Huda ta yi,ta ce"ya shugabata yana faɗar gaskiya duk dacinta ni a gani na mai zai hana a duba maganarshi kafin a yanke masa hukunci?
Zuwa yanzu dai mun fara gane kyawawan halayensa "
(Ga masu son VIP group ga number ta nan a ƙasa)
#Nusy_bee
08125952284
🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Page 9
Wani murmushi ya kubcewa Hayat,ta ce"Huda kina yabonshi da yawa fa
Kar fa ki manta ba musulmi bane ballantana na ce za'a yi ƴar gida"
Huda ta ƙyalƙyale da dariya ta ce"ya shugaba ta ai ko da ace na so shi ya cancanci a so shi ɗin, kyakkyawa ne ajin ƙarshe,sannan gwarzon jarumi ne,kuma shi namiji ba'a san shi da tsoro ba, sannan mafi girma kuma ya ceci ran shugaba ta har sau biyu,dole na girmama shi na mutunta shi"
Bata san menene dalilin ba,amma haka kawai ta ji gabanta ya faɗi,kuma sam bata yi farin ciki da maganar Huda ba,amma sai ta dake tana yaƙe,ta dubi Huda da take ta ƙara taƙarƙarewa tana faɗar kyawawan halayen Kazuzi,ta ce"to yanzu ta ina kike ganin zan iya mayar da shi kamar ku?
Kar ki manta shine ya kashe min ɗan'uwa,silar haka mahaifiya ta ma ta rasu,kuma babu alamar nadamar hakan a tattare da shi fa"
"Shine silar shahadar yarima,ya bar duniya mai cike da ruɗani da ababen ƙi ya shugaba ta,ya mutu akan hanyar daukaka kalmar Allah, wadda Allah ya sanar da mu a Alkur'ani cewa su rayyayu ne
Sarauniya kuma,ki gafarce ni ya shugaba ta, kowanne mai rai sai ya ɗanɗani mutuwa,amma ta hanyoyi dabam-dabam,ko da ace Sadauki Kazuzi bai kashe Yarima ba, tunda kwanansu ya ƙare za su koma ga mahaliccinsu
Maganar nadama kuma,ya shugaba ta ki gafarce ni,bai yi abin da zai yi nadama akai ba har yanzu,shi ba musulmi bane,da musulmai suka tunkare su da yaƙi sai aka ba shi umarnin tunkararsu, kuma ko da ace musulmi ne don musulmi ɗan'uwanshi ya yaƙe shi babu laifi ya kare kanshi
Su ba su san kalmar Allah ba, ballantana su yi tunanin ɗaukaka ta,a duba magana ta ya shugaba,amma idan akwai wata matsala a magana ta a yi min aikin gafara "
Hayat da ta zuba mata idanu kawai tana kallonta ta ja ajiyar zuciya,sannan ta ce"na ji duka,kuma zan duba,amma har yanzu ina cike da jin haushin wulaƙancin da ya yi min don yana kallo na ina wanka na yi masa magana
Ya ce wai ni ba mace ba ce, Malli ce kaɗai mace a idanunshi "
Kallonta sosai Huda ta yi sannan ta ce"ya shugaba ta wannan ai ba abin damuwa bane,ba ya faɗa bane don ya wulaƙanta ki,da alamu ya faɗa soyayya ne mai wuyar sha'ani,a duk lokacin da mutum ya faɗa soyayya da wani ko wata,ba sa ganin kowa a rayuwa sai waɗannan masoyan nasu,komai da kowa ba sa wani burge su,duk kyau da ƙawatuwar su kuwa
Yanzu da ace za ki ga yarinyar da yake so ɗin ke gani za kiyi bata dace ba ma, saboda bata kai a kira ta mace ba ma,amma ita soyayya ba haka take ba,bata duba komai, sai wanda ake so ɗin"
Hayat ta jinjina kai ta ce"soyayya!to Allah ya sa mu dace,amma menene a soyayya ne da yake rufewa mutane idanu? menene abin burgewa a cikinta?"
Huda ta yi ƴar dariya ta ce"ya shugaba ta ai soyayya ta yi, ita ce mahaɗin rayuwa,sam ba za ki gane me nake nufi ba har sai kin faɗa soyayya "
Ƴar dariya Hayat tayi ta ce"to malamar soyayya,bar ni haka da wannan surutun naki, lokacin shiga ta cikin gida ya yi "ta miƙe tsaye,Huda ta rissina ta kwashe mata kilishin da suka shimfiɗa mata,suka nufi cikin gidan
*DAULAR KAIZUR*
"A ina aka tsaya? Har yanzu ban ji amsa daga gare ka ba kamar yadda ka ce za kaje wajen boka lamzur,har yanzu ban ji bayani ba"
Ɗaga kai ya yi daga inda yake zaune yana kallon uwar sharri da ke tsaye akanshi tana jiran amsarshi ,a hankali ya girgiza kai,ya ce"ban samu yadda nake so daga gare shi ba,asalima ya yi fushi da mu,ya ce kar na sake komawa sai nan da wata shida"
Shiru uwar sharri ta yi na ɗan lokaci kafin ta samu waje ta zauna,a hankali ta ce"to yanzu ya za'a yi kenan?
Ka ga abubuwa ba sa tafiya yadda ake so"
Uban shaiɗanu ya girgiza kai ya ce"kar mu yi gaggawa,muka yi jimirin shekaru ashirin ma,don dai wata shida sai ya gagara?aiki ɗaya ya rage,wanda daga shi ne ni da ke mun samu burinmu da biyan buƙatarmu"
Jinjina kai uwar sharri ta yi,sannan ta ce"Allah ya nuna mana, lokaci ya yi da za mu cimma burinmu,mu canja tsarin wannan zalunci irin na wannan mutumin"uban shaiɗanu ya jinjina kai, kafin ya yi magana uwar sharri ta sake faɗin "amma da sharaɗi,kar ka yi tunanin za ka ci amanar uwar sharri, don tabbas za ka haɗu da sharrin da ya girmi tunaninka "
Ɗaga kai ya yi yana kallonta da mamaki ya ce"me ya kawo wannan maganar ne kuma uwar sharri?"
Murmushi kawai ta yi, sannan ta gyara rufin fuskarta, ba tare da ta yi magana ba ta bar wajen,ya bi ta da murmushi,a ranshi yana ayyana abubuwa da yawa
*DAULAR TAYAAR*
Kwana biyu kenan da tattaunawar gimbiya Hayat da kuyangarta,ta gamsu sosai Da maganar Huda,amma bata san yadda zata yi don ta yi masa magana ba,asalima tun daga ranar bata sake fitowa daga sashenta ba ballantana har ta saka shi a idanunta,asalima wata kunyar shi take ji saboda abubuwan da ta rinƙa yi masa a baya
Tana zaune a ɗakinta, kuyanginta guda biyu suna taya ta shiryawa bayan ta fito daga wanka sai ta ga abu ya gifta,da farko bata kawo komai ba, musamman da ta ga alamu cewa su Huda ba su ga komai ba,sun cigaba da yi mata hira yadda suka saba
Sake ganin giftawar abu ta yi,ta tsayar da su Huda, lokaci guda suka yi shiru suna saurare
Kamar an ce kalli can,ta hango wata ƙatuwar kada a