Share this page
8 / 9
tsafi Saboda ƙarfin tsafinsa da yadda yake sarrafa aljanu yana iya barin ƙasar ya je wata nahiyar ya dawo a yini guda ko kuma a cikin dare,sannan kuma gwani ne a fannin farautar manyan namun daji,kama daga kura,kyarkeci,kada,damisa, da sauran su, dama ba'a maganar maciji da waɗanda ba su kai shi ba, Waɗannan ma bai ɗauke su wani abu ba Abu ɗaya ne tawayarshi a rayuwa, tsawon shekaru sama da ashirin da aurenshi har yanzu bai taɓa haihuwa ba,duk dabara da surkulle na tsafi ya yi,amma babu wani cigaba, matarsa Hasa,bata gajiya da yawace-yawacen wajen bokaye da malaman tsibbu ba don su samu haihuwa,amma amsar ɗaya ce,ba shi da rabon haihuwa A dalilin haka ne Hasa ta canjawa mijinta,ya daina gane kanta,ta tayar da rikicin ita lallai sai ya sake ta, hakan ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba,amma ya cigaba da lallaɓa ta ko don shekarun da suka ɗauka suna zaman tare Sanadin haka ya sa ya ɗan mayar da hankalinsa kan farautar shi ta ɗan lokaci,sau tari idan ya bar nahiyar ta su bisa umarnin da yake bawa aljanunsa sai ya kwashe kwanaki bai dawo ba, musamman da Sarkin lokacin wato Jiyaaz ya yarje masa, kasancewar ana amfana sosai da farautar shi,har Giwa ya kan farauto ya feɗe ta, ba'a maganar su damisa,kura da sauran dabbobin daji,yana kawo fatocin dabbobi iri-iri a duk lokacin da aka buƙata a Baruda, hakanan kuma ya iya haɗa dafin macizai kala-kala musamman waɗanda ake shafawa makamai da wanda ake yiwa abokan gaba izaya Tsawon lokaci bai ziyarci dajin kalaar ba, saboda akwai isassun namun dawa a dazukan kewayensu,amma yau yana son ziyarar yankin Dajin Malug yana a wani yanki ne wata daular Musulmai mai suna JASUS, saboda yadda Baruda bata shiri da musulmai ya sa ko da ace Murad zai ziyarci wannan dajin sai cikin dare,ya je ya yi uzurinsa kafin ketowar alfijir ya dawo Baruda Yau ma kamar yadda ya saba ya kammala farautarsa,ɓauna ya samo, saboda ita yake buƙata yana son amfani da fatarta,ya dafa kujerar tsafinsa don ya koma Baruda kenan ya fara jin kukan jariri Ba yau ya saba shiga dazuka ba,yana iya bambance muryar jaririn mutum da ta aljani idan suka kwaikwaye shi, don haka ya yi matuƙar mamakin samun mutum mai rai a cikin wannan ƙungurmin dajin,mutum mai rai ɗin ma jariri,don haka ya bazama yana duddubawa Ai kuwa ya yi dacen samun jaririn a cikin wani buhu,an yasar da shi a bakin hanya,ya yi saurin ɗaukar buhun ya kwance yana ƙarewa jaririn da ba zai haura watanni uku ba a duniya kallo Tsananin kyan jaririn ya shagaltar da shi ya yi ta kallonsa,daga baya ya yi tunanin nemar masa abinci,don da gani yunwa yake ji,bai yi wata wata ba ya koma baya inda ya gano wasu masu kiwon raƙuma a daf da dajin,suka ba shi nonon raƙumi ya ba wa jaririn,sannan ya hau kujerar tsafinsa don komawa Baruda Ya riga ya san dokar Baruda,ko ɗan tsako ne muddin ba nasu bane ba sa ƙaunar ya raɓe su ballantana ɗan mutum,shi kuma yana da tunani mai kyau akan jaririn,ya san tunda ya ganshi a gefen daular Jasus to tabbas ɗan cikin garin ne,tunda su musulmai ba sa sonshi shi zai raine shi ya koya masa yaƙi,ya nuna masa soyayya ya ba shi makami ya yaƙi Musulmi Iya wannan tunanin da ya yi kawai ya saka shi murmushi,a ranshi ya fara wassafa yadda zai mayar da wannan jaririn,ya yi nasara akan dukkan abokan hamayya,da ƙarfin tsafi da ƙarfin tuwo Kai tsaye daga nan fadar sarkin Baruda Jiyaaz ya wuce,duk da kasancewar shi sananne a fadar,kuma ana girmama shi da mutunta shi amma sai da ya jira aka yi masa iso,sannan ya shiga Bayan ya gaida sarki Jiyaaz kamar yadda ya zama al'ada,ya gabatar da jaririn da ya tsinta a dajin kalaar Ɗif fadar ta yi,wannan ya kalli wannan,wancan ya kalli wannan, Yarima Akaal, ɗan sarki Jiyaaz a wancan lokacin ne ya fara hasala,ya dubi mafarauci Murad a fusace ya ce"kai tsoho! Da alamu ka rikicin tsufa ya fara mantar da kai dokoki da iyakokin ƙasar Baruda ko? Na san ka sani,kuma ka tabbatar babu wani baƙo da yake zuwa Baruda ya zauna a matsayin garinsu,kai kuma ka kawo jariri,a wanne dalilin?" Rissinawa Murad ya yi, cikin ladabi ya ce"abin bauta ya albarkaci zamaninka ya shugaba na,ina da kyakkyawar niyya da cigaban Baruda a zuwan wannan jaririn Niyya ta na tsaface shi, tunda musulmai sun yar da shi ba sa so,ni zan raine shi,na koya masa al'amuran yaƙi da tsafi,idan ya so sai mu rinƙa amfani da shi yana yi mana yaƙi,da zarar ya kai shekaru goma zan kai shi wajen Sarkin yaƙi ya koya masa al'amuran yaƙi,Ni kuma na cigaba da koya masa al'amuran tsafi,idan ya kai wasu shekaru a fara fita yaƙi da shi,amma ya ka gani?" Tuni fuskar Sarki Jiyaaz da ta fadawanshi ta washe,suka jinjina wa wannan shiri na mafarauci Murad Bayan Sarki ya sallame shi kai tsaye gida ya wuce,Hasa tana zaune tana saƙar tufafin da yake sana'ar ta Murad ya shigo rungume da jaririn fuskarsa a washe Da kallo Hasa ta bi shi tana mamakin inda ta samo jariri,ya miƙa mata shi ya ce"maza yi masa wanka Hasa,ki ba shi nonon akuya bayan ya ƙoshi ki zo za muyi magana " Babu musu ta yi duk yadda ya ce,don so take yi su yi magana ya gaya mata inda ya samo wannan yaron Bayan ta gama shirya shi,har ya koma bacci,ta dawo wajen mijin nata da jaririn, Murad ya amshe shi yana murmushi, sannan ya ce"tsintarshi na yi a dajin Jasus,sai na ɗauko shi,kin ga dama bamu da ɗa,ga shi kuma ina so ya zama mayaƙi tunda ni ban zama ba"daga nan ya yi mata bayanin yadda suka yi da mutanen fada da kuma niyyarsa akan jaririn Sam bai kula da irin mugun kallon da take aika masa ba sai da ta ya gama bayani,tana yi masa kallon banza ta ce "yanzu duk yaran da ake haifa a Baruda Babu wanda ka tsinta sai wanda aka haifa a wata duniyar? To gaskiya ba zan iya ba,ni ba don ma ka ce Sarki ya yarda da zamansa ba da babu abin da zai hana ya baƙunci lahira yau ɗin nan" Murad ya ce"ai ba kyauta za ki kula da shi ba, za'a biya ki,har sai ya kai shekaru goma" Sai a lokacin ta sassauta fuska tana kallonsa ta ce"me za'a biya ni da shi?" Murad ya ce"duk wata za'a biya ki dirhami biyu" Hasa ta yatsina fuska ta ce"gaskiya bai yi min ba,dirhami. ......" "Zan ƙara miki da mudun alkama biyu" Hasa ta yi murmushi ta ce"yanzu na san ka shirya na yi maka rainon yaro" Murad ya yi ɗan murmushi sannan ya ce"a don haka na zaɓi suna na nasara a garin Baruda,na sanya masa suna KAZUZI,daga yau har zuwa ranar da zai bar duniya zai amsa sunan KAZUZI IBN MURAAD!" 💫 Wata iriyar zabura gimbiya Hayat ta yi tana nuna Kazuzi da yatsa amma ta gagara magana,ya yi ɗan murmushi kawai ba tare da ya yi magana ba,da ƙyar ta iya faɗin"dama kai ba ɗan mafarauci Murad bane? A'a,dama kai ba haifaffen garin Baruda bane? Ya aka yi ka san da hakan?" Kazuzi ya ce "za kiji yadda aka yi na sani"daga nan ya cigaba ba tare da ya damu da yadda take kallonshi da tsananin mamaki ba 💫 "Rayuwar Kazuzi a cikin garin Baruda rayuwa ce mai wahala tun yana jariri,Hasa bata damu da shi ba,bata kula da shi sai abin ya ba'a rasawa saboda kuɗin da ake biyanta A haka ya kai shekaru biyu, shi kanshi Murad ba damuwa ya yi da shi sosai ba,sai idan al'amuran asirin ko na tsaface shi da yake yi, bai taɓa damuwa ba idan ta ga yana kuka,bai taɓa jin ya kamata ya lallashe shi ko ya ji damuwarsa ba, ballantana kuma a kai ga yi masa maganin damuwarsa Ga yara kuwa abin babu sauƙi, sanannen abu ne a cikin Baruda cewa Kazuzi ɗan tsintuwa ne, ba'a san asalinshi ba,amma abu mafi rinjaye da ka iya yiyuwa shine Kazuzi ya kasance yana da alaƙa da musulunci,shi kuma musulunci shine abu mafi zama abin tsana da ƙyama a Baruda A dalilin wannan abu ko wasa ba'a barin Kazuzi ya yi da sauran yara,tun bai shekara biyar ba a duniya yake fuskantar tsangwama,har ta kai shi ga daina shiga yara shima Tun Kazuzi yana ɗan ƙarami ya taso da izza,da ji da kai,da nuna isa,sannan bashi da tsoro ko kaɗan,gashi baya ɗaukar raini,hakan ya farantawa Murad sosai,don a zatonsa aikin shi ne yake tasiri fiye da yadda yake zato Tun Kazuzi yana da shekaru biyar Murad ya fara ɗaukarshi zuwa farauta, abin da shi kanshi Murad ɗin ya ɗimauta shi ya firgita shi shine kashe maciji mai dafin gaske da Kazuzi ya yi yana da shekaru shida kacal,wannan abu ne ya sa Murad jin alfahari,ranar da ya dawo daga farauta washe gari ya ɗauki Kazuzi zuwa fada Bayan an yi masa iso cikin farin ciki ya sanar da sabon sarkin da aka naɗa babu jumawa bayan murabus da sarki Jiyaaz ya yi,cewa yana son a fara koyawa Kazuzi al'amuran yaƙi tun daga yanzu, saboda duba ga rashin tsoron shi da jarumtarshi tun yanzu,sarki bai yi musu ba,ya amince,aka kai Kazuzi wajen Sarkin yaki Anudu, don ya fara koya masa al'amuran yaƙi Ko a wajen koyon yaƙin ma Kazuzi yana ganin rayuwa, saboda irin horon da ya kamata a ba shi ba irin shi ake ba shi ba,ba iyaka horon yaƙi ba,ko laifi ya yi ake so a hukunta shi ana gana masa azabar da ta fi ƙarfin shekarun shi Bai taɓa ɗaukar abin da aka yi masa a matsayin zalunci ba, asalima yana ƙoƙarin ganin cewa ya kiyaye dokokin da aka kafa masa,sannan yana ƙoƙarin ganin cewa ya iya abubuwan da aka koya masa a wajen horon yaƙin (Ga masu son VIP group ga number ta nan a ƙasa su yi min magana) #Nusy_bee 08125952284 🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑 ✍️Nusy bee ❤️ Young talented writers association YOTA ❤️ (Under YOTA'S AMAZING PENS) Page 16 Kafin Kazuzi ya cika shekaru tara da haihuwa sai da ya zama ya iya abubuwa da yawa,ya koyi jure zafi da wahala,dama tuni ba shi da tsoro, yanzu rashin tsoron shi ya ƙaru, horon yaƙi kuwa ya iya abubuwan da wani babban ma bai iya ba A gefen mafarauci Murad kuwa yana ta iya bakin ƙoƙarinsa don ya tsaface shi,yana cin nasara sosai,don zuwa yanzu Kazuzi ya zama wani ƙaramin matsafi,da yawa daga matsafan ƙauyen nasu ma ya zarce su,duk da kasancewarsa yaro ƙarami A lokacin ne yaƙi na farko ya tashi tsakanin wata daular musulmai TAYAAR da BARUDA, shekaru goma sha biyar kenan rabon da su gwabza, ƙasar Tayaar ƙasar musulmai ce, sannan shugabansu mutum ne mai adalci da daraja ɗan adam,bayan haka ƙasa ce mai tarin dukiya da ƙarfin runduna, waɗanda ba sa tsoro,kusan sau huɗu kenan ana gwabzawa tsakanin Tayaar da Baruda amma duk da ƙarfin tsafi da na makami sai dai a yi ragas Murad ne ya bayar da shawarar a fara fita yaƙi da Kazuzi,wanda a wancan lokacin shekarunsa tara kacal da haihuwa,shi kansa sarki Akaal ya ga wautar Murad,amma Murad ya ƙarfafe shi da nuna masa duk abin da ake buƙata daga gwarzon mayaƙi a Baruda Kazuzi yana da shi, ƙarfin damtse,rashin tsoro,dabarar yaƙi,iya farauta da ƙarfin tsafi,akan haka aka fara fita yaƙi da Kazuzi " Kazuzi ya ɗago ya kalli Hayat da ta yi shiru jikinta a mace tana kallonsa,ya cigaba da faɗin"na fara fita yaƙi tun ina da shekaru tara da haihuwa,ƙasar farko da na fara fuskanta ita ce ƙasar Tayaar,wato wannan ƙasar taku,duk yadda nake zaton yaƙi ba haka yake ba,ni dai saboda yarinta a lokacin da aka ce zan fara fita yaƙi murna na yi sosai,don na yi tsammanin zan je na ga irin yadda ake ba mu horo ne a yaƙin Ranar fita yaƙin na shirya tsaf don na fita yaƙi,tun lokacin da na saka dakarun Baruda a idanu na na fara jin karaya,amma da yake tsoro ba ya cikin ɗabi'u na sai na dake,wani dakare ya ɗaga ni ya ɗora ni akan doki,aka buga gangar yaƙi muka dumfari ƙofar fita daga Baruda A wani ƙaton fili muka dakata,babu ɓata lokaci dakarun yaƙin ƙasar Tayaar suka iso wajen, ba'a ɗauki dogon lokaci ba ƙazamin yaƙi ya rincaɓe tsakanin Tayaar da baruda Yaƙi na farko da na fara gani da idanu na, sai a lokacin na fuskanci ashe duk wani kwatance da ake koya min iska ne,duk yadda nake da jarumta da dabarun yaƙi duk suna ne,tuni na firgice na fice a hayyacina,ban san lokacin da na zame daga kan dokin na faɗo ƙasa ba,daga nan kuma ban san me ya faru ba sai farkawa na yi naga ɗaya daga cikin ƴan tawagar Tayaar ya kawo ni inuwa,yana zuba min ruwa A firgice na tashi,ya riƙe hannu na da kulawa yana faɗin "sannu ka ji yaro? Ya kake jin jikin naka?ka samu sauƙi?" Karo na farko kenan a rayuwa ta da wani ya nuna ya damu da ni,har yake tambaya ta don ya ji matsala ta,a take na ji ashe duk wata jarumta da rashin tsoro da nake da shi a lokacin da ina Baruda na rashin gata ne,a take na ji ni a matakin yaro mai shekaru na, wanda yake buƙatar kulawar wani babba,yake buƙatar mai son shi da damuwa da rayuwarshi,a take na ji raunina da bai taɓa bayyana ba ya bayyana a karo na farko,a take na faɗa jikin wannan badakare na fashe da kukan da yake fitowa daga ƙasan zuciya,ya rungume ni sosai yana shafa kaina, cikin kwantar da murya ya ce"gani na yi ka faɗo daga doki ana cikin yaƙi, shine na zagaye na ɗauke ka na kawo ka nan don ka huta,ko baka da lafiya ne" Cikin kuka na ce masa"Ni bana son nan wajen,ka ɗauke ni daga nan, tsoro nake ji,kar a kashe ni,bana son ganin jini ka taimake ni ka ɗauke ni daga nan wajen" Dakaren cikin tausayawa ya fara bubbuga baya na yana faɗin "kwantar da hankalin ka,in sha Allah zan ɗauke ka daga nan wajen,ba za ka kara ganin jini ba ka ji ɗana? Kwanta ka huta saboda......"daidai nan maganar ta yanke,kafin ƙiftawar idanu jini ya wanke min jiki,a take kuma jikin dakaren ya saki,na ɗago daga ƙirjinsa a firgice ina kallon Sarkin yaƙin garinmu Anudu da ya ɗaukewa wannan dakaren kai a cikin ƴan daƙiƙu Faɗar irin gigicewa da ɗimaucewa da ta same ni a take ma ɓata baki ne,take na yi suman zaune ina kallon Sarkin yaƙi da yake kallona cikin wani irin fushi da ɓacin rai, kafin na yi wani yunƙuri ya finciki gashin kaina ya ja ni a ƙasa mun koma inda ake gwabza yaƙin,amma kuma ya kai ni wani waje ɗan nesa da wajen ya ɗaure ni tamau a jikin wata bishiya " Kazuzi yana zuwa nan gimbiya Hayat ta kasa jurewa,ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya,ya yi shiru kawai yana kallonta ba tare da ya ce komai ba Sai da ta yi mai isar ta sannan ta ɗago tana kallonsa,cikin rawar murya ta ce"amma iyayenka ba su yi maka adalci ba! Ba su kyauta maka ba,wanne laifi ka aikata kana jariri da har ka cancanci a yasar da kai,gashi irin waɗannan azzaluman mutanen sun ɗauke ka? Tun da nake a rayuwata ban taɓa jin kalar zalunci irin wannan ba,wa yaro ƙarami wanda bai san menene duniyar ba,kawai saboda wata manufa ta zalunci da son zuciya Wallahil Azeem a duniya mutanen Baruda sune maƙiyanka na farko,masu biye musu kuma sune waɗanda suka sa aka jefar da kai,ko da ace iyayenka ne,amma ya aka yi ka kawo war haka?har ka zama gwarzo wanda ake alfahari da shi a Baruda? Ka cigaba da ba ni wannan labarin" Kawar da kai Kazuzi ya yi,ya ce"ki gafarce ni ya shugaba ta,ba zan iya ba ki labari na ba,wannan ɗin ma na yi dana sanin farawa " Wani kallo ta yi masa kafin ta ce"meyasa to?" Kai tsaye ya ce"saboda kin yi kuka,babu abin da na tsana a rayuwa ta kamar kukan mace " Da sauri ta goge hawayenta ta ce"na daina kukan to,kuma na yi maka alƙawarin ba zan sake ba,ka cigaba da labarin to" Murmushi ya ɗan yi,ya ce"zan cigaba zuwa anjuma,amma yanzu ina son zan gana da sarkin yaƙi Ra'uf ne"Hayat ta ce"akan me?meyasa?" Kai tsaye ya ce"ina son cika alƙawarin da na ɗauka ne" Hayat ta miƙe tana murmushi ta ce"fatan alkhairi, Allah ya dafawa rayuwar ka ya ba ka nasara"murmushi ya yi,ya rissina sannan ya nufi hanyar fita daga lambun,itama ta bi shi a baya don komawa sashenta *DAULAR KAIZUR* "Muna matuƙar godiya da amsa gayyata ya shugaba na" Sarki Mu'iz ya jinjina kai cike da izza fuskarsa babu yabo babu fallasa yana faɗin"mhmmm!" Sarki Imran,wanda shine mahaifin gimbiya Nufaisa, mahaifiyar Yarima Jamal,ya sake rissinawa duk da a haife ya yi jika da sarki Mu'iz,ya ce"a gafarce ni ya shugaba na,na zo ne kan batun jikana da kuka kama" Cikin izza sarki Mu'iz ya ce"ya yi laifi ne,ya ci amana gami da zagon ƙasa,kuma sanannen abu ne cewa sarki Mu'iz ba ya yafe cin amana,akwai shaidu masu yawa da suka nuna Jamal a matsayin maci amanar ƙasa,idan ka ga an sake shi sai an gama bincike an tabbatar ba shi da laifi,idan kuma aka same shi da laifi dumu-dumu kuma za'a yanke masa irin hukuncin da ya dace da shi ne" Tuni ƙwalla ta tararwa dattijon,cikin raunin murya ya ce"a gafarce shi ya shugaba na,jikana ba ya cin amana, amma idan an same shi da laifi muna roƙon a yi masa adalci ya shugaba na" Shiru Sarki Mu'iz ya yi, kafin ya ce"ban cika son jayayya ba, don tana fusata ni Hukuncin ɗaya ne,idan ba'a same shi da laifi ba za'a sake shi,idan kuma an same shi da laifi za'a yanke masa hukuncin kisa kamar yadda aka sani Na sallame ku" Babu damar magana, sarki Imran ya rissina yana faɗin"a tashi lafiya ya shugaba na"Sarki Mu'iz ya jinjina kai cikin izza,sarki Imran ya miƙe jiki a saɓule,ya fice daga fadar Al'amarin kuyanga Munaya kuwa yanzu ya lalace sosai,don zuwa yanzu ta daina magana ma ballantana a cigaba da samun wani ƙarin bayani daga bakinta,kuma sarki Mu'iz ya ce lafiyarta ƙalau babu wata cuta da ta same ta,kawai ta yi shiru ne saboda makirci,don haka ya bayar da umarnin a sake sabon salon azabtar da ita,don duk tsiya sai ta faɗi inda ta kai yarima Sahal Gaba ɗaya garin ya sake hargitsewa a cikin kwana biyu kacal,a tsakanin kwana bakwai mutum biyu aka yankewa hukuncin kisa saboda laifuka dabam dabam,hakan ya sake jefa razani da tsoro a zuƙatan al'ummar kaizur Ɓangaren sarauniya Amna kuwa gaba ɗaya duniyar ta canja mata,don yadda ta firgice a lokacin tamkar lokacin da aka sace Yarima Sahal,a duk lokacin da sarki Mu'iz ya ga irin halin da take shiga,da wahala a shiga zaman fada a fito ba'a yiwa wani tsatstsauran hukunci a cikin kaizur ba A dalilin haka wasu daga cikin al'ummar kaizur suka zaɓi su yi hijira zuwa garuruwa dabam dabam, saboda a yanzu zaman kaizur ba zai yiwu cikin kwanciyar hankali ba, saboda kowa a razane yake *DAULAR TAYAAR* "Ya shugaba na! A ƙa'idar dokar ƙasar nan ba'a yin yaƙi a haka,ta yaya za'a rinƙa yayyanka mutum tamkar an samu dankali? Ko a addini Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce idan za muyi kisa mu kyautata kisan,amma an fara sarewa mutum mai daraja hannu,yana cikin malelekuwar azaba sai a ɗauke masa kai,kuma a ce babu zalunci a cikin wannan lamari?a duba magana ta ya shugaba na" Gaba ɗaya fadar ta yi shiru, izuwa yanzu Sarkin yaƙi Ra'uf ya tabbatar da zarginsa na cewa akwai wata a ƙasa tsakanin Amjad da Kazuzi, wanda tunda aka kira shi wajen bayan gaisuwa bai sake ko da ɗaga kanshi ba,yanzu ma da Amjad yake yin wannan bayanin ko a fuska bai nuna alamun zai kare kanshi ba Sarkin yaƙi Ra'uf ne ya katse shirun,ya dubi shugaban dakaru ya ce"to yanzu me kake ganin za'a yi akan wannan batu da ka kawo?" Kai tsaye Amjad ya amsa"a hukunta shi ranka ya daɗe,idan ta kama ma a kore shi daga masarautar nan ko don kasancewar shi kafiri har kwanan yau duk da kyautatawar da muka yi masa hakan ya nuna bai zama Lallai ya amshi musulunci ba" Ra'uf ya dubi Amjad fuska a ɗaure ya ce"kamar baka nan aka yi zamanin sarkin yaƙi Ilyas kenan! Shekarunsa nawa a Tayaar kafin ya amshi musulunci?duka duka kwanan Kazuzi nawa a Tayaar?ko watanni uku fa bai yi ba" Amjad ya rissina ya ce "ya shugaba na shi fa Sarkin yaƙi Ilyas dama can ƙasar su ba su da aƙidar ƙi da tsanar musulunci kamar Baruda,shima a haka ya ɗauki shekaru kafin ya karɓi musulunci,ko iya wannan ya isa ya nuna idan kafirci ya yi shura ba safai karɓar musulunci yake yiwuwa ga mutum ba" Sarki Iyaad ya dubi Amjad ya ce"akwai asalin kafirai tun a zamanin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama waɗanda aka yi tunanin ko ba za su karɓi musulunci ba,amma a ƙarshe suka zama manya-manyan jiga-jigai a musulunci Iya wannan ya isa ya sa ka gane ba mutum ko ra'ayinsa ne shiriya ba, shiriya ta Allah ce Sanna magana ta biyu, akan batun irin kisan da ya yiwa sarki Al'as,kai ma ka ce ba musulmi bane,to me ya shafe shi da dokarmu kuma? A rinƙa sara ana duban bakin gatari Amjad " Cikin baƙin ciki Amjad ya rissina yana faɗin"a gafarce ni ya shugaba na " Sarki Iyaad bai sake bi ta kanshi ba ya mayar da hankali kan Kazuzi da duk wannan cecekucen da ake yi bai ko da ɗaga kai ba, ballantana ya nuna ya san me suke yi, sarki Iyaad ya dube shi da kulawa ya ce "Kazuzi! Haƙiƙa ka cika gwarzo,ka yi aikin da bai zama lallai dakaru ɗari biyar su iya ba,kai ɗin cikakken namiji ne kuma sadauki jarumi Na yarda da jarumtar ka,na yarda da sadaukantakarka,mafi girman abun sha'awa shine riƙon amanarka da gaskiyar ka, wadda ba kowa ake samu yake riƙewa kamar yadda ka yi ba Sannan abu na gaba ina mai sake kwaɗaita maka addinin tsira addinin rahama,addinin musulunci,ban yi maka dole ba,amma zan yi fatan na ganka a cikin musulunci,da tabbas na yi alfahari da farin ciki da wannan ranar,sannan abu na gaba da ni da jama'a ta suna miƙo saƙon godiya na ƙoƙarin ka a wajen yaƙi,kuma muna yi maka fatan samun lafiya mai ɗorewa musamman da ka gamu da wanna tsautsayin,ina yi maka fatan alkhairi Kazuzi ibn Murad " Sai a lokacin Kazuzi ya gyara zama yana jan ƴar ƙaramar ajiyar zuciya, cikin nutsuwarshi ya ce"ya shugaba na a karo na farko ina jin mafita ta rayuwa ta wuce amanar da na ɗauka A karo na farko a rayuwa ta na zaɓi cigaba na fiye da farantawa wasu Ranka ya daɗe ina son na shiga addinin tsira addinin aminci,wato musulunci!!!" *Ya kuke ganin rayuwar Kazuzi a matsayin musulmi?me kuke tunani game da rayuwarsa ta baya?sannan ya kuke ganin alaƙarshi da gimbiya Hayat zata kasance?ya zata kaya tsakanin shi da Sarkin dakaru Amjad?ya kuke ganin chakwakiyar masarautar kaizur ne???ku biyo alƙalamin Nusy bee kawai😁* Wannan shine ƙarshen free pages,ga duk mai son cigaban labarin regular #500 ne kacal, VIP kuma #1000,kar ku bari a yi wannan tafiyar babu ku 💃💃💃💃 Ga masu son payment za su biya #500 kacal ga regular,ga VIP group kuma 1k,sai a tura ta wannan account ɗin 8125952284 Nusaiba Ibrahim Rimi moniepoint,sai a tura shedar biya ta wannan number 08125952284 a Whatsapp,ku dai kar ku bari a yi babu ku, yanzu za'a fara wasan💃💃💃💃 #Nusy_bee 08125952284 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku

Chapter 8 of 9