Share this page
5 / 9
kwance a gefen gadonta ta buɗe baki, ihu ta kurma tana nuna ta da yatsa,su Huda suka gigice, don da alamu ba sa ganin abin da take gani,nan da nan suka rikice, ɗaya kuyangar mai suna Humaida ta fice daga ɗakin da gudu ta nufi inda su mai martaba suke don a nema mata iso ta sanar da abin da ya faru Kafin sarki Iyaad ya zo inda Hayat take tuni ta suma,abin mamaki har yanzu babu wanda ya ga komai a ɗakin,mai maganin masarautar aka kira don ya duba ta Sai dai tsawon kwana goma tun daga wannan ranar gaba ɗaya gimbiya Hayat ta zama wata iriya,bata da aiki sai zabura da firgita,gashi kuma har yanzu lokacin ta kasa magana ballantana ta gayawa mutane abin da yake faruwa da ita,aikin kenan daga kuka sai zabura 💫 Duk abin da yake faruwa Kazuzi yana da masaniyar komai,sai dai bai taɓa nuna ya sani ɗin ba ko da a fuska ne,amma abin da yake ji game da halin da gimbiya take ciki yana damunshi Don haka a yau bayan ya fito daga lambun gimbiya da yake gyarawa kullum duk da bata fitowa yanzu,kai tsaye ya wuce wajen ɗakunan dakarun gidan,yana zuwa bai yi wata wata ba ya faɗa ɗakin da yake buƙata ba tare da wata shakka ko tsoro ba Dakare Amjad da yake zaune tare da matarsa ya yi firgigit yana kallon Kazuzi da ko sashen da matarshi take bai kalla ba,ya ƙure shi da idanu, Amjad ya miƙe a firgice yana kallonshi, kafin ya ce"mahaukacin ina ne kai da za ka shigowa mutane ɗaki ba tare da neman izini ba? Ko a addinin naka ba'a koya maka ladabin sanin dokar shiga waje sai an nemi izini ba? musamman idan mutum yana tare da matarsa?" "A addini na an koya min ladabi da neman izini ne daga waɗanda suka cancanci hakan kaɗai,don haka yanzu magana nake so na yi da kai,za ka wuce ta lalama ne ko kuwa?" Amjad ya jefe shi da kallon tsana, kafin ya yi magana matarshi ta fara magana cikin fushi "Tsinuwa da la'nar Allah gami da azabarshi su tabbata ga zindiƙi kafiri kuma azzalumi irinka,wanda bai san darajar rai ba ballantana ya san darajar wani, kuma ka gaggauta fice min daga ɗaki,ko na kai ka ƙara inda za'a ƙarar da rayuwarka" Kazuzi ya kalli yadda take faɗa da tsananin ɓacin rai,amma sai ya ɗauke kai ya mayar da kanshi ga dakare Amjad da yake watsa masa nashi kallon tsanar,bai damu ba ya ce"ka wuce mu yi magana,idan kuma ba za ka fita ba babu laifi sai mu yi a gaban matar taka, duk da cewa ba abin mamaki bane idan ya zamana kai da ita abokan cin mushe ne" Dakare Amjad ya ce"duk abin da za kayi kar ka fasa,amma kai ba ka isa ka saka na fito daga ɗakin matata ba, fita na ce" "Zan fita,amma sai ka warware abin da ka yi" Kallonshi Amjad ya yi a ɗan ruɗe, Kazuzi bai damu ba ya ce"ka warware abin da ka yi mata tsawon kwanaki, saboda ita ba ƴarka ko matarka ba ce shiyasa za ka cuce ta,idan har kai namiji ne ubanta za ka cewa ya ɗaura ɗamara,kai ma ka ɗaura ku ɗauki takubba a ba ku fili ku gwabza Namijin gaske ba ya laɓewa a bayan tuggu da makirci ko asiri ya yi cin amana" Dakare Amjad cikin rashin damuwa ya ce"ba zan warware ba! Idan har tsafi abin ƙi ne kai bai kamata ka faɗi hakan ba, saboda shine ya gina daularku ta zalunci Baruda,da shi aka raine ka ka zama mutum,kuma shine yake ba ka nasarar yaƙi Kuma da kake maganar namiji,idan Ni da na laɓe a bayan asiri don ganin bayan yarinyar don ɗaukar fansa,to kai kuma menene makomarka? Ba zaka iya ɗaukar fansar ba kenan?tsafin naka ya daina tasiri ne? shi yasa ka zaɓi zama bawan da mace ta mayar tamkar karenta? Kar ka ɗauka ban san irin wahalalliyar rayuwar da ka yi a Baruda ba,amma ka zaɓi ka zamar musu bawa don baka da galihu daga kai har wanda ya tsince ka,don sanannen abu ne kai ɗin baka da asali!idan ubanka Murad bai sanar da kai ba ni yanzu na sanar da kai,ya ɗaura maka baƙar laya a damtsenka na hagu wadda take ba ka ƙarfin da za ka iya karawa da rundunar da bata da iyaka,ni na bawa Waleed izinin ya tsinke ta, don yana daga cikin matakin nasara ta shine na fara karya ka,tabbas sai na ɗauki fansa akan abin da ka yi min na kashe min yara na Na samu nasarar farko ta hanyar ganin bayan budurwar ka Malli,zan yi nasara akan Sarkin Tayaar ta hanyar ganin bayan tilon ƴarshi,kuma babu wanda ya isa ya ya dakatar da ni!!!" Tabbas maganganun dakare Amjad sun yi tasiri a zuciyar Kazuzi, zuciyarshi ta yi rawa musamman ambatar Malli da Amjad ya yi,amma sai ya dake ya yi murmushi,sannan ya fara magana "Ka yi gaskiya! Tabbas da tsafi aka raini Kazuzi,amma idan ka yi tunanin tsafi shine ƙarfin Kazuzi baka yiwa kanka adalci ba, kai ganau ne ba jiyau ba,ka ga asalin Wanene Kazuzi lokacin da ka tura damisa ta farmaki gimbiyar Tayaar Maganar Malli kuma haka zancen ka yake,malli ita ce dukkan rayuwa ta,mutuwar ta daidai yake da rasa farin ciki na,ka yi nasara sosai da ka saka aka kashe min ita Sai magana ta gaba,me ma ka ce? yadda ka ga bayan Malli sai ka ga bayan gimbiyar Tayaar ko?za mu gani idan za ka iya hakan,ban zo nan don bani da yadda zan yi ba,ko don ban san yadda zan yi da abin da ka yiwa ƴarinyar da bata ji ba bata gani ba,sai don ka san cewa ina sane da abin da ka yi,kuma idan ka cigaba kamar yadda na faɗa za kayi nadama mara amfani a rayuwarka A ƙarshe,da alfahari nake faɗa cewa Ni Kazuzi ibn Murad tsintacce ne kamar yadda ka faɗa, wulaƙantacce a Baruda kafin na zama mayaƙi,kuma a ƙarshe bawan mace,ina alfahari da hakan tunda ban kasance maci amana ba a tsawon shekaru na rayuwa ta! Ina yi maka jajen ranar da asirinku zai tonu ku ji kunya a bainar jama'ar da suka ɗauki yarda suka ba ku,kuma ba ku cimma mugun ƙudirinku akansu ba,don muddin Kazuzi yana cikin Tayaar har abada ba za ku cimma mugun ƙudirinku ba"yana kai wa nan ya juya da takunshi na isa ya fice daga ɗakin ba tare da ya sake saurarar abin da za su faɗa ba (Ga masu son VIP group ga number ta nan a ƙasa) #Nusy_bee 08125952284 🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑 ✍️Nusy bee ❤️ Young talented writers association YOTA ❤️ (Under YOTA'S AMAZING PENS) Page 10 Da kallo Amjad da matarshi suka bi Kazuzi da ya fice daga ɗakin babu alamun damuwa a kan fuskarsa,matar Amjad ta fashe da kuka tana riƙe hannun mijinta, cikin kuka ta ce"yanzu menene abin yi abu Huzaifa? Ina tsoron kar wannan kafirin yaron ya tona mana asiri,mu ba muyi hakan don wani abu ba sai don zaluncin da aka yi wanda ya zama silar mutuwar yaranmu uku,ka je ku yi magana da shi" Kallonta Amjad ya yi, cikin taushin murya ya ce "kar ki damu Layla,babu abin da zai iya,barazana ce kawai" Layla ta girgiza kai ta ce "to ka warware abin da ka yiwa gimbiyar Tayaar,a tsorace nake da abin da zai faru, sarki Iyaad zai iya yanke mana hukuncin kisa akan wannan abu da muka yi" Girgiza kai ya yi, cikin taushin murya ya ce"na gaya miki babu abin da zai iya,yanzu ba sai anjuma ba zan tsaface shi,babu abin da zai iya akai,mantawa ma zai yi da abin da ya gani,ki kwantar da hankalin ki" Hankalin Layla ya kasa kwanciya,ta dubi Amjad ta ce"ko ka manta ne Abu Huzaifa? Shima matsafi ne fa,babban matsafi kuma,ba ka tunanin zai iya ɗaukar matakin kare kanshi,kuma a karshe ya ce zai yi mana raddi?" Ƴar dariya Amjad ya yi, cikin nishaɗi ya ce"a dalilin haka ya sa na saka Waleed ya yanke layar da aka ɗaura masa a dantsensa na hagu,duk wani sihiri da tsafi da yake ji da shi na karya alkadarin " Murmushi Layla ta yi zuciyarta na sakewa,ta jinjina kai ta ce"na gamsu abu Huzaifa,mu yi ƙoƙarin ganin bayan wannan azzalumin,ban taɓa tsanar wata halitta ba Kamar yadda na tsane shi,yara na huɗu ya kashe min uku ya bar min ɗaya "ta ƙarasa magana cikin kuka sosai" Zuciyar Amjad ta girgiza,ya dafa kafaɗarta, cikin taushin murya ya ce"ki kwantar da hankalin ki Ummu Huzaifa,nasara akan wannan fajirin kamar mun samu mun gama ne in sha Allah" 💫 Yana barin ɗakin shugaban dakaru Amjad kai tsaye ya wuce ɗakinshi da aka ba shi bayan an fito da shi daga ɗakin duhu, ɗakin bashi da tazara da lambun gimbiya Hayat,a lokacin da aka ba shi ɗakin akwai kayan more rayuwa fiye da lokacin da yake rayuwarsa a Baruda,amma sai da gimbiya Hayat ta saka aka fitar da komai,aka bar masa ɗan mayafin da zai shimfiɗa da wanda zai rufa Yana zuwa ya zauna akan dandagaryar daɓen da ke ɗakin,ya haɗe kanshi da gwiwa yana tunani,shi ba mutum bane mai yanke hukunci cikin fushi,amma tabbas ba don haka ba babu wanda zai kalli idanun shi da alfahari ya gaya masa shi ya kashe masa Malli amma ya rabu da shi,da sai ya ɗauke kanshi da takobi idan ya so komai zai biyo ya biyo daga baya Bai taɓa jin zafin gorin rashin asali da aka yi masa a Baruda ba,amma bai san meyasa ba yau karo na farko sai ya ji zafin gorin da Amjad ya yi masa,ya sauke zazzafan numfashi, lokaci guda kuma ya miƙe zumbur kamar wanda aka tsikara ya fice daga ɗakin Kai tsaye sashen gimbiya Hayat ya nufa,tunda yake a tsawon rayuwarsa bai taɓa shiga ba,ko da ya kasance a cikin masu yi mata hidima ba ya wuce aikace-aikace ko kuma kula da lafiyarta,amma yau kanshi tsaye ya nufi sashen A bakin ƙofa ya gamu da Huda, fuskarshi babu walwala ya ce"ina son ganawa da gimbiya" A ɗan daburce ta ce"am.....um... Gimbiya?dama....." Wani mugun kallo da ya watsa mata ne ya sa ta matsa masa ya wuce jikinta yana karkarwa,bai sake kallonta ba ya kutsa kai cikin ɗakin gimbiya A kwance ya ganta tamkar gawa,mai maganin gargajiya da aka kira yana ta ƙoƙarin gano abin da ya same ta,amma yadda a tsawon kwanakin nan bai samo komai ba yanzun ma hakan take,gefe kuma ga kuyanginta guda biyu Humaida da Bilƙees, Kazuzi ya dube su gaba ɗaya fuska babu rahama, cikin dakakkiyar muryarshi irin ta mazan fama ya ce"ina buƙatar ganin kowa ya fita" Mai magani ne ya ɗago ya kalle shi,dama su Humaida da Bilƙees tuni jikinsu ya fara kyarma,mai magani ya ce cikin kwantar da murya "Haba yaro! Me za ka iya yiwa gimbiya?menene dalilin da ya sa kake so kowa ya fita alhalin kai baligin namiji kana ɗakin?menene dalilin....." "Cewa na yi kowa ya fita,ba magana na tambaya ba"ya faɗa cikin tsawa Da gudu suka fara fita a tsorace,suna daf da fita ya ce "ke!"cikin tsawa A tsorace Humaida da Bilƙees suka tsaya jikinsu yana kyarma,da yatsa ya nuna Humaida ya ce"ke! Zo nan,ke kuma fice ki ba ni waje"a guje Bilƙees ta juya ta fice daga ɗakin kamar zata kifa don tsoro A razane Humaida ta ƙaraso wajen da Kazuzi yake, tana zuwa ta zube a gabanshi,tana shirin fara gaishe shi cikin tsawa ya ce"ɗauko min abin da shugaban dakaru Amjad ya ba ki ki ɓoye a ɗakin nan" Ƙara firgita ta yi,tana shirin fara rantse-rantse ya daka mata tsawa,take ta fashe da kuka,tuni fitsari ya kubce mata,ya sake cewa cikin dakewa "fito min da abin da Amjad ya ba ki,kar ki bari na sake tambaya" Cikin kuka Humaida ta ce"ka yi min aikin gafara,na rantse bai ba ni komai ba" "Ƙarya kike yi! Tunda kika ji na faɗi haka ya kamata ki san na san komai,don haka ba ni kawai" Tana kuka ta ce"na gaya maka ban san komai ba akai,ka gafarce ni don...."damƙar gashin kanta da ya yi da tsananin ƙarfi,hakan ya sa ta yi ta ƙwala uban ƙara, cikin kukan azaba ta ce"zan ɗauko,ka yi min afuwa zan ɗauko maka" Sakinta ya yi yana kallonta,jiki na rawa ta miƙe ta nufi bayan ƙayataccen gadon gimbiya Hayat ta zaro wani ƙulli,ta ƙaraso ta durƙusa ta miƙa masa,bai amsa ba ya ce"kwance ƙullin " Babu musu ta kwance jikinta yana rawa,wani dunƙulallen abu ne a cikin tsohon tsumman da aka ƙulle ya bata umarnin ta fasa shi,babu musu ta lalubo abin fasawa ta fasa,take gimbiya Hayat ta kama wata iriyar jijjiga, Kazuzi ya mayar da idanunshi kanta amma bai yi yunƙurin zuwa inda take ba Sake mayar da kallonshi ga Humaida ya yi, wadda take durƙushe jikinta yana ta rawa, hawaye wani na korar wani,cikin kakkausar murya ya ce"wuce ki rufe ƙofar ɗakin nan" A gigice ta miƙe tana faɗin "in tafi?" Wani mugun kallo ya watsa mata,a gigice ta ce"ka yi min aikin gafara"sannan ta wuce bakin ƙofar ta rufe,ya mayar da kallonshi ga Hayat da ke kwance a ƙasa, zuwa yanzu ta daina jijjigar,tana kwance ta yi shiru,a kausashe ya fara magana "Daga yau bana buƙatar ƙara ganinki a duk wani abu da ya shafi gimbiya,ki san me za ki gaya wa mutane,amma na haramta miki zuwa inda take,idan kuma kika kuskura na ganki ko a kewayen ɗakinta ne,kar dai ki manta nine KAZUZI IBN MURAAD,ina nan a yadda kika san ni ko na ce kike jin labari na, bambancin wajen zama kawai na samu,don haka tashi ki fice daga ɗakin nan" Babu musu ta miƙe jikinta yana kyarma ta nufi ƙofar ɗakin,a kausashe ya ce"zo ki kwashe tarkacenki"babu musu ta dawo ta durƙusa ta kwashe abin da ta kwance, sannan ta koma bakin ƙofar ta buɗe ta fice, Kazuzi ya mayar da kallonshi ga gimbiya da ke kwance Bai yi mamakin ganin idanunta a buɗe ba tana kallonshi,don ya san zuwa yanzu abin da aka yi mata ya sake ta,ya rissina a gabanta kanshi a ƙasa kamar yadda ya saba, cikin taushin murya, Kamar ba shine ya gama daka tsawa yanzu ba ya ce"fatan tsawon rai mai albarka da lafiya mai amfani ga gimbiyar Tayaar " "Kazuzi ibn Murad!ba ka san sunana ba?"ta faɗa cikin sanyin murya tana ɗan murmushi Kallonta ya yi a ranshi yana mamakin murmushin da ya ga ta yi,kafin ya yi magana sai ga sarki Iyaad da Sarkin yaƙi da dakare Amjad sun shigo a firgice, Amjad ya nuna Kazuzi da ke durƙushe gaban Hayat yana faɗin "ka gani ya shugaba na! Wannan fajirin ya kori kuyangi da mai maganin gimbiya don ya samu damar aikata alfasha da ita,ya shugaba na wannan bawan yana da tsaurin idanu da yake tunanin zai iya aikata alfasha da gimbiya,ya kamata a ladabtar da shi ko hakan zai zama darasi ga ƴan baya" Cikin tsananin ɓacin rai da baƙin ciki sarki ya dubi Sarkin yaƙi ya ce"a kama shi "a take gimbiya Hayat da ke kwance ta yunƙura tana ƙoƙarin yin magana,a ɗan tsawace Kazuzi ya ce"A'a ya shugaba ta! Abu ɗaya nake so da ke, na san kin ji komai,zai yi kyau ki rufa asiri ko don sake bayar da dama, mutum zai iya dawowa kan hanya idan aka ba shi lokaci ba'a hukunta shi akan laifin da aka san ya aikata ba"yana kai wa nan dakarun da suke tare da Sarkin yaƙi suka damƙe shi, ba tare da ɓata lokaci ba suka yi waje da shi Hayat da ke kwance ta bi su da kallo tana hawaye,sarki Iyaad ya ƙaraso kusa da ita hankali a tashe yana faɗin"sannu ƴata! Bai yi miki komai ba dai ko?"bata iya cewa komai ba,ya kama ta ya zaunar da ita,da idanu ya bawa bayi da sauran dakarun da suke ɗakin umarni, suka rissina sannan suka fice daga ɗakin Ya yi farin ciki sosai saboda alamun sauƙi da ya gani a tare da ƴar tashi,duk a tunaninsa aikin mai magani ne,ya kwantar da ita akan gadon sannan ya juya ya fice daga ɗakin *DAULAR KAIZUR* "Na san kin san su wanene suka sace min ɗa,ko na ce da haɗin bakinki aka sace shi,har zuwa yanzu na kasa gane dalilin ki na aikata hakan, Munaya! gobe idan Allah ya nuna mana da rai da lafiya, za'a sake fitar da ke a yi miki rajamu Kamar yadda yake a ƙa'ida duk shekara,idan na ga dama zan bari mutane su jefe ki har mutuwa,don haka tun wuri ki gaya min,ina ɗana Sahal yake? Kasancewar shi a raye ya tabbatar min da cewa kin san inda yake,amma a kwanakin nan na ga alamu yana cikin matsala, Munaya,ina ɗana Sahal yake?" "Allah ya ja da ran shugaban Daular kaizur,na yi magana tun a farko,ban san inda Sahal yake ba,Nima ba zan so ya nisance ni tsawon shekaru ba, aƙalla ko gani na yi ya wuce zan ji sanyi a raina Idan har baka gamsu da maganar da nake ta maimaitawa ba tsawon shekaru ashirin a yiwa mutane izinin su jefe ni har mutuwa" "Munaya!"sarki Mu'iz ya daka mata tsawa, cikin ɓacin rai ya cigaba "Da alamu taurin kai da izza tana damunki,yanzu ba sai anjuma ba zan saka a yi min maganinki"ya mike a zafafe ya fita,jum kaɗan ya dawo da wasu zaratan dakaru su uku,ya dube su fuskarshi a matuƙar haɗe ya ce"ku yi mata hukunci,kar ku saurari kukanta,kar ku saurari magiyarta,kuma kar ku saurara mata,kar ku duba kasancewarta mace ko don shekarun girma"yana kai wa nan ya juya a fusace,su kuma suka kama Munaya don aiwatar da aikin su Iya azaba sun ganawa Munaya amma ta dake,ko sau ɗaya bata nuna musu raki ba,sun dake ta,da suka ga dukan bai yi ba suka ɗaure ta kanta a ƙasa suka rinƙa nana mata ƙarfen da ya yi ja a wuta,sai da suka kwashe fatar bayan nata duka, sannan suka lafta gishiri a wajen,bayan sun gama ɗanyen aikin suka sake mayar da ita suka ɗaure ta sannan suka fice daga ɗakin Washegari da sassafe aka fito da ita bainar mutane,sarki Mu'iz da muƙarrabanshi suna zaune a inda suka saba zama, cikin su har da sarauniya Amna, Yarima Zaffar da Yarima Jamal,aka kai ta inda aka saba ɗaure ta,bayan komai ya natsa shugaban dakaru na ƙasar kaizur,wato Dawud ya dube ta ya ce"Munaya! Sarki ke umartarki ki sanar da mutane inda kika ɓoye yariman kaizur,don tabbas idan kika yi turjiya ba za ki kai wata shekarar ba" Shiru ta yi tsawon wasu daƙiƙu, Dawud ya sake maimaita abin da ya gaya mata, kanta a ƙasa ta ce "A yi min afuwa ya shugaba na Tabbas ni mai laifi ce a cikin MASARAUTAR KAIZUR,kuma na san laifi na ya wuce yadda za'a yi min afuwa Amma ina roƙon wannan sarki mai adalci da ƙaunar talakawan shi,da ya bincika jama'ar da ke cikin fada,tabbas a cikinsu aka samu wanda ya sa aka ɗauke Yarima,ni amfani aka yi da ni,tun daga lokacin da aka kawo ni MASARAUTAR KAIZUR zuwa lokacin da aka sace Yarima,an cimma wani buri ne,kuma wannan burin da ake son cimmawa ba iyaka kan yariman kaizur ya tsaya ba,har da kai ya shugaba na Idan na faɗi wani abu wanda ba daidai ba ina roƙon tausayawa da rangwame daga wajen wannan sarki mai adalci #Nusy_bee 08125952284 🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑 ✍️Nusy bee ❤️ Young talented writers association YOTA ❤️ (Under YOTA'S AMAZING PENS) Page 11 Shiru ilahirin wajen ga ɗauka duk da yawan mutanen,jikin yarima Jamal yana rawa ya miƙe ya nuna ta a kiɗime,ya ce"me kike nufi? Annamimanci za kiyi mana? ƙasƙantacciyar baiwa irinki zata ƙulla makirci a cikin masarautar nan? wacece ke da kika isa ki raba abin da kika zo kika samu tsawon shekaru?" Kallonshi ta yi kai tsaye ta ce"Allah ya taimake ka,a tsawon zamana a kaizur ba'a taɓa kama ni da wani laifi mai kama da makirci ko tuggu ba, kuma ko yaudara da cin amana da ake zargi na da shi ina da tabbacin za'a gane gaskiya nan da ɗan lokaci ƙalilan Kamar yadda na faɗa da farko,ya shugaba na a jarraba,a gwada binciken" Sarki Mu'iz ya dube ta a fusace ya ce"Munaya! Zuwa yanzu ya kamata ki gane mu ba ƙananan yara bane!har tsawon wanne lokaci za ki ɗauka kina raina mana hankali?" "Ka gafarce ni ya shugaba na,ban kai na raina muku hankali ba,iya abin da na sani nake faɗa " Sarki Mu'iz zai sake magana sarauniya Amna ta dakatar da shi,da hawaye a idanunta ta dube shi ta ce"a jarraba bincikawar ranka ya daɗe, ba'a ƙin ta mutum "ta dubi dakarun da ke tsaye suna jiran umarni ta ce"a mayar da ita inda take kulle,a canja nau'in azabtarwa,a rinƙa ba ta abinci sau ɗaya a rana,ruwa ma haka,kar a dake ta, a yi mata wannan horon na tsawon sati guda mu gani, sauran al'umma kuma za su iya tafiya,an sallami kowa"tana kai wa nan dakarun suka rissina,suka kama Munaya suka wuce da ita kurkuku, sauran mutanen suka fara watsewa suna tsinewa da yiwa Munaya Allah wadai *DAULAR TAYAAR* Tunda Kazuzi ya zo Tayaar ba'a taɓa shayar da shi narkon azaba irin wanda ake yi masa yanzu ba, gaba ɗaya ya fice a hayyacinshi,banda aiki mai tsanani ga horon yunwa,ga wahalhalu kala-kala,haka ya kasance a cikin wannan halin tsawon kwanaki uku bisa jagorancin badakare Amjad wanda duk da wannan azabar da yake gana masa har yanzu nazari yake yi ta hanyar da zai ga bayanshi Daga ɓangaren gimbiya kuwa,tsawon Wadannan kwanakin tana ƙarasa jinya ne,bata fita ko'ina,kuma idan sarki Tayaar ya shigo inda take baya taɓa yarda ya ba ta dama ta yi masa magana akan Kazuzi,hakan yana matuƙar damunta Sauran kuyangin nata abin ya yi musu daɗi, saboda yawancinsu sun tsani Kazuzi saboda halayensa,don haka sun yi farin ciki sosai da halin da Kazuzi yake ciki,a cikin su Huda ce kawai bata cikin farin ciki, asalima tunda aka kama Kazuzi bata ƙara kwana guda cikakke ba da farin ciki,kuma hakan yana da alaƙa da yadda ta ga uwar ɗakin nata Hayat Yau kam Hayat ta tashi da wata iriyar damuwa,ko abinci kasa ci ta yi,sai kuka kawai,har lokacin abu biyu yake damunta,cin amanar da dakare Amjad da kuyangarta Humaida suka yi mata,don tabbas ta ji komai,sai kuma kama wanda ya ceci rayuwarta har sau uku a matsayin mai laifi dalilin haka yau ta kasa cin abinci,ta kasa walwala yadda ya dace Huda ce ta kai wa jakadiya Rubayya labarin abin da yake faruwa,babu ɓata lokaci ita kuma ta nemi iso wajen sarki da yake zauren shi na hutawa yana miƙe ƙafa, kuma ba tare da ɓata lokaci ba ta sanar masa da abin da ya faru Cikin damuwa ya ƙaraso zuwa ɗakin gimbiya Hayat,da a yanzu iya Huda ce kawai baiwarta da ta yarda ta raɓe ta,bayan sarki ya shigo da sallama Huda ta rissina ta gaida shi,ya amsa sannan ta fice daga ɗakin A gefen gadon da Hayat take zaune ya zauna, cikin rarrashi da nuna ƙauna ya dafa kafaɗarta,bata yi wata-wata ba ta faɗa jikinshi tana kuka mai tsuma zuciya Ɗan bubbuga bayanta ya fara yi alamar rarrashi,a hankali kukan nata ya fara raguwa, cikin kwantar da murya ya dube ta ya ce"yanzu gaya min, Wanene ya taɓa gimbiyar Tayaar ne?" "Abby don Allah ka sa a sake shi, don Allah Abby"ta faɗa cikin kuka Da kallon mamaki ya bi ta,kafin ya ce "Wanene kike magana akai?" "Kazuzi Abby Haƙiƙa Abby baka yin abu ka yi nadama saboda dogon nazari da kaifin tunani irin naka,a wannan karon ma ina roƙon ka yi amfani da wannan baiwar taka akan Kazuzi,kar ka yanke masa hukunci daga baya ka zo kana yin danasani" A hankali Sarki Iyaad ya girgiza kai ya ce "laifin Kazuzi ya kai na hukunta shi ne gimbiya Menene dalilin da ya sa kaf matan masarautar nan babu wadda ta yi masa sai ke? A matsayin shi na bawa,kuma wanda bai amshi musulunci ba? A ƙa'idar Tayaar,ke ma kin sani da tuni ba ya raye,amma na saka aka ɗage hukuncin don kawai na nuna masa ƙauna,ya ji cewa duk da kasancewarsa wanda bai amshi addinin musulunci ba amma hakan bai saka na ƙyamace shi ba,amma sai gashi na ganshi a ɗakinki,ya kike tunanin zan ji?kuma me yake nufi da abin da ya faɗa kafin dakaru su fitar da shi?" A hankali tana girgiza kai hawaye suna zubo mata ta ce"ba abin da kake tunani bane Abby Da za ka ji abin da ya yi godiya za kayi masa,ba ka sa a kama shi ba, Abby kar ka manta a baya na tsani Kazuzi,amma nagarta da halayensa

Chapter 5 of 9