ya girgiza kai ya ce"a Tsawon rayuwar Kazuzi bai taɓa zama a gida tare da mata alhali maza sun fita yaƙi ba,don haka nima zan bi ku "
Sarkin dakaru Amjad ne ya sake yin sauri wajen faɗar"ko kuma so kake ka ce za ka samu yan'uwa da za ka yaƙe mu tare da su ba?
Mu mun wace yaudararka yaro!"
Wannan karon cikin idanu Kazuzi ya kalli shugaban dakaru Amjad ya ce"cin amana da zamba cikin aminci ba ɗabi'ar namiji ba ce,sharri da makirci,sai mata,ko maza ƴan daudu, Kazuzi kuma namiji ne!!!"
A zafafe shugaban dakaru ya kalle shi saboda ya san me yake nufi da maganarshi, sauran dakarun kuma abin ya yi matuƙar burge su, Sarki Iyaad ya dafa kafaɗarshi ya ce"muna matuƙar alfahari da kai sadaukin sadaukai,maza shirya,fatan Sa'a jarumi na"Kazuzi ya rissina sannan ya miƙe ya koma cikin rukunin ɗakin bayi inda nashi ɗakin yake
Da shirinsa cif ya fito don fita yaƙi,,takobinsa a rataye a bayansa,hannunsa riƙe da garkuwar yaƙi,sai sauri yake yi don ya cimma sauran dakaru,don baya son a jira shi,kar ya shiga haƙƙin mutane
Tsayawa ya yi da mamaki yana kallon Hayat da take tsaye a bakin sashenta,ya ƙarasa gabanta ya rissina ya ce"Barka da wannan lokaci ya shugaba ta"
Kallonsa take yi kawai, saboda wannan tashin yaƙin ya ɗaga mata hankali sosai,a hankali ta ce"har da kai za'a fita?"
Jinjina kai ya yi,a hankali ya ce"haka ne ya shugaba ta"
"Me yasa za ka je?"ta tambaya da damuwa ƙarara a fuskarta
Kallonta ya yi,a hankali ya ce"ke ma kina zargin zan ci amana ne na yaƙi mutanen Tayaar ko?"
Buɗa idanu ta yi da mamaki ta ce"menene ya kawo wannan maganar?
Na ga mun yi da kai za ka bani labarin Malli,kuma yanzu na ga ka shirya za ka bi su Abeey"
"Ba ɗabi'ar namiji ba ce zama a gida a lokacin da maza suka fita yaƙi"
"Yaƙi fa ba gasa ba ce Kazuzi, musamman namu na musulmai,ana yi ne don ɗaukaka kalmar Allah,abin zai yi wani iri idan aka fita da kai a matsayin ka na wanda ba musulmi ba"
Kamar daga sama ta ji ya ce"to babu laifi idan nima na zama musulmi?
Zan iya zuwa idan na sauya zuwa musulmi?"
"Za ka zama musulmi ne don za ka je yaƙi ko za ka zama musulmi ne don Allah?"
"Ina son na musulunta idan an ba ni dama,na ɗauki lokaci musulunci yana burge ni,har ma na kasance ina aikata wasu ayyukan na musulmi,wasu lokutan ma ba tare da na sani ba,ban san wanda zan tunkara bane,daga baya kuma na so na same ki amma kika kwanta jinya,kuma ƙarshe ga jarabtar da ta same ni "
Kabbara mai ƙarfi gimbiya ta yi idanunta suna cika da ƙwalla,ya miƙe yana ɗan murmushi ya ce"na yi miki alƙawarin dawowa Tayaar a matsayin musulmi ya shugaba ta"yana kai wa nan ya wuce da sassarfa inda dakaru suke jiranshi
Gimbiya Hayat ta bi shi da kallo, hawayen farin ciki suka zubo a kan fuskarta,a bayyane ta fara faɗin"alhamdulillah! alhamdulillah ya Allah!
Allah ga bawanka! Allah ka tsamo shi daga ɓata ya hayyu ya ƙayyum "
💫
Kallon farko da yawancin dakarun suka yiwa Kazuzi sai da zuciyarsu ta kaɗa saboda tsorata,don ya fito a asalin Kazuzi ɗinshi da suka sani a filin yaƙi, yana zuwa ya rissinawa sarki Iyaad,sannan ya kama ingarman dokinshi ya hau,babu ɓata lokaci suka fara tafiya don barin cikin masarautar
Saboda yadda kazuzi yake kaɗa dokinsa da azama ya sa ya yi gaba sosai, shugaban dakaru Amjad ya dube shi cikin tsananin tsana ya ce"ka ga!
Dakata mana!a tsarin tunkarar yaƙi na musulmai sai an fara tsayawa daga baya an faɗi kalmar shahada, idan sun maimaita shikenan sai a janye yaƙin,idan ba su faɗa ba kuma sai afka,kai yanzu idan ka yi gaba me za ka faɗa su maimaita?ko an gaya maka yaƙin musulmai haka ake afkawa kamar faɗan dabbobi?"
Maganar ta zafafi Kazuzi,amma ya dake,ya ja linzamin dokinshi ya yi baya batare da ya yi magana ba,wasu daga cikin dakarun ba su ji daɗin abin da Amjad ya yiwa Kazuzi ba,har suka yi masa magana akan hakan,wasu kuma musamman waɗanda suke jin haushinshi suka ce ai gwara a gaya masa,tunda gaskiya aka gaya masa
Shi dai Kazuzi bai ce komai ba,suka cigaba da keta dajin suna nufar inda mayaƙan Haura suka yada zango suna jiran su
Ba su yi wata doguwar tafiya ba suka isa,daga nesa suka hango tarin dakarun da sarki Al'as ibnu mugaar ya fito da su,sai suka ga dakarun nasu sun koma tamkar wani zomo a gaban Giwa, don da yawa daga cikin su ma har sun fara karaya
Suna tunkarar yaƙi,amma ba su taɓa tunkarar dakaru masu tsananin yawa irin haka ba, Sarkin yaƙi ne ya fara jan linzamin dokinshi ya tsaya yana kallon sarki Iyaad
Sarki Iyaad ya dube shi ya ce"Ra'uf ya dai?"
Ra'uf ya girgiza kai ya ce "ka gafarce ni ya shugaba na,amma wannan karon abu ne mai wahala mu haye makircin wannan fajirin"
Sarki Iyaad ya yi murmushi ya ce"nasarar Allah a kowanne lokaci a kusa take, Allan da ya bawa musulmai nasarar ɗaukaka kalmar Allah a yaƙin badar shine zai ba mu nasara a wannan yaƙin
Da ikonsa da izininsa nasara ta mu ce....."dukkan su shiru suka yi suna bin Kazuzi da kallo da suka ga ya tunkari rundunar kafiran nan a guje, ba tare da ɓata lokaci ba su ma suka kaɗa linzamin dawakansu suka bi shi
Sai da ya je daf da su ya ja linzamin dokinshi ya tsaya yana kallon su ba tare da wani tsoro ba akan fuskarshi,su ma su sarki Iyaad suka ƙaraso suna mamakin Kazuzi,duk da cewa sun san wanene shi tun ba yanzu ba
Sarki Al'as ya kalli sarki Iyaad yana murmushi ya ce"gaskiya na daɗe ban ga mara kunyar sarki mai ji da isa a inda bai isa ba irinka Iyaad,ba sai na gaya maka ba,ka sani,an fi ƙarfin ka da rundunarka,mai zai hana ka yiwa kanka karatun ta nutsu ka zubar da makamai?"
Sarki Iyaad ya yi murmushi,ya buɗe baki da zummar bayar da amsa Muryar sadauki Kazuzi ta katse su
"Taron yuyuyu ba shi bane nasarar yaƙi ko ƙarfin mayaƙi,ka sa a ranka ya kai wannan raunataccen sarki,duk yawan ɓeraye kyanwa ɗaya ta isa ta tarwatsa su,ka ɗauki rundunarka a matsayin ɓerayen"
Gaba ɗaya dakarun suka waiwaya inda kazuzi ya ja tunga yana kallon sarki Al'as cikin idanu yana mayar masa da magana fuskarsa babu annuri,sarki Al'as ya ce"ku gama da shi,ku kawo min kanshi nan"
Kafin ya rufe baki dakarun sun afkawa Kazuzi sun rufe shi ruf,bayan yan daƙiƙu sai ga su sun ƙare tas,don tamkar mai wasa da takobi haka Kazuzi yake kashe su,hakan ne ya fusata sarki Al'as ya ce dakarun su afkawa rundunar Tayaar,kafin ƙiftawa da bismillah wajen ya rincaɓe da ƙazamin yaƙi
Ga duk wanda bai san wanene ainihin KAZUZI IBN MURAAD ba idan ya ga yadda yake yaƙi a wajen sai ya ɗauka ba mutum bane,idan ya ɗaga takobi ya sauke sai dai a ga kawuna suna zuba kawai
Cikin ɗan lokaci ƙalilan kazuzi ya yiwa rundunar Haura illa irin wadda ba su taɓa tunanin wani mahaluki zai yi musu ba, sarki Al'as ya bayar da umarnin a kama masa Kazuzi, Kazuzi ya kalli dakarun da suka taho da zummar kama shi, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ya ƙarar da su ya koma ya cigaba da abin da yake yi
Daga yamma da suka fara yaƙin kafin ketowar alfijir Kazuzi ya yiwa dakarun Haura illa ta ban mamaki,yana gab da samun nasarar ƙarar da su wani dakare ya daka tsalle ya kai masa sara a wuya, cikin tsananin zafin nama ya goce, takobin ta yanke shi a gefen wuyanshi zuwa kafaɗa,take jini ya wanke masa kafaɗa
Ɗaga kai ya yi ya ƙarewa mai wannan ɗanyen aikin kallo ba tare da ya yi magana ba,ya ɗauke kanshi ya cigaba da kai farmaki har sai da ya ƙarar da kaso mafi yawa daga dakarun Haura,sauran babu shiri suka gudu,ganin Sarkin nasu ma yana shirin guduwa sai ya hau dokinshi ya take masa baya,suka kasa tsere, Kazuzi ya shammace shi ya jefo shi daga kan dokin
Daga nan ƙazamin faɗa ya sarƙe tsakanin Kazuzi da sarki Al'as,sarki Al'as yana cikin lokacin faɗanshi ne kasancewar ko sau ɗaya bai yi yaƙi ba,yayin da jini ya fara ɗibar Kazuzi,ga gajiya kuma na tsawon lokacin da ya ɗauka yana faɗa,amma saboda tsananin jarumta da naci ya kasa haƙura
Fuskantar wahalar da ya yi ne ya sa sarki Al'as ya cigaba da wahalar da shi,sai da ya tabbatar ƙarfin halin nashi yana daf da ƙarewa sannan ya shammace shi ya jefar da shi a cikin ƙasa,kafin ya yunƙura ya tashi sarki Al'as ya ɗora masa takobi a maƙogwaro
#Nusy_bee
08125952284
🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Page 14
Iya tsananin tashin hankali da firgici Sarki Iyaad ya shige shi lokacin da yake daf da ƙarasawa inda suke,don a bayyane yake cewa Kazuzi ya fara gazawa, murmushi sarki Al'as ya yi cikin ƙasaita yana kallon Kazuzi da shima yake kallonsa, cikin isa da gadara yake faɗin "gwara kawai ka saukar da kai yaro,don nasara kuwa mun gama yin ta a kanku,idan...."
Ba sarki Al'as ba,hatta sarki Iyaad da sauran dakarun shi da suka shiga tashin hankali sai da suka zabura ganin wani irin zafin nama da dabarar yaƙi irin ta Kazuzi, tuni ya saka takobin shi da babu wanda ya kula da lokacin da ya ɗago ta,ya daki ta sarki Al'as da ƙarfin tsiya,har sai da tartsatsin wuta ya tashi,sarki Al'as ya yi baya taga-taga kamar zai faɗi saboda tsananin ƙarfin dukan,kamar kuma wanda yake aiki da aljanu zumbur sai gashi a tsaye cikin tsananin zafin nama kamar ba shine wanda jikinsa ya fara gazawa ba
Da mahaukacin gudu sarki Al'as ya taho don ya ɗauke masa kai da takobi,amma Kazuzi ya sare hannun,a wajen ya faɗi yana malelekuwar azaba yana kallon hannunsa da ya faɗi can gefe cikin tsananin mamakin wannan Sadauki,bai gama dawowa hayyacinsa ba Kazuzi ya sare masa kai a fusace,hatta da rundunar Tayaar sai da suka razana,ya ɗauko kan sarki Al'as ya ya taho zuwa gaban sarki Iyaad ya rissina ya ajiye yana faɗin "fatan nasara da cigaba mara yankewa ya shugaba na!"
"Sannunka da ƙoƙari gwarzo kuma jajirtaccen mayaƙi sadaukin sadaukai!"a cewar sarki Iyaad cikin tsananin farin ciki da mamaki,bai yi magana ba, sai su Sarkin yaƙi Ra'uf ke ta maimaita kabbara
Babu jumawa suka gabatar da sallar asuba da ake cikin lokacinta,duk da kasancewar akwai waɗanda suka raunata nasarar yaƙi bata ba su damar jimami ba
Shugaban dakaru Amjad ne ya jagoranci sallar,kafin ya tayar da sallar sai da ya aikawa Kazuzi wani kallo,shi kam Kazuzi abin ma dariya ya so ba shi,ya matsa kusa da ƙaton kogin da yake kusa da filin da suka yi yaƙin ya fara wanke duk inda jini ya ɓata a jikinshi
Bayan an idar da sallar Liman ya miƙe ya yi jawabai sosai,na nuna tsantsar farin ciki da godiya ga Allah da wannan nasara da ta samu fiye da yadda suke tsammani a rayuwa,da godiya da yabo da jinjina ta musamman ga sadaukin sadaukai Kazuzi wanda ya bayar da kaso mai yawa don samun nasarar ta su,ba shi kaɗai ba,da yawan dakarun ma sun nuna jinjina da yabo ga Kazuzi da yake gefe kaɗan da su, kanshi a ƙasa ba tare da ya kalli kowa ba
A nan ne liman ya sanar da mutane Kamar yadda aka saba bayan ɗagawar rana za'a nufi komawa cikin Tayaar,amma kafin nan za'a duba mayaƙan da suka ji ciwo a yi musu magani
Hakan kuwa aka yi,a cikin mayaƙan da aka yi wa magani har da Kazuzi, wanda aka yanke shi a gefen kafaɗarshi,mai maganin ya tsorata sosai, saboda ya ga alamun akwai dafi a jikin takobin da ta yi wannan ɗanyen aikin,amma saboda jarumta da juriya ba lallai a gane hakan daga yanayin Kazuzi ba
Yana zaune yana ƙarasa cin abincin da aka kawo masa, kamar wanda aka ce ɗaga kai,ya hango dakare Amjad yana isowa inda yake,ɗauke kai ya yi kamar bai ganshi ba,ya cigaba da cin abincinshi,dakare Amjad ya ƙaraso wajen ya zauna,amma kafin ya ce komai ya ji muryar Kazuzi yana magana
"To yanzu yaya ka ji?wacce nasara kake samu idan ka kai min hari?
Menene ribarka idan ka yi makirci ka kashe Kazuzi?"
Duk da Amjad ya girgiza da yadda ya gane shine ya yanke shi,don ya canja kaya lokacin,kuma ya rufe fuskarshi,amma ya dake ya ce"har yanzu kana jin za ka cigaba da zama a cikin garin Tayaar tare da mu?
Har yanzu kana nufin shishshigin da kake yi kana samun mummunan sakamako bai ishe ka ba?
To ka cigaba,na yi maka alƙawarin watarana sai ka samu mutuwa muddin ina raye"
"Kasancewar ka a raye ra'ayin Kazuzi ne,ba na shakkar kashe ka a bainar jama'ar da ka saka fuskar mutanen kirki kana yaudarar su suna yi maka kallon na gari, saboda ni ba munafuki bane, irinka"
Amjad ya ce"kai ba munafuki bane,sai kafirci ko?
Kai yanzu don Allah ba ka ji kunya ba muna sallah kana gefe kana kallon mu?"
"Da me sallah ta zata ƙare ka dattijo?"ya faɗa yana kallonsa,don tun ɗazu maganar da yake yi ko sashen shi bai kalla ba
Irin yadda ya tsare Amjad da idanu ya sa hantar cikin Amjad ɗin ta kaɗa,wani kwarjini da kamala ta musamman ya ga ya ƙara,hakan ya sa bai sake magana ba,shima dama Kazuzi tuni ya watsar da lamarin shi ya cigaba da abin da yake gabanshi
Da ɗagawar hantsi suka bar wajen,bayan sun kwashe shahidansu sama da ashirin da rundunar Haura ta ƙarar musu
*DAULAR KAIZUR*
Tunda aka rufe kuyanga Munaya tsawon kwanaki uku kenan ana yi mata sabon horo,don abu ɗaya ake buƙatar ta faɗa,amma hakan bai yiwu ba,shine inda Yarima Sahal yake,amma har yanzu babu amsa
A ɓangaren yarima Jamal ma za mu iya cewa babu sauƙi, saboda duk yadda su sarki Mu'iz suka so jin wani abu daga gare shi hakan ya ci tura,sai nanata musu yake yi cewa da MASARAUTAR KAIZUR da duk abin da ya shafe ta baya gabansa,ba shi da lokacin ɓatawa akan neman mulkin kaizur,wanda a bayyane yake,babu adalci da bin dokar addini yadda ya kamata a masarautar
Yau ma Yarima Zaffar ya ziyarce shi,sai dai yau ziyarar a fusace yake ba kamar farko ba, cikin ɓacin rai ya dube shi ya ce"Jamal!
Baka da hanyar kuɓucewa kamar yadda kake tunani
Wacce mace ce wadda kuke haɗuwa lokaci zuwa lokaci kuna tattaunawa da wani zaurance wanda ba'a ganewa?ko kana tunani babu mai ganinka a ƙatuwar masarauta irin kaizur?
Faɗar gaskiya shine yiwa kanka da iyalanka adalci,akasin haka kuma kamar jefa kanka cikin masifa kake yi kawai,da ƙara bar wa ahalinka abin faɗa a kaizur, yanzu gaya min, menene shirin ka na gaba?me ka shirya a baya? wacece wadda kuke keɓewa da ita kuna magana?"
Kwarai da gaske yarima Jamal ya shiga tashin hankali fiye da tunani saboda bai taɓa tsammanin wani zai iya gano wani shirinsa har haka ba,amma hakan bai saka ya rissina ba,ya ce"kai ka san kana da wannan hujjar kuma ka zo nan ka turke ni?a maimakon a ganni a wajen rataya?"
Yarima Zaffar ya dube shi ya ce"ba zuwa na yi nan don ka yi min izgilanci ba,ɗan yayana da ka saka aka sace,ina aka kai shi?"
Yarima Jamal ya girgiza kai ya ce"ba za ka samu amsa ba, saboda nima kaina ban san abin da ya samu yarimanku ba,a taƙaice ma dai ba ni na saka a sace shi ba,ku cigaba da bincike ko ku ɗauki mataki akaina,ba wannan ne karo na farko da kaizur ta yanke hukunci cikin fushi da son rai ba,kuma ba sai ka maimaita min ba,na san Sarkin ku ba ya nadama"
Kalmar ta yiwa yarima Zaffar zafi,amma bai iya yin magana ba sai kallo da ya bi da Jamal da shi, Yarima Jamal bai damu ba,ya sake duban Yarima Zaffar cikin tsananin tsana ya ce"amma tabbas akwai ranar ƙin dillanci Zaffar, musamman akan baiwar da kuka kulle tsawon shekaru ashirin kuna gana mata azaba,don matsayi da iko yana hannunku,idan ba ka da abin faɗa za ka iya tafiya "
Bai yi musu ba ya miƙe yana kallon Jamal da rinannun idanunsa, Jamal ma ƙyar yake kallonsa,a fusace ya ce"za mu haɗu nan gaba,zan dawo"daga haka ya juya ya fice daga ɗakin fuuuu, Yarima Jamal ya bi shi da mugun kallo cikin tsana
*DAULAR TAYAAR*
Kamar yadda aka saba na al'ada idan aka yi nasarar yaƙi kaɗe-kaɗe da masu tsaron ƙofa suke ji daga nesa ne yake alamta musu nasarar yaƙin da suka yi,hakan ya sa yau ma da zafi-zafinsu suka busa ƙarar sarewa, cikin ƙanƙanin lokaci gari ya hargitse da tsananin farin ciki,duk da cewa bai kai na nasara akan Baruda ba,mutane da yawa suka gabato don taryar mayaƙansu gwaraza
Da yawan mutane sai suka koma kallon Kazuzi da mamaki, musamman da wasu suka fara ƙyanƙyaso shine ƙarfin nasarar yaƙin ba tare da an wahala ba sosai,an yi masa magani a gefen kafaɗarshi an rufe ciwon,kanshi a ƙasa kamar yadda ya saba,kusan shine a gaba-gaba bayan sarki Iyaad,Sarkin yaƙi Ra'uf,da badakare Amjad, shi kuma yana daga bayansu ,ya ɗaure gashinsa ya sake shi bayanshi
Da yawan mutane musamman yan matan da suka fito da kallo suka bi Kazuzi da ya wuce bai kalli sashen da kowa yake ba,sauran dakaru suka bi bayanshi, dama haka yake? kyakykyawa ne,ga cikar zati da kamala,kuma dama sun ji labarin ko da ya kasance bawa har yanzu bai yarda ya rissinawa wani an wulaƙanta shi ba,dama a bayyane yake Kazuzi baya tsoron mutuwa
Ana sauka kai tsaye Kazuzi ɗakinsa ya wuce ransa yana ɓaci,ya yiwa gimbiya alƙawarin karɓar musulunci kafin ya dawo daga yaƙin nan,amma sanadiyyar Amjad ya fasa,bai taɓa zama ya yi tunanin ɗaukar wani mataki akan wani ba sai Amjad
Bayan ya yi wanka ya sauya kaya yana jin ana ta nemanshi a fada amma ya yi banza,har zuwa lokacin da abokinsa khidr ya shigo yana nemansa,amma sai ya yi kamar barci yake yi,dole khidr ya juya ya koma, saboda masarautar Tayaar masarauta ce da take da tsananin bawa wanda yake ƙarƙashinta haƙƙinsa
Yana nan kwance ya lumshe idanu ƙamshin gimbiya Hayat ya ziyarce shi,da sauri ya buɗe idanu ya zauna,idan ya ce bai yi kewarta ba ya yi ƙarya,kai tsaye zai iya cewa tana ɗaya daga cikin waɗanda suka shiga rayuwarsa wadda ba zai taɓa mantawa da ita ba, tunaninsa ya yanke a lokacin da ta shigo ɗakin da sallama
Ɗaga kai ya yi yana kallonta, fuskarta ƙawace da murmushi, sai dai jikinta ya yi sanyi ganin ciwo a jikinsa,ta ƙaraso ta zauna tana kallonsa, kafin ta ce"an ce kai ne gwarzon wannan yaƙin,kai ne ka jagoranci wannan tafiyar, saboda kai ne ƙarfin yaƙin,na yi farin ciki sosai,amma kuma na ji babu daɗi da na ganka da ciwo"
Ɗan murmushi ya yi,ya ce"Barka da zuwa ya shugaba ta!
Ina fatan mun same ku lafiya
A yi min aikin gafara ya shugaba ta, ban samu nasarar sauke alƙawarin da na ɗauka ba"
Shiru ta yi tana bin shi da kallo, kafin ta ce "ko dai wani abu ya sake faruwa tsakanin ka da dakare Amjad?"
Kanshi a ƙasa ya jinjina kai a hankali
Gimbiya Hayat ta harzuƙa,a fusace ta ce"menene dalilin da ya sa ba za ka ɗauki mataki akan shi bane?
Ko ƙarfinka ya fi ne?
To tunda kai ba za ka ɗauki mataki akanshi ba zan sanar da Abby komai,idan ya so shi sai ya ɗauki matakin da ya dace"
Ɗan murmushi Kazuzi ya yi,ya ɗago yana kallonta tana ƙoƙarin tashi tsaye,ya ce"
Ya shugaba ta yaushe kika shirya jin labarin soyayyar Kazuzi da Malli ne?
Ni kaina na ƙosa na ba ki tarihin"
Komawa ta yi ta zauna ta ce"ko a yanzu ma a shirye nake,amma na ga a gajiye kake,ga ciwo,zan bari sai gobe da safe,ya yi?"
Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, gimbiya Hayat ta cigaba da magana "bari na saka a kawo maka abinci"Kazuzi ya rissina kai ya ce"godiya nake ya shugaba ta"
Har ta kai bakin ƙofa sai kuma ta juyo tana kallonsa ta ce"wai ka san suna na ma kuwa?"bai amsa ba ya yi murmushi kawai, ita ma murmushi ta yi ta fice daga ɗakin,ya bi ta da kallo yana lumshe kyawawan idanunshi
Washe gari da wuri ta tashi,bata san menene dalili ba amma ta ƙagu ta ji labarin Kazuzi,ko da yake ta san dalilin ba zai wuce yadda ta fuskanci irin ƙuncin da ya shiga a rayuwa ba,da kuma irin yadda ya rasa Malli ɗinshi da yake ganinta a matsayin komai nashi
Bayan ta kammala karyawa da ƙafa ta taka har cikin lambunta, kuyangarta Huda tana biye da ita,bayan ta isa zuwa rumfar da take zama take hutawa Huda ta shimfiɗa mata kilishin da take zama,ta zauna sannan ta kalli Huda ta ce"ki yiwa dakare ɗaya magana a cikin waɗanda suke gadin lambun nan ya kira min Kazuzi,ke kuma ki je na sallame ki"Huda ta rissina ta ce"an gama ya shugaba ta, Allah ya ƙara miki iymani d tausayi"daga haka ta miƙe ta fice daga lambun
Jim kaɗan Kazuzi ya iso,a ɗan kallon da ta yi masa ta fuskanci ya ƙara jin sauƙi akan jiya,ya ƙaraso cikin lambun, Kamar yadda ya saba ya rissina ya gaisheta,bata amsa ba ta umurce shi ya zauna,sannan ta dube shi ta ce"na kasa haƙura akan batun labarin nan, saboda na ƙagu na ji me ya faru da Malli ɗinka har ta rasa ranta"
Ɗan murmushi ya yi,yana matuƙar girmama gimbiya Hayat,yana jin ta a ranshi saboda yadda ta damu da Malli,a hankali ya ce"na yi Miki alƙawari,kuma tabbas zan cika ranki ya daɗe,to ga labarin Kazuzi da Malli;
*Menene a cikin labarin Kazuzi da Malli haka ne?wanene Kazuzi ibn Murad? menene a ɓoye a rayuwar shi a Baruda wanda muke hasasowa?
Ku biyo alƙalamin Nusy bee don warware komai
Likes da comments fa suna qaranci sosai yanzu,ko kun gaji ne🥺
#Nusy_bee
08125952284
🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Page 15
*SHEKARU ASHIRIN BAYA*
*DAULAR BARUDA*
Garin Baruda yana ɗaya daga cikin daulolin da suka kafu suka tsaya da ƙafarsu dalilin yaƙe-yaƙe, duk da cewa yaƙi yana kassara daula kamar yadda ya zamo sanannen abu a duniya,amma ga Baruda abin ba haka yake ba
Ƙasar Baruda ta ɗauki shekaru sama da ɗari biyar tana gina kanta don ganin bayan abokan gaba,ko kuma na ce don ta yi zarra ga duk wata daula da ke makwabtaka da ita
Ta yi nasara!inda daular ta shahara a ɓangaren horar da matasanta don zama mayaƙa,hakan bai yi ba sai da suka ƙara da koyar da tsaface-tsaface,a taƙaice ma, daular Baruda tana daga cikin manyan dauloli uku da suka shahara da tsafi a duniya,sannan kuma aka zo fannin yaƙi ba'a taɓa cin nasara akansu,idan ma basu yi nasara ba suna yin ragas da abokan gaba
Mafi akasari daular Baruda bata cika yin yaƙi da ƙananan ƙasashe ko waɗanda ba su da komai ba,suna yaƙi ne da ƙasar da take da dukiya,su yi nasara akan ƙasar su kwashe dukiyar
Ba su da wani abin bauta a duniya sama da rana,sai kogin Baruda da suka ɗauka abu mai tsarki da zai taimaka musu ga ibada,tsawon shekaru aru-aru sun yi imani da hakan,kuma akan hakan suke tafiya har zuwa sanda daular Tayaar ta rusa su
Babban sirrin garin Baruda kuwa ba sa amsar baƙo,ba su yarda da baƙo ba duk tsanani,ko da kuwa baƙon ɗan kaza ne,ba su yarda ɗan ƙasar ya rinƙa barin ƙasar yana ɗaukar lokaci bai dawo ba,a cewar su duk Waɗannan idan aka samu a Baruda za'a iya yi musu shigo-shigo babu zurfi,ko dai a yi amfani da baƙo mai shigowa ko kuma a yi amfani da ɗan gari da yake barin gari,hakan zai iya sakawa watan watarana a ci su da yaƙi
A dalilin wannan tsatstsauran ra'ayi irin na su ya sa ko baƙo ne ya yada zango a Baruda matuƙar bai je ya nemi izinin Sarkin garin ba suke kashe shi a take da zarar sun kama shi,idan kuma ya nemi iznin sarki za'a saka masa abin da bai wuce kwana uku ba,ko dai ya bar garin ko ya bar duniya
Wannan kenan!!!
💫
Mafarauci Murad mazaunin ƙasar Baruda ne,a wani ƙaramin ƙauye da ake kira da kalaar,ya shahara sosai akan sana'ar shi ta noma,sannan kuma babban matsafi ne wanda a duk ƙauyen nasu har ma da ƙauyukan maƙwabta babu wanda ya kai shi ƙarfin