ya sa yanzu ina ganin ƙimarshi, Abby ko don darajar sayar da ran da yake yi a kaina duk da kasancewar sa bawa a wannan masarautar me zai hana a ba shi wata dama?
Maganar abin da ya gaya min kamar yadda ya ce zan ba wa masu laifin damar ƙarshe don su gyara kurensu,idan ba su gyara ba kuma zan ɗauki mataki,ko ma na gaya maka komai akansu"
Sarki Iyaad ya jinjina kai ya ce"to babu matsala
Na yarda da maganarki,zan saka a sake shi,amma zan saka a saka masa idanu"Hayat ta rungume sarki Iyaad tana murmushi da hawaye ta ce"na gode Abby
Amma ina roƙon alfarma daga gare ka"
Sarki Iyaad da yake cike da mamakin yadda ta damu da Kazuzi ya ce"ina jin ki ƴata"
Hayat ta gyara zama ta ce"waɗanda za ka saka su su kula da shige da ficen Kazuzi ka haɗa da sarkin yaƙi Ra'uf, badakare Adnan da kuma shugaban dakaru Amjad "
Bai yi wani dogon tunani ba ya ce"to ƴata, idan na yi hakan ya yi Miki ko?"
Tana murmushi sosai ta ce"ya yi min Abby, Allah ya tsare ka daga dukkan sharri "ta sunbaci goshinshi sannan ta ce"Abby bari na je da kaina na fito da shi,dole na nuna masa ban manta sadaukar min da ranshi da ya yi ba har sau biyu"sarki Iyaad ya yi murmushi sosai,bai kawo komai ba a ranshi sai halayen mahaifiyarta da ta ɗauko na tsananin tausayi da girmama ɗan adam
A keken dokinta ta je har ɗakin hukunci inda aka kulle Kazuzi ana yi masa azaba iri-iri,ba iyaka badakare Amjad ba,har wasu daga cikin masu azabtar da shi suna matuƙar jin haushinshi,don ma wani lokacin Ra'uf yana hana wasu abubuwan,shi dama banda dalilin doka ce daga sama da so ya yi ya ji hanzarin Kazuzi,duk da cewa shima Kazuzin wani lokacin murɗaɗɗe ne ba lallai ya faɗa ba
Tare suka tafi da amintacciyar baiwarta Huda,kanta tsaye ta shiga ɗakin hukunci bayan dakaru sun buɗe mata ƙofa,tana shiga ta bi Kazuzi da kallo gabanta yana faɗuwa ganin yadda aka mayar da shi, muryarta na rawa ta ce"ku kwance shi"
Babu musu aka kwance shi,duk da halin da yake ciki sai da ya durƙusa a gabanta ya ce"Barka da wannan lokaci ya shugaba ta"
Bata iya amsa wa ba,sai zuba masa idanu da ta yi tana mamakin ƙarfin halinsa,suna cikin wannan halin ne badakare Amjad ya shigo ɗakin a gaggauce,labari ya same shi cewa gimbiya Hayat ta shiga ɗakin duhu, cikin girmamawa duk da yadda ranshi ya ɓaci ya dube ta ya ce
"Ya shugaba ta wannan umarnin mai martaba ne,shi ya ce a hukunta shi saboda abin da ya aikata a gare ki,ya shugaba ta kin san hukuncin mazinaci a cikin Tayaar, ballantana kuma wanda ya yi nufin aikatawa da gimbiya,a gafarce ni idan na faɗi abin da bai dace ba ranki ya daɗe"
Kallonshi take yi zuciyarta cike da matsananciyar tsanarsa,bata manta abin da ta ji ba,sannan ta sake titsiye Humaida ta gaya mata gaskiyar abin da ya faru na shirin da ya yi ba tare da ita kanta Humaida ɗin ta san niyyar shi ba,ba tare da tunanin komai ba ta ɗaga hannu a fusace da niyyar ɗauke shi da mari,amma ta ji an riƙe hannun
Da sauri kuma a fusace ta waiga, Kazuzi ne,ya sakar mata hannu sannan ya sake rissinawa ya ce"ina roƙon a yi masa afuwa ya shugaba ta,ina roƙar masa alfarma a duba shekarunsa,komai ya yi a ɗaga masa ƙafa "
Ƙasa magana ta yi da farko, ƙwalla ta cika mata idanu ta dube shi ta ce"ai ka san komai, menene dalilin da zai saka ka yi tunanin zan iya girmama tsufansa?"
Kan Kazuzi a ƙasa ya ce"wani lokacin maƙiyi shiru shine yake firgita shi, musamman idan ya gaza nasara akanmu,a jarraba hakan ya shugaba ta"goge ƙwallar idanun nata ta yi ta ce"haka ne,to biyo ni,ina son mu yi magana da kai"daga haka ta juya ta fice daga ɗakin,sauran dakarun suka bi ta da kallo,kansu a ɗaure saboda maganganun da suka yi da Kazuzi yanzu,wanda ke nuni da wata a ƙasa tsakaninsu da badakare Amjad
Shi kuwa badakare Amjad ji ya yi kamar ya nutse saboda kunya da tashin hankali,a zuciyarsa tsanarsu ta ninku,amma sai ya dake,ya juya ya fice daga ɗakin ba tare da ya kalli kowa ba
Kai tsaye ɗakin Kazuzi suka nufa,yana shiga ya samu waje akan daɓen ɗakin ya zauna,a ranshi yana ɓoye mamakinsa ganin an sauya masa kayan kwanciya,ya nuna mata makwancin nashi ya ce"Barka da zuwa ya shugaba ta,ga waje ki zauna"
Girgiza kai ta yi ta ce"ba zama zan yi ba,kawai tambayarka zan yi,ya aka yi ka gane cewa dakare Amjad ne yake neman rayuwa ta?"
A hankali ya lumshe kyawawan idanunshi ya sake buɗewa,ita dai Hayat ta shagala da kallon ikon Allah, saboda zata iya cewa a tarihin rayuwarta bata taɓa ganin namijin da ya amsa sunan kyakykyawa mai cikar zati irin wannan sadaukin ba,a hankali ta ji muryarshi yana faɗin
"Babu wani tsafi da za'a yi wanda Kazuzi bai san yadda yake ba,bai san makarinshi ba
A iya tsawon rayuwata ilmi uku na samu daga wajen babana, shine ilmin tsafi,ilmin yaƙi da na farauta,na koyi yaƙar duk abin da ya saɓa da tsarina,na koyi farautar dabbobi masu haɗari tun ina ɗan ƙaramin yaro, kazalika na koyi ilmin tsafi don kariya,da kai farmaki
Babu wani kalar tsafi da za'a yi na kasa ganewa,da damisa da macijin da suka farmake ki duk ba na gaske bane, dukkansu tsafi ne,kuma da an bar su wajenki kawai za su zo ba za su cutar da kowa ba, tunda dama don ke aka turo su
Da ya ga na yi nasarar rusa shirinshi har sau biyu shine dalilin da ya sa ya sake shiri,ya yi amfani da kuyangarki Humaida ya ba ta ajiya ta ajiye a ɗakinki,a ƙarshe kuma da na yi masa magana don ya warware aikin ya ƙi har ya shirya min makirci
Ya so ya yi nasarar yaƙa ta da tsafi,sai dai shi a ilimin tsafin babu abin da ya sani,don a bayyane yake babu tsafi a musulunci,ba kamar namu addinin ba da ya zama tamkar ibada,shi bai san haka ba, shiyasa ya yi tunanin ya tsaface ni,amma haƙanshi bai cimma ruwa ba"yana kai wa nan ya lumshe idanunshi kawai ba tare da ya sake magana ba
Shiru ya biyo baya na ɗan lokaci,tuni gimbiya Hayat ta samu waje ta zauna tana kallonshi, kafin ta katse shirun da cewa "to yanzu ta yaya kake ganin za'a hukunta shi?"
Buɗe idanu ya yi,kanshi a ƙasa ya ce"lokaci ne zai hukunta shi ya shugaba ta,ina ganin a ba shi dama ko zai gane ya dawo hanya
Babu abin da hukunci cikin fushi yake haifarwa sai nadama da danasani,da ace zan yi masa hukunci cikin fushi da yanzu ba ya duniyar "
Girgiza kai ta yi a sanyaye ta ce"ba laifinsa bane kama ka da azabtar da kai,abbana ne,ka yi masa aikin gafara ya yi ne a rashin sani da son yin kishin tilon ƴarshi,daga gare ka kam na tabbatar Amjad ba zai iya yin nasara ba"
A hankali Kazuzi ya girgiza kai ya ce"azabtar da Kazuzi ba shi da bambanci da sanya ƙarfe a wuta,duk juyin da zai yi sai dai ya canja na ɗan lokaci ƙanƙani,amma ba za'a kassara shi ba
Sai dai tuni Kazuzi a kassare yake,kuma ba kowa bane ya kassara shi sai Amjad "ya yi ɗan shiru yana sauke numfashi cikin damuwa,kafin ya sake faɗin"ya kashe Malli!
Ita ce farin cikin Kazuzi,amma a yau babu ita, tabbas rayuwar Kazuzi bata da amfani,bata da alƙibla muddin babu Malli a cikinta"
#Nusy_bee
08125952284
https://chat.whatsapp.com/Is0HqhjNITL3VZIagV42u7?mode=gi_t
🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Page 12
Shiru ya sake yi yana jan numfashi a hankali,har yanzu idanunshi suna ƙasa,ita kuwa Hayat ƙamewa ta yi a inda take zaune tana kallonshi cike da tsananin mamaki da tausayin da suka daskarar da ita a inda take zaune, Malli ɗin da yake faɗa,yake bege a koda yaushe, wadda ta zama muradin ranshi bata raye dama?
Tunaninta ya yanke a lokacin da ta ji yana faɗin "da ace Ni mai yanke hukunci cikin fushi ne babu abin da zai saka Amjad ya kwana a duniya ranar da ya kalli idanuna da alfahari yana gaya min shi ya sa aka kashe min Malli,kashe ta bashi da bambanci da kashe dukkan farin ciki da burin rayuwa ta kamar yadda na gaya miki,kafin shigowar Malli rayuwa ta bata da wata ma'ana,zuwan Malli cikinta shine ya sa na fara yiwa kaina kallon mutum"
A hankali gimbiya Hayat ta ja numfashi mai nauyi ta ce"kenan kana nufin Malli bata raye?
Na kasa yarda da wannan maganar"
Kallonta ya yi, kamar a mafarki sai ta ga ya yi murmushi,duk da cewa murmushin mai ciwo ne sai ta ga ya ƙara ƙawata kyakkyawar fuskarsa, musamman da ya kasance bata taɓa ganin murmushin shi ba,a hankali ya ce"Malli bata raye,a dalilin barinta duniya ne ya sa nake a wulaƙance a nan,don bana jin har abada zan iya yafewa kaina, saboda gani nake yi kawai nine na yi silar mutuwar ta "
Da sauri Hayat ta girgiza kai,ta ce"ko da ban taɓa soyayya ba na san ba ƙarya ba ce,na tabbatar a yadda kake sonta ba za ka taɓa bari ko tsinke ya soke ta ba ballantana har ta rasa ranta, ƙaddara ce kawai"
"Idan haka ne kuwa ƙaddara bata yi min adalci ba,a lokacin da nake tunanin zan zamo mutum mai daraja sai ta jefar da ni na zama abin ƙyama"
"Ƙaddara abu ce mai kyau,ba kamar yadda ka faɗa ba,wani lokacin ta kan takura zuciyar bawa har ya yi zufa,don ta sanya zuciyar a ganiyar farin ciki, saboda......"
"Ki gafarce ni ya shugaba ta,amma ni ban ga ta inda farin ciki zai ziyarce ni ba,ko na ce ni a tsawon rayuwata ma ni ban sanshi ba sai shigowar Malli cikinta
Duniya cike take da abubuwa masu yawa,amma ababen ƙi sun fi yawa a cikinta "
Gyara zama Hayat ta yi tana kallonshi, a hankali ta ce"zan so na ji labarin Malli,ban taɓa ganinta ba,ban santa ba,amma na ji ina ƙaunarta "
Ɗaga kai ya yi da sauri ya kalle ta, murmushi sosai ya bayyana a fuskarsa,bata yi mamakin ganin hakan ba,a hankali ya ce"a tsawon rayuwa ta na ga mutane da yawa da suka tsani Malli saboda ta nuna Kazuzi a matsayin abin da take so,amma karo na farko kenan da na ga wadda ta so Malli saboda yadda ta so Kazuzi "
Murmushi ta yi ta ce"wataƙila ba su ga kirkinka da na gani ba, shiyasa suka tsane ka"
Kazuzi ya ce"halayena da ɗabi'u na ba su taɓa canjawa ba ranki ya daɗe, yadda nake mu'amalantar mutane a nan haka nake mu'amalantar mutane a ko'ina,sai dai mutane suna mu'amalanta ta da dabi'u dabam-dabam,ba na damuwa da hakan saboda ɗabi'ar ɗan adam ba ya zama ɗaya
"Kai ba abin ƙyama bane, mutum ne mai daraja,babu wani a duniya da yake tsallake tarko da gwagwarmaya face ya kasance mai daraja,kamar kai
Musamman ma ya kasance ya zama macecin al'umma, darajar shi ta dabam ce"
Shiru ya yi ba tare da ya yi magana ba,a hankali ta ce "zan iya tambayar wani abu?"
Ya ɗaga kai ya kalle ta ya ce "komai kike so ki tambaya kawai ya shugaba ta"
"Labarin MALLI nake so ka ba ni,ko na ce, labarin ku kai da Malli, rayuwarku da irin soyayyar da kuka yi a Baruda
Da alamu soyayyar ku ta dabam ce"
Jinginar da kanshi ya yi a jikin bango yana sauke numfashi a hankali, cikin wata iriyar raunananniyar murya ya ce"Labarin soyayyar mu da Malli ba mai daɗi bane,ba labari bane da zai saka ki farin ciki kamar yadda kike tunani ya shugaba ta"
Gimbiya Hayat ta ce"na fahimci da wani zafi ko na ce tabo a rayuwarka,amma tabbas na san soyayyar Malli,ko na ce tarayyarku da Malli ya yi maka maganin ciwon,idan na canka daidai zan iya cewa tsawon zamanka da Malli babu wata damuwa da take yi maka tasiri,amma menene gaskiyar hasashe na?"
Shiru ya ɗan yi na yan daƙiƙu, kafin ya ce"zan iya ce miki eh,kuma zan iya ce miki A'a,a tsawon rayuwar Kazuzi bai san wani abu farin ciki ba,amma kasancewar Malli a rayuwa ta hakan ya bayar da ma'ana da a baya babu a rayuwata"
Hayat ta miƙe tsaye ta ce"shikenan, yanzu lokacin shiga ta na huta ya yi,amma zuwa gaba kaɗan zan sake nemanka,don tabbas na ɗokanta da jin labarin Malli "Kazuzi ya rissina ya ce"a sauka lafiya ya shugaba ta"Hayat ta fice daga ɗakin ba tare da ta sake magana ba,duk jikinta a sanyaye
*DAULAR KAIZUR*
A cikin ƙasa da kwana ɗaya da yini ɗaya kaizur ta hargitse gaba ɗaya,sarki Mu'iz ya dage babu ji babu gani sai ya yi bincike akan ɓatan ɗanshi Sahal,zuwa yanzu an kama yarima Jamal, kasancewar shine abin zargi na farko saboda ɗabi'ar da ya nuna jiya a gaban mutane,sarki Mu'iz ya bayar da umarnin a rufe shi don tuhuma
Sarauniya Amna kuwa rufe kanta ta yi a ɗaki,sai da ƙyar ta buɗe, saboda gaba ɗaya hankalinta ya kai ƙololuwar tashi, izuwa yanzu ta fara sarewa akan batun Yarima Sahal,ta fara cire rai da bayyanar shi, saboda akan binciken da ya fito wasu sababbin al'amura kawai ake tonowa,amma babu batun bayyanar shi
A killatacciyar kurkuku ta manyan mutane masu manyan laifuka aka kulle Yarima Jamal da ya firgice da tashin hankali,tsawon kwana uku ana hukunta shi cikin ruwan sanyi,duk wannan lokacin Sarki Mu'iz bai bi ta kanshi ba ko sau ɗaya, Yarima Zaffar ma hankalinshi yana kan ɗan'uwanshi wanda ya fi kowa zama abin tausayi, saboda cin amanar da yake zargin ɗan'uwanshi na jini ya yi masa
A hankali Yarima Zaffar yake taku zuwa ɗakin da aka rufe Yarima Jamal,dakarun da ke gadin ɗakin ya saka suka buɗe masa ɗakin, ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga
Yarima Jamal yana zaune,ya jingina kanshi da jikin bango,gaba ɗaya kanshi ya kulle,bai taɓa shiga ruɗani irin wannan ba,ya ɗago yana duban Yarima Zaffar da yake kallonsa shima,kafin ya yi wani ɗan murmushi ya samu waje ya zauna yana kallonsa
"Yarima Jamal!
Barkanka da wannan lokaci ɗa ga sarki Ammar ibn SUHAIF BIN YASSAR!!!
Amma na yi mamakin abin da ka aikata, saboda sanannen abu ne wannan jini mai daraja basa cin amanar kowa,ko da ace maƙiyinsu ne a filin yaƙi kuwa,amma sai gashi kai ka ci amanar ɗan'uwanka da kuka fito daga tsatso ɗaya,me hakan yake nufi?
Babu yadda zan yi,dole na zargi mahaifiyarka, dama na ji ƙishi-ƙishin sarautar mahaifinta da cin amana ya same ta,to gashi kuwa an samu a tsatso
Duk da haka ina tantama,don in dai kai jinin SUHAIF BIN YASSAR ne babu kai babu cin amana,sai dai idan an samo ka a wani wajen ne don ka gaji abin da ba naka........"
"Zaffar!"Jamal ya daka masa tsawa, jikinshi har rawa yake yi saboda ɓacin rai"ina gargaɗinka da ka iya bakinka Zaffar, mahaifiya ta ta fi ƙarfin dattin tunaninka,ko da ace na yi faɗa akan kujerar kaizur na isa ne, saboda nima ina da haƙƙin gadarta "
Wata dariya Yarima Zaffar ya yi,ya ce"babu shakka!
Ashe har zuwa yanzu kana da ƙarfin hali kuma ba ka rissina ba,na jinjina maka,wannan ma ɗaya daga cikin ƙarfin hali ne irin na jinin SUHAIF BIN YASSAR
Amma yanzu tambaya ɗaya ce zan yi maka zuwa biyu,ina ka kai Min ɗan ɗan'uwana? menene manufarka ta yin hakan?kuma me ka cimma zuwa yanzu?"
Kai tsaye yarima Jamal ya ce"baka da isar da za ka iya saka ni a gaba da tuhuma Zaffar!
Ka fara zuwa ka gayawa shi ɗan'uwan naka wanda mahaifiyar taku babu abin da ta iya sai haifar annoba irinku,cewa ya daina zaluntar waɗanda ba su ji ba ba su gani ba,kuma idan zai hakura da batun ɗan shi gwara ma tun wuri ya cire rai
Don ba zai taɓa dawowa ba"
Da kallo yarima Zaffar ya bi shi kanshi har yana juyawa,kafin Jamal ya ankara Zaffar ya sauke masa wani mari ya cakumi wuyan rigarshi,sam Jamal bai damu ba,sai da Zaffar ya cika masa wuya yana huci,sannan ya kalle shi yana wani murmushin ƙularwa ya ce
"Daga kai har sarki Mu'iz tunaninku ragagge ne,duk da cewa ina son Sarautar kaizur amma a halin yanzu babu dalilin da ya sa zan yi wani faɗa akanta,da zan yi faɗa akan sarauta da na yi tun lokacin da sarki Ammar ya bar duniya
A yanzu na bar wa wawaye rigimammu sarautar da babu komai a ciki sai zalunci da son zuciya,dangin mahaifiyata ni kaɗai ne magajin sarautar su,don haka ku rabu da ni haka nan"
Wani mugun kallo Zaffar ya watsa masa kafin ya ce"kai ba ka isa akan wannan ƙasƙantacciyar masarautar ta su mahaifiyarka ka ciwa Sarautar kaizur mutunci ba, sanin kanka ne kaf nahiyar nan babu wata masarauta da ta kama ƙafar ta kaizur a girma da daraja, ballantana wata Sarautar su mahaifiyarku wadda bata wuce matsayin mai unguwa ba a kaizur
Ban da wannan ma,ka san da hakan kenan amma ka shiga ka fita ka ɓatar da magajin garin nan ko?"
Murmushi sosai Jamal ya yi,sannan ya ce"za ka iya faɗar komai yadda kake so, lokaci ne Zaffar,amma ni bani da lokacin ɓatar muku da abin da nake da ninkin shi sau babu adadi,yara ne?maza ko mata?kaf MASARAUTAR KAIZUR na tabbatar babu mai yawan ƴaƴana,don haka ka tashi ka fita salin alin,kar allura ta tono harma"
Bin shi da kallo Zaffar ya yi na ɗan lokaci kafin ya ce"me kake nufi da maganarka jamal?"
Jamal ya kalli cikin idanunshi ya ce"ina nufin surutunka ya fara hawa min kai,bana buƙatar hayaniya,ka tashi ka fice daga nan"
Murmushi Zaffar ya yi yana kallon cikin idanunshi ya ce"kana so na miƙe na fice daga ɗakin nan?
To ka gaya min, menene alaƙarka da Nayyab da nake ganin ku wasu lokutan cikin dare kuna tattaunawa?
Me kuke cewa?kuma akan me kuke magana?"
A razane Jamal ya ɗago yana kallon Zaffar, Zaffar ya yi wani miskilin murmushi ya ce"kar nake kallonka Jamal,a kowanne lokaci ka gwada zalunci a shirye nake na ga bayanka,sai an jima"ya miƙe ba tare da ya sake magana ba ya fice daga ɗakin cikin zafin rai, Jamal ya bi shi da kallo yana tunanin yadda zai fitar da kanshi
*DAULAR TAYAAR*
Yau an tashi da ɗimuwa da tashin hankali lokaci ɗaya, sakamakon buga gangar yaƙi da aka yi,hakan ya nuna an kawo wa daular hari kenan, tunda in dai su za su kai hari suna zaman tattaunawa a san yadda za'a yi,amma yanzu tunda aka ji bugawar gangar yaƙin hakan ya nuna an kawowa daular hari ne, kuma maharan suna kusa da garin
💫
A yammacin ranar Alhamis,ranar da Kazuzi da gimbiya Hayat suka tattauna game da rayuwarshi ta baya da Malli ɗinshi,wanda a dalilin wannan tattaunawa gaba ɗaya jikin Hayat ya yi matuƙar sanyi,bata taɓa tunanin zata ji tausayin wata halitta ta damu da wani Kamar yadda take damuwa da Kazuzi ba,hakan ya sa ta ƙuduri aniyar dole sai ta ji labarin shi,kuma sai ta ribace shi ya karɓi Muslunci daga nan kuma ta lallaɓa mahaifinta ya ƴanta shi,ko babu komai sai ya samu rayuwa mai daɗi da farin ciki a cikin Tayaar
Tana cikin wannan tunanin a sashenta su kuma su sarki Tayaar suka samu baƙin saƙo daga wani ɗan aike daga ƙasar Haura,ƙasar Haura mutane ne masu bautar gumaka,a wasu watanni baya Tayaar ta taɓa yaƙarsu,amma Sarkin da wasu daga jama'ar shi suka samu suka tsere,hakan ya sa suka ɗauka ko sun yi galaba akansu ne
Magatakarda aka kira don ya karanta wasiƙar da aka rubuta a jemammiyar fatar damisa, rubutun an yi shi da baƙar tawada,ya zauna ya fara karatun kamar haka
Zuwa ga sarkin ƙasar Tayaar, ƙasar da shugabansu yake jin kanshi kamar wani ne shi
Ya kai Sarki Iyaad, wancan karon ka zo har daula ta ka samu nasara akai na,ka kunyatar da Ni a idanun duniya,an gaya min kana yaƙi don ɗaukaka kalmar ku ta musulunci ne, to in dai ina raye,ni Al'as ibnu mugaar sai na durƙusar da wannan kalmar, yanzu haka tsakanin mu da garinku tafiyar yini ɗaya ce kacal,mun baka nan da gobe war haka ka fito,ko mu shigo har cikin garin naku, mu kashe ku,mu kwashi matanku a matsayin ribar yaƙin mu
Ka ɗauki hakan a matsayin gargaɗi na ƙarshe, sannan magana ta gaba kuma ko da a ce kun yi shiri ko ba kuyi ba maganar dai ɗaya ce,dole mu ci nasara a kanku, saboda kyakkyawan shirin da muka yi
Daga Sarkin garin Haura, Al'as ibnu Mugaar
(Ga masu son VIP group ga number ta nan a ƙasa)
Nusy_bee
08125952284
🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Page 13
Shiru fadar ta ɗauka na wasu ƴan daƙiƙu,kowa na kallon kowa,zuwa can sarki Iyaad ya katse shirun da faɗin "babu komai, Allah ya nuna mana gobe lafiya,in sha Allahu za mu tare su,kuma za muyi nasara akansu da izinin Allah"kowa ya yi na'am da maganar shi
Sarkin yaƙi Ra'uf ya dubi sarki Iyaad ya ce "Allah ya taimake ka ya shugaba na,shin za mu iya yiwa Sadauki Kazuzi tayin zuwa yaƙin?"
Kafin sarki Iyaad ya yi magana dakare Amjad ya kalli Sarkin yaƙi fuskarsa babu annuri ya ce"ya shugaba na maganar yaƙar kafirci ake yi, ta yaya za'a yiwa kafiri tayin yaƙar kafirci?ko ya amsa zai yi hakan ba ka tsoron ya je da zummar yaƙar abokan gaba ya ɓige da yaƙarmu?"
Shiru fadar ta ɗauka da farko, kafin waziri ya ce"da gaskiyar Sarkin dakaru Amjad,maƙiyi yana iya yin dukkan wani shiri don ganin bayan maƙiyansa, musamman ma mutum irin Kazuzi wanda mun riga mun san ba don an fi ƙarfin shi ya kamu ba, kawai baiwa ce daga Allah ya ba mu nasara"
Sarki Iyaad ya katse jayayyar da faɗin"duk wanna jayayya da kuke yi har yanzu shi wanda ake yi don shi ma bai san kuna yi ba
A shawarce idan har ya nuna yana so a bar shi ɗin,mu je da shi,ko da ace ya nufi yaƙarmu muna tare da Allah,zai ba mu nasara akan dukkan wanda ya nufe mu da abin ƙi da izninsa da yardar shi "sauran al'ummar fadar suka yi na'am da maganar asalin sarki Iyaad,da haka fada ta tashi
Khidr,ɗaya daga cikin dakarun da ke aiki tare da Kazuzi, Wanda ya kasance shi kaɗai ne baya jin komai game da Kazuzi,wani lokacin ma sama-sama ya kan yi masa hira duk da cewa shi Kazuzi bai cika amsa shi ba,shine ya nufi ɗakin Kazuzi kai tsaye bayan saƙon ya isa gare su,har lokacin yana zaune inda gimbiya Hayat ta bar shi duk da ta ɗan ɗauki lokaci da fita
A ɗokance ya ƙarasa inda yake zaune, Kazuzi ya ɗago yana kallonsa,ya zauna yana faɗin"da alamu baka san halin da gari yake ciki ba ko?
Yaƙi za'a fita gobe fa, ƙasar Haura ne suka kawo farmaki "shi dai Kazuzi da idanu ya bi shi har ya gama zancen nashi ya fice daga ɗakin
A ranar Kazuzi bai yi bacci ba, saboda maganar yaƙin nan ta taɓa shi,ga maganar da suka yi da gimbiya Hayat ya tayar masa da wani miki a zuciya wanda ya kasa mantawa da shi a rayuwar shi, washe gari yana jin su suka fara fita zuwa bakin masallaci inda suke haɗuwa,bayan sallar asuba za su ɗauki hanya
Har ya gama jin haɗuwarsu bai ji an yi masa magana ba,ranshi ya ɗan ɓaci, ba tare da tunanin komai ba ya miƙe ya fito daga ɗakin nashi,kai tsaye ya nufi inda suke tsaye cikin kyakykyawan shirin yaƙi
Tun daga nesa wasu daga cikin dakarun suka nufi hana shi ƙarasawa bisa umarnin badakare Amjad,amma sarki Iyaad ya ce a bar shi ya ƙaraso,yana zuwa ya zube a gaban sarki Iyaad, fuskarsa babu sassauci ya ce"Barka da war haka ya shugaba na"
"Barkanka dai jarumin jarumai, da alamu kana tafe da wani babban abu mai muhimmanci"
"Na zo ne don na ji dalilin da ya sa ba'a yi min tayin fita yaƙi ba"
Shiru wajen ya ɗan yi, kafin badakare Amjad ya yi farat ya ce"ɗaukaka kalmar Allah za mu je yi,kuma musulmai ne kaɗai ke yi,tunda sune suka yarda da Allah"
Ko kallo bai ishi Kazuzi ba, Sarki Iyaad ma bai jin daɗin abin da ya yi ba,amma kafin ya yi magana sarkin yaƙi Ra'uf ya ce"za muyi yaƙi ne saboda Addinin mu Kazuzi,idan muka tilasta maka,ko na ce muka katse maka hanzari da maganar fita yaƙi akan son zuciyarmu kamar ba mu kyauta maka bane, shiyasa bamu yi maka magana ba"
Sadauki Kazuzi