Ke dai mutuniyar mu sanya labule ki ji bayani , kiji nufi na kar ki yanken hukunci baki ji hujja ta ba ,!"idan ban da abun ki ai Abun da ke ga amarya shi ta kan ba ango " Ya furta hakan yana jan hannu madam saly wacce take wurga masa harara ,tamkar idanuwan ta zasu faɗo ,"
Bayan shuɗewar mintoci sha biyar madam saly da ɗan liti suka dawo ,"
Ke yaks na yadda ki zauna anan tare da su larki a ɗakin su , zasu ɗan matsa miki wajen kwana domin wannan babban ɗakin kulle sa zan yi , ƙanin naki kuma zai bi ɗan liti su dunga kwana tare idan ya so kullum da safe ya dunga zuwa nan yana min wanke-wanke kafin ya tafi barar sa ," daga yanzu bazan biya ki ko sisi ba domin zan dunga ciyar da ku sau uku a rana da ke da ƙanin naki ,idan kin yadda toh idan kuwa baki yadda ba sai a bi wani sarkin ,!
Ba tare da tunanin kome ba yakaka da falmata suka amince bayan sun bi ɗan liti da madam saly da doguwar godiya tare da addu'o'i ,
Toh sai ƙanin naki ya biyo ni yaga ɗakin kwanan koh ? duk da dai ba gani yake yi ba amma ya ɗan tattara wajen da zai sa ƴan haƙarƙarin sa ," ni ya ma sunan sa ne ??
sunan sa kachalla !
Ah kachallari ne toh tashi zo mu tafi mikon hannun ka ,"
Tare da rashin sakewa falmata ta jefa hannun ta cikin na ɗan liti , wanda ɗumi tare da laushin fatar hannun falmata tuɓus-tuɓus , suka nemi ruɗar da shi a karon farko ,"
Da ido yakaka ta raka su cikin ranta tana fatan Allah ya sa madam saly ta zamto gatan su ,!
Kichibus yagana suka yi ita da su falmata wacce ɗan liti ya matse mata hannu gam cikin nasa yana ɗan luguiguitawa , a ɗan fisge ta dube su tare da gaishe da ɗan liti sai dai kuma fuskar falmata da ta gani a fisge ya sanya ta sake waiwayowa da zabari sai dai bata ci nasarar sake kallon fuskar yaron ba sai bayan sa ',
Tana shigowa ta ci karo da yakaka cikin mamakin ganin ta a wurin aikin tare da alhinin abun da ya faru da su a daren jiya wanda duk a zaton ta har yanzu su yakaka suna asibitin ne ta kamo hannun yakaka ,
Yakaka ya jikin falmata ??tana ina ? Ta samu sauki da fatan babu abun da ya same ta ??
Sai da yakaka ta ɗan hah-hanga ta ga babu kowa a cikin rumfar da suke saida burkutu wanda a halin yanzu take kan tattarawa tare da goge gujeru da teburan da masu saye ke zama ," tace
Yagana jikin falmata da sauki , kuma a halin yanzu tana gidan nan mun taho tare , yagana dan Allah ki rufa mana asiri domin a saboda abun da ya so faruwa ga falnata jiya mun bar sansanin mu mun dawo nan gidan da zama sai dai a matsayin falmata namiji , zaki ganta cikin shigar maza da askakken kai tana amsa sunan kachalla , domin Allah kar ki faɗawa kowa ita mace ce kin ji ? Ki rufa mana asiri !
Tare da maɗaukakin mamaki yagana take kallon ta ,
falmata ta koma namiji kuma ??kuma kun dawo nan gidan da zama ? Anya yakaka wannan hanyar mai billewa da kyau ce ? Kin san fa gidan nan cike yake da ƴan iska da ma unguwar baki ɗaya , ke da kan ki hatsari ne kwanan ki cikin gidan nan kina dai ganin yadda da ƙyar muke kwatar kan mu a hannun ƴan iskan nan idan suka sha kunun madam saly , ni a ganina gwara mazan sansanin mu basa shan wannan ruwan da ke fitar da mutum a hankali ya sa hauka, ni dai idan har kin ɗauki shawara ta ku koma sansani duk lalacewar sa yafi nan ,
Yagana falmata tace baza ta koma ba , ta riga ta tsorata , sanin halin mazan gidan nan ya sa na ɗauki matakin mayar da falmata namiji domin kare ta daga idanun su ,"
Katse ta yagana tayi ,"
Toh idan kin kare falmata ke kuma fa ?? Bakya tsoron su cutar da ke ??
Ɗan murmushi yakaka tayi ,"
Zan iya sadaukar da kome nawa domin na bada kariya ga falmata , falmata miskiniya ce bata da kowa daga Allah sai ni ," ki mana addu'a kawai yagana kuma ki rufa mana asiri ,'
Kallon ta yagana tayi na ƴan dakikai ,
shikenan dan ta ni kam baku da matsala koh cewa kika yi kar na nuna na san falmata bazan nuna ba , me ma kika ce sabon sunan ta ??
Kachallah
Kachallah , ta maimaita
Suka haɗa ido gami da kwashewa da dariya , ga alama zuciyar yakaka ta samu ƴar nutsuwa a karon farko tun bayan barowar su garin su .
Niamey Niger
Yau kwanakin su siyama da gnala goma sha huɗu wanda kuma a gobe ne suke da niyyar komawa maraɗi saboda hutun da ta ɗauka a wurin aikin ta gobe yake ƙarewa ,
Zaune suke a ɗakin ubboh wacce ta kama kan siyamar tana kitsewa kamar yadda ta saba yi mata tun siyamar tana ƙanƙanuwa ,har ɗan tasawar ta kafin a aurar da ubboh ,"
Ho addah ke kouwa yaushe ne zaki bar mini kitson hittoɓe ? Haba mana adda baki ganin na girma da wannan kitson ??
Ɗan murmushi ubboh tayi tana me kallon fuskar siyama da ta shagwaɓe fuskar ta ta jikin mudubi ,"
Kauna ta kin kouwa san yadda kitson hittoɓe yake fidda kyauwou tare da cikar surar ki ?? Na kou jima ina faɗi miki babu kitson da ke haska ki yaa shi ina mai tabbatar miki akwai wani sirri cikin kitson ga ki riƙe shi da kyawou har gidan amren ki,"
Shiru siyama tayi domin ubboh ta fama mata ciwon da ke nuƙurƙusar ta cikin rayi ," da nazarin sauyin da ya bayyana akan fuskar ta ubboh ta tsaida kitson da ta fara yi ,"
Ban san yauhe ne munka fara ƴar haka da ke ba kaunata ,?? Yauhe ne kin ka fara boye mini damuwar da ke a zuciyar ki ? Yanzu duniya da gaskiya siyama kina da ƴar uwa da ta fice ni ?? Tuno da kusancin da ya wanzu tsakanin mu tun tsawon lokacci shin kou kuowa dai matsayi na ya sauyu gare ki ?
Juyowa siyama tayi ta fuskanci ubboh , fuskar ta da alamun rashin jin daɗin maganganun ubboh ,"
Kou kussa adda matsayin ki gareni wallah basshi sauyuowa , ke kou me zai sanya ki wagga irin tounani adda amm ??
Shafar fuskar ta ubbo tayi ," cikin ranta ƙaunar siyama na sake linkuwa,
Tun zouwar ki nan wurina na fahimci kina tare da damuwa amma juyin duniya nayi da ke ki faɗi min me ke ad damun ki kin ki faɗi mini toh ƙaƙa kike so in yi da rayi na ? Shin kou kuwa dai a chan gida an ka bata miki rayi ??
Ajiyar zuciya siyama tayi domin ta ga wannan ce damar da zata yi amfani da ita wurin fidda abun da ke boye cikin ran ta , sake marairaice fuska tare da shagwaɓe ta tayi bayan ta karya wuya ,"
Adda amm ni kam ban san dalili guda wadda ya sa hamma youssouf ya ƙi jini na ba , tun tasowa ta nake hangen ƙiyayyar da ke mini cikin idanouwan sa
Da sauri ubboh ta kai hannu ta ɗan make bakin siyamar , tare da maɗaukakin bacin rai akan fuskar ta tace ,"
Wanne irin kalami kike haka ga ɗan ouwan ki siyama ? Shi youssouf ɗin ne basshi ƙamnar ki ? Ƙaƙa kin kai ga fahimtar hakan ,? Ƙou kouwa shi da baki nay ya furta hakan gare ki ? yi samri ki sanar da ni ƙaƙa anka yi wagga mummunan tounani ya kai ga ɗarsuwa cikin rayin ki ?
Hawayen da daman suna kurkusa sune suka samu dalilin ballowa da gudu akan kumatun siyama ," cikin ranta tana faɗin "ayi a ƙare yafi a bari sai gobe ,"
Hamma youssouf bai ɗaouke ni matsayin kauna gare shi ba , har ya gaza boye hakan a gare shi Shi ɗai , sai da ta kai ya bayyana ga bayun masarauta agades , inda ya danganta ni da baƙuwa garai a gaba gare su ,"sun ka maishe ni marar muhimmanci ga har ta kai bayun sun nemi taka ni ,'
Cikin takaicin jin abun da youssouf ɗin ya aikata ga ƴar lelen ta ubboh tace ,"
Yi shirun ki kaunata ki kuma daina wagga mummuna tounani , youssouf yana dawouwa ya iske ni nan cikin gida na zan kuma yi masa magana , yo a rabe magirbin yakuwa ne da na rama ?? Bar ni da shi ,"
Cikin sanyin murya da cikin ran ta ba haka ta so ba , tace
Adda kar ki masa faɗa bissa dilili na bani son ko ƙaƙa ran sa ya baci a sanadiyya ta , bacin ran sa ba zaya dadaɗa mini ba ,"
Cikin son fahimtar abun da ta hango tattare da siyamar ,"ubboh" tace
Ke ko ƙauna ta faɗi min gaskiya ƙou kouwa dai son hamman naki kike ?? Kou amren dangin kike so ?
sunkui da kan ta tayi a lokaci guda tana wani ɗan kyakkyawan murmushin da tun zowar ta ubboh take son ganin irin sa a fuskar ta , kamo haɓar ta tayi ta ɗago fuskar ta ,tana dariya tace
"ni ƴar uwa nake gare ki bai kyautu ba ki boye min kome idan Allah ya yarda youssouf sai ya zama miji gare ki , ina bayan ameren ku ɗari cikin ɗari , ai ba domin lamurran sa da wagga ɗiyar buzouwa ya kankama ba ai da ba'a bawa dawa ba gida ba ta ƙoshi ba ," ki kauda wagga mummunan tounani naki , youssouf ɗan ouwan ki ne kuma zai zamto miji gare ki bisa yarda Allah , ki samu kusanci da shi , kin ji kou ? Ni zan yi maganar ku da hajiya umma ,"
Cikin matsanancin farin cikin da siyama ta gaza boye shi ta miƙe bisa kan guiwar ta tare da rungume ubboh wacce ke zaune bisa bakin gadon ta na alfarma ," zuciyar ta cike da farin cikin da ta daɗe rabon ta da jin irin sa tamkar dai ubboh ta riga ta ɗaura mata aure ne da biyamuradi youssouf ɗin ,"
Nagode nagode nagode , kawai ita ce kalmar da take fitowa bakin ta saboda ta gaza doguwar magana
Cikin sanɗa saɗaf-saɗaf gnala ta koma da baya wacce ta taho domin kawo wa siyama lamurjen da ta sanya ta haɗa mata , ta zo bakin kofar ta tsinkayi tattaunawar su da ta jaa hankalin ta har ta tsaya daga bakin kofar ta ji kome ,"
Sai dai kan ta ya ƙulle ashe daman siyama ba ƙanwa take ba ga biyamuradi youssouf ??ashe kishiya take ga uwargijiyar ta ? To amma ya aka yi gimbiya maimouna bata kai ga sanin hakan ba ??
Jikin ta har rawa yake lokacin da ta mayar da lamurjen ɗakin girki tare da komawa cikin ɗakin da aka yi mata masauki ta murza ɗan makulli , cikin ujila ta fiddo wayar ta tare da danna kiran uwargijiyar ta tana me zumuɗin sanar da ita wannan labarin , domin tun zuwan su sau uku gimbiya maimouna na kiran ta a waya tana tambayar ta ko akwai wani labari koh sun koma maraɗi ??ita kuma Tana shaida mata har yanzu suna niamey ɗin kuma bata ci karo da wani abun da ke bukatar fashin ɓaki ba ,"sai tsantsar ƙaunar da ta fahimci tana tsakanin ƴa da ƙanwar, wanda gimbiya maimouna ta gwatsale ta tare da cewa bata tambaye ta wannan ba ta kuma sake gargaɗin ta tare da jaan kunne akan ta kula da abun da ya kai ta kaɗai ,!
Sai dai har wayar ta gama karaɗin ta daga chan wurin gimbiyar bata ɗaga ba , "tana kuma jin tsoron sake kiran ta kar tayi laifi , dan haka ta maida wayar tare da dasa zaman jiran kira daga gimbiyar ,!
Maraɗi
Lokaci yayi kusa da zaki iddasa aykin da kin ka faro shi saratu , koh kin manta cikin watan ga mai kamawa youssouf yake cika shekarun sa talatin cif ne ? Kou kouwa dai kin manta da abun da zai faru a ranar zagayowar haihuwar sa na cikon shekarun sa talatin ,
Ban manta ba hajiya uwa ba kuma zan manta ba tou ƙaƙa ma za'a yi na mance wannan lokaci ?bayan shi zai zamto shiri na na karshe akan tarwatsa rayuwar safiyyah tare da duk wasu masu ƙaunar ta ??
Ke dai Allah shi kai mu karfe 23:59h na ranar goma ga wattan biyu ,"
Ni ma nace Allah ya bani ikon ɗorawa !
Kar ku manta da nunan ƙauna !
#umm'muaz
#comment
#vote
#share
[6/24, 10:58 AM] +234 701 013 7848: *©Fikrah Writers Association*
*MAFARI*
(hargitsin rayuwa)
*Umm"muaz*
*17*
Cikin sati biyu da tarewar su yakaka a gidan madam saly ,sun zama ƴan gari a da'irar ta yadda yakaka ta san ɗakunan manyan kilakai da ƙananun karuwan da suke unguwar saboda aiken ta da madam saly take wurin su , a gefe ɗaya kuma ta zama ƴar ɗakin samy baby , wacce bayan dawowar yakaka gidan madam saly ta gama nazarin yarinyar tsaf , ta gane bata san ma mai kalmar bariki take nufi ba kamar yadda da tayi zaton yakakar ƙaramar karuwa ce , sai ta fahimci ashe yakakan neman abun sawa a bakin salati take tare da wajen da zata sanya haƙarƙarin ta , dan haka sai ta jaa ta a jiki ta maida ta mai gyara mata ɗaki tare da yi mata ƴan kananun aike da aiki , ita kuma tana bata ƴan kuɗaɗe bayan jibgin suturun ta da ta fitar ta bata kwance , tun yakakan tana ɗari-ɗari ganin abun da samy baby tayi mata a farkon haɗuwar su , har dai ta zo ta saki jiki da ita , sosai take kyautatawa samy baby da ta riƙa a matsayin uwarɗakin ta , wacce take samun alheri tare da sakewa a wurin ta , domin a lokuta da dama har ƴar hira samy baby take zama su yi da yaks ,
Aikin gidan madam saly kuwa tuƙuru yakaka take yin sa domin gwanintar da take nunawa ya faranta ran madam saly da take ganin ta a matsayin ginshiƙin su cikin duniya a yanzu , bata da wani lokaci nata na kan ta sai na aikin burkutu wanda ba'a sanya ba ma yi take kamar su wanke dawa , juya ruwan dahuwar burkutun da kuma tace shi wanke kayan madam saly da gyara mata ɗaki , tun safe idan ta kama aiki sai dare karfe sha ɗaya take samun hutu ," wanda hakan ke matuƙar farantawa madam saly rai har take ganin wautar kan ta da farko, da ta so korar su ashe dai maganar ɗan liti dutse ,
Ga falmata ma sai sam barka domin kuwa har ɗan kumatu tayi ta sake mul-mul , sakamakon cika mata ƙundu da ɗan liti yake da cimar daɗi kullum dare kafin su kwanta bacci , ga kuma labaru masu sanya nishaɗi da yake bata har bacci ya ɗauke ta ,bata zuwa ko'ina daga ɗakin ɗan liti da yake daga wajen filin rawa sai cikin gidan madam saly da take aikin wanke-wanke kofuna tare da farantan aikin burkutu tsawon yini a cikin gidan , bata da wata matsala saboda duk lokacin da yakaka ta ɗan zagaya zata taho bakin fanfon da take zaune din-din a gefen sa ta shafi kan ta koh kuwa fuskar ta , ta kuma tambaye ta bata da wata matsala koh ? Nan zata amsa mata cikin farin ciki da ita bata da wata matsala ,
Haka zata sake komawa bakin aikin ta tana mai farin cikin sauyin rayuwar da suka samu , musamman farin cikin da take hangowa a fuskar ƙanwar ta wacce ɗan liti ya wadata ta da ƴan kayayyakin gonjo na ƴan matasan yara maza sa'annin ta fes-fes da ita hasken ƴar luwai ɗin fatar ta ruwan zuma yana bayyanuwa,
Ranar da suka kwana huɗu a gidan ɗan liti yayi mata kyautar kayan wanda daga ita har falmata kyautar bata wani faranta musu ba , saboda ƴan rigunan basu da wani girma kayan turawa ne , su kuma sun san kayan nan burguza burguza da falmata ke sanye da su sune rufin asirin su a kasantuwar falmata namiji saboda kayan ya boye ɗan tudun kirjin falmatan wanda suka fara tasowa tare da bunƙasa ,
Da kƴar yakaka ta shawo kan falmata wacce da farko ta tubure akan shawarar da yakaka ta kawo na falmatan ta dunga sanya riguna biyu bayan ta tamke kirjin ta da ɗankwali ,saboda boye tudun tare da yi mata gargaɗi kada ta yadda ta sauya kaya a gaban ɗanliti duk juyin duniya , ta kan ce
Kiyi hakuri falmata har mu ɗan tara abun da muka tara anan ɗin zuwa lokacin kuma mun san gari sosai idan ya so sai mu koma wani wurin da babu ƴan iska mu raɓa ki koma saka kayan mu na mata , kamar kowacce mace ina nan ina ware miki kayan ki cikin kayan da nake samu ,"
Ranar da ta fara ɗaure kirjin ta yini tayi tana fama da ciwon kirjin , amma da ta kwana biyu sai ta saba ta daina jin ciwon ,
Bata taɓa yin wanka sai sun tabbatar da ɗan liti ya bar da'irar wajen sannan zata yi wankan a gurguje yakaka ta raka ta ta sauya kaya tare da sake gyara mata ɗaurin kirjin ta wanda ya taimaka ƙwarai wurin boye halittun kirjin ta , sai dai salon takun tafiyar ta tare da tudun bayan ta ke sa samy baby tana yawan tsokanar ta da
"Kachallah me jikin mata ,"
tafiyar ka sai kace ta hamshaƙan mata , koh kuwa tace shege kachallah da kai mace ne da anyi manyan kaya a wurin ka ,"
Idan yagana tana wurin tayi ta sheƙa dariya ,wacce ita ma a yanzu sha'awar rayuwar su yakakan take , domin kuwa har kuɗi da suturu yakaka ta bata daga cikin wanda samy baby ta bata ,"
Haka kwanaki suka yi ta tafiya har suka samu wata guda da ƴan kwanaki a dafdalar wannan gidan , wanda zuwa lokacin yakaka tayi jazur wannan maɗaukakin hasken fatar ta ta ya sake bayyana dal tamkar fitila haka take a waje , ƴar kyakkyawar ƙaramar budurwa mai sanyi tare da yawan fara'a koyaushe cikin murmushi take , ko magana yakaka take haka zaka ga fuskar ta da yalwatattacen murmushi dasashin ta a waje , wanda hakan yake tasiri matuƙa wurin bayyana ƴan ƙananun kyaun ta wanda hasken da take da shi ya fi jaan hankalin mazan da suka fara ƙaraƙaina akan ta fiye da kyan nata ,"
Zuwa lokacin samy baby ta fara jaan ɗamarar wanke yakaka daga dauɗar datti gami da ƙazantar ƙauye a cewar ta yakaka haja ce me matuƙar tsada , wacce sayan ta sai alhajin da ya rufu ya tada kai , " sai ya so zama tamkar gasa a tsakanin ta da madam saly wacce ita ma take bada sumfurin tata kulawar ga yakaka domin ta farga gaba kaɗan yakakan zata zame mata hanyar samun arziki ,dan haka ta fara kokarin janye ta daga wurin samy baby da ta lura tana son kawo mata tsaiko domin kuwa ga alama so take ta fanɗarar da yakaka ta sanar da ita daɗin ƴancin kai kamar yadda ita take da nata ƴancin a hannu domin samy baby ba'a ƙarƙashin kowa take ba cikin magajiyoyin gidan , da karfin ta ta shigo bariki da kuma nawin aljihunta tare da gatan ta domin ba kukan yunwa koh na rashin wurin kwana koh kuwa na neman kuɗin zuwa asibiti zubda ciki ne suka kawo ta bariki ba , ƴar cikin ƙwaryar gari ce da gatan ta da kome iyayen ta ma manyan mutane ne sanannu , uwa uba bata da duhun jahilci domin kwalin digiri ke gare ta ," sha'awar rayuwar barikin take tare da taimakon matar uban ta wacce take sake ingiza ta , uwa uba shaiɗan da yake tsakiyar kan ta yana buga ganga ,
Gidan kakaf ba wata tsohuwar kilaki da take shakka , sai ma su da idan jarabar su ta busa sigari koh afa ƙwayoyi suka motsa , kuma suka laluba lalitar su suka ji wayam , su je wurin ta neman ƴan kuɗaɗe sanin da suka yi kaf cikin karuwan gidan ba wacce ta kai ta kama kuɗi , da kuma kyauta domin hannun ta a sake yake bata da rowa ,"
Ranar wata litinin da safe yakaka ta wayi gari da wani irin matsanancin ciwon mara wanda tun kwanaki biyu da suka wuce take jin sa kaɗan kaɗan amma ta daure ,
Har zuwa yanzu da take kan hanyar ta ta zuwa ɗakin samy baby domin ta gyara mata ɗakin ,bayan ta gama kintsa na madam saly kamar yadda ta saba kafin su duƙufa aikin sana'ar su ,"
A dudduƙe da jaan ƙafa ta ƙarasa cikin ɗakin samy wacce take kwance tana sharar bacci daga ita sai ƴar ficiciyar rigar bacci kan gadon duk a hargitse kayayyakin ta tun daga kan rigar mama da ɗan kafai duk a wurge a kan gadon , tayi ɗai-ɗai da kafafu gashin dokin da yake kan ta ya baje akan filon da tayi matashin kai da shi ," idan da sabo yakaka ta saba tadda ta a haka kullum .
Tana shiga ɗakin ta zube akan shimfiɗar kafet ɗin ta kwanta gami da dunƙulewa wuri guda tana murƙususu , dunƙulewar da tayi ta haɗe guiwar kafafun ta da kirjin ta sai ya sa taji rangwamen kartawa tare da murɗar da marar ta ke mata har ɗan wani bacci ta fara ji yana figarta saboda rashin bacci da tayi daren jiya a sakamakon ciwon cikin ," bata ankara ba bacci mai karfi ya fisge ta , ta sake jiki sosai tana baccin ta ,
Samy baby ce ta farka bayan da taji baccin ya soma gundurar ta , ta daina jin dadin sa , doguwar hamma ta hangame baki ta jaa babu neman tsari daga shaiɗan babu salati , ta gantsare bayan ta ya bada sautin ƙaƙas , tana zira ƙafar ta ƙasa ta sauke akan yakaka wacce baccin ta yake kai mata karo har tsibirin keemala na ƙasar bankok,"
Da farko ta firgita da ganin mutum kwance a gaban gadon ta sai dai fahimtar wacece a kwance ya sa ta ƙewaye ta gami da nufar kofar banɗakin da take ta cikin ɗakin nata , a ranta tana raya cewa gajiyar aiki da rashin bacci ne suka sa yakaka ta bingire anan ta na bacci , tare da sake aiyana niyyar taimakon yakakan har ta samu karfin tsayuwa da kafafun ta muddin yakakan zata yadda ta bi hanyar da zata ɗora ta ," yo ina ma zata ƙi ?? Ai duk wanda ruwa ya ci shi idan aka miƙa masa takobi sai ya kama ,"
A firgice yakaka ta farka lokacin da samy baby take tashin ta , "cikin inda-inda ta fara bata haƙuri bayan ta gaishe ta, tare da faɗa mata cikin ta ne yake ciwo amma yanzu ya lafa ,"ta daina jin ciwon sa sosai , sai dai lema-lemar da take ji
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 111