buɗe , ɗaukar robar tayi tana kallon abincin da ana gani an san ƙarshen tukunya ne ƙanzo-ƙanzo ,babu wani mai da yaji na kirki cincirindon ƙudajen da suka tashi daga kan abinci ya sa ba shiri yakaka ta juye shi a bakin makwarari ta wanke robar ta ɗauraye ,
Ta ɗauko malmalar ɗaya ta sawa falmata ta sake gutsuro rabi ta ƙara mata ta juye mata fiye da rabin miyar , ta kai mata tuwon gaban ta ,' tare da taro mata ruwa a kofi daga bakin fanfo , ita ma ta zauna daga gefe tana cin guntun tuwon ! Suna ƴar taɓa hirar su kamar yadda falmata take so , cikin hirar su take sanar da ita ta shirya gobe zata kai ta ita ma a wanke mata kan ta tare da yi mata kitso !
Bayan sati biyu
Rayuwa tayi wa yakaka tsanani wanda ba kome ya jawo hakan ba sai rashin bature kam silum , domin cikin satin biyun da suka biyo bayan ranar haɗuwar su ta ƙarshe , kamar yadda samy baby ta alƙawarta mata zata nemo mata shi ta wurin abokin sa ,!
Ta je barracks ɗin sai dai bata tarar da shi Colonel nuhu ba, an tabbatar mata da ya tafi bakin aiki ,! Wanda hakan sam bai mata daɗi ba kuma ta kirayi duk numbobin sa basa tafiya ta rasa dalilin haka ! ?
Zuwan ta daban-daban uku bata samun sa , dan haka ta ɗan tsahirta .tare da cigaba da lallaɓar yakaka wacce ta lura tayi zurfi cikin mahaukaciyar soyayyar mutumin da a yanzu take hasashen yayi wa yakaka nisa , sai dai a nemo madadin sa ! Wanda bata ga alamun samun haɗin kan yakaka wurin nemo madadin na sa ba ! , babu ranar da yakaka bata kuka akan soyayyar bature kam silum , ɗakin samy baby nan ne wurin fakewar ta ta sha kukan ta domin ita tasan matsalar ta ita tasan dalilin kukan ta , kuma ita take zaton zata iya share mata hawaye , sai dai a yanzu labarin ya sha banban kuma wankin hula na neman kai su dare ,!
A yau yakaka ta tashi bata da ko sisi domin satin da ya wuce ta kai falmata asibitin ido da kuɗaɗen hannun ta inda kuɗin magunguna da wasu aune-aune , ya lashe fiye da naira dubu takwas , a cikin sauran dubu goma sha biyu da ƴan kai da suka rage mata ,
Da sauran kuɗin tayi amfani wurin cigaba da hididimun yau da kullum , musamman abinci wanda shine kan gaba wurin lashe mata ƴan kudaɗen domin kwanan nan ta tsinci kan ta cikin wani irin bala'in kwaɗayi , bata iya cin abincin da bai wadatu da kayayyakin ƙawata girki ba , bata kuma cin abinci babu nama sannan a rana bata sha lemon kwalba "pepsi " ba tasha guda uku safe rana dare ,' idan kuwa bata sha ba babu zaman lafiya wani iri bala'in yunwa mai tafe da tashin hankali zata dunga ji ,"
Da haka kuɗaɗen hannun ta tas suka ƙare !
Duk da tarin damuwar da take cin ta cikin rai , kallo ɗaya za'a mata a gane ta sauya , ta sake fari har tana ɗaukar ido ta cika tayi luwai-luwai kyaun idanun ta kamar gilashi sun sake haskaka ,! Tana zuwa wuri take ɗaukar hankalin jama'ah .
Ture jakar kayan tayi gefe ta ƙarasa bajewa ta zauna daga durƙuson da tayi ta tallafe kumatun ta da hannu, wannan shine karo na uku tana chaje cikin kayan ta a safiyar yau ko Allah zai sa tayi gamdakatar da wani makararren chanji , sai dai koh alamar kuɗi bata gani ba idan aka ɗauke kuɗin sefa ,"niger", wanda basu da wani maraba da babu a wurin ta ,"
A hankali ta miƙe tana haɗa hanya saboda wata azababbiyar yunwar da take wuji-wuji da ƴaƴan hanjin ta ,'
Ɗakin samy baby tayi wa tsinke ,'
Saɓanin zaton da tayi zata tadda ta tana bacci ta jira tashin ta , sai ta tarad da ita tayi shiri tsaf , tana zaune bakin gado tana shirya kayan ta cikin ƴar jaka ta matafiya ! Gaishe ta tayi cikin ladabi !
Yauwa yaks daman yanzu nake son na tura a ƙira min ke , tafiya ta taso min jiya-jiya cikin dare Honourable yake sanar min zamu yi tafiya tare da shi zuwa abuja inda zai je wani aiki watakila ma mu wuce dubai daga chan ," ga waɗanan kayan ki ɗauka na bar miki su , ni nasan a chan zan taho da wasu masu zafi ," ta furta hakan tana mai turawa yakaka wasu kayayyaki da ta ware su gefe,!
Yakaka wacce tun da taji kalmar tafiya jikin ta ya sake yin sanyi laƙwas ,! Ta durƙusa bisa guiwar ta ,' a gurin samy baby take ɗan samun nutsuwar zuci , take kuma ɗan taimakon ta da wasu abubuwa , baza ta so ba ta tafi ta bar ta a wannan halin tsaka mai wuya da take ciki ,
Cikin sanyin murya tayi mata godiya , bayan ta haɗa kayan ta ƙulle su a ɗankwali ,'
Cigaba tayi da zama tana bin kowanne motsi na samy baby da ido cikin ran ta tana ayyana dama ita ma da bature kam silum ya tashi tafiyar sa ya nemi rakiyar ta mana ? !
Lura da yadda jikin ta yayi sanyi yasa samy baby , ta ce
Ni bani ma lambar wayar ki idan naje ma dunga yin waya , ba kina da waya ba ?
Gyaɗa kai tayi
Amma ban san nambar ba wayar ma tana ƙasan kaya na babu chaji ,
Mts idan banda ke yaks waye zai saka waya ƙarƙashin bacco ? To wannan ai ko yariman ma ya kira ki ba sani zaki yi ba ," gidadancin ki yayi yawa yaks bari dai na dawo daga tafiyar nan inaga darasi zan fara baki dalla-dallah
Ƴar takarda ta ɗauka daga jakar ta ta rubuta mata lambar wayar ta ta miƙa mata ,"
Ga lamba ta nan ki kira ni idan kin saka wayar a chaji kuma ki daina ajiye wayar a nesa watakila ma shi baturen naki yayi ta nema bai same ki ba ,'
Cikin ɗan ɓurɓushin farin cikin jin an ambaci sunan masoyin ta tace
Toh anty zan dauko yanzu idan na koma ɗaki , anty kuma yaushe zaki dawo ?
Ban sani ba yaks ni ƴar rakiya ce ! Sai lokacin da ya gam Abun da ya kaushi zamu dawo tare .
Gƴaɗa kai ta sake yi !
Toh anty sai kin dawo Allah ya kiyaye hanya ! ta furta hakan bayan ta miƙe tsaye da ƙullin kayan ta ," har ta je bakin kofa ta tsinkayo muryar ta
yaks ungo wannan kƴa ɗan sayi pepsi ki sha tun da yanzu naga yayin ɗaga ƙwalbar pepsi kike ! Ta ƙarasa zancen da ƴar dariya
Dubu biyu ta bata , da murnar ta ta ƙarba ," tana jero godiya
Zuwa tayi ta kai kayan da ta bata ɗaki ta dawo domin yi mata rakiya,
Tare suka jera yakaka ta ɗaukar mata jakar kayan nata , suna tafe tana sake karfafawa yakaka guiwa ganin yadda duk ta bi ta damu da tafiyar da zata yi , har zuwa bakin babban titi inda ta samu "mai adai-daita ", ta shiga tare da yin bankwana da yakaka !
Akan hanyar ta ta komawa gida tayi zurfi cikin tunanin ƴar ƙanƙanuwar duniyar ta ,wacce babu kome cikin ta sai tarin ƙalubale , mutanen duniya tausayi yayi ƙaranci a zuciyar su , son kan su tare da son dukiya sun makantar da su wurin duban na ƙarƙashin su da ƙyautayi da kyautatawa , kaɗai suna duban na ƙasa da su ne idan wata buƙata tasu ta tashi wanda suke buƙatar wannan ya kawar musu da ita ,
Da ƙarewar kuɗin hannun ta da tsayuwar rayuwar yancin da ta fara dai-dai suka zo domin tun lokacin da madam saly ta fahimci fa yanzu ta koma faƙiriyar ta kuma ta daina ganin gilmawar mutumin da ya tsaya mata tare da jin yayyafin nerar da yake yi mata , ita ma taci burki daga duk wani mutunci da lallaɓawar da take yiwa yaks , ta koma karta mata walakanci tare da bautar da ita ," ah toh me zata jira ? Ai kawai ungulu ta koma gidan ta na tsamiya , jaki ya tai gidan uban sa !
Ita ba gallazawar bautar aikin yafi damun ta ba illa yadda ƙarfi da yaji madam saly ta fara kai ta gaban ƴan iska tana tallar ta , ita baza ta jure hakan ba , bayan bature kam silum bata jin zata iya yadda da wani ɗa namiji har suyi abun da suke yi tare da shi , cikin su wanene mai kamannin sa ? Mai tsaftar sa ? Mai wayewar sa ? Mai gayun sa ? Mai irin ƙamshin sa ? Babu ! Idan kuwa haka ne ita baza ta yadda da kowanne ƙaton ɗan iska ba bata son su !
Zata jure kowanne irin aikin bauta da wahala , amma ban da harkar taimako ta wannan sigar , bature kam silum kaɗai yake da wannan ƙimar a gurin ta , zata zauna zaman jiran sa har ranar da zai dawo gare ta !
Da wannan tunanin ta ƙaraso shagon "fashe mai shayi ! Tace a fasa mata ƙwayaye shidda a soya su da indomi manya biyu , a haɗa mata shayi da madarar ɗari bonbita na hansin ! Ta miƙa kuɗin aka bata ƴan chanjin ta .
Aka sarrafa mata aka zuba a leda ta ƙarba , Shagon gefen sa ta wuce ta sayi lemon kwalba na pepsi mai sanyi ,
Ran ta ƙwal ta dawo cikin gidan kai tsaye ta wuce cikin ɗakin su falmata , a zaune ta tarar da ita , ta ajiye kayan hannun ta gami da ficewa taje ta wanko kofuna biyu da faranti ɗaya ta zo ta juye musu ,
Falmata matso muci!
Lomar yakaka ta ɗaya ta biyu ta zare hannun ta daga cikin abincin sakamakon ji da tayi zuciyar ta ta wani hautsina ta yamutsa kamar zata fito ta baki , nan take tsinkakken miyau ya taru a bakin ta ," ta matsa gefe tana jan numfashi .
Jikin ta har rawa yake ta balle murfin pepsi da haƙorin ta ta kafa kai tana kwankwaɗa , ba dire ba sai da ta shanye ,"
Sai dai me wani irin ƙugi da cikin ta yayi falmata da kan ta ta jiyo , kafin ta ankara wani kakkarfan amai ya taho mata , nan ta dunga kwarara shi a ɗakin daga bakin kofa , kaf abincin da ta ci tun daga na jiya da dare da bai kai ga narkewa ba har zuwa ƴar indomi ɗin yanzu sai da ta amayo su , amai har ta hanci , ga hawaye da yake ta tsiyaya a idanun ta , yunƙurin aman ta har kofar rumfar su ana jiyo sautin sa ,' har ta koma sai kakaru bata amayo komai sai koren yawu ,"
Falmata ta gigice da ya sa ta fatali da kofunan shayin nasu tare da bi ta cikin farantin indomi ta ɓarar da sauran , cewa take
Yakaka yakaka yakaka , meye ya same ki ? Meye ne ? Baki da lafiya ne daman ? Me kika ci kike amai ? Da lalube ta ruƙo yakakar zuwa jikin ta bayan tayi zaune dirshan cikin aman da yakakar tayi ,
Rashin amsa mata da yakaka tayi wacce take ta yunkurin amai har muryar ta ta shige ciki ya sa falmata fashewa da kuka tare da fara kwala ƙiran neman agaji ,' ihu take tana neman taimako
Daga bakin maƙwarari inda hema da larki suke wankin dawa suna jin su duk yunƙurin aman da yakaka take sun ji sarai sun kuma riga sun yi hasashen abun da ka iya sanya ta aman dan haka suka yi biris , ! Yo ina ruwan su ? Sun ga ire iren ta yafi sau shurin masaƙi , '
Rabu da shegiyar yarinya , ba dai ita tace bariki zata yi wa shigar sojan badaskare ba ? Sama ta ka ba tare da ta ɗau darasi ba , ai kuwa zata ɗanɗani kuɗar ta , wannan somin taɓi ne daga cikin illolin faɗawa bariki ba tare da an nemi ilmin sa ba ," cewar hema
ihun da ya yawaita ya farkar da madam saly daga baccin tofon girar da take shaƙa a gigice ta bazamo kan ta babu ko ɗan kwali guiguyayyar ƙeyar ta da sanƙon ta sai ɗaukar ido suke a hasken ranar da ta fara ɗagowa , " cewa take
Wace masifar ce ta faru da farar safiyar ne ? Waye ya mutu ? Waye ya sha azaba ? Ake faman kururuwa haka ?
Kai tsaye ta nufi ɗakin su hema inda take jiyo tashin ihun falmata ,"
Turus ta jaa ta tsaya ," yawata idanun ta tayi cikin ɗakin tana ƙanƙan da ido kafin ta lailayo wata ƙazamtatciyar ashariya ta watso ," ta ɗora da
Na shiga uku na lalace ni salaha dan uban uban ku yakS me nake gani haka ? Gasar amai kuke koh me ?wace iriyar shegiyar ƙazamta ce wannan irin taku ta ƴaƴan ƙauye kuke gwada min haka a cikin gida ? Tab toh da sakel wallahi baza ku korar min kostomomi ba , yo wannan ai idan ɗaya daga cikin kostomomi na suka ga wannan iskancin ƙazantar da kuke babu ni babu ƙara ganin wani ya zo sayan ruwa ," dan babu mai yadda ya ci abun da kazamtattu irin ku suka taɓa ,!
Wata irin damuƙa tayi wa kafaɗar yakaka ba tare da ta kula da halin galabaita da take ciki ba , ta hankaɗo su waje tare da falmata wacce ta maƙalƙale jikin yakakar ," suka tafi suka faɗi tare nan yakaka ta ƙarasa bajewa a ƙasa cikin halin rashin sanin inda take ,
Shegiya tsinanna yo wani ɗan iskan ya aike ki kije ki maƙalo ɗan tayi a mahaifar ki ? Ai ni daman kallon ki kawai nake ina jiran ranar da cikin zai baiyana kan sa , ko ta arziƙi ko ta tsiya , amma tun tuni na farga da shi , shegiya marar sa'a daga fara bariki har kin ɗauko ciki , to kar ki ji da wai ni bana rainon ƴaƴan shegu a cikin gidana dan haka ku san inda dare yayi muku , arziƙi nake nema ba tsiya ba baza ki raɓe ni da shegen abun da yake cikin ki ku maƙalamin asara da rashin sa'a ba ," yo ƴaƴan halas ɗin ma wasun su amfanin me suke tsinanawa kan su da iyayen su idan ban da masifa ? Haure kafafun yakakar tayi , idan kin gama watangaririyar ki a ƙasa sai ki tashi ku hau shiri , ban ji zan iya ba rainon ɗan shege ! ki bar ni naji da kaina !
Wani irin bugu zuciyar falmata take da kalaman madam saly suke sauƙa a kunnuwan ta , wai me take cewa ?waye yake da cikin shege ? Ɗan shege waye zai haife shi ? ta san ɗan shege sarai domin kuwa akwai wata ƴar makotan su da ta taɓa yi , iyayen ta suka kore ta , kowa a unguwar su ya tsane ta , jama'ah suka ta yin Allah wadarai da ita , mamar ta ta dunga kuka har ta daina fita layi , bata san ma'anar cikin shegen ba sai da ranar ta nacewa maman su da tambayar ma'anar kalmar,"a taƙaice ta bata amsa haihuwar yaro ba tare da anyi aure ba shine cikin shege," har garin su ya watse ba'a san inda wannan yarinyar take ba , tabbas cikin shege abu ne marar kyau matuƙa , madam saly tana nufin irin shi yakaka tayi ?
Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji yakaka ta jaa wani numfashi tare da sake yin wani yunƙurin aman ,"
Wani sabon ihu ta sake saki ,"
Dan Allah ku taimaka min kar yaya ta ta mutu dan Allah ku taimaka mana ," yakaka ki min magana dan Allah ki daina shiru , ki tashi yakaka ki tashi ,
Larki ce ta bar abun da take gami da nufar bakin fanfo ta taro ruwa a wani kwanon silver gami da sanya wani bokitin a bakin fanfon , a kaikaice ta ɗago yakaka wacce take ta sakin numfashi'ita ba sumammiya ba ita kuma bata motsin kirki ," ta kafa mata kwanan a baki ,
Bata wani shaa na kirki ba ta cigaba da yunƙurin aman,"
Aifa lalle kin gamu da wahala , gwara ma idan zaki tashi ki ta shi domin a gidan nan babu wanda zai damu ko mutuwa zaki yi a nan a yashe sai dai a tsallake ki a wuce , masu mutuncin ciki sune zasu jaa ki gefe a samo mai miki salla a je a turbuɗe ki , dan haka ma gwara ki bar lamɓo ciki ba kan ki aka fara ba , laulayi kuma dole ne tun da har kika iya zuwa kika kai kan ki aka maƙala miki maƙalalliya, kin dai ji abun da ,"saly fara," tace ki fara shirin bar mata gida ,"
Juye mata ruwan bokitin da ta ɗauko tayi akan ta baki ɗaya ta jiƙa su sharkaf har da falmata wacce take ƙwaƙume da yakakar , daga ita har yakaka ba sauraran bayanin bakin larki suke ba ,"
wacce ita ce ɗaya da ta kula su , ta zo kan su duk da cikin walakanci take musu Abun da ita a wurin ta taimako ne !
Nan ta dangwarar da bokitin gefen su ta wuce bakin aikin ta tana cewa ,"
Sai ke kuma ki tashi ki je ki wanke ɗakin da kuka gama chaƙuɗa shi da kazantar , sakarkarun yara ƙyauyawa !
Sanyin ruwan ya taimaka wurin farfaɗo da yakaka daga halin gigitar da ta shiga ," da taimakon falmata ta miƙe zaune ," yadda kan ta yake juyawa tare da wani irin bala'in ciwo ya sa ta kama kan nata da hannu biyu,"
Falmata kaina zai fashe ,'!
Sannu yakaka ki tashi na kai ki ɗaki ki kwanta ,'
A wajen kwanciyar ta, ta taimakawa yakaka ta kwanta , fita tayi ta lalubi bokitin da larki ta ajiye ta ɗauka taje ta taro ruwa a cikin sa ta komo ɗakin ,"ita bata san inda tsintsiya yake ba a gidan , dan haka ta laluba ta tattara kofunan da farantin ta haɗa su wuri ɗaya , kasancewar ɗakin daman Ledar sa ta riga ta ratattake ta zama gutsirarra ,ta wurin da suke kwanciyar , daga tsakiyar sa zuwa bakin kofar dandaryar siminti ne , sai kawai ta kwarar da ruwan ta wuraren da take jin lema-lema , ta sa takalman ta biyu ta kwarfe ruwan ta tura shi wajen kofar ,'
Duk abun da take yakaka wacce idanun ta suke lumshe tana jin ta , karfin tashin ne bata da shi , wata iriyar mummunar kasala take ji tana bin duk gabobin jikin ta , ga juyawa da kan ta yake yi ɗakin kan sa juya mata yake ,"
Gefen yakaka ta dawo ta zauna , cikin ran ta tana fatan lafiya ga yakakar wacce take zaton bacci take ,"
Ko mintoci biyu basu ƙarasa ba suka ji muryar madam saly tana ɗuro musu ashar ,"
Ni za'a kawo wa iskanci da tsaurin ido , dan uban ku ni da gidana ina cewa ku fita kuna yin biris da ni , sai kace da uwar ku muka haɗa kuɗin sayan gidan ?? To billahi minti goma yayi kaɗan zan sa a fitar min da ku bayan an chasa min ku ," yau naji jaraba da maSifa ,"
Tana gama hanya ta fito ta durƙusa a gaban madam saly gami da fashewa da kuka ,"
Madam dan Allah wanne laifi na miki zaki kore mu ? Ke kaɗai ce gatan mu dan Allah ki yafe min laifin da nayi miki , idan mun bar nan bamu da wurin zuwa ,"!
Ji min mayyar yarinya ? Ta ina na zama gatan ku ? Babu dangin iya babu na baba ? Na gaya miki yaks ni bana jurar asara , asara ce babba na ci da ke na ci da ɗan cikin ki ? Yo wanne aiki kike min da har ya kai na dunga ci da rai uku a biyan aikin ? Ga ki ga ƙanwar ki kuma ga ƙarin wani yanzu kin maƙalo a cikin ki ,' idan har kina son zaman gidan nan sai dai ki samo uban cikin jikin ki nayi masa lissafi kuɗin abincin ɗan sa ya lale ƙuɗi na ya biya ni sannan ,! Tab ina zan iya asara ?
Ɗa a cikin ta ? Wacce magana ce wannan madam saly take faɗi ? Ko dai kunnuwan ta sun daina ji daidai?
Madam wane ɗa ? Ina ɗan yake ?
Yana ƙundun uwas ki yaks nace yana ƙundun uwas ki , ni zaki yiwa bariki ? Ah lalle fa gwada min firirita irin ta sabuwar karuwa ,"
Sunkui da kai yakaka tayi kan ta yana sake ƙullewa ,"
Wai zaki ki kira ɗan iskan da ya ɗirka miki cikin ya zo ne ko kuwa kin zaɓi barin gidan ?
Da sauri tace !
Zan kira shi madam
Na baki nan zuwa gobe duk inda ɗan iskan yake ki nemo shi yazo ya biya kuɗin ci da ɗan tayin sa ko kuwa yasan inda zai yi da ke ,! Madam saly ta furta hakan tana mai wucewa ta bar wurin cikin ran ta kuwa tana ayyana irin kuɗin da zata iya samu akan cikin jikin yaks domin kuwa ta san da mutum ɗaya tak yaks tayi harka , bata shakkun shi ya fara sanin yaks kuma shine uban cikin jikin ta , idan kuwa haka ne ai ita ranta ƙwal ,
tun da ta lura da samuwar cikin take farin ciki tare da ƙulla yadda zata yi wannan ciki ya buɗe mata sabuwar hanyar kama kuɗi a hannun wannan hamshaƙin attajirin da yayi mata ɓarin naira akan taraiyar sa da yaks , wanda bata tantama wani hamshaƙin attajiri ne mai muƙami , ko kuwa dai ɗan attajiran , da har yau take mamakin ina baƙauyiya kamar yaks ta samo shi ,? shi kuma cikin jerin gogaggun matan duniya da suka dace da shi ya rasa ta zaɓa sai ya tsallako kan yaks ? Kai ita tafi danganta tarayyar sa da yaks ma da neman wani cikar burin sa na daban , wata ƙila sa'a aka bashi aka ce ya haɗa da neman kuchakar mace irin yakaka ,wata ƙila kuma wani al'amari ne mai girma ya jirkita tunanin sa da har ta kai shi ga neman yakaka , ita dai ta san ruwa bai tsami banza !
Koma meye ita gaba ta kaita !
Harƙƴalla da irin su babbar sa'a ce .
Ko batun korar da tayi wa su yakakar , barazana ce kawai ta shirya mata domin ta zaburar ta ta nemo mutumin da ta lura a yanzu bai cikin rayuwar yakakar , da ita kuma take ganin rashin sa a matsayin wani babbar asara , dole ya dawo ya cigaba da harka da yaks ita kuma ta cigaba da samun maƙudan kuɗaɗe ta sanadin hakan ,!
Ta shafe fiye da mintoci biyar a durƙushe nan wurin tana tunani , sai dai duk yadda ta kai ga son fahimtar inda maganganun madam saly suka dosa ta gaza ganewa ,"
Wanne irin ciki ? Ta san ciki ake a haifi ɗan mutum , to amma ita bata da wani sani akan yadda ake a ɗau cikin ɗan mutum ! Tasan dai sai anyi aure ake haihuwar , to ai ita bata yi auren ba ! Kuma da madam saly take cewa tana da ciki , ina
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 111