akan wata ɗalibar ta da ta koyar wacce aka ce daga baya ta zama kamar 'yar ta saboda kusanci da ta samu da ita , sunan yarinyar Amina .
Shiru Liman ya sake yi kafin yace 'Kana nufin Amina Mustapha Dilmari yarinya 'yar Maiduguri ?
" ita fa Malam .
"Allah sarki yarinyar kirki ce ai Amina , ta koma can garin su a halin yanzu har an aurar da ita sati biyu da suka wuce , Malama Maryam da kake nema ai Mata ta ce , kuma ita ce Malamar Amina tsawon shekaru Shida da suka yi tare , bari na shiga gida sai nayi mata bayani na haɗa ku , amma kafin nan zan so jin ko kai wane ne ? Kuma daga ina kake ?
Cike da jin daɗin ganin sauƙaƙuwar lamura Doctor Hamza yace " Malam ai ni ne Mijin Amina bayan haka kuma ni wan ta ne da muke 'ya'yan mata biyu .
" Masha Allah ka ce babban baƙo ne da mu , to Bismillah mana mu shiga daga cikin Falona kafin na yi mata magana .
Ganawar Doctor Hamza tare da Malama Maryam ya zo masa da wani irin sauyi mai girma da yake sauraren bayanan da take yi masa game da baki ɗayan rayuwar da Yakaka tayi tare da ita har ma da wanda tayi gidan uwarɗakin ta samy baby da a farko su kayi zaton yayar ta ce , kafin daga baya lokacin da ta faɗa musu haƙiƙanin gaskiyar kome game da ita ,su gane cewa basu da wata alaƙa ta 'yan uwantaka .
" alaƙar ta da Samy Baby da duk irin Yaudarar da tayi mata . har yadda daga baya Samy baby take son tilasta ta shiga harkar banza amma ta ƙi yarda da hakan shine ya kawo sanadin komawar ta Maiduguri .
Nisawa Malama Maryam tayi tana murmushi ta cigaba da cewa " Abu mafi daɗi da yasa nake yin Alfahari da Amina shine jajircewar ta wajen neman ilmin addini fiye da na boko , Amina ta fara karatun addini bata kai ga sanin ayoyi bakwai na Suratul-Fatiha ba amma sai ga shi cikin shekaru shidda da Yarjewar Allah ta samu cikakkiyar kyakkyawar Haddar izif talatin .
" bata san yadda ake yin cikakkiyar Alwala ba a shekaru shidda baya a yanzu Amina daga kan farillai , sunnoni da mustahabbai har makruhi na alwala ta sani , haka kuma sharuɗɗan Sallar ta sun inganta ta kuma san yadda zata yi gyara ga Sallar ta idan ta ɓaci.
" Amina ta san baƙi , ta iya karatu da rubutun Arabic ta kuma samu tarin ilmi daga littatafan addini da hadisai masu inganci dan haka ta san dukkanin haƙoƙin Ubangiji dake kan ta .
" Alhamdulillah shine kawai abunda zance da Allah ya rataya min nawin tallafa mata ta hanyar samu ilmin addini , ya kuma bani ikon koyarda ita tare da ni da sauran Malaman da ta ɗau ilmi a wajen su , nagodewa Allah da kafin barin ta wajena ta fita daga duhun jahilci .
"Halaye da ɗabi'un Amina mafi rinjayen su masu kyau ne ababen koyi , tundaga lokacin da tasan irin tarin zunubin da yake cikin kuskuren da tayi na baya bata sake kwatanta aikata makamancin sa ba , tayi kyakkyawan tuba da irin sa ake son duk wani mumuni ya yi .
" babu shakka kayi sa'ar Mata , Allah ya ɗorar da zaman lafiya a tsakanin ku, a ƙarshe shawarata shine kayi ƙoƙarin ganin ta samu cigaban karatun ta na addini kamar yadda ta ke fata a koyaushe watarana ta haddace Alkur'ani Mai girma Dan Allah ka bata dama ka taya ta wajen samun cikar burin ta irin Amina sune Al'umma suke amfana da su .
" Ya Rabb lakal-Hamdu , Alhamdulillah , Masha Allah .
Doctor Hamza yake furta haka fuskar sa ɗauke da wani irin annuri na farin-ciki , har wani irin zillo yake ji zuciyar sa na yi masa .
fuskar sa ɗauke da faffaɗan murmushi ya miƙawa Malam Idris ( Mijin Malama Maryam ) Hannu suka yi musabaha , lokacin da yake miƙewa da shirin tafiya , bakin sa ɗauke da duk wasu kalmomin da ake iya amfani da su wajen godiya ga mutumin da ya kai maƙura wajen yi maka Alkhairi .
Da farin-ciki su ma suke amsa masa suna masa rakiya , fitowar su tsakar gida ya zira hannuwansa duk biyu a Aljihu , kuɗaɗen ciki da bai ƙirga su ba su ya tattaro baki ɗaya ya danƙawa Sadiq da yake tsaye a gefe cike da ladabi ya sanya hannu biyu ya amsa yana godiya .
Sun rabu cikin mutunta juna ya jaa motar sa yana barin unguwar , daga cikin zuciyar sa yake jin ɗaguwar wani abu mai kama da nannauyan dutse da ya danne masa zuciya ya taƙaita masa walwalar sa shekara da shekaru ,
ji yake kamar an tsamo sa daga cikin wani zuzzurfan ramin da ya faɗa a ciki , yanayin da yake ji bai taɓa tsintar kansa a ciki ba soyayya mahaɗi ce ta rayuwar kowanne ɗan Adam wanda da zarar an samu tangarɗa ta bangaren ta sai rayuwa ta zama kamar lami babu armashi a cikin ta .
Tuƙin da yake yi yaji yana neman gagarar sa zuciyar sa na neman abokin taya ta murnar da 'yancin da ta samu , dan haka ya gangara gefen titi ya tsaya , jingina kansa yayi da jikin kujerar motar bai ankara ba ya tsinci kansa da yin murmushi lokacin da ya ji wani ruwa-ruwa na taruwa a gurbin idanun sa ( ƙwallar farin-ciki ) shi kaɗai kawai yake ta murmusawa wanda bai san shi ba wanan lokacin zai zaci mutsa-mutsai ne suka hau kan sa .
" Alhamdulillah ,yace yana kai hannu kan wayar da take ajiye a gefen sa ya ɗauka laluben wanda zai ƙira a dai-dai lokacin yake yi ,
Doctor Suleiman shine wanda ya fara faɗo masa arai domin ya raba farin-cikin sa da shi, saboda sanadin sa ya samu kubta daga ramin da zargi ya haƙa masa a zuci ya faɗa .
sai dai tunowa da ya yi da alaƙar da ta taɓa giftawa a tsakanin sa da Yakaka ya sa shi fasa ƙiran sa , daga ƙasan ran sa yake jin tasowar kishin son da Suleiman ya taɓa yiwa Yakaka .
Ajiyar zuciya yayi yana jin yadda zuciyar sa ke bijiro masa da wacce tafi dacewa da ya ƙira a lokacin .
Tunowa yayi da ba shi da number ta , ba ma shi da tabbacin ko tana da waya,ko babu , shiru yayi jim ! Yana tunanin ina zai samu layin ta ? Yana jin nawin Amnee da Khaalty Rahima ba zai iya tambayar su ba .
Rahima ƙarama ita ce ta faɗo masa , yasan muddin dai tana da waya zai samu layin ta wajen Rahima '
Yana ƙiran ta kuwa ta ɗaga , bayan sun gaisa ya ɗan yi gyaran murya kafin yace " Rahima kina da number Mata ta kuwa ?
Ɗan shiru Rahima tayi kafin tace " eh Big bro ina da number Auntie Sofiya...
" Ba sofiya nake nufi ba Number My Pure Woman nake nema ai tana da waya ko ?
Murmushi Rahima tayi lokacin da ta fahimci wacce yake nufi amma dan ta sake tabbatarwa sai tace " number Yakaka ko Big Bro ?
"Yakaka ba suna bane ku daina ƙiran ta da wanan sunan ku dai samar mata da wani sunan da ya dace da ita mai daɗin saurare idan ba za'a ƙira ta da Aminah ba. Ya zarce da cewa "ki turo min da Number ta yanzu . bai saurari dariyar da take yi ƙasa-ƙasa ba ya sauƙe wayar sa .
Ba'a cika mintuna biyu ba Rahima ta turo number , cikin zumuɗi ya danna ƙiran yana fatan Allah yasa ta ɗaga da sauri .
Yakaka wacce tunda ta ji irin zagin da Sofiya ta biyo ta da shi , ta tsorata jikin ta kuma yayi sanyi lakwas daga haka tana iya hango kusancin da suke da shi da Matar sa tunda har tana iya ɗaga wayar sa idan an ƙira , wani sashi na zuciyar ta ma raɗa mata yake cewa duk a gaban sa sofiya ta ƙira ta da Akuya .
Hawaye ta ji yana neman zubo mata , ita kam wannan auren nata bata hango jin daɗin sa ba .
Jiki a sanyaye ta fito daga ɗakin, ta sauƙa ƙasa inda ta tarar Amnee na yiwa Falmata ƙunshi a ƙafafun ta da ƴan yatsu zama tayi tana taya Amnee gyarawa Falmata tsaruwar layin ƙunshin , fuskar ta babu walwala sosai tace " Falmata naso raka ki har ɗakin ki , na mayar da ke saboda ni nayi sanadin tahowar ki , amma ban samu dama ba Yaa Dakta bai barni ba , amma insha Allah idan kin haihu zan je kin ji ko ?
Gyaɗa kai Falmata tayi da ɗan murmushi tace " Yakaka ai daman nasan Yaa Dakta ba zai yarda ba Amaryar sa ta kama hanyar ƙasar Niger rairayin ƙasa ya turbuɗe masa ke ..
" ki min shiru , Yakaka ta katse ta tana 'yar hararar ta tare da satar kallon Amnee wacce tayi kamar bata jin me suke cewa ,
Dafe baki Falmata tayi kafin tace "to nayi shiruna Allah ya kai mu.
Daga haka tayi shiru daga ƙasan ran ta tana ji rashin daɗi da bata samu rakiyar Yakaka ba saboda duk guri idan har da Yakaka tana jin wata irin kariya ta musamman daga jiki har ruhin ta .
Bayan Yakaka ta idar da Sallar azahar tana zaune akan sallayar wayar ta ta fara ƙidan shigowar ƙira .
Da sauri ta miƙa hannu ta ɗauki wayar zuciyar ta na ƙirgo mata waɗanda zasu iya ƙiran ta a dai-dai lokacin , number da ta gani ta sa bugun zuciyar ta sauyawa, take zuciyar ta ta bijiro mata da tambayar "me kuma Sofiya ta ƙira ta sake cewa ? Ko cin mutuncin da tayi mata ne bai ishe ta ba ?
Har wayar ta tsinke bata ɗaga ba , a take kuma aka sake ƙira , tsoron ta ya sake ninkuwa da ta tuno ko dai shine yake ƙiran nata ? Kar kuma tayi laifi idan taƙi ɗagawa Dan haka kafin wayar ta kai ga katsewa sai ta ɗaga ƙiran a ɗan tsorace ta kara wayar a kunnen ta tayi shiru .
Doctor Hamza da ya ƙagauta da ya ji muryar ta ya saita sautin sa ƙasa kaɗan kafin yace " Hello Wafaa , ya kike ?
Shiru Yakaka tayi tana son daidaita nutsuwar ta dan ita gaba ɗaya ma a gigice take da jin muryar sa dan haka sai tace " Salamu Alaikum Yaya Dakta , ba Wafaa bace ba ni ce .
Shiru ta ji yayi kamar baya kan wayar ɗan dubawa tayi ta ga yana nan akan layin tsoron kar ya kashe wayar ba tare da ta faɗa masa abunda take son cewa ba yasa ta cigaba da cewa " Daman ina so ne Dan Allah.....
" Shiiit ki tsaya mu gaisa Wafaa , ko haka ake gaishe da Masoyi?
Saƙato Yakaka tayi da wayar tana jin mamakin sa a take tayi tunanin ko dai bacci yake yana mafarki da wata can wai wafaa ?
Dan haka cikin sanyin murya ta sake cewa "Yaa Dakta ni ce fa ?
Dariyar da take taso masa ya danne yana sake ƙasa da murya yace " ke ce wa?
Kamar zata fashe da kuka tace " Ni ce fa Yakaka yayar Falmata .
Murmushi yayi yana rufe idanun sa cikin ran sa cewa yake " tana son sunan nan tana kuma son ƙanwar ta .
" sunan ki ba Yakaka ba , sunan ki Amina kin ji ko wafaa ?
Shiru tayi , tana son haɗa kalmar da za ta faɗa a lokacin fahimta da tayi zuwa yanzu ya gane ta kawai walaƙanci ne ya sa shi ƙiran ta da wata wai wafaa , ɓata rai tayi kamar yana ganin ta tace
. "Ni dai daman iznin raka Falmata Niger nake nema a wajen ka ? 'Yan uwan mijin ta sun zo zasu koma da ita shine zan raka ta .
Wani irin bugu zuciyar sa ta shiga yi kamar tana gaban sa ya tattare girar idanunsa cikin muryar sa da bata cika ƙarfi ba yace " Wafaa me kike son cewa ? Da auren nawa akan ki za ki tafi har Niger ? Ki je ki ga wannan ɗan....
Shiru yayi yana son dawo da nutsuwar sa da kishi yake neman raba shi da shi nan take , da wani irin sauti yace " baza ki tafi ba kina jina ko ?
A tsorace tace " ina ji .
. "Good .
yace kafin ya kashe wayar sa .
Wani irin zafi yake ji a zuciyar sa kan cewa da tayi zata je Niger garin su wannan ɗan iskan sojan har cikin gidan sa kuma ?
Alhalin da yau yana da iko bayan duk labarin da Malama Maryam ta sanar masa har auren sa da Falmata a halin yanzu ko Fatima ba zata sake kwana da igiyar auren sa ba , tunani ma ya dunga yi kan me yasa Baa ya ba shi auren Fatima ? Alhalin shi ɗin bai can-canta ba .
Ko ma meye shi dai zai killace matar sa daga yin duk wata mu'amala da shi ko dangin sa duk kuwa da cewa yana auren ƙanwar ta ba zai jura ba ya ga ko da kalmar gaisuwa ta sake shiga tsakanin su.( anya kuwa likita ayi haka ?? )
Bai bari maganar da ta faɗa ta ɓata masa farin-cikin sa ba saboda zuwa yanzu yasan wacece haƙiƙanin ta , mace ce mai kyautayi da son kyautatawa mai saurin yarda da yawan sadauƙarwa halinta kenan halittar ta ce shiyasa ya raɗa mata suna ( Wafaa ).
Abun da ya ɗan so tayar masa da hankali bai wuce rashin sanin matsayin sa ba a wajen ta ? sai dai ya yarda da kan sa shi ai Namiji ne zai iya sauya ta zuwa yadda yake so ya koyar da zuciyar ta ƙaunar sa da hakan shi zai samar da nishaɗi a zaman su tare da taimakon sassanyar zuciyar ta mai cike da tausayi da jin ƙai .
Tayar da motar sa yayi yana nufar gida cikin ran sa cike da ƙudirin zuwa Maiduguri a ƙarshen sati mai zuwa ya fara kafa gwamnatin sa tun yanzu kafin nan da ƙanƙanin lokaci da zai dauƙe ta ta dawo kusan sa .
Har zuwa lokacin da ya koma gidan ya tarar da Sofiya yadda ya bar ta , sai daɗuwar damuwa da tashin hankalin da yake iya gani akan koɗaɗɗiyar fuskar ta
Kamar wacce take jiran sa yana zama ta zo ta zauna a ƙafafun sa tana kaɗa ido tace " Doctor na har ka dawo ? .
"Har na dawo Sofi ta daman ai na faɗa miki ba zan daɗe ba .
Murmushi tayi tana raɓa kan ta a kafadar sa ta cigaba da cewa " Doctor na bayan fitar ka na yi mana wani tunani , akan yarinyar nan ƙanwar mu Yakaka take ko wa ?
Bata tsaya ba ta cigaba da cewa " me zai hana ta dawo nan gidan ta zauna a ɗakin nan na 'yan aiki kafin a samu wajen da za'a wurga ta tunda kaga fa irin halin ta na cuɗanya da maza ta riga ta saba da 'yan taɓe-taɓe da tsotse-tsotse da kwakule.....
" kin ga bana son shirita ki faɗa min magana kai tsaye kawai .
Ya furta hakan a taƙaice fuskar sa na bayyana wani yanayi na daban saɓanin wanda ya shigo da shi '
Ajiyar zuciya tayi shirin da suka haɗa ita da Samy baby yana mata yawo a zuci , sannan makirar zuciyar ta na cigaba da mata huɗhuba tace " ina nufin tunda Yarinyar nan kowa dai ya riga yasan irin rayuwar da take yi kafin a laƙaba maka auren ta dan haka na ga gara ka dawo da ita nan kana lura da ita dan saboda kar ta cigaba da yin ''yan harkokin ta tunda dai mai hali bai fasawa daga haka kuma ta kwaso mana ƙajaga ta shafa mana ko kuwa a maƙalo baragurbin ƙwai a liƙa maka ya ƙyanƙyashe ya zamar mana bala'i a doron ƙasa ko me ka gani Doctor na ?
Shiru ta ji bayan gama bayanin ta , sai ta ɗago kanta a hankali ta ɗaura ganin ta kan fuskar sa .
Yanayin da ta hango akan fuskar sa ya tsinka mata zuciya ta ɗan yi yaƙe sanan ta ce "Docto....
Da hannu ya dakatar da ita wani irin murmushi yake da ya mata wuyar fassara yace , " Sofi kin yi tunani mai kyau , wanda na riga ki yin makamancin sa .
. Ya ɗan yi shiru yana kallon yadda faffaɗan murmushi ya cinye fiye da rabin fuskar ta , ya cigaba da cewa
" Fitar da nayi a ɗazu gidan da tayi rayuwa tsawon shekarun da tayi bata gida nan naje , kuma Alhamdulillah Amina ta samu shaida saɓanin wanda ni da ke da wasu tsirarun mutane wataƙila ka iya hasashe , Amina ba rayuwar banza tayi ba , asalima yaudarar ta aka yi aka taho da ita Abuja .
" babu wata hujja ɗaya da zata sa a cigaba da yi mata kallon wacce tayi yawon banza, da ya wuce mummunar ƙaddarar da ta faɗa mata da kuma Allah ya iyakance mata shi , dan haka ina so daga yau ke ma ki cire wannan zargin daga ran ki Wafaa nitsattsiyar mace ce wacce ta tafi neman ilmi kuma ta samu dai-dai gwargwado da fatan kin gane ?
Ya ƙarasa zancen yana kallon cikin idanun ta da suka yi wani irin mitsi-mitsi tana kallon sa , bai jira amsar ta ba ya cigaba da cewa
"Amma duk da haka na karɓi shawarar da kika kawo na dawo da ita kusa da mu dan haka ina ga ranar juma'ah zan tafi Maidugurin sai kawai mu zo tare amma ba a ɗakin 'yan aiki zata zauna ba ɗakin 'yan aiki na 'yan aiki ne ita kuma Mata ta ce dan haka zata zauna a ɗakina kafin na samu gida nan kusa da .....
Zuruf! Sofi ta miƙe daga kan ƙafafun sa jikinta har mazari yake ta fara cewa.
" wallahi Hamza baka isa ba , baka isa ka mayar da ni wata wacce bata san kanta ba , dan ka je an faɗa maka ƙarya da gaskiya shine zaka hau kai ka zauna ba bincike ba kome ni nan na san har gidan da tayi rayuwa a ciki tana sheƙe ayar ta a 'yan iskan samarin garin Abuja kaf ɗaya-ɗaya ne basu kwana da ita ba dan haka wallahi ba zan yadda ina zaman-zamana a kwaso min ciwo a yarɓa min ba sai dai ka zaɓa wallahi ko ni ko ita .
Da sauri ta juya har tana tuntuɓe kome yana shirin kwaɓe mata dole ta yi yunƙurin ɗaukar mataki mafi tsauri da zai kawo mata ƙarshen kome
****
Mutanen Maraɗi sun juya tare da Falmata da Hajja a ƙarƙaahin rakiyar Amnee da zainab wadanda kwana biyu kawai zasu yi su wuce Chad Amnee zata je yiwa dangin su na can gaisuwar bangajiyar biki tare da godiyar hidindimun da suka yi musu..
Sun samu tarɓa mai kyau daya shafi wajen kwana tare da cimaka masu kyau da kuma tarin girmamawa daga bayu da hadiman gidan sarauta.
Daga Hajiya Umma kuwa babu yabo ba fallasa tun zuwan su sau uku kaɗai ta zauna da su waje ɗaya. Ranar farkon zuwan su da kuma washegarin zuwan su da suka je gaishe da Maimartaba sai kuma yau da suke yi mata Bankwana
nan ma kadaran-kadahan suka gaisa Amnee ta ɗanka mata amanar Falmata , tana sake jaddawa akan a yi kiwon ta saboda yarintar ta kada a bar ta da kankin kanta .
Amsar da Hajiya Umma ta bayar ya sanyayawa Amnee jiki domin kuwa cewa tayi " Ɗa ai na kouwa ne itta kouwa ɗabi'a ta mai itta ce hali kuma shi ke samar da gurbi .
" Babu Shakka.
Amnee ta amsa mata .
Tafiyar su ta karya zuciyar Falmata yadda bata zata ba , ta dunga kuka tana hangowa kanta rayuwar da zata yi a cikin wannan makeken gidan alhalin shi wanda take zaune domin sa bai ma san da zuwan nata ba.
Tun bayan tafiyar su sai Falmata ta zama shiru koyaushe tana cikin babban ɗakin da aka mallaka musu ita da Hajja , wanda yake cikin falo na farko a shiyar , abunda ke fitar da ita gaishe da Hajiya Umma da suke zuwa yi kullum safe ita da Hajja daga sun dawo bata kuma fita sai kuma wata safiyar ,
Bayi biyu da aka ware mata su ke hidimar abincin ta tare da kula da tsaftar ɗakin da take , babu abunda take daga zama sai kwanciya , baki ɗayan rayuwar bata mata daɗi ga zaton ta idan sun iso zata samu ko da damar da zata dunga yin waya da Biyamuradi Youssouf sai ta tarar da rayuwar masarautar ba yadda ta saba ba , kowa a cikin gidan bisa umarnin na sama da shi yake aiwatar da lamura .
Duk yadda Siyama da Aicha suka so su dunga jaan ta fira zuwa falo taƙi yarda ,dan haka suka ƙyale ta lokaci-lokaci Siyama kan shiga ɗakin su gaisa sannan su ɗan taɓa hira saboda gidan sarauta suke kome kake idanu na kan ka zai iya zama abun magana ko ma gorantawa ace kullum ita ke zaryar shiga wajen Falmata a matsayin ta na kishiyar ta .
ita kuwa Aicha daman bata cika zaman gidan ba saboda tana shirin kammala karatun ta , dan haka Falmata kaɗaici ya mata yawa .
har gara Hajja da daman ita bata ɗau zaman ɗakin ba ficewar ta take can shiyar Bayin gidan su sha hirar su duk da cewa ba wai aiki take yi ba .
Yau tun safe ta tashi da ciwon baya da ƙafafu saboda cikin kwanaki biyun abunda ke cikin ya fara mata nawi ga yawan motsi da yake yi dan haka sai ta gagara ko da zuwa gaishe da Hajiya Umma kamar yadda ta saba tayi kwance lamo tana jin yadda abunda ke cikin ta ya cure gefe ɗaya.
Hajja ita ɗaya ta tafi gaishe da Hajiya Umma ita ma ba wani sakar mata fuska Gimbiyar take yi ba "ah to Hajiya Umma ce fa ɗiyar Saraki matar Sarki ?
Hajja ta so ta sanar da Hajiya Umma rashin jin daɗin da Falmata take fama da shi a yau sai dai yadda tayi wofintar da ita ya sa ta gaza shigar da batun Falmatan, ta ga sai umarni take bayarwa ga bayu ga Alama dai wani shiri na musamman ake yi yau a gidan .
Dan haka sai Hajja ta miƙe jiki a sanyaye ƙasa-ƙasa tace "bana iya ba wannan gurfanon ya na me neman gafara ni ba lafiyar ƙafa na cika ba , a ƙare ƙalau wannan bautar mai ciwo ? ai ni ba sayo ni aka yi ba dan haka ba baiwa bace da za'a isheni da wani ƙaburi, duk na gundura da zaman gidan nan Babban Soja Allah ya baka lafiya mu samu mu koma gidan mu inda muke a sake ba wata takura .
Bata koma ɗakin ba sai ta fita can inda ta saba hira cikin bayu amma yau sai bata same su sun yi sansanin hira ba kamar yadda suka saba , sai shiga da fita kowaccen su take yi akan aiyukan su hankalin su bai kan ta.
Ɗan zaman mintoci tayi ta miƙe domin komawa ciki kan hanyar ta suka ci karo da Babbar baiwar da take kula da shiyar abincin gidan wanda a shekaru aƙalla zasu yi sa'o'in juna bayan sun gaisa har Hajja ta gota sai Tabawa ta dawo da baya tayi ƙasa-ƙasa da murya tana ɗan leƙen baya tace " Hajja Hauwa da fatan dai kin taya Uwargiyar ki shiri ? Dan Kin kouwa san ɗiyan yanzu ba irin mu bane masu duƙufawa bauta ga Miji .
A ɗan jahilce Hajja tace "Shirin me fa Tabawa ?
Kama haɓa tabawa tayi tana ɗan karkata kai tace "kada dai kice min Uwargijar ki Gimbiya batta da sanin Yarima na daf da shigowa Masarauta ba ? dan kouwa a halin yanzu ma suna Niamey zuwa yammaci kouwa suke shigowa nan .
Da hannu biyu Hajja ta dafe ƙirji muryar ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 94 Chapter of 111