babban titi , lokacin gari ya fara yin ɗan haske shaa ,' Alfijir ya keto ,' cikin nutsuwa suka tsallaka titin , yakaka tana mai waiwayawa kallon kwarin unguwar a ran ta tana jin har abada baza ta sake tako kafafun ta cikin unguwar ba !
.
A cikin rumfar bakin wani shagon da yake jikin kasuwa suka yada zango , yakaka wacce ta gaji tilis da ƴar tafiyar da suka yi sakamakon rashin ƙarfin jiki , ta kwanta a dandaryar sumintin gaban shagon gami da yin matashi da baccon ta , falmata kuma ta zame ta zauna daga jikin bango ,"
Falmata ke zan ajiye ki wurin barar ki na da idan an fito kasuwa ni kuma zan ɗan kewaya na nemi wani ɗan aiki , ko dako ne ma nima nayi na ɗan samo mana wani abu kafin mu ga yadda Allah zai yi da mu koh ?
hakane yakaka , amma ke ki zauna kawai kin san fa baki da isasshiyar lafiya kar ki je kiyi aiki kuma ki cutar da kan ki da yaron mu ,!
bazan yi aikin wahala ba daidai karfi na zan yi falmata .
Toh shikenan yakaka .
Suna nan zaune gari ya waye tangarai mutane suka fara kai kawo masu sana'ar safe suka fara hada-hada gasu nan iri-iri, nan yakaka ta hango wata mai sayar da ƙosai da fanke wanda ƙamshin suyar ta ya bugi hancin yakakar , nan take ranta ya biya ,"
falmata ga masu abin karyawa sun fara mai zan karɓo mana ?
ki sayo mana duk abun da ran ki yake so yakaka !
to ki kula mana da jakar kayan mu sosai .
Toh
Ƙosai ta saya tare da fanke , ta ƙarasa wurin wata mai sayar sa koko ta sayo masu , har zata wuce ta ga mai masa nan ma ta tsaya ta saya ," tace a zuba mata yajin ƙuli ya ji sosai ," nan aka baɗe mata kan masar da yajin ƙuli,"
Nan suka zauna suka ci suka gyatse , falmata ta sha ruwa daga randar da take daura da rumfar da suke, yakaka tace ita baza ta sha ruwa yanzu ba domin tana sha amai zata yi ,
anan suka cigaba da zama suna ƴar hirar su jifa-jifa har zuwa tara na safe lokacin da ƴan kasuwa suka fara fitowa ,"
mutumin da yake mamallakin shagon da suka yada zango bakin sa , shi ma ya fito ,
da kallo ya fara bin su da shi cikin shakku da rashin yadda musamman da ya ƙƴalla ido ya ga baccon kayan su ai sai ya jaa baya ,
lura da shi yakaka ta yi dan haka ta fara gaishe shi nan falmata ma ta fahimci akwai mutum a wurin ita ma ta fara miƙo tata gaisuwar amma maimakon ya amsa sai ta ga ya juya ya nufi wata ƴar hanyar da ta ratso tsakanin shaguna ya tafi ya bar su
Nan yakaka ta shaa jinin jikin ta ,"
Falmata kin ga wannan mutumin ƙila nan da muke zaune shagon sa ne , kuma muna gaishe shi naga ya tafi ya bar mu " ko dai bai yadda da mu bane ? Tashi mu tafi kar ya ƙira mana hukuma a kama mu ., yakaka ta ƙarasa zancen tana miƙewa ,"
nan ita ma falmata ta miƙe ,
mu yi sauri mu tafi yakaka kar a kama mu !
Har sun fara tafiya suka ji an dakatar da su , ta hanyar daka musu tsawa tare da basu umarnin tsayawa ,"
Chak ! Suka tsaya zuciyoyim su na bugun lugude ,!
[6/24, 10:59 AM] +234 701 013 7848: Mafari .......
( Hargitsin Rayuwa )
umm'muaz
21
A tsorace suka juyo , yakaka tayi arba da wani mutum jikin sa sanye da shuɗin kaya hannun sa ɗaya rike da wata ƙatuwar kulki , gefen sa kuwa wannan mutumin da take zaton sun yi masauƙi a bakin shagon sa ne
Nan take ran ta ya aina mata , ", ya ƙira musu jami'in tsaro ne ," dan haka ta matso falmata gami da sake riƙe hannun ta ƙam-ƙam ,
Daga chan inda yake tsaye yace !
Su waye ku ?
Kuma daga ina kuke ?
Meye kuma kuke tafe da shi a baccon hannu ku ?kuyi gaggawar sanar da mu kafin naje na kira sojoji .
Mukut ! Yakaka ta haɗiye yawun tsoro .
Mu mune su falmata kuma mu ƴan gudun hijira ne daga ƙauyen mairambiri , kayan mu ne a cikin bacco .
Falmata ta amsa musu cikin dakiya .
Wanne irin kayan ?
Kayan sawar mu .
Suka haɗa baki wurin amsa masa !
Ku buɗe mu gani ?
filla-filla suka yi da suturun nasu , ba tare da gardama ba .
Meyasa kuke yawo da kaya ? Ina ne sansanin ku ? Bai kamata kuna yawo da jakar bacco ba saboda kun san halin da gari yake ciki ba'a yadda da duk wani mutum da aka gan shi da kaya niƙi-niƙi kuma yana nuƙu-nuƙu a cikin taron jama'a bare ma ku yara mata ga kuma irin yanayin ku , kowa ya gan ku dole zai zarge ku har ma ya tsora ta , saboda yadda mafi yawancin lokaci ake amfani da ku ta hanyar rataya muku nakiyar bam ku shiga taro ku tayar ,
Ku godewa Allah ma lokacin da na gan ku a bakin shago na ba jami'an soja ko na ɗan sanda na kira ba mai gadin kasuwa ne , da ace ɗaya daga cikin jimi'an tsaro ne da sai sun hukunta ku dan haka nake baku shawara da ku koma sansanin ku , ku ajiye wannan jakar kayan naku sannan idan ma zaku shigo gari harkokin ku sai ku shigo , yawon ku a haka hatsari ne ga rayuwar ku ,!
Duk wannan dogon bayanin da mutumin nan yake musu yakaka ta zurfafa cikin tunani , jin ya ambaci komawar su sansanin ƴan gudun hijira ,"
Cikin ran ta ta ƙudurce baza su koma sansanin su ba , saboda tun bata tare da ciki ma ƙuƙaƙƙiyar wahala ce zaman sansani ƴan gudun hijira , sanan ga tozarci uwa uba fyaɗe da ake yi wa mata , to bare fa yanzu da take ɗauke da cikin da bashi da uba , ta koma sansanin su a gan ta da ciki ,? Tace aina ta samo shi ? Alhalin duk wanda ya san ta ya san ta ne a matsayin budurwa wacce bata taɓa aure ba ,
ai ta tabbatar fanne baza ta bar ta ta kurɓi ruwa ba zagi da aibatawar da zasu dunga mata sai ya samar mata da cuta , dan haka gara sun hakura da zaman sansanin sun nemi wani wurin fakewar ,"
Da wannan tunanin ta ɗago kan ta ta dubi mutumin , da taji falmata na bashi amsa da cewa
Sun ɓata ne sun kuma manta sunan sansanin su .
Malam dan girman Allah ka taimaka mana ka samar mana da wurin da zamu dunga kwana , " bamu da kowa a garin nan mamar mu da ƙannen mu sun ɓata tun a ƙyauyen mu baban mu ya mutu , mijina ma ba'a san inda yake ba ,"
Ta ƙarasa zancen tana mai sunkui da kai domin gujewa kallon rashin yadda da wannan mutumin yake jifan ta da shi ," cikin ranta kuwa kunyar sabuwar ƙaryar da ta gilla take yi ,
Saitin inda take jin tashin sautin muryar yakaka , falmata ta maida fuskar ta , cikin ran ta tana mamakin yaushe su duka suka koyi ƙarya ? ?
Shiru yayi yana nazari , kwarai zai so ya taimakawa yaran ko dan kasancewar su mata , duk da cewa cikin ran sa ba wai ya gama aminta da zantukan su bane gaba ɗaya ,
toh amma shi ya san ba ƙaramar fitina zai tadawa kan sa ba muddin ya ɗauki yaran nan ya kai su gidan sa ya jefa su tsakanin matan sa uku ," yana da tabbacin sai an dafa su da ran su , shi kan sa ruwan gidan sai ya gagare shi shaa da kwanciyar hankali , dan haka da muguwar rawa gamma ƙin tashi .
Yarinya ni bani da wajen da zan kai ku , ku samu wurin kwana saboda yanzu duniya ta lalace ba'a saurin yadda da mutum . Alfarma ɗaya zan muku shine na yadda duk lokacin da dare yayi muku kuna tsakanin nan bakin kasuwa ku gangaro cikin rumfa ta ku kwana bazan hana ku ba ,' har ma tabarma zan ajiye muku , bayan na sanar da masu gadin kasuwa wanzuwar ku awurin kun ji ko ?
Ya furta hakan yana danne yanayin da yake ji na rashin kyautawa yana taso masa , ya san ba haka ya kamata yayi musu ba yasan taimakon da suke nema ya wuce wannan yasan bai ji tausayin su bai kuma basu kariya ba , toh sai dai yana jin iyakacin taimakon da zai iya basu kenan ,
Ga mamakin sa godiya suka dunga sauke masa kwando-kwando tamkar wanda ya basu wurin kwana a ƙuryar gidan sa , hakan ya sa tausayin su ya sake baibaye shi ,"
Ku dawo da jakar kayan ku ajiye cikin shago na ," kuma ku tabbatar kafin cikar karfe huɗu da rabi kun bar duk inda kuke kun dawo kun amshi kayan ku domin ni karfe huɗu da rabi nake rufe shago ,"
Cikin daɗin rai yakaka ta kawo falmata dai-dai wurin da take zaman barar ta ,' ta ajiye ta bayan sun gaisa haba-haba da ɗan dattijon da yake sayar da kayan miya a gefen wajen wanda suka tarar da shi yana fidda kayan lambu ɗangin su yakuwa , alehu , zogale , rama da sauran kayan lambu yana shirya su akan ɗan teburin sa ga alama bai jima da isowa ba , har yake jajen kwanaki da dama baya ganin falmata ,"
Nan suka ce hana su fitowa aka yi daga sansanin su ,"
Falmata ga naira ɗari ki sayi wake da shinkafa da salat ki ci anjima da rana , kar ki ce zaki zauna da yunwa kin san bana so ," kuma kar ki tafi ko'ina , nima ba nisa zan yi ba zagayen kasuwar zan kewaya ko Allah zai sa na samu ko dako ne nayi na ɗan samo mana ƴan kuɗi kin ga ƙarshen kuɗin hannu na ne ɗarin da na baki , bayan ita bamu da ko sisi ki kula da kan ki sosai kin ji kou ?
Naji yakaka
ta furta hakan tana mai miƙewa tsaye daga kan ɗan dutsen da yakakar ta ajiye ta , gaban ɗan teburin mai kayan miyan ta ƙarasa
Baba ɗan Allah ko zamu samu chanji ? Tana mai miƙa masa gudan ɗarin ,
Ƙarɓa yayi , ya bata hansin biyu ,ta ƙarba tare da lalubar hannun yakaka ta danƙa mata gudar hansin ɗaya ,
Idan kin bani duk kuɗin ke kuma da me zaki ci abincin anjima ? Kin fini buƙatar abinci yakaka , ke da baki da lafiya ,kar kiyi aikin wahala da yawa wanda zai sa ki samu matsala , idan kin shiga matsala ni kuma yaya zan yi yakaka ? Dan Allah ki lallaɓa kan ki , kuma ki dawo da wuri ,"
Toh madam falmata
ta furta hakan tana murmushi jin yadda falmata ta zage tana bata umarni kamar dai ita ce babba .
Hanya ta miƙe tana tafe tana raba ido cikin fatan son ganin inda zata ɗan samu wani aiki ta je ta kama ko da ba'a sa ta ba , amma har ta kai kan gadar kasuwar bata ci karo da wani wajen da ake buƙatar ƴan aiki ba , hasalima yanzu ne ƴan kasuwar suke kan buɗe shagunan su , tare da fito da kayayyakin sana'o'in su ,"
Har ta yanke shawarar komawa wurin falmata ta ɗan jira zuwa anjima , sai idanun suka hango mata mattatarar masu niƙa a ƙwarin gadar ,
Sai ta yanke shawarar ta ƙarasa wurin ƙila ta samu aikin yi tun da ta hango wajen a cike ,"
Gangarawa tayi ta sauka wajen , ga mamakin ta masu injinan niƙa ne birjik ta ko'ina a wajen , ƙarar inji kuwa ba'a cewa kome domin ko maganar na kusa da kai baka iya ji sai fa idan yayi ihu ,'
Da gudu ta ga wasu ƴan matasan yara maza da baza su gaza falmata ba sun nufo ta ,"
Yaya ta niƙa ne ? Ki kawo na kai miki injin mu yau yau muka kai faifan injin washi , laushi luƙui za'a miki ,
Yaya ta injin su mutuwa yake ana cikin niƙa , anjin mu yafi lafiya kuma ga arhar niƙa ,"
Ita dai da ido take bin su da kallo ba sosai take fahimtar su ba , saboda ƙarar injin da ya cika mata kunne ,
Ita ma da ɗan karfi ta amsa musu
Ba niƙa na kawo ba , aiki nake nema ,
Haɗa ido yaran suka yi suka kwashe da dariya , suka maimaita
Wai aiki take nema ? kut wannan ƴar na'u ce ita ma .
Juyawa suka yi suka bar ta nan tsaye ba tare da sun bata ansa ba .
Har sun ɗan yi nisa sai kuma ɗayan ya komo ,
aikin tankaɗe dusa kike nema ??
Batare da ta kai ga fahimtar sa ba ta gyaɗa kai ,
Zo muje injin abokin yayana jiya sun ɓata da mai yin tankaɗen dusar sa ,
Da murna yakaka ta bisa a baya har wata ƴar siririyar hanya , bayan ƴar gajerar tafiya suka bullo a wani babban fili faffaɗa , saɓanin injinan da ta tarar a waje waɗannan manyan injina ne girkakku , ƙaran su mai matuƙar karfin gar diri yake a cikin ƙasa ,"
Gaba yaron yayi zuwa wurin wani da yake tsaye a gefen ɗaya daga cikin injinan yana juye hatsi a cikin injin bayan ya gwamtsa shi da ruwa .
A kunne yayi masa maganar yana mai nuna yakaka da ɗan yatsan sa ,"
Bayan sun gama magana ya dawo wurin yakaka ,'
Yace wai shi ba zai biya ki ko sisi ba dusar da zaki tara ita ce ladan aikin ki ," kin yadda ?
Cikin sanyin jiki yakaka ta gyaɗa kan ta , "bata da zaɓi ! Amma cikin ranta tana tababar ta yaya dusa zata zama ladan aikin ta me zata yi da dusa toh ? Ko suna nufin ta ci ??
Bayan yaron ya faɗa masa amincewar yakaka , da kan sa ya taso ya zo inda take ,
Keh yane ƴar na'u ? Kin gane ne aikin yana da yawa dan haka zaki samu alheri , ina ga nima har sai kin ware min wani abu a ciki , ya ƙarasa zancen yana kwashewa da wata hautsinannan dariya ,
Biyo ni na nuna miki aikin ,
Cikin wata babbar rumfa ya kai ta , wacce take cike da mata tsoffafi da ƴan mata irin ta da ma waɗanda suka fita , wasun su a tsaye suke suna faman zirta hatsi , masara , dawa , alkama , a manyan-manyan turamen da suke watse a cikin rumfar , wasu kuma suna zaune a ƙasa suna ta faman bushe abun da suka zirtan , suna tara dusar a buhun gefen su ,"
Wani babban buhun masara da na hatsi ya nuna mata ,"
Ƴar na'u wannan ne aikin ki yau ake so , kiyi aiki mai kyau dan gaba a neme ki , kuma banda waskiya ai kin gane ? idan masu shi suka kama ki kin waske musu abun su , suka ciya miki ni babu ruwa na ai kin gane ko ?
Na gane
Toh ki zo mu je na baki aron faranti dan naga baki da shi , kuma waɗannan ƴan ciki baki baya kwalta ne , ba baki aro zasu yi ba !
Zungui zungui ta bishi a baya ,'
Daka da surfe ba sabon abu bane wurin yakaka , toh bare wannan da zirtawa ne ba surfawa ba , manyan injinan su ke yin surfe ," nan take ta kama wani turmi da ta ga babu kowa akan sa , ta ɗauki wata ɓasgararriyar taɓaryar da take jefe a gefe ta kama aikin ta babu tsayawa hira , to ma wa ta sani a wurin da har zasu yi hira?? Babu !
Kafin la'asar yakaka ta zirce hatsin da masarar tas , ta hau bushe dusar har da gyarawa , la'asar lis ta gama ta tara dusar daban-daban fiye da rabin buhu kowannen su , iyakar gajiya ta gaji , ga yunwa ga kishirwa , nan gefen ɗan buhun ta samu ta zauna tana mayar da numfashi , dayawa daga matan sun gama aiyukan su suna zaman hutawa ,'
Ba'a jima ba masu kayan suka zo ɗauka ƙarƙashin jagorancin "ubangidan ta "mai surfen , nan suka duba kayan su ," yakaka ta jawo buhun dusar ta nuna musu ,
Ɗan saurayin da ya zo ɗaukar kayan ya ciro naira ɗari biyu ya miƙa mata ya ce ta haɗa da dusar ta riƙe kamar yadda suka saba ,
Da murnar ta ta sanya hannu biyu ta ƙarbi kuɗin , cikin ran ta tana tambayar kan ta toh ita kuma me zata yi da dusa ? Ina zata kai ta ?
Tunanin ta ya katse lokacin da ta ga wasu dattawan maza da mata sun fara shigowa , da gudu ta ga kowacce mace tana surar buhun dusar ta tana kaiwa gaban su ," wannan tace tata ta masara ce , wannan ta ce ta hatsi , wannan ta dawa , alkama , su kuma suna tambayar kwano nawa ne ?? ko kuma daro nawa ?? Sai ta ga an fara cinikin dusar , ita dai tana tsaye tana bin su da ido cikin son fahimtar abun da suke ,
Kafin kace meye wannan tas mutanen sun gama saye dusar nan har sun fara lodawa a wulbaro ana jide musu , fahimtar da tayi masu sayan dusar ne , ya sa ta janyo nata buhun-hunan ta kawo gaban su ,"
Cikin tsanaki ɗan dattijon yake kallon ta duk alamun gajiya da yunwa sun bayyana a gare ta fatar bakin ta har ta bushe , jikin nan busu-busu da ƙurar dusa ,"
Kwano nawa ne ƴan mata ?
Nima ban sani baba
Ungo wannan daron hashimu juye ka auna dusar yarinyar nan kwano nawa ne ,"
Tana tsaye aka auna kwano biyar biyar ne , ta masarar da ta geron ,
Kuɗin ki naira ɗari huɗu ne ƴan mata kowanne kwano murtala biyu muke sayan sa idan dusa mai nawi ce irin taki , idan kuwa faya-faya ce naira ishirin da biyar ne kowanne kwano ,
Ɗari biyar ya miƙa mata tare da buhun ta ,'
Bari na nemo chanji baba ta furta hakan tana jin wani zallar farin ciki kamar tayi tsalle ,"
Ki bar chanji yarinya ki sayi abinci da ruwa ki sha , ki daina zama da yunwa a wannan halin da kike ciki babu kyau , Allah yaye mana talaucin da ya addabi ƙasar mu !
Har ƙasa yakaka ta sunkuya tana jero kalaman godiya kamar zata kwanta ,"
Sauri sauri ta wanke jikin ta tare da ɗaura alwala da ruwan randunan ƙasa da ta gani birjik a filin wajen , ta lura har babban bayan gida ne a wajen wanda ake shiga a yi wanka da kama ruwa bayan an gama aiki ,
Gudu-gudu tayi sallolin ta na azahar da la'asar , ta ninƙe buhun ta ta cusa shi a ɗan wani lungu , ta fito tana kallon rana yadda ta tafi tana gaf da faɗuwa , hankalin ta baki ɗaya yayi kan falmata ,
A haka ta kama hanyar kasuwar busu-busu da ita sai cin karo take da mutane waɗanda su ma suke cikin sauri domin su bar bakin kasuwar ,
A zaune ta tarad da falmata inda ta ajiye ta tayi shiru da ita ta sunkui da kai , mafi yawancin mutanen da suke hada-hadar su a wurin duk sun watse hatta baba mai kayan miya baya nan,"
Cikin sauri ta dafa falmata ,"
Falmata na dawo ,
Yakaka kin dawo sannu da zuwa , baki gaji sosai ba koh ? Baki yi aikin wahala ba ko ? Kin ci abinci ? Ya jikin naki ?
Ƴar dariyar ƴake tayi , tana mai jin yadda jiri ke kwasar ta , ƙarfin hali kawai take wurin tsayuwa akan kafafun ta ,
Falmata tashi mu ƙarasa rumfar da zamu kwana kin san fa mutumin nan cewa yayi kar mu wuce karfe huɗu da rabi , yanzu kuma ina ga kamar biyar ma ta ɗan wuce kin ga kar ya fasa taimakon mu da yace zai yi mu dunga kwana a bakin shagon sa ,:
A tSaye suka tadda shi a gaban rumfar shagon sa sai faman duba agogon hannun sa yake ," ba dan yadda yake jin tausayin yaran ba da tuni yayi tafiyar sa domin a ka'idar sa baya wuce karfe huɗu da rabi a kasuwa , sai ga shi yau har biyar da wajen minti ishirin , cikin ran sa ya aiyana ya ƙara musu mintoci goma idan basu zo ba zai yi tafiyar sa .
Sai gasu sun iso ,
A gurguje ya ansa gaisuwar su ya shiga shagon sa ya fiddo musu da jakankunan kayan su gami da tabarma mai biyu da kuma wasu robobin abinci da suke rufe guda biyu , sai jakar ruwa ɗaya , yayi musu sallama bayan ya gargaɗe su a Kan su kula da kan su ,"
Ga mamakin yakaka sai ta ga ya sauke musu jibga-jibgan labulen da aka yi da yadin tamfol duk kusurwa uku na rumfar wanda aka yi domin kare zubar ruwan sama zuwa cikin rumfar ,
kirif suka rufu daga barin idanun mutanen da suke kai kawo ba za'a san ma da mutane a ciki ba idan ba leƙawa aka yi ba , yana daga waje yayi musu sallama akan sai da safe , suka bishi da doguwar addu'a tare da godiya !
Cikin jim daɗin karamcin da yayi musu yakaka ta shimfiɗa musu tabarmar tare da kama hannun falmata ta zaunar da ita a gefen jakar kayan su daga jikin bangon shagon sai lokacin ta lura da ledar mai ɗan girma da take hannun falmatan ,"
Falmata menene wannan a cikin ledar hannun ki ??
Abincin ki ne yakaka , naga yanzu kin fi son tuwo miyar yakuwa shine na saya miki lokacin da naji baba mai kayan miya yace mai abinci ta kawo mishi , shine nima na bada kuɗi aka kawo miki , na naira ɗari da hamsin ne , ga sauran kuɗin da na samu yau ƙirga ki gani , "ta miƙa mata ledar da ta tara kudin a ciki ,
Da tarin ƙaunar ta da tausayi ta karɓi kuɗin ta kirga su naira ɗari hudu da sittin ne idan aka haɗa da kuɗin abincin da ta saya mata ya zama ɗari shidda da goma , ai kuwa lalle sun samu kuɗi ita ma ga nata naira ɗari bakwai hansin ɗin safe na abincin ta, kuɗin su sun kama dubu ɗaya da ɗari biyu da goma ,"
Falmata nima na nayi aiki na samu kuɗi har ɗari bakwai kin ji su ,
ta ɗora mata kuɗin akan hannun ta , da murna ta shafa kuɗin
kai yakaka amma wallahi mun ji daɗi kin ga sai muyi ta tara kuɗin da zaki dunga zuwa asibiti ana duba lafiyar yaron mu kamar yadda likita ranar ya faɗa ," kuma mu dunga ware ko ɗari ɗaya ne kullum muna ajiyewa dan mu sayi kayan jarirai koh ?
Idon ta cike da ƙwalla ta ce
hakane falmata kin kawo shawara .
Bari na ci abincin yunwa nake ji sosai falmata , ke ma ki ci wanda mutumin nan mai kirki ya bamu ga shi har kwano biyu , ɗayan sai mu bari da safe mu ci koh ?
Ni ban jima sosai da cin abinci ba yau sau
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 111