Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Umma , idan na dawo daga niamey zamu tafi dosso tare. bata jaa ba tayi masa addu'o'i kamar yadda ta saba tare da ƴan nasihohi , ƙarshe ta sake tunasar da shi girman nawin da ke kan sa a yanzu , ! **** Tunda ya hau kujerar zaman sa a jirgin da zai ɗaga da shi zuwa niamey ya zurfafa cikin tunani daki-daki , Da hantsi ya samu isa ƙofar gidan , kan layin shiru , da yake unguwar babu yawan mutane , ya cire ƙuɗin me taxi ya biya shi , ƙarasawa yayi jikin ƙofar gidan ya ƙwanƙwasa Hajja wacce take tsakiyar sharar ƴar harabar gidan ta saurara da kyau ta tabbatar cewa gidan nasu ake bugu , ta ajiye tsintsiyar ta ƙaraso jikin ƙofar ta tambaya wanene ?? Hajja ni ne ,     Ta shaida muryar sa dan haka ta zare sakatar ƙofar ya samu shigowa gidan , sai fara'a take masa tana lale marhabin da shi ,    Shiga ciki Babban soja bari na ƙarasa ture ɗan wajen nan zan zo mu gaisa , sannu ka sha doguwar tafiye ince kwana kayi a hanya ? Murmushi yayi ba tare da ya amsa mata ba ya sanya kai cikin gidan , Ƙiiii    Ƙarar turo ƙofar sa ta sanya ta ɗago kan ta ta dubi sashin da ta ji motsi ,    Hajja sannu da aiki ! Tace cikin ƴar muryar ta , Bai amsa ba saboda baki ɗaya hankalin sa da idanun sa na ga fuskar mama wacce take jingine da jikin falmata akan cinyar ta  , su duk biyun suna fuskantar , Taku ya fara yi yana jin yadda shauƙin son ta ke ɗibar shi , da sassarfa ya ƙarasa gaban su ya tsugunna gami da kai hannun sa ya kama ƴan kafafun ta da suke sanye da ƴar safa ya sunkuyo da fuskar sa ya sumbata yana me rufe idanun sa da jin yadda ƙaunar ta ke sake ratsa shi tare da wata nutsuwa ta musamman , me yake ƙauna irin ta tsakanin ɗa da iyaye ƙarfi tare da tsafta ??. Lokacin da ya ɗago kan sa falmata ta kawo hannunwan ta duk biyu ta ɗora akan fuskar sa , a hankali tayi yawo da hannuwan ta tana shafar fuskar sa da idanun sa ke rufe , Tamkar wuta ta jaa ta ta janye hannuwan ta da sauri , tana ɗauke mama ta ɗora kan kafaɗar ta ,   Da farko tayi zaton hajja ce ta shigo, sanin cewa daga ita sai hajja a gidan . Wa-waye ne ? Tace tana ƙoƙarin miƙewa ,       Koma ki zauna Fatima ni ne , Ya kai hannu yana ƙoƙarin karɓar mama , Ta gane muryar sa dan haka ta sakar masa mama a hankali , tana dai-daita numfashin ta da firgici ya sa shi hargitsewa , Yana karɓar ta yayi mazauni akan ɗaya daga cikin kujerun wajen ba tare da ya janye idanun sa daga kan ta ba ya shiga sumbatar kumatu zuwa goshin ta , Bai ko ji gaisuwar da falmata wacce ta zauna daga ƙasa a gefe take yi masa ba ,     ita ma shiru tayi ganin bai amsa ba Shigowar hajja ya sanya shi rungume mama a jikin sa suna gaisawa shi da hajja ,      Soja garin nan na ku kuwa ya karɓe ka , ka ga yadda kayi fes da kai kana ƙyallin fuska sai ka ce sabon ango ? Ah lalle miyar umma da zaƙi ta sa kayi shar da kai duk wannan hautsinewar sojin sun kau , ke Fatima kin kuwa gaishe da maigidan naki ?? Na gaishe shi hajja , To ban ga kin kawo masa ruwa ba , ? Zata miƙe ya dakatar da ita ƙyale ta hajja ita da take da larura baza ta iya aike ba ! Ƴar dariya hajja tayi Zata iya Babban soja ai matar ta ka ba dama akwai lura da kaifin ƙwaƙwalwa saurin gane waje ne da ita , ka ga dai ba mu rufa wata guda ba a gidan nan amma ta haddace kusan muhallin kome da kome da yake cikin gidan nan , ita da kan ta take zuwa ta ɗau ruwa a firiza ko ta je kitchen ta haɗa madarar mama , kullum addu'a nake mata Allah shi kawo mata waraka . Ɗan murmushi yayi yana duban falmata wacce ta koma ta zauna ta juyar da kan ta gefe , Kalaman hajja sun tuno masa da abunda ya so mantawa , watau kai falmata asibiti tare da samar mata gurbin karatu , Ya zama dole yayi duk wani abunda zai iya yi gurin kyautata rayuwar falmata ko domin ya samu girman laifin sa ya ragu a wajen Allah . Hajja ku shirya zamou tafi babban hospitalisé a duba lafiyar idanun fatima yanzu. !    To to yanzu kuwa , falmata tashi ki shirya bari nima na ɗan kintsa , ! Niamey national hospitalisé nan suka je , inda basu wani ɗau dogon lokaci ba suka ga ƙwararren  ophthalmologist , bayan haske-hasken da tarin tambayoyin da yayi mata akan idanun nata , a ɗakin gwaje-gwaje . Suka dawo ofishin sa inda youssouf ke jiran su , bayani ya soma yi masa daki-daki A sakamakon binciken da nayi a zahiri ban hango wata cuta ba a idanun nata sai dai raunin ƙwayar idanun nata watau ainahin jijiyoyin idanun suna da rauni , a tambayoyin da nayi mata nayi ƙoƙarin sanin tayaya ta fara samun rashin gani ko da shi aka haife ta ?  amma sai ta shaida min bata da masaniya akan mafarin samuwar rashin gsnin ta , A takaice cikin binciken da muka gudanar da kuma sakamakon amsoshin da ta bayar yayin yi mata gwaji da akwai yiyuwar dawowar wani kaso daga cikin ganin ta idan har za'a samu ƙwararrun kayayyakin aikin da zasu taimaka wajen dawo da ganin nata , Sai dai a halin yanzu bamu da waɗannan kayayyakin a nan gida niger da sauran ƙasashe masu tasowa , sai a manyan ƙasashen duniya da suka yi fice wajen samun ingantattun asibitoci masu isasssun kayayyakin aiki tare da ƙwararrun likitoci , Dan haka a yanzu abunda zamu iya yi mata kaɗai shine zamu bata magungunan da zasu iya taimakawa wajen bada kariya ga idanun nata daga kamuwa da wasu cututtukan da zasu iya kassara sauran ƙarfin jijiyar idanun da kuma hana idanun yin ciwo ƙaiƙayi da zubar ruwa ,    Da fatan kun fahimce ni ? Mun fahimta Doctor mun goude zamu dawou gare ka idan buƙatar neman taimakou game da asibitin da ya kamata a kai ta a wata ƙasar ya tasou mun goude ƙwarai Madallah . Washegarin ranar Biyamuradi bai zauna ba , ya shiga binciken makarantar makafi me kyau da yake son ya kai falmata ta fara karatu kafin lokacin da zai sake yunƙuri me ƙarfi akan lafiyar idanun nata a karo na biyu . Association Nationale Pour la promotion des aveuglés , nan ne inda ya ji gamsuwar sa akan ya kai falmata nan ta fara ɗaukar darasi , wacce jibiya ce ta koyar da makafi tare da basu tallafi me tushe daga ƙasar amurka , da ta tanadi ƙwararrun malaman makafi , Cikin sati guda yayi mata rajista da duk wasu abubuwan da ya kamata , ya samar mata da direba bayan ya sa an kawo masa ɗaya daga cikin motocin sa da suke maradi ya danƙa makullin ga hajja wacce take cike da farin cikin wannan cigaba da falmata zata samu a rayuwa . Ranar da zai bar garin zuwa bakin aikin sa jahar dosso , ya yi musu sayayyar kayan abinci da abubuwan da zasu iya buƙata tare da ƴar ƙaramar waya me sauƙin amfani ya ba wa hajja bayan ya zuba mata lambobin sa a wayar ya adana ta su a ta shi wayar , Suna zaune a falo yana musu sallama akan yau zai koma bakin aikin sa , sai kuma zuwan ƙarshen wani watan zai komo Godiya me tarin yawa hajja ta yi masa ,     Ya amsa tare da waiwayawa sashin falmata da take ta faman lila mama akan ɗan lilon ta wanda baban ta ya sayo mata su tarkacen kayan wasan yara iri-iri har da wanda ya fi ƙarfin shekarun ta , tun daga kan lilon yara , kekunan koyon zama har zuwa ƴar mota ta yara da ƙananun kayan wasanni irin na ƴaƴan gata na sosai  , bayan suturun da ya daɗa jibgo mata.    Fatima baki da wata matsala kou ? Shiru tayi tana ɗan lila mama a hankali ,   Falmata hala kin samu kurunta ? Kina jin Babban soja na magana kin yi shiru ? Uhum yau ni naga abunda ya shallake tunani na ,      Babu kome kawai ina son unmh     Uhum ina jin ki me kike so ?? A kaini makaranta   Ai na sanya ki makaranta fatima sati me kamawa zaki fara zouwa ,! Na islamiya ? Ina so a cigaba da koya min karatun addini ma ,! Toh babu damouwa idan Allah ya yarda zan bincika a samu me koyar da ke na Islama ma , Akwai wata damouwa bayan wannan ? Daman ka gaya musu zan dunga zuwa da mama makarantar ko ? Babu inda zaki dunga goyon ta kina tafiya da ita anan waje na zaki dunga barin ta idan ya so kafin ki dawo na sauya ta , ko kuwa na gudu da ita,  kina nufin baza ki maida hankali kan karatun naki bane ? Zaki dunga ɗaukar ta kina zuwa da ita makaranta ki ɓige da raino memakon karatu ni ke meyasa ana nuna miki hanya kina daɗa bauɗewa ne ?? Ɓata rai tayi ta ɗauke kai Murmushi youssouf yayi , shi dai rigimar hajja da falmata na ba shi dariya  Duba fatima ki bar mama a wajen hajja har ki tai école ki dawo Kin ji kou ?  Ba'a tafiya da yara école. Shiru tayi idanun ta na kawo ƙwalla ita dai bata ƙaunar abunda zai raba ta da mama ko na ƴan mintoci ne bare fa makaranta da awanni zata yi a can , kai anya zata iya , ? To hajja mu dunga zuwa tare da ke mana makarantar ? Sai ki dunga riƙe min mama nayi karatun na fito ? Ke raba ni da wannan gudun birin , gotai gotai da ni zani makarantar ? Yaushe rabon duniya da ayyaraye ?  Babu inda za ni ke kaɗai zaki tafi makarantar ki ki dawo ki same ni ina nan , ilmin ai shine Babban gatan ki falmata kin ji ko ? Naji hajja Yauwa mutuniyar ai shiyasa nake son ki akwai ki da saurin fahimta , Sallama suka yi da youssouf yana sake yiwa hajja godiya me tarin yawa tare da ɗanka mata ƴan kuɗaɗe wanda da kyar hajjan ta yadda ta karɓa sai da yayi ta roƙon ta da Allah  . Daga nan Dosso yayiwa tsinke bai jin marmarin zuwa maraɗi duk da cewa fiye da kaso talatin na ɓacin ran sa game da sha'anin sa da gimbiya maimouna ya kau , domin har sun yi waya ma cikin kwanaki biyun .    Assalamu Alaikum kowa da kowa ! Da fatan kuna lafiya ? Ina neman afuwar ku bisa jinkirin zuwan wannan shafin , hakan ya faru ne sakamakon tafiya da ni zuwa gida , ban samu zama ba ziyarar dangi da sauran Al'amuran yau da kullum . Da fatan zaku cigaba da haƙuri da tsaikon da ake samu cikin ajizanci irin na ɗan Adam ? Nagode     [9/3, 10:14 PM] +234 806 122 1116: Fikrah writers association MAFARI ( Hargitsin Rayuwa ) Umm'muaz 32 Bayan Shekaru Biyar Lokaci baya jira sai dai a jira shi , ba'a masa shamaƙi a yayin wucewar sa , Lokaci gudu ne da shi fiye da saurin  bugun zuciyar ɗan adam , Lokaci yayi juyi ya juya ya zo da sauyi ta mabanbantan fuskoki a rayuwar mutane a cikin tsawon shakaru biyar . Yakaka tana ɗaya daga cikin mutanen da suka samu sauyi ta fuska me kyau tare da tarin nasarori daki-daki cikin rayuwar ta , wanda a yau ta kawo matakin kammala makarantar ta secondry wacce ta rayu tsawon shekaru biyar tana faɗi tashin neman ilmi a cikin ta , da jajircewar ta tare da nuna ƙwazo ya sa aka ɗaga ta aka mata tsallaken aji na shekara guda daga jss3 zuwa ss2. Da hakan ya kawo kammaluwar karatun nata cikin shekaru biyar kachal . Ta fito da sakamako mafi kyau da ya sanyata farin ciki ita da duk wasu makusantan ta musamma malama maryam da lubna waɗanda da jajircewar su cikin taimakon yakaka a harkar ilmin ta har ta kawo wannan matsayin . Samy baby ma wacce ta tashi daga matsayin samy baby ta koma ,Hajiya samira ,"  ita ma ta taya yakaka farin cikin kammala karatun ta wanda duk wasu kuɗaɗen hidindimun karatun daga farkon sa har ƙarshen sa ya fito ne daga aljihun Alhaji Gali da har kawo yau suke liƙe a naniƙe da juna , bata da wata maraba da matar sa , kai har ma ta zarta matar sa ta aure iko da shi tare da samun kuɗaɗen hannun sa , Alhalin kuwa har yau da suke samun wajen shekaru takwas tare sun gaza yin aure ."illar bariki kenan ,! Karo na uku yakaka ta ajiye ƴar madaidaiciyar taɓaryar hannun ta da take dakan fura da ita , ta murza tafin hannun ta da suka yi ruwan hoda hoda saboda dakan da basu saba yin irin sa ba ,    Ta ɗago fuskar ta tana yamutsa ta , Ummi wallahi nagaji da dakan nan ɗan Allah ummi a min sassauci ki yadda na tafi ko'ina ne cikin garin nan na nemo furar nan nayi sadakar nan da ita , Allah bazan iya yin fura da hannu na ba , Malama maryam wacce take zaune daga gefe akan kujerar tsakar gida tana karatun littafin Al'mauduat Al'kubra , ta ɗan janye littafin daga fuskar ta    Fuskar ta babu alamun wasa ta ce ,    Sai fa kin daka furar nan yakaka kiyi sadaka da abunda kika sha wahala wajen samun sa yafi ɗaukaka darajar sadakar ki a wajen ubangiji , tsawon shekaru biyar kina faɗi tashin neman ilmin nan , a yanzu kin samu kin kai wata gaɓa me kauri ashe baza ki iya dakan fura kaɗai kiyi sadaka domin nuna godiya ga ubangijin ki ba ?? Jikin yakaka a sanyaye ta amsa    Zan iya ummi , To maza kiyi sauri ki gama dan shabiyu ta kusa , kar har  a sauƙo daga juma'ah baki gama ba kin ga kamata yayi a ce ki rabar da ita ga mabaratan da suke bakin masallacin juma'ar unguwar nan kin ji ko ?   To ummi tace tana saɓar taɓaryar ta fara daka ,    Lubna wacce take zaune a gefe kusa da ita kan ƴar darduma tana yankar ƙumba , ta ɗago kan ta fuskar ta da murmushi ta sanya hannu cikin faffaɗan kwanon silver da aka ajiye guntun dafaffiyar furar da ba'a kai ga daka ta ba , ta gutsuro wata ƙatuwa ta sake jefawa cikin turmin da yakaka ke daka ,    Yauwa ƴar ummi yi maza ki daka,  na ɗebo madara na fara damu ni ce ta farkon sanya Albarka a result ɗin nan kin sani ko ?    Ummi kina ganin ta fa ? Tana ƙara min wata bayan na kusa gama dakan   Lubna maza ajiye nails clipper nan ki karɓi dakan nan ki taya ta ,    Ta furta hakan tana gyara zama gilashin idanun tana cigaba da karatun ta .   Ummiii , dan Allah ni lokacin da nayi nawa dakan futar gama makarantar ta taya ni Haba ummi dan Allah,    Wallahi na taya ki kin manta ranar ....    Yanzu aikin samun ladan kuke yiwa haka ?    To shikenan duk ku bari ni zan zo na ƙarba nayi tunda da alamu ku lada yayi muku yawan da ya sa har kuka fara gudun sa ,   Da sauri lubna ta zaburo tana ƙoƙarin karɓe taɓaryar hannun yakaka ita kuma yakakar ta riƙe gam ta hana ta ,   Dan Allah ki bar ni na taya ki kin ji sahiba ta.     Tare da marairaice murya   Naƙi ɗin  , nima zan daka kaya na duk na mulmula na ɗau abuna a kai naje na rabar , kin ji sahiba ta . Wayar lubna da ta ɗau kiɗa ita ta raba musu gardama    Cikin sauri lubna ta ɗau wayar ta ta yi hanyar falo tana satar kallon ummi wacce bata nuna alamun ta san duk abunda suke a wajen ,   Yakaka ta bi bayan ta da kallo tana murmushi Ta kai gaf da shiga falon ta ɗaga murya tana cewa ,    A gaishe min da yayan namu da kyau da kyau kin ji sahiba ta ? Da gudu lubna ta ƙarasa shigewa falon tana dariyar jin kunyar ummi . Ƙarfe biyu dai-dai da idar da sallar juma'a yakaka da lubna sun kammala ɗaura fura guda uku uku a cikin farar leda tare da kindirmo me ɗan dama shima a ƙulle a leda daban , suka haɗa su suka zuba a ƴar bakar leda daban daban , ba laifi dayawa , Yakaka ta jaa hijabinta saka lokacin da ta gama saka socks ɗin ta a kafa ta zura hijabin tana kallon lubna wacce take ƙoƙarin ɗaura niƙaf ɗin ta ,    Sahiba dan Allah muyi sauri kar mabuƙata su watse ,     Taku biyu tayi ta ɗauko niƙab ɗin ta ruwan madara , mahaɗin hijabin ta ta  fara ƙoƙarin ɗaurawa a fuskar ta , Da sauri lubna ta riƙe niƙaf ɗin ,   Haba sahiba ta ? Ina mun yi cewa kin daina saka niƙab ɗin nan haka sai bayan kin yi aure ?? Hararar ta tayi    Shiyasa na ga ai kema yanzu da za ki fita babu naƙib ɗin a fuskar ki , ni dan Allah sakar min mahaɗin kwalliya ta , cikamakon martaba ta ,na sanya abuna ,    Amma ai ni kin san dai an riga an sanya rana , babu sauran wani ɗa namiji da zai sake cewa yana so na na kula shi ,    Ok to maza yi min gorin aure sahiba ,    Ta furta hakan muryar ta babu alamun wasa .   A hankali ta sakar mata niƙab ɗin , Allah ya baki haƙuri sahiba ba manufata ba kenan .  Mu tafi . Yakaka wacce bata furta zancen da wata manufa ta daban ba daga cikin ran ta sai domin ta samu lubna ta sakar mata niƙab ɗin ta da take neman ƙarfi da yaji ta hana ta sawa a cewar ta shi yake hana samari kula yakakar tunda ba ganin fuskar ta suke ba , duk sai ta ji ta ba daɗi da ta ga kamar zancen ta ya sa aminiyar ta a damuwa . Tafe suke akan hanyar su ta dawowa daga rabar da furar suna tafe suna hirar su hankali kwance irin ta shaƙiƙan ƙawayen da halin su da ra'ayoyin su suka zo ɗaya suke kuma ƙaunar juna domin Allah , Motar da take tahowa daga bayan su sannu a hankali saboda ruwan sama  da ya kwanta bisa kan kwaltar , wacce ta fito daga layin gidan su yakaka ,ita ce ta matsa musu hon , Su biyun suka haɗa ido , yakaka ta janye hannun lubna , da nufin ko Suna bisa hanya ne sun matsa daga hanyar , Maza biyu ne a cikin motar wanda kallo guda za'a musu a gane cewa ba ƙananun samari bane , mazaje ne waɗanda suke kan ganiyar shekarun su na 40 cif , wayewa tare da gogewar da ta bayyana kan ta a jikin su ita take nuni da tarin ilmin da yake jibge a ƙwanyar su , ɗaya yana mazaunin direba yayin da ɗayan yake daga gefen sa , Na gefen ya kai hannu a karo na biyu da nufin sake danna hon , na gefen nasa ya tare hannun nasa ,   Suleiman meye hakan kake kuma ? Yace yana kai kallon sa gare shi ,    Dan Allah abokina yi parking ka bani mintuna biyu zan fita ,   Bai ce masa ƙala ba saboda yanayin sa da bai tare da nishaɗi ya sa baya buƙatar doguwar magana , ya gangara daga gefe ya tsayar da motar , Da sauri suleiman ya fice daga motar , A hankali yayi musu sallama cikin nutsuwar da take halittar sa tun ƙuruciya , Tana jin muryar sa ta gane shi , shine dai maƙalemata manne matan da ya liƙe mata tsawon shekaru uku yana bibiyar ta ba tare da ta taɓa saurarar sa ba , Matsa hannun lubna da yake cikin nata tayi , ta mata alama da kar ta kula sa , sai dai irin nutsuwa tare da kamala da ƙwarjini na musamman da lubna ta hango a gare shi ya sa ta fahimci ba irin sa ne mazan da mata ke gwatsalewa ba dan haka taƙi amfani da umarnin yakaka ta ja ta tsaya tare da amsa sallamar sa  Baiwar Allah naji daɗi da ki ka tsaya kika amsa sallama ta domin nasan da ta ƙawar ki ce baza ku tsaya ba , dan kuwa tsawon shekaru kusan uku kenan ina bibiyar ta amma bata taɓa tsayawa ta saurare ni ba,   Da sauri lubna ta kai kallon ta ga yakaka wacce ta yi gaba kaɗan ta tsaya tare da ɗauke kai daga barin kallon su . Dan Allah kayi hakuri, tace da shi , girman sa na sake cika mata idanu Babu kome duba da cewa a yanzu bisa titi muke ba darajar mu bace yin magana anan dan haka ki sanar da ni adireshin da zan same ki ko kuma number ta wayar ki saboda ina son yin magana da ke game da ƙawar ki idan kin bani dama , Da sauri lubna ta ba shi number wayar ta , tana jin farin ciki na ratsa ta , a karon farko yau wani namiji ya nuna yana da ra'ayi akan yakaka , namijin ma gangariya irin wannan ai kuwa yau ummi na da farin labari . Bayan ya karɓi number yayi mata sallama ya juya wajen motar su , da ƴar dariya a fuskar sa ya dubi abokin sa da hankalin sa ke gefe guda da alama yayi zurfi cikin tunani . Abokina ka taya ni murna ga alamu na sanya ƙafa a kasancewa mijin mata biyu , ramla ta kusan samun abokiyar zama , tsawon shekara uku da nake bin yarinyar nan tana yin biris da ni , sai yau nayi sa'ar haɗuwa da ƙawar ta ga alamu ita zata min tsani na samun ta ,  na rasa me yake fusgata akan ta alhalin sau biyu kawai na taɓa ganin fuskar ta , Da alama akwai rabo ne a tsakanin mu me ƙarfi , A hankali ya tada motar ba tare da ya bada muhimmanci a zancen nasa ba , To ai sai ka ɗau harama , takaicin matan duniya ne bai ishe ka ba , ko kuwa ma nace har yau baka san wacece mace ba da irin tarin abubuwan ƙi da yake tare da ita da ace ka sani da baza ka yi sha'awar ajiye su har su biyu kamar kayan ado a gidan ka ba , Wuce su suka yi a hankali , Lokacin da suleiman ke bashi amsa Hamza kenan kai dai na rasa wanne irin tabo mace tayi maka a duniya kake musu irin wannan kuɗin goro , duk kuwa da yadda safiyya take tarairayar ka tare da lelen ka kamar wani jariri sabon haihuwa , bana jin ta taɓa saɓa maka a rayuwar zaman auren ku . Ya ƙarasa zancen tare da dariyar shaƙiyanci . Murmushin takaici doctor hamza yayi ,    Baza ka taɓa ganewa ba suleiman ! Ya maida ganin ga madubin  motar sa , yana hango ta ta jikin madubin ƙwarai tafiyar ta ta ɗau hankalin sa , mace ɗaya ya taɓa gani da salon takun nan , wacce bai ko son giftawar tunanin ta cikin ran sa sai fa yau da ya sake ganin wata wacce fuskar ta take a rufe  Bai kai ga ganin kamannin ta ba

Chapter 57 of 111