ɓalle murfin motar ta fita , hankalin ta gaba ɗaya yayi kan falmata , bata damu ba sam da sauyin yanayin da ta gani tare da shi da damuwar da ta bayyana a gare shi , bare har tayi wani dogon nazari akan hakan ,"
Gyara zaman hijabin ta tayi tare da sake riƙo ledar hannun ta da kyau ,ta kama tafiya ,"cikin ran ta tana aiyana baza ta sha wannan kayan daɗin ba falmata zata ajiyewa tana farkawa ta bata ta ci ta sha !
Tuƙi yake yi akan hanyar sa ta komawar sa gida amma rabin hankalin sa bai tare da shi , yana ga tunanin halin da yarinyar ta tsinci kan ta a ciki , ba zai yiwa kan sa ƙarya ba tun da jimawa ya fahimci ya faɗa tsundum cikin so da ƙaunar yarinyar da ko a mafarki idan aka ce masa shi zai so mace irin ta zai ce ƙarya ne , toh amma tun da ya gagara kaucewa faɗawa a soyayyar ta , sai ya ɗauki hakan a matsayin kaddarar sa ce watakila matar auren sa ce ubangiji ya turo masa ita a haka , dan haka sai ya shiga neman hanyar da zai yi ya gyara ta ta zamto irin macen da shi yake son ta kasance matar aure a gare shi , karatu yake da nufin sa ta a farko bayan ya kai ta gidan su wurin mahaifin sa , tayi karatu mai ɗan zurfi zuwa ko da matakin diploma ne sai ya aure ta ,
Toh sai kuma ƙwatsam ta ɓace masa , ya sha wahalar neman ta bata nan ! , har ya fara dangana da rashin ta sai kuma ta ɓullo da wani al'amari mai girma a tare da ita ,"ciki ba tare da tayi aure ba , baya tunanin ko uban cikin jikin nata ta san shi ," Al'amarin ba ƙaramin firgita shi yayi ba ya taɓa ran sa fiye da zato , saboda soyayyar gaskiya yake yi mata ,"
A tun bayan barin ta da yayi yanzu ya kamo hanyar sa yake bincikar kan sa tare da ƙwanƙwasar zuciyar sa ko Allah zai sa ya ji wani sauyi na daga soyayyar da yake mata ta zuwa wani yanayi na ƙi ko kaɗan ne a saboda girman bakon al'amarin da yake tare da ita marar kyau ?
Wanda zai yi amfani da hakan wurin yakice ta daga cikin ran sa baki ɗaya ya shafe babin rayuwar ta daga ran sa ?
Sai dai ko kusa shi ya gagara ya ji alamun ya tsane ta , a maimakon tsanar sai yake jin wani matsanancin tausayin ta yana sake lulluɓar shi , zuciyar sa tana raya masa FYAƊE aka mata , fin ƙarfi aka gwada mata ba da son ran ta bane , ita ɗin abar a tausayawa ce , abar a tallafa ce a bata kulawa , a tsaretar da rayuwar ta daga faɗawa mummunan yanayi dangane da irin halin da ta tsinci kan ta a ciki a ƙarancin shekarun ta ,"
Sashi mafi rinjaye na zuciyar sa ya ji yana ƙarfafar sa akan Ya tallafe ta , kar ya guje mata , ya zamto gata a gare ta kar ya ƙyamace ta , ya Aure ta ya taya ta riƙo tare da tarbiyyartar da abin da zata haifa HAKAN TAMKAR JAHADI NE a gare shi ,
Da wannan dogon tunanin ya ƙaraso gidan su da yake kan titin danboa road yayi hon maigadi ya buɗe masa kofa ,
kai tsaye falon mahaifin sa yayi wa tsinke bayan ya ajiye motar sa ,
kamar yadda ya saba a zaune ya tarad da shi bisa wheelchair hannun sa riƙe da Alqur'ani mai girma yana ƙarantawa da mabayyanin sauti .
Sai da ya ɗan tsimaye shi ya ƙarasa ayar da ya ɗauko ,
Sannan suka gaisa cikin kulawa da nuna tsantsar ƙauna daga mahaifin sa ," ƴan tambayoyi yayi masa game da yanayin aikin sa kasantuwar mahaifin na sa professor ne da ya sha ya ƙoshi ya tumbatsa a harar ilmin kimiyya , yanayin rayuwa ya juyar da lamarin sa haka ya kasance zaune bisa kujerar marasa lafiyar ƙafa bai zuwa ko'ina .
Ji yake batun yakaka yana zungurar sa akan ya faɗawa mahaifin sa , wani sashin ya dakatar da shi da ya bari har ya samu ƙarin bayani daga bakin yarinyar dalla-dallah ta yadda zai ji karfin zuwa da maganar tare da amsa duk wasu tambayoyi da ka iya zo mar daga baban sa !
Dan haka ya miƙe yana mai yin sallama da baban nasa ,
Har ya ɗauki hanyar sashin sa , sai kuma ya dawo ya kutsa kai zuwa ainahin cikin gidan sashin mahaifiyar su da yanzu ƙannen sa ne ke rayuwa a ciki ,
A babban falon ya tarar da su suna harkokin su , ƴan mata ne su uku ya da ƙanwa , babbar cikin su zata yi kimanin shekaru ishirin da biyar sai mai bin ta sai kuma ƙaramar su ,
Har suna rige-rige wurin gaishe da yayan nasu inda shi kuma ya amsa musu da yalwatatciyar fara'a bisa fuskar sa ,'
Girls , so nake ayi girki mai kyau wanda marar lafiya zai ji daɗin ɗanɗanon sa a bakin sa , kamar girki kala biyu haka , a dafa tea da kunu nan da awa biyu zan shigo na ɗauka ,"
Toh company
Suka haɗa baki wurin amsa masa tare da barin abun da suke suna nufar hanyar kitchen , ta cikin falon
Ƴar dariya yayi yana girgiza ,"
Nace muku sunan nan ya fita a bakin ku ko ? Ya furta hakan yana mai nufar hanyar barin falon
Har ya fita , ya dawo ,"
Zahra !
Ƙaramar su ta amsa gami da dawowa baya ,
Na'am big bro
Nace ba ! a cikin kayan ki ki ware kamar kala biyar masu kyau ki ajiye idan na zo ɗaukar abincin marar lafiyar zan haɗa da kayan na kai musu ,
Toh big bro zan ɗauko yanzu , biyar sun isa ko ?
Sun isa! ya ansa yana barin falon .
A duk ranar da ya kwana a asibiti toh yini yake yana bacci idan ya dawo , sallah kaɗai ke tashin sa sai ko cin abinci , kafin zuwan wani daren , saɓanin yau da sam ya gaza yin bacci sai juye juye yake yana kallon agogo , zuciyar sa ta zurfafa wurin son samar masa da mafita , shin daga ta haihu ne zai aure ta ko kuwa zai bari tayi karatu kamar yadda yake da buri ??
Tunowa yayi bai san matsayin sa ba ma tukun a gurin yarinyar duk wannan tsare-tsaren iska yake , daga ta nuna ƙin amincewa kome ya rushe ,
ba shiri ya miƙe daga kwanciyar da ya samu kusan awanni biyu yana yi ,
Karfe ɗaya da mintuna goma agogon ɗakin ya nuna , lokacin sallar azahar ya shigo ,
Kai tsaye ya sake shiga banɗaki ya sakarwa kan sa ruwa tare da sake ɗaura alwala ya fito ,"
Mai ya shafa sama-sama ya buɗe ma'ajiyar kayan sa , ya ɗauko wani shuɗin yadi marar nawi mai haske ya saka , ƴar saisayayyar sumar sa ya taje har zuwa ɗan zagayayyen sajen da ya ajiye a gefe da gefen fuskar sa , ya ɗauko turarukan sa ya fashe jikin sa .
Ya zurara bakaken takalman sa yana ɗora igiyar ɓakin agogon hannun sa ,
Ficewa yayi a ƙafa ya nufi babban masallacin da yake bakin titin shigowa unguwar su domin yin sallar azahar .
Ƙarfe biyu dai-dai tayi masa a harabar asibitin , kai tsaye ya nufi emergency ward , hannun sa riƙe da ɗan kyakkyawan gwandon roba mai ɗan girma da aka zubo kulolin abinci zuwa ƴan ƙananun flask guda biyu da cups biyu , chokula biyu da plates guda biyu sai serving spoon , ɗayan hannun nasa kuma ya riƙo ɗan ƙaramin akwati ,
Da gudu security ya taso ya karɓi kayan hannun nasa yana masa sannu da zuwa ,"
Yana shiga ya tarar da babu gadon falmata , ya tambayi likitan ina yarinyar da take gado mai lamba goma ?
Nan yake sanar da shi ta farka har an mata chanjin ɗaki zuwa cikin ward , dan haka ya nufi ward , security biye da shi .
Tun yana shiga ya hango su falmata daga ƙuryar ɗakin gado na ƙarshe , tana kishingiɗe an ɗago mata gadon ta wajen kan ta domin ta ji daɗin kwanciya ,"
Yakaka tana ɗosane a bakin gadon ta tattara hankalin ta baki ɗaya ga falmata tana shayar da ita hollandia yogurt sannu-sannu ,
Tana labarta mata irin jimawar sa tayi a sume da taimakon da dakta hamza yayi musu ,"
Sannu patient ɗina kin tashi ? Ah lalle jiki yayi kyau tunda ga shi har kina shan yogurt , to yaya me kike ji yanzu a jikin ki ? Akwai inda yake miki ciwo ?
Da ƴar fara'ar ta ta waigo inda take jin tashin muryar sa ,
Da sauki dakta , dai-dai wurin raunin kawai shine yake min zogi , sai kuma kaina da yake min ciwo kaɗan-kaɗan , mun gode dakta Allah ya saka da aljanna ,"
Murmushi ya mata , cikin ran sa yana jin tausayin makantar ta ,"
Babu kome ɗan pain ɗin da kike ji saboda sabon rauni ne , daga ya ɗan yi kwana biyu zaki daina ji , ciwon kan da kike ji saboda sabon jinin da ya shiga jikin ki ne , zai daina da zarar jikin ki ya dai-dai ta ,' akwai magungunan ɗauke zogin ciwo za'a kawo miki ," ki dunga cin abinci sosai saboda ki samu ƙarfin jiki ,"
Duban sa ya mayar ga yakaka wacce tun da ya ƙaraso ƙamshin turaren sa ya bigi hancin ta ta ji zuciyar ta ta hautsina , sam ƙamshin bai mata ba , dan haka ta koma daga gefe ta tsaya tana yatsina fuska gaba ɗaya gumi keto mata yake amai yana sasuƙar ta sai dai kuma babu kome a cikin ta idan banda ruwa ,"
Ga abinci nan ku ci , kiyi wanka ki sauya kayan jikin ki , ga kaya nan na taho miki da shi a cikin nan ,
Ya mata nuni da kayan da security ya ajiye a gefen gadon ya tafi, "
Kai ta gyaɗa kafin ta ce
Mun gode Allah ya biya ," cikin ran ta tana Allah-Allah ya tafi saboda warin turaren sa da ke neman kai ta ƙasa , babu abun da take so a yanzu irin ta shaƙi ƙamshin turaren bature kam silum , wanda ta san babu damar hakan domin kayan su yana kulle cikin shagon ", Abuwar mai yadi ," dan haka ta Kai hannun ta biyu ta sa ta rufe rabin fuskar ta daga kan hancin ta zuwa ƙasa ,"
Ware idanun sa yayi sosai yana kallon ta , yadda ta toshe hanci ya sa shi ɗan shaƙo numfashi ko zai ji inda wari yake tasowa amma shi bai ji ba ,"
Bai ce kome ba ya juya ya fara tafiya , tare da cewa watakila zan dawo zuwa yamma ," !
Gaskiya kwana biyu ina mutunci kut! 😂
Watau rubutu nake muku babu kakkautawa, duk domin na Baku nishadi. 😍
Da fatan nima zaku bani tukuici , ta hanyar fada min ra'ayoyin ku, / Me kuka tsinkayo zai faru nan gaba?
Wai shin bakwa cigiyar biyamuradi YOUSSOUFA ne? ? 😂
[6/24, 10:59 AM] +234 701 013 7848: MAFARI......
( Hargitsin rayuwa )
umm'muaz
23
Cikin sati guda da suka yi a asibiti sun ga gata tare da kulawa daga wurin doctor hamza , har ma da ƙanwar sa rahima, domin kuwa kusan kullum sai ta zo da yamma ta taho musu da abincin da take girka musu na dare , shi kuma doctor hamza ke zowa da na safen ," da rana kuma ya yo musu take away daga sidic's ,ruwa kan sa na roba suke sha , ga lemuka da kayan shayi irin na garari , biscuits, cake , lokar gadon su cike take taf da cimaka iri-iri , tamkar dai wasu ɗiyan attajirai ,
Rahima tana da matuƙar surutu da wayon tsiya, yarinya ce da kaɗan ta girmewa yakaka , bai wuce shekaru biyu ta bata ba , ita ce ƙarama a ƙannen doctor hamza ," a halin yanzu ta gama secondry sch tana jiran sakamako , "
doctor hamza shi yace mata ta dunga zuwa ta na ɗan taya su hira ko da ta awa biyu ce , bayan ya nemi iznin mahaifin su , yayi masa bayanin su falmata da ƙudirin sa akan su na taimaka musu, sai dai ya boye masa cikin jikin yakaka na banza ne ,maimakon ya fadi gaskiya sai ya ce masa boko haram ne suka kashe mijin ta tun a garin su ,"
Maifinsa bai ƙi ya kawo su gidan su zauna ba , sai dai yayi masa gargaɗi mai karfi kamar yadda ya saba yi masa a kullum cewar ,"Ya tsoraci MATA tare da ƙaidin su yayi hankali da lamarin mata domin sau dayawa su ɗin ba'a gane gaskiyar su , wanda duk ya bada gaskiyar sa a gare su tabbas zasu takaita shi watarana ,"
Kamar koyaushe ya amsa masa yana jin yadda wani ɗaci ke yawo a zuciyar sa , sam bai so ba da mahaifiyar su ta zamto silar da ya sa mahaifin su ya samu mummunan tabo akan mace da yakasance kullum kalaman sa masu tsauri ne akan MATA ,
*********
Yau yake da niyyar kai yakaka ayi mata scan tare da gwaje-gwajen da ya kamata ayi wa mata a tun farkon samuwar cikin su , duk da cewa har kawo yau bai sake tada maganar cikin ga ita yakakar ba wacce ya lura ita bata da wata damuwa da zaman cikin a jikin ta ,
abun da bai kai ma ga gama fahimta ba kamar son cikin take sosai , saɓanin sauran matan da ya sani da suke shiga damuwa tare da ƙin abun da yake cikin nasu a duk lokacin da suka samu cikin ta haramtatciyar hanya irin nata ,
sai dai ya danganta hakan da kasancewar yakaka yarinya ce kuma akwai ƙarancin wayewa da rashin ilmi a tare da ita , ko ma menene shi daman ba shi da burin raba ta da cikin jikin ta wanda ya riga ya fahimci yayi ƙwari a mahaifar ta .
Ya zaɓi ya kaita wani asibitin daban a duba ta ne a saboda ƙoƙarin sa na kare martabar ta ko da anan gaba ya aure ta , domin a halin yanzu kowa ya san ba shi da mata , to kuma duk sauran likitocin da zai iya haɗa yakaka da su , abokanen aikin sa ne da suka riga suka san juna sosai ,ya kai ta wurin su a zuwan matsayin me take a gare shi ?
Bai son a kodayaushe ya dunga yin ƙarya dan haka ya fi son ya kaucewa duk wani abun da zai sa shi yayi ƙaryar ,"
Sai da ya bari rahima ta zo misalin karfe huɗu da rabi , ta hau sama ofishin sa tare da ajiye masa na shi abincin , nan yake sanar da ita zata Zauna tare da falmata , shi da yakaka zasu je wani waje su dawo ,"
Tare suka shiga ward ɗin inda suka tarar da su suna ƴar hirar su , babu laifi cikin sati guda falmata ta ji sauki sosai saboda kulawar magunguna masu kyau da take samu zuwa abinci mai inganci , uwa uba kwanciyar hankalin da ta samu , yini take a kan gado iskar fanka tana kaɗa ta , ga ta ga yakakar ta a gefen ta , wanda hakan shi yafi kome sanya ta farin ciki ,
Cikin fara'ar da jin muryar su ya sanya ta take gaishe da doctor hamza da zuwa yanzu take matuƙar girmama shi tare da ganin ƙimar sa har ma take jin sa a matsayin wani jigo cikin rayuwar su ita da yakaka ,
Shima faram-faram ya amsa mata yana mai sake tambayar ta yanayin jikin nata , kafin ya maida duban sa ga yakaka wacce take zaune bisa kujerar gaban gadon , "suna gaisawa ita da rahima wacce suka yi sabo da juna cikin ƴan kwanakin ,"
Duban ta ta mayar kan doctor hamza tana mai gaishe shi , cikin ƴar siririyar muryar ta ,
Fuskar sa a sake ya amsa mata yana mai kallon fuskar ta da take fayau babu ko ɗigon kwalliya sai ƴan siraran shunkuran ta "zane" da suke tarwai akan farar fuskar ta ,
Fatima zamu je na kai yayar ki wani wuri baza mu daɗe ba zamu dawo ga rahima nan zata kula da ke kafin dawowar mu kin ji koh?
Toh yaya dakta sai kun dawo ! Yakaka sai kun dawo !
Zo mu tafi ,"
yace da ita yana mai fara taku ,"
Tiris ! tayi akan kujerar , ina kuma za su ? ? Ita fa sam bata son kaɗaicewa da shi , duk ya bi ya ishe ta da kallo ga warin wannan ƙaƙƙarfan turaren nasa da ba so take yi ba ,"
Kallon fuskar rahima tayi wacce ita ma ɗin ita take kallo cikin nazari , dan haka ta miƙe a sanyaye gami da yi musu sallama bayan ta jaddadawa falmata akan yanzu zata dawo !
A motar sa suka fita a asibitin , duk da cewa har zuwa yanzu bai faɗa mata inda zasu ba ," sai da ya hau titi ɗoɗar tukun ya juyo ga kallon sa kan ta da ita kuma ta juya fuskar ta ga kallon titi ,"
Ƴar kwantatciyar sumar da take gefen kunnuwan ta zuwa gaban goshin ta da tayi luf-luf yayi wa kallon daƙiƙai kafin ya maida kallon sa ga titin gami da yin gyaran murya ,"
Asibiti zan kai ki a auna ki tare da duba lafiyar abun da yake cikin ki , dan haka ina son sanin sunan ki mai kyau , domin ayi amfani da shi wurin buɗe miki file ,"
A hankali ta juyo da ganin ta kan shi ,"
Cikin ran ta tana jin daɗin yau karo na farko bayan ita da falmata wani ɗan adam ya nuna kulawar sa akan cikin jikin ta har ma zai kai a duba lafiyar abun da yake cikin , "
Sai dai tambayar sa ta ƙarshe ta bata mamaki daman duk zaman su bai taɓa sanin sunan ta ba ???
Babu shakka ita bata taɓa ji ya kira sunan ta ba , ko magana zai mata kawai yana jefa maganar sa ne a saitin ta kai tsaye ba tare da ya kama sunan ta ba ," amma ai yana ji koyaushe falmata tana kama sunan ta a gaban shi , sai dai idan wani walakanci ne hakan ," zai ce bai san sunan ta ba .
Kamar ya san tunanin da take
Ba tare da ya dube ta ba yace ,"
Sunan ki mai kyau nace ,"wannan sunan da ake kiran ki da shi ba suna mai kyau bane dole akwai ainahin sunan ki ,
Bani da wani suna bayan wanda ake kira na da shi ,"
Ta bashi amsa ƙasa-ƙasa , a ran ta Kuwa tana jin haushin kalmomin sa ya za'a yi yace sunan ta bashi da kyau ??
Ba wanda ya sake cewa ƙala har suka ƙaraso ɗan ƙawatatcen asibitin mai zaman kan sa da yake cikin unguwar G.R.A ,
Jerowa suka yi suna tafe tamkar sabbin ma'aurata , ta wutsiyar ido ya kalle ta tana sanye ne da wata atamfa ruwan ɗorawa da aka yiwa dinkin doguwar riga wacce ta buɗe daga ƙasa , ɗaya daga cikin kayan da rahima ta ba su ne ," nan ya ga yadda ɗankwalin kan ta yayi baya sosai har ya bayyana lallausar sumar da take gaban kan ta , gyalen ta da ta rufu da shi daga kafaɗar ta iskar juyin yanayi da ake na ta kaɗa shi ,"
gani yayi ta yi masa kyau ba kaɗan ba ,"
Sam baza'a ce mace mai ciki bace , domin idan ban da cikar da ta sake yi tayi ƴar ƙiba kaɗan tare da ƙarin haske , babu wani alamun ciki , cikin bai bayyana a sarari ba ,"
Ki gyara ɗan kwalin ki , kuma ki rufa gyalen zuwa kan ki ,"
Ta tsinkayi muryar shi yana bata umarni ,"
ba tare da ta ce uffan ba tayi yadda yace lokacin da suke ƙarasawa cikin ainahin asibitin ,
Ba tare da ɗaukar lokaci ba ya shige gaba ya kammala kome da ake yi a dokar asibitin kafin a ga likita , wanda kuɗaɗe ne tsababa saboda asibitin na manya ne ,
Wurin bada sunan ta ne ya so shiga ruɗani kafin lokacin da zuciyar sa ta yanke masa shawarar abun da ya kamata ,"
Aka yi musu jagora zuwa wajen ainahin babban likitan mata da yakasance shine mamallakin asibitin baki ɗaya ,"
Nan ya tare su da fara'a duk da cewa ba wai ya san doctor hamza bane amma yanayin sa ya bayyana masa wayewar sa tare da ilmin da ya hango tare da shi , "
Bayan bayanin da doctor hamza yayi masa akan a duba lafiyar uwar da abun da yake cikin ta tare da son sanin ranar da zata iya kasancewa ranar haihuwar ta ,"
Likitan ya fara aikin sa cikin gwanancewa, nan ya fara da ɗaukar jinin ta domin yin gwaje gwaje , ya kuma bata wata ƴar roba yace ta kawo fitsarin ta tare da ƙiran ɗaya daga cikin nurses akan ta gwada mata banɗaki , bayan ta dawo yayi mata awun blood pressure, ya ga jinin ta dai-dai ne , sai yayi umarni da ta hau wani ɗan gadon duba marasa lafiya da yake gefe guda cikin ofishin domin yayi mata scanning ,"
Da jaan ƙafa ta ƙarasa bakin gadon ta hau ta zauna ,"
Kallon ta likitan yayi lokacin da yake jona na'urar da jikin babban tv da yake kafe a gefe ,"
Amarya gyarawa zaki yi ki kwanta mai kyau ki miƙe kafafun ki ,"
A ɗarare tayi yadda ya umarce ta tana mai sake gyara rigar jikin ta da kyau ,"
Da ido doctor ya yi wa hamza alama akan ya mata bayani yadda zata gane ,"
Ki ɗaga rigar ki , ki buɗe cikin ki hoton jariri za'a yi ta haka za'a gane lafiyar sa ," ya furta hakan yana mai maida ganin sa ga fuskar wayar sa ,"
Hoton jariri??
Ai kuwa zata so ta ga hoton abun da yake cikin nata ," wataƙila yayi kama sosai da baban sa ? ," tuno da hakan da tayi ya sa wani siririn murmushi ya bayyana kan fuskar ta ,
ta tashi tsaye ta tattara doguwar rigar ta , dogon wondon da ta sa ta ciki ya bayyana ,"
Cikin nutsuwa ya fara mata scanning ɗin , yayin da shi da dakta hamza suka maida hankalin su baki ɗaya ga fuskar tv lokacin da ƴar jaririyar da take cikin mahaifiyar ta ta bayyana tana ta hidimar ta hankali kwance, a yau tana da sati goma sha tara da kwanaki biyar , "komen ta yana lafiya ƙalau a yanayin da ya dace ,hasashen ranar haihuwar ta ya nuna biyar ga watan goma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 111