Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 9
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels KOWA YA RAINA TSAIWAR WATA 3 Bilkisu S. Ahmad Funtuwa Wanshekare ran asabat da sassafe katon din madara da na suga da gwangwanayen bonbita, sannan gaba daya but din motarsa an danno shi da biredi dan bisije, wannan saye-saye Yusuf ne ya aiki Falanke da direbansa har garin Funtua aka sawo, ya ce akai gidan marigayi Baba Kado. Haka nan ya bada sakon kaji hamsin da shinkafa da kayan miya ya baiwa Gwaggo Halima ya ce ta girka akai sadaka gidan Baba Kado. Da la'asar sakaliya kuma ya aiki Falanke ya amso inda ya kai gashin rago shi ma ya ce akai sadaka gidan Baba Kado, yadda ya rinka aikawa kuwa da lemon kwalba kuwa ko bikin diyar manajan kanfanin lemo sai haka.Wannan abubuwa da Yusuf ke yi bai daurewa kowa kai ba domin an san matsayin Baba Kado a wajensa, illa dai kawai zargi na mutane da ba'a hana su. Abinci kam gidan Alhaji Kado ko bikin Amiru da Hadiza za'a yi iyakarshi kenan, almajirai su kam kamar sallah a wajensu ,haka nan gidan ya kara samun jama'a yan zarnan makoki albarkacin abincin da ake ci. Jama'ar Hadiza na wajen aikinta sun zo yi mata gaisuwa haka nan Rilwan da iyalansa sun zo dagaJos hatta Yallabai Mamud da ya sami labarin rasuwar. Ya gaisa da kungiyar su Amiru da Yusuf inda suka yi shinfidar su can nesa da ta dattawa, ya so kwarai anuna masa mijin da Hadiza zata aura amma hakan bata samu ba. Amiru ya fara tsarguwa lalle abubuwan da Yusuf ya ke yi a bisa dalilai uku ya ke yin su: na farko matsayin Baba Kado a wajen Yusuf sai na biyu saboda Hadiza sannan na uku a daliiin shi Amiru amininsa. Wa'annan abubuwa sun taru a lokaci guda sun rudewa Amiru, duk yadda za'ayi Hadizan shi itace ainihin Dijen daYusuf ya guje mawa saboda son Fa'iza, Dijen da ya muzanta akan wai bata da fasali, shin in ko haka ne itama Hadiza ta rufe masa gaskiyar labarinta, domin cewa tayi dan`uwanta ne ya guje ta a dalilin ta yi masa kankanta, me yasa Hadiźa ta sakaya wannan lamari a gareshi? Ya yi sauri ya kawad da zarginta a zuciyarsa ai dole ne ta sakaya har yaushe za ta fada masa wannan fallasa da Yusuf ya yi mata?Abin damuwa dai daya ne anan shi ne Yusuf wannan rawar kafar da ya ke yi akwai abinda ya ke so, don sai ya yi takatsantsan da shi, kai amma Yusuf zai 1 iya mai cin mutunci irin haka don ko budurwa suka gamu da ita duk irn yadda ta burge Yusuf da zarar Amiru ya nuna sha'awarsa shi kenan Yusuf ya haranta ta. To amma rudin da ya ga Yusuf ya shiga a tun daren jiya da ya ga Hadiza abin na tada hankalin Amiru. A cikin gida kuma suma su Inna Tambai abinda suke ta kiyastawa rayuwankansu kenan, da wacce riga Yusuf ke wannan irin wannan hidima ?Yayin da bai iya minti ashirin a waje sai ya shigo cikin gida ya leka dakin da Hadiza ta ke ya gaishe su. A tun daren jiya da akai rasuwar Gwaggo Halima ta ke zuwa amsar gaisuwa haka nan da zarar ta gama abinci ta kan shiryo ta taho.Duk da dai yanzu zumuntar ta su ta yi sanyi tun batawar Yusuf da Dije sai su kashe shekara ma ba su nemi juna ba hatta lokacin bikin su Hassi da Sarai ko da Halima ta kai ma Tambai goro bata je ba sai dai ta kai mata abin hasafi. A yarda aka shirya ran lahadi da la'asar su Yusuf da Falanke za su koma Abuja yayin da Amiru zai zauna anan gidan Yusuf har sai an yi sadakar bakwai to amma zumudin Yusuf da irin yadda ya ke nuna maitarsa a fili sai duk Amiru ya rinka zarginsa. yi A daren asabat din bayan Amiru ya kira Hadiza don su sallama, sun gama sallamarsu a natse har sun shiga mota sai Yusuf ya tsayar da su ya ce "don Allah su jira shi yana zuwa minti biyar"ya koma cikin gidan su Hadiza ya leka har dakin da suke zaune ita da Inna Tambai da Yaya Amina da bakin mata guda biyu da suka shiga a lokacin gaisuwa, ya ce, "don Allah Hadiza zo nan minti biyar". Ta mike ta fito ba tare da sa ma ranta komi ba. Suna tsaye a filin daga shi sai zaure, ya kara kallonta sannan ya sunkuyad da kai, ga dai Hadiza da ya kwana ya wuni tunani a gabansa,duk wata kalma da ya ke tunanin fadi mata ya san ba za ta yi tasiri ba, domin wannan ba Dijen da ba ce, in ma da hali zai iya cewa wannan babu wani wayon da zai iya nuna mata a halin yanzu. Ya cije ya daure ya ce, "wallahi ban san wai Baba ne ke kwance a asibiti ba, me zai hana ni zuwa gaishe shi?" Ta daga ido ta dube shi kawai, sai Yusuf ya ji gabansa ya fadi domin 2 idanun Hadiza sun canza mai, ba kowacce mace ke da irin wannan idanun ba, a karo na biyu yá sake wata rashin kunyar ya се, "Amma ke ma Hadiza ba ki san ni ne Yusuf din da ki kai ma waya ba?" To anan sai Hadiza ta sha mur ta ce, `wai me wannan mutumin ke nufi, yana tsammanin ta na da lokacin shi ne har yanzu duk da dai bata san shi din ba ne amma bari ta gwasale shi taga sai me?' Sai tace, "ina ruwa na da sanin kai ko wanene, ni kam na yi maka waya ne a bisa bin umarnin mijina Amiru!" Nan da nan wani gululu ya iso wuyan Yusuf amma sai ya tokare shi ya tuna wannan ba irin`yan matan da su ke zagi ba ne, ya gyara kurensa ya ce, "To Hadiza ni kam gobe zan koma Abuja Ubangiji Allah ya gafartawa Baba halayyarsa na kirki Allah yasa sun bi shi, Allah ya kara hakuri". Anan sai ta dan saki ranta tace, "Mungode, mungode Allah ya saka da alhairi a bisa dukkan abinda akai mana." Kafin ya ce wani abu ta juya zuwa cikin gida. To wannan shi ya kara sukurkutar da Amiru da suka isa gida sun jima ana hira da su Falanke amma sai Yusuf ya nufi can gidansu wajen Gwoggo Halima yana ta raragefen hirar Hadiza amma dai kunya da jin nauyi sun hana ya tambayi Halima ainihin labarin Hadiza abinda ya ke son ji. Ita kanta Gwoggo Halima ta zargi Yusuf na Cıkin yanayin damuwa amma sai ta dogara damuwarsa akan rasuwar Alhaji Kado domin'sanin shakuwar da ke tsakaninsu. Abu daya mutuwar Alhaji Kado ta kawo mata, wato ta janyo mata Yusuf domin ta fuskanci hankalinsa ya dawo gida tamkar da, saboda yaushe rabon da ya zo ya zauna su yi hira irin ta wannan zuwan? Har ta manta, a koyaushe ya zo yana can sabon gidansa duk lokacin da zai zo gare ta cikin sauri don kawai kada ta yi mai fadan aure. Gwoggo Halima ta dago kai ta dubi Yusuf yayi wani zama rashasha kamar wanda aka zare ma lakka duk yadda Allah ya halicce shi ya saki sharaf. Ta ce, "idan ка кoma Abujan kuma sai vaushe?" Yusuf ya sa hannu ya shafi hancinsa ya ce, "Ina tsammanin ha zan dade ba zan dawo, kiia ma nan da sati biyu." Gwoggo Halima ta ce. "ai gara ku je ku kwanta dare ya yi ga tafiya a gabanku gobe." 3 Ya mike yana rangaji ya nufi motarsa ya ja va nufi gidansa ,anan ya cimma su Amiru da su Falanke ana ta hira ya jima cikinsu amma bai iya cewa komai babu abinda ke azazzalal zuciyarsa sai yadda zai amshe Hadiza hannun Amiru tabtas mutuwar Baba Kado tamkar shi kadai akai mawa, domin idan da ya na da rai a yau yaje ya same shi ya ce, atabau shi Dijen shi ya ke so, to lallai ya yi imani Baba Kado zai rushe maganar Amiru ya ba shi. Wannan tunanin ya kara tsinkar masa da jijiyoyi, dole ne ya nemi hanyar da zai san inda Hadiza ta ke zaune a Kaduna haka nan ya nemi lambar wayarta, idan ya sami wannan zai yı abubuwansa cikin sirri kenan. Wanshekare ran lahadi kenan bayan sun je anyi addu'a da su, Yusuf ya riga Amiru dawowa ya bar shi a can saboda haka yana isowa bai tsaya ko ina ba sai dakin da ya sauke Amiru ya fara kwance masa jaka zuwa akwatinsa neman cikakken bayanin Hadiza, me zai faru? Amiru ya dawo don ya dan kwanta ya huta, amma sai ya cimma Yusuf a dakin da ya zan nan ne masaukinsa duk ya yi kaca-kaca da hotunan Hadiza sannan yana ta bincike masa takardu. Amiru ya tsaya bakin kofa yana kallon ikon Allah yayin da Yusuf ya yi kasake na rashin gaskiya na lokaci mai tsawo sannan ya ce, "Amma ka ba ni kunya, me za ka nema wanda ba za ka iya tambayata ba?" "Tabbas na san bai shige al`amarin Hadiza ka ke nema, kana zaton zan rubuta wayar mata ta a takardu ko adireshinta: Ni ko wane irin dakiki ne da ba zan iya hardacewa a kai na ba? Idan su ka ke nema, ka bani biro na rubuta maka, kana tsammanin Hadiza wawa ce kamar kai da har za ta iya saurarenka? Ka tuna fa kai ne ka ce baka aurenta don rashin fasalinta har dakin innarta ka je ka fada? Amma ka ba ni kunya, kai ba amini ba ne, maci amana." Yusuf ya daga mai hannu ya ce, "Dakata don Allah Mallam, maganar fa ta isa, sai ka gaya min waye ba ya kuskure? Na yi kuskure kuma na gane kure na duk abinda za ka yi zan koma neman Dije kuma insha Allah ni ne mijin Dije ba dai kai ba, komi kake takama wallahi akan Dije na shirya." Amiru ya ja tsaki ya ce, "Wawan banza, kada ka rinka 4 mantawa yau saura kwana ashirin da biyu Hadiza ta je dakina duk wani abu na sharuddan aure na kammala tun mahaifinta na da rai, abu biyu suka rage a sharuddan aurenmu da Hadiza su ne sadaki, da shaidu su shafa Fatiha." Yusuf ya yi dariyar keta ya ce, "ka san Allah Amiru abu daya zan iya raga maka shi ne idan an daura aurenka da Dije, wanda Insha Allah hakan ba za ta yiwu ba": Amiru ya ce, "Idan har ka cika shaidani ko an daura mana auren ka amshe Hadiza in ka isa". Yusuf ya ce, "Ban iya wannan shaidancin ba sai kai, mai raba miji da mata wanda kai in ban da bin matan aure babu abinda ka aje". Anan ne fa Amiru ya yi turus bakinsa ya bushe ya rinka kokarin tattara sauran yawun da zai iya samu, sannan ya sa halshe ya lashe busassun labbansa. La'asa sakaliya Yusuf da Falanke da dayan abokinsu da direban Yusuf sun isa Kaduna har sun yanki hanyar Abuja. Yusuf dai rungume da casbi yana wuridi bai iya cewa komi, sai su Falanke ke surutunsu. A gidan Yusuf na Abuja na`urar sanyi ta sanyaya ko ina a gidan, a falo Suzi ce zaune rungume da kan waya suna hira da kawarta shigar Yusuf ta aje wayan da sauri ta mike ta tarbe shi tare da sumbatar kumatunsa ta ce, `You are welcome darling' ya dan kauce mata ya amsa gaisuwar ta dakale ya ce, "Yawwa" Duk hanyar da ta san tana jan hankalin Yusuf Suzi ta bi, amma dai wannan karon bata shawo kan shi ba, data matsa mai da tambaya sai ya harareta ya ce ta manta ne ya ce mutuwa aka yi masa? Ta ce ta yi zaton sirikin Amiru ne; ya ce, `E kwarai kuwa, ya gano shi kuma Babansa ne'; sai da ya ci abinci ya yi wanka can da daddare duk `yan hira sun watse ya nufi (bas kwata) in da su Falanke ke kwana ya iske Falanke zaune a daki yana sa maballin wasu riguna da ya ke zaton gobe masu shi zasu amsa. Yusuf ya yi sallama ya shiga Falanke ya ce, "Ranka shi dade lafiya, baka aiko mai aiki ayi kirana?" Yusuf ya yi murmushi ya ce, "Babu komi Falanke kammala aikin gabanka ka zo mu fita waje magana na ke so da kai". Falanke ya ce, "Ai saura maballi daya ya rage na kusa kammalawa". Suka zauna a can wani bangare na cikin gidan Yusuf Falanke ya yi kasake yana sauraron abinda Yusuf zai ce masa domin shi ma ya damu saboda kwana biyu ya san Yusuf na cikin 5 wata matsala, addu'ar Falanke duk bata wuce Allah yasa dai ba daga wajen aikinsa ba ne, domin Falanke yadda ya ke jin dadin sana'arsa a birnin Abuja zai yi bakin cikin ace ubangidansa ya sami matsala da zai bar aiki. Yusuf ya ce, "Falanke a iya saninka ba ni da matsala da mahaifiyata baya ga kullum kukanta akan na yi aure". Falanke ya ce, "kwarai wannan nì zan ba wani labari domin ai ni take aikowa wajenka akan zancen auren naka". Yusuf ya ce "To madallah wallahi Falanke tun rabuwata da Fa'iza duk son wata diya mace ya fita kai na, ba na ganin darajar kowace irin`ya mace a duniya in ba mahaifiyata ba da kannena, a dalilin tozartawas da na samu daga neman auren Fa`iza duk da dai na san bata yaudare ni ba, amma ni na san da ina da kudi ba za ayi min yadda a kai min ba a lokacin, sai dai abin mamaki a hankali na rinka fahintar cewa babu wani don da na ke ma Fa`iza illa sha`awa da kwadayi na tashen balagar kuriciya a wancan zamani domin Fa`iza ta cika ta batsa yayin da Dije wadda zan aura bera ce babu komi na cikar mace a tare da ita, ni kuma wata wautar kuriciya ta hana ni na gane hakan, buri na kawai a lokacin na yi auren sha`awa don na kawad da sha`awata in kuma kwantar da kwadayina. To ban fahinci so ba ban gane ma` anonin so ba sai idan na tuno da kalaman da na kan gaya ma Dije da irin kalaman da take gaya mani, to na kan yi sauri na kawad da wa` annan maganganun na dauka shirme ne, amma yanzu gani na da Dije sai na san matsayin so na amince ina son Dije so na hakika, son da babu algus domin na nemi mata har ban san iyakarsu ba, amma wallahi ban taba jin wadda na ke so ba, har na yi sha`awar aurenta a zuciyata. Sai dai matsalar yanzu itace Falanke wannan Dijen da na ke maka magana ita ce Hadizan da Amiru babban aminina zai aura, diyar Baba Kado." Falanke ya sa hannu ya toshe bakinsa ya yi shiru yana mai girgiza kansa sannan zuciyarsa cike da al`ajabi, shi kan shi yana mamakin Dijen da ya sani wadda ke tallar goro itace wannan ta zama sai ka wanke hannu ka taba ta. Ya dubi Yusuf ya ce, "Yanzu Dijenka ce ta koma haka Yallabai?" Yusuf ya yi murmushi ya ce, "Wallahi ita ce, Falanke". 6 Falanke ya gyara zama ya ce, "To ai Yallabai sai an gwada akan san na kwarai, kuma ma ai mata tafi amini, ba wai zan hada ka da Amiru ba ne, amma gaskiya duk hanyar da za mu bi ya dace mu bi ta ka amso matarka". Yusuf ya yi ajiyar zuciya ransa yayi kal tunda ya sami goyon baya akan aurensa da Dije. Ya ce, "E Falanke to yanzu yaya ka ga zan bi na shawo kan Dije, ka san dai ba karamin tashin hankali ba ne, raba ta da Amiru da kuma kuskuren da na yi mata tun farkon rabuwarmu, maganar dai na rude ta da kudi wannan shirme ne, domin me za` a nuna mata yanzu, ko shi Amiru ya yi kadan ta aure shi don kudinsa ballantana ni, wanda na ke takama shi ne Baba Kado ya rasu". Falanke ya ce, "Wannan duk haka ne, abinda za`a yi shi ne ka shirya takarda ka rubuta ban hakuri duk wanda ka ke iyawa, ni kuma zan je ran jumma` a na kai mata tunda shi Amiru ran alhamis zai bar Bakori idan na dawo ran asabat muna iya komawa ran lahadi, ko ya ka gani?" Yusuf ya ce, "A`a ran alhamis za ka tafi, jumma` a zai ka zo na ji yadda ku ka yi, domin na san ran alhamis da wuri zai bar Bakori saboda haka na san ba za ku hadu ba." Aka bar ta a haka ya koma falo ya cimma Suzi na nan na jiransa, ya rungumeta suka nufi dakin baccinsa, sannan ne Suzi ta yi ajiyar zuciya. Yusuf ya fara aiki da kwarjini de daukaka sannan da iya aikin, har ya kai kaf a kamfanin kamar shi ne Babba saboda kwarjininsa da tsare aikin kuma babu hainci a bisa aikinsa а dalilin hakan shuwagabanninsa ba su jin kyashin sakar masa dukiya don suna ganin ya cancanci hakan saboda kwazon da ya ke nunawa kanfanin. Yusuf kafin ya ankara ya zama daya daga cikin sabbin matasa masu tashen kudi a birnin tarayya Abuja, to` yan mata kuma da suka kyalla suka hango motar zamani ga saurayi matashi mai cikan halitta a ciki, sannan namiji daya da daya a 7 cikin maza, mai tsarin kyau na usili, ga cikar lafiya, tamkar don shi kadai a ka shirya rayiwa a kullum cikin shi shar kamar jariri sabon haihuwa, abinda ma ya fi birge mata akan Yusuf shine kwarjininsa ai fa shi kenan ko bai je ba a zo masa, wannan ya kara dasa tsanar mata a zuiciyan Yusuf va rinka ganin kamar duk mata halinsu daya, ya zame masa canza mace kamar yadda zai canza takalmin kafarsa. A kullun aiken Gwaggo Halima ya zo ya yi aure amma shi yana ganin auren ba dole ba ne tunda ga matan nan yana biyan bukatarsa da su, da wuya Yusuf ya yi nema da hausawa sai dai wasu kabilu daban. Yusuf kenan. Amiru fa? Jirgi daya ya debo su da Yusuf a kullum fadan da iyayensa ke yi kenan akan lokaci ya yi da zai aje mace, domin duk kannansa sun yi aure sun hayayyafa amma shi ya ki. To mararrabar Yusuf da Amiru daya ce: Yusuf `yan mata ya ke nema yayin da Amiru shi kam sai matan aure, ko mi mutuncin auren mace muddin Amiru ya kyalla ido akan ki yana so sai va yi yadda ya nemi ki, da zarar kun yi nisa da nema zai ma ki alkawarin aure to da kin kashe aurenki shikenan kin zame wà Amiru jidali zai fara gudunki sai kuma a shiga rayuwar wani gidan (Allah ya shirye mu, amin) Wa'annan samari biyu`yan fitina su ke son diyan Baba Kado da aure, (kamilallah Hadiza). KASHI NA GOMA SHA UKU Ranar alhamis da sassafe a ka taru a kofar gidan marigayi Alhaji Kado akayi masa addu`a, a cikin gida ma haka, sannan ga abinci nan kala-kala an dafa a ka rinka bayas wa sadaka. Misalin karfe goma na safe Amiru ya shiga har dakin da su Hadiza su ke, ya same ta ita da Inna Tambai da su Ankudi ya ce, "To Hadiza Allah shi kara mana hakuri Allah ya jikan Baba" Aka amsa gaba daya "Amin Amiru Allah ya saka maka da alheri kuma Allah ya ba ku`ya`yan da zasu jikanku haka." Amiru kan shi a sunkuye hannunsa na bisa yatsansa na 8 kafa ya ce. 'Amin, to zan koma Kano a yau ina fata babu komi?" Hadiza ta dago kai ta ce, "Ina son ka aje mu gidan Inna Tambai zan kwana biyu can kafin na shige Kaduna, saboda a gaskiya bana iya ci gaba da zama anan dakin Baba, sai in ta ganin kamar zan gan,shi". Su Ankudi a ka yi narai - narai da ido suka ce, "Haba Dije bayan kin gina mana gida muna ta jin dadi kina debe mana kewa kamar Alhaji na nan, kuma za ki bar mu?" Hadiza ta ce "A'a Gwoggo kada ku damu zan rinka zuwa". Inna Tambai ta ce, "Kun ji shirmen naku ko, me Hadizan zata zauna ta yi maku, wadda zata gidan mijin ta kwanan nan?" Amiru ya kara jin sa` ida cikin ransa ya dan muskuta ya gyara zama, amma kuma sai Inna ta ce,Af, Amiru daman akwai sakon da zan gaya ma, a dalilin wannan rasuwa da ta gitta, a jiya ni da Mallan Hiya da Hadiza mun sake shawara akan ranar bikinku an daga mun mayas ranar da za'a yi arba'in din marigayi Alhaji saboda, ka san bikin ba zai yi armashi ba daga rasuwa a kama shagalin biki." Amiru ya ji zuciyarsa ta buga dam, babu halin ya nuna wata alamar cewa ya damu, domin nuna damuwarsa tamkar nuna bai damu da bacin ran Hadiza ba kenan na game da rasuwar mahaifinta ya ce, "Allah dai ya jikan Baba", aka ce "Amin" Ya kwashi Hadiza da Inna Tambai da kayansu ya kai su gidan Inna Tambai, ta yo mai rakiya har cikin mota tana kara yi mai godiya a bisa dawainiyar da ya yi masu tun daga asibiti har zuwa yau, ya ce, "Babu komi yanzu ran lahadi za ki koma Kaduna?" Ta ce` Insha Allah' ya ce "Zan yo waya da yamma kenan." Ta koma dakinlinna Tambai nan da nan ta dora ruwa bisa wuta don ta yi wanka, domin kwana bakwai din nan jin jikinta ta ke yana yi mata danko, ta lalubo wani akwatinta cikin wa'anda ta dawo da shi daga Hajji anan kalkashin gadon Inna tambai ta duba man shafawarta wato zaitun domin shi ne man Hadiza, rudanin ciwon Baba Kado bata tsaya ta dauko ba sai dai ta dauko sabulun wankanta wato sabulun salo amma dan Ghana wanda tàke cakudewa da zuma yar usili da jar kanwa da kwai, idan ta yl wanka da wannan sabulun sai ta mulke jikinta har gashin kan ta da man zaitun wannan shi ne sirrin Hadiza na ko yaushe fatar 9 jikinta na salki da sulbi, haka nan idan mata sun kai dubu launin fatar Hadiza ta fita daban tamkar danyar roba ga sheki da salki. Da la'asar şakaliya suna zaune ita da Inna Tambai suna maimaita ciwon Baba Kado wani yaro ya shigo ya ce, "wai a zaure ana sallama da Hadiza!" Kamar ta ce `Ace ya shigo' ta san`yan gaisuwa amma sai ta dauki mayafinta ta nufi zaure. Ta sami Falanke tsugunne a zaure ta ce, "A'a Shu'aibu telan zamani? "Barka da fitowa ranki shi dade ya karin hakurin mu?" Ta ce "mun gode Allah". Anan fa Falanke ya shiga yabon Baba Kado ya na nuna wannan rasuwa ta jama'ar Bakori ce gaba daya inda yake shiga ba ta nan yake bulla ba, a bisa kyakkyawar lafazin sai Hadiza ta ji wani sanyi a ranta ta rinka raya ma ranta cewa mahaifinta na can Aljanna Fiddausi domin yabon jama'a shi ne rahamar mamaci, ya ci gaba da cewa "yanzu duk dattawan garin nan akwai mai halin dattako irin na Baba Kado? Ki duba fa saboda dattakonsa yaron nan Yusuf ba shi da komai amma Baba ya ce ya ba shi ke sai dai kuma wani shaidan da ya gilma Allah bai ida nufi ba lokacin, amma mu masoyan Baba Kado muna nan muna rokon

Chapter 1 of 9