rungume sunnar Manzo bil hakki da gaskıya yana
tare da dukkan nasara duniya zuwa lahira. Ina so na gargade ka
anen Yusuf wato a yadda al amuran aurenku suka kasance kai
da Dije vanzu dole ne kai ka zama mata: ita zata zama mijin,
54
abun nufi anan a dalilinka ta shiga hali iri-iri wanda ya ja batawarta da mahaifiyarta bayan tsegunguman jama'a, to kaga anan yanzu
tana cikin radadin kunar zuci, dole ta tsinci kanta cikin tsanar ka
wanda zai jawo ta kasa kyautata maka, amma idan duk akai hakuri za ka amshi mulkinka a hankali."
Maganar Mallan Iliya ta shigi Yusuf sosai ya kuma
amincema ransa zai bi shawarar Mallan din. Bayan sun baro gidan
Mallan lliya Falanke yace, "Ya dace anjima mu je ka gayas da
Inna Tambai Malunfashi dai mallan lliya ya gargade mu kada mu
je yanzu sai can gaba in kura ta lafa." Yusuf ya shafa kansa
yace, "Wallahi Falanke ban ki ba na koma da zama gidan Inna Tambai amma ni tsoron idon Hadiza nake don baka san yadda
muka yi da ita ba ne a karshe." Falanke yace, "Ka san Allah
lafiya lau domin jiya da naje mun sha hira nace ango na gaisuwa
ta ce, nima ina gaida shi dazun kuma da safe kafin ka tashi mun
je ni da Basiru, wallahi abun da ta fara ce min `yaya Sha`aibu
ya aiko ka ne?' Na ce "E cewa yayi in zo in ga tashin lafiyarki."
Yusuf ya yi murmushi yace, "Ku take nuna ma fara'a amma yanzu
da żata ganni sai tsana zan je dai amma ba yau ba ina tsoron
bacin ran Hadiza."
Sai da Yusuf ya sami kwana hudu a Bakori amma bai leka
Hadiza ba sai dai dan kwarako Falanke na nan bisa hanya kullun.
Inna Tambai na dai lura da Hadiza irin nasihohin da take mata
suna shigarta don haka da alama tana kaunar ganin mijin nata.
Shi kan shi Yusuf duk ya kagara a kawo masa Hadiza kila a
gidansa ba za ta rinka yi mai kallon nan da bai so ba wanda ya ke
firgita shi amma kuma yadda Falanke ke cewa ta canza yana
kwadayin ganin nata, don haka sai ya shirya shawara ya baiwa
kaninsa Basiru kudin cefane ya ce ya je ya sawo kayan ciki da
wake ya kai ma Hadiza yace, tayi mai farfesun kayan ciki da
alale. Hadiza ta amshi kayan girki tace ma Basiru 'ka je ka
tambayo shi kamar na mutun nawa za'a girka kuma da karfe
nawa ya ke so?'
Haba murna da dadi suka lullube Yusuf da ya ji aiken Hadiza
55
ya ce "Kа ce mata kamar na mutun hudu da karfe biyu da rabi
na rana za'a zo a karba." Abinda ya kara birge Yusuf shine a irin
kwanonin da Hadiza ta zubo abincin sannan kuma irin alalan da
ta taba yi masa tun zamanin suna samartaka a wani zaman
jinyarasa da ta yi.
Karfe takwas na dare Yusuf ya fesa wanka ya zuba wanda
da riga na shakwara da janfa na kirim din boyel ya mulke jikinsa
da wani turare mai dadin kanshi da ake kira (hold the heart of
your love). Ya fito yana tayas da mota Falanke ya iso da sauri
yace, "Yallabai ba zan yi rakiya ba?" Yusuf yace, "Bisimillah, za
ni ban gajiyar aikin abinci ne." Falanke yace, "Ai yau kam amarya
ta biya mu."
Inna Tambai na zaune tsakar gida tana shan iska ita ko
gimbiyar na cikin daki tana sauraron wa'azin Mallan, hasken
musulunci. Su Yusuf su kai sallama suka shiga, bayan sun jima
suna hira da Inna, sai Innar ta ce "Ku shiga daki mana ai Dijen na
ciki."
Suka shiga tana zaune ta mike kafafuwa, sanye da jallabiya
mai ruwan zuma, ta amsa sallamarsu kan ta na sunkuye, Falanke
ya gaisheta sannan ya dubi Yusuf ya ce "Ranka shi dade zan je
cikin mota na jira fitowarka." Yusuf yace, "Babu laifi ga makullan,
sai na fito."
Yusuf ya zauna bisa tabarma shi ma ya mike na shi kafafun
ya dubi Hadiza a sunkuye ya ce, "Amarya wa`azi ake saurare
ne?" Bata iya dago kai ba ta amsa`E' yace "Allah yasa wanda
zai anfanemu ne." Tace "Amin" Ya sake cewa "Ya gajiyar aiki?"
Tace, "Babu gajiya."
Sun yi shiru kowanne na sake-sake cikin ransa, har yanzu
dai Hadiza bata iya dubar Yusuf ba, shi din ma a kasa-kasa ya ke
kallonta duk maganar da zai furta mata yana zullumi don yana
tsoron kar ta birkice masa, don haka a dosáne yake, haka nan
itama Hadizan ta lura da cewa a firgicen ya ke, amma babu
abinda zata iya ce masa, illa dai kawai ta yi alkawari ba za ta
sake yi mai tsiya ba a dalilin maganganun da su ka yi da Mallan
56
Iliyasu ta tabbatas wa ranta duk duniya babu mai son mahaifinta
Baba Kado sai ita da Yusuf haka nan ta na alfaharin har ya mutu
yana kaunar Yusuf, don haka ya dace ta auri Yusuf a ko wane
mataki na fannin farantawa mahaifinta rai, kamar yadda Inna
Tambai kejaddada mata cewa 'Dije kin gamawa marigayi komi
tunda ki ka auri Yusuf a dalilin son da ke tsakanin mahaifinki da
shi Yusuf.'
Hadiza na son Amiru tana kaunar halayansa, taso kuma
kwarai ya zama mijin aurenta amma kuma soyayyarta da Yusuf
wata irin kaunace wadda ke cikin jininsu illa kawai bacin rai ya
haddasa tsana da kiyayya mai tsanani a tsakaninsu, wadda kuma
yanzu gatancin da Yusuf ya nuna wa marigayi Alhaji Kado
yasa Dije na jin nauyi da tausayin Yusuf, don haka ta yi alkawarin
shanye duk wani batanci da yayi mata, ko a da bai son ta tunda
yana son mahaifinta ya gama mata komi.
a
Yusuf ya katse zaman shiru yace, "Bari na tashi na tafi
kila na takura ki, kin sadda kai kin kasa sakewa." Sai Hadiza ta
daure ta dago kai a hankali ta dan dube shi kadan tace, "Na ce
ba, ko zai yiwu gobe ka ba Basiru mota ya kai ni Kaduna akwai
wasu kaya da nake son daukowa, kuma akwai zancen bayas da
katunan da ka aiko min."
Yusuf har ya so ya karyata kunnuwansa, shin da gaske ne
Hadiza ke mai wannan lafazin a hankali mai ratsa jiki, ko dai zolayarsa take? Yusuf cikin murmushi na rudani yace "Me zai
hana ya yiwu sai dai zan fi so ni na kai ki domin akwai bukatar
zuwanmu Kaduna ni da ke a dalilin taransufa na aikinki komawa
Abuja, haka nan akwai wani dinki da nake so mu je wajen telolinki
na Kaduna za mu kai na wani boyel les wanda za mu sa a daren
dina." Ta dube shi tace "Me zai sa ba za ka ba Shuaibu ba?" Yace
"Ai na bashi aikin hannu na wani farin boyel na ga ma har yanzu
bai gama mana ba." Hadiza tace, "Amma ina ganin zai fi kyau
mu tafi da zinaran nan Kaduna mu aje a banki ko?"
Yusuf ya kara matsawa kusa da Hadiza ya tabbatas Hadiza
ra'ayinsu daya sha'awarsu daya tunaninsu daya yace, "Wallahi
57
abinda nace ma Gwoggo kenan a ranar da za'a kawo kayan
amma ta hau ni da fada kin dai san halin Gwoggo komi tace an yi
rashin kunya."
Hadiza ta mike ta dauko kit suna kara dubawa, yana gaya
mata wanda ya saya a London tun wani zuwansu da Shugaba,
da wanda ya taba sawowa a umarar shekara biyu da ta wuce da
wa'anda ya saya farkon zuwansa aikin hajji, da wa'anda ya saya
a Indiya. Hadiza tace, lo Gwoggo kake ba ajiya?" Yace, "Wallahi
banki na ke aje abuna kin san mutanenmu ba su faye sanin daraiar
wa annan abubuwan ba".
Tun Inna Tambai na jin maganar Hadiza da Yusuf samasama har bacci ya kwasheta, yayin da Yusuf sai da yasa Dije ta
gwada duk sarkokin nan da zabba da abun hannu an yi sa'a abun
hannun mai sukuro ne, ana iya ragewa ko kara girmansu, a Madina
wata balarabiya 'yar kasai Jordan ta sa Yusuf ya saye su domin
yace bai san size din matar da zai aura ba.
Bai bar dakin Inna Tambai ba sai misalin karfe goma sha
biyu na dare. Falanke ya dade da bacci a mota ba don tausayin
Inna Tambai na kwance a waje ba kila Yusuf da sai an kira asuba
zai bar gidan, duk ilahirin kayan lehen nan kuwa babu wanda
basu yi daidai da shi ba. Shi da Hadiza suna dubawa, yana fada
mata yadda ya sayi kowanne. Ta dube shi tace, "Akwai irin
wannan turaren da ka shafa cikin kayan nan?" Ya dan lunshe ido
ya ce, "Kina son shi ne?" Tai mai murmushin da ya shekara bakwai
bai gani ba, ta ce, "Irin turaren da na fi so kenan domin bai
yamutsa hankali." Suka dubi juna suka yi dariya, yace, "Ba irin
sa anan amma na yi alkawarin aje maki nawa". Ta ce, "Lah ka
bar shi ka rinka shafa abinka". Ya ce "A'a idan kin zo mun rinka
shafawa tare."
Wanshekare karfe goma da rabi na safe ya iso shi da
Falanke don daukar Hadiza tafiya Kaduna. Ta fito ta cimma masa
yana tsaye gindin motarsa rike da wata 'yar karamar rediyo mai
kama tashoshin kasashen waje. Kwalliyarta irin ta kamamnun
musulmai ta kayatar da Yusut ainin ya kuma yi alfahari da ita
58
har zuci, ta dafa gefen mota ta dan rusuna ta gayas da shi.
Ya bude mata kofar gaba ta dube shi tace, "Ba da Sha aibu
za'a ba?" Yace, "Da shi za mu mana." Tace, "To ai shi ya fi dacewa
ya zauna a gaba ni na zauna a gidan baya." Suka dubi juna su kai
dariya shi da Falanke."
Ta koma gidan baya ta zauna Yusuf ya shiga, amma kafin
ya tayas da motar sai da ya dauki lokaci yana yin saitin madubin
gaba a daidai fuskar Hadiza, ta dago ta duba suka yi ido hudu ita
da Yusuf ta madubi, nan da nan su kai ma juna murmushi, Yusuf
ya saukar da wata sansanyar ajiyar zuciya.
Sun kwana sun yini ana zirga-zirga a Kaduna kafin su gama
abubuwan da suka kai su, don haka sai cikin dare suka isa Bakori.
KASHI NA GOMA SHA BIYAR
Da karfe biyu na rana Baba lliyasu ya daura auren Yusuf
da Hadiza, an gabatar da addu'a ta musamman ga marigayi Alhaji
Kado daurin aure da 'yar kwarya-kwaryar walima ta kayatar,
duk dawainiyan abinci na gidansu da na gidan Inna Tambai Yusuf
ya yi komi domin ya san dai karshe Hadizan ce za ta yi.
Baba Rilwan, Baba Garba da Baba Malan Isa zuwa kannen
Hadiza su Saminu sun halarci daurin auren, haka nan matar Baba
Garba da Mama Binta da Hadizan Jos su kadai za mu iya cewa
sun halarci bikin a bangaren dangin yaya Amina mata.
A ranar da biki zai tashi tun da safe Yusuf ya sa Falanke
ya sawo mai zabbi guda biyu yace ya a adana su can a gidansa
wato Falanken.
A can ma Kano an daura auren Amiru da Salma a daidai
lokacin da ake daura na su Yusuf. Karfe goma sha daya na dare
Yusuf ya dubi Falanke kowannensu a gajiye likis, yace "Falanke
na gode, Allah va bar mu tare, amma kafin ka tafi gida ka kwanta,
nima ba zan shiga wajen amarya ba sai ka yi min wani aiki daya."
Falanke da kyar yake daga ido don tsabar gajiya yace,
59
"Me ya kuma rage Yallabai?" Yusuf yace, "Ina son ka je ka dauki
zabuwa daya ka kai ma Talle mai tsire ya gashe min ita yanzu ka
kawo min, ita kuma daya zabuwar ka mikawa Gwoggo kace ta
soyo ta gobe da safe ta aiko min."
Falanke yace "Tirkasahi! Wannan aikin amarya ne ko? To
amma ka san kila su Gwoggo yanzu gajiyar biki tasa sun kwanta
ba ka bari da safe na kai mata?"
Yusuf yace, "To yi sauri ka cimma Talle mai tsire ya gaso
dayar."
Falanke ya dawo karfe daya saura 'yan mintoci na dare
yana magana a gajiye yace, "Yallabai ga zabuwa an yi sa'a yarinya
ce zabuwar mai maiko, a sha amarci lafiya. Ubangiji ya bada
raboa daren yau, amma fa a sa mai suna Shu'aibu." Yusuf ya yi
dariya yace, "Kai ka yarda a fara sa sunanka, bayan ga sunan
Baba Kado." Falanke yace, "Tuba na ke Yallabai kai na bisa wuya,
Allah ya kawo mana takwaran Baba Abdulkadir, mu kwana
lafiya."
Yusuf ya shigar da mota garejin gidansa, sannan ya yi
wata addu'a wadda Mallan Tukur ya ba shi. Ya shiga falonsa
kamar ya doshi dakin Hadiza amma ya kanne ya nufi na shi dakin,
ya sunce kaya ya fada kewaya ya yi wanka tare da alwala sannan
ya fito ya dauko maganinsa na ciwon jiki ya kora ya saka kayan
baci ya dauki turaren da Hadiza tace, tana so ya nufi dakinta.
Abin mamaki karfe biyu ta yi amma sai ya rinka jin karatun
Alqurani na fitowa daga rediyon dakin Hadiza yace a ransa kada
dai ace Hadiza ba ai bacci ba?
Ya murda kofar a hankali ya shiga, ta yi dai dai bisa gado
a bisa dukkan alamu bacci mai nauyi ya dauke ta, ya nufi inda
rediyonta yake ya kashe ta yi firgigi ta tashi nan sai ta tsuke mai
fuska tace, "Don me zaka kashe min? Ni na riga na saba, kwana
na ke da karatun Ahmad Sulaiman domin rediyon mai juya kanta
ce." Yusuf ya dan firgita da yanayin fuskar ta yace, "Na yi zaton
ba ki sani bane." Ya tsaya shi bai zauna ba haka nan shi bai
kunna rediyon ba, amma Hadiza ta kara tsuke fuska fiye da
60
shigowarsa, ya cije yace, "Hadiza akwai bukatar mu gabatar da
nafila tashi ki yo alwala?" Sai da ta bata lokaci sannan ta je ta
yo alwalar, bayan sun idas da nafilar ya dade yana masu addu'a
a fili tana amsawa da "Amin".
Sai ya juyo da sauri ya kamo hannuwanta ya rike zai kai bisa kirginsa ta fisge ta mike ta koma can gefen gado ta tsaya
yace, "Me kuma ya faru?" Ta juyo ta dan harare shi ta kawad da
kai ya dauki turaren da ya shigo da shi ya je zai fesa mata tace "ba na so" cikin tsiwa.
Baya son rigimar ta yi tsami sai ya fita da niyyar ya je falo
ya yi tunani ko zai iya tunano abinda zai shawo kanta, amma sai
ya ci karo da gasassar zabuwar sa ya dauka ya juya ya koma dakin Hadiza don ya cika alkawarin da ya daukar mata. Yanzu tana zaunè bakin gado ta yi tagumi, ya tsaya a
gabanta ya langabe kai ya ce, "Ki dubi girman Allah ki saurareni
na gabatar da nauyin alkawari daga bisani kina iya ci gaba da
musguna mani, zan iya jurewa har Allah yasa ki daina." Ta daga kai tace, `Wai menene?' Ya tsugunna a gabanta da `yar leda à
hannu yace, "Akwai wani zamani idan ba za ki manta ba na yi alkawarin cewa ran da duk na gan ki a dakina, a rannan zan
kawo maki zabuwa wadda zan yi maki lakabin sunan da nake so
wato KUBRA, to Allah Ya yarda yau ga ki a gidana kuma kin ci
ma'anar sunan wato BABBA da larabci shine Kubra, a yau kin
zama babba a gidana, a zuciya ta, a cikin gidanmu ma keсе babba tunda kece matar babban yaya.
Hadiza ta yi wata irin`yar siririyar dariya `yan kananan
hakoranta masu daukar hankali suka bayyana a idon ango Yusuf
tace, "Allah da gaske ka ke, idan da gaske ne bude ledar na gani
idan zabuwar ce!" Yusuf bai san yadda zai bayyana farincikinsa
ba a wannan lokacin, sai ya dube ta ya ce, "Ina zuwa ki jira ni."
Ya mike ya nufi kicin don ya kawo faranti ya dora zabuwar a kai,
amma sai ya tsaya cak yana alajabin yadda Hadiza ta cika masu
kicin da na'urori na girke girke, ya rinka mamakin a ina Hadiza ta
sawo wa` annan na` urori masu tsadar tsiya? Ya yi murmushi ya
61
ce lalle Hadiza na shirin sangartashi, ya dauko faranti ya koma
dakin Hadiza, ya zauna a gabanta dirshan ya fid do zabuwa ta yi
narai-narai da maiko, an kuma shafe ta da magi mai tauraro da
atarugu da albasa. Yusuf ya yago cinya ya ce, `Kubra'. Ta dago
kai a hankali ta yi mai wani irin kallo wanda ya zarce wanda ta
taba yi masa a wancan zamanin da suka yi irin wannan magana,
tsigar jikinsa ta tashi yar, ya lumshe ido sannan ya dan bude ya
ce "Kubra, Allah! Allah!! Yasa ki haifa min`yan mata shidda
masu irin idonki su rika kallona kamar yadda kike kallo na." Ta
tumshe ido.
Ya mika mata cinya ta kai bakinta tana ci, ya ce, "Amma
kin ba ni mamaki yanzu nan kin nuna min bacin ranki tamkar
nayi laihi yanzu kuma na ga kin huce." Ta ce, "Haba Yaya ai dole
ne na yi ma haka, a zatona ka manta da wannan alkawarin wanda
yana daya daga cikin abinda ya gina kaunata da kai haka nan
yana daya daga cikin abinda ya sa na tsane ka, domin ina
mamakin wanda zai fada wa diya mace wa`annan kalamai
sannan ya dawo ya ce bai son ta."
Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Har yanzu inan nan a yaya? Ni
ma ai an yi min alkawarin raba ni da suna Yaya ko?"
Ta dan rusunar da kwayan idanunta ta ce, "Idan na kira
ka da D ya isa?" Ya ji wani irin dadi ya rastsa shi ya ce, "Me ke
nan kike nufi?" Ta ce, "Ina nufin Darlin ko?" Ya sake tsinkewa
don dadi yace, "Me zai hana ki ce Darling din gaba daya?" Tace,
"Yanzu a gabansu Gwoggo da su Basiru da irin su Sha'aibu ba
zan ji nauyi ba? Amma ko idan na ce D kamar su Gwoggo ba za
su gane ko me nake nufi ba." Yace, "Na gamsu, na gode, ni ba za
ki samman zabuwar taki ba?" Sai ta dan zolaye shi tace "Ta
Kubra ce fa mara fasali". Haba nan da nan ta jagula masa lissafi,
amma sai ya dake ya maida shegantaka yace, "Haba ba dai Kubra
dina ba, kine zancen wata yarinya ce Dije" Sai ta dan yi murmushi
tace "Oho dai ai yan karin magana sunce kowa ya raina tsayiwar
wata ya hau ya gyara idan zai iya." Yace, "Haka ne, ko da can
rashin wayau ne ya hanani gyarawa, amma yanzu zan kara mikar
62
da komi ba ki ji abinda Inna Tambai tace ba ne? Cewa ta yi namiji
shi ke mikar da mace......."
Yusuf ya kammala shirnsa tsab Hadiza na tsaye rike da
agogansa, fuskarsa a murtuke tana nuna alamun bacin rai da
damuwa Hadiza ta ce, "D kawo hannunka na daura maka
agogonka, wai me kuma aka yi ma ne sai huci kake? Ya mika
mata hannu yayin da ya zuba ma fuskarta ido, yace "Na yi maki
tambaya, saboda Allah Kubra yau kwana nawa da bikinmu?" Ta
ce, "Yau kwana shidda wani abu?" Ya ce "Abunda ke bata min
rai shi ne wa'annan matan masu isar mu da zuwa wai ganin
daki, sun hana mu sakat mu kwanta mu huta wannan wacce irin
aladace! Da sassafe karfe takwas zasu tayas da mu har mu
kwanta bacci gidan nan ba a kara barin mu sakat haba ina dalili,
mutun ba za a bar shi ya huta ba?" Hadiza ta yi dariya tace "Ga
wasu mattan ma can falo suna zaman jiranka tun kana wanka
suka zo, ina zaton a bayaninsu daga kauyensu Gwoggo su ke."
Yusuf ya girgiza kai yace, "Bana iya zama har hutun wata daya
a garinnan ki shirya abinda kike so wa'anda za ki yi anfani da su gobe insha Allah za mu koma Abuja."
Da yamma Yusuf na gaba Hadiza na bayansa suka shiga gidan Gwoggo Halima, kai ka ce Gwogo Halima bata taba ganin
danta Yusuf ba da Hadiza sai a wannan rana, sun birgeta sun bata sha'awa haka nan sun tsuma mata zuciya domin sun yi
matukar dacewa da junansa ko wanne sai kwarjini da kuriciya
ke bayyana daga gare shi. Murna da jin dadi suka hana Gwoggo Halima kulle bakinta.
Bayan an kammala gaishe gaishe da ban gajiyar biki Yusuf
yace, "Gwoggo gobe da sassafe Falanke zai tafi Abuja da motar
kayanmu, yayin da ni da Kubra za mu tafi da azuhur." Gwoggo
Halima ta sha bula tace, "Ni fa ba na son sokonci ca na ke hutun
naku wata daya ne shi ne za ku gudu tun jama'a ba su gama
ganin daki ba." Yusuf yace "Ai kin ji matsalata wa'annan mutanen
da ke hana mu kwanciya mu huta, su za su kore mu."
Gwoggo Halima ta dubi Hadiza tace, "Ke Hajiya Hadiza
60
kin amince da hakan?" Hadiza ta yi dariya tace, "To Gwoggo
yadda yace yana so ai haka za'a yi ko?" Gwoggo Halima ta dan
harare su tace, "A to ke ke daure masa gindi Hadiza." Hadiza ta
kyalkyale da dariva ta ce, "Allah Gwoggo babu ruwana." Gwoggo
ta ce "idan haka ne, shi ya tafi ke ya bar ki anan jama'a su gama
ganin dakin amarya." Yusuf ya yi zanbur yace, "Haba Gwoggo
ai itace shugaban tafiyar". Gwoggo ta dalla mai harara ta ce
"To shugaban yan rashin kunya ban yi da kai ba."
Da suka gama hira sun tashi tafiya Gwoggo Halima tace
"Babu abinda za'ai maku wanda za ku tafi da shi?" Hadiza tace,
"A yi mana hura Gwoggo." Sai Gwoggo tace, "Insha Allah za'ayi
idan kun je wajen Tambaya ku ce ina gaishe ta ina sauraronta
jibin don mu je Malunfashin."
Yusuf da Hadiza sun sami yadda su ke mafarkin son rayuwar
ta kasance komi ya yi masu acan acan, yau kwanansu ashirin
da shidda da aure, Yusuf ya dauko katin bikin Amiru da Salma
yana dubawa ya ce, "Amma Kubra ban yi zaton da Amiru zai
sake wata hulda da ni ba balle har ya gayyace ni liyafar bikinsa."
Tana daga can kwance bisa doguwar kujera a falonsu na Abuja
ta dubi Yusuf tace, "Ni kam ban yi mamaki ba domin irin wannan
ta sha faruwa daga bisani kuma ai ta zumunta tamkar wani abu
bai taba faruwa ba. Don Allah idan ka je wajen bikin nan ka
nunawa yawancin abokan nan na,ku tsakaninka da Amiru babu
wata damuwa sai zumunci, domin na fuskanci akwai masu son
su ga batawarku."
Ya dube ta ya yi dariya ya ce'"Har kin amince min na je
kenan?" Ta lumshe ido tace, "Me zai hana ka zuwa D? Ai tunda
har ya aiko maka, ya dace ace ka yanke duk wasu al`amuranka
ka je." Yace, "Amma da ke za mu ko?" Ta ce, "Haba D kamar ba
mu da wayo! Kai kadai za ka idan ka je da ni, dole `yan tsegumi
su yi halin nasu babu ma kamar abokanku da `yan uwan Amiru."
A ranar da Yusuf za shi Kano wajen liyafar Amiru tare da
64
Hadiza suka taho ya aje ta gidansu na Bakori domin zata sallami
kannanta komawa makaranta. Tun mahaifinsu na da rai ta yi
kokarin ganin sun je babbar makaranta, wato Kuluwa da Larba
suna kwalejin 'yan mata da ke Katsina sai Juma da Munari sun
je makarantar 'yan mata da ke Kabomo.
Tunda Hadiza ta sauka Bakori sai ta tsinci kanta da
canzawar yanayin jikinta da farko abinda ta dauka rashin isasshen
bacci ne da bata samu ba a daren jiya, sannan kuma a yau sun yi
sammakon tafiya, to amma sai ta ji ciwon kai na neman kwantar
da ita haka nan bayan ta kwanta wai ko ta ji sauki sai kuma
zazzabi ya dirar mata, tana cikin wannan halin ne har kimanin
awa daya da rabi sai ga Hassi kanwar Yusuf ta je. Bayan sun
gaisa ta ce "Ai ina gida na ji an ce kina nan gida shi zai wuce
Kano." Hadiza ta daga kai a hankali ta dubi Hassi tace, "Kin gan
ni na iso Bakori da ciwon kai ya su Gwoggon? Da maigidanki?"
Hassi tace, "Kowa lafiya lau, Gwaggon ma tana cewa na gaisheki
tana can tana shirya maku abinci tace ko akwai ani abu da ki ke
sha'awa?" Hadiza tace, "Anya zan iya ma cin abincin nan? Sai dai a dafa saboda su Yaya da wanda ya shigo ni kam ruwan zafi
za ki dafa min ki zuba min a flas, na fi son shayi." Nan da nan Hassi ta nufi kicin ta jona butar ruwan zafi `yan mintoci ruwa
sun tafasa ta shiryo ma Hadiza kayan shayi ta kai mata. Bayan Hassi ta mike don ta koma gida ta yi ma Gwoggo bayani sai Hadiza tace, "Don Allah Hassi a sami wani yaro a tura shi can gidanmu a yi min kiran su Larba da Munari."
Har misalin karfe biyar na yamma Hadiza na dakin baccinsu
a kudundune ciwo na cinta, sai kannanta su Larba ke kai da komowa a cikin gidan. A lokacin ne Basiru ya kawo Gwoggo Halima don ta duba jikin Hadizan, to ganin yadda Hadian take ya dan tsorata Gwoggo tace, "Hajiya Hadiza ko za ki yi karfin hali ki je asibiti? Tunda ba'a san lokacin da su Maitaman za su dawo
ba?" Hadiza tace, "A'a Gwoggo a yi hakuri sai sun dawo domin ba za su kwana a Kano ba, in dai akwai fanadol mai kyau Basiru
ya samo mani." Gwoggo tace "To shi kenan Basiru je ka ka samo
65
mata fanadol din."
Basiru sai ya davvo da wani malamin asibiti abokinsa ya
zankadawa Hadiza allura biyu har da ta bacci, ya danna mata
wasu kwayoyi guda shid da ta hadiye. Bacci mai nauyi ya dauke
ta, sannan Gwoggo ta gargadi su Larba akan su rik.a duba Hadiza
kuma kada su tsananta hayaniya don kada su danme ta, ta koma
gidanta.
A Kano inda Amiru ya kama ya cika makil da bakin larabawa
zuri'arsu Salma. Kami kam ya kayatu acan acan, abin sai in ka
gani da idonka. Masu kidan Sudan ke cashewa a hankali cikin
nishadi suna fidda sunan Amiru da Salma a tsanake kai kace
akan su aka fara kirkirar vvannan wakar. Amiru da amarya Salma
zuwa manyan abokan su