Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 9
suna zaune a tebir na musamman. A lokacin ne Yusuf ya danno cike da kwarjininsa da haskensa na amarci da annurinsa na zama kamilallen mutun, wato na zama mai auren sunna. Ako ina Yusuf ya ke ya kan fita daban domin halin sa daban ne da na sauran jama'a yana shiga fili bai nemi wajen zama ba sai ya zarce kai tsaye wajen mawakan Sudan ya shiga manna masu 'yar wa-zo-bia har sai da daya daga cikin yaran maiwaka ya nemo sunan Yusuf, nan take lasifika ta dauka gaba daya da Y-U-S-U-F amanar K UBRY. Salma ta dan rusuna zuwa kunnen Amiru tace "Yaya wannan kuma fa?" Amiru ya kai bakinsa zuwa kunnenta yace, "Shine babban aminina wanda na bar wa Hadiza!" Suka yi murmushi Salma da Amiru sannan daya daga cikin kannan Amiru ya mike ya je inda Amiru ya kirasa, ya dan rusuna, Amiru yace, "Babangida ina son ka baiwa Yusuf kujerarka." Babangida yace "An gama Yaya." Babangida ya nufi inda Yusuf ya ke ya taho da shi zuwa tebir na musamman. Kafin Yusuf ya zauna sai da ya kai gaisuwa wajen ango da 99 amarya da sauran jama'ar dake tebir na musamman. An yi tandetande da ciye-ciye haka nan an cashe da makada na zamani yadda rayika ke so, na tsawon lokací mai yawa. A karshe Yusuf ya rinka tunanin tashi galleliyar amaryar Kubra na can zaman zuru zai fi kyau ya yi ma Amiru bankwana don ya koma wajen ta. Sun kebe gefe daya Amiru da Yusuf suna sallama, inda Yusuf ke zolayar, Amiru da cewa "Irin wannan jajayen mutane Amiru kamar muna a Saudiya?" Amiru ya dan doki kafadar Yusuf yana dariya yace, "Ka san mahaifiyar Salma halarabiya ce, to kuma Salma itace diya mace ta farko a gareta don haka ta yi anfani da wannan damar na gayyato zuri'arta. Amma fa ina gadiya Yusuf da ka nuna min karanci ka halacci bıkinmu." Yusuf yayi murmushi yace, "Ni ya dace na yi ma godiya da ka kai min katin gayya har gida ina fatan kuma abotarmu da zumuntarmu zata ci gaba kamar da, haka nan kaman kullun kofar gidana a bude take a gareka ina maraba da kai da iyalinka ni da kubra, har abada ba zan taba zarginka da Kubra ba." Amiru ya yi murmushi ya ce, "Na yi murna da jin haka daga wajenka in Allah ya yadda babu abinda zai shiga tsakaninmu sai zumuncin da muka kullo tun muna samari amma fa Yusuf kana daya daga cikin al'umman Annabi masu rabo a duniya wai na tambaye ka mana kai ko me ka ke ma Sarki Allah?" Yusuf ya dan yi shiru sailin da ya zuba idonsa a kasa, nuna alamun tunani zuwa can ya dubi Amiru ya ce, "Ka yi min tambayar da ban yi zato ba amma kuma sanin kana daya daga cikin aminina na hakika illa kawai wani rabon auren mu da ya gitta a lokaci daya kuma a wani rudadden yanayi sai dai kawai na san daga ni har kai muna da kyakkyawan tunani wanda za mu iya cewa aurena da kubra da neman ta da ka yi wani mukaddari ne daga Allah. Lalle Amiru ka yi min tambaya mai kyau domin sanin kan mu ne mun sabi Allah ta hanyar zinace-zinace wanda babu tantama laihi ne tsakanin mu da Sarki Allah, sai dai kuma a wancan zamanin da shaidan ya rudı zuciyarmu ban taba nemar 67 matar aure ba, saboda shiga hakkin wani, saboda ka ga laihi biyu kenan dole ka nemi gafarar mijinta haka nan ka nemi gafarar Allah wannan ken ina tabbatar maka tun zamanin da mahaifina ya rasu ban taba yarda mahaifiyata ba ta tonawa kan ta asiri inde duk zan shiga zan bi don inga na kare hakkinta da na kannena, haka nan babu abinda nake iya rutewa Gwoggo wanda na san tana alfahari da hakan, bana iva cin abinda na san ba zan iya mallakawa Gwoogo ba sannan na roki Ubangiji kada ya ba ni hatsabibiyar macan da zata zama sanadiyar raba ni da Gwoggo. A kullun na yi sallah da asubah bana tashi sai na gabatar da salatin Manzo cikin casbi hailalah cikin casbi sannan istingifari cikin casbi komi saurin da na ke yı haka nan idan na yi sallar isha'i yayin da na kammala da komi na yi shirin bacci, na kan yi kokari na ga cewa kalmata ta karshe ita se (Astangafirillah lazi taila ha illallah Huwal Hayyul kavyum wa atubi ilaihi) sau uku, haka nan na kan gabatar da wannan istingifarin a dukkan sallolina na farillah." "To kuma ka san halina Amiru ban iya cin naman mutun ba, kowaya taba ni nan take zan sanar da shi, ka dai san matsayin cin naman mutun wajen Allah, ina ganin dai duk namijin da ya tsare tsakaninsa da Ubangijinsa da mahaifiyarsa da kame bakinsa daga giba to lalle zai rinka samun saukin al amuransa. Zan kara maka haske daya Amiru a tun ranar da aka aiko min an ba ni Kubrə na yi nafila na yi godiya zuwa ga Sarki Allah na daga hannayena bayan ra gabatar da shugaban istingifari nace, Ya Arrahamin Rahim sau uku, Kai ka halicceni kai ne ka azurtani da mata saliha ka tsirar da ni daga zaluntar ta, kar ka karkatar da ni zuwa-ga aikata zina." "Sai kuma na sami ingantattar addu'a wajen Babana Malan Tukur na rinka sha da zuma na tsawon kwana uku, itama ta neman tsari daga zina." "Sai kuma na samí wata ingantattar addu a wajen Babana Malan Tukur na rinka sha da zuma na tsawon kwana uku, itama na neman tsari daga zina." 68 Amiru ya yi galala yasa hankici ya goge fuska yace, "Don Allah ya addu'ar take Yusuf?" Yusuf yace (Walata karabu zina innahu kanafahi shatan wasa'a sabila) kafa goma sha daya. Amiru yace, "Na yi murna da zuwanka wajen bikin nan fiye da kowa Yusuf.Ubangiji Allah ya gafarcemu gaba daya, Allah ya ba mu ikon rike matanmu da gaskiya da amana." Yusuf da Falanke suka mike hanyar Bakori ya sai banza ya sai wofi na ciye-ciye wanda zai kai ma Hadiza. Ba su iso kofar gidansa ba sai goma na dare. A falo ya cimma su Larba sun yi dai dai bacci na dibar su, haka nan kuma sun kunna kandir, ya ca "Ina Kubran?" Suka ce "Ai tana daki tana bacci." Ya ca, "Don mi ba ai ma maigadi magana ba ya tayas da injin da aka dauke wana sai ku zauna a haka?" Munari ta ce, "Ai antin ce bata fito be tunda aka dauke wutar ko sallah ma bata yi ba, saboda bata lafiya amma Basiru ya kawo mai yi mata allura shi ne Gwoggo ta ce kada mu tashe ta." Munari na kai karshen maganarta, Yusuf ba zai iya cewa ya tantace da komi ba ya watsar da abin da ke hannunsa ya waiwaya ya dubi Falanke, sai yasa kai zuwa dakin da Hadizan ke kwance, wani abun al ajabi ya cimmata ta yi laga-laga ta galabaita cikin amai a bisa kafet duk amaine Allah dai ya rufa asiri aman ya tsaya na ruwa, domin ruwa da shayi ne kawai a cikinta. Nan da nan kwalla ta kawo ma idon Yusuf a yanayin da ya riske Kubra, ya zauna a firgice cikę da zullumi ko zai rasa Kubra ne? Ya ciccibo kirjinta gaba daya va rungumeta bisa cinyoyinsa muryarsa ta kasa tsayawa daidai, ya daure cikin rudanin murya yace "Kubra me ke faruwa da ke?" Tayi layau da hannunta ya yin da ya cafe hannun ya dora kan kirjinsa sai ya ji hannuwan sanyi karara, cikin murya ta rashin lafiya tace "Wayyo Allah D kai na, tun bayan tafiyarka na fara ciwon kai sai zazzabi, to shine nace ma Basiru ya samo min fanadol mai kyau amma sai ya zo da abokinsa su kai mani allura. Da farko na ji dadin allurar domin na sami bacci amman tunda na farka ban yi zaton zan vi kwanan duniya ba." Yusuf ya kara shiga wanin rudanin har bai san kome kuma 69 zai yi ba yace "Kubra shirya mu je asibitin Funtua." Tace "D bana iya zama ka jure ka hakura har zuwa gobe mu koma Abuja a duba ni a can." Ya kwantar da ita yace "Ina zuwa". Ya cimma Falanke yace, "ya ba ku tayas da injin ba?" Falanke ya ce, "Mun duba ashe babu mai ne a ciki, ya jikin Hadiza?" Yusuf yace "To ni kam sai kuma abinda Allah ya yi domin idan ma da ciwon da jahilcin wannan bakauyen yaron Basiru, wai dubi sokonci daga ta nemi fanadol ya debo wani wawan abokinsa ya zuba mata allura, babu nazari balle bincike." Falanke ya bude baki yace "Me ya sami Basiru da inin wannan kankanbar?" Yusuf ya ce "Oho! Raini mana, don Allah ga kudi aje a sawo man injin. Falanke daga nan ka biya ka zo min da Basiru." Ko da falanke ya dawo sai da su ka yi kiciniyar tayas da injin haske ya sawwaka a gidan sannan Yusuf ya zarewa Basiru jan ido yace, "Basiru a bisa wacce hujja za ka debo wani wawan abokinka ayi ma Kubra allura?" Basiru ya shiga yarfar da hannuwa yana yan kame kame ya ce, "Haba yaya ka ko ga yanayin jikin Hajiya Hadiza a lokacin, ya zame min dole na nemo taimakon gaggawa ganin ba ka nan." Yusúf ya galla mai harara ya ja tsaki yace "To ga ta can kwance rai hannun Allah idan har ta mutu kai ne sanadi kuma kada ka yi zaton zan taba yafe ma, tabbas ka ja an yi mata alluran da suka gama aiki." Basiru ya yi rau-rau alamun kuka, ya yi kokari ya baiwa Yusuf hakuri amma kalaman su ka ki fita hankalinsa gaba daya ya jagule. Sai su Falanke da Yusuf ke kai da kamowa akan Hadiza. Hadiza ta sami bacci amma Yusuf zaune ya kwana yana rungume da Hadiza, in ta motsa ya juya ta yana yi mata 'sannu har karfe shidda na safe ya sa ruwa da tawul ya goge mata jiki tsab kamar ta yi wanka. Yusuf da kan shi ya fiddo kwalayen da suka yo ma kannan Hadiza saye-sayen komawa makaranta ya mika masu tare da makuden kudade yace su biya kudin makaranta. Sannan yace idan gari ya yi haske su koma gida amma su shaidawa Inna Tambai Kubra ce babu lafiya shiyasa ba za su tsaya ba sun koma Abuja don ta ga likita. 70 Karfe shidda da minti goma sha shidda na safen ya tsaya da mota kofar gidan Gwoggo Halima ya yi mata sallama yace sun shige Abuja domin kwana ya yi akanı Kubra jiki dai ya ki dadi. Ta yi masu kyakkyawar addua. Suna isowa Zariaya sai idon Yusuf ya kyallo wani shahararran asibiti mai suna Mayfair Cliniic. Ya juya ya ce "Falanke yi ribas mu shiga asibitin nan, a zamanin da na ke karatu anan na san labarin asibitin akwai wata mata jair fata mai suna Dr Banu kamar aljana tai ke don sani, bari mu shiga ta duba min Kubra." Bayan nas ta amshe su an bude masu kati an auna nauyin Kubra an auna yadda B.P din ta yake sannan ta rubuta dukkan rufotonta a katin. Nas ta shaida masu ga likitan da za su gani. Yusuf yace, shi Dr Banu ya ke son gani, tace yau lahadi tana gida. Yusuf ya nemi kwatancen gida akia yi masu. Cikin sa' a Dr Banu ta duba Hadiza a gidanta, a kalla sai da su Yusuf suka kwashe awa biyu a gidan [Dr Banu tana diba Hadiza da yi mata abunda ya dace, cikin ikon Allah ciwon kai ya sauka, sai rashin jin dadin jikinta da kwabewar ibaki, bakinta ya yi takab kamar wadda ta yi watanni tana ciwo. Daga karshe Dr Banu ta shaidawa Yusuf kada a kara yi ma Hadiza allura ko shan magani sai da izinin likita domin tana da shigar ciki na sati uku. Yusuf yayi jagwale ya rinka jin kamar ya koma Bakori ya shake Basiru, wai cikin da ya ke addu'a tun kafin ya mallaki Kubra shi ne a lokaci guda Basiru ya nemi halakawa don tsabar kauyanci da sokonci. Amma dai abu daya ya karfafawa Yusuf zuciya har ya manta da tsanar Basiru shi ne bayan sun fito daga gidan likita Falanke ya mike hanya santal sai Hadiza ta rausayar da sanbala sanbalan hannayenta a bisa Yusuf yayin da shi kuma duk ya tattaro hankalinsa ya dora akanta yana hanzarin son ya ji abin da zata fada. Tace a hankali "D bakina babu dadi amma da zan samu sakwara miyan ganye da na ci." Nan da nan murna da zumudi suka kama Yusuf tabbas sauki ya samu, ya umurci Falanke da su biya Shagalinku. Anan ma an yi sa'a domin sai da gidan cin abinci na Shagalinku suka lissafa masu suna da miyar ganye kala 71 uku, Yusuf ya dubi Hadiza sai ta yi mai murmushi tace, "Na fi son miyan shuwaka." Yusuf bai yi odar na shi abincin ba sai da ya ga majinyaciyarsa ta dan ci abin kirki sannan ya yi odar dankali da koda da kwai da shayi ya dan kakkafe ido yana zolayar Kubra yace "Kubra a zo a taya ni mana kada ki manta ni ma fa na sa ma naki abincin albarka." Hadiza ta rausaya kai tace, "Haba D, so kake na yi amai ko?" Yace "Sai na tara maki hula ta ki yi a ciki." Tace "Baka jiye min wahala kenan?" Yace, To me kike so na sai maki yanzu?" Ta dube shi ido cikin ido tace "lemo tanjirin da goro." Ya yi dariya yace, "Oh ni dan Yusufulle Allah Yasa dai cin goron ba mai dorewa ba ne domin bana son wa'annan kyawawan hakoran su yi ja." Ciki dai sai da ya shiga wata hudu sannan Hadiza ta koma hayyacinta har ta fara jin dadin amarci. Sau biyu Inna Tambai da Gwoggo Halima Basiru na kawo su har Abuja suna gayas da Hadiza. Ba wai gidan Yusuf ba kadai hatta 'yan aikin gidan Gwoggo Halima kamar ta hade su don so da kauna. Albarkacin Yusuf, babu jin dadinta irin yau ga ta a gidan Yusuf na Abuja tare da matar da suke so kuma har da juna biyu; ko tari Hadiza ta yi sai Gwoggo Halima ta ji har cikin ranta, wannan irin son ya rinka dawo ma da Hadiza tunanin mahaifinta, ina ma yana da rai ta auri Yusuf? Amma anya ko Yaya Amina na son ta domin ko da ta ji labarin rashin lafiyar Hadiza na juna biyu ne babu abinda ta yi illa tsaki da kin yadda ayi maganar. To wajen aikin Hadiza ma dai har yanzu tana bisa aikinta tun tarewanta Abuja takardan taransufa dinta ta iso a daidai lokacin da ta sami wata biyu gidan Yusuf haka dai ta rinka zuwa aikin cikin ciwo ga wani masifan kyau da tayi saboda haka sai ta rinka ganin kamar duk mazan da ke shiga bankinsu ita kadai suke kallo, wannan abu ya dami Hadiza don haka sai ta yanko yadi kala-kala ta baiwa Falanke ya dinka mata manya-manya 72 hijabai ta rinka zubawa idan zata aiki amma duk wannan bai janye wasu kwazababbun mazan ba da yawaita kallonsu a fuskarta ko kuma kyawawan yatsunta. Yauı wata bakwai kenan da auırensu kuma watannin cikinta. da yamma tana kwance bisa cinyar Yusuf hannun Yusuf na bisa kan Hadiza yana warware mata kitso, yayin da idanun Hadizan ke lumshe tunani ya rinka karakain a a zuciyarta, ita dai kawai ta san ta yi sa'ar miji domin irin dawainiyar da yake yi akan ta itta ta san bata tba shi wadatattar kulawa saboda yanayin aikinta, sau tari bata dawowa daga aiki saigab da mangariba kullun shi Yusuf aka fi samu a gida yana aiwatar da abinda ita ya dace ace tana yi sannan kuma bai nuna damuwarsa haka nan ita gaba da ya a tsarin rayıuwarta sai take ganin aikin banki bai dace da ita ba in dai tana son gyara lahirarta. Waya ta yi kara ta katse tunanin Hadiza, Yusuf ne ya mikar da hannunsa ya dauki wayar, Hadizan Jos ce bisa layi tace, "kwana hudu Yusuf ba zuwa babu waya, ka san dai don ta Hadiza ba za a yi zumunci ba daman kai ne mai kwaranniyar gidan na ku." Yusuf ya yi dariya yace "Gaskiya ne Hadiza kwarai ko na kwna biyu ban kira ki ba abubuwan ne sun mani yawa, ga kula da Kubra sannan ga lura da shi ainihin bebin domin yana matsawa Kubra da rigima sai idan ina kusa ina taya ta hidima da shi." Hadizan Jos ta kyalkyale da dariya tace "Da alama za' a haifo mai rigima inn ka." Hadiza ta mike zaune ta ams he wayar daga hannun Yusuf tace "To ina jin irin sharrin da ake man har jaririn da ke ciki ba ku raga masa ba ko?" Sun jima ana wasanni irin na aminan junan daga bisani Yusuf ya roki arziki da cewa 'yar JJos ta shirya ta raka su sayesayen jariri gobe. Aka aje wayar da wannan alkawarin. A vvata alhamis rannan Hadiza ta yi sa'a ta dawo aiki da wuri kamar kowanne ma'aikaci, bayan ta idas da sallar la'asar sai ta fiddo akwatuna har uku na kayan jariri tana gyarawa tare da kiyasta kudinsu a zuci yanzu dai cikinta wata takwas hatta kayan da zata saka ran suna D din ta ya kammala ko hankicin da 73 zata yi anfani da shi ba wai bebin ba sai da ya tabbata ya saya. Hadiza ta yi jigun tana tunani to wai ita ina anfanin aikin da take yi? Na farko dai bata baiwa Yusuf kyakkyawar kulawa sannan ga shiga fitinar maza kullun, kuma ko sisi baya bari ta kashe cikin albashinta ya dauke mata nauyin komi, shin wai me zai sa baza ta hakura da wannan aikin bankin ba ta rungume Yusuf da kyautar da Allah ke shirin ba su? 'Salamu Alaikum' Yusuf ne ya turo kofar dakin Kubra ya shiga ya cimmata zaune dirshan bisa kafet ta yi daidai da kayan jaririnsu ta waiwaya ta amsa masa yace, "Na kwalla kira Kubra kamar sau uku amma na ji ki shiru, duk shirye - shiryen haihuwar ne, ai ni ba ki sani ba Shugabana zai takura min kwarai ainin, wai London za mu ni da shi nan da sati biyu." Ta dube shi tace, "Shi ne me D, kai za kai min haihuwar? Don Allah kada ka damu kuyi tafiyarku, inda duk ka ke addu` a ce taka, ni ba ka san ma abinda ke damuna ba wallahi ni fa so na ke na aje aikin nan." Yusuf ya fiddə ido yace "Me ke damun ki ne Kubra? Ki aje aiki fa ki ka ce!" Ta yi dariya tace, "To menene na zaro idon aiki kala nawa ne ya halatta ga diya mace?" Yusuf ya aje hularsa a jikin gado ya je ya zauna kusa da ita ya ce "Don Allah Kubra idan har da gaske ki ke to ki fasa ki rufa min asiri da bacin ran Yaya Amina don ba za ta so aje aikin ki ba." Hadiza tace "Bacin ran ta za mu duba koko haduwa ta da Ubangiji? Ka ma daina wannan maganar, ilmi dai na yi don tspron lalura amma aiki na hakura da dai na zabi fannin da ya dace ne to." Yusuf yasa hannú ya dafe kai ya dago ya dube ta yace, "Kubra ban amince ba, ki tuna fa duk wahalad ilmin ki babu wanda ya sani sai Yaya Amina da `yan uwan mijinta, dama - dama idan da Baba Kado da ni mu ka sha dawainiyar ilminki sai na amince, amma yanzu kullun ina kokarin na ga mun shirya da Yaya Amina sai kuma ta ji ance kin aje aiki dole zata kara tsanata." Hadiza ta sha mur tace "Kana nufin ta nemar min ilmi ne don na nemar mata kudi koko?" Ya dube ta nan da nan ya razana don ya ga irin kallon da baya so idan ranta ya baci ya gyara zama yace "Look Kubra ki fahince ni mana wane irin zance kuma ki ke...... 74 " Tace, "To na fahinta kai ma ka fahince ni. Zan bar aiki don tsakanina da Mahaliccinmu ka gane?" Ya dan dube ta har yanzu bata daina irin kallon da bai so ba sai ya ce "To na ji amma don Allah ki ban lokací zan yi tunani ko mi kenan zan sanar da ke." Ya yi haka ne domin baí son abinda zai kawo rudani tsakaninsa da Kubra saboda ya lura ta fusata, shi kuma ba wai yana son aikin nata bane dole sai dai yana tsoron Yaya Amina. Bayan sallar isha'e da Yusuf ya dawo masallaci ya tsaya jikin wata itaciya a harabar gídansa yana tunanin matakin dauka yadda ba zai batawa Yaya Amina ba kuma ba zai cutar da Hadiza ba. A karshe ya yanke shawarar da ya ke ganin ta dace. Ya iske Kubra kwance bisa gado ya isa gare ta ya zauna a bakin godo, ya yi tagumi da hannaye bibbiyu ya kira sunanta 'Kubra' ta amsa 'Na'am' yace "Zai yi kyau ki shirya ki je gida can Malunfashi wajen Yaya Amina ki nemi shawararta kaman yadda ki ka nemi tawa ko?" Ta dan runtse ido tabbas itama tana shakkan tunkarar Yaya da wannan magana, sai tace, "Amma tare za mu ko?" Shi ma gabansa ya fadi ras domin irin yadda Yayar ke nuna masa abun ya fara baci, a kwanan baya za su Katsina daurin aure sun biya gayas da ita shi da abokinsa da kyar ta amsa, da zai tashi ya aje mata dubu biyar, amma abin mamaki yana shiga mota ta aiko karamin danta ya aje mai kudin a cikin motarsa, wannan abu ya yi ma Yusuf ciwo domin ko darajar abokinsa bai sa Yaya ta raga mai ba. Ya ja dogon ajiyar zuciya yace, "To Kubra idan dai kina na raka ki zan raka ki, amma zan ba ku hili ku yi shawara wallahi tsoron Yaya nake." Tace, "menene abun tsoro game da maganar lahira, ni dai idan ba ka zuwa ni ma ba za ni ba." Ya jingina jikinsa zuwa jikin Hadiza ya lumshe ido ya shiga tunanin yadda za su wanye da Yaya Amina. Ranar asabat da azuhur suka isa gidan Yaya Amina, sun yi sa'a Yayan na daki tare da wata tsohuwa Gwoggon Yayarce, don haka sun sami kyakkyawar marba wajen Gwoggon da ta zan kaka ce ga Hadiza, ta rinka yi ma Yusuf wasa na maigida. 75 a Bayan sun jima cikin barkwanci Yusuf ya dubi Hadiza yacе, "Zan koma dakin Saminu na jira ki." Sai Yaya Amina tace "Tafiyar me za ka yi, itama ta tashi ku tafi mana." Gwoggo ta juya fusace tace. "ke Amina ya kamata ki sakar ma yaran nan mara, ina dalilin irun wannan riko? Ko wannan rabon ai ya dace ace kin janye hushin ki." Amina ta kawad da fuska gefe daya cikin nuna jin zafi tace "Ni ban ce ina hushi da su ba Gwaggo, harkarsu се dai babu ruwa na." Yusuf dai ya mike ya yi waje. Hadiza ta karkace kai ta ce, "Yanzu ma matsawa ya yi wai sai na kawo ma Yayan shawara don na ce masa ni, fa zan aje aiki." Yaya Amina ta galla mata harara tace, "zancen wofi ina kuma ruwa na da aje aikinki? Ke daman yanzu kina da wani aiki ko sha'awa wanda ya zarce nashi? Ai bukatarki ta biya kin fake da karatu sannan aiki kina zaman jiransa to kin same shi me kuma zaki ci da aiki?" Nan da nan hawaye tar daga idanun Hadiza tace, "Wallahi Yaya ba haka ba ne, matsalar aikin namu ne, ba ta matar aure ba ne---". Gwoggo tace, "Ke Dije kuna dai zaman lafiya da mijinki ko?" Hadiza tana share hawaye tace, "E gwoggo. Tace "To ki aje aikinki ki bi mijinki sau da kafa, Amina ko ki bar ni da ita kada ki kara kawo mata irin wannan shawarar." Da suka tashi tafiya Yusuf'ya kawo kudi kamar yadda ya saba ya baiwa Yaya Amina itama Gwoggo aka bata na ta rabon mai tsoka. Kamar Gwoggo Halima ta san da zuwansu dan lokaci kankani ta shirya masu abinci iri iri, Hadiza ta yi rashe-rashe a dakin Gwoggon tana ta zuba shagwaba, kai ka ce Gwoggo tà kawo ta duniya, ita ko Gwoggo Halima sai kara rawan jiki take yı ganin ciki dai ya bayyana fili jikin Hadiza. Yusuf vace, "Gwoggo ina son ku je Abuja ku zauna ke da Inna Tambai nan da sati biyu saboda zan yi tafiya London." Gwoggo tace, "To Allah Ya nuna mana; a dai dai nan Malan Tukur ya shigo, bayan an jima da gaisawa Halima ta sanar da shi bukatar Yusuf, Mallam yace "ban yadda ba, abu duk taron mata?" Nan da nan Yusuf va rude yace, "Baba wai saboda asibiti kuma ga 76 Falanke." Mallam Tukur yace, "Wani abu ne Falanke? Me zai iya yi, haihuwar farko ce fa, sam ka maido mana ita nan Bakori a gabanmu, kai ko ka tafi wajen aikinka." Yusuf ya yi jagwale yana son ya hada ido da Hadiza amma ta ki yadda. Yadda Mallam yace hakan aka yi domin baya da ubar da ya fishi, yace, "Ni abin da yafi damuna shi fa Baba saboda wankan ganye ya ke son a maido ki Bakori ni ko ba don sun yi min ta karfin tisya ba ban yi niyyar su yi ma ki wankan gargajiyar nan ba." Hadiza ta yi dariya tace, "kai D wallahi ka daina irin wannan rudewan akan al` amurana, kada ace ka faye zakewa akan mace, menene idan ma na yi wankan, ina ce suma su Gwoggon sun yi ga su nan sumul ina ma laifinisu, ita Yaya ko kallo cikin ma ya ishe ta?" Yusuf ya shafa kai yace, "Ai itama Yayan da dalili take yi mana haka babu komi mu ci gaba da addu'a insha Allah sai ta yi ma wannan jaririn rawa tana juya shi." Hadiza dai ta rubuta takardar aje aiki ta kuma kai masu kayansu, yanzu ta mike kafa a gidan Yusuf. Ana sauran kwana biyu tafiyar su Yusuf ya hada kayan Hadiza da

Chapter 7 of 9