Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 9
da kut zata aura." Yallabai ya yi shiru tausayin Yusuf ya kama shi balle ma da yaron ya nuna mai shi maraya ne, duk zuri`arsu a kan shi aka rataya, sai ya ce ma Yusuf "To kai ba ka dan sakarma iyayenta 31 kudi ne ko kamar abokin na ka?" Yusuf yace, "Inal Yallabai ai wa'annan sun fi karfin a rude su da ku". Yallabai ya yi dariya yace "kai wawa ne ba ka san halin kanawa ba kenan. Bari na baka wani guntun labari: akwai wani bakano za shi England neman auren baturiya fara kal, sai abokansa suka ce masa 'wai wai Alhaji ka rufa mana asiri, kai da ba ka jin turanci ita kuma bata jin hausa? Ka dai ci gaba da auro filanin mata kyawawa', sai Alhaji ya yi dariya ya sa hannu aljihu ya fid do takardar 'yar wazobia wata naira hamsin ya daga masu ita yace, 'kun ga wannan, to babu yaren da ba ta ji a duniya, sai dai idan baka da ita'. Yusuf da Alhaji suka bushe da dariya. Yallabai yace, "Gobe zani gida Katsina sai ka shiriya zan tsaya Bakori na ga iyayen ita yarinyar wa anda su ke da karfi akan maganar, sai ka shirya da wuri karfe takwas na safe." Yusuf ji yake kamar an ce an bashi Hadiza dan murnar Yallabai zai sa baki a al'amarin. Karfe goma sha daya na safe suka isa gidan Inna Tambai. Yusuf ne ya fara shiga ya firgita Inna da cewa ta yi manya-manyan shinfidu ga shugabansu nan gaba daya ya zo ganinta, ai ko Inna ta rude har wata darduma ta shinfida bisa tabarma. Sun jima ana gaisawa yawancin gaisuwar a bisa matuwar Baba Kado. Sannan Yallabai ya gangaro bisa zancen Hadiza shi dai Yusuf na gefe ya takure, (manya na magana). Yace, "To Inna Tambai ai ina ganin da kai da kaya duk mallakar wuya ne, ki tuna fa ke mai nemarwa Yusuf aure ce, bayan kuskuren da yayi domin ko ita takun Ubangiji na iya jarabar ta da irin hakan, shin ashe idan da ta yi wani aure sannan ta fito ta zo tace a duniya kuma babu wanada take so sai Yusuf ashe mahaifiyarsa bata isa ta tursasa Yusuf ba akan ya yi hakuri ya auro Hadiza, domin kamar kanwa ce a gare shi? Dole ne kuma ya aureta ba zai ki ba domin kuskuren aure ba inda ba a yin sa. Amma yanzu inna kuna kallon Hadiza kun kyale ta zata bar dan uwanta akan wani kuskure kalilan na kuriciya?" Inna Tambai nan da nan ta ga gaskiyarsu anan, domin ta sha ganin yarinya ta 32 ki mijin sai daga baya, a dawo a neme shl bayan ta yi aure ta hayayyafa, kuma a rnatsawa namijin dole ya aura hakanan bayan a da can babu irin wulakancin da bata yi mai ba. Yallabai ya katse tunaninta yace "Wannan Amiru ba fa halin sa kuka sani ba, bayan Yusuf tun yana cikin ciki kun san halinsa. Don Allah ki natsu ki sami lokaci ki yi ma Hadiza nasiha irin taku ta manya". Inna Tambai tace, "Ranka shi dade wannan zance na ka fa abun dubawa ne, na yi ma alkawari zan yi iyakar kokarina, sai dai kuma idan haka Allah Ya kaddaro, to sai Yusuf yasa hakuri" Yallabai ya ji vwani irin sanyi domin babu wanda bai son ya nemi alfarma a ki yi masa, to anyi mai alkawari yace Yusuf ya dauko mai jaka cikin mota. Yusuf ya fita da sauri ya kawo jaka ya tsugunn yaba shi, ya bude ya fiddo bandir din 'yan wazobia sabbi fil na dubu as hirin ya baiwa Yusuf yace ya mikawa Inna Tambai. Inna ta bude hannaye tace, "kai Yusuf ina zan kai wa annan kudi ku bar su kawai". Ya yi dariya yace, "Haba Inna ku amsa, karamin aikin Yallabai kenan idan ki ka ji babban sai ki rike baki." Sun isa gidan Malan Iliya motar Yusuf ce gaba ta Yallabai na biye, sun kuma ci sa'a Malam din na gida. Bayan an gama gaisawa Yusuf ya gabatar da Yallabai kamar yadda ya gabatar da shi wajen Inna Tambai, shi kuma Yallabai ya shiga kurunta matsayin Malam Iliya a wajen Baba Kado, ya nuna masa shi kadai zai iya lankwasa Hadiza har ta saurari Yusuf. Malam lliyasu yace, "Ba haka ba ne, shi sha anin aure ba ai mai shishigi, haka nan ba za mu iya ja da ikon Allah ba, sannan ni yanzu Hajiya Hadliza tausayinta na ke ji, sanin tsakaninsu da mahaifinta, ba zan so na kara mata wani zafi ba a zuciyarta idan na yi haka ban taimake ta ba, na zalunce ta. Yallabai yace, "A'a ba wai muna son ka tursasata ba ne, a`a cikin nasiha dai". Yace, "Na yi maku alkawari in dai har ta nemi shawarata zan nuna mata gaskiya abinda ya dace". Anan ma aka danna mai dubu goma, suka kidima mai 33 kwanva. Yusuf basu yi sallama da Yallabai ba sai da ya kara gargadarsa da cewa lalle ya makalewa wa'annan 'yan tsaffin guda bıyu yana ganin akwai nasara a wajensu. Y isa gida wajen mahafiyarsa. A gaskiya ran gwoggo Halima ya fra jaqulewa a yadda ta lura da sigar dan ta Yusuf ta fara canzawa, ya zauna ya yi jagwale bai son yin ko wacce irin magana domin va san ba abinda gwoggo Halima zata yi masa, ta shiga kawo mai labarai amma bai kula ta ba domin bai san ma abin da take cewa ba, itama sai ta sa masa ido ta yi shiru zuwa can tace, “To wai kai yanzu haka za kai ta jerangiya bisa hanya akan neman auren da bashi da tabbas, ni fa ina jiye ma aikinka?" Yusuf ya yi kasake yace, "Ba haka ba ne gwoggo, yau ma tare mu ke da shugaban nawa har gidan Inna Tambai na kai shi, a bisa dukkan alamu mun fara samun kan Inna Tambai." Abin ya yi ma Halima dadi, sai ta ce “Ni ma zan shiriya na je anjima da yamma". KASHI NA GOMA SHA HUDU lyakan tika-tika tik komi ya yi farko zai yi harshe, masu tatsuniya kan ce tsakani-tsakani tsakanin gizo da koki in a gizon ba koki, to mu kuma anan mun ce in ba Yusuf ba Amiru, yau dai sauran kwana goma sha takwas kacal ayi sadakat arba'in din Baba Kado haka nan a bisa alkwari sauran wa'annan kwanaki a aurad da diyar Baba Kadon Hadiza ga mai tsananin rabo. Zamu iya cewa zamani rikicewar rayuwar zuri'ar gidansu Hadiza da Yusuf da Amiru, yayin da kowa ya ke fadar albarkacin bakinsa. Duniya ta yi wa Hadiza kunci, komi daci ya ke mata na cikin duniya babu abinda ke birgeta babu wanda ya ke bata sha'awa, maganar soyayya kwata-kwata wannan baya cikin ranta illa daga Amiru har Yusuf tana ganinsu bakirkirin, domin ta ga ita iyakar gwargwado tana nunawa Yusuf wulakanci, to amma shi Aniru a 'yan kwanakin nan ya fitittike mata sai a zaba akan wai 34 laifin ta ne Yusuf ke zuwa gidan iyayenta, tace "kana nufin tare da shi na ke yawo koko?" To ire-iren wannan maganganun ya fara haddasa masu matsala har to fara tsanar Amiru, yayin da shi ko Yusuf tana ganinsa akan mara tausayi wanda bai damu da kowa ba sai kansa, domin duk shi ya haddasa mata wannan bala'in maimakon ya bar ta taji da dacin mutuwar mahaifinta. A Abuja su Yusuf da Falanke sun lura da yawancin abokansu, yanzu an rabu gida biyu, akwai masu zuga Yusuf akan lalle shi ya dace ya auro Hadiza yayin da wasu suka zabi Amiru suna ganin Yusuf bai yi adalci ba. To a wannan 'yan kwanakin ne da suka rage kowanne ke nuna tashi bajintar don dai aga wanda zai nasara. Su Yusuf suka zuba kamar mutun uku wa'anda ke bin Amiru a gindi a gindi don a san abinda ya ke ciki, rufoton farko an kawo mai labarin cewa ga cikakken adureshin kanfanin da ya kai ayi mai aikin katin biki wato (invitation cards) kenan. Yusuf ya yi shiru, sai ya mike ya jawo waya ya latsa lamber Jos gidan Baba Rilwan kenan, yasa aka nemo masa Hadizan Jos bisa layi, bayan sun dan yi bakwanci yace, "Don Allah kanwata taimako daya na ke son ki mani" Tace "menene?" Yace, "Na san dai ba kya rasa haton mutuniyar mai kyau ita kadai don Allah ki taimaken ki ba ni yau din nan za aiko a karba". Hadiza ta dan yi shiru sannan tace, "kai Yusuf wai kai har yanzu baka hakura ba? Don Allah ka kyale yarinyar nan kada ka sa mata ciwon zuciya". Ya yi murmushi yace, "Haba kanwata Ubangiji ya baka abu, ka yi wasa da shi, kada ki damu wannan damuwar ta Hadiza duk ta dan lokaci ce, da mun kasance tare sai kun yi mamaki". Hadizan Jos tace, "To Allah dai ya zaba mafi alhairi sai ka aiko din". Karfé goma da 'yan mintoci Falanke ya dawo Abuja daga Jos da wasu hotunan Hadiza guda biyu kamar wadda aka kera da luu-luu don sheki. Wanshekare da safe Yusuf da Falanke suka je inda Amiru ya kai aikin buga katin gayya, sai da suka sa babban ma'aikacin a kwana suka ji ko nawa Amiru ya biya kudin aiki, sannaa suka bada na su da hoton Hadiza da na Yusuf ya linka masa kudin Amiru sau uku amma yawan katunan daya, mai aiki ya yi mamaki. Vusuf ya ce, "Ina son kayi min abu daya". Yace, "Ranka shi dade fadi ko minene za'a yi". Yusuf ya gyara tsayiwa yace, "Wa'annan kudin na ba ka su kyauta, kada ka buga min wani kati illa kawai idan Amiru ya zo ka fiddo hotuna na da na amaryata ka nuna masa ka ce masa, 'yaya a kai bikinmu ya zo rana daya, kuma sunan yarinya daya sannan a gari daya?' Sai ka ja bakinka ka yi shiru kada ka kuskura ka nuna mai cewa na san ya kawo aiki anan." To a wannan 'yan tsakanin Yusuf da Falanke ba sa iya cewa ga iyakar zuwansu Bakori, domin wani lokacin tsakar dare suke shirya tafiyar sai dai jama'ar Bakori su wayi gari su gan su. Ba tare da sanin Yusuf ba Falanke ya shirya ya je Tsiga wajen wani tsohon Malami aminin kakansa, ya fede masa bire har bindi na halin da Yusuf yake ciki. Tsoho ya yi shiru sannan ya ce, "Ina son ka yi kokari ka kawo min abu daya daga cikin wa'annan ko dai ka yanko min gefen kallabinta ko kuma sawun kafarta insha Allah idan na hada wani abu in dai har nan da kwana biyar babu magana mai karfi to ya hakura ba matarsa ba ce Falanke ya koma ya yi sa'a Hadiza na gidan Inna Tambai ya tsaya a kofargida gindin wata itaciya ya aika a kira mai Hadiza aka ce ya shiga, ya kafe ba zai shiga ba, ya matsa mata da aike sai da ta fito, ya shiga kuranta ta yana wasa Yusuf, zúwa can ta ce, "Abinda ya kawo ka kenan Falanke?" Yace, "Don Allah ki auri dan'uwanki Hadiza mai kaunarki". Tace, "Falanke kuna son ku zama sanadiyar batawa ta da mahaifiyata ne?" Yace, "Me zai sa ki zarge mu da wannan? Ai shi aure tunda aka halicci duniya aka san shi da rikici insha Allah mahaifiyarki sai ta yi alfahari da aurenmu". Ta yi dariya tace, "a cikin satin nan zan fara raba kati insha Allah ba zan manta da na ku ba Falanke, ni ka ga tafiyata, sai anjima". Ta juya ta rinka tafiya a tsanake, shi ko Falanke tafin kafarta kawai yake kallo, yana kallon in da take takawa sawunta 36 na bayas da shaida. Ya duba ko ina bai hangi kowa ba, ya fiddo wata leda ya durkusa ya debi sawun kafar Hadiza na hagu da dama, ya kulle a leda sai Tsiga wajen Baba Tsoho. Baba tsoho ya dan danki kadan ya ce ta isa. Falanke ya mayas da sauran cikin aljihu, Baba tsoho yace, "In dai na yi wannan aikin nan da kwana biyar babu bayani to ya kyale ta". Falanke ya fiddo kudi dubu biyu ya bashi, Baba ya girgiza kai ya ce, "Na gode mai da kudinka ai wannan kulla sunnan Manzo ne Allah ya ba mu lada, ya fi min wa'annan kudin." Wannan kenan a gidar Gwoggo Halima kuma, kullun a rikice take, gani take yi tamkar zata rasa dan da ta ke ji da shi a dalilin Hadiza, ya bi ya sukurkuce ya rame ya tsangwame kan sa kamar ba wata mace a duniya sai Hadiza, to har sai ta rinka raina taimakon da Malan Tukur ke masu. A wani marece ta shiriya ta je kauyensu Danja wajen wani tsohon Malami aminin mahaifinta, rabonta da shi tun zamanin tana goyon Yusuf da suka rinka samun matsala da Babansu Yusuf shi ne ta kai kukan ta wajensa, ya yi mata istihara yace, ta yi hakuri domin shi ne uban 'ya'yanta, haka nan akwai daukaka a cikin 'ya'yan da zasu haifa, ya kawo taimako ya bata suka zauna lafiya lau da Babansu Yusuf har sai da mutuwa ta raba su. Ta isa Danja ta je wajen Malam ya rinka yi mata fada domin bata kula shi, "Ya dace ace ko su Yusufa kina turowa suna gaishe ni". Ta ba shi hakuri tace, "ko yanzu ma zancen shi wannan din na zo maka da ita". Yace, "Lafiya ko?" Ta kwashe tun farkon lamarin Dije da Yusuf ta gaya ma Malam. Malam ya yi shiru yace, "Aure kenan! Yau sauran sati biyu da` yan kwani bikinsu da shi wancan abokin nasa?" Tace, "E Baba, ni kam idan wannan aure ba mai yiwuwa ba ne, na fi son ka yi mai asirin da zai ji ta fita ransa kwata-kwata, wallahi ba ka ga yadda yaron nan ya lalace ba". Mallam yace, "Ba komi, zan yi istahara kwana uku ki dawo. Idan fa matarsa ce ai ba mu da yadda za mu yi, in kuma ba matar ba ce dole ne ya hakura". 37 Gwoggo Halima duk ta kosa taji abinda kwana ukun za ta haifar domin cudewar lamuran ta isa. A can kuma Abuja bom din su Yusuf ya fara tashi domin Amiru ya isa Abuja ya je ofis din wani abokinsu Ashiru bayan sun gaisa, Ashiru ke cewa "To kai Amiru mu fa ba mu gane ba wai daurin auren wa za mu cikinku kai koYusuf?" Amiru yacе, "Wanda kuka zaba". Ashiru ya yi murmushi yace, "ni fa ina tsoron yarinyar nan Hadiza a cikinku na rasa wanda take yaudara, yanzu ran nan suna waya da Yusuf lokacin ta je Jos har ya ba ni mu ka gaisa kai ka ce sun riga ma sun yi auren, yanzu haka cikin satin nan Yusuf ya zo da hotunan ta, to amma duk ace wai kai zata aura ni fa ina tsoron yanmatan zamanin nan wa'anda idonsu ya bude, kada kana takamar ka yi aure ashe Yufuf ka auro mawa, abinda fa mutun ke yi shi ke samunsa Amiru". Anan zufa ta rinka karyo ma Amiru, duk wani son Hadiza sai ya ji ta fita ransa fit, amma ya cije bai nunawa Ashiru ba, ya mike yace, "Kai ni wannan bata damuna an ce matar mutun kabarinsa sai kun zo daurin aure". A mota ya rinka sake-saken ba zai yadda Hadiza ta yi aiki ba, ko alama, domin a ganinsa itace barakar da zai bar wa Yusuf da Hadiza har su rinka saduwa. Ya isa wajen buga katuna anan ma ya cimma sakon Yusuf kamar yadda ya umurci ma aiki ya aiwatar, ganin wani matsiyacin hotan Hadiza da na Yusuf, sai kawai Amiru ya amincewa ransa, wannan aure ko ya auri Hadiza shi da Yusuf ke da ita domin idan ya hana ta zuwa aiki zai hana ta ziyarar 'yan'uwanta ne a Bakori? Komi zai iya faruwa idan taje ganin gida wannan tunanin ya rikitar da komi na Amiru. Da ya bar wajen buga kati sai ya fasa komi na al'amurar kasuwancinsu ya koma Kano. Da aka yi sallar isha'i ya kintsa ya nufi falon manifinsa ya cimmasa tare da Alhaji Kabir. Bayan ya gayas da su, ya koma gefe daya ya takure, Alhaji Kabir yace, "Yaya ne Amiru wani abu ke tafe da kai?" Alhajinsa yace, "Ai shi ne, shi da muka yi sallama jiya akan ya tafi Abuja sai jibi zai dawo kuma ga shi na gan shi yanzu." Amiru yace, "E Baba daga Abujan na dawo, dole ce ta ja min dawowar, a gaskiya lamarin auren nawa yana ba ni tsoro, shi dai wannan abokin nawa Yusuf kusan yanzu ince ya fara juyarwa da Hadiza hankali, to ni abinda nake zullumi daya ne, kada mu yi aure da ita, daga baya ta rinta munafunta ta suna hulda ta can garinsu idan na yi magana tana iya cewa ya zata yi kamar wa ne a gare ta, To wannan shi ne üzuri na yanzu haka inda na bayar da aikin kati na iske shi ma ya kai na shi aikin katin shi da ita." Alhaji Kabir yace, "Kai Amiru kada ka zama wawa mana ka san Katsinawa fa shakiyay ne. Yanzu haka ya kai na shi katin ne, ganin ka kai don ya ruda ka, ka zargi yarinyar." Alhajin yace, "E da wannan amma ka san halin Katsinawa shegen hadin kai ne da su, ni kam tun kwanan baya na shawarce shi ya kyale auren nan, duk a yi a gama hade mai kai za su yi. To bai hakura ya dawo gida ya auri kirinmu? Ni kam idan za ka bi shawarata ka kyale su, domin har auren ya fita kai na, wannan irin fitina! Bana son fitina ni ka gan ni nan." Alhaji Kabir ya gyara zama yace,"'Ya'yan yanzu ne ba a sha ma ku alwashi, amma mene ne abun zuwa neman aure har Bakori Amiru, ga ya ya nan a gidana? Yanzu haka za`a sami yan mata shidda wanda suka kammala karatu, sun kuma isa aure. Da za ku amince sai kaje gidana ka fidda wadda ka ke so, Insha Allah ranar da aka sa maka ba a fasawa za`a kawo maka mata." Amiru ya koma dakinsa ya kwanta ya yi lamo tunanin rayiwar da yaso ya shirya da Hadiza ya rinka rushe ta a hankali, yasan zai so 'ya'yan Baba Kabir domin su Maryam da su Salma da sauransu duk babu ta yardawa kodayake babu mamaki matan Alhaji Kabir biyu amma fa larabawa ne, ya yi kuma sa'a gaba daya 'ya'yan sun debo kalar iyayensu mata. Kashegari da azuhur ya daidaici lokacin da Alhaji Kabir 39 bai gida Amiru ya kai ma gidan ziyara,ya cimma 'yan matannan shidda cif har da 'yan gutsatsi suna zaune a falo malaninsu na yi masu karin karatu, abun ya burge shi domin kowacce ta sauke alkurani tilawa take yi. Amiru ya zauna yana kallonsu daya bayan daya ya rasa wadda zai zaba don kyau (daman Bakano da farar mace?). Bayan an yi addu'a an shafa kowacce ta juyo tana cewa "sannu da zuwa Yaya". Ya amsa masu sannan yace, "Ashe Baba Malamai ya tara mana a gida haka?" Suka yi dariya, yace "zan sami lokaci na zo daya daga cikinku ta rinka koyar da ni". Suka yi dariya. Salma ce sarkin wayonsu da surutun tsiya itace tafi zakewa wajen zance da shi har tana cewa, "Yaya mune dai 'yan gaba gaba wajen liyafar bikinka ko?" Yace, "Babu ma kamar ke, ga kujerata ga taki". Ta ce, "Wai Yaya an ce 'yar Katsina ce kuma wani dan Katsina na son ta?" Ya yi dariya kawai tace, "To Yaya a ina za ku zauna ba dai can Katsinan ba kada fa ta raba mu da kai.” Maryam ta daka mata tsawa ta ce, "wai ke me yasa kike da shegen surutu ne Salma?" Amiru ya yi murmushi yace, "Kyale ta mana, ai ni ina son mace mai fadar abinda ke ranta, bana son kumbiya kunbiya. Gobe ma ki shirya. Salma zan zo ki raka ni kasuwa, amaryata ta ba ni sako ni kuma ban iya sayayyar mata ba." To a gaskiya Amiru ya kwana tunanin yadda Salma ke surutu ko babu komi ta debe mai kewar damuwan rashin Hadiza, haka wanshekare ya dauketa suka yini tare yana yi mata sayesaye, ya kawo kayan dakin sa ya aje da niyyar'su zai bata а ranar sayen bakinta mai surutu, amma a yinin rannan ya mallake zuciyar Salma kaf. A kwana daya, kwana biyu zuwa kwana uku Amiru ya gama shiryama zuciyarsa cewa Salma ta dace ta zama uwargidansa ta kowanne irin mataki, haka nan ya san shi mutun ne ba mai son yawan magana ba, amma yawan surutun Salma sai ya zamar masa abin yabawa, domin sai ya rinka jin wasu 40 maganganun nata suna da ma'anar sauraro. A kullun ya kan kira ta a waya amma sai karfe goma sha dava na dare, yayin da zasu kai har asuba suna bayyanawa junansu irin rayiwar da su ke sha'awar shiryawa. Bayan komi ya daidaita tsakanin gidan.su Aminu da na Salma abin nufi sun amince za'a daura auren Amiru da Salma kaman yadda a kai niyyar yi a da da Hadiza amman mahaifiyar Salma ta nemi alfarmar a bar shagalin biki sai bayan sati hudu domin 'yan'uwanta na birnin Misira su sami halarta. Sati biyu kacal yanzu ya rage a daura auren Amiru da Salma, Hadiza fa, Allah ga wa? Amiru ya yi waya Kaduna aka ce ai Hadizan na Bakori.Ya yi murna da jin haka sai kawai ya dauki yukunbonsa suka nufi Bakori. Hadiza da Inna Tambai suna tsakargida suna sallamar wasu samari da suka sa aikin shirya masu kaya a dakin zaure wato kabet ne da gado da madubi da waduruf Hadiza ta yo oda daga wani kanfani a Kaduna na gogaggen katako sai walkiya da sheki su ke, Inna Tambai, ta rinka yabawa tace, "Kai Hadiza amma fa kin yi kaya da kyau sai dai tsada". Hadiza ta yi murmushi tace, "Amma Inna rai da rai ne fa! Idan ka gaji da wannan fantin za ka iya canzawa, kuma katakon bai komi." Yakunbon Amiru ta yi sallama ta shigo, nan da nan Hadiza ta fara sunkuye- sunkuye nuna alamun jin kunya, Inna Tambai ta kai ta daki ta debo mata ruwa suka shiga gaisawa sannan Hadiza ta leko daga can bakin kofa a tsugunne ta gaida Yakunbo, sai Yakunbon tace, "Ke Hadiza tare muke fa da Amiru yana can kofargida." Hadiza ta mike a cikin jin kunya ta surutuka, ta ce, "To". Ta nemi tabarma ta nufi zaure, yana tsaye a zaure rike da wata yar karamar casbaha, ya daga kai ya dubi Hadiza ya amsa mata sallama yana mai 'yar siririyar dariya yace, Hajiya Hadiza!' Tayi murmushi tace, "Yallabai barka da zuwa, zauna mana". Ya cе, "Na gode". Ta zauna itama a gefe guda na tabarma tace "Menene na godiya kuma?" Ya ce "Ai dole ne wanda aka karrama da 41 gurin zama?" Sun jima yana yi mata dan barkwanci, sai ya rasa ta fuskar da zai iya bullowa Hadiza da cewa ya fasa aurensa da ita, domin mutuncinta da kamun kan ta zuwa kwarjinin da Allah ya yi mata sun cika masa fuska, zuwa can Hadiza ta ce, "Ina fatan ka zo mana da katin gayya domin ina son aikawa da na jama`ar nesa". Amiru ya tsurawa Hadiza ido sannan ya sunkaya yace, "Anya ko Hadiza zan kawo katunan nan kenan?" Gaban Hadiza ya fadi ras "Me kuma ya faru, Amiru?" Wannan itace tambayar da ta fito daga bakin Dije cikin murya mai fargaba. Amiru yace "E to ya zama dole na yi nazari a bisa al'amuran aurenmu da ke daga bisani na nemi shawarar magabata na, to sun nuna min yin hakuri zai fi alhairi a gare mu" Hawaye wasu na bin wasu daga idanun Hadiza har ta kai Amiru bai iya hada fuska da fuska da ita don tsabar tausayi saboda ya tsani mace na kuka balle macen da ya ke da tabbacin ransa na so ya dai hakura da ita ne akan tilas. Cikin murya mai sheshekar kuka ta ce, "Amma Amiru idan ka bar ni ka ci amana ta, me aka fasa cikin shirye-shiryen aurenmu?" Ya kara kawad da kan shi gefe daya yace, "Hadiza ban ci amanarki ba domin na dawo maki da wanda ki ke so ya ke son ki, kuma dan uwanki kamar yadda ki ka gaya min tun farko". Ta kara share hawayenta da gyalenta yayin da wasu suka tararo tace, "Wannan zance kana yi ne a bisa son zuciyarka babu wani son da ke tsakanina da Yusuf wanda har zai sa kace ka fasa aurena." Ya dan yi shiru yana tunani shin ko dai kishi ya ja masa ya yi wawanci! Lalle Hadiza na son shi, to yanzu ya zai yi, ya ce ma Yakunbo ta bar kaya kar ta amsa a ci gaba da aurensu shi da Hadiza har da ita Salmar, nan ne ma zai gane wadda tafi son shi idan suna rayiwar aure? Yace "To Hadiza yanzu kam zancena ya koma hannun manya!" Tace "me ka ke nufi?" Yace, "Baba Kabir ya ba ni mata 42 Gaba daya tun daga zuciyar Hadiza har cikin idonta sai ta rinka ganin duhu lunfashi ya rinka kokarin dauke mata, ta sa hannu ta danne kirjinta, ta rinka kuka a bayyane, Amiru ya juyo a firgice yace, "Shi kenan Hadiza zan iya hada ku ku biyu idan su Alhaji a can Kano sun amince min." Hadiza ta girgiza kai tace, "Babu komi Amiru ban ce ka roki kowa ba wai don ka aure ni insha Allahu Allah zai ba ni miji lokacin da ya dace na yi aure". Ta rinka addu` a a ranta wadda zata sami natsuwar ranta don hakalinta ya dawo jikinta, yayin da shi kuma Amiru ya rinka lallashinta yana yi mata nasiha, ta yi shiru sai dai goge hawaye akai akai. Amiru yace, "To Hadiza na gode kwarai da irin kaunar da ki ka nuna min Ubangiji Allah Ya sa yadda mu kai din nan ta zamar mana alhairi baki daya". Hadiza ta yi juriya tace "Amin Amiru, ni ma ina godiya ga niyyarka ta aurena

Chapter 4 of 9