Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 9
Allah yasa ke Hajiya Hadiza da Yusuf sai kun yi aure don a kulla wannan zumunta da marigayi ya so kullawa saboda duk wanda ya san Yusuf ya san ya zama abin tausayi saboda ga dai dukiyar ya tara amma ya kasa auren a dalilin tunanin abinda ya yi ma ki Hadiza da Baba" anan sai Falanke ya sa habar riga ya rinka goge kwalla, "takaicinsa a kullum bai da inda zai samu labarinki sai a wannan mutuwar Allah ya hada shi da ke." Hadiza ta tsargu da abinda Falanke ke nufi babu tantama wasu zancen banza ya ke nufi don haka ya tsuge da magana ta juya ba tare da ko sai anjima ba ta shige gida. Anan fa Falanke ya yi turus kai wannan shawo kanta sai Allah, tunda wa'annan maganganu ba su ratsa ta ba bai san kuma irin wanda zai yi mata ba. Ta zauna kusa da Inna Tambai tana ta fada tana fada mata abinda Falanke ya zo da shi. Inna ta ce, "kai anya Yusuf zai aiko shi da irin wa`annan maganganun?" Hadiza ta ce "wallahi Inna zai iya ban fa gaya maku ba ne kin ga rannan sai da ya fara min wasu maganganuan na kyale shi na shige gida abina, shi kan shi 10 Amiru na lura yana zargin Yusuf da abubuwa da dama sai dai kawai yana dannewa ne saboda mutuwar Baba". Anan Falanke ya kara aiko wani yaro`wai Shuaibu Tela ya ce wai Hadiza tai mai arziki don Allah ta zo!' Hadiza ta ce, "kai fita ka ba mutane waje ka ce na ce ya fita hanya ta". Sai Inna ta ceba haka za'a yi ba, je ka ce na ce ya shigo cikin gidan.' Inna ta mike ta fiddo tabarma ta shimfida masa daga can nesa, yayin da ita Hadiza suke zaune a bisa wata tabarmar a bakin kofar daki. Haba sai murna wajen Falanke aka shiga gaisawa da Inna Tambaya, sannan ya ci gaba da yabon Alhaji Kado kamar yadda ya yi ma Hadiza a zaure kowacce ta yi tsit ta na sauraronsa sai ya kutso maganar Yusuf kamar yadda ya fara. Inna ta ce, "kai Shuaibu kar ku mai da mu mutanen banza in dai batun Hadiza ku ke yi ba mai samu mu ji kunya a kasar nan, don rasin kunya zai ce bai san inda zai samu labarin Hadiza ina ce ya na zuwa gaida marigayin? Kuma ai ni ba bakuwarsa ba ce bai zuwa ya tambayan, to tsaya na gaya maku ba na son na kara jin zancen Hadiza a bakinsa, auren su ita da Amiru ba mai fasawa". Falanke ya ce, "kin san Allah Innarmu tsoro da zullumi da jin nauyi ya hana Yusuf zuwa gareku don ya ji labarin inda Hadiza ta ke, ya gwammace yai ta zama a haka cikin jimame da damuwa a nan ne ya fidda wasikar Yusuf ya je har gaban Hadiza ya aje, bata taba ba haka nan bata tsinka masa ba. Ya mike ya yi masu sallama ya tafi da niyyar sai ya dawo gobe saboda jin bayanin amsar wasikar. A can Abuja kuma Yusuf sai ya ga ai lokaci na kara kurewa mai zai hana ya bi Falanke gobe jumma'a don ya kara yin dan kokarinsa a kan Hadiza? Saboda haka sai ya yi ma kanensa Basiru waya wanda ke aiki a konannen bulo da ke Funtuwa, cewa idan ya koma Bakori ya sanar da Falanke kada ya taho gobe va jira shi zuwa ga shi nan tafe gobe jumma'a. Hadiza ta yi tagumi tana kallon rubutun Yusuf wanda shi ne ya ki ta anan gidan Inna Tambai kuma yau shine mai wannan wasikar cike da kalamai a dakin duk a dakin dai Inna Tambai wanda ita a ganinta wannan wasikar ba komai ba ce bayan bala'i ga wasıkar Sallama a gareki Dijena, 11 Sallama a gareki Dijena, Bayan miliyoyin addu`o`en da na ke mikawa wajen Sarki Allah akan ya yi ma BabaKado rahama da gidan aljanna, ya Allah ya ragwantawa Baba kado halinsa na alhairi ya sa ya bisa amin. Mu kuma da muka rage ya bamu guzirin cimma sa amin. Hadiza don Allah don Annabi ki bani aron kwakwalwarki ki tsaya ki yi tunani sannan ki auna maganganun da zan gaya maki. Da farko dai ina son kisani a duk lokacin da Allah Subahanahu WaTa'ala zai yi hukuncin baiwarsa akan wasu adilan bayinsa guda biyu wato macen kwarai da namijn kwarai ya kan jarabancesu ta hanyoyi da dama haka nan za ki ga ya'yan ya ku bayi wa'anda ba su aje ba basu ba wani ajiya ba Ubangiji ya yi masu kyautar 'ya'ya masu kyau da kwarjini da basira wa'anda akarshe sai kinga 'ya'yan nan sun cilla duniya ko'ina an san da su bayan iyayensu ba kowan kowa bane. To anan na san babu ko shakka ni na san wata baiwar Allah ce haka nan kema wata babbar baiwa ce a duniya, ina kuma tabbatas ma ki abinda ya gudana a tsakanina da ke ba komi ba ne face jarabawar Ubangiji. A lokacin da aka so aure na da ke Allah ya yi nufin abubuwa da dama akan ki na samun daukakar duniya da lahira wanda ta yiwu a lokacin in da mun yi aure, matsalolin aure su tauyeki har su hana ki kai matsayin wayewar da ki ke a yanzu. Ni kaina ko da na yi aure kila rabo zai kai ni amma daukaka ta da darajata suna wajenki dole Ubangiji ya sake kawo hanyar saduwarmu har mu yi aure sannan na cimma sauran alhairina. Lalle na san Baba Kado shi ne usilin soyayyarniu da ke, amma ina son na tabbatas ma ki, Allan ne ya kulla sovayarmu can cikin jininmu don haka ina son ki ba ni dama na nuna maki hakan, domin a yau babu Baba Kado a duniya kuma ga shi ina ji a jikina da gangar jikina alkawarin Allah zai cika akan Yusuf da Hadiza. Hadiza dan Allah ki yi nazarin yadda mu ka rinka shirya rayiwarmu, amma kash! Allah ya hana, to ni abinda na dauki wanna jarabawar Ubangiji ce, saboda ga shi ni yanzu Allah ya kai ni wani matsayin da zan iya rike mace hudu amma bani da 12 ko daya a dalilin rashin ke Hadiza wadda aka halitta Yusuf dan ita, yayin da ke dinma na san dole ki sha kwaranniya da yan maza a bisa baiwar daraja uku da Allah ya yi maki wato kyau na usuli, ilnni da samun iyaye dattawa amma kuma mijin bai bayyana ba wato ni kenan da aka halittaki domin ni. Hadiza don, Allah kada ki tauye mana hakkinmu, ki yi hakuri ki gafarce ni a bisa kuskuren da na yi ma ki a can bay a, ki yafe min ki bar ni na fito mu yi aure, wannan ranar da aka sa ma ki ban a son a canza sai dai a maido kai na. Hadiza ki tuna babu wanda bai kuskure a duniya, na tuba ki gafarce ni, Insha Allah ba za ki taba samu na da saba mа ki ba, domin ina son ki son da ban taba zaton zan yi ma dan Adar Kacda ki ce, tafi can mayaudarin banza wallahi wallahi Hádiza ke kadai na ke so, wancan son da na yi ma Fa'iza son kuriova ne amma son ki na gaskiya ne domin na so ki da kuniciya yanzu kuma ina sonki a lokatin da na mallaki hankalina. Bana tsammanin zan iya son wata mace kamar ke, don haka a da Baba Kad'o ya hadamu amma yanzu mu za mu hada kan mu, Insha Allah wannan soyayyar ta mu sai ta kai ma Baba Kado har cikin Aljanna Fiddausi. Na ki mijinki Insha Allah Yusuf. Hadiza tasa hanmu ta goge kan hancinta, duk kalma daya da Yusıf ya rubuto ta razana ta sai dai har yanzu zuciyarta ibata saduda ba, tana ganin babu abinda zai raba ta da Amiru, ko wacce irin daukaka Yusuf ke hango masuita kam tafi ganin ta wajen Amiru illah dai kawai daga ita har Inna Tamban kalaman Yusuf sun razana su, Inna Tambai ta ce, "ke kin ga min yaro in da duk ya kashe min jiki da daddadan maganganu? Tamkar an yo masa wahayin maganganun?" Hadiza ta ce, "Rabu da shi kawai Inna, shedananci ne rin na sa, wa ki ka taba ganin an yi wa wahayi in ba Annabin rahama ba? Wallahi idan kana sauraron irin su Yusuf sai su halakar da mutun." Inna ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Gaskiya ne maganar ki ai wannan sai mu rinká neman tsari da shi kar ya ja mana fitina cikin gari. Hadiza ta, yi murmushi ta ce, "Nan fa ya yi karya Inna 13 Insha Allah, tunda ya kawo kan shi gare ni, to sai ya raina kan shi, sai na nuna mai iyakar sa a garin nan." Washegari Gwaggo Halima ta fara shirye-shiryen abin ci domin Basiru ya sanar da ita zuwan Yusuf tana tunanin duk yadda akai akwai magana cikin Yusuf har ta vi niyyar kiran Falanke ta tambayeshi amma sai ta yi tunanin wannan rage ma kanta daraja ne, koma menene idan Yusuf na so ta ji shi zai sanar da ita. La'asar ko na yi sai ya Basiru ya iso da sauri ya ce, "Gwaggo ga Yaya Yusuf ya iso, ga direban shi nan da kaya ya ce akawo maku sannan a kai masa abincinsa can gidansa. Bayan Basiru ya gama shiga da tsarabar Yusuf ya ce, "Yaya Yusuf ya ce manshanu da kifi da suka fi yawa na babban gidan Mallam Tukur ne danyen kifi kuma na Mallam din ne. Gwaggo Halima ta ce,. "Au to ku tafi da shi mana idan kun aje ma Maitama abincinsa ba sai ku je can gidan mallam din ku kai masu ba? Kwa ce ina gaishe su". Yusuf bai sami zuwa wajen Gwaggo Halima ba sai bayan sallar isha'i. Tunda ya iso ya kira Falanke don yaji bayanin Hadiza bai ji dadin rifot din da Falanke ya kawo mashi ba, amma sai Falanke ya ce, “Haba Yallabai bana son ka nuna ragwanci ka tuna ka yi laifi tun farko don haka tunda mun gani muna so dole mu yi shirin daukar duk wulakancin da za`ai mana mu dai burin mu idan bukata ta biya ai shi kenan. Zancen Falanke haka ya ke, to amma matsalar da bai gane ba ita ce wai ta ina zai shawo kan Dije ta wacce hanyar? Ko alama maganar janyewa ya san ba tashi ba domin son Dije ya yi tasiri a zuciyarsa har bai son ya hasala komi in ba al`amuranta ba. Babban takaicinsa yanzu shine bai so Gwaggo Halima ta ji, don gudun kada ta hana shi a dalilin Amiru, shi kuma a gaskiya ya yi niyya babu fashi sannan kuma bai son bata wa Gwaggo Halima, to yana cikin`yan shawararinsa da zai gaya ma Gwaggo Halima idan ta kawo mai cikas. Ya isa gidan ya cimma Gwaggon na kaye-kayen kwanonin da ta wanke wa'anda aka kai ma Yusuf din abincin dare yace, "Salamu alaikum Gwaggo ko kun ganni". Ta vi murmushi ta ce, `mun ganka yanzu da ka shigo'. Ya ce, `ku yi hakuri Gwaggo 14 wallahi jama'a ne wannan ya je wannan ya je kuma kowanne da matsalar sa dole ne kuma mu saurare su tunda sun haifemu". Ta ce "ai hakan shi ne mai kyau ai arzikin jama'a shine arziki, shiga dakin ina zuwa". Ya zauna na dan lokaci ya dauki wani littafi na tauhidi yana dubawa da ya ji shigowarta ya aje suka gaisa sannan tabo can tabo nan na hirar da da mahaifi, can daja sama Yusuf ya rinka matsa yan yatsunsa ya ce, "Yanzu saboda Allah Gwoggo ashe kun san Hadiza ba ta yi aure ba, amma ba ku taba yi man maganar ba illa kullum ku matsa man in yi aure?" Ta yi jigum ta na kallonsa ta ce, "wacce irin magana ce wannan Maitama? Dijen da ka sa na dinga zúbda hawaye akan ka aureta ka ki, to don mi daga bay a zan dinga yi maka nacin maganarta?" Ya ce, "To amma Gwaggo kun san Dije ta canza ba kamar da ba." Ta yi dariya ta ce "au kai da haka ka ke ai kaima ka canzar" Ya ce “To ni dai gaskiya Gwaggo in zanyi aure to Hadiza zan aura". Ta dau lokaci kafin ta amsa tace "Maitama in kayi haka kuwa ka kyauta kenan? In ce Amiru ake maganar ansa masu rana yadda naji labari mai an ce, akwatunan lehen sa a kasashen turai ya hado su wasu sun ce shidda ya yin da vvasu ke cewa dozin ne. Yusuf ya sha mur ya ce, "Ni Gwaggo ina ruwa na da wannan, ni har ga Allah da zuciya daya na ke son Hadiza don haka ba na jin zan iya bar ma Amiru sai dai in Allah ne bai ba ni ba." Itama Halima ta shiiga tunani to yanzu akan Amiru za ta ki na ta ne? Balle ma yadda ta zaku da ya yi aure, sai dai tana ganin wata babbar matsala ce domin ta san Hadiza da wuya a shawo kanta idan an tuna da, illa dai kawai ta na ganin wannan ita ce damar da ya dace ace danta Yusuf yai aure haka nan, balle samun mace kamar Hadiza ba karamin shiryuwa ba ce a gidan dan ta Yusufa. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "za mu ta ya ku addu'a akan Allah ya zaba abinda yafi alhairi. Idan aure da kai shi ya fi alhairi Allah ya mayas kanka, idan kuma da Amirun shi ya fi alhairi. Allah ya kara kullawa." Yusuf ya yi murna da amincewar gwaggo sai ya ji wani karfi tamkar ya shawo kan Hadiza. 15 Wanshekare da safe ya sha ado da wata tsaleliyar shadda dogon wando da riga, ta yi mai kyau dan birni dan boko sosai yana janye da motar Falanke na zaune gefensa, sun nufi gidan Inna Tambai wajen Hadiza, sai Falanke ya ce, "Yallabai albishir a gareka". Yusuf ya ce, "mai kuma ya faru?" Falanke ya ce, "wai naji ance an mayas da bikin Hadiza sai ranar da za` ai sadakar arba'in din Baba Kado". Yusuf ya yi murmushi har kwarjininsa ya bayyana ga lafiya na tumbatsa kamar ruwan da ke sauka daga samaniya. a Ya fito daga cikin motar ya jingina daga gefen motar ya tsurawa wa zauren Inna Tambai ido ya na jiran ya ga fitowar Falanke tare da Hadiza, amma sai Falanke ya fito fuskarsa yamutse ya ce, "Yallabai wai kuma kaji wai Hadizanna Malumfashi?" A cikin rudewa ya ce, "yaushe ka ji ana cewa za ta dawo?" Falanke ya ce, "ni ban gane kan Inna Tambai ba na yi ma ta wannan tambayar ta ki man hannu". Yusuf ya sadda kai ya yi shiru ya ce shigo motar mu je Malumfashin. Suna isa Malumfashi gidan Mallam Isa mijin Yaya Amina, Saminu zaune a kofar gidan bisa dakali kanin Hadiza ne mai bi mata anan gidan Mallam Isa, ya mike da sauri ya nufi su Yusuf domin wani ikon Allah a duniya babu wanda Saminu ya ke gani da girma irin Yusuf. Dalilin kuwa shi yaro ne bai da mantuwa å lokacin da Yusuf zai auri Hadiza a duk lokacin da Yusuf ya zo gaida Yaya Amina, Yusuf ya kan rungume Saminu ajikinsa ya na sai masa biskit yana ba shi labarai tare da nuna mashi muhimmancin ilmi don haka ne Saminu ya mike da neman ilminsa a yanzu har yа shiga jami`a neman zama cikakken likita. To ko da ya ji ance an fasa auren yayarsa Hadiza daYusuf dauka ya yi lokaci ne bai yi ba, ko kuma Hadizan ce ta bata masa rai amma da ya ga aure ya zo tsakanin Hadiza da Amiru sai ya yi murna ga samun miji ga Hadizan to sai kuma mai? A daren jiya sai ya ji Hadiza na gaya ma Gwaggo cewa Yusuf ya dawo da niyyar aurenta, sai ya ji Yaya Amina na masifa kamar ranta zai fita ita ma Hadizan na taya Yaya Aminar masifar shi ne Saminu ya ce`menene na masifa haka amma kun san da Baba Kado na da rai dole ne a maida auren kansa, kuma ma ni banga laifinsa ba wanene a duniya ba ya yin kuskure? Tunda har ya gane kurensa ni ina ganin ai 16 gara na gida wanda aka saba da iyaye da kakanni'. Hadiza ta се "Idan ka isa sai ka zo ka kaini gidan Yusuf koko a yau ka haifi diya ka ba Yusuf karewar kauna daga yau bana son ka kara saka sünan mahaifina cikin al`amuran Yusuf ya na kaunarsa ya ci mana mutunci?" Saminu ya fice ya kyale su. To yanzu da hantsi kwatsam sai ga Yusuf. Saminu ya amshe su hannu bibbiyu ya kai su dakinshi na zaure, Yusuf ya ce, "Saminu an ce Hadiza na nan ko?" Ya ce "tana fa nan". Ya ce, "to don Allah don son manzonSa je ka ce ina son ganinta." Suna zaune a tsakar gida suna gyaran kayan miya Yaya Amina da Hadiza, Saminu ya shiga cike da fara'a ya ce, "Don Allah idan kina son saduwa da rahamar Manzo ki zo ku gaisa da Yusuf". Ta galla mai harara ta ce, "Saminu ni dai ba na wasa da kai kuma ko muna wasa ba na son maganar Yusuf domin ni ba shaidaniya ba ce ka ce ya fita hanya ta ban ga dalilin da zai sa ya matsa man ba". Nan da nan tsiya ta kaure tsakanin Hadiza da Saminu har ana neman a gaya ma juna magana, amma sai yaya Amina ta yi karaf ta ce, "Ni ina ganin har da laifin Halima uwar Yusuf, idan ba har Halima ta zama shashasha ba yaya za ta kyale Yusuf har ya dawo gare mu? To idan yana iko da ita mu ba ya iko da mu mai akai akai Halima balle wani danta Yusuf?" Anan ne kuma Hadiza ta sadda kanta kasa zuciyarta ta rinka bugun uku uku, me zai kai Yaya ta rinka zagin Gwaggo Halima koma menene ai Yusuf yai masu ba ita ba, haka nan kuma ita Yaya ai babbace me zai sa ta zagi Gwaggo Halima, bayan ta tabbata su Yusuf za su iya jin wannan zagin domin dakin Samınu da tsakargida ba wani nisa ne da shi ba a kalla komi Yusuf yai masu iyayensa sun fişkarfin zagi a wajensu kamar yadda ta yi ımani komi zai hada su da Yusuf ba zai taba iya zagin iyayenta ba. Daga Hadiza har Saminu sai suka yi shiru takaicin zagin Yaya Amina kawai ya ishe su, Saminu ya juya ya koma wajen su Yusuf ya na basu hakuri. Babu tantama sun ji zagin Yaya Amina domin Yusuf din cewa ya yi don Allah ka shiga ka ba Yaya Amina hakuri ka ue idan da hali ta ba ni dama na shigo na yi mata bayanin irin yanayin da Gwaggo Halima ta shiga a 17 lokacin da na yi kuskure, amma wallahi Gwaggo ba ta da laihi ni ne mai laihi." Saminu ya san halin mahifiyarsa don haka ya rinka bawa su Yusuf hakuri akan su tafi kawai babu komi, shi kuma Yusuf ya kafe a dole aje a baiwa Yaya hakuri a roki arziki shi ma ya shigo ya wanke Gwaggo Halima. Saminu ya shigo ya na ba Yaya hakuri amma sai ta kara haukacewa tana fadan cewa wannan danyen kai ake son aka wo mata. Hadiza ta ga an kwashi lokaci mai tsawo ana jayayya kan magana daya, ta riga ta san halin Yusuf mutum ne mai kafiya da shegen nacin tsiya idan ya nace kan abu sai ya ga karshensa kafin ya dangana saboda haka kawai sai ta mike ta shuri silifas din ta sai kofar gida. Saminu ya bita yana rada mata "Anti Hadiza kin dai san karshen mai wulakanci, don Allah ki bi sa a hankali ku rabu lafiya ban da wulakanci, mutanen nan komi ya yi mana mahifiyarsa ba ta cancanci zagin da Yaya ke mata ba." Hadiza dai ba ta ce masa uffan ba. Ta isa dakin Saminu ta yane labulen ta shiga ba ta zauna ba, sai kawai ta jingina ta mayas da hannayenta bisa kirjinta ta murde fuskarta ba alamar walwala. Ta yi ma Yusuf kyau fiye da kullum, idon ta sumul ba kwalli amma sai yusuf ya ga kamar mata su daina adon kwalli za su fi kyau a idonsa.Tsayinta ya mike sámbal cikin nan ya dafe daf sai kace kirar kwalbar coca - cola. Yusuf ya tsumu ya yi ajiyar zuciya sannan ya nuna mata kujera da hannu ya ce "To zauna mana Hadiza". Ta dube shi ido cikin ido dubar rashin mutunci ta ce, "Yusuf ba zama nazo yi ba na zo ne don na gargadeka kawai, don Allah ka daina zuwa inda na ke, domin ni babu komi tsakanina da kai." Falanke ya mike yana rawar jiki ya na fadin "Haba ranki shi dade kin fi karfin haka wajen Yusuf, ki natsu ki kwantar da hankalinki ki saurari Yallabai kaunar da yake maki ta shige duk yadda ki ke zato". Falanke ya fi minti biyar ya na bayani har dai karyarsa ta fara karewa, da Yusuf ya lura da haka sai ya dagawa Falanke hannu ya ce, "Je ka waje ka jira ni ina zuwa." Yusuf shi ma ya mike ya fara langabe kai ya fara `yan rantse rantse, "Wallahi, Wallahi Hadiza komai za ki man na 18 amince, iclan ma zagi na zaki yi na amince zagar ni na yadcla in dai za ki huce ki yarda da ni Hadiza kuskure ne na yi kuma ra yi maki bayani da takarda don Allah Iki yafe min kure na". Ta dlube shi ta ce, "Kiskure fa ka ce! To ni vvallahi ban taba daukar don mutum ya ce bai son wani abu ba don bai da FASALI kuskure ne, ai wannan ba kuskure ba ne, ba kuma abin jin haushi ba ne don ni abinda na dauki wa annan mutanen masu yin aure don kyau ko clon fasali wawaye maras a sanin ciwon kansu idain da cewa kayi ina da mugun hali na` yan iska shi ne abun jin zafi amma ni iabun tsana a gareka shi ne kai namijin ZARA ne ina kuma yi rna Allah godiya da ya hana min aure da kai". Ya ce, "Wallahi Hadiza ba ni da zara ke kadai na ke so!" Ta ja tsalki ta ce, "kai yianzu za ka iya tuna ko mata nawa ka nema a duniya?" Ya ce, "ni dai wallahi Hadiza ke kaclai na ke so ke kadai kika rudi zuciyata clon Allah ki tausaya man ki rufa ma rayuwata asiri, sai ya koma kwalla su ka cika mai ido taf ya bude tafin hannuns a ya saka fuskarsa ya ce, Hadiza ki rag wanta man ki yi hakuri mu yi aure Hadiza ta kara tsanarsa da ta ga yana kuka ta ja tsalki ta ce, "Ka sian Allah na yadda ka na so na, to amma don Allah ka yi hakuri ka bar ni na auri wanda na ke so. Yusuf ya yi tagumi ya na kallonta gaba daya ta canza masa, idonta babu tausayin da ya saba gani a da babu soin da ya saba gani a da ya yi kokari ya ji zai iya ce mata ya hakura amma ya kasa, kuma ya rasa kalrnar da zai ce mata. Ta juya ta shige gida abin ta, suna isa Bakori dakin mahaifiyarsa ya zarce bayan ya yi sallama ya wuce ta a tsakar gida ya shiga daki ya zauna ya dage kai sama har ta shigo bai ce mata uffan ba, ta tambaye shilafiya?' ya kai har sau uku amma bai amsa ba sai zuwa can ya ce "Hadizan ce". Gwaggo ta ce, "Hadizan ce mai?" Ya ce, "daga ni har Falanke mun yi mun yi ta ki ha kura can mu ka same ta a Malumfashi." tGwaggo Halima ta ce, “To kun shiga kun yi ma Aminar magana". Yusuf ya ce, “Ai gara ma Hadizan amma ita Yayan ta fi daukar abin da zafi don kin yarda ma ta yi mu ganta!" Halima ta ce, “E kam abin da ka yi da zafi amma kuma ai kai dan 19 ta ne ban da abun Amina, mai zai hana ta saurareku Allah ba shi ko ba za su ba ka Hadiza ba ta gárgade ka don gaba? To Allah ya zaba mafi alhairi, sai ka je Mallan na son ganinka a bisa maganar domin na ga ya mai komi tun jiya". Yusuf ya zuro ido ya ce, "Gwaggo kina ganin zai iya hana ni ko?" Ta ce "Anya ai na ga ya yi murna da zancen sai dai ban san abinda istaharar daren jiya ta nuna masa ba a game da lamarin." Yusuf ya mike ko abinci bai nema ba, sallah ma a can gidan Mallan ya hada ya yi wato azuhur da la'asar domin azuhur a gaban Hadiza ta same shi a lokacin yana ta ban hakuri da magiya. Bayan sun gaisa da Mallam ya yi mai nasiha sosai a bisa hakkin dan adam ya nuna mai `wannan maganar Allah ce, dole wanda ka zalunta Allah sai ya tozarta ka a kan shi, ka ga anan Allah ya nuna ka zalunci Dije ga shi ka shiga hali mai wuya, to ka yi murna da sakayyar ta tsaya a kanta ba akan wasu matan ba, ka ci gaba da hakuri wannan duk yana cikin jarabawar Ubangiji, ka tuna itama a lokacin da ka ki ta ta shiga yanayin da ya fi naka wahala, amma a yau ga shi ya wuce, to kai din ma zai wuce ne, idan kuma matarka ce wannan duk bai hana aurenku sai ka je wajen Mallan lliyasu ka ba shi hakuri ka ce, akan maganar da na yi mai dazun sannan, ka je wajen ita Inna Tambayan". Ya miko masa wata takarda mai rubuce da addu`o`en ya ce, ka ci gaba da yin wa`annan ni ma zan yi nawa itama mahaifiyarka zan bata addu'ar da zata rinka yi ma ku, Allah ya zaba mafi alhairi. Ya ce "Amin Baba. Ni wallahi Baba na daukan ma rai na duk wulakancin da Hadiza zata yi min in dai

Chapter 2 of 9