jariri ya tayas da
motar ofis zuwa Bakori sannan wanshekare shi da ita suka isa Bakorin. "Insha Allah Kubra sai na dawo a gabana za ki haifu." Tace, "Haba don Allah D ka yì min addu ar na haihu cikin satin
nan mana, don ba ka ji yadda wahalad daukar ciki take ba ni." Yace, "kada dai ki shagale da zarar kin haihu ki ma jaririn addu` o en da na koya maki sannan ki yi kokari ki ba wa ko nas din ce kyamara a dauke ku hoto ke da bebin." Hadiza tace, 'In Allah Ya yarda zon gabatar da komi in dai na haihu lafiya!" Bayan Yusuf ya koma Abuja Hadiza na zaure gidansu na Bakori a nan Inna Tambai ta baro gidanta ta komo gidan su Hadiza yayin da Gwoggo Halima to mayas da gidan waen hirarta, duk dai ana tarairayar Hadiza.
Lokacin da Yusuf ya sami kwana tara a London da azuhur
Inna Tambai da Hadiza na zaune a falo sai kawai Inna taga Hadiza na fisge-fisge kamar wadda lantarki ke fisga, dan lokaci kadan ta fara canza kamanninta nan da nan Inna ta aiki yaro aka
77
kira Gwoggo Halima da Mallam Tukur. Duk wani kokari na Mallam
Tukur amma ina! Abun yace tura, nan da nan aka nufi asibitin
Funtua da ita, sun isa tana a some.
Kwana da yini babu tabbacin za'a sami Hadiza a raye, a
rannan ne Basiru ya yi ma Falanke waya ya zo. Likita ya bada
shawara cewa ayi ma Hadiza tiyata shi ne abu mafi sauki a
same ta kila. Falanke ya janye Mallm Tukur yace idan dai tiyata
za'ai mata yana bada shawara aje asibitin Mayfair da ke Zariya.
Kowa ya amince aka nufi asibitin Zariya. Ankudi ce ta
nufi Malunfashi cikin mumunnan yanayi tana kuka tana shaidawa
Yaya Amina halin da Hadiza ke ciki, Yaya Amina ta yi shiru kamar
maganar bata dame ta ba, amma sai ta mike ta nufi kewaye ta
rinka tsuga zawo, to yo alwala ta zo ta gabatar da nafila ta roki
gafaran Ubangiji ta rinka rokon Allah Ya ba wa Hadiza lafiya,
idan kuma ajali ta dauka Allah ya yi mata sakamako da gidan
aljanna.
Ta yi sallama ta mike tace ma Ankudi "Yanzu su Tambayan
suna can asibitin?" Ankudi tana 'share hawaye tace, 'E tunda
safe can na baro su, kai Dije kam na cikin hali Ubangiji Ya tayas
da kafadar wannan yarinya idan aka rasa Dije mu ai tamu ta
same mu, yarinya ita da mijinta sun kama kannansu sun rungume?"
Amina ta shirya suka nufi asibitin Funtua itá da Ankudi,
suna isa suka ci karo da Sabura tana kuka tace, 'Ai Dije kuma
sai yadda Allah Ya yi domin an nufi Zariya da ita za a yi mata
tiyata.'Amina ta dafa sandar baranda sai hawaye shar, su Ankudi
na bata hakuri, tace idan har ban sami Dije da ranta ba, su Ankudi
ku ne shaida na yafe wa Hadiza, Allah Ya yi mata albarka, Allah
Ya sada ta da rahamarsa.'
Amina da Ankudi da Sabura har bayan la'asar suna jele a
garin Zariya kafin Allah Ya ba su sa'a su gano asibitin May Fair
Clinic. Sun samu har an yi ma Hadiza aiki. Amina bata kara saduda
ba ta kara tsinkewa da raunana sai da ta ga yaddə Allah Ya
mayas da Hadiza. Wato Hadizan na kwance ga karin ruwa ana yi
mata ta kumbara sumtum tamkar zata fashe, a dakin da take
78
kwance ita kadai ce sai Inna Tambai zaune gefenta ta rike hannun
Hadizan wanda ake yi mata karun ruwa, a can wata kwana Gwoggo Halima na zaune ta makure taci kuka har ta ji kukan babu dadi.
Yaya Amina ta kama kafafun Hadiza ta rike tana salati
tare da cewa "Allah me na yi maka zaka dauke min Hadiza, yarinya mai hakuri da nisan hankali? Ya Ubangiji Ka baiwa Hadiza
lafiya ko na sami kafar gafara daga gare ka, domin na san tsakanin da da mahafi akwai hisabi ---" Halima tace, "Haba
Amina, ki yi hakuri ki kwantar da hankalinki don Allah ki aje
wa` annan maganganu cikin ranki in Allah Ya yarda Hadiza za ta
warke, ga abinda aka fid da mata can muna jira ta farfado a
nuna mata kafin aje a rufe." Amina ta yi kwal kwal tace, "Yanzu
duk wannan wahalad da aka sha babu dan?" Gwoggo Halima
tace, "Sai idan da kin ga Hajiya Hadiza a shekaranjiya da jiya wa
ke ta jaririn mu dai addu`armu yanzu a same ta aaye."
Amina da su Ankudi suka bi inda aka nade sambalelen
jariri a zanin Hadiza, Gwoggo Halima ta bude masiı, yaro mai
kyau kamar yana bacci. Amina ta share kwalla tacę, "Halima a
fuska kamar Maitama ko?" Gwoggo Halima ta goge nata kwallan tace "Wallahi hatta kafafunsa da `yan yatsunsa kamar an ciro
na Maitama." Su Ankudi suka ce "Allah ya baiwa uwansa lafiya. Allah Ya sa mai cetonmu ne a can."
A lokacin da Hadiza ta farfado an yi sa'a hankalinta ya
dawo jikinta, illa kawai ba a jin abinda take fada domin sautin
muryarta ya dakushe haka nan halshenta ya raunana saboda
taunewar da tayi ma halshan. An kawo mata jaririnta sai dai
bata san ya mutu ba, tana ta kokarin su fahinci abinda take fadi
wai a sa shi jikinta ta yi mai addu'a amma su Inna ba su gane ba,
ta rinka nunawa Basiru ya je gida ya kawo kyamara anan ma
babu wanda ya fahinci abinda take fadi, har hawaye suka rinka
zuba mata, an dauka ta gane dan ya mutu amma ina!
Sai bayan isha'i su Mallam Tukur da Basiru suka tafi da
jariri, a gidan Gwoggo Halima aka bisne shì.
79
A kwana daya da yi ma Hadiza aiki zuma kwana uku jikinta
ya yi kyau har tana zama tana kuma cin abinci ta kuma san babu
jarini amma Hadiza ita ke baiwa su Gwoggo hakuri illa dai kawai
tana nacin cewa ita Yusuf take tausayi ya kwallafa rai akan
cikin nan.
Ana gobe za'a sallami su Hadiza daga asibiti ana hira, Inna
Tambaya tace, "Diyata kin dai sha albarka wajen su o'o" ( ta
rinka nuna Amina). Aka kyalkyale da dariya yayin da Hadiza
kanta na sunkuye ta rinka murmushi tana dan kallon Amina a
cikin jin kunya sannan tace, "Don Allah Yaya shi ma D ki rinka sa
mai albarka wallahi duk abinda mutane ke fadi game da shi karya
ne. Mijine na gari, tunda muka yi aure daidai da rana daya bai
taba bata min ba." Amina a kunyace, tace, "O ni Amina Allah ya
kawo mu zamani Tambaya! Ai ni maitama kuma yanzu har
kunyarsa na ke ji idan na tuna da fuskar jaririnsa, Ubangiji dai ya
ba ku wani dan wanda zai sa zuciyarku ta yi sanyi."
To Yusuf Maitama dai bai dawo ba sai da Hadiza ta sami
sati uku cur da haihuwa. Ta Kano ya sauka don zai fi mai saukin
zuwa Bakori. Falanke ya je taryarsa tun a waya Falanke ya ki
sanar da shi abinda ake ciki, bar sai da ya dauko shi suka iso
Bakori, sannan ya sanar da shi an fa haihu da namiji amma babu
yaron. Yusuf ya yi dif kamar lunfashisa zai dauke, nan da nan ya
sami sauyin ido sun kada jajur, zuwa can ya fara inna lillahi wa
inna -- a zuci, yace, "Falanke koma hanyan baya muje gida
wajen Gwoggo Halima" tunda Falanke ya ke da Yusuf bai taba
jin sautin murya mai daci daga gare shi, tabbas muryar ta tsuma
Falanke tausayi da jimame suka kama Falanke illa babu abin yi
sai hakuri.
Gwoggo na zaune ta yi jigum itama cikin jimaman zuwan
Yusuf din take sai ko ga shi duf kamar an jefo shi, ta dube shi
bayan ya zauna sun gaisa a sanyaye, sai tace, 'Amma ba ka je
gida ba?' Yace, 'Bana son ganin Kubra wallahi tausai take ba ni
gwoggo, wai ya abun ya faru ne?' Gwoggo Halima ta warware
masa komi, nan da nan Yusuf ya zuba fuskarsa cikin tafunansa
80
yana wani irin kuka mai ban tausayi, Gwoggo ta mike ta fice
tsakargida, sai da ya yi ya koshi sannan ya sa hankici ya goge
fuska ya mike ya fito yace, "Gwoggo ina aka bisne shi?" Ta mike
ta shige gaba yana biye ta nuna mai kushewar dansa.
Ya jingina jikin bangon ya murde hannayensa a kirjinsa ya
zubawa kabarin ido, daga shi sai Allah sai ko zuciyarsa ya san
irin addu'o'en da yake karantawa a wannan lokacin. Na tsawon
lokaci sannan ya juya ya yi ma Gwoggo sallama ya nufi gida.
A falo kannen Hadiza ne su Larba, a dakin Hadizan tana
kishingide bisa gado, Inna Tambai na kwance bisa kafet ita Yaya
Amina bata dade da zuwa ba, tana zaune, Yusuf ya yi sallama ya
shiga murya a shake, ya nemi guri ya zauna ya rasa yadda zai yi
ya hada ido da Hadiza kansa a sunkuye, gaisuwar da yake ma su
Inna ma muryarsa na rawa. Yaya Amina da Inna suka shiga ba
shi hakuri nan da nan kwalla ta rinka cika mai ido ya mike da
sauri ya nufi dakinsa.
Inna Tambai na kwalla tace, "Je ki Hadiza ki ba shi magana,
kin ji, ki jure kada ki kara masa wani nauyin."
Hadiza ta sami Yusuf zaune a bakin gado ya zuba fuska
cikin hannayansa, ta yi sallama a hankali ta je ta zauna daf da
shi ta matse da jikinsa sosai, sannan ta dora kan ta a kafadartą
ta sa, hannun ta tana shafa hannuwansa, tace, "Haba D ka yi
ma Allah godiya da ka same ni, wallahi wannan rashi da muka yi
ba komi ne ba sai godiya wajen Allah, ka san abinda Allah ke
nufi da yi mana haka? Kuma ma fa abinda wannan yaro zai mana
a can ya fi nan duniya anfani, ni kam irin ciwon da na yi ama
tunda Allah Ya ban lafiya sai nake ganin wannan rashi ba komi
ba ne, sai hamdala.". Yusuf ya dago ido ya dube ta yace, "Ai ni
duk tausayinki ne ya fi damuna sai na ke ganin tun farko bai
dace na yi wannan tafiyar ba." Tаce, "Haba Di! Ko kana nan ka
isa hana Allah ikonSa?" Ya grigiza kai, tace, "kada ma ka fara
zargin kan ka don Allah."
Ya janye, yace, "Kwanta na ga inda akai maki tiyatar." Ta
kwance zani ta dage rigar sama ta kwanta yana dubawa yace,
81
"Amma fa aikin ya yi kyau, kin ga wajen na neman bacewa?"
Taca "Ai ka san an cigaba yanzu domin akwai wani kirim da
suka ba ni ina shafawa sun ce nan da wata shidda gurin zai
koma tamkar ba a yanka ba." Yace, "Ya nononki fa?" Tace, "Har
yanzu akwai ruwa kadan kadan." Yace, "yaushe za ki koma
asibitin?" Tace, "Yadda likitan tace idan na sami wata uku sai na
je za'a samin roba don hana daukar ciki." Yusuf ya fiddo ido
yace "kin ji wata matsalar kuma?" Suka kyalkyale da dariya.
A dadafe dai Hadiza ta yi wata biyu a Bakori. Yusuf ya
matsa suka koma Abuja, anan ma ya matsawa likita aka manna
mata robar bayan wata biyu da haihuwarta. A bisa dokar likita
an so ta sami kaman shekara kafin ta dauki wani cikin, amma
ina bayan wata shidda Hadiza ta sami ciki.
Ba su da wani aiki illa addu'a, da ziyarar likita, tunda cikin
Hadiza ya sami kimanin wata hudu a kullun da safe idan Yusuf
ya kammala sallar asuba, bai bari ya yi magana da kowa zai je
inda Hadiza ke zaune tana jan casbi ta bude barin cikin ta ya
dafa ya karanto Suratur Rahaman ya shafa akan cikinta, itama
akwai addu'o'en da take yi na musamman.
Wata tara cif ana lallashin ciki a wani marece Yusuf yace
'Kubra sati mai zuwa zan aika azo mana da su Gwoggo da Inna
Tambai domin ina ganin yadda cikin nan na ki ya bunkasa ba ki
wuce sati biyu nan gaba'. Tace, 'E gaskiya ka aika su zo, bana
fatan ma na kara sati daya.'
Amma sai kuma me? Cikin daren nan karfe biyu saura
Hadiza ta rinka girgiza Yusuf tana, cewa, "Di! Di!! Ka tashi ina
jin zan haihu". Ya mike yana salati ya dauko makullin mota ya
rungume Hadiza sai asibiti. Yana nan yana sintiri har asuba, ya
duba agogo dake manne a asibitin ya ga ya dace yaje yayi Sallah,
a lokacin ne ya tuna ko na shi agogon bai dauko ba. Amma sai
nas ta tarye shi da murna tace, ya zan baba, an sami kyakyawan
saurayi, sai dai kuma ya kara jira nan da zuna awa daya za'a
sake haifar wani bebin. Mamaki da al'ajabi suka kama Yusuf wai
tagwaye Kubra za ta bashi? Bai damu da ganin yaron ba don an
82
ce ana mai wanka sai ya leka ya hango Kubra na cije lebe, don haka ya nufi masallaci mafi kusa ya yi sallah ya dade yana addu'a sannan ya koma aka ce ta kara haihuwa sambaleliyar budurwa. Yace, "Alhamdulllah! Godiya ta tabbata wajen sarki Allah. Ya kutsa kai ya je ya yi ma yaransa addu'a.
Yana isa gida Basiru ya yi ma waya a Funtua, yace, ya
kawo su gwoggo sannan ya je Malunfashi ya sanar wa yaya Amina.
Murna da zumudi wajen Yusuf abin bai fassaruwa sai
wanda ya je barka ko suna zai gane ma idonsa, ita ko gimbiyar
sai ta kara zama mai yanga da takama kamor zata zauta Yusuf.
A ranar suna aka radawa yara, Abdulkadir da Halimat Sa'adiya, har da Salma da Amiru aka sha yinin sunan.
Shekara kwana ce ga mai yawan rai yau shekarar su Abdul
da Sa'adiya hudu, sun nuna kamanninsu a zahiri. Abdul Kubra
sak Sa'adiya Yusuf kamarsu daya hatta rashin jin halin Babansu
ne. Burin Hadiza ya cika domin ta mallake zuciyar mijinta tas ta fannin girke-girke bai iya cin wani abinci idan ba na tan ba, haka itace mai kula da duk hakkin nauyin gida bai san ace yau babu shikafa ba ko makamancin haka, hatta zancen wutar lantarki,
waya, gidan ruwa, kula da makarantar yaran su nauyin na kan
ta. Duk lissafin abinda zai kashe a manya-manyan gonakinsa na Funtua da Bakori Hadiza ke lissafin, ita ke kula da nauyin abinda za'a baiwa manajan gonar ya biya masu aiki, a kalla Yusuf na
noma uhun masara kimamin dubu biyu da dari takwas a shekara,
yana noman waken suya mai dinbin yawa, haka da hannun jari a
manyan kanfanoni kamar uku, sannan su uku shi da wasu abokansa sun kafa kanfanin da ake yin corn flakes mallakarsu, yayin da Yusuf ne ke noma masarar da kanfanin na su ke sirfawa
ta zama corn flakes, tirkashi!
Yau yana zaune a ofis ya sami bako wanda ya bashi mamaki, kun san ko wanene? Awal ne wanda suka yi jami'a
83
tare, sun yi murna da ganin juna, Yusuf yace, "Yanzu a ina ka ke
aiki?" Awal yace, "Ba dai kun yi mana wayau ba, kun bar mu da
alli? Ina can ina koyarwa Kaduna Poly." Wasila na san dai yanzu
'ya'va na han rututu? Awal ya sadda kai ya ce, "Allah ya yi ma
Wasila rasuwa Yusuf". Yusuf yace, "Oh my God ban sani ba
Awal ya akai?" Yace, "Wasila ta jima tana karatu kamar yadda
muka shiriya, daga bisani muka yi aure ta dade ma Allah bai
bata ciki ba har mun fara damuwa rannan ciki ya samu a wajen
haihuwa ta rasu ta bar ni da diya mace ta na nan hannun
mahaifiyata." Yusuf ya ce "Allah ya jikanta insha Allah ta yi
shahada Awal." Awal yace "Haka ne Yusuf" sai Awal ya juyo
wani hoton Kubra da ke aje bisa tebir din Yusuf daya gefen kuma
na Yusuf din ne da su Abdul duk sun dare bisa wuyansa, Awal
yace, "Haba wanan irin shuwa din nan ne na Maiduguri?" Yace,
"yaya akai ka gane da sauri?" Awal yace "Ai kyan ne ya isa, ga
'ya'ya kuma tubarkallah."
Yusuf ya jawo waya ya danna gida, Larba ce ta dauka
yace, "ke ina antin taku kira ta?" Kubra ta amshi waya ta се,
"Salamu alaikum D ya aiki?" Yace, "An gode Allah". "Kubra yau
ina da baban bako sai ki shiriya mana abinci da shi." Tace, "An
gama Yallabai."
Bayan an tashi aiki Awal da Yusuf suka nufi gida, Yusuf
yace "ina fatan za ka kwana biyu a gidana tunda aiki ka zo."
Awal yace, "Nagode ka ga na huta sauka a hotel."
"Salamu alaikum, I am home Kubra" Nan da nan sa Abdul
suka tsinko a guje suna ihu "Oyoyo Dady" Di ya suresu gaba
daya. Daga can kicin Hadiza ta bullo a bayanta Larba ce da kayan
abinci ta fara shirya tebir.
Kubra ta zauna suna gaisawa da Awal, Awal na mamakin
yadda Yusuí ya ari mace mai kyau haka fiye da Faiza, ga natsuwa
da hankali, kai wasu dai da sa'a su ke a duniya. Yusuf ya mallaki
komi na duniya anan ne, Yusuf yaa dariya yace, "Kubra wannan
shi ne Awal wanda ya kai ni wajen Faiza ya raba ni da ke." Hadiza
ta yi wal tace, "Kai D wacce irin magana ce wannan!"
84
Awal ya yi kasake, kunya da kakabi syka mamaye shi, sai
kai anya wannan ce Hadizan shi? Kuma ya kira ta Kubra, ya
dago kai ya dubi Hadiza yace, "ke malama za ki iya yadda da
hakan?" Tace, "ka dai san halinsa mutun ne mai son tsokanan
rigima." Aka kyalkyale da dariya sannan Yusuf ya sa Hadiza ta
yi ma Awal gaisuwa. Bayan ta shiga daki ne sun fara cin abinci
Yusuf ya bayyana masa lalle Kubra itace Dijensa wadda ya bar
ta domin Faiza a hankali ya warware masa labari kaf.
Cikin kwana biyu da Awal yayi tare da su Yusuf ya yaba
kwarai da iyalen Yusuf har Yusuf yace yana so a baiwa Larba
gurbin karatu a Kaduna Poly. Awal ya yi murmushi yace, "Idan
Larba ba zata ce min tsoho ba da nace ni har a gidana ma da na
ba ta gurbi." Yusuf yace wannan zance na Larba ne, "Abdul kira
mana anti Larba."
Cikin wata daya rak an kammala da komi Larba ta sami
miji ga kuma karatu ta fara.
Zaman Yusuf da Hadiza zama ne wanda kowácce mace
ke kwandayin samu, sai dai an ce babu dan adam din da kan
rasa matsala, to ita kam Hadiza matsalar ta daya da Yusuf wato
yadda ya ke sangarta 'ya'yansu, ko ita bata isa a kwaba masu
ba, Yanzu nan ya hau ta da fata kuma a gaban yaran, saboda
haka kwata-kwata yaran ba su tsoran ta, wani abun haushi abin
mamaki shi ne Sa'adiya ce ke tsalle daga saman bene zuwa
kasa sai Hadiza tace "Haba Sa'adiya ki fa bari kada ki ji ciwo."
Sai ko Sa'adiya ta yi dariya tace, "Ai ko na ji ciwo ke Dady zai
ma fada." Abun ya daure ma Hadiza kai idan ta nemi ta nuna ma
Yusuf kada su girma babu tarbiya sai yace, 'Haba Kubra, gida
nawa su ke yara ne fa!'
Me zai faru? Kubra na kicin na shirya ma Yusuf hadadden
abincin rana, yara na wasa daga waje, yaronsu mai wanki na
shanya ya gama wanki, Sa'adiya na hayewa bisa waya sai Ima
yace, "Sa`adiya ki bari fa za ki ji ciwo ke fa ba kya ji." Sa'adiya
tace, "Ina ruwa na da kai, banza kawai" karaf a kunnen Hadiza
85
yayin da Abdul ya rugo yana kara gaya mata.
Zuciya ta kulle Hadiza ta kama Sa'adiya tana bugunta,
har da fitsari domin ba'a taba yi mata irin wannan dukan ba,
hatta shi ma Abdul ya tsorata.
Yusuf ya cimma Sa'adiya taci kuka har fuska ta kumbura,
ya ji abinda ya faru haba ya shiga yarfa ruwan bala'i, yace,
"wannan kina son kashe min diya ne ba komi ba, ina abun duka,
to wallahi ba zan yadda ba, don ba ki so na sai ki huce kan
`ya`yana kada ki manta ina sane da kalaman rashin kaunar da
ki ka sha fada min ----'Hadiza ta shige dakin baccinta ta
balle babin kuka wannan itace rana ta farko da rigima ta kunno
kai tsakaninta da Yusuf. Kowanne ya shiga hushi da juna abinda
ba su taba yi ba.
A wannan rana Hadiza ta raba dakin bacci da Yusuf, shi
ma ya nuna hakan ta yi mai dai dai domin zuciyansa na tafarfasa
da kunar zafi akan abinda ta yi ma Sa'adiya. Kwana daya da yini
daya suna ta rafka hushi da juna, babu inda su ke haduwa, kafin
ya iso ta kammala mai komi na abinci. Idan waya akai mai ko
yana falo sai ta hau sama ta kira Abdul ya sanar da shi. A kwana
na biyu kai kace gidan an yi mutuwa ne hatta yaran sun rage
walwala domin ada sun saba jin dariyar iyayen na cika gida.
A ofis yawancin wa'anda suka saba harka da Yusuf sun
ga canji amma abinda suka dauka kila wani daga cikin iyalansa
ne babu lafiya, ya kan zubawa hoton Kubra ido a ofis tunaninta
da sha'awarta su kan dame shi, wai me yasa ta doki Sa'adiya
har ta ja sanadiyar hushinsu? Yana jin griman kai akan shi ya
fara yi mata magana, yayin da matukar kaunarta da sha'awar
ta suka dame shi a zuci, ya rasa dabarar da zai bullo da ita, sai
ya lalubi waya ya kirata amma yana jin taushin muryata sai
kuma ya rasa abun cewa ya tsinke layin. Hatta jinin jikinsa da
fatarsa da hannayensa sun san sun yi wani rashi na 'yan kwanaki.
Ko da Hadiza ta dauki waya ba a yi magana ba aka aje
ran ta ya so ya raya mata kila Yusuf ne, amma jin zafin abinda
ya yi mata ta kawad da tunanin. Tana son Yusuf tana sha'awansa,
86
amma ita kam wannan rashin tarbiya ta yara shi ke damunta
wannan hushi da suke yi bata iya baccin kirki, a kullun ji take
kamar ta je dakinsa ta bashi hakuri amma na ta girmen kan da ganin laihinsa sai ta ji bata iyawa, lokutta da dama ta kan sami dalilin da ya dace ace sun yi magana domin hushin ya shige sai girman kai da miskilanci ya hana ta. Ko waya aka yo Yusuf ya kan ki dauka da gangan wai ko Kubra ta dauka tace wayanka
ce, shi kenan sun shiriya amma sai ta ki.
Akwai lokacin da aka yo ma Yusuf waya yana fale yayin da ta dauka a kicin amma don tsabar miskilanci ta:sige shi
kwance a falo ta je har dakin baccin yara ta tayar da Sa adiya
cikin magagin bacci har Sa'adiya na faduwa tace, je ki falo ki ce
ma Dady ya dauki waya. Wannan al'amari ya batawa Yusuf rai
amma tunda yana neman shiri dole ya kyale Kubra.
A ranar da suka wayi garin kwana uku ana wannan
badakar hushi, Yusuf ya kai iyakar galabaita ya kwadaita ainun
da Kubra, komi ya tsaya,mai cak sai sha'awarta kadai, inda duk
yake ya kan zauna shiru, yana neman hanyar da zai-yi magana
da Kubra, domin shi ma mutun ne mai shegan jin kan tsiya.
Yana ofis aka bada sanarwar akwai mitin na shuwagabanni
da karfe hudu na yamma. Yusuf ya koma gida kafin lokacin, ya
cimma Hadiza kwance da wani litafi wai Allura Cikin Ruwa kusan
kullun cikin karatu take shiyasa ta manta da bacin ran Yusuf.
Ya yi kokari ya tanka mata ya kasa amma sai ya samo
dabara ya rubuta mata wasika kamar haka, My Kubra,
Za mu shiga mitin karfe hudu na yamma, amma a yanzu
zan kwanta na yi bacci, don haka ki tashe ni karfe uku dai dai
don kada na makara.
Di Yusuf
Ya je ya aje mata bisa tebir inda ya san dole ta je wajen ta
gani ya yi baccin sama-sama yana son ganin shigowar Kubra don
ya ruke ta. Yana aje takarda ta duba ta yi murmushi, karfe uku
ta murda kofardakinsa a hankali itama ta aje mai wasika a tebirin
da ke gefrn gadonsa ta fice, Yusuf idonsa a kanne yana kallonta,
87
ya mika hannu ya dauki takarda ya ga amsarta:-
Karfe uku ta yi ka tashi kada ka makara.
Kubra.
Ransa ya baci ya mike a cikin hushi ya same ta, rike da
takardar yace, "Me ye wannan?" Ta dube shi tace, "me zan maka,
wanda ya fi amsa?" Ya zura mata ido na tsawon lokaci sai kawai
ya kankameta yace, "Kubra kada fa na mutu! Wallahi kwana
ukun nan na galabaita, zancen yara na gane kuskurena tabbas
ba irin tarbiyar da akai mana ba kenan, na amince zan ba ki
goyon baya amma don Allah a dai na duka ---." Ta sunne kai
bisa kirjinsa tace, 'Di wai ni za kai ma gorin bana sonka bayan a
gabanka uwata ta tsine min saboda kai, duk da haka ban fasa
aurenka shine ---."Ya kammala bakinta cikin nashi yace, "Nace
fa ki yi hakuri ni ne da kuskure na dauki wannan laihin." Ya lalubi
cingam din da ke bakinta ya mayas a bakinsa yana tauna, ya
janye daga gareta yana murmushi, yace, "yau kin biya ni cimgam
dina dana taba baki ada, idan kin tuna na taba ce ma ki wanda
za ki bani sai kin tauna! Kin ga a yau mun zama gamgam."
88
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu