Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 9
zan shawo kan ta ta hakura ta aure ni". Mallam ya dube shi kawai domin ya san zafin radadin irin wannan kaunar a zuciyar namiji, ya ce, "ba komi, komi na Allah ne." Ko da Yusuf ya koma Abuja bai da wani kuzari balle tunanin kirki duk Hadiza ta gama rikirkitar masa da komi da ya mallaka, ya yi ma Basiru kaninsa waya yace ya je maza Malunfashi ya zo masa da Saminu yana son magana da shi. Nan da nan Saminu ya zo ko babu komi Saminu cikin kudi ya ke domin a ranar da Yusuf ya je dubu biyar cif ya danna masa. Bayan sun gaisa ya ce, "Saminu ina ka ke jin Hadiza ta ke a halin 20 yanzu?" Saminu ya ce, "'Tana Kaduna yaya, ai ta koma aiki". Yusuf ya ce, "Kana da wayar gidansu da ofis?" Ya ce 'E' ya bashi har da ta Jos domin ya ce, Hadiza Jos ta haihu karshe za ta je Jos. Ya yi mashi kwatancen gidansu na Kaduna. Suna aje waya ya latsa wayar gidan Yaya Garba, wani yaro ya dauka yana jin an ce Hadiza a ke son magana da ita sai ya ce mata, "Anti Hadiza ga Baba Amiru". Ta je da saurí ta dauki waya ta ce, "Na yi hushi angona, haka mu ka yi da kai saboda Allah Amiru?" Yadda Hadiza ta rausayar da murya ta tsumar da Yusuf amma a lokaci guda kishi ya dirar masa wai Haidizansa ke ma Amiru magana mai dadi irin wannan? Kamar ya aje amma kuma bai iyawa, ya ce, "Ba Amiru ba ne, Yusuf ne. Kina lafiya?" Ta ja tsaki ta aje wayar. Hadiza na sauraron aiken Amiru ne domin ya yi mata alkawarin turo direba zai kai ta wajen taron sunan Hadizan Jos, to amma shiru a zaton ta shi ne ya yo waya ta dauka da niyyar ta yi masa tsiya sai ta ji Yusuf, to bayan ta dawo ta zauna sai kuma Amirun ya yo wayar ya na bata hakuri akan ta yi hakuri tafiya sai gobe, domin ya samu ya kammala `yan hidimomin gabansa ne don haka shi ne zai kai ta ba direba ba. Yusuf ya je ofis a washegari, ya rinka duba fayal-fayal don ganin irin ayyukan da ke gabansu, a kalla akwai zuwa Legos don shigar da wasu takardun kwangila da aka ba kanfaninsu na sa wutar lantarki a garin Zariya, haka nan akwai zirga-zirgar zuwa Kaduna kamar sau biyu a satin nan shi ma ana bukatar kula da kwangilar hanyoyin da kanfanin su ke yi, akwai son akai ma gwamnan jihar Kaduna wasu takardu don sa hannu suma na sabon shigar aiki ne. Yusuf ya ja birki daga nan ya ce, "Yauwa". Maganar zuwа Kadunan nan ita tafi damunsa domin wata dama ce da zai samu ta kusantar Hadiza ba tare da aikinsa ya raunana ba, ya mike ya nufi ofis din Shugaban kanfanin, ya gayas da shi bayan ya yi sallama. Yusuf ya shiga nuna mai mahimmancin kasancewarsa a Kaduna na tsawon lokaci don ya samu ya gudanar da wa`annan ayyukan da suka taso. Shugaba ya duba a tsanake sannan ya ce, "A lalle kam, bayan wannan ma akwai wata takarda da ta iso a 21 daga Kaduna za` a zauna mitin da gidan gwamnatin da kamfaninmu a sati mai zuwa don haka ina ganin kai ya dace ka wakilci kamfaninmu, saboda haka duk sauran maganar shiryeshiryen maganar kudaden tafiya sai ka sami Yakubu akawuntanmu sai in ce sai mun ji waya ko kuma ince sai Allah ya dawo da kai lafiya". Yusuf ya ce, "zan yo wayar domin ta yiwu wani abun ya taso daga baya." Ya isa gida ya yi sallama da su Falanke ya kara jaddada ma Falanke cewa kada a kara barin wata 'yar iska ta shigo mai gida. Falanke ya ce, "Haba Yallabai tun yaushe wannan ta kwaranye mu dai addu'ar mu Allah Ya bamu Hadiza a matsayin matar sunna". Yusuf aka yi murrmushi aka сe "To Amin, mun tafi farautar aure sai mun dawo." A gidan Baba Garba babu kowa daga Hadiza sai mai aiki sai ko mai gadi yana can bakin get. Hadiza ta ci kwalliya amma a saukake kwalliyar matafiyi yadda ba zata wahala ba, jefi-jefi ta kan dan dubi agogon hannunta ta na zargin Amiru da son ya ja masu tafiyar dare. Yusuf ya isa gidan Baba Garba ya rubuta ma Hadiza wasu "yan maganganu na rokon arzikin son ya ganta, maigadi ya kai mata wasika har gabanta ya fadi a zaton ta ko Amiru ne ya kara aikowa yana bada hakuri, to sai tagaYusuf ya rubuto ta ja tsaki ta tsaida maigadi ta rubuta masa amsa kamar haka Yusuf Ni Hadiza yanzu na manyanta a halin yanzu a gani na kuma wannan zamani na da zan sarrafa al'amurana na zabin aurena saboda haka ya dace na auri mutumin da bana so? Maigadi ya mika ma Yusuf takarda wani daci ya daki zuciyar sa, wai shi ko maye ne bai kyale yarinyar nan ne? Tabbbas ya san ya yi nacin son Fa'iza to amma itå Fa'iza bata nuna masa masifar kiyayya irin haka; nan da nan idanunsa suka yi jajur ya rinka ganin duhu har shi maigadin, yayin da ita kuma Hadiza tana can tsaye gindin taga tana kallon irin halin da Yusuf ya shiga da ta ga ya shiga motarsa ta saki labulen ta dan rintse 22 idonta ta ja tsaki ta ce,`shit kawai'. Ta kwanta bisa gado ta rinka tuno irin son da ta nuna masa a da anan ma ta kara tsanarsa. Yusuf na kokarin fidda motarsa daga gidan Baba Garba yayin da Amiru ke kokarin cinna tasa motar ciki, suka rinka huci na jirı zafin dayansu yayin da shi Amiru na jin zafin me ke kawo shi wajen Hadiza idan ba yana samun fuskar Hadizan ba ne? Yayin da shi Yusuf yana jin zafin wai kan wannan Hadiza ke muzanta shi? Tunda Hadiza ta shiga motar Amiru taga canjecanje da dama, ranta ya bata ganin da yai ma Yusuf ne, don haka itama sai ta share shi ta daure ta ta fuskar. Sun sami kimanin tafiyar awa daya da rabi, kafin Amiru ya dan juyo ya dubi Hadiza ya ce, "yaya kina son wani abu mu tsaya nan garin?" Hadiza kanta a sunkuye ta yi tagumi bata tsinka masa ba sai akwai ta girgiza kanta nuna alamuna'a, ta kara takurewa jikin taga, to anan ne kuma abinda rai ke so sai Amiru ya dan rikice ya yi yakace dama bai bullo ma Hadiza da hushi ba, ai fa sai ya shiga rarrashi, na tsawon lokaci amma bai shawo kan Hadiza ba. Amiru ya ce, "Amma a gaskiya Hadiza kin bani mamaki ca nike idan duniya da gaskiya nine da hushi, ki duba tsakanina da Yusuf? Amma kin hada mu kina gara mu kamar wasu 'yan yara, ai ni a zato na bai kamata ki rinka sauraron kowa ba, bama Yusuf kadai ba, haba Hadiza dlarajar da Allah ya yi wa mahaifinki kin fi karfin haka ya kamata ace duk wata hulda da wani namiji kin jingine ta." Hadiza ta ce, "zaka iya rantsewa akan yau Yusuf ya gan ni?" Amiru duk nauyin Hadiza ya lullube shi ta kara cewa "ka tabbatas tunda na tsayar da zancenka na sake kula wani da namiji? Duk shirmen Yusuf me ka ji ance nayi nuna alamun zubar da mutuncina? Dan Allah Amiru idan za'a zarge mu a rinka jiran ana kama mu dumu-dumu amma ban da zargi, domin ni dai ma'aikaciya ce idan mun fara samun irin haka kaga ba karamar matsala zargi zai haifar mana ba a rayiwar aurenmu. Amiru ya ce, "To don Allah wannan ta shige haka nan, 23 wallahi sanin halin Yusuf na yi shegen mutum ne, duk abinda ya kallafa rai yana so sai yaga bayan sa. Hadiza ta juyo ta dubi Amiru ta ce, "Ba dai komi ba me ya hana shi auren wadda ya mutu yana ciwon so Fa'iza?" Amiru ya ce, " ai lokacin da shirmen kuriciya bai kai munzalin da dabararsa zata mallaka masa komi ba". Hadiza ta ce, "gaskiya ban yadda da kai ba anan ai idan mutum jarumin namiji ne ya dace ace da kuriciyarsa ya nuna kwazo ya amshe ma wa'anda suka fi shi mata." Amiru ya janye hannunsa daya daga kan sitiyarin mota ya shafa kansa ya ce, "Ai shi kuma aure ba haka ba ne Hadiza na Allah ne yadda duk ba ki tsammani haka yake faruwa, yanzu ba gashi da can da Yusuf zaku yi aure amma Allah bai yi ba, a wancan zamani babu irin lallashin da ban yi masa ba akan kada ya kyale ki amma ya ki, cikin ikon Allah sai gashi Allah ya hada mu zamu yi aure." Hadiza ta shayar da Amiru mamaki ta ce, "tsakaninka da Allah idan ka ganni a zamanin da Yusuf ya ki aure na zaka iya aure na?" Amiru ya ce, "menene na wannan tambayar?" Ta ce, "haka dai na tambaya don Allah fada mani?" Ya ce, "sanin gaibu sai Allah! Suka yi shiru cikin motar kowanne da tunaninsa, tabbas Amiru ya tuna hotunan Hadiza tana 'yar shekara shabiyar wanda Yusuf ya taba nuna masa ko kusa bai taba tsammanin za`a sami sambaleliyar mace ba kamar wannan. Da yamma likis suka isa gidan Baba Rilwan gida kam ya fara cika da`yan suna na murnar diyar da Hadizan Jos ta haifa gobe ta ke suna. Amiru ya ce, "To Hadiza ki gayas man da maijegon sai na zo da yamma ni zani in nemi masaukin kwana. Ta ce, "To sannu o, Allah huta gajiya". Ya dube ta su kai murmushi, abinda ya fi damun Amiru shi ne Hadiza sai kodewa ta ke yi ta rame ta yi fari fat abinda da ya dauka rasuwar mahaifinta ne, to amma ya san matsalolin Hadiza sun fi karfin kidaya sai du'ae kawai. Ranar suna aka radawa jaririya sunan Mama Binta wato Fatima. To Hadiza ta sami kanta cikin rashin hutu ranar suna Ja 24 washegarin suna domin duk kawayensu ita ke kula da su haka nan Dr Sani ya dora mata nauyin yawancin hidimomin sa da kula da jama'arsa. Saboda haka ma ko da Amiru ya zo ranar suna a tsaitsaye ya ga Hadiza da mai jego amma sun karrama shi ta fannin abincin suna da kayan kwalan na suna, su kai sallama ya ce zai tafi Lagos sai kuma bayan sati biyu su hadu a Kaduna. Kashegarin suna Hadiza ta shiga kintsa ma mai jego kayanta da ta samu suna kara tantancewa. Maijego ta roki Hadiza don Allah ta kara kwana kafin ta wuce Kaduna, itama Hadizan ta amince domin rudanin da ke kanta duk ya sukurkutar da ita, tun tana daukar Yusuf wawa bata da lokacin sa shirme ya ke, to yanzu ko al'amarin sa ya fara tayas da hankalinta, don haka ne ma ta yanke shawarar idan ta koma Kaduna zata shirya ta je Bakori ta yi ma Inna Tambai bayani don ta je ta yi ma Gwoggo Halima magana saboda a tsawata masa ya fita hanyarta. Yusuf a Kaduna yana ci gaba da gudanar da ayyukan ofis din su, kullun ya sami sukunin tunanin Hadiza babu abinda ya fi bata masa rai irin wasikar da ta rubuta masa, anya Hadiza ta iya tabbataswa kanta cewa bata son shi? Ya nemo takardar ya kara karantawa ya-yi mata kyakkyawar nazari sai ya ga ma ashe shirme ya ke yì, wannan takarda na bukatar a kara tattaunawa. Da yamma ya shirya ya nufi gidan Baba Garba don ya ga Hadiza. Maigadi ya ce ai ta je Jos bata dawo ba, Yusuf ya nemi ganin matar gidan, aka shigar da shi falo ta tabbatas masa Hadiza na can Jos suma yau suka dawo. Ya ce, "Ita fa sai yaushe?" Ta ce, "Ba na iya cewa domin na je maijegon na cewa ta kwana biyu a can". Yusuf ya yi shiru sannan ya ce, "Don Allah a yi min kwatancen gidan Baba Rilwan". Ta ce, "idan ka je Jos ka san dai jami'ar Jos ba boye take ba, kana isa get gidajen Malaman zaka iya hangen wani sabon gida zaboda ba su fi wata biyu a cikin sa ba, to nan ne gidan Baba Rilwan." 25 Karfe sha daya da `yan dakoki Yusuf ya sauka gidan Rilwan shi da direban Kanfaninsu, su Hadiza sun koma daki kanan sun raka Dr Sani zai koma Abuju, Mama Binta ta aiko wai su je falon baki ga Yusuf can na san ganin su. Hadizan Bakori ta dafe kirji ta dubi `yar Jos ta ce, “Ke da gaske ne fa wasu mutanen suna da maita a cikin jikinsu, to na yadda shi dai Yusuf yana da maitar, kin ga wasikar da na rubuta masa kuwa ina nuna masa a shagube bana son sa amma wai kin ji mayen ya biyo ni har Jos, to ba zai ganni ba, ya gaji da zamansa ya tafi, Hadizan Jos ta ce, "Tafdijam! Ai wallahi sai mun je Yusuf din da na ke ji kamar na je har gaban mahaifiyar sa na ci mutuncinsa ace yau ga shi a gidanmu ba zan je na fada mai maganganu ba wannan shi ne kuma karya!" Murna da dadi suka kama Hadizan Bakori domin ta sami mai yi mata maganin Yusuf yadda zai daina zuwa gareta. Suka shirya don zuwa falo, abin mamaki har Mama Binta ta shirya masa abinci an kai masa ya ma gama cì, shi ma direbansa yana can waje an kai masa. Hadizan Jos ce a gaba yayin da Hadiza ke bayan ta rungume da Fatima an nade ta cikin tawul amma idonta biyu. Ya amsa sallamar Hadizan Jos yana mai murmushi ya сe "Kar dai ace min ke ce mai jegon, lalle godiya ta tabbata ga Sarkin halitta da ya sauke ki lafiya ga ki tangaran-kamar ruwan sama, wannan ina baki shawara kanwata idan kin tashi komawa gidan Dr. Sani sai ya baki sabon sadaki domin na sabon amarci". Haba nan da nan `yar Jos ta kyalkyale da dariya ta ce, “To na amince kai ne mai amsar mani tunda kai ne yayana" Ya mike ya nufi Hadizan Bakori ya cę, "Masha Allah bebin kenan? ya amsa cike da murmushi ya koma ya zauna ya dade yana kallon Fatima ya sha mur ya ce, "A duniya yauşhe rabon da na ga jariri ma kyau irin wannan? Ya Allah! Ya Allah!! Ya Allah!!! Ka ba ni irin wannan kyakkyawar jaririyar nan da wata tara!"`Yar jos ta kyalkyale da dariya ta ce, "ka san ko abinda ka ke fadi, nan da wata tara fa ka ce! Don Allah ka kara watanni". Ya kara zubaw 26 aririyar ido ya ce "Ai ni idan ma zata rayu ban ki ba a haifar min ko nan da wata biyar ne kanwata". Ya kai fuskarsa daidai kumatun Fatima yana sumbatarta ya dago ya dubi su Hadiza da Hadiza ya ce, "Kin gama ma Dr. Sani komi Hadiza". Hadizan Jos da Yusuf suka kyalkyale da dariya tace, "Ashe haka kake, gaskiya ba ka da dama". Suka shiga yi ma juna bayanan anguwarsu a can Abuja Yusuf ya fara kwatanta mata gidansa ya ce ya san kanfanin Dr. Sani amma bai san gidansa ba.Yar Jos ta ce "Ni ma na gane naka gidan inda teloli suke, wa` anda sun fi yin'aikin hannu, na taba raka Dr. amma na zauna cikin mota domin maza sun fi yawa a wajen". Yusuf ya yi dariya ya ce,."Yes, kin gano gidana kenan." Tunda suka shigo falo Hadizan Jos ta canzawa `yar Bakori yayin da`yar Bakori ta sha mur tana ta hararar`yar Jos akan ta daina yi ma Yusuf dariya ta shiga zaginsa kawai. Fatima ta shiga rigima tana dan korafin kuka, Yusuf ya yi galala yana dubar su Hadiza ya ce, "To kun ga fa inda za ai rikici da ni ban san yadda ake rarrashin jariri ba, domin sai na ga tamkar zan matse shi". Ya mike ya nufi Hadizan Bakori da Fatima ya mika mata, ya ce, “Ga ta Gimbiya". Yana murmushi yayin da ita ta sha bula, sai ta rungume Fatima a kirjin ta tana riritata nan da nan ta yi shiru, sai Hadizan Jos ta mike ta ce, "ina zuwa, bari na kawo mata ruwa na canzó mata hula kila wannan ta yi mata nauyi." Bayan tafiyarta an yi `yan mintoci Yusuf na kallon Hadiza da Fatima babu abinda ya ke yi sai addu` a Allah ya bashi Dije ta haifar masa kamar Fatima. Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ranki shi dade, ina gajiya? Ta dago kai ta galla masa harara ta ce, "Wai me ya kawo ka nan, ba ka ga abinda na rubuta ma ba ne?" Ya yi dariya yace, "Oh yes! Na ga ni mana, ai shi yasa na zo don muyi shawara, ina fa zan yadda ina matsayin yayanki ki auri wanda ba kya so?" Anan kuma ya saki layin wasa ya sha mur ya ce, "Don Allah don Annabi Hadiza kin galabaitar da ni, kin wahalad da ni, na 27 azabtu na shiga halin da ban taba zatun diya mace zata sáka ni ba, duk a dalilin dan kuskure kalilan, ki yi hakuri (anan sai ya mike ya isa gabanta ya durkusa gwiwa bibbiyu) yana afi da hannuwa yana hada ta da girman Allah, ga kwalla taf da idonsa itama Hadiza anan taji jikinta ya yi sanyi karara, ta tuno irin matsayin Yusuf a gidansu yadda mahaifiyarsa da kannansa ke ji da shi, amma a yau gashi tsugunne gabanta yana kuka yana mai rokonta. Idonta ya kada ya yi jajur ta dubi Yusuf ta ce, "Wallahi Yusuf ban rike ka da komi ba, domin ai ka so ni lokacin da na ke shan wahala Allah ne bai yi aurenmu ba sai dai a gaskiya wallahi ka ji na rantse bana iya fasa auren Amiru a wannan lokacin". Har yanzu Yusuf na tsugunne ya ce "Hadiza don ba kya so na kin fi son Amiru ko?" sai kawai Hadiza ta sami kan ta tana jin tausayin Yusuf amma kuma tace mashi, “E to„ba wai bana son ka ba ne, ai kai ma na so ka a lokacin da na so ka din, yanzu kam gaskiya Amiru na ke so". Wasu kwalla suka sake taruwa a idon Yusuf ya fiddo hankicinsa ya goge idonsa ya yin da kwayar idon ta yi jajur, a daidai nan ne Hadizan Jos ta iso da niyyar kawo ma diyarta ruwa amma ganin Yusuf na tsugunne a gaban Hadiza vana kuka, sai ta ja da baya ta koma daki. Yusuf ya koma ya zauna dirshan a gaban Hadiza sai gugar kwalla ya ke mata, ya ce, "ina son na ga Mama ta nan gidan". Hadiza ta mike da sauri ta fita, daman zaman ya gallabe ta, yaya zai tasa ta ya rinka yi mata kuka ita lokacin da ta yi nata kukan rashinsa yana ina? Ba yana can ya sami Fa`iza ba, to itama yanzu ta sami Amiru don haka kada ya matsa mata. Ta sanarwa da Mama sakon Yusuf sannan ta cimma Hadiza a daki ta kwantar da Fatima ta koma inda Hadiza ke kwance ta zauna, ta dubi`yar Jos tace, "A gaskiya kin ba ni kunya wai duk bakinki da irin tsiwarki amma wai ki ka kasa ce wa Yusuf komi sai ma wani gatanci da ya samu wanda ban ga Amiru na ya samu ba". Hadiza ta tashi zaune 'ki vi hakuri, ni kai na nayi mamakin yadda na yi ma Yusuf, saboda na tsane shi a bisa 28 labarin da ki ka bani, to amma ina shiga falo yadda na gan shi sai na ji duk na sare domin kwarjininsa da barkwancinsa ya fi karfin a yi mai wulakanci. Na san a da Yusuf ya yi laifi to amma yanzu Hadiza ki tausaya masa, ki duba fa har tsugunnawa ya yi bisa gwiwowinsa yana kuka? Haba! Hadiza ai namiii irin su Yusuf komi su kai idan har $un gane kurensu sai a yafe masu haka nan, wallahi yadda ya tsugunna a gabanki ba don kuka ya ke yi ba ni kam yau da na dauke ku hoto da sauran fim din Fatima, kin ga irin kyan da ku ka yi kuwa? Kai Hadiza ke da Yusuf Allah ya yi ajiyarsa!" Hadizan Bakori ta daga kai ta dube ta ta ce, "kina da hankali kuwa? Kin manta an tsaida min miji Amiru?" Hadiza ta ce, "Na fi kowa sani, amma in gaskiya ta zo a fade ta, haka nan kuma sau nawa ake sa rana a warware wani lokacin ma ana gobe za'a kai amarya gidan miji ake canza mijin" Hadiza ta cе, "Tunda ba'a yi akan ki ba, insha Allah ba za`a yi akai na ba, su Fatima ga su can gidan Amiru". Suka dade suna kallon juna sannan suka kyalkyale da dariya. Hadizan Jos ta ce, "Tafdijam! Ina ganin Bakatsine ba na auren Bakano, sadda duk miji zai saka hulà sai dai kiga (birki kunne) haka nan za su ranbadawa idanunsu kwalli bajau wa ya aike ni!" Hadizan Bakori ta dingi dariya har tana kwantawa ta ce, "Wai ya ake sa hula birki kunne kuma Hadiza?" Ta ce, "Idan Amiru ya zo ki dube shi tsab za ki gani, amma kin hada da su Yusuf gogaggun Katsina idan an saka hular nan a murza ta sai ta kusa danganewa da gira, ke komi na Bakatsine fa daban ya ke, idan har an sami tsantsar Bakatsine za ki same shi da daddadan lafazi mai tsima jiki da kashe kwanya sannan ga kyan iya shirya lafazi yadda zai shigi bil adam, sai kuma wata baiwa da Allah ya yi ma su na kamun kai, wanda shi ne ya haifar da wata ilhama ta kwarjini na musamman a gare su, to kin ji dalilin da yasa Katsinawa su ka yi zarra, amma fa ba su danne `yan Bauchi ba domin suma sun hada yawancin abinda Katsinawa suka tara, ko kin san duk Nigeria ba wanda ya kai jama'ar Bauchi da Katsina mulki irin na 29 Kuma sun iya domin irirn jininsu kenan. Hadizan Bakori ta ce, "kai Hadiza da dai Dr Sani ba dan Katsina ba ne, sai na ce ya ba ni da bakin ki, to Allah ya taimakeshi ya fito daga jiharku ta Katsinan. Ni kam ina kin Yusuf ne a dalilin ina ganinsa a namiiin zara irin su ne a kullun suka hango abun sha'awa jikin wata za su bar ka zuwa gare ta".. Ina son kuma ki fahinci abu daya a wajen Kanawa kamar yadda ki ka fahinci Katsinawa wato a duk kabilar arewa babu masu ladabi da biyayya da sanin ilmin Islama kamar 'ya'yan Kano daga nan sai`ya`yan Maiduguri, in da duk Bakano ya ke yana girmama na gabansa, haka nan bai iya saba maganar iyayensa ko yaya take, sannan za ki same su cikakkun mutane masu sana`ar gado tun suna `yan kanana, amma kin hada da yaranmu na jihar Katsina yawancinsu sun faye girman kai da nuna isar ba a isa ba, da sauransu, to kin ji abinda ke ba ni sha' awa da halayyar kanawa. A can falo kuma Yusuf ya yi zaman dirshan bisa kafet gaban Mama Binta ya fi awa daya yana kashe ta da lafazinsa masu dadin sauraro, ya ce, "Wallahi Mama ina tausayin kaina ina tausayin Hadiza domin yadda na ke sonta itama ni kadai take so, to kin ga na kyale ta ta cutu akan wani jin kai da kunya?" Mama ta ce, "E to sai na yadda da kai anan domin zurfin cikin Hadiza yawa ne da shi, duk yadda ka ke da ita da wuya ka san abinda take so ko wanda bata so, haka nan mu dai tunda muke da ita a gidan nan ba mu san ko me ke bata ran Hadiza ba." Yusuf ya gyara zama ya ce, “To kin san Allah daya ne Mama, duk duniya daga ni sai Baba Kado wato mahaifinta muka san cikin Hadiza da bai dinta, yanzu idan da yana da rai tabbas ya san tafi so na fiye da Amiru babu tantama ba zai tsaya sauraronta ba zai umurtai ni na ci gaba da shirye-shiryen biki, yanzu haka idan zan aika na kira ta zata zo, illa dai zata rinka fada min maganganun wulakanci amma idan na dubi kwayar idonta wani zubin zan ga ba har cikin zuciyarta take min ba, sai dai saboda jin dacin abinda na yi mata, na kuma tabbatas idan da 30 ni ne aka sa mana rana babu yadda za ai ta fito wajen wani idan ya kira ta." Mama ta ce, "Lalle Yusuf dole ne ka nace domin ba a san rabo ba, ni dai shawarar da zan baka shi ne tunda ka fahinceta a hakan, to sai ka koma can Bakorinku ka nemi daurin bakin su Inna Tambai da aminan Babanta domin sanin kan ka ne, a duniya Hadiza bata da uwa kuma aminiyar shawara bayan Inna Tambai, sannan kuma tafi son Babanta fiye da komi na duniya, idan ka sami amincewarsu ina gánin za su shawo maka kan Hadiza." Yanzu a duniya Yusuf ji yake bai da masoya irin Saminu da Hadizan Jos da Mama Binta. A ran nan ya koma Kaduna kashegari ya yi ayyukan kanfaninsu da dama ya yi sa` a daya daga cikin wa`anda ke da alhakin mallakar kanfanin ya na nan ya je Kaduna, ya yaba da aikin da Yusuf ya gudanar har ya nemi Yusuf da ya zo gidansa da yamma, gaban Yusuf ya fadi ras domin a niyyar Yusuf so ya ke da yamma ya nufi Bakori ya kashe su Inna Tambai da Baba lliya da dadin bakinsa, amma sai ya tuna aikinsa na gaba da komi, idan babu aikin nan matar ma tsanarka ta ke. Ya cimma uban gidansa da karfe tara daidai na dare sun yi rubúce-rubuce har zuwa karfe biyun dare akan kanfaninsu. To a lokacin ne Yallabai ya lura ba haka Yusuf ya ke ba akwai dai wani abu a kalkashin ransa, yana tambayar Yusuf bai tsaya wani kawaici ba ya warware mai irin damuwar da ke cin sa a rai, nan da nan Yusuf ya fara kawo kwalla ya ce, "Yallabai ni na san na yi kuskurena amma yarinyar nan ta ki hakura, ga shi abin haushi wai abokina na kut

Chapter 3 of 9