An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
KOWA YA RAINA
TSAIWAR WATA
3
Bilkisu S. Ahmad
Funtuwa
Wanshekare ran asabat da sassafe katon din madara da
na suga da gwangwanayen bonbita, sannan gaba daya but din
motarsa an danno shi da biredi dan bisije, wannan saye-saye
Yusuf ne ya aiki Falanke da direbansa har garin Funtua aka sawo,
ya ce akai gidan marigayi Baba Kado. Haka nan ya bada sakon
kaji hamsin da shinkafa da kayan miya ya baiwa Gwaggo Halima
ya ce ta girka akai sadaka gidan Baba Kado. Da la'asar sakaliya
kuma ya aiki Falanke ya amso inda ya kai gashin rago shi ma ya
ce akai sadaka gidan Baba Kado, yadda ya rinka aikawa kuwa
da lemon kwalba kuwa ko bikin diyar manajan kanfanin lemo
sai haka.Wannan abubuwa da Yusuf ke yi bai daurewa kowa kai
ba domin an san matsayin Baba Kado a wajensa, illa dai kawai
zargi na mutane da ba'a hana su.
Abinci kam gidan Alhaji Kado ko bikin Amiru da Hadiza
za'a yi iyakarshi kenan, almajirai su kam kamar sallah a wajensu
,haka nan gidan ya kara samun jama'a yan zarnan makoki
albarkacin abincin da ake ci. Jama'ar Hadiza na wajen aikinta
sun zo yi mata gaisuwa haka nan Rilwan da iyalansa sun zo
dagaJos hatta Yallabai Mamud da ya sami labarin rasuwar.
Ya gaisa da kungiyar su Amiru da Yusuf inda suka yi
shinfidar su can nesa da ta dattawa, ya so kwarai anuna masa
mijin da Hadiza zata aura amma hakan bata samu ba.
Amiru ya fara tsarguwa lalle abubuwan da Yusuf ya ke yi
a bisa dalilai uku ya ke yin su: na farko matsayin Baba Kado a
wajen Yusuf sai na biyu saboda Hadiza sannan na uku a daliiin
shi Amiru amininsa. Wa'annan abubuwa sun taru a lokaci guda
sun rudewa Amiru, duk yadda za'ayi Hadizan shi itace ainihin
Dijen daYusuf ya guje mawa saboda son Fa'iza, Dijen da ya
muzanta akan wai bata da fasali, shin in ko haka ne itama Hadiza
ta rufe masa gaskiyar labarinta, domin cewa tayi dan`uwanta
ne ya guje ta a dalilin ta yi masa kankanta, me yasa Hadiźa ta
sakaya wannan lamari a gareshi? Ya yi sauri ya kawad da zarginta
a zuciyarsa ai dole ne ta sakaya har yaushe za ta fada masa
wannan fallasa da Yusuf ya yi mata?Abin damuwa dai daya ne
anan shi ne Yusuf wannan rawar kafar da ya ke yi akwai abinda
ya ke so, don sai ya yi takatsantsan da shi, kai amma Yusuf zai
1
iya mai cin mutunci irin haka don ko budurwa suka gamu da ita
duk irn yadda ta burge Yusuf da zarar Amiru ya nuna sha'awarsa
shi kenan Yusuf ya haranta ta. To amma rudin da ya ga Yusuf
ya shiga a tun daren jiya da ya ga Hadiza abin na tada hankalin
Amiru.
A cikin gida kuma suma su Inna Tambai abinda suke ta
kiyastawa rayuwankansu kenan, da wacce riga Yusuf ke wannan
irin wannan hidima ?Yayin da bai iya minti ashirin a waje sai ya
shigo cikin gida ya leka dakin da Hadiza ta ke ya gaishe su.
A tun daren jiya da akai rasuwar Gwaggo Halima ta ke
zuwa amsar gaisuwa haka nan da zarar ta gama abinci ta kan
shiryo ta taho.Duk da dai yanzu zumuntar ta su ta yi sanyi tun
batawar Yusuf da Dije sai su kashe shekara ma ba su nemi juna
ba hatta lokacin bikin su Hassi da Sarai ko da Halima ta kai
ma Tambai goro bata je ba sai dai ta kai mata abin hasafi.
A yarda aka shirya ran lahadi da la'asar su Yusuf da
Falanke za su koma Abuja yayin da Amiru zai zauna anan gidan
Yusuf har sai an yi sadakar bakwai to amma zumudin Yusuf da
irin yadda ya ke nuna maitarsa a fili sai duk Amiru ya rinka
zarginsa. yi A daren asabat din bayan Amiru ya kira Hadiza don su
sallama, sun gama sallamarsu a natse har sun shiga mota sai
Yusuf ya tsayar da su ya ce "don Allah su jira shi yana zuwa
minti biyar"ya koma cikin gidan su Hadiza ya leka har dakin da
suke zaune ita da Inna Tambai da Yaya Amina da bakin mata
guda biyu da suka shiga a lokacin gaisuwa, ya ce, "don Allah
Hadiza zo nan minti biyar". Ta mike ta fito ba tare da sa ma
ranta komi ba.
Suna tsaye a filin daga shi sai zaure, ya kara kallonta sannan
ya sunkuyad da kai, ga dai Hadiza da ya kwana ya wuni tunani a
gabansa,duk wata kalma da ya ke tunanin fadi mata ya san ba
za ta yi tasiri ba, domin wannan ba Dijen da ba ce, in ma da hali
zai iya cewa wannan babu wani wayon da zai iya nuna mata a
halin yanzu.
Ya cije ya daure ya ce, "wallahi ban san wai Baba ne ke
kwance a asibiti ba, me zai hana ni zuwa gaishe shi?" Ta daga
ido ta dube shi kawai, sai Yusuf ya ji gabansa ya fadi domin
2
idanun Hadiza sun canza mai, ba kowacce mace ke da irin wannan
idanun ba, a karo na biyu yá sake wata rashin kunyar ya се,
"Amma ke ma Hadiza ba ki san ni ne Yusuf din da ki kai ma
waya ba?" To anan sai Hadiza ta sha mur ta ce, `wai me wannan
mutumin ke nufi, yana tsammanin ta na da lokacin shi ne har
yanzu duk da dai bata san shi din ba ne amma bari ta gwasale shi
taga sai me?' Sai tace, "ina ruwa na da sanin kai ko wanene, ni
kam na yi maka waya ne a bisa bin umarnin mijina Amiru!" Nan
da nan wani gululu ya iso wuyan Yusuf amma sai ya tokare shi
ya tuna wannan ba irin`yan matan da su ke zagi ba ne, ya gyara
kurensa ya ce,
"To Hadiza ni kam gobe zan koma Abuja Ubangiji Allah ya
gafartawa Baba halayyarsa na kirki Allah yasa sun bi shi, Allah
ya kara hakuri". Anan sai ta dan saki ranta tace, "Mungode,
mungode Allah ya saka da alhairi a bisa dukkan abinda akai
mana."
Kafin ya ce wani abu ta juya zuwa cikin gida. To wannan
shi ya kara sukurkutar da Amiru da suka isa gida sun jima ana
hira da su Falanke amma sai Yusuf ya nufi can gidansu wajen
Gwoggo Halima yana ta raragefen hirar Hadiza amma dai kunya
da jin nauyi sun hana ya tambayi Halima ainihin labarin Hadiza
abinda ya ke son ji. Ita kanta Gwoggo Halima ta zargi Yusuf na
Cıkin yanayin damuwa amma sai ta dogara damuwarsa akan
rasuwar Alhaji Kado domin'sanin shakuwar da ke tsakaninsu.
Abu daya mutuwar Alhaji Kado ta kawo mata, wato ta janyo
mata Yusuf domin ta fuskanci hankalinsa ya dawo gida tamkar
da, saboda yaushe rabon da ya zo ya zauna su yi hira irin ta
wannan zuwan? Har ta manta, a koyaushe ya zo yana can sabon
gidansa duk lokacin da zai zo gare ta cikin sauri don kawai kada
ta yi mai fadan aure.
Gwoggo Halima ta dago kai ta dubi Yusuf yayi wani zama
rashasha kamar wanda aka zare ma lakka duk yadda Allah ya
halicce shi ya saki sharaf. Ta ce, "idan ка кoma Abujan kuma sai
vaushe?" Yusuf ya sa hannu ya shafi hancinsa ya ce, "Ina
tsammanin ha zan dade ba zan dawo, kiia ma nan da sati biyu." Gwoggo Halima ta ce. "ai gara ku je ku kwanta dare ya yi ga
tafiya a gabanku gobe."
3
Ya mike yana rangaji ya nufi motarsa ya ja va nufi gidansa
,anan ya cimma su Amiru da su Falanke ana ta hira ya jima
cikinsu amma bai iya cewa komai babu abinda ke azazzalal
zuciyarsa sai yadda zai amshe Hadiza hannun Amiru tabtas
mutuwar Baba Kado tamkar shi kadai akai mawa, domin idan da
ya na da rai a yau yaje ya same shi ya ce, atabau shi Dijen shi ya
ke so, to lallai ya yi imani Baba Kado zai rushe maganar Amiru
ya ba shi. Wannan tunanin ya kara tsinkar masa da jijiyoyi, dole
ne ya nemi hanyar da zai san inda Hadiza ta ke zaune a Kaduna
haka nan ya nemi lambar wayarta, idan ya sami wannan zai yı
abubuwansa cikin sirri kenan.
Wanshekare ran lahadi kenan bayan sun je anyi addu'a da
su, Yusuf ya riga Amiru dawowa ya bar shi a can saboda haka
yana isowa bai tsaya ko ina ba sai dakin da ya sauke Amiru ya
fara kwance masa jaka zuwa akwatinsa neman cikakken bayanin
Hadiza, me zai faru? Amiru ya dawo don ya dan kwanta ya
huta, amma sai ya cimma Yusuf a dakin da ya zan nan ne
masaukinsa duk ya yi kaca-kaca da hotunan Hadiza sannan yana
ta bincike masa takardu.
Amiru ya tsaya bakin kofa yana kallon ikon Allah yayin da
Yusuf ya yi kasake na rashin gaskiya na lokaci mai tsawo sannan
ya ce, "Amma ka ba ni kunya, me za ka nema wanda ba za ka
iya tambayata ba?"
"Tabbas na san bai shige al`amarin Hadiza ka ke nema,
kana zaton zan rubuta wayar mata ta a takardu ko adireshinta:
Ni ko wane irin dakiki ne da ba zan iya hardacewa a kai na ba?
Idan su ka ke nema, ka bani biro na rubuta maka, kana tsammanin
Hadiza wawa ce kamar kai da har za ta iya saurarenka? Ka tuna
fa kai ne ka ce baka aurenta don rashin fasalinta har dakin innarta
ka je ka fada? Amma ka ba ni kunya, kai ba amini ba ne, maci
amana."
Yusuf ya daga mai hannu ya ce, "Dakata don Allah Mallam,
maganar fa ta isa, sai ka gaya min waye ba ya kuskure? Na yi
kuskure kuma na gane kure na duk abinda za ka yi zan koma
neman Dije kuma insha Allah ni ne mijin Dije ba dai kai ba, komi
kake takama wallahi akan Dije na shirya."
Amiru ya ja tsaki ya ce, "Wawan banza, kada ka rinka
4
mantawa yau saura kwana ashirin da biyu Hadiza ta je dakina
duk wani abu na sharuddan aure na kammala tun mahaifinta na
da rai, abu biyu suka rage a sharuddan aurenmu da Hadiza su
ne sadaki, da shaidu su shafa Fatiha." Yusuf ya yi dariyar keta
ya ce, "ka san Allah Amiru abu daya zan iya raga maka shi ne
idan an daura aurenka da Dije, wanda Insha Allah hakan ba za ta
yiwu ba": Amiru ya ce, "Idan har ka cika shaidani ko an daura
mana auren ka amshe Hadiza in ka isa". Yusuf ya ce, "Ban iya
wannan shaidancin ba sai kai, mai raba miji da mata wanda kai
in ban da bin matan aure babu abinda ka aje". Anan ne fa Amiru
ya yi turus bakinsa ya bushe ya rinka kokarin tattara sauran
yawun da zai iya samu, sannan ya sa halshe ya lashe busassun
labbansa. La'asa sakaliya Yusuf da Falanke da dayan abokinsu
da direban Yusuf sun isa Kaduna har sun yanki hanyar Abuja.
Yusuf dai rungume da casbi yana wuridi bai iya cewa komi, sai
su Falanke ke surutunsu.
A gidan Yusuf na Abuja na`urar sanyi ta sanyaya ko ina a
gidan, a falo Suzi ce zaune rungume da kan waya suna hira da
kawarta shigar Yusuf ta aje wayan da sauri ta mike ta tarbe shi
tare da sumbatar kumatunsa ta ce, `You are welcome darling'
ya dan kauce mata ya amsa gaisuwar ta dakale ya ce, "Yawwa"
Duk hanyar da ta san tana jan hankalin Yusuf Suzi ta bi, amma
dai wannan karon bata shawo kan shi ba, data matsa mai da
tambaya sai ya harareta ya ce ta manta ne ya ce mutuwa aka yi
masa? Ta ce ta yi zaton sirikin Amiru ne; ya ce, `E kwarai kuwa,
ya gano shi kuma Babansa ne'; sai da ya ci abinci ya yi wanka
can da daddare duk `yan hira sun watse ya nufi (bas kwata) in
da su Falanke ke kwana ya iske Falanke zaune a daki yana sa
maballin wasu riguna da ya ke zaton gobe masu shi zasu amsa.
Yusuf ya yi sallama ya shiga Falanke ya ce, "Ranka shi
dade lafiya, baka aiko mai aiki ayi kirana?" Yusuf ya yi murmushi
ya ce, "Babu komi Falanke kammala aikin gabanka ka zo mu fita
waje magana na ke so da kai". Falanke ya ce, "Ai saura maballi
daya ya rage na kusa kammalawa".
Suka zauna a can wani bangare na cikin gidan Yusuf
Falanke ya yi kasake yana sauraron abinda Yusuf zai ce masa
domin shi ma ya damu saboda kwana biyu ya san Yusuf na cikin
5
wata matsala, addu'ar Falanke duk bata wuce Allah yasa dai ba
daga wajen aikinsa ba ne, domin Falanke yadda ya ke jin dadin
sana'arsa a birnin Abuja zai yi bakin cikin ace ubangidansa ya
sami matsala da zai bar aiki.
Yusuf ya ce, "Falanke a iya saninka ba ni da matsala da
mahaifiyata baya ga kullum kukanta akan na yi aure". Falanke
ya ce, "kwarai wannan nì zan ba wani labari domin ai ni take
aikowa wajenka akan zancen auren naka". Yusuf ya ce "To
madallah wallahi Falanke tun rabuwata da Fa'iza duk son wata
diya mace ya fita kai na, ba na ganin darajar kowace irin`ya
mace a duniya in ba mahaifiyata ba da kannena, a dalilin
tozartawas da na samu daga neman auren Fa`iza duk da dai na
san bata yaudare ni ba, amma ni na san da ina da kudi ba za ayi
min yadda a kai min ba a lokacin, sai dai abin mamaki a hankali
na rinka fahintar cewa babu wani don da na ke ma Fa`iza illa
sha`awa da kwadayi na tashen balagar kuriciya a wancan zamani
domin Fa`iza ta cika ta batsa yayin da Dije wadda zan aura bera
ce babu komi na cikar mace a tare da ita, ni kuma wata wautar
kuriciya ta hana ni na gane hakan, buri na kawai a lokacin na yi
auren sha`awa don na kawad da sha`awata in kuma kwantar
da kwadayina.
To ban fahinci so ba ban gane ma` anonin so ba sai idan na
tuno da kalaman da na kan gaya ma Dije da irin kalaman da take
gaya mani, to na kan yi sauri na kawad da wa` annan maganganun
na dauka shirme ne, amma yanzu gani na da Dije sai na san
matsayin so na amince ina son Dije so na hakika, son da babu
algus domin na nemi mata har ban san iyakarsu ba, amma wallahi
ban taba jin wadda na ke so ba, har na yi sha`awar aurenta a
zuciyata. Sai dai matsalar yanzu itace Falanke wannan Dijen da
na ke maka magana ita ce Hadizan da Amiru babban aminina zai
aura, diyar Baba Kado."
Falanke ya sa hannu ya toshe bakinsa ya yi shiru yana mai
girgiza kansa sannan zuciyarsa cike da al`ajabi, shi kan shi yana
mamakin Dijen da ya sani wadda ke tallar goro itace wannan ta
zama sai ka wanke hannu ka taba ta.
Ya dubi Yusuf ya ce, "Yanzu Dijenka ce ta koma haka
Yallabai?" Yusuf ya yi murmushi ya ce, "Wallahi ita ce, Falanke".
6
Falanke ya gyara zama ya ce, "To ai Yallabai sai an gwada
akan san na kwarai, kuma ma ai mata tafi amini, ba wai zan
hada ka da Amiru ba ne, amma gaskiya duk hanyar da za mu bi
ya dace mu bi ta ka amso matarka". Yusuf ya yi ajiyar zuciya
ransa yayi kal tunda ya sami goyon baya akan aurensa da Dije.
Ya ce, "E Falanke to yanzu yaya ka ga zan bi na shawo kan Dije,
ka san dai ba karamin tashin hankali ba ne, raba ta da Amiru da
kuma kuskuren da na yi mata tun farkon rabuwarmu, maganar
dai na rude ta da kudi wannan shirme ne, domin me za` a nuna
mata yanzu, ko shi Amiru ya yi kadan ta aure shi don kudinsa
ballantana ni, wanda na ke takama shi ne Baba Kado ya rasu".
Falanke ya ce, "Wannan duk haka ne, abinda za`a yi shi
ne ka shirya takarda ka rubuta ban hakuri duk wanda ka ke
iyawa, ni kuma zan je ran jumma` a na kai mata tunda shi Amiru
ran alhamis zai bar Bakori idan na dawo ran asabat muna iya
komawa ran lahadi, ko ya ka gani?"
Yusuf ya ce, "A`a ran alhamis za ka tafi, jumma` a zai ka
zo na ji yadda ku ka yi, domin na san ran alhamis da wuri zai bar
Bakori saboda haka na san ba za ku hadu ba."
Aka bar ta a haka ya koma falo ya cimma Suzi na nan na
jiransa, ya rungumeta suka nufi dakin baccinsa, sannan ne Suzi
ta yi ajiyar zuciya.
Yusuf ya fara aiki da kwarjini de daukaka sannan da iya aikin, har ya kai kaf a kamfanin kamar shi ne Babba saboda kwarjininsa da tsare aikin kuma babu hainci a bisa aikinsa а
dalilin hakan shuwagabanninsa ba su jin kyashin sakar masa dukiya don suna ganin ya cancanci hakan saboda kwazon da ya ke nunawa kanfanin.
Yusuf kafin ya ankara ya zama daya daga cikin sabbin
matasa masu tashen kudi a birnin tarayya Abuja, to` yan mata
kuma da suka kyalla suka hango motar zamani ga saurayi
matashi mai cikan halitta a ciki, sannan namiji daya da daya a
7
cikin maza, mai tsarin kyau na usili, ga cikar lafiya, tamkar don
shi kadai a ka shirya rayiwa a kullum cikin shi shar kamar jariri
sabon haihuwa, abinda ma ya fi birge mata akan Yusuf shine
kwarjininsa ai fa shi kenan ko bai je ba a zo masa, wannan ya
kara dasa tsanar mata a zuiciyan Yusuf va rinka ganin kamar
duk mata halinsu daya, ya zame masa canza mace kamar yadda
zai canza takalmin kafarsa.
A kullun aiken Gwaggo Halima ya zo ya yi aure amma shi
yana ganin auren ba dole ba ne tunda ga matan nan yana biyan
bukatarsa da su, da wuya Yusuf ya yi nema da hausawa sai dai
wasu kabilu daban. Yusuf kenan.
Amiru fa? Jirgi daya ya debo su da Yusuf a kullum fadan
da iyayensa ke yi kenan akan lokaci ya yi da zai aje mace, domin
duk kannansa sun yi aure sun hayayyafa amma shi ya ki. To
mararrabar Yusuf da Amiru daya ce: Yusuf `yan mata ya ke
nema yayin da Amiru shi kam sai matan aure, ko mi mutuncin
auren mace muddin Amiru ya kyalla ido akan ki yana so sai va yi
yadda ya nemi ki, da zarar kun yi nisa da nema zai ma ki alkawarin
aure to da kin kashe aurenki shikenan kin zame wà Amiru jidali
zai fara gudunki sai kuma a shiga rayuwar wani gidan (Allah ya
shirye mu, amin)
Wa'annan samari biyu`yan fitina su ke son diyan Baba
Kado da aure, (kamilallah Hadiza).
KASHI NA GOMA SHA UKU
Ranar alhamis da sassafe a ka taru a kofar gidan marigayi
Alhaji Kado akayi masa addu`a, a cikin gida ma haka, sannan
ga abinci nan kala-kala an dafa a ka rinka bayas wa sadaka.
Misalin karfe goma na safe Amiru ya shiga har dakin da
su Hadiza su ke, ya same ta ita da Inna Tambai da su Ankudi ya
ce, "To Hadiza Allah shi kara mana hakuri Allah ya jikan Baba"
Aka amsa gaba daya "Amin Amiru Allah ya saka maka da alheri
kuma Allah ya ba ku`ya`yan da zasu jikanku haka."
Amiru kan shi a sunkuye hannunsa na bisa yatsansa na
8
kafa ya ce. 'Amin, to zan koma Kano a yau ina fata babu komi?"
Hadiza ta dago kai ta ce, "Ina son ka aje mu gidan Inna Tambai
zan kwana biyu can kafin na shige Kaduna, saboda a gaskiya
bana iya ci gaba da zama anan dakin Baba, sai in ta ganin kamar
zan gan,shi". Su Ankudi a ka yi narai - narai da ido suka ce,
"Haba Dije bayan kin gina mana gida muna ta jin dadi kina debe
mana kewa kamar Alhaji na nan, kuma za ki bar mu?" Hadiza ta
ce "A'a Gwoggo kada ku damu zan rinka zuwa". Inna Tambai ta
ce, "Kun ji shirmen naku ko, me Hadizan zata zauna ta yi maku,
wadda zata gidan mijin ta kwanan nan?"
Amiru ya kara jin sa` ida cikin ransa ya dan muskuta ya
gyara zama, amma kuma sai Inna ta ce,Af, Amiru daman
akwai sakon da zan gaya ma, a dalilin wannan rasuwa da ta
gitta, a jiya ni da Mallan Hiya da Hadiza mun sake shawara akan
ranar bikinku an daga mun mayas ranar da za'a yi arba'in din
marigayi Alhaji saboda, ka san bikin ba zai yi armashi ba daga
rasuwa a kama shagalin biki."
Amiru ya ji zuciyarsa ta buga dam, babu halin ya nuna
wata alamar cewa ya damu, domin nuna damuwarsa tamkar
nuna bai damu da bacin ran Hadiza ba kenan na game da rasuwar
mahaifinta ya ce, "Allah dai ya jikan Baba", aka ce "Amin"
Ya kwashi Hadiza da Inna Tambai da kayansu ya kai su gidan Inna Tambai, ta yo mai rakiya har cikin mota tana kara yi
mai godiya a bisa dawainiyar da ya yi masu tun daga asibiti har
zuwa yau, ya ce, "Babu komi yanzu ran lahadi za ki koma
Kaduna?" Ta ce` Insha Allah' ya ce "Zan yo waya da yamma kenan."
Ta koma dakinlinna Tambai nan da nan ta dora ruwa bisa
wuta don ta yi wanka, domin kwana bakwai din nan jin jikinta ta ke yana yi mata danko, ta lalubo wani akwatinta cikin wa'anda
ta dawo da shi daga Hajji anan kalkashin gadon Inna tambai ta duba man shafawarta wato zaitun domin shi ne man Hadiza,
rudanin ciwon Baba Kado bata tsaya ta dauko ba sai dai ta dauko
sabulun wankanta wato sabulun salo amma dan Ghana wanda
tàke cakudewa da zuma yar usili da jar kanwa da kwai, idan ta yl wanka da wannan sabulun sai ta mulke jikinta har gashin kan
ta da man zaitun wannan shi ne sirrin Hadiza na ko yaushe fatar
9
jikinta na salki da sulbi, haka nan idan mata sun kai dubu launin
fatar Hadiza ta fita daban tamkar danyar roba ga sheki da salki.
Da la'asar şakaliya suna zaune ita da Inna Tambai suna
maimaita ciwon Baba Kado wani yaro ya shigo ya ce, "wai a
zaure ana sallama da Hadiza!" Kamar ta ce `Ace ya shigo' ta
san`yan gaisuwa amma sai ta dauki mayafinta ta nufi zaure.
Ta sami Falanke tsugunne a zaure ta ce, "A'a Shu'aibu
telan zamani? "Barka da fitowa ranki shi dade ya karin hakurin
mu?" Ta ce "mun gode Allah". Anan fa Falanke ya shiga yabon
Baba Kado ya na nuna wannan rasuwa ta jama'ar Bakori ce
gaba daya inda yake shiga ba ta nan yake bulla ba, a bisa
kyakkyawar lafazin sai Hadiza ta ji wani sanyi a ranta ta rinka
raya ma ranta cewa mahaifinta na can Aljanna Fiddausi domin
yabon jama'a shi ne rahamar mamaci, ya ci gaba da cewa "yanzu
duk dattawan garin nan akwai mai halin dattako irin na Baba
Kado? Ki duba fa saboda dattakonsa yaron nan Yusuf ba shi da
komai amma Baba ya ce ya ba shi ke sai dai kuma wani shaidan
da ya gilma Allah bai ida nufi ba lokacin, amma mu masoyan
Baba Kado muna nan muna rokon