Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 9
da ka yi, wanda yasa mahaifina ya rasu cikin kwanciyar hankalin ya bar ni da miji na gari na gode da wannan taimako a kodayaushe ba zan manta ba." Yace, "Babu komi Hadiza aure nufin Allah ne, insha Allah ba za ki yi dana sani ba da auren Yusuf". Ta daga mai hannu ta ce, "Zancen Yusuf ba ya tare da ni don haka ka bar zancen kawai." Yace, "To na bari, ina da hoton Salma a mota ko kina da bukatar gani na kawo maki?" Wannan shi ne lokaci na farko da ta taba tsanar Amiru tace, "A'a bani da bukata". Ya dan cije lebe yace, "Ba dai kishina ki ke ba ko Hadiza?" Ta dube shi da kyau ta ce, "idan ma har na yi kishi a wannan lokacin ai daidai ne". Ya duba agogon hannunsa yace, "Ai gara ki yi ma Yakumbo magana mu tafi kada dare ya yi mana." A cikin gida babu abinda ke fitowa daga bakinsu Inna da Yakumbo sai ban hakuri ga junansu, bayan Inna Tambai ta fiddo mata kaya akwati shidda ta dubi kaya babu ko kallabi da ya salwanta, aka kira yara suka rinka fidda kaya zuwa motar Amiru. Bayan sun tafi Hadiza ta shiga dakin Inna Tambai tana 43 wanisaboon kukan tana fadin "Ni dlai Inna na shiga uku anya ko zan yi aune a duniya?" Inna Tambai cikin nata bacin ran, ta danne ta ce, "Dori me za kima kanki mummunan lafazi, lɔabu komi gara da hakanı ma ta faru, daga wajensu ba wajenmu ba, ta shi ki wanke ido mu tafi Malunfashi." Farar-farar ana gab da kirar mangariba suka isa gidan Yaya Amina, a lokacin Yaya Aminar na kwashin tuwo ta rinka yi mıasu sannu da zuwa, bata kawo komi a ranta ba sai tunanin shiryeshiryen biki ne ke tafe da su, ta kammala kwashin tuwo taa kai ma Mallan Isa dakinsa, ta rufe na sauran jama'a a kicin yayin da ta shiga da na su Inna Tambai daki, har Hadiza ta tayas da sallar mangariba ita ma Innar ta shigo karnmale da alwala. Amina tace, "To bari ni ma na je na yi sallar kafin mu gaisa ko?" Hadiza dai na can gefe daya na jan casbi lokaci-lo kaci tana share kwallan da ke zuwa mata yayin da Inna Tambai da Yaya Amina ke cin tuwo a cikin kwano daya. Suna ci suna hira can Yaya Amina tace, "Wai ita kuma waccan kukan me take ne?" Inna tambai ta rinka side yan yatsunta daya bayan claya itama kukan ya zo mata tace, "Wallahi al'amarin ne na Hadiza Amina kamar almara, abubuwan da daure kai, dazun nan ne sai ga su Amiru da Yakumbonsa sun zo amsar kayansu wai sun hakura ta auri Maitama." Amina ta yi shiru yayin da Hadiza da Inna suka ci gaba da sharban kukansu. Inna Tambai tace, "Ba ki ce komi ba?" Amina ta amsa da cewa, "To me kike so nace Tambaya? Ta kore shi yadda ta saba korar sauran jama'arta dole sai wannan mara kunyar yaron wanda ya zo har gabanki yace bai son ta ita kuma shi take so, to ai shikenan gata ga shi nan, sai ta zaba ko ni ko shi, idan har ta auri Yusufa ba ni ba ta." Inna Tambai ta yi wal da ido tace, "Haba Amina ke ko meyasa ba kya da tausayi ne? Idan ba a tausaya ma Hadiza ba lalle ko ba a ga laifinta ba, me ta yi anan?" Amina ta mike tsaye tace, "ke dama ai ba kya ganin laihinta, to duk 44 abinda za kuyi a fidda ni a ciki". Ta fice daga dakin ta nufi dakin mijinta a can ta yi hirarta har sai lokacin bacci ta je ta baiwa sU Inna Tambai kayan shinfida ta kara fita ta nufi dakin mijinta ta kwana a can don ma kada a kara yi mata zancen Hadiza da Yusuf. Da safe sun kammala kalaci, Inna Tambai bata taba bacin rai irin na wannan rana ba, me zai sa Amina ta yi masu haka, da kyar ta samu Aminar ta zauna da ita ta saurareta inda Inna Tambai tace, "Wai ke ko Amina kin taba sawa, an yi ma ki istahara a bisa al` amuran auren Hadiza?" Amina ta girgiza kai, Tambai tace, "To ni na sa an yi mani an kuma tabbatas mani aurensu da Yusuf ba fashi domin akwai rabo". Amina tayi tsaki tace, "Nace ke ce ke daure mata gindi kin yi mani musu, wane irin rabo! Ko uban wa ta aura idan dai mai haihuwa ce zata haihu, ba, dolé sai Yusufa ba, ni dai na gaya mata tabbas ta auri Yusuf ba ni ba ta." Daya daga cikin kannan Hadiza ya shigo yace, "Yaya ga su Yusuf sun zo suna son ganinku." Gaba daya falon aka yi tsit can ita Yaya Aminar tace "kace su shigo." Dalilin zuwansu Yusuf shi ne a daren jiya ya isa Bakori ya isa gidan Inna Tambai aka shaida masa lalle sun tafi Malunfashi ita da Hadizan, da safe ma ya koma aka ce acan suka kwana, to abun ya basu tsoro shi da Falanke don haka suka yanke shawarar zuwa Malunfashin. Inna Tambai zuciyarta ta rinka raya mata koma menene ba kiran arziki Amina ke ma su Yusuf ba, komi ya kara jagule mata, ita dai Hadiza na zaune na jin su idonta duk sun yi firi-firi har kukan ya fara janyewa don kan shi. Yusuf da Falanke suka zauna a takure bayan sun gayas da su Yaya da Inna a lokacin gaban Yusuf ya rinka bal, bal, bal saboda yadda ya ga fuskar Yaya babu annuri. Bayan gaisuwa ba a sake cewa komi ba a falon, daga can gefe Falanke ya kara rusunawa ya dan goge fuskarsa da habar babbar rigarsa, yace, "To Inna muna nan dai muna bada hakuri a kara baiwa Yaya Amina hakuri mun.........." Amina ta dakatar da shi tace, "Duk 45 ku tsaya ni ba tsohuwar banza ba ce, ba'a magana biyu da ni, idan har wannan yarinyar ta amince da ku, to ni ba ni ba ta abinda nake son fada maku kenan." Maganar Yaya Amina ta bugi kirjin Tambaya, bata san lokacin da tace "To Amina wacece tsohuwar banzan mai magana biyu? Idan ni kike nufi da zargin son su Maitama ga su nan me na taba ce masu aure ne na Hadiza da Yusuf daga Allah ne, duk iyakar kokarinmu mun yi amma komi ya gagara saboda haka ya dace mu hakura a bar wa Allah ikonSa." Amina ta harzuka tace, "Daman na san abinda ke ranku kenan, to ku je a yi aure amma tsakanina da ke Hadiza Allah Ya isa! Allah Ya tsine maki!! Allah Ya wulakanta ki a duniya!!!" Haba nan da nan Hadiza ta sa hannu a ka ta shiga ihu na kururuwa tace "Ai ga Yusuf din nan idan na taba amince masa a bisa bukatarsa nan da nan tsaffin cikin anguwa kamar su Hanne mai kuli da Uwa mai kitso suka danno kai gidan su Yaya Amina suna tambayar "lafiya ake ihu da kururwa ko mutuwa a kai?" Bakaken maganganun da Amina da Tambaya suke fada ma junansu ya baiwa su Hanne bayanin abinda ke faruwa rigimace ta zancen auren Hadiza. Daga Falanke har Yusuf sun firgice sun daina baiwa kowa hakuri, sai su Hanne ne ke baiwa su Amina da Tambaya hakurin. Hadiza ta mike ta dauko gyalenta da na Inna Tambai ta mika mata cikin kuka ta lalubo hannun Inna Tambai ta nemi ta tashi su tafi Bakori don ta ga rigimar ta fara tsanani. Suka baro gidan Yaya Amina cikin rudani da yanayi na fitar hankali wanda duk ya gan su a kan hanya sai ya tsaya ya dube su yana tunanin ko rasuwa aka yi masu? Sun kusa isa tasha Falanke da Yusuf suka sha gabansu, daga Innar har Hadizan sun nuna kin amincewa su shiga motar Yusuf, amma ganin jama'a an fara zuba masu ido, dole Tambaya ta ruko hannun Hadiza ta bude masu motar Yusuf suka shiga. Har suka isa kofar gidan Inna Tambai Hadiza kuka take yi. Haka nan babu wanda ya tsinka balle ya sami bakin baiwa Hadiza magana. Inna Tambai ta fara shiga gida yayin da Hadiza ta bi 46 bayanta Yusuf ya yi sauri ya bi ta zaure yace, "Hadiza". Ta tsaya ta dube shi yace, "Ji nan mana." Tace, "Me kake so na ji duk jawabin da yaya ta yi bai gamsar da kai ba, koko tsinar da ka ja mani ce bata ishe ka ba?" Yasa halshe ya lashe busasshen labbansa yace, "Wallahi Hadiza ko daya bani da niyya baile ra ayin son na hada ki da yaya, ki kwantar da hankalinki in dai irin wannan zagin ne bai yi ma auren sunna komi sai albarka, tsinuwa bisa auren da aka shinfida akan gaskiya bata tabbata sai dai ta zama albarka". Hadiza ta tsinka mai harara tace, "Makaryacin banza, dan yaudara, kai yanzu nan har wata albarka zan tsinta gare ka, wawa wanda bai san ciwon kanshi ba, wallahi randa duk ka kara zuwa gare ni Allah ya isa tsakanina da kai, wawa kawai." Ta juya ta shiga gida shi ma ya juya ya ja motarsa ya nufi sabon gidansa, ya kulle kansa a dakinsa ya yi kuka. Ya yi irin wannan kukan akan Fa'iza, daga lokacin ya daina son Fa'izar, don haka a yau ma yana tabbatarwa zuciyarsa zai kyale Hadiza, tsiya da wulakancin sun isa. Ya mike yayi alwaia ya zo ya gabatar da nafila yana rokon sauki akan jarabawar da Allah ya dora masa akan Hadiza. Sai bayan sallar la'asar ya fito falo ya dubi kwanonin abinci ya kawad da kan shi ya koma gefe guda ya zauna har yanzu abinda ke mai kuna a zuci shine tsinewar Yaya Amina, wai shin me ya yi haka da har Yaya ba za ta iya gafarta mai ba? Ko dai dama can Yaya bata kaunarsa ne, ya mike ya shuri takalman sa, jikinsa jallabiyace 'yar madina koriya ya nufi gidan Gwoggo Halima a kasa ba cikin motarsa ba. Ya samu tana sallar la'asar, ya nemi kujera ya zauna sharaf babu kuzari a tare da shi duniya ta hadu ta cakude masa, fatarsa a lokacin da ma ya san gidan da mutuwa take da ya kai kan sa. Gwoggo ta sallame ta tsaya tana kallonsa, yana can wata duniyar bai san a inda ya ke ba tunanin bacin ran da ke tattare da shi kawai ya dame shi. Ta ce, "Wai kai ko lafiya ka ke? Kaman kan ka faro komen neman aure da ka ke neman ka lalata kan 47 ka?" Yusuf ya rausayar da kai gefe guda, gwanin ban tausayi kwalla suka cika taf a idonsa yace "Ai dai shikenan gwoggo, na hakura da Hadiza ta yi min kashedi da ita' Gwoggo ta yi shiru tana kallon dardumar sallarta, sannan tace, "Ba zai yiwu ba ka kyale ta in ba dai aure aka daura mata ba. Yanzu nan dawowata daga Danja wajen Malan abokin Babana, ya yi istahara har kwana uku ya ce lalle insha Allah za'a yi aurenku da Hadiza domin akwai rabo." Yusuf ya zaro ido komi na shi ya saki yace, "Gwoggo rabo fa kika ce? Rabon aurenmu!" Kanta a sunkuye tace "Har ma rabon haihuwa. Malan yace, idan muna shakka mu jaraba da kanmu mu gani, wato istaharar yace idan mun kammala dukkan hidimominmu za mu kwanta sai ayi alwala mai kyau kada a sake magana a karanci sabbi raka'a daya rak da niyyar abinda kake so to insha Allah Ubangiji zai nuna ma wani abu cikin baccinka haka nan Malan ya yi mani wani alkawari yace, idan har na samo mai sawun kafar Dije zai hada wani sirri in Allah ya yarda da kansu za su aiko mana." Yusuf ya ji wani irin dadi yace "To Gwoggo a ina zamu samo?" Tace, "zan san yadda na yi a daren yau na samo gobe a kai mashi domin lokaci na kurewa." Yusuf yace, "Ina zuwa Gwoggo bari na yi ma Falanke maganar kila zai iya samowa domin dabara gare shi." Yusuf na tuntubar Falanke da maganar Falanke ya yi dariya yace, "Ai ina da sawun Hadiza." Yusuf ya tambayi yadda akai, Falanke ya bashi bayani ya dauko masa ya kai ma Gwoggo Halima. Gwoggo Halima tace, "Oni Halima to kaga Shu aibu har ya fi ka kokari kai ka zauna sai sukurkucewa kake yi, ka kasa tabuka komi." Yace, "To ai ni gwoggo ina ganin kaunata da Hadiza kamar ba sai na yi mata asiri ba addu`ar da na ke yi ma ta isa." Tace "E haka ne amma ance ko kana da kyau ka kara da wanka sannan ina tsoron bakano wa ya san irin yasin din da suke aiko wa Dijen da mahaifiyarta suke mana wannan tsiyar?" Yusuf ya dube ta ya ce, "Wace irin yasin gwoggo?" Tace "Ai ka san shi 48 bakano akwai shi da aiki da yasin don cin galabar al amuransa а dan kankanin lokaci. Yayi shiru yana tunani shi kam yana ganin kamar Amiru ba zai iya yi mai wani mugun abu ba kila dai sai ko iyayensa idan sun ji zafin abinda yayi. A cikin daren nan gwoggo ta sa Basiru ya kai ta gidan Malan a Danja a motar Yusuf. Mallan yace, "Madallah ku kwantar da hankalinku in dai matarsa ce to babu fashi zasu aiko maku har gida." Kwana daya da yini daya Inna Tambai ta shiga yi ma Hadiza nasiha akan ta janye akidarta na kin auren Yusuf ta hakura su yi aurensu domin wannan sako ne daga Allah. Hadiza tace, "Inna ki yi hakuri idan de ina da rabon aure a duniya zan sami wani mijin ne amma duk wulakancin da Yusuf ya yi min sannan kuma ace daga bisani na zo na aure shi a bisa tsinuwar mahaifiyata?" Inna Tambai ta hasala zuciyarta, ta kara turnuka tace, "sai ki ta zama har duniya ta nade, tunda ke da uwarki Amina kun fi kowa zuciya a duniya ba a yi maku laifi ku yafe, daga yau insha Allah babu ruwana bisa zancen aurenki ran da duk akace an daura maki aure da wanda kike so, idan ina duniyar ban mutu ba kamar ubanki na zo na shiga cikin 'yan rakiya". Hadiza ta yi raurau da idanu tace, "Don Allah Inna me yayi zafi haka?" Tace "Don ba ni na haife ki ba haka nan kin nuna min Allah bai ba ni haihuwa ba." Nan da nan Inna tasa kuka ita ma Hadizan kukan ne dai wiwi. Sun wuni zungur cikin mummunan yanayi babu mai cewa wani abu, ko wanne zuciya kamar ta fashe don daci. Bayan sallar issha'e Hadiza ta yanke shawarar zuwa ta ga Mallan lliyasu sun jima da Mallan din a dakinsa suna hira. Zuwa can Hadiza tace "Don Allah Baba na zo da wata muhimmiyar matsala ina so kada ka rufe mın komi ka sanarshe ni komi dacin amsar babu komi ka gaya min." Ya dube ta da kyau 49 ya tausaya mata yace, "ina jin ki Dije, ki sawa ranki tamkar kina magana da mahaifinki ne." Tace, "Wai Baba bayan rigimar aurenmu da Yusuf sau nawa Yusuf ya kara zuwa wajen Babana?" Malan Ilyasu ya dan daga kai sama nuna alamun tunani yace, "A gaskiya Dije babu adadi ba zai kirgu ba." Tace, "Zaka iya tuna kalaman da mahaifina ya rinka yi akan Yusuf bayan rabuwarmu kafin ya rasu?" Mallan lliya ya girgiza kai ya ce "Ai daidai da rana daya ban taba jin marigayi Alhaji Kado ya yi mummunan lafazi ba akan Yusufa bayan na yabonsa da yi mai kyakkyawar addu`a kamar yadda na san yana yi maki a kodayaushe domin lokacin da muka sami labarin an fasa aurensa da Faiza babu abinda ya fito bakin bawan Allah nan mahaifinki sai cewa ya yi`kila dai rabon yaron nan sai ya auri Dije ne ka ji wai an fasa aurensa, itama kuma Dijen ka ga bata sami miji ba a can Malunfashin',sai na ce don Allah Mallan Kado kada na sake jin zancen yaron nan Yusuf daga bakin ka,y a yi murmushi ya ce Mallan Iliya ba dama." Hadiza ta yi jigum a ranta ta rinka tunanin wai wannan wane irin so ne Baba ke yi ma Yusuf? Tayi ajiyar zuciya tace "To Baba tunda ake zuwa neman aurena tun daga kan Yallabai Mamud har zuwa Amiru ya taba nuna maka gara su da Yusuf?" Malan lliya ya yi shiru sannan yasa habar riga ya goge kwalla ya ce, "Ai akwai wata maganar da marigayi ya taba yi mani a lokacin yana kwance asibiti ba lafiya farkon tafiyarki Malunfashi kenan, ya nace da zancen Yusuf sai na rika yi mai fada nace ka san wanda Allah zai ba Hadiza kila ma yafi Yusuf? Wallahi Allah ya jikan bawan Allah nan yana kuka ya rinka ce mani shi kowa za ki aura bai kai Yusuf ba, ko da kuwa shugaban kasa ne domin shi yana ganin Yusuf tamkar yayanki Tasi'u inda kuma na ji dadín Yusuf shi ne, har Alhaji Kado ya bar gidan duniya bai yada shi ba ya nuna masa gatanci kamar Tasi`u ne domin lokutta da yawa zai zo nan gidana ya ba ni kudi sabbi masu yawa yace ga wannan ni ma na taba idan nace ina ka sami kudi har ka ke rabo ya kan yi dariya yace, "Dana Yusufa ya zo ko yayi min aike." 50 Hadiza na share hawaye tace "Baba!" Ya amsa, "Na'am Hajiya Dije?" Tace, "Wannan rana da aka sa za`a yi arenmu da Amiru kada a canza a daura da su Yusuf din amma fa Baba Yaya Amina sau takwas tana tsine min jiya akan Yusuf." Yace, "Wannan duk ba komi ba ne idan kin bi Allah kin kuma yi biyayyar aure babu abinda zaki gani sai albarka, ki ci gaba da kyautatawa mahaifiyarki tare da neman gafararta." Wanshekare lokacin da Mallan Iliyasu ya je wajen Inna Tambai suna daidaita yadda zasu sawa su Yusuf kudin sadaki sai ga Hadiza ta kawo mai wasika tace ya kai ma Yaya Amina ta neman gafara. Malan Iliyasu ya isa gidan su Yaya Amina ya yi sa'a ya cimma mijinta Malan Isa, bayan sun gaisa da Isa, ya shigar da shi zaure ya kawo mai tabarma sannan suka fito shi da Amina. Duk hanyar da Malan lliyasu ya bullo mata sai ta bulke haka dai suka hadu shi da mijinta ana lallasinta ana bata hakuri, daga karshe tace aje ayi aure ba za ace ta hana 'yar ta aure ba, domin ta san in ba Yusuf ba Dije ba za ta yi aure ba amma fa babu sauran wata hulda tsakaninsu. Mallan Isa yace, "Zancen wofi kenan idan kince babu hulda babu ruwanki da ita kenan" Ta ce, "Shikenan Mallan tunda dai kun tilasta min na yafe a yi aure amma kowacce irin matsala ta sami kanta kar ta neme ni haka nan dukkan walakacin da zata sami kanta gidan Yusuf babu ni babu zuri`ata." Mallan Iliyasu ya mike ya shuri takalmansa yace, "Aure kam za'a daura domin wannan shine burin mahaifinta a zahiri insha Allah kuma kowa sai yace gwamma da aka yi kuma albarka na tare da Hajiya Dije duniya da lahira saboda tabi iyaye yadda duk Ubangiji ke son dan kwarai ya bi. # * * Bayan Mallan Tukur ya dawo sallar azuhur ya shiga dakin gwoggo Halima fuskar nan cike da annuri, bayan ya zauna ne, Halima ke cewa, "Kai Mallan wannan irin fara'a haka kamar an aiko mana an mana gafara?" Yayi murmushi ya ce, "Halima kail Ai dole ne na yi murna da na ya sami aure?" Halima ta 51 danne murnarta ta nuna kamar bata gane ba tace, "Wane dan kuma?" Mallan ya dube ta da kyau ya yi dariya yace, Mata sarakan gulma kamar wadda ke iya bacci, wadda bata da wani sukuni duk kin fita kamanninki a dalilin wannan auren shi ne yanzu na zo da albishir har za` a a rinka nokewa a nuna min ba'a san abinda na ke nufi ba, to da na Yusuf da Dije alkawarin Allah ya cika, Mallan Iliyasu ya zo min da zancen sadaki da komi da komi na aure yau sauran kwana goma sha daya a daura aure ayi biki, na aiki yaro a kira min Basiru ya zo ya je ya yi ma Yusuf din waya a Funtua. Halima ta kasa danne murnarta, ta ce "Allah Yasa alhairi". Anan ne Basiru ya yi sallama ya shigo ya durkusa yace "Ga ni Baba an ce kana nemana?" Malan yace, "E ka je ka yi ma Yusuf waya ka sanar da shi an bashi Dije." Sai Basiru ya rike baki yace, "Ikon Allah! Baba wannan albishir din ai gara na je Abujan ta fi karfin waya." Gwoggo Halima ta yi dariya tace "Don ka tatse shi ko, ya fiddo kudin sabon mashin din da ka ke nacin ya sai maka", aka kyalkyale da dariya. Malan yace, "Amma ina ji maka tafiyar dare". Yace "Babu komi Baba, ku yi min dai addu`a Allah Ya kiyaye hanya." Basiru bai isa gidan Yusuf ba na Abuja sai misalin karfe goma saura na dare, ya iske su Falanke amma Yusuf na tare da shugabansa suna gudanar da wasu ayyukansu don haka bai zo ye işke bakonsa ba sai karfe goma sha biyu da minti arbain da tara ya shiga gida, ya sami Basiru ya langabe a falo yana avengyadi. Abinda Yusuf ya fara kawo ma zuciyarsa shine cikin daya biyu ko zancensa da Hadiza ko kuma wani babu lafiya a gida "Kai me ya faru Basiru, waye babu lafiya, don me baka yo min waya?" Basiru ya yi dariya yace, "Babu komi sai alhairi yaya, kwantar da hankalinka zancen aurenku ne ya tashi kai da Hajiya Hadiza, har sun sa sadaki Baba Tukur ma ya biya," Yusuf a tsaye yake sai ya nemi kujera ya zube yana washe baki yana shafar kai yace, "Godiya ta tabbata ga Sarki Allah, Ubangiji Allah Ka ba ni ikon rike amana, wai ka fadawa Falanke kuwa, ya ban iske shi nan ba?" Basiru ya ce, "Gaskiya kin gaya mai na yi domin ina ganin wannan albishir din kai ya fi cancanta na fara sanar mawa." Yusuf ya kwallawa yaronsa Jerry kira yace, "Kira Falanke a baskwata." Falanke ya iso ido cike da bacci, Yusuf yace "To. shugaban mayaka, aure fa ya tabbata akan mu, ni da Hadita Faianke yace, "Ranka shi dade idan na yi guda ban yì laifi ba? Yusuf yace, "Don Allah kada kayi domin ko wajen matan ma ance babu kyau balle kuma namiji." Ai sai Falanke ya shiga rawa. yana juyawa dama abu ga mai kiba Yusuf da Basiru dariya suke suna tintsirawa har dai Yusuf ya mike ya fiddo kudi a aljihunsa ya rinka likawa Falanke suna ta tintsirar dariya Yusuf yace, "To ya isa Falanke sai kuma ran biki rannan za kayi rawa da `yan koroso." Falanke yace, "Ana magana ran ka shi dade? Amma don Allah ina rokon shaddar nan wadda ka zuba a ranar da muka je gaisuwar Baba Kado, ita zan zuba ran daurin aure." Yusuf yace "baka son a dunka maka sabbi?" Yace, "Wa`ancan nake so ranka shi dade." Basiru yace, "Ni ma yaya ina tunin mashin dina." Yusuf ya ce, “Kai sakarai ne wata mota nake son saya maka ko don saboda kai su Gwoggo anguwa, kila ma gobe za` ai cinikin motar.". Basiru ya rasa kalmar da zai yi godiya anan ya kara amincewa lalle ba karamin so yaya ke ma Hadiza ba. Yusuf kwana yayi bai runtsa ba, bayan ya gabatar da nafila ya yi ma Baba Kado addu'a domin ya san darajarsa ya sami Hadiza sannan ya yi ma Jallah godiya sai ya zauna ya fiddo biro da takarda ya shiga rubuta abubuwan da zai shirya a lehen Hadiza. Da safe bai nufi ofis ba sai gidan shugabansa ya yi masa albishir. Anan ne Shugaba yace "zancen tafiyar mu Legos aiki babu kenan. Sai ka fara hutu daga gobe don ka ji dadin gudanar da hidimar bikin tunda lokaci ya kure." Yusuf yace, "A'a ranka shi dade za mu iya zuwa aikin Legos domin zan yi anfani da wannan damar na hado lehe daga can." Yusuf ya sallami Falanke da Basiru yace su tafi da motarsa 53 su jirasa a Kaduna za su aiki Legos na kwana biyu. A Legos Yusuf ya dauki yarinyar kanfaninsu Bimbo suka shiga kasuwa ya zabo lesisika na shiga tsara da atanpopi na fita kunya, da duk wani abu da ya dace da rayiwar diya mace 'yar bimi. Bimbo ta sa Yusuf ya sayi akwati hudu da kit na biyar. A gaskiya ya ci mutuncin naira, naira kuma ta mutunta kaunarsa ga masoyiyarsa Hadiza. Da suka yi sallama da Shugaba ya kawo cek na dubu dari biyu da hamsin ya bashi yace, "Ga wannan a sai ma amarya dan kunne sai mun zo daurin aure." Yusuf ya ce, "Ranka shi dade wannan ai kace a sai ma `yan Bakori dan kunne ba amarya kadai ba, Allah ya saka da alhairi." Jirgi ya sauke Yusuf a Kaduna su Felanke na jiransa ya zuba akwatunan lehe sai gida Bakori. Wanshekare dangin Gwoggo Halima suka shirya zuwa kai lehe. Yusuf ya kashe ya tsare yana fadin don Allah Gwoggo idan an je ace ma Inna Tambai ta ba Hadiza wannan dan karamin akwatin ta adana domin duk zinari ne a ciki, idan ba zata iya adanawa ba a dawo min da shi zan kai banki saboda taron jama'a." Gwoggo Halima ta danna mai harara tace, "Wai kai mevasa ba ka da kunya ne, lehen ma sai ka fadi yadda za`a yi?" Bayan masu kai lehe sun nufi gidan Inna Tambai su Ankudi da Sabura sune 'yan taryar baki. Duk da su Ankudi suke kauyawa amma sun san darajar zinari don haka suka fara rade-radin ko ba komi lehen Yusuf ya fi na Amiru tsada idan akai la'akari da tsadaddun zinaran da ya zuba. A daidai lokacin da ake shagalin amsar lehe, shi kuma Yusuf da Falanke na can takure zauren Mallan lliya suna godiya waien Mallan din, anan ne Mallan lliya yace, "To Yusufa aure abu ne mai wuya ga wanda bai fahinci dokokin Allah ba amma kuma abu ne mai sauki idan aka bi tsarin Sarki Allah, haka nan wanda duk ya

Chapter 5 of 9