Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 8
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 🛥️ABDURRAHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE🛥️ (RENEW) 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚* Na Fadila Sani Bakori, Page 1 Tafiya ta ke yi da ga gani sauri takeyi,idan ka kalli fuskarta zakaga ta nuna yanayin damuwa. Matashiyar budurwa ce da bazata wuce shekara goma sha takwas ba. Wani ma dai-dai cin gida ta shiga. Zaune ta iske su sun sa Mahaifinsu a tsakiyar su suna ai kinyi mai sannu.Na'ima da shigowarta kenan kallan Mahaifinta tayi dake kwance cikin wani hali ta ce "Sannu Baba ya jikin?." "Yauwa Na'ima ,ina Hassan d'in? " Cewar mama kafin ta bata amsa Hassana yayi sallama ya shigo, da saurinshi yak'ara in da malam Yahaya yake kwance." Sannu baba ya jikin naka?" Yauwa Hassan jiki alhamdulillah" Baba jikin ne ya sake ta shi? ". Mama ce ta amshe maganar ta hanyar cewa" Hassan dan Allah salanke zaka ka amso mai magani yanzu, adafa mai ko Allah zai sa jikin ya lafa"Tom mama amma wallahi bani da kudi ko na mota balle na maganin". kafin mama tayi magana malam Yahaya ya ce" Mariya ya d'auki buhun masarar da ya yi saura ya saida shi sai yayi kud'in motar da su ya amso maganin. " Cikin minti goma Hassan ya kai buhun masarar kasuwa ya Saida yahau motar salanke. Dayake tsakanin sabon yalwa da salanke bawani nisa bane can-can cikin awa d'aya Hassan yadawo, cikin sauri mama ta amshi maganin ta wanke tasa jar kanwa ta d'ora maganin a wuta. Cikin yardar Ubangiji malam Yahaya yana shan maganin yaji dama-dama so sai yaji jikinshi duk ya sake bakamar daba. Masha Allah cikin kwana uku jikin malam Yahaya yayi sauk'i Sosai. Malam Yahaya zaune yake da iyalansa suna fira Sosai yana basu labaran duniya Hassan yayi sallama ya shigo, goye da jakar goyo abayansa, gefan malam Yahaya ya zuk'unna bayan sun gaisa ne Hassan ya ce "Baba yau ne tafiyarmu,kasan nacema exam d'in da mukai sunana yafitu tom yau ne suke nemanmu muje dan ganinmu"Masha Allah Hassan naji dad'in jin maganar nan, Allah ya tai maka Allah yayi maka albarka Allah yabaka Wanda zai mayema gurbin uba kamar yadda kamaye min gurbin d'a, nagodee Sosai da kulawarka gare......." Sallamar da yaji ce ta hana shi k'arasa abinda yake son fada..... Yayyan malam Yahaya ne su hud'u su ka yi sallama suka shigo. Malam Yahaya da fara'arshi ya tarbi 'yan'uwanshi ya ce " A'a yaya Jimmai kune barkanku da zuwa ,yaya Rabi'u ,yaya Ya'u ku zauna mana ga guri ya shimfid'a musu tab'armar kusa da shi ". Bayan sun Zauna ne anyi gaishe-gaishe jimmai tace" Ya'u Ka fad'ama Yahaya abun da muke tafe da shi. Wanda akakira da Ya'u kara gyara zama yayi sannan ya kalli Yahaya ya ce" Yahaya game da auran Na'ima ne tom mun yanke shawarar k'arshan watan nan za a d'aura auran Na'ima da gali kamar yadda muka sanar da kai akwanakin baya. Ba Na'ima ka d'aiba hatta malam Yahaya da mama idan ka kalle su zakaga tsantsar furgici a fuskar su. "Munji shiru Yahaya kai muke saurare "cewar Rabi'u. Numfasawa Malam Yahaya yayi sannan ya ce "Dama ni yaya Rabi'u wani hanzari ba gudu ba nace dama inda ita Na'imar tadage bata son gali mai zai hana abashi w........ "K'arya kake wallahi dama ba ra'ayinka kona Na'ima mukazo ji ba a'a mun zo ne muce muku ku shirya k'arshan watan nan zamu d'aurama Na'ima aure da gali" Mahaifin Na'ima numfasawa yayi sannan ya ce " Yaya Rabi'u ina gudun abun da nasani ne nan gaba shi yasa bawani abu ba ind...." Hannu Rabi'u ya d'aga mai yace " Ya'isa hakanan!,Yaya jimmai ku tashi mu tafi " Cikin hanzari Na'ima ta kama k'afar jimmai tace" Gwaggo dan Allah ki taimakan wallahi nayarda zan auri koma waye amma bana son yaya ga......" marinda Ya'u yawanka ma ta ne yasa takasa karasa abinda tayi niyya cikin wata kid'ima da rawar jiki ta kama kafar Rabi'u tace" Baba Rabi'u kataimakan karku aura min......."Wata in giza Rabi'u yayima Na'ima wadda mahaifiyar Na'ima batasan sanda taje da sauri zata rik'e taba amma ina sai datakai kasa cikin wahala da azaba Na'ima ta fasa wata uwar kara kafin kace me sai ga jini na zuba abakinta. "Aunty jimmai,Yaya Rabi'u, yaya Ya'u ku yi hak'uri bazan iya aurar da Na'ima ba agun Wanda bata so" cewar malam Yahaya mahaifin Na'ima. "K'arya kake aure dama bakai ka had'a ba Allah ne yahad'a dan haka kamar anyi angama ne" cewar yayar su jimmai tana kai wa nan ta ce "ku muje Rabi'u " . Allah sarki malam Yahaya daya rasa abunyi sai ya fa she da kuka cikin kid'ima Na'ima da sauran k'annanta suka karasa wajan babansu, Hassan ne ya zaunar da shi yace dan Allah kabar kuka baba yawuce. Na'ima kallan Mahaifinta ta yi da ke kuka ta ce" Baba dan Allah kabar kuka ni na yarda zan auri yaya gali" kai mahaifin Na'ima ya girgiza ya ce" A'a Na'ima bazaki auri gali ba" Mahaifin Na'ima ya fad'i maganar yana mai d'aukar butar dake kusa da shi yanufi hanyar bayi tari ne ya turnik'e shi ya fad'i gurin, da sauri Na'ima ta karaso gun tarik'eshi ganin yadda yake tarin ta ce" Baba dan Allah ka kwantar da hankalinka ni na yadda zan aure shi ". Mahaifin Na'ima Kiran sunan Na'ima yayi har yanzu cikin tarin yake ya ce "Na'ima indai ni ne mahaifinki tom bazaki auri gali ba" " Amma baba kaji yadda su gwaggo jimmai suka ce" Kai Manaifin Na'ima yake girgiza mata magana yake son yi amma tari yahanashi yi, mahaifiyar Na'ima ya yafito da hannu, da sauri tak'araso inda yake. Cikin rawar murya mahaifin Na'ima ya fara magana kamar haka " Ma.ri. ya ko bayan raina banyarda Na'ima ta auri ga.. li ba" cikin sar kewar harshe yake maganar, tarinda yaci k'arfin shine yasa basa jin abinda yake cewa sai kalmar shahadar shi sukaji, cikin gigita mama ke girgiza shi ganin baya nunfashi. Cikin kuka mahaifiyar Na'ima ke girgiza shi tana cewa" Malam dan Allah kar kai mana haka dan Allah katashi. " Kullunafsin za'ikatul maut rai ya riga yayi halinshi. Kukan su Na'ima ne ya shigo da mak'ocin su......... 🛥️🛥️ABDURRAHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE🛥️🛥️ (RENEW) 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚* Na Fadila Sani Bakori Page 2 & 3 Allah sarki duk mai rai mamaci ne, haka akayi zana'idar malam Yahaya aka kai shi gidan shi na gaskiya. Ranar sadakar bakwai haka 'yan'uwan Malam Yahaya suka taru akai addu'ar bakwai. Bayan mutane sun tafi ne Yayyan marigayi suka nemi suna son magana da Mahaifiyar Na'ima da Na'ima, bayan sun nemi gune sun zauna suka sake yima mama gaisuwar rashin Mijinta,sannan wan mariyagin ya fara magana kamar haka "Mariya yau ne akai addu'ar bakwai na d'an'uwan mu Masha Allah, Allah ya jaddada rahamarsa agaresa" Yacigaba da cewa" Mariya nasan kin sanda maganar auran Na'ima da gali ko?" Mahaifiyar Na'ima dai bata ce mai ko mai ba. Yaci gaba da cewa "Tom kamar yadda mu ka tsaida k'arshen watan nan ne auran Na'ima da gali, tom yana nan yadda yake bazamu d'agaba, yanzu zamu d'auki buhun dawar shi uku da yayi saura mu saida kud'in mu had'a mu yi ma Na'ima kayan d'aki dasu, ina fatan haka ya yi mi ki? "Ya tambayi mahaifiyar Na'ima. Allah sarki Mahaifiyar Na'ima rasa abinda zata ce mai tayi, kai kawai tad'a ga mai. " Tom ai shike nan inda hakan yayi mata ku tashi mu tafi yace ma sauran abokan tafiyar nasa, " Yau saura kwana goma d'aurin auran Na'ima kamar yadda yayyan Mahaifinta su ka ce. Na'ima zaune kusa da Mahaifiyarta so ta ke tayi mata maganar auranta da gali ganin lokaci nata gabatowa amma tanajin ba kinta yayi nau yi bazata iya ba, can dai ta daure ta ce" Mama!" Kai mahaifiyar Na'ima ta d'ago tana kallan ta alamun inajinki.Na'ima kuwa cikin rawar baki ta fara magana kamar haka "Dama mama ni bawai auran Yaya gali bane bana so, a'a wallahi na hak'ura kawai dai ina duba maganar da baba yayi ne yana gab da barin nuniya beyarda ko bayan ranshi in auri Yaya gali ba, amma naji kin yi shiru da maganar gashi lokaci sai tafiya yake" Tom Na'ima wallahi ba wai nayi shiru bane ,a'a rashin mafitane ya sani yin shirun dole, amma Na'ima ya kike gani zanyi ki fad'amin? ". Mahaifiyar Na'ima kamar zatayi kuka tai maganar. Na'ima shiru ta yi sannam ta ce "Mama ko gidan nan zamu saidane mu tashi mu koma inda basu sani ba?" Da sauri mama ta d'ago kai tana kallan Na'ima,ta ce "Na'ima mu saida gidan nan mu koma ina da zama ga tarin k'annan ki? " Na'ima za tayi magana ne sallamar Hassan ta hanata. Mama ko da murnarta ganin Hassana ta ce " Kai-kai sannu da zuwa maraba Hassan kai ne yau agarin, lallaikam ,Na'ima shimfid'a mai tabarma" Hassana ckin dariyar shi ya ce " Wallahi mama ni ne kin ganni sai yau, naso in zo ayi addu'ar bakwai dani amma Allah be nu faba" Bakomai Hassan "cewar mama. Hassana kallan Na'ima yayi ya ce" k'anwata ya akaine naga ba akulani ba tun da nashigo?" Mahaifiyar Na'ima ce taba Hassan amsa da cewa"Na'ima nacikin damuwa Hassan ko ince munacikin damuwa,naji dad'in dawowarka wallahi muna cikin damuwa sosai Hassan Nida Na'ima"Nan dai mahaifiyar Na'ima ta kwashe halin da suke ciki tafada ma Hassan kaf. Hassan shiru yayi yana nazarin inda za'abulloma lamarin dan yasan halin 'yan'uwan mahaifin Na'ima kaf, bayan dogon nazarin da Hassana yayi ya kalli Mahaifiyar Na'ima ya ce "Mama yanzu ke yadda za ki yi kina gani zasu aurar da yarinyar nan agun Wanda bata so, ba abinda zaki yi akai?"Tom Hassan ya zanyi?, Kana gani shi kan shi mahaifin yarinyar nan nuna mai suke kamar sun fishi iko da ita, tom bare kuma ni da basu d'aukan bakin komai ba " Hassana kallan Mahaifiyar Na'ima yayi ya ce "Idan kin yarda mama ni zan d'au Na'ima in kai ta gurin gwaggona ta Kaduna? " Mahaifiyar Na'ima kallan Na'ima ta yi ,sannan ta maida kallanta ga Hassan batare da shakkuba dan ta yadda da Hassan sosai ta ce"Badamuwa Hassan nasan bazaka kai Na'ima gurin da kasan zata cutu ba, na yarda na amince ka kai ta, amma tunanina d'aya ne in suka zo me zan ce masu?, ina zan ce masu na kai Na'ima Hassan?" "Tom mama ni dai yan zu sai in ga kamar wannan ita ka d'ai ce mafitar mu mafi sauki " Shiru mama tayi nawani lokaci ta ce "shikenan Hassan Allah yasa haka shi ne abinda yafi alkairi"Da ameen suka amsa. Wa she gari da wuri mama suka shirya tafiya kaduna kai Na'ima gurin gwaggon Hassan kamar yadda suka tsara, kasan cewar banisa tsakanin sabon yalwa da cikin garin kaduna yasa cikin awa (hour) daya suka k'arasa kaduna dan ma motar haya ce, Hassan yayi masu jagora har gidan gwaggonshi,kasan cewar Na'ima sun san juna da gwaggon cikin mutunci ta tar besu, bayan ta basu ruwa sun sha aka gaggaisa Hassan ya zayya ne ma gwaggo abinda yake tafe da su game da barin Na'ima da suke sonyi . "Allah sarki mutuwa kenan me to nan asiri bako mai karkiji ko mai zan rike Na'ima har izuwa lokacin da yayi muku " Godiya sosai mahaifiyar Na'ima ta yima gwaggon Hassan. "Haba ai anzama d'aya" cewar gwaggon Hassan d'in. Nan su kai sallahma suka tafi su ka bar Na'ima da gwaggon Hassan tare. Haka mahaifiyar Na'ima suka dawo sabon yalwa cikin fargabar abinda zata cema yayyan mijinta duk sanda suka zo game da d'aurin auran Na'imar. Yau kwanan Na'ima biyu kenan awajan gwaggon Hassan ,duk wani aiki kusan Na'ima ta d'auke ma gwaggo shi ,hakan yasa Na'ima ta shiga zuciyar gwaggo sosai. Yanzu haka Na'ima Zau ne ta ke tana wanke-wanke koda ta gama cigaba tayi da zama wajan wanke-wankan tayi tagumi hannu biyu, tunanin Mahaifiyarta duk ya da meta yadda zata k'arke da 'yan'uwan Mahaifinta in sunzo. Sannan asaninta basu da sauran abincin da fawa ko ya suke yi. Gwaggon Hassan dafa kafad'ar Na'ima tayi ta ce" Cire tagumin nan dan Allah bashi da kyau kinji Na'ima" Tom gwaggo wallahi abun ne yayi min yawa ga tunanin koya mama zata k'arke da yayyan babana ga tunanin kome suke ci oho, wallahi gwaggo harma narasa wane tunani zanyi"Gwaggo shiru tayi sannan ta ce "Na'ima za ki iya aikin cikin gida irin Wanda nake zuwa?" Sosai ma kuwa gwaggo ai nama samu abinda zan rika tai makamasu da shi" "Shikenan dama matar da nakema aiki tace in samarmata 'yar aiki k'awar ta na naima, inkina so sai in mata magana ki fara zuwa?" "Aiko inaso gwaggo nagodee "Cewar Na'ima cikin murnarta. Ai ko gwaggo na zuwa gidan da take aiki ta fada ma hajiyar gidan tasamu 'yar aikin da tace ta samar mata, take hajiya ta kira k'awar ta awaya ta fad'a mata tasamu 'yar aikin. Godiya k'awar hajiyar tayi ta ce "zata iya fara zuwa aiki gobe " Aiko koda gwaggo ta dawo gida ta sanar da Na'ima ta hada kayan ta gobe zata fara aikin, kuma acan zata zauna, duk da Na'ima bata so zaman can ba bata nuna ma gwaggo ba godiya tayi mata sosai. Washe gari gwaggo tare da Na'ima su ka tafi gidan da take aiki, suna zuwa ko hajiya suwaiba tasa yaran aikinta yaraka Na'ima gidan hajiya Rahina wadda zata yima aiki, koda ya kaita a palon ya ce ta Zauna ta jira hajiyar kafin ta sakko tasan da zuwan ta" Na'ima ta dad'e sosai kafin hajiya Rahina ta sakko, amma abin mamaki hajiya tazo ta wuce ta ga ban Na'ima amma bata saniba "keeeee!" Hajiyar takira su nan Na'ima amma Na'ima ta shiga duniyar tunani bata jiba. Ciikin tsawa hajiya Rahina ta sake cewa "keee bakya ji ne?" Cikin furgici Na'ima ta tawo daga duniyar tunanin da ta fad'a ta ce "Wallahi banji bane yi hak'uri dan Allah ina kwana?" Shiru hajiya tayi tana kallan Na'ima nawani lokaci sannan ta ce" Lafiya ,yasu nan ki?, 'yar nan kaduna ce ke? " "Sunana Na'ima muna Zaune ne a sabon yalwa kusa da jaji" Kai hajiyar ta jinjina ,sannan ta ce "Kinnsan aikin da za ki min ? "A'a bansani ba" "Ok zaki rika min Shara da goge-goge sai wanke- wanke, zan rika baki dubu sha biyar duk wata yayi miki? " "Nagodee sosai yayi mommy " cewar Na'ima. Yau kwanan Na'ima uku da fara aiki kuma yau yake saura kwana uku d'au rin auran ta da gali kamar yadda yayyan babanta suka sa, hakan yasa hankalin Na'ima yata shi sosai duk Wanda yaga Na'ima ko be son taba kallo daya zai mata yagano cikin damuwa take. Can ko sabon yalwa fad'in damuwar da Mahaifiyar Na'ima take sai Allah ,ta yi bak'i taramai sosai kullum cikin zullumi take na zuwan 'yan'uwan Mijinta, yanzu haka Zau ne take akan dadduma ta idar da sallah, sallamar su binta ce tadawo da ita daga tunanin da ta ke ciki. Bak'aramin furgici mama ta shiga ba ganin su Ya'u, amma sai ta danne suka gaggaisa , bayan sun gama gaggaisawa ne, Binta ta ce "Tom Mariya ga kayan lefan Na'ima nan mun kawo" bud'e akwa tin Binta tayi tana nuna ma Mahaifiyar Na'ima kayan, atamfofi ne guda shida d'aya ce cotton amma sauran duk roba ne Sai ta kalmi d'aya hijab d'aya. Bayan Binta ta gama nuna ma Mahaifiyar Na'ima ne ta ce " Gashi nan Mariya ku yi hak'urin abunda babu in ta shi ga yayi mata kin san de yaran nan basana ace gare shi ba "Yayi ma k'okari" cewar ya'u. Binta ko taji gaba da cewa " Yaya Jimmai ta ce ace maku daga an d'aura aure za azo atafi da amarya kin san hanyar tamu Sai ahankali..." Mahaifiyar Na'ima dai ta kasa cewa komai,ganin haka Binta ta ce "Mariya baki ce komai ba?" Mahaifiyar Na'ima dai bata tankaba dan batasan me zatace ba. Ya'u Wanda mahaifin Na'ima ke bimawa ya ce "Rabu da ita Binta, ko tayi magana ko kar tayi mude mun bada sa k'on da akabamu akace mubada ku tashi mu tafi" Binta da bataga Na'ima kallan Mahaifiyar Na'imar ta yi ta ce "Mariya wai In Na'imar ne Banganta ba ?" Mahaifiyar Na'ima nan ma banza tayi da su. kwafa Ya'u yayi ya ce" ku mu je" Yau juma'a kuma yau yakama ranar d'aurin auran Na'ima da gali kamar yadda akasa, haka ko ta kasance anadawowa sallar juma'a aka d'aura auran Na'ima da gali, bayan gama d'aurin auran ne badadad'ewa ba masu d'akko amarya suka kamo hanya zuwa d'aukar Amarya. Mahaifiyar Na'ima na zaune cikin fargaba da tashin hankali dan yaune d'aurin auran Na'ima kamar yadda suka ce. Mahaifiyar Na'ima na nan zaune cikin fargabar yadda zasu kaya da Iyayan Na'ima masu d'aukar amarya suka shigo............ 🛥️ ABDURRAHIM🛥️ MATUK'IN JIRGIN RUWA NE (RENEW) 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚* Na Fadila Sani Bakori Page 4 & 5 Da bud'ar su su ka shigo gidan. Mahaifiyar Na'ima cikin fad'uwar gaba tafito daga d'aki. D'aya daga cikin masu d'aukar Amaryar ce ta ce "Tom Mariya yau dai Allah yayi Na'ima ta zama matar gali, afito mana da amarya sauri muke kin san hanyar tamu". Mahaifiyar Na'ima shiru tayi,sannan ta Binta ta ce"Binta d'an shigo daga ciki muyi magana."Binta binta tayi batare da tunanin komai ba tashiga. Bayan Binta ta shiga d'akin Mahaifiyar Na'ima ne, Mahaifiyar Na'ima ta kalli Binta ta ce" Binta banfa san inda Na'ima take ba" Wani uban ashar Binta tayi ta ce" wallahi Mariya tun daga ni sai ke ki fito da Na'ima kafin su yaya Ya'u suji maganar nan!" Wani banzan kallo Mahaifiyar Na'ima tayi ma Binta ta ce "Kowa zaki fad'amawa ki je ki fad'a mai Binta nace miki bansan inda Na'ima takeba". Tana kai wa nan tajuya tayi tafiyar ta. " Binta waya ta d'auka ta kira jimmai uwar ango ta fad'a mata abinda Mariya tace. Uwar ango wanda take amazaunin yayyar mahaifin Na'ima,cikin fushi ta ce "Binta ku jirani ganinan zuwa"Daya ke banisa tsakanin tudun malam da sabon yalwa hakan yasa cikin k'ank'anin lokaci jimmai ta iso." Tun kafin Jimmai ta k'arasa shigowa gidan take fad'in" ke Mariya duk inda kika kai Na'ima kiyi gaggawar d'akko ta kafin in shigo, dan wallahi in har na shigo banga Na'ima ba sai kin san dani ki ke, dan Yahaya ma bai isaba bare ke karan ka'da miya" Allah sarki da yake Mahaifiyar Na'ima bata saba rigima ba, jikinta kota ina rawa yake. Jimmai ko na zuwa ta shak'i wuyan Mahaifiyar Na'ima ta ce"Mariya wallahi ko zaki mutu ba zan sakeki ba sai kin fad'a min ina ki ka kai Na'ima?" Wujijjiga Mahaifiyar Na'ima Jimmai take da duk k'arfin ta, masu hankali ne daga cikin wa inda suka zo d'aukar amaryar sukaga in sukabar jimmai zata yima mariya illa, in abun yazo da k'arar kwana ma ta kashe ta. Dak'ar aka b'anb'are Jimmmai daga jikin Mariya, dan bada wasa ta shak'e taba. "Dan Allah ku bar ni da ita."A'a yaya Jimmai ki b'arta, mu bata nan da kwana biyu mugani "cewar Binta. Jimmai da kallan Mahaifiyar Na'ima tayi ta ce "Mariya kwana biyu na baki wallahi duk inda ki ka kai Na'ima ki kawota kafin nan da kwana biyu, in kuma bahaka Hmmmm". 'Yan d'aukar Amarya ko haka aka hak'ura aka koma ba amarya. Allah sarki mahaifiyar Na'ima ranar kusan kwana tayi kuka saboda bak'in cikin abinda Jimmai taimata yaranta na tayata. Aiko washe gari dawuri Mahaifiyar Na'ima ta shirya ta nufi kaduna. bata tsaya ko ina ba sai gidan gwaggon Hassan, lokacin ita kuma gwaggo tayi shirin zuwa gidan da take aiki.Gwaggon Hassan da mamaki take kallan Mahaifiyar Na'ima ta ce "Kai Mariya ke ce da wuri haka,Allah dai yasa lafiya,amma daga ganin zuwan nan nasan banawa bane, dan haka zo muje in kaiki gidan da Na'imar ke aiki" Aiki kuma gwaggo?" Nan dai kwaggo ta fahimtar da mahaifiyar Na'ima dalilin aikin nata dan ta taimakamusu ne. mahaifiyar Na'ima bata wani damuwa ba saboda tasan gwaggo bazata kai Na'ima inda zata cutu b. Koda su gwaggo suka isa gidan da Na'ima ke aiki, mai gadin gidan sukai ma magana yakakira masu Na'ima. Na'ima ko kullum damuwarta k'ara k'aruwa take, gafargabar auran ta, tana cikin wannan tunanin ne, mai gadin gidan yazo yace meta tayi bak'i. Na'ima Cikin fargabar kosu waye ke nai manta tafita. Koda ta hangi mamar ta cikin fad'uwar gaba ta k'arasa inda suke,dan daga ganin zuwan bana lafiya bane. "Oyoyo mamana ,sannun ku da zuwa".Cewar Na'ima.Nan dai suka gama gaggaisawa,Sannan Mahaifiyar Na'ima ta kalli Na'ima ta ce"Na'ima sauri nake je ki d'auko kayanki mu tafi"Mama lafiya dai ko? "Mahaifiyar Na'ima kallan Na'ima tayi ta ce "Yi abinda nace sauri nake na baro k'annanki gida su kad'ai"Na'ima cikin rawar muraya ta ce " Tom mama amma hajiyar bata nan tafita sai dai in tadawo, kinga ni kadai ce a gidan ba zaiyuwu inbarmata gida ba ba kowa" Shiru Mahaifiyar Na'ima tayi ,sannan

Chapter 1 of 8