ta ce "Na'ima bazan iya jiran kiba, amma daga tadawo ki dawo gida yau yau d'in nan, dan jiya Iyayanki suka d'aura maki aure"
Na'ima bak'aramin jarimta tayi ba dan danne damuwarta dan kar mahaifiyarta tafahimci hakinda take, amma ainihin gaskiya ita kadai tasan halin da takeciki.Na'ima kallan Mahaifiyarta tayi ta ce
"Mama tom ya maganar da Baba yayi, kafin yabar duniya? "
"Na'ima ki yi abinda nace kinji, Iyayanki jiya bakalar cin mutuncin da basuyimin ba"Na'ima cikin damuwa ta ce
"Shikenan mama zan dawo yau d'in in tadawo, amma mama kina son auran ne yanzu?"
"Tom Na'ima ya zanyi?, amma maganar so ko bazan tab'a so auranki da gali ba"Shikenan mama sai nazo"
Na'ima koda tadawo gida , bak'in ciki yawa yayi mata, ga haushin abinda akai ma Mahaifiyarta ga takaicin auran da aka ce an d'aura mata da gali. Palon ta zauna tana ta kuka, har hajiya Rahina ta shi go amma bataji shigowar ta ba"
Hajiya Rahima kusada Na'ima ta zauna amma abin mamaki har yanzu Na'ima bata ji motsin hajiya a polon ba, kukan ta kawai takeyi a bunta.
"Ke! lafiyar ki? "Cewar hajiya Rahina.Sannan taci gaba da cewa
"Nalura da ke , tun da kika zo gidan nan baki da wani aiki sai tunani, tom idan bazaki iya aikin ba zan samu wata, inda abun naki k'arak'aruwa yake, yanzu abun ya zama sai kizo ki zauna ki tamin kuka, ina Tambayar ki kuma kin min shiru kin zuba min ido, tom wallahi bazan d'auka ba"
Na'ima shiru tayi tana sauraran hajiya, sannan ta ce"ki yi hak'uri dan Allah"
Zama hajiya Rahina tayi tana fuskantar Na'ima sannan ta ce"Me yasaki kuka yanzu nake son in sani? "
"Dama mama nace tazo yanzu tace wai duk abinda na keyi in dawo gida yau, tom ni kuma bana son komawa gidan"Saboda me?" Cewar hajiya Rahina. "Saboda 'yan'uwan babana sun min aure ni kuma bana son auran da su kai min,kuma Babana ma kafin ya mutu yace kar su auramin Yaya gali"
"meyasa bakya son galin? "
"Saboda babana yana gaf da mutuwa yace ko bayan ranshi be yarda ba in auri yaya gali"Na'ima hannun hajiya Rahina ta kama kamar za tai kuka ta ce "Hajiya dan girman Allah kitaimakan ki kaini, kasar nan danaji kina cewa za akawo miki kaya kuma zasu dad'e basu dawo ba, dan Allah hajiya hakane kawai zai sa in gujema auran Yaya gali da Babana ma baya so "Shiru Hajiya Rahina tayi ,sannan ta ce "Zan taimakeki amma sai naji cikakkyan tarihinki, naji dalilin dayasa mahaifinki be so ki auri d'an'uwanki?"
Shiru Na'ima tayi kamar mai tunani, sannan tafara magana kamar haka.
"Kakana Abdullahi yanada mata biyu Jamila da kuma Habi, Habi ita ce matar kakana ta fari dan haka ita ta haifama kakana manyan 'ya'ya, gwaggo Jimmai itace babbar yarinyar kakana sai baba Ya'u sai baba Kabiru sai autar su Binta. An haifi gwaggo binta ba dad'ewa kakana ya auro mahaifiyar babana wato kakata, kakata tun da ta haifi babana bata sake haihuwa ba, kuma ta haifi babana badadewa Allah yayi ma kakana Abdullahi rasuwa, babana yataso cikin maraicin uba dan duk wani abu da yayye sukema k'annan su tom su baba Ya'u basama babana, amma fa in dai akazo maganar aiki tom akokacin zasu ce ai shine K'arami, da kakata ta lura wahala zata kassara d'anta d'aya tilo sai ta kai shi sabon yalwa almajiranci. Bakalar fad'an da su baba Rabi'u basu yiba amma kakata ta share, bayan tafiyar babana almajiranci badad'ewa kakata ta kwanta k'aramar jinya, wadda tazama sana diyar ajalin ta, babana yayi nisa da karatu alhamdulillah, saidai kash suna cikin karatu Allah yayi ma malamin nasu mutuwa shima sakamakon k'aramar jinyar dayayi, tom daga nan ne fa Babana ya koma aikin gona ana biyan shi, ahaka ahaka Allah yabud'a mai har ya tsaya da k'afarsa, cikin k'ank'anin lokaci ya sai fili yafara gini, yana cikin gini Allah yahad'a shi da mamana,kasan cewar itama 'yar'uwar babana ce ma'ana marainiya ce babana bai wani sha wuya ba aka bashi auran mamana. Tun da su baba Ya'u sukazo bikin sukaga abinda babana yayi na kud'i tom daga nan fa duk wani Wanda da muwar kudi ta tashi mai sai ya d'aurata akan babana, in ta kai cemiki har sai da sukaga sun karya shi sannan Suka b'arshi.
Masha Allah Allah ya azurta mahaifina da haihuwa dan mu biyar ya Haifa, ni sai k'anwata Aisha, sai Aminu da umar sai auta auwal. In ta k'aice miki tunda gali d'an gidan gwaggo jimmai ya fara nuna yana sona babana yahanani zuwa hidimar wajan su, dalili ko duk yarinyar da gali ya d'auka ido akanta sai ya lala tata.
Yaje gidan yari (prison) yafi ak'irga amma abin sai abinda yayi gaba, dan yanzu ma har sata yake"Numfasawa Na'ima tayi sannan ta ce ci gaba da ce wa "Wannan shine dalilin da ni da babana bama son aurena da yaya gali"
Nan Na'ima taitaba hajiya labarinta har izuwa auran ta da aka d'aura da gali kamar yadda mahaifiyarta tasanar da ita.
Hajiya Rahina kallan Na'ima ta yi ta ce "Na'ima naji labarinki kuma koni ban goyi bayan ki zaman aure da mutum kamar gali ba, dan haka zan kira gwaggonki in shaida mata in har ta yadda tom ba shakka dake za a, sai dai fa a jirgin ruwa zakuyi tafiyar,kuma tafiya ce ta wata shida kin yadda?"Eh Mommy na yadda "
Waya hajiya Rahila ta d'auka ta kira k'awarta hajiya suwaiba akan dan Allah ta turo mata da gwaggo mai ai kinta.
Driver hajiya suwaiba tasa ya kawo gwaggo har gidan hajiya Rahila.
Bayan sun gaisane. Hajiya Rahila ta kalli gwaggo ta ce" Gwaggo nasan zakiyi mama kin kiran ki da nayi, tom Na'ima ce tarok'eni wata alfarma atafi da ita Landon kinsan acan ake kawomin kaya"Nan dai hajiya tafad'ama gwaggo duk yadda su kai da Na'ima,ta d'aura da cewa"Gwaggo kin san HALIBIZ SHOPPING MELL tawace tom dama in dai shekara tazo tsakiya muna ai kawa akawomana kaya, kin san tafiyar ta jirgin ruwa ce, tom suna yin wata shida ahanya,tom kin aminta atafi da Na'ima ko ko?, amma fa ni badani za ai tafiyar ba.........
🛥️ ABDURRAHIM🛥️
MATUK'IN JIRGIN RUWA NE.(RENEW)
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚*
Na
Fadila Sani Bakori
Page 6 & 7
Hajiya Rahila kallan gwaggo tayi jin tayi shiru ta ce" Gwaggo bakice komai ba, kin yarda in tura Na'ima London d'akko kayan sabuwar shekara da zamuyi ? "Numfasawa gwaggo ta yi ta ce,
"Tom Hajiya bawai nayi shiru bane a'a wallahi kin san Na'ima ba yarinyata bace shine nake gani kibani nan da zuwa gobe inje in tambayi mahaifiyar Na'ima inta yarda tom."
Kafin Hajiya Rahila tai wata magana, Na'ima ta yi wuf ta ce.
"Ahalin yanzu mamana tana cikin k'uncin rayuwa, yayyan babana sun tasata gaba akan auran nan, tun da gwaggo kikaga mama tace sai dai in dawo gida akai ni d'akin yaya gali, tom wallahi bak'aramin furgita ta sukayi ba".
Na'ima kamar za tai kuka ta maida kallanta ga Hajiya Rahina ta ce,
"Hajiya kima girman Allah ki amshi tayin tafiyar nan tawa ko dan in cika burin mahaifina na rashin auran nan da har ya komama ga Allah baya son shi. "
Hajiya Rahina gwaggo ta kallah ta ce,
"Tom gwaggo kin ji abinda Na'ima tace,kin aminta ayi tafiyar nan da ita?"Tom, ni bawai nak'i tafiyar Na'ima bane, a'a wallahi kawai dai kin san yanzu muna wata irin rayuwa ne, sai ka yi Abu da niyar taimako nan gaba yazamarma matsala"
Kai hajiya Rahina ta jinjina ta ce"Hakane gaskiya,dannima bazan d'auki Na'ima ba bada amincewar kowa ba in kaita wannan kasa mai nisa kuma tafiya ce bata yau ko goba ba."
Gwaggo kallan Na'ima ta yi da ke Shirin fasa kuka ta ce,
"Badamuwa Hajiya amanar Na'ima ahannu na take dama, dan haka na amince Allah yasa jin shirun da zasuyi ya zamo silar rigujewar auran"
"Ameen ya Allah"cewar Hajiya Rahina,sannan ta kalli Na'ima ta ce,
"Ki je gida ki shirya dan goba ne tafiyar"Kai Na'ima ta girgiza ta ce "A'a babuwani shiri da zanyima"
Duk wani shiri da Na'ima za tayi tayi shi, fatan ganin gobe kawai take.
Washe gari Na'ima zau ne a gaban Hajiya Rahila tagama duk wani shiri da za tayi.
Hajiya Rahila kallan Na'ima ta yi ta ce,
"Tom Na'ima Allah yakiyaye hanya Allah ya sauke ku lafaya, yanzu ga driver nan zai kai ki airport kaya ko mai da komai anriga angama shiryawa daga kun je sai tafowa, amma fa zaki sha sanyi yarinya, zakiyi kalar tafiyar da nake sha'awa Amma ni tsoro yahananiyi danni tsoran jirgin ruwa na ke"
Murmushi Na'ima ta yi ta ce "Shekara d'aya da wata hud'u zamuyi ko hajiya?"
Dariya sosai hajiya Rahila tayi, sannan ta ce "Yanzu ai a jirgin sama zaku, wajan dawowa ne dai zaku dawo a jirgin ruwa saboda kaya".
Driver Hajiya Rahila ya kai Na'ima airport,suna isa ko babu da d'ewa jirginsu ya tashi.
"Ikon Allah sai kallo wai yau ni ce a London"Na'ima al'ajabi duk ya isheta lokacinda ta take kwance kan kadon hotel d'in da zata kwana .
Kwance take akan tafkekean gadon hotel d'in da Jamilu abokin tafiyar ta ya kamamusu.
Juyi kawai take sanyin k'asar da tunanin halin da Mahaifiyarta ta ke ciki yahanata bacci.
Washe gari koda Na'ima ta tashi kasa wanka tayi tsabar sanyin da take ji, Jamilu da kan shi ya kawo mata tea da wani farfesun nama.
"Tashi ki k'arya dan yanzu zaku Kama hanya, Amma fa zakiyi doguwar tafiya ,dan Allah in tambaye ki mana?"Jamilu ya tambayi Na'ima.
"Ina jinka"cewar Na'ima.
"Dan Allah me yajawo miki wan nan wahalar haka?".
Na'ima kallan Jamilu tayi
da mamaki akan fuskarta ta ce "Wahala kuma tame fa?".
"Ta tafiya a jirgin ruwa mana, waya fad'a maki su kaya dole sai an tsare su, ai daga anba direbobin shike nan, ba sai an had'a da mai tsaron kaya ba",Jamilu ya fad'a.
"Tom nima sha'awar tafiyar ce kawai" Na'ima ta fad'a ma Jamilu haka ne kawai dan ta wuce maganar.
Na'ima da Jamilu tsaye suna sallama dan yanzu jirgin su zai kama hanya. Jamilu kallan Na'ima yayi ya ce,
"Tom shikenan Na'imatu Allah ya isomana dake lafiya, Allah ya karemana ke gaba da baya".
"Ameen "ta amsa.
Jamil bashi yabar gurin ba har sai da yaga jirgin su ya tashi sannan.
Can b'angaran Mahaifiyar Na'ima kuwa bayan ta koma gida, tun tanasaran zuwan Na'ima har ta gaji, har ta fara tunanin k'ila hajiyar ce bata dawo ba sai gobe, tom Allah yasa dai goban ma tazo da wuri, kafin guyababbun Iyayanta su zo.
Washe gari ma haka ya faru ba Na'ima ba dalilinta, Mahaifiyar Na'ima ganin har rana tayi Na'ima bata dawo ba abin sai ya fara bata tsoro, dan tasan tun da tacema Na'ima tadawo tom ba'abinda zai hanata da wowa. "Tom ko dai an sace tane" Haka Mahaifiyar Na'ima tai ta tik'a da warwara akan rashin dawowar Na'imar.
Mahaifiyar Na'ima nanan kwance tana tunanin rashin dawowar Na'ima tajiyo sallamar su Ya'u ,cikin kid'ima Mahaifiyar Na'ima ta fito da tab'arma a hannunta tana k'ok'arin shimfid'amu su , Ya'u ne yad'aga mata hannu ya ce.
"Dakata Mariya,bazama ya kawo mu ba, mun zo ne kibamu 'yarmu kuma matar d'an mu ko kuma wallahi Mariya hukuma zata rabamu da ke".
"Wallahi! Wallhi!! Wallhi!!!" Sonawa narantse Ya'u?" Cewar Jimmai.
"Sau uku, yaya jimmai".
Kai Jimmai ta karkad'a ta ce,
"Wannan shine gargad'i nak'arshe Mariya, ki fitomin da surukata in kuma bahakaba tom zaki san ruwa ba tsaran kwando bane Wallahi"Tana kai wa nan tai gaba.
Ya'u kusa da Mahaifiyar Na'ima yadawo ya ce ahankali yadda Jimmai bazataji ba"Mariya ni zan tai makeki,inma baki son auran Na'imar ne, amma sai da sharad'in in kin aminta zaki auran?".
Wani mugun kallo mahaifiyar Na'ima tayi mai ta ce "Ba aure atsakanina da kai amma ba abin mamaki bane dan ka fad'i haka inda nasan akwai k'arancin rashin sani atattare da kai".
"Kamarya Mariya bangane ba,me kuma ya kawo rashin sani anan? "
"Nufina bakasan haramun ba bakasan halaliiba".
"Haba Mariya mai Ya kawo maganar haramun kuma da halali ana.... ".
Maganar Jimmai da Ya'u yaji ce tasa ya canza abinda yayi niyar fad'a tahan yar cewa "kin ji dai abinda nace maki kinada damar samun mafita, in kinyarda in kuma kink'i tom ya rage naki"Yana kai wa nan yayi gaba abinsa.
washe gari da sassafe mahaifiyar Na'ima ta nufi kaduna, sakamakon wani munmunan mafarki da tayi akan Na'ima.
Gidan gwaggo Mahaifiyar Na'ima ta sauka.
Cikin gwaggo sai da ya kad'a dan ganin mahaifiyar Na'ima da tayi, dan bata san abinda zata ce mata ba game da tafiyar da Na'ima tayi bada izinin taba, haka ma fa na d'aukar mata yarinya na kaita gidan aiki bada sanin taba,kuma koda tazo bata nunamata damuwa ba, ai ko yanzu da kunya in ce mata bata k'asar, tom inama zance mata taje. Haka gwaggo tai ta maganar zuci.
Muryar mahaifiyar Na'ima ce ta dawo da gwaggo daga tunanin da ta lula.
"Gwaggo ki yi hak'uri karkiga nadaimeki da sintiri ,wallahi abubuwane ne sun kacamemin gashi itama Na'imar da nace tayi hak'uri tazo a kaita d'akin mijin ta shine tak'i zuwa, ni hattasani ma afargaba, na fara tunanin ko lafiya"
"Lafiya"cewar gwaggo da batasan ma abinda ta ce ba.
"Alhamdulillah ,dama wani mafarkine nayi akan Na'imar mai ban tsoro, shine nazo ingani ko lafiya, daga nan kuma k'afarta-k'afata".
Wani irin kuka cikin gwaggo ya yi, cikin rashin sanin abinda zatace ma ta ta ce "Tom tashi mu je gidan da take aikin".
B'angaran Na'ima kuwa al'ajabi duk ya isheta wai yau ita ce acikin jirgin ruwa.
Su Na'ima ba su yi tafiya mai nisa ba,suka farajin
Wani irin k'ara daga k'asan jirgin kamar ana balla Abu, cikin kid'ima captain d'in jirgin ya fara sanarwa jirgi yasamu matsala, kafin kace wani abu, jirgin yafara mangar-mangar.
Na'ima kuka tafarayi ganin ruwa yafara tud'ad'owa cikin jirgin.
Ahankali ahankali jirgin yafara k'asa ruwa yana k'ara shigowa cikin jirgin sosai kamar ana k'ara antayo shi.........
🛥️ ABDURRAHIM 🛥️
MATUK'IN JIRGIN RUW NE (RENEW)
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚*
Na
Fadila Sani Bakori.
Page 8 & 9
Banda salati da kuka ba'abinda Na'ima ke iya yi.
Shugaban jirgin ruwan, (captain) ya bada rigar ruwa (life jacket) ya ce
Aba duk matan dake jirgin su sa,sannan ya k'ara da cewa"mu na so dan Allah kowa ya kwantar da hankalin sa, ba abinda zai faru dan mun kai sanarwa (report) ababbar headquarter ta mu, za akawomana agaji yanzun nan" cewar captain d'in jirgin.
Duk maganar da yake cikin speaker yake yinta, in bahaka ba ba kowa zai ji shi ba, dan jirgin nada girma sosai balefi.
Bak'aramin razana mutanan dake cikin jirgin nan su kayiba, ganin jirgin nasu saura k'iris ya nutse, gashi har yanzu basuga alamun masu ceto ba.
Shikan shi captain d'in jirgin yagama sadak'arwa.
B'ak'aramin rud'ani captain d'in ya shigaba, ganin b'angaran matuk'an masu control d'in jirgin gabad'ayan shi ya nutse cikin ruwan .
Gudu mutanan kusa da b'angaran da ya rufta suketayi suna dawowa b'angaran da yake da dama -dama.
Allah sarki kusan baka ganin mutane sai kawu nan su kakegani.
Bindiga carptin d'in ya sa ya harbi kan shi, dan ba zai jure ganin ruftawar jirgin gabad'aya ba.
Rabin jirgin duk ya nutse, duk wata hayaniya da mutane ke yi duk sun baryi, banda mutun uku daga cikin matuk'an jirgin da su kai saura, duk dasu tsabar amanace irin ta su ta turawa, amma su sun iya ruwan da zasu iya taimakon kansu, tom amma su turawa sunada amana duk runtsi duk wuya sai dai amutu tare badai su gudu ba, dan duk sun iya ruwa sannan ga rigar ruwa amma sai sukak'isawa suka ba matan sukasa. Allah sarki su kansu mutum ukun da su kai saura sunriga sun gama galabaita suna ji suna gani haka suka sadaukar da rayuwar su, tsabar alk'awari irin nasu, Mutum d'aya ne da shima yagama galabaita, hannu yake ta d'agawa sakamakon k'arar jirgin da yake ji yana nufo su, dan ko ba afad'a ba yasan su akakawo ma agaji.
Jin jirgin nata shawagi yasa ya lalibo usir d'insa yahura yasan k'arar zata ankarar da su dan yasan sakamakom ruwan da yasha kansu ne yahana masu kawo masu agajin sugan su.Tun k'arfin shi yahura usir din.
D'aya daga cikin masu kawo agajin ne yajiyo k'arar husird'in,
nuna ma sauran abokan tafiyar ya yi inda yajiyo k'arar .
Da saurin su su ka k'araso in da su ke ji yo k'arar hura usir d'in.
Shiko Azera da yajiyo alamun tahowar su cigaba da hura usir d'in yayi yana bubbuga hannun shi aruwan da d'an sauran k'arfin da yarage mai.
ta ke suka gane inda al'amarin yafaru, suka k'arasa wajan.
Cikin ikon Allah su kai ta fito da mutane daga cikin jirgin da had'arin yafaru, basuyi wani wahalar fito da mutanan ba, k'asan cewar yawancin matan duk asaman ruwa suke, saboda rigar ruwa da akabasu sukasa .
Sun d'au dogon lokaci suna fito da mutane acikin ruwan, inda duk Wanda aka ciro asibiti ake wucewa da su.
Ikon Allah duk iya sa idona danayi banga Na'ima ba cikin muta nan da aka ciro, har suka gama cirowa, ban ga alamu da sauran mutum ba, dan har na'urorin su saida suka haska basuga komai ba, sannan suka nufi da wa inda aka ciro asibiti.
Tafe yake cikin d'an ma dai-dai cin jirjin sa. Matashi wanda kallo d'aya zakai mai ka tabbatar da kwanciyar hankalin ya wadatai, dan dagani ba sai an fad'aba kallo d'aya za kai mai kagane hakan, Sauri yake yak'osa yaje gida saboda uzirin da yake da shi agidan, wani tudu-tudu yake gani na tun karo shi da alama koma meye igiyar ruwa ce ta jawo shi.
Tun kafin abun ya iso kusa da shi ya tabbatar da mutun ne, parking ya yi da jirgin nasa acikin ruwan, sannan yasa wata sanda dake cikin jirgin yarika jawo abun nan ahankali, sai dai tun kafin ya iso wajan shi ya tabbatar da mutum ne, dan yaga rigar ruwa ajikin mutum d'in ,shi ne dalilin da yasa bai nutseba acikin ruwan.
Cikin jirgin sa ya sata sannan ya tub'e mata rigar ruwan da ke jikin ta.
Al'ajabi ne ya isheshi ya ce " ikon Allah tom wannan kuma daga ina mutum cikin ruwa kuma mace"
Tafiya yake yana sake- saken yadda zai yi da ita, kai ko dai in yadda ta ne, tom in kuma fa nayadda ta kuma bata mutu ba fa?"
Nan dai ya yanke ma kan shi shawara akan ya kai ta gidansa alabashi yakira alheri ta dubata ta tagani ko tanada rai.
Bashi ya isa gida ba sai shida na yamma (6: 00pm) lokacin garin yafara duhu.
Yana shiga gidan ya d'akko ta daga mota kasan cewar yana fita gab'ar ruwan yayi parking a inda suke aje jiragan su. Ya d'auki drop d'in mota har gidan sa."
Bayan ya kwantar da ita ne nalura she Na'ima ce.
Waya ya d'auka ya turama alheri sako tazo yanzu yana son ganin ta.
Cikin mintina kad'an alheri ta iso gidan.
Alheri kallan shi tayi damamki ta ce,
"Abdurrahim wannan fa, ina kasamota?. "
Banza Abdurrahim yayi da ita kamar bazai amsa mata ba, sannan ya ce ahankali kamar an mai dole "Tsintarta nayi, ki dubata mana"
Alheri da mamaki take kallan Abdurrahim , so take tak'ara tambayar shi amma bataga fuskar hakan ba, dan haka taja bakin ta tayi shiru, ta fara aikin da yakawota.
Alheri tad'an kwashi mintina tana dubata, sannan takalli Abdurrahim ta ce,
"Abdurrahim k'alau take inajin furgicin da tayi ne yasata cikin wannan yanayin amma bari ina zuwa akwai allurar da zan mata yanzu.
Cikin k'ank'anin lokaci Alheri tadawo da allura tayima Na'ima, sannan ta ce mai zata tafi gida.
" Ok, thanks" Abdurrahim ya ce ma alheri sannan yazaro kud'i dayawa yabata.
Alheri kallan Abdurrahim ta yi ta ce "Haba Abdurrahima ai kawuce haka aguna, kodai kana kokwanton matsayinka k aguna ne? "
Kai Abdurrahim ya girgiza mata alamun a'a t"Tom nagoge" Abdurrahim ya ce mata ahankali cikin natsuwar shi da rashin son hayaniyarshi.
Abdurrahim tun da yaba Na'ima awa d'aya bata farkaba kamar yadda alheri tace mai, tashi yayi ya shiga d'akin dake kusa da nata, yayi sallah ya shiga kitchen yayi makan shi abu mai saukin ci, sannan yakoma d'akin da ya kwantar da ita ya kuma dubawa ko ta tashi ,ganin bata tashi ba ya nufi d'akin shi.
Cikin tsakiyar dare Na'ima ta farka, da wata irin k'ara mai rud'arwa, ihu take tana salati sai tangal tangal take ita kad'ai akan gadon.
Abdurrahim jin k'arar mutum cikin furgici yafito dan shi harga Allah ya manta da wata yarinya agidansa.
"Keee!,keee wata irin mahaukaciya ce" cewar Abdurrahim da kwatakwata baya son hayaniya.
Na'ima ko da batason abinda takeyi ba dan har yanzu ba wai tadawo natsuwarta ba ne.
Sannan jin tsawar da Abdurrahim yayi mata sai ya k'ara rud'ata. Wata uban k'aratasaki Wanda yasa Abdurrahim rufe kunnuwan sa da sauri, yana ja baya.
Lura dayayi kamar ba ahayyacin ta ta ke ba yasa shi Saurin barin gurin. Dan shi mutum ne Wanda baya son hayaniya, kallo d'aya zakai mai kagano hakan.
Ruwa mai sanyi Abdurrahim ya d'akko ya watsa mata.sannan Na'ima ta sauke ajiyar zuciya wadda ko ba afad'a ba kasan tadawo ahayyacin ta. Sannan ta jawa wani uban numfashi .Na'ima
Abdurrahim ta k'ure da ido tana kallo, can kuma ta ce"Bawan Allah dan Allah inane nan? "
Abdurrahim banza da ita yayi yajuya zai koma d'akin shi, tayi saurin sakkowa daga kan gadon ta ce dan Allah Bawan Allah ina nake?,ko na mutu ne" Harga Allah Na'ima take tambayar Abdurrahim duk da tambayar ta ta ta so ta sa shi dariya, cigaba yayi da tafiyar shi, itako tacigaba da tambayoyin ta. " Bawan Allah dan Allah ya akai nafita daga cikin ruwan nan?."
Abdurrahim agogon hannun shi ya nuna mata, sannan ya kwantar da fuskar shi akan hannuna shi yanuna mata gadon da ya ajeta alamun taje ta kwanta .Duk da Hannu yake mata kwatancan, kamar dai yadda kurame ke yi.
Ba yadda Na'ima ta iya haka takoma gadon ta kwanta da tunanin yadda za ta iya magana da kurma in gari ya waye. "Kai Allah dai kasa a Nigeria nake ma, shikenan yanzu inaji ina gani zan kwanta gidan wani kuma d'aki d'aya, tom ai kamar d'aki d'ayan ne inda daga yafito zai ganni aiko bazanyi bacci ba ma, dan ba'abinda natsana kamar wani yaga kwanciyata" Duk ita kadai ke maganarta cikin zuciya, ahaka dai bacci ya kwasheta ga wata bala in tattar yunwa da take ji.
Washe gari Abdurrahim yagama duk abinda zaiyi amma bata farkaba.
Alokacin da Na'ima tafarka lokacin shi kuma Abdurrahim yagama abinda zai yi har yafita aikin shi.Gidan ko rufe abin shi yayi kamar yadda yasaba in zai fita aiki.
Da wata irin yunwa Na'ima ta farka dan cikin tama har gefe daya na rike mata, zama tacigaba dayi akan gadon tun tana tunanin fitowar Wanda tagani jiya har ta kasa jurewa ta tashi taje kusa da k'ofar d'akin shi,sai dai da alama yafita saboda tatura k'ofar taji arufe take.
Kasa daurewa tayi ta fita daga d'akin ,kitchen ta shiga Allah ya tai maketa tasamu wani tea da yasha ya rage sai dai ya huce sai wainar kwai itama da alama yaci yarage ne,ta d'auka ta cinye tass sanna ta d'an ji sauk'in yunwar, sai dai me tana gama ci amai ya biyo baya aiko taita kwarashi agun.
Rasa abinda zata kwashe aman tayi ta shiga tolait d'in