Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 8
batadasu"tom shikenan sai ki bari duk radda ki ka samu kud'in jirgin Sai ki tafi" Na'ima fusge hannunta tayi daga ruk'on da Abdurrahim yayi mata dan in batsabar rainin hankali ba inazata samu kud'in jirgi, dazai ce wani innasamu kud'i ta tafi. Abdurrahim ko bin bayan Na'ima yayi da kallo, yana tunanin me ke damunsa,yarasa gane takamaimai abin da ke damunshi akanta,tun radda yayi ido biyu da halittun jikin Na'ima yarasa natsuwarshi, ko baccin kirki kwana biyun nan baya samu daga yarufe ido ta yake gani, yanzu haka ya dawo daga rakon Hafiz ne shine ya dawo gida ya huta ya kuma to zali da halitarta da ta kasa fitar mai a ido tai mai tsaye a cikin sak'on tsakiyar gwagwalwar kanshi ,hakan sai ya k'ara da gulamai lissafi ,tom shi ne fa baima san ya isa gurinta ba dan da tayi gangancin yin shiru........ Masha Allah Na'ima sun dawo zama da Abdurrahim kamar yadda suke da, magana batacika had'asu ba dan sai tayi kwana biyu bata gan shi ba sai dai motsin shi da take ji na fitarshi da dawowarshi. Sai dai shi Abdurrahim ana shi b'angaran abin yayi mai tsanani gaba d'aya halittun Na'ima sun hana shi sukuni,dan yanzu ko tsayuwar kirki bai iya wa tsabar ciwan da mararshi ke mai, yanzu haka yau kwanan shi biyu agida bai fita ba dan tsayuwa nanaiman gagararshi yadda yake jin marar na k'ulle mai. Na'ima zaune tayi shiru tunanin duniya duk ya isheta, dan ita yanzu bata da burin da ya wuce taganta agidansu gaban mahaifiyarta dan ahalin da take jinta yanzu har auran galin ma zata iya hak'ura dashi ta zauna dashi ta amshi k'addararta na auranshi. Na'ima na nan zaune tunanin Abdurrahim ya fad'o mata,tana tunanin abin da ya hanashi fitowa kwana biyu,dan yau kwana biyu ke nan Na'ima batasa Abdurrahim a idonta ba. Tunani tafara yi ko ta je ta d'an lek'a tagani lafiya,Na'ima tashi tayi tana tafiya ahankali-ahankali kamar wata b'arauniya cikin sand'a Na'ima ta tura d'akin da Abdurrahim yake kwance,ciki ta hango shi akwance dafe da mararshi dan yanzu ko abu zai d'auka sai dai da rarrafe yake zuwa yad'akko.Kallo d'aya zakai mai kagane ciwan banawasa bane dagaske yake, cikin tausaya mai dan Na'ima akwai tausai ta k'arasa inda yake kwance tace"Sannu, bakada lafiya ne ?" Kai Abdurrahim ya d'agamata, dan ganinta da yayi sai ya ji ciwan nak'ara yun k'uro mai. Na'ima cikin tausayawa ta ce"Ayyah sannu" juya mata baya Abdurrahim yayi dan gabad'aya ji ya yi yana nai man sumewa ganinta da ya ke yi tsaye akanshi, itako Na'ima da batasan dalilin juyawar ba d'ayan b'angaran ta koma tace"ko in kawoma abincine ? "Nan ma banza Abdurrahim yayi da ita yasake juyawa inda ta baro. Allah sarki Na'ima ganitake tsabar ciwone yasashi juye-juyan, ai bata gaji ba sake binsa tayi d'ayan b'angaran tace"Sannu in kawoma abinc..." maganar kakarewa tayi sakamakon jawota d'in da Abdurrahim yayi. Na'ima cikin furgicin jin yadda Abdurrahim ya fusgota ta ce"Kai ma girman Allah kasake ni" dan Na'ima sosai ta tsorata da ruk'on da Abdurrahim yayi mata, Abdurrahim cikin sanyayar murya irin ta Wanda ya gama galabaita ya ce "ba abin da zan miki ,dan Allah ki taimakan zan iya rasa rayuwata ,kuma Kinga kema bakisan ina zaki zauna ba "duk maganar nan da Abdurrahim yake yana rik'e da Na'ima. Na'ima cikin rawar baki ta ce "tom ni mai zanma?" Tace mai tana yunk'urin tashi daga jikin shi ,shi kuma yana k'ara riketa.Abdurrahim kallan Na'ima yayi irin ki tausayamin ya ce "nan d'inki kawai zan tab'a" yanuna mata kirjinta, cikin kid'ima dajin kalaman shi Na'ima ta dage ta fusge daga ruk'on dayayi mata taruga dagudunta falo ,sai dai kafin ta zauna ta ga Abdurrahim agabanta,Abdurrahim be tsaya wata-wata ba ko jin abin da Na'ima ke cewa d'akkota ya yi cak tana ihu tana rikon shi dan son da ya ke ma iyayan shi kar ya yi ma ta komai, amma ina Abdurrahim be saurari Na'ima ba sai da ya kaita har d'akinshi.Na'ima na ihu tana rok'on Abdurrahim amma ina.... Cikin lokaci k'alilan Abdurrahim ya keta mutunci Na'ima. Wasu irin hawaye ke zuba a fuskar Na'ima masu zafi gaba d'aya gani takema rayuwarta bata da amfani, take tunanin auran da aka d'aura mata ya fad'o mata arai ,yanzu mai zata cema gali, kai cona danakasa yin hak'uri da abin da 'yan'uwan mahaifina suka zab'amin, mahaifiyata ta hak'ura mai yasa ni ban yadda da auran gali kaddarata bace ,ashe wanna munannan k'addararce tasa nakasa hak'ura na ta kura hajiya sai anyi fatiyar nan dani. Na'ima tuntana kuka ahankali hatta dawoyi da k'arfinta, Abdurrahim ko yana jinta amma yagaza cemata komai duk da maganganun da tayi acikin zuciya tayisu bajinta yayi ba. Abdurrahim yakasa cema Na'ima komai girgiza mata kai kawai yakeyi alamun tayi shiru, amma kamar yana k'ara zigata Abdurrahim bayan Na'ima ya dawo yana bubbugawa kad'an-kad'an,dole tasa Na'ima tayi shiru bawai dan tayi niyar shirun ba.Gashi tayi tayi Abdurrahim ya barta ta sauka akan gadon yak'i haka ta hak'ura dole ta kwanta ba dan ta soba ahaka har bacci b'arawo ya d'auketa. Washegari Abdurrahim har ya ta shi Na'ima bata ta shi ba, lallab'awa yayi yasakko daga kan gadon gudun kar ta tashi, wanka yayi agugguje dan so yake ya gudu kafin Na'ima ta tashi,dan nauyin had'a ido yakeyi da ita. Abdurrahim yafita da jimawa sannan Na'ima ta ta shi, koda ta tashi Na'ima ta tuno abin da ya faro da ita kuka ta fasa ta koma takwanta tsabar bak'in cikin halinda taga kanta ciki, tayi kuka kamar ba gobe har tagaji ta lalla shi kanta tayi shiru ta lallab'a ta ta shi taje tatsarkake jikinta. Gaba d'aya bata jin dad'in jikinta gawani irin tsanar zaman gidan da take ji. Abdurrahim kamar yadda yasaba dawowa haka yadawo, kwance ya isketa a falon kanta na kallan sama iya tausai Na'ima taba Abdurrahim, k'arasawa yayi inda take kwance, Na'ima naganin shi tayi saurin d'auke kanta cikin fad'uwar gaba, kallanta Abdurrahim yayi yace"Tabbas ni mai lefine wajan ki, dan girman Allah kiyi hak'uri ni kaina bantab'a aikata zina ba wallahi sai akanki" Na'ima cikin kuka ta ce "insha Allah sai Allah ya sakamin ,haihuwar fari da za kai insha Allahhu mace zaka haifa kuma insha Allah sai Allah yasa ammata fiye da abin da kai min "Na'ima na kaiwa nan ta tashi tabar mai gun ta shiga d'akin da yake ama zaunin na ta. Fita Abdurrahim yayi dan siyo ma Na'ima wani abun ko allah zaisa tayi hak'uri ta yafemai ,dan ya girgiza da addu'ar da tai mai.Tsabar saurin Abdurrahim yake ne yasa yamanta bai rufe gidan ba ita kuma Na'ima jin fitar shi datayi yasa ta dowa falon amma da mamaki sai taga k'ofar falon abud'e bai rufe ba. alhamdullilah tace dan tun d'azu taso barin gidan taji k'ofar a rufe. Na'ima da hanzarinta ta tashi ko kayanta bata tsaya d'auka ba ta fita daga gidan da saurinta ,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,, 🛥️ABDURRAHIM🛥️ MATUK'IN JIRGIN RUW NE. 📚📚🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚📚🖊 Na Fadila Sani Bakori Page 24 & 25 Cikin sauri Na'ima ta bud'e d'an ma daidai cin get d'in ta fita. Sauri kawai ta ke yi ko gabanta ba ta gani sosai so ta ke kawai taga tafita daga Unguwar gabad'aya. Abdurrahim na cikin wata plaza yana siyayya ya hango Na'ima sai sauri ta ke, banza yayi da ita saida ya gama abin da yake yi amma duk yana han gyanta daga inda yake.Bayan Abdurrahim ya gama biyan kud'in siyayyar da yayi ne ya kin kimi kayan da ya siya yasa su a mota. Abdurrahim bin Na'ima ya rik'ayi abaya -abaya, ita ko Na'ima zuwa yanzu ta fara gajiya dan gabad'aya ba ta jin k'arfin jikinta ga yunwa inda bata ci komai ba, tafiya Na'ima ta ke tana haki dan wani irin amai take jin yana zuwa mata tsabar yunwar da take ji kuma tsabar naci ta dage sai tafiya take yi wadda bata san inda zata ba, duk inda yayi mata nan take bi. Abdurrahim ko parking d'in motar shi yayi yana han gyanta daga inda yake inda tafiyar kad'an-kad'an take yi, wani bak'in kare Na'ima ta hango ai tun kafin ta gama tantance babbane ko k'arami ta juya da gudunta ta koma baya. Abdurrahim ko duk yana zaune a cikin mota yana han gyanta, shi ko karan bin ta shi ma yayi da na shi gudin,ihu Na'im ke yi tun k'arfinta da sauri Abdurrahim ya bud'e mata murfin matar ta shiga, dan ita bata san koma waye ba tana ganin ceto kawai ta afka. Ayyah Na'ima inda ki ka fito ki ka koma😅. Ciki gigin tsoran da Na'ima ta ke tace" dan Allah ka taimaka min wallahi ban san ina zani ba" tom badamuwa"Abdurrahim yace cikin k'asa da murya gudin kar ta gane shi, aiko da ya ke Na'ima ba cikin isassar natsuwarta take ba ba ta ga ne Abdurrahim d'in ba har sai da suka shiga gidan ya bud'e mata murfin motar ya ce "fi to"Sannan jin muryar shi da Na'ima tayi yasa tayi saurin d'aga kai ta kallai tace"kai ne dama ? Tom Wallahi bazan fi to daga Motar nan ba ai na riga na gama zaman gidanka inda kai baka da amana ba zan tab'a komawa ba har abada". Abdurrahim zamanshi yayi a Motar, ya da d'e yana kallan Na'ima ita kuma sai kau da kai take alamun bata son kallan da yake mata, cikin natsuwa Abdurrahim yafara magana kamar haka "Na ji ba za ki koma gidana ba yanzu ina zaki tom? "Ba bu ruwanka da inda zani" Cewar Na'ima. Shiru Abdurrahim yayi sannan zuwa can ya ce" Shikenan za ki iya tafiya, sai dai ki sa ni nan ba Nigeria ba ce abin da ya fi abin da naimiki zai iya faruwa da ke, sannan za ki iya had'uwa da masu yan kar kai dan mu nan da ki ke gani akwai restaurant d'in farfesun naman mutane amma in kin ga za ki tafi tom badamuwa za ki iya tafiya"Shiru Na'ima tayi tana tunani sannan zuwa can tace"dan Allah ana yanka mutane da gaske anan? Ka fad'a min gaskiya"Kin ga ne je ki kawai, ni da ma taimakonki naso yi dan kar nukan garin nan da ki ke gani zasu iya cin ye ki ma kafin ki had'u da masu yanka muta nan"Abdurrahim na kai wa nan ya bud'e murfin mutar zai fita, da sauri Na'ima ta kamo hannun shi tace" dan Allah tom zan koma gidan naka wallahi ina tsoran kar nukan garin nan da masu yanka mutane dan Allah zan bika amma dan Allah ba za ka sake cin amanata ba?" Kai Abdurrahim ya d'aga ma Na'ima alamun Eh, "yauwa tom na gode,nama kusa yafema k'ila" Cewar Na'ima. "Tom na gode" Ta re suka shiga falon gidan, kayan da Abdurrahim ya siya ma Na'ima ne ya d'akko ya aje mata a gabanta ya ce"Ga kaya nan na siyo mi ki ki ta sawa abin ki" Na'ima kallan kayan ta yi tace"Ni dai ba kaya nake so ba So nake ka taimaka ka mai da ni garinmu dan Allah"Na'ima ta ida maganar tana zubar da hawaye. Shiru Abdurrahim ya yi na d'an lokaci sannan ya ce"Ki bari k'arshen watan nan ne zan je gida ba kin ce Kaduna ki ke ba? " Kai Na'ima ta d'aga ma Abdurrahim alamun Eh.Abdurrahim yaci gaba da cewa" tom ki bari sai mu wuce tare" A'a ni dai ina so in fara wuce wa" Cewar Na'ima, "Shikenan sai kin dawo in ki na da kud'in Jirgi" Abdurrahim na kaiwa nan ya tashi yayi shigewar shi ciki ya barta. Na'ima ma tashi tayi ta shiga kitchen ta sa mar ma kanta abin da zata ci. Yau Sati hud'u ke nan da faruwar abin da yafaru tsakanin Abdurrahim da Na'ima.Alhamdulillah ko hannun Na'ima Abdurrahim bai sake ta b'awa ba, sai dai zaman nasu ya canza salo, dan yanzu sukan sauna suyi hira bakamar da ba, hakan ya d'an rage ma Na'ima abin da ke damunta dan wani lotun in ta gaji da zaman gidan har addu'a take Abdurrahim ya shigo tasamu abokin hira. Yanzu haka zaune suke suna hira duk da yawancin hirar Na'ima ke yin ta. Na'ima kallan Abdurrahim ta yi tace"yauwa dan Allah me ya sa ka kori alheri a gidan nan? "Kallanta Abdurrahim ya yi ya ce"Na koreta kuma?". "Tom banaga ta zo tana kuka ba ta kwashe kayanta"Oh! Babanta ne yarasu" Ayyah shi yasa ta ta tafi..." Bugun k'ofar gidan da suka ji ana yi ne yasa su kai shiru ,Abdurrahim yana mamaki dan ba wanda su ka zai zo wajan shi, tashi yiyi ya je ya bud'e k'ofar cikin mamaki ya ke kallanta dan shi ya ma manta da ita, kallan shi alheri tayi tace" dama irin damuwar da ka ke cewa kayi dani kenan ko? Daddyna ya mutu amma so d'aya ka kira kai min ta'aziya me ya sa?" Abdurrahim hannun alheri ya rik'o ya ce"Yi hakuri zo mu je ciki in fad'a mi ki dalilin rashin kiranki da banyi ba" Hannunta Abdurrahim ya kamo har Falon, haka nan Na'ima sai ta ji ba ta ji da d'in hannun alheri da Abdurrahim ya rik'e ba. Alheri ko zama tayi tana wani cicin magani ganin Na'ima da tayi dan ta d'auka tsawan wannan lokacin ta wuce. Abdurrahim ko kallan alheri yayi ya ce "kin gane ko abin da yasa ban kiraki ba na yarda Wayana ne tom shi ne fa narasa number ki"Shikenan ba damuwa"Cewar alheri.Alheri nuna Na'ima tayi tace" Abdurrahim wannan yarinyar tana nan kenan?"Kai Abdurrahim ya jinjina ma ta.Alheri ta ce"Ta'iya girki? "Shiru Abdurrahim yayi kamar ba zai bata amsa ba sai kuma yace"in ta'iya ya akai?" "Dama na gajine isowata kenan ta d'an dafamin ko indomie ce"Abdurrahim kallan Na'ima yayi ya ce "Na'ima je ki dafa mata indomie taci kin ji yanzu ta iso" Haka nan Na'ima sai ta ji ranta ya b'aci sa ta d'in da Abdurrahim yayi ta yi ma alheri girki . Ba dan Na'ima ta so ba ta shiga kitchen ta soya ma ta indomie ta kawo mata. Tun daga ranar yazamana Na'ima ita ke masu girki dukan su, tsakanin ta da alheri ko sai dai harara, amma magana ko gaisuwa bata had'asu, tsakanin Na'ima da Abdurrahim ko sun dawo kusan 'yar gidan jiya hakan yasa Na'ima sai ta ji duk haushin su ta ke ji gashi yawan cin 'yan kwanan nan bata jin k'arfin jikinta ga wani irin ciwan kai da ke damunta ga yawan fad'uwar gaba da ke da munta ,hakan yasa yau ko girkin ma ta kasa yi ta had'a tea ta sha tai kwanciyar ta . Na'ima na nan kwance alheri ta shigo gidan wacce dawowarta kenan daga aiki, ko kallan ina Na'ima take alheri bata yi ba, wayarta ta d'akko tana danne-danne sai zuwa can tace" kee ina abincina?" Banza Na'ima ta yi da ita, alheri kallan Na'ima ta yi da mamaki wai wannan abarce take ma magana tai banza da ita, Alheri cikin d'aga muraya tace"kee ba da ke na ke ba, ina abincina na ce?"Na'ima gudun fitina dan ba k'arfin jikinta ta ke ji ba yasa tata shi zata bar ma alheri falon. Fusgota alheri tayi sannan ta turata tun k'arfinta zuwa hanyar kitchen d'in.Da yake Na'ima ba k'arfin jikinta ta ke ji ba yasa ta fad'i gun ta ciki,wata uwar k'ara Na'ima ta yi wadda sai da ta ba alheri tsoro, ko da alheri ta duba Na'ima sai taga kamar suma ta yi, sauri alheri tayi ta bar gidan. Fitar alheri kamar da minti goma Abdurrahim ya shigo gidan, kwance ya ga Na'ima kamar ba rai cikin gigita Abdurrahim ya idasa gurinta yana jijjigata yana kiran sunan ta amma ina batasan yana yi ba tashi yayi da sauri ya shiga kitchen d'in ya d'ebo ruwa ya yayyafamata .Wata doguwar ajiyar zuciya Na'ima ta sa ki ta bud'e idonta tana kallan shi sai kuma tasa kuka, Abdurrahim jawota yayi yajikin shi ya rungumeta yana tambayar ta me ya sa meta, banza Na'ima tayi dashi ta ci gaba da kukan ta, ga kanta da ya ke wani irin jijjuyawa ma ta ga cikinta tana jin ya k'ulle ma ta. K'ok'arin tashi tayi daga jikin shi shi kuma yana k'ara riketa, ya ce"Lafiya wai me ya samekine haka?" Na'ima cikin sanyi ta ce " Ka sakan d'aki zani" Abdurrahim sakin Na'ima yayi yana kallanta, taku bai fi biyu ta yi ba ta yanke jiki ta fad'i agun, da sauri Abdurrahim ya matso ya d'auketa yayi motar shi da ita, a mota ya sata ya kaita wani k'aramin asibiti da ke kusa da su, aiko yana kai ta aka amseta, cikin k'ank'anin lokaci likitan ya gano abin da ke damun Na'ima. Likitan takardar scanning d'in ya ba Abdurrahim da magunguna yace "ko wana lokaci in ta farka zasu iya tafiya" Abdurrahim ko bai tsaya duba ta kardar scanning d'in da likitan ya bashi ba yace ma doctor zai d'auke ta tafarka agida sabo da yana sauri ne" likitan bai mu sa mai ba. Abdurrahim ko da suka shiga gida bedroom d'in shi yayi da Na'ima ya kwantar da ita, tsayawa yayi yana k'aremata kallo haske yaga ta yi mai sosai sai 'yar k'iba da ta d'an yi,Abdurrahim kwanciya yayi gefan Na'ima shima ya jawota jikin shi yana shafa kanta sosai yake jin Na'ima na burge shi ,haka Abdurrahim ya yi ta wasa da sassan jikin Na'ima ,haka ya tsinci kan shi cikin nishad'i,Abdurrahim matse Na'ima ya kuma yi sosai ajikin shi rigarta ya d'aga dan ba abin da ahalin yanzu yaji yana son gani kamar k'irjinta sosai shaid'an ke k'ara k'awata mai ita. Ita ko Na'ima da bata san abin da ke faruwa ba k'ara shigema Abdurrahim tayi jin d'umin jikinshi sai yayi mata dad'i. Abdurrahim ko jin Na'ima nak'a shige mai ai sai yak'ara kaimi wajan abun da yakeyi mata, bakinsu ya had'e guri d'aya yana mata zazzafan kiss,haka Abdurrahim yayi yadda ya ke so da Na'ima . Bayan komai yalafane Na'ima ta fara jin yungurin amai tashi tayi dakyar tashiga toilet d'in shi tai ta kwara amai. Alheri da dawowarta kenan gidan ta kardar scanning d'in da ta gani da magunguna ta k'arasa ta d'akko tana dubawa. "Ciki"Alheri tace da k'arfi, Abdurrahim ko dama Na'ima na shiga toilet d'in shi ya fita daga d'akin ya shiga nata toilet d'in da sauri yayi abin da zai yi dan so ya ke yayi ya kintsa jikinshi dan lokacin sallar magriba yayi, yana fitowa yazira jallabiyar shi yafita falon, alokacin kuma alheri ta d'auko takardar scanning d'in Na'ima tana gani, dai-dai lokacin da take cewa" ciki" Abdurrahim ya fito ya kuma ji abin da ta ce. Abdurrahim Kallan rashin fahimta yayi ma alheri ya ce" Ciki kuma?Wa ke da cikin?" Yarinyar da ka ke tare da ita mana, yarinyar da ka ce wai taimakonta ka ke yi ita ke d'auke da cikin shege na tsawan wata d'aya ga shi nan likita ya rubuta muku baku gani bane........... A yi hak'uri da wrong typing 🙏🏻🙏🏻🙏🏻 NI NA YI NAN DAN NAGA ABDURRAHIM YA TSORATA DA JIN LABARIN CIKIN NA'IMA🏃‍♀️🏃‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️ 🛥️ABDURRAHIM🛥️ MATUK'IN JIRGIN RUWA NE. 📚📚🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚📚🖊 Na Fadila Sani Bakori 1)SO NE SILA 2)OGA HABIB 3)IN DA RAI 4)DAGA ALLAH KO D'AURA MA KAI 5)RAYUWAR HAIDAR 6) MENALLYN DADDY 7) ABDURRAHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE Page 26 & 27 Cikin rud'ewa Abdurrahim ya fusge takardar hannun alheri yana karantawa, wata irin zufa Abdurrahim yaji tana keto mai kota ina, kallan alheri yayi ya ce" alheri ban yarda ba zo ki dubata dan Allah wannan ma ai shirman banza ne yaza ai ma ce wai tana da ciki akan me?" Wani irin kallo alheri ke ma Abdurrahim, Abdurrahim ko hannun alheri ya kamo ya ce"dan Allah mu je ki duba yarinyar nan danni ban yarda ba Wallahi ace wai tana da ciki" cikin masifa alheri ta fusge hannunta tace" bazan duba ta ba d'in!" tana kaiwa nan ta d'au wayarta tafita daga gidan gabad'aya. Abdurrahim zagaye d'akin ya ke ta yi dan ya ka zama, ana cikin wannan yanayin ne sai ga Na'ima ta fito falon dan samar makanta abin da zata ci dan wata irin yunwa take ji, garashin k'arfin jiki da ke damunta. Ko inda Abdurrahim yake Na'ima bata kalla ba kitchen ta shiga ta had'a tea tai zamanta kitchen d'in tasha,abin da ya ba Na'ima mamaki duk dad'e war da tayi a kitchen d'in haka ta dawo ta iske Abdurrahim yana ta kewaye falon da takardar scanning d'in ahannun shi inda ita Na'ima batasan ya kai ta asibiti ba inda har yakaita ya dawo da ita bata cikin hayyacinta. Kallan shi Na'ima ta yi ta gefan ido ta tana tunanin ta kardar da ya ke ta faman juyawa ko ta meye ,juwa ta yi zata tafi ," keeee! " Abdurrahim yakira ta, juyowa Na'ima tayi tana kallan shi dan raban da yayi mata irin wannan kiran harta manta. "Wai dagaske ne ki na da ciki?"Abdurrahim ya tambayi Na'ima yana mai k'ureta da ido. "Allah yarabani yin ciki dama fatan da ka ke min kenan? Tom Wallahi bazan tab'a yin ciki ba" cikin kuka Na'ima ta idasa maganar tana kaiwa nan ta juya zata shige bedroom d'inta , da sauri Abdurrahim ya rik'o hannunta ya ce" ke duba nan ki gani" yana nuna mata takardar scanning d'in , zaro ido Na'ima tayi tace"tom ai bani Na'imar ba, wannan bakaga Na'ima Abdurrahim akasa ba? Ni kuma Na'ima Yahaya sunana, kuma ni akan me ma zan yi wani ciki"Na'ima ta fad'i maganar tana turo baki ta ci gaba da cewa "San nan ni ban je asibiti ba" "Zauna "Abdurrahim yace mata. Zama Na'ima ta yi kamar yadda ya'umar ce ta. Shiru Abdurrahim yayi yana kallan Na'ima sannan ya ce"Kin san dai bana miki wasa ko? "Kai Na'ima ta d'aga mai alamun Eh, " Yauwa tom, jiya ba ki da lafiya kika fad'i anan gun ki ka suma na d'auke ki na kaiki asibiti tom shi ne bayan an dubaki suka ban takardar scanning d'in nan da kike gani" zin bur Na'ima tayi ta ta shi tace" Ni wallahi k'arya suke min banda wani ciki!"cikin kuka Na'ima ta fad'i maganar.Shiru Abdurrahim ya yi nad'an lokaci yana tunanin maganarta fa kamar gaskiya ce, yaza ai ace tana da ciki , kallan ta Abdurrahim yayi yace "dai na kuka ni ma da ma banyarda ba"Amsar takardar scanning d'in Abdurrahim ya yi daga hannun Na'ima ya yayyagata ya ce" tom ki dai na kuka kin ga ma na yayyaga takardar ko dan in tabbar masu da k'arya suk dan haka share hawayan kinga dai na yaga takardar ko?" Kai Na'ima ta d'aga mai, "yauwa tom yanzu ki je kiya sallah abinki kin ji?" "Tom "Na'ima tace, sannan ta ta shi ta shiga ciki. Na'ima cikin kwanciyar hankali taci gaba da gudanar da komai nata dan ita bata yarda tana da wani ciki ba kamar yadda shi ma Abdurrahim bai yarda ba. Yau kwana biyu kenan dayin maganar cikin Na'ima kuma cikin kwana biyun bawani zama gida Abdurrahim ya ke ba, lokacin da zai dawo Na'ima kuma ta yi bacci. Yau ta kama weekend Abdurrahim na gida tun safe yake falon dan so ya ke kawai yaga Na'ima , jin shirun ta yi yawa yasa Ya lek'ata yaga ko ta ta shi amma still akwance ya iddata, matsawa Abdurrahim yayi ya d'an bubbugi k'afarta, ido Na'ima ta bud'e tana kallan shi ya ce"Ya dai ? Na ji shiru baki tashi ba" "ban da lafiya ne"Na'ima tace mai." Me ke damunki?" Abdurrahim ya tambaye ta, "jikina ko'ina ke min

Chapter 6 of 8