ciwo, dan Allah yau she zaka k'asar ku d'in? Na k'osa in koma gida ina son ganin Mamana" Shiru Abdurrahim yayi sannan ya ce"tom tashi ki yi breakfast sai muyi maganar zuwa gidan", cikin sauri Na'ima ta sakko, kitchen ta shiga ta samarma kanta abin da zataci dan haka nan sai taji yau tagaji da tea d'in,haka yasa ta dafa taliya, saidai be fi loma uku taci ba ta ji amai nataso mata, da sauri ta ta shi ta k'arasa toilet sai da ta amayar da ita duka.
Abdurrahim shiru yayi yana tunanin In ba zai mantaba ya tab'a jin mommyshi nafirar daga tasamu ciki duk abin da taci sai tayi aman shi. Bayan Na'ima ta fito daga toilet d'in ne Abdurrahim ya kalleta ya ce" Shirya mu je asibiti"
Cikin k'ank'a nin lokaci Na'ima ta shirya. Wani baban asibiti Abdurrahim yakai Na'ima , yayi ma doctor bayanin abin da suke so, wata roba doctor yabashi yace taje tayi fitsari takawo mai. Abdurrahim inda yabar Na'ima yaje yakai mata rob'ar yanuna mata toilet yace taje tayi fitsari takawo mai, amsa Na'ima tayi taje tayi fitsarin takawoma Abdurrahim shi kuma yakaima doctor, wani d'an ma dai-dai cin d'akin dake cikin office d'in doctor yashiga yayi aune aunan da zai yi sannan ya kawo ma Abdurrahim wata takardar Wanda ke d'auke da bayanan abin da ke damun Na'ima,Cikin fargaba Abdurrahim ya bud'e takardar, sai dai abin da waccan takardar ta fad'a mai ita wannan ta fad'a mai. Abdurrahim cikin zuciyar shi yake mai-mai ta innalillahi'wa inna ilaihirraj'un! Abdurrahim ya dad'e zaune dafe da kai yana tunanin mafita, doctor ya tambaya za'a iya mata theater acire cikin, magani doctor yabashi yace inda cikin baiyi kwari ba yabata tasha zai zube, kud'i dayawa Abdurrahim yaba doctor yakoma inda yabar Na'ima wadda batasan me ke faruwa ba.
Abdurrahim suna cikin mota suna tafiya ya kalli Na'ima ya ce" dama maganar da doctor nan gaskiya ne ashe?" Wata magana?" Na'ima ta tambaya. "Maganar ciki mana" "Wayyo nashi ga uku ! , Da gaske ka ke?" cewar Na'ima idonta har ya kawo ruwa.
Abdurrahim kai ya jinjina mata ya ce"da gaske ne mana ,amma ki kwantar da hankakinki Allah ya kawomana mafita ga magani nan likitan ya bamu yace daga kin sha cikin zai zube" Ai Na'ima ko jin shi bata yi ba kukan ta kawai take yi, banza Abdurrahim yayi da ita har suka isa gida, Abdurrahim da kan shi ya je kitchen ya d'akko mata ruwa yakawo mata yace"amsa ki sha daga kin sha likitan yace cikin zai zube"Na'ima ko kallan Abdurrahim ba tai ba bare yasa ran zata amshi maganin daga hannun shi, kukanta kawai take yi mai tattare da nadamar biyema shawarar zuciya da tayi, dan tasan da tanaimi izinin mamarta bazata bari ta zo k'asar ba bare abin da yafaru da ita har ya faru da ita.
Na'ima kukanta taci gaba da yi tana cewa"wayyo ni ya zanyi in koma gida? Wayyo dan Allah ka tai makamin!" Maganin Abdurrahim ya k'ara mik'a ma Na'ima ya ce" na ce mi ki ki amsa ki sha zaki rabu da cikin yanzu-yanzun nan daga kinsha"Wayyo ni wallahi bazan sha ba sanadiyar mutuwar Jamila kenan, ni kam inajin tsoro inje in mutu!" Abdurrahim kai ya girgiza ya ce " ok ,ashe ko zaki haifi cikin agidanku ,daga nan kuma sai ki naimo Wanda yayi maki cikin!"Abdurrahim na kai wa nan yabar mata gidan ma gabad'aya.
Inda Abdurrahim ya bar Na'ima nan yadawo yasameta, kamar ya wuce sai kuma ya fasa ya dawo, gefanta ya zauna ya ce" Yau she ki ke son komawa gida?" Shiru Na'ima tayi da kukan da take tana kallan Abdurrahim.Shi kuma jin tayi shiru ya kuma cewa" yau she ki ke son koma gida na ce!?" Ni dai ba zan koma da ciki ba gaskiya mamana saita kashe ni, sai dai in da Kaga kai ne kai min ta k'arfi in za ka zo muje ka fad'amata gaskiyar yadda akai in da kaga ni dai ba laifina ba ne" kallan baki da hankali Abdurrahim yayi mata, sannan yace" Ni aina fita hak'inki in da na kawomiki magani kin k'i sha,amma in ki na so in rakaki tom kisha maganin nan sannan"Ni dai gaskiya bazan sha ba wallahi inje in mutu" kafad'a Abdurrahim yamak'e alamun ko ajikin shi, sannan ya tashi ya ce "ki shir ya cikin satin nan zaki koma" yana kai wa nan ya juya yayi tafiyar shi.Na'ima ko cikin kuka ta ce" Ni Wallahi ba zan je gida ba da wannan cikin"Okay, zamu gani "cewar Abdurrahim.
Da daddare koda Abdurrahim ya kwanta kasa bacci yayi dan yana tunanin anya kuwa in ya bar Na'ima ta tafi da cikin nan nan gaba baza asamu matsala ba inda tabbas yasan cikin shi ne, kai gara dai ya matsa mata koda tsiyane ta sha maganin cikin ya zube zai fi samun kwanciyar hankali, nan dai yayanke makan shi shawarar koda tsiya da safe sai ta sha maganin.
washegari Abdurrahim zaune a falo ya gama breakfast yana zaman jiran Na'ima tata shi, yana nan zau ne sai gata ta fito." Ina kwana"Na'ima tace mai "lafiya" Abdurrahim yace. Kitchen Na'ima taje ta had'o makanta tea dan shi ne kawai abin da take iya sha bata amayar ba, in ba shi ba komai ta ci sai tayi aman shi .
Tea d'in Na'ima ta d'akko ta zo falon ,Abdurrahim rik'e da wayarshi yana daddannawa amma kallan Na'ima ya ke afakaice har ta gama shan tea d'in.
"Kin gama shan tea d'in?" Abdurrahim ya tambayi Na'ima, kai Na'ima ta d'aga mai alamun Eh. "Am sa ki sha"Abdurrahim yamik'a mata maganin, amsa tayi tace"Maganin me ye?"
"ki sha magani ne" cewae Abdurrahim.Na'ima juya maganin tayi a hannunta tana kallo ta ce " ni gaskiya bazan sha maganin da bansan ko maganin me ye ba" Abdurrahim cikin jin haushin maganarta ya ce"Maganin zubar da cikin jikinki ne kuma dole ki sha wallahi!" Ni wallahi bazan sha ba" cewar Na'ima tana turo baki, Abdurrahim tashi zaune yayi daga shin gid'an da ke ya ce cikin muryar daga ji kasan ba wasa,
"Sha maganin nan na ce!" Idon Na'ima ruwa yafara kawowa ta ce"Ni dai dan Allah bazan sha ba" fusgota Abdurrahim yayi tadawo kusa dashi, kuka Na'ima ta fasa dan taji zafin musgowar da yayi mata. Abdurrahim zare ma Na'ima ido yayi ya ce"sha na ce!" Na'ima k'ara rik'e maganin tayi da k'arfi tace ni dai wallhi bazan tab'a sha ba".
Abdurrahim rik'e Na'ima yayi ya b'anb'are maganin ahannunta da k'arfin tsiya,sannan ya bud'e bakinta da tsiya ya tura mata magnin ya d'akko ruwa ya tsiyaya mata irin yadda ake ma yara d'ure ya matse hancinta,,, ,,,,,,,,,,,,
AYI HAK'URI DA WRONG TYPING 🙏🏻
🛥️ ABDURRAHIM🛥️
MATUK'IN JIRGIN RUWA NE
📚📚🅙︎𝗮𝗿𝘂j𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚📚🖊
Na
Fadila Sani Bakori.
Page 28 29
Na'ima cikin fitar hayyaci jin yadda Abdurrahim ya matse mata hanci ta fusge kanta ta furzar da maganin daga bakinta. Abdurrahim kallan ta yayi cikin b'acin rai ya ce"ba za ki sha ba Sabo da kina son cikin ko?" Kai Na'ima ta girgiza mai tace cikin jin wahalar matsar da ya yi mata" Ni Allah tsoran sha na ke kuma ni bana son cikin" Abdurrahim tsabar takaici rasa abin da zaice ma Na'ima ya yi, kawai sai yayi banza da ita yafita gidan, Na'ima ko d'akinta ta koma tana kukan ta kai cin cikin, gashi harga Allah tana tsoran zubar da cikin.
Abdurrahim kamar yadda yasaba dawowa haka ya dawo, zaune ya iske Na'ima a falon tayi tagumi, takardar hannun shi yawurga ma ta ya ce"Gashi nan ticket d'in jirgi ne gobe zaki tafi da safe dan haka ki shirya" Abdurrahim na kaiwa nan yayi tafiyar shi yabar Na'ima agun, Na'ima kamar za tai kuka ta ce "Ni wallahi bazan tafi da ciki ba" Abdurrahim yana jinta yayi banza da'ita.
Washegari da wuri Abdurrahim ya tashi dan shi ya matsu ya ga Na'ima tabar gidan dan jin cikin jikinta yake kamar wani kaya ne agun shi.Abdurrahimda kan shi ya shiga kitchen ya had'ama Na'ima abin kari (breakfast) amma shiru-shiru ba'alamun Na'ima zata fito, gashi har 9:15 Am, Abdurrahim tashi yayi da niyar zuwa ya tada Na'ima sai gata ta fito , dan dolece ma tasa ta fitowa amma batayi niyar tashi ba sai lokacin da yace mata ya wuce dan ita wallahi ba taga abin da zaisa ta koma da cika ba acewar ta,Na'ima ko inda Abdurrahim yake bata kalla ba dan ita ala dole wai fushi takeyi da shi, hanyar kitchen ta nufa Abdurrahim yace" Ga shi nan na had'ami ki" yana nuna mata tea d'in da ya had'amata, dawowa Na'ima tayi ta zauna tana sha kad'an-kad'an, " ki yi sauri ki gama lokaci zai k'ure" cewar Abdurrahim da yafad'i maganar ba alamun wasa." tom ni ai nace bazan je ba ko?"cewar Na'ima.
Abdurrahim tashi yayi daga kishin gid'an da ya ke ya ya kalli Na'ima ya ce" tom sai dai ki ne mi gurin zama amma Wallahi ba dai gidan nan ba, lokaci ya kusa k'urewa dan haka ki yi sauri Malama!"Na'ima ganin babu wasa a fuskar Abdurrahim yasa tace"tom bari in d'akko kayana dama nayi wanka"ko kallanta Abdurrahim be yi ba bare ta sa ran tanka mata, Na'ima na shiga d'akin ta sa key ta rufe k'ofar, Abdurrahim da mamaki yake kallan k'ofar dan be tab'a tunanin zata yi haka ba da sai dai ta tafi ahaka.
Abdurrahim tashi yayi yaje yana bubbuga K'ofar kamar zai b'alla ta ya ce"Na'ima ki bud'e k'ofar nan kar ki sa inyi asarar kud'in ticket d'ina, ki bude!" banza Na"ima tayi da Abdurrahim sai da ya gaji da bugawa dan kan shi sanna ya hak'ura.
Yau kwana biyu kenan da Na'ima ta rufe kanta a d'aki tak'i bud'ewa, Abdurrahim sai dai a falo ya ke kwana, jiya ma sai dai a plaza yaje ya sai kaya, inda tarufe d'akin da kayan nashi suke, tunanin yake tom inama take samun abinci dan yalura kamar cin abincinta yak'aru sosai, murmushi yayi dan tabbas yasan hasashan shi gaskiya ne, wayo ta ke yi sai taji futar shi sannan take fitowa tasamarma kanta abinci, tashi yayi yabud'e k'ofar falon da k'arfi sanna ya maida ya rufe batareda ya fita ba ya koma kitchen ya b'oye.
Na'ima ko dake d'aki taji alamun fitar Abdurrahim fitowar ta daga wanka kenan daga ita sai k'aramin towel tafito falon, kitchen ta nufa direct tana zuwa Abdurrahim ta gani tsaye a kitchen daga gani kasan jiran shigowarta yakeyi, Na'ima naganin Abdurrahim tajuya da gudu zata koma inda tafito amma ina gudu ba d'aya ba befi taku biyu tayi ba Abdurrahim ya cabketa, kara Na'ima tayi tana bashi hak'uri ta ce" ka yi hak'uri Allah zan tafi yau-yau d'in nan ma" Abdurrahim banza yayi da'ita ya d'auke ta cak yayi d'akin shi da ita duk irin hak'urin da Na'ima ke ba Abdurrahim be saurareta ba saida yayi yadda yaga dama da'ita, bayan komai ya lafa ne yace mata "Wallahi ko ki shirya ki tafi gobe ko kuma kullum sai nayi yadda naga dama dake zab'i yarage naki, kuma tun da nabiya miki kud'in jirgi ki ka sa nayi asararsu yanzu sai dai ki nemo me biya mi ki"Na'ima banza ta yi da Abdurrahim ta ci gaba da kukan bak'in cikin kusantar ta da yayi.
Abdurrahim ko a halin yanzu yana son zama da Na'ima saidai cikin jikinta yake tsoro inda yayi da ita tasha magani ya zuge tak'i ,kuma shi ma yanzu tsoran tasha maganin ma yakeyi kar aje asamu matsaka ta mutu kamar yadda tace,hakan yasa yake ganin gara kawai ta tafi.
Can cikin dare
Abdurrahim ya jiyo kukan Na'ima dan tun abin da ya faru tsakaninsu ta ke kuka har yanzu tak'i yin shiru, Abdurrahim ji yayi kamar ya shareta amma jin har yanzu kukan take yasa yatashi ya zura jallabiyar shi yafito, zaune ya isketa ta ta tura kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka, kusa da'ita Abdurrahim ya zauna ya tafata, amma ko d'ago kai bata yi ba bare yasa ran zatama saurarai, d'ago kanta Abdurrahim yayi ya ce"yi hakuri ki daina kukan nan dan Allah baki tsoran kanki yayi ciwo, haba kukan yayi yawa mana, yanzu fad'amin me ye damuwar ki atafiyar? "Shiru Na'ima tayi tana nazarin abin da zata cema Abdurrahim, sai zuwa can ta ce " Ni mamana na ke tsoro"tom yanzu ya ki ke so ayi? "Shiru Na'ima d'an yi sannan ta ce" So na ke dan Allah muje tare da kai sai ka fad'a ma mamana balaifina bane kaine ka yi min dole, dan Allah ai dai balaifina bane ko? " Na'ima ta tambayi Abdurrahim,kai Abdurrahim ya d'aga mata ,Na'ima tace "tom dan Allah za ka je kai ma Mamana bayani ?"Eh zan zo in mata bayani ince mata balaifinki ba ne laifina ne"
Allah sarki Na'ima cikin jin dad'i ta ba Abdurrahim address d'in inda suke. Abdurrahim ko tabbatar ma Na'ima yayi da ya na nan zuwa,sannan ya tashi ya ce "tom ki kwanta ki yi bacci dan Allah kinga dare yayi kuma gobe da wuri zaki wuce"tom ba kace bazaka biyamin k'ud'in jirgi ba?" cewar Na'ima tana goge hawayan da ya zubo ma ta, Abdurrahim cikin jin tausayinta ya ce "wasa na ke mi ki zan biya mi ki" nan dai Abdurrahim ya lallashi Na'ima tare da tabbatar mata da in taje zai zo daga baya sannan yabarta ta kwanta.
Washegari Abdurrahim da kan shi ya shiga kitchen ya had'a ma Na'ima tea ya soya mata kwai anufin shi duk dan kar taji yunwa dan shi tausai yanzu ta ke ba shi. Bayan Abdurrahim ya gama komai ne ya tada Na'ima.
Bayan Na'ima tayi wanka ne tasa sabuwar rigar da Abdurrahim ya siyo mata wadda bata ta b'a sawa ba ,bayan ta gama shirin ta ne tafito falon, kallanta Abdurrahim yayi nad'an lokaci dan sai ya ga batatab'a mai kyau ba kamar yau ba.
Bayan Na'ima ta gama shan tea d'in ne tabar mai kwan shi agun, kallanta Abdurrahim yayi yace"me ya sa baza ki ci k'wan ba? "Amai zai sani" "Okay"Abdurrahim yace.
Abdurrahim dakan shi ya d'auki Na'ima ya kaita har airport.
Abdurrahim hannun Na'ima ya ruk'o lokacin da zata sauka daga motar ya ce" Tsaya mu yi sallama mana,Na'ima dan Allah kar ki bari ki haifi cikin jikinki kin ji?"Abdurrahim ya fad'i maganar cikin sanyi ahankali, dan ji yake jikin shi duk yayi sanyi na rabuwar da zasu yi, sannan yaci gaba da cewa" kin ga gida zaki dan Allah in ki ka je kiyi k'okarin zubar dashi acan kinji?" Kai Na'ima ta d'aga ma Abdurrahim.Abdurrahim kuma cikin sanyi ya ce"kin yi min alkawari za ki zubar ?" Nan ma dai kai Na'ima ta k'ara d'aga mai," ki yi magana da bakinki sannan in yarda"cewar Abdurrahim.
Na'ima cikin sanyi itama ta ce" na yi alkawari zan zubar insha Allah" ta fad'i maganar tana share hawayan da ke zubar mata.
Wata leda Abdurrahim yamik'a ma Na'ima ya ce"gashi nan da akwai wata takarda aciki in kinje gida ki karanta kinji? "Amsa Na'ima tayi still tana goge hawayan da ke zubar mata.
Abdurrahim kallanta yayi ya ce" me ya sa ki ke kuka? " "Ni ma bansan ina yin kukan ba" Hannunta Abdurrahim ya kamo ya ce" Allah ya k'addara saduwar mu" yana kaiwa nan yabud'e mata murfin motar ta fita.
Abdurrahim na nan tsaye yana kallan Na'ima yaga ko zata waigo,amma Na'ima har ta shiga jirgin bata wai goba.Abdurrahim ta da motarshi yayi ya tafi. Jikin Abdurrahim asanyaye ya koma gida.
Na'ima basu suka sauka gida ba sai cikin dare, direct Na'ima gidan hajiya Rahina ta nufa tad'au drop din mota,suna zuwa tai ta bubbuga gidan, mai gadin cikin tsoro ya matso kusa da get d'in ya ce"waye?" Baba ni ce" cewar Na'ima."ke ce wa?"Mai gadin ya tambaya. "Baba Na'ima ce" Ai Baba mai gadi najin haka ya matsa kusa da get d'in cikin wani sabon tsoran dan shi asanin shi ance Na'ima ta mutu a accident d'in da su kai na Jirgin ruwa har kayan hajiya suka hallaka, wayar hajiya Rahina Baba mai gadi yakira.
Hajiya Rahina cikin bacci taji wayarta na ringing dubawa tayi taga number baba mai gadi, d'auka tayi tace"Baba lafiya? "Hajiya Wallahi ba lafiya ba, bubbuga k'ofar gida ake na tambayi waye ne akacemin wai Na'ima ce yarinyar ta akace ta mutu" Hajiya Rahina ma cikin kid'ima ta sakko tayo wajan mai gadin, tsaye tagan shi can nesa da get d'in, ita kuma Na'ima har yanzu bata bar bugawa ba tana cewa"Baba ni ce ban mutu ba Wallahi" Ai Hajiya Rahina najin haka tace"Baba bud'e Na'ima ce wallahi ga muryar ta nan wata biyar ai bazai sa inkasa gane muryar ta ba"
bud'e get d'in mai gadin yayi, Na'ima ciki tashigo tana goge hawayan da batasan takamaimai na me ye ba, na murnar dawowarta mahaifarta ne Ko ko na bak'in cikin dawowa da cikin shege ne, Hajiya Rahina rungume Na'ima ta yi tana cewa "alhamdulillah dama Na'ima baki mutu ba ? Alhamdullilah!" abin da Hajiya Rahina ke cewa ke nan.Hajiya Rahina dakan ta ta rik'e kayan Na'ima suka shiga cikin gidan, d'akin da aka tanada dan bak'i Hajiya Rahina takai Na'ima,sannan ta kawo mata tuwan shinkafa. Na'ima ko yunwa take ji amma ta san ko da taci aman shi za ta yi dan haka ta kalli Hajiya Rahina tace"Mommy da dai akwai tea ne da shi na sha" dariya Hajiya Rahina ta yi tace "Allah sarki anyi doguwar tafiya ko ciki ya cin ku she"Shiru Na'ima tayi Hajiya Rahina kuma da kanta ta Had'o ma Na'ima tea d'in ta kawomata tai mata sai da safe dan ta huta washegari sa zanta.
Bayan Na'ima ta gama shan tea d'in ta ne ta d'akko ta kardar da Abdurrahim yabata ta bud'e ta fara karantawa kamar haka,
"Ki yi hak'uri Na'ima bazan iya zuwa gidan ku ba, hasalima address d'in da ki ban namanta shi, sannan ki taimaki kanki ki zub'ar da cikin da ke jikinki, ga kud'i nan ki yi hidimar zubar da cikin dasu.
Bissalam.
🛥️ ABDURRAHIM🛥️
MATUK'IN JIRGIN RUWA NE
📚📚🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚📚🖊
Na
Fadila Sani Bakori.
MARUBUCIYR
1)IN DA RAI
2) RAYUWAR HAIDAR
3) SO NE SILA
4) OGA HABIB
5) DAGA ALLAH KO D'AURA MA KAI.
6) ABDURRAHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE
7)MEENALLYN DADDY
Page 30 & 31
Bayan Na'ima ta gama karanta letter da Abdurrahim yabata dafa kanta tayi tana kuka sosai tana cewa" Wayyoo Allah na na ba ni wa zan ce ya yi min cikn nan Allah na rok'eka ka d'oramin cikiwan da zai zubar da cikin nan ba tare da na sha magani ba" Na'ima ta dad'e tana kuka har ta samu bacci b'arawo ya sace ta.
Washegari da wuri Na'ima ta ta shi ta tayi wanka kasan cewar yanzu saurin jin yunwa gareta yasa tafita ta ga ko hajiya Rahina ta ta shi in da da kan ta ta ke girkin ta bata da 'yar aiki, Na'ima ce ka d'ai wadda ke mata aiki ita ma kuma share-share ne kawai da wanke-wanke .Na'ima a kitchen ta hangi hajiya Rahina tana ta aikin had'a abin kari( breakfast) Na'ima har ta shiga kitchen d'in ta fito da sauri k'arnin k'wain da ta jiyo dan bata shiri da k'arni, tun kafin Na'ima tak'arasa shigowa hajiya Rahina ke kallan Na'ima ganin irin yadda ta yi k'iba tayi haske, bak'aramin mamaki hajiya Rahina ta yi ba ganin Na'ima tafasa shigowa ta koma tana dod'e hanci," Yarinyar nan lafiya kuwa?" Cewar hajiya Rahina, bayan hajiya Rahina ta kammala had'a kayan Karin ne ta Kira Na'ima ta bata nata. Na'ima tea d'in kawai ta d'auka tabar doyar.Na'ima d'auka ta yi zata shiga d'akin da yake mazaunin nata hajiya Rahina ta ce"zauna ki sha anan mana, nakira hajiya Suwaiba na ce mata ta turomin gwaggon ki Allah bashi sai ki fad'a mana halin da ki ka kasan ce bayan tunanin kin mutu da mu ka yi"Na'ima cikin sanyi ta ce" tom mommy ba damuwa Allah ya kawota lafiya"
Bayan Na'ima ta gama shan tea d'in da shi ka dai take iya sha, ta share falon ta goge duk wata k'ura da ke falon.Bayan ta gama ne ta na nan zaune gwaggo ta yi sallama ta shigo falon.Da gudu Na'ima ta ruga ta rungume gwoggo ta na kuka." laaa ka gamin shirman banza, me ye kuma na kuka ke da za ki yi farin cikin dawo da ki kai cikin danginki da Allah ya yi"Cewar gwaggon Na'ima. Hajiya Rahina ce ta fito jin shigowar gwoggo da tayi.Bayan sun gama gaggaisawa ne hajiya Rahina ta ce "dama gwaggo na kiraki ne dan ina so ko mai Na'ima zata ce game da b'atanta ta fad'a gabanki inda ni ke ce nasani amatsayin mahaifiyar Na'ima" Hajiya Rahina kallan Na'ima ta yi ta ce"Na'ima mun shi ga rud'u jin bacewarki kwata-kwata inda duk wa inda suka rasa ransu anga gawarsu, amma ke ba ki ba gawar ki, ina ki ka shiga Na'ima har tsawan watanni biyar ko shida? " Tun da hajiya Rahina ta fara magana gaban Na'ima ke fa'duwa, shiru Na'ima tayi dan tarasa ta inda zata fara.
"kin yi shiru Na'ima?" Cewar hajiya Rahina.
Na'ima cikin sanyi ta ce "Ni ma Wallahi ta ka mai-mai Ban san ya akai ba Wanda ya taimakan ya taimakeni,dan betab'a ban labarin ba ,abin da dai na sani bayan faruwar hatsarin Jirgin mu na farka na ganni agidan wani bawan Allah ba haushe ne kuma kuma musilmi anan naci gaba rayuwata na tsawan wata shida da na yi har Allah yasa ya biyamin kud'in Jirgi na dawo"Cewar Na'ima tana share hawayan dake zibar mata.
Hajiya Rahina kallan Na'ima tayi ta ce"takardar fa da na gani waya baki ita ?" Hajiya Rahina ta ciro letter da Abdurrahim ya ba Na'ima tana nunama Na'ima ita. Ita ko Hajiya Rahina ta ga takardar ne lokacin da ta shiga d'akin Na'ima ita kuma lokacin Na'imar bata ta shi daga bacci ba,anan taga takardar ta d'auka ta karanta.
Gaba d'aya Na'ima ta gama rud'ewa kuka ta fasa tana cewar"Wallahi gwaggo ba da yarda ta haka ta faru ba da..."Gwaggo tare Na'ima tayi dan ita basan me ya ke faruwa ba,ta kalli hajiya Rahina ta ce" wai hajiya mai me ke faruwa ne ,takarda me ye ne ki ka gani ?"
Shiru hajiya Rahina tayi dan tarasa ta inda zata fara yi ma gwaggo bayani ,sannan ta ce"tom gwaggo abi sa ga alama dai Na'ima da ciki ta dawo"Wata irin zabura gwaggo ta yi ta ce"Ke 'yar nan ki rufa min asiri ciki kuma! Kamar ya? " Na'ima ko ta dage kukan ta kawai ta ke yi.
Hajiya Rahina ta ce"tom Na'ima ta kuka kuma ai ta k'are in da aikin gama ya gama, amma taya haka ta faru Na'ima? Bayan kin san da aure kanki Na'ima!" Cikin kuka Na'ima ke cewa"Wallahi mommy f'yade ya yi min bada son raina ba ne"Daga hajiya Rahina har gwaggo shiru ka wai su kayi dan dukkansu sun rasa abin cewa, gwaggo ko kuka ta fasa tana cewa"Na'ima ya zanyi da mahaifiyarki? Me zance mata Na'ima? Da wa na ido zan kalleta?" Na'ima cikin kuka ta kuma cewa"Wallahi gwaggo ba da son raina b,,,,,,,,,,," Ke da Allah can yi min shiru yaza ai ki je ki zauna gida daga ke sai Namiji,wanda ba muharraminki ba ba d'an'uwanki ba ba dangi iya ba na baba balle ya kalliha" Cewar gwaggo.
Hajiya Rahina ta ce "Haba gwaggo tom ita da ba 'yar k'asa ba ina ta sani ai aikin gama yariga ya gama yanzu tashi zata yi mu je aima mahaifiyarta bayani"Gwaggo kai ta jinjina ta ce"Wallahi hajiya ba zan iya had'a ido da Mariya ba ince mata 'Yarta na d'auke da ciki, ina ba zan iya ba" Cewar gwaggo tana nai man