Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 8
d'akin nan ma bata ga wani alamun abunda Zata goge ba ko ta share, komawa tayi ta zauna duk da duk atsorace take agidan dan bata saba zama guri ita ka dai ba. Abdurrahim kamar yadda ya saba dawowa ya dawo gidan, har ga Allah ya manta da wata Na'ima sai da ya tun karo gidan ya tuna. Zaune take duk tata kure jikin ta, kallo d'aya za kai mata kagano atsorace take. Tanajin an bud'e k'ofa zumbur ta mike daga zaunan da take tana zare ido. Kallo d'aya Abdurrahim yayi mata ya dauke kan shi, kitchen yanufa dan haka d'abi'arshi take daga yadawo aiki bazaiyi komai ba har sai yasamar ma kanshi abinda zaici, dan shi bai iyacin abincin siye ba tsabar kyankyami irin nashi. Na'ima na nan zaune Abdurrahim ya fito ta ce "Bawan Allah dan Allah ina kasamoni tana mai maganane tana nuni da hannu kamar tana magana da kurma ,dan ita duk atunanin ta kurma ne. Wani banzan kallo Abdurrahim yayi mata ,tare da mamakin maganar da take mai da kurame. Banza yayi da ita ya shiga kitchen dan samarma kanshi abinda zai ci. Yana shiga kitchen d'in yaci karo da aman da Na'ima tayi mai aciki ,da ta rasa abin kwashewa tab'ar shi agun. Da sauri yadod'e hancinsa yadawo baya da sauri, kallanta yake rai abace ya ce" Kee, amma dai ke baki da hankali ko,kuma inajin asalinki talaka ce ke, dan su ke aikata rashin hankali irin wannan, kuma ke ko atalakar bagidajiyar talaka ce"Abdurrahim nuna Na'ima yayi da hannu yaci gaba da cewa, "wallahi nabaki minti d'aya ka cal ki goge min wan can k'azantar, sannan kuma ki zo ki bar min gidana yanzu-yanzun nan........ ๐Ÿ›ฅ๏ธ ABDURRAHIM๐Ÿ›ฅ๏ธ MATUK'IN JIRGIN RUWA NE.(RENEW) ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION๐Ÿ“š* Na Fadila Sani Bakori. Page 10 & 11 Wata uwar tsawa Abdurrahim yayi ma Na'ima ya ce"ba ki ji ne?, ki je ki goge min wannan k'azantar da ki kai min a kitchen, sannan kuma ki bar gidan nan yanzun nan." Na'ima ko tsabar al'ajabin maganar da Abdurrahim ya ke yi ce tasa takasa tashi, dan ita duk atunaninta Abdurrahim kurma ne. "Keeee!,wai ba ki ji ne"Abdurrahim ya sake nanatawa ganin Na'ima ta tsaya tana kallan shi. Da sauri Na'ima ta tashi ta shiga kitchen d'in amma still bata ga tsumman da zata goge aman ba, dawowa palon tayi tace cikin rawar muryar" Banga tsumma ba ne shi yasa tun d'azu ban goge ba"Banza Abdurrahim yayi da ita ya ciro wayar shi yayi Kira alheri. "Hello alheri ki zo yanzu please" bejira amsar ta ba ya kashe wayarshi. Cikin k'ank'anin lokaci alheri ta shigo gidan, kasan cewar tasan indai Abdurrahim yakirata ba lafiya ba, dan tasan baya kiranta hakanan kawai da wuya.Cikin damuwa dan ita duk atunanin ta ko be da lafiya ne, tak'arasa inda yake tsaye da waya yana dannawa. "Abdurrahim lafiya ka kirani ,gani nazo amma bakace min komai ba? " "Kitchen d'ina zaki d'anyi min mopping" Koda alheri ta shiga kitchen d'in taci karo da amai da sauri tayo baya dan adduniya ba abinda take kyama kamar amai, bata goge ba dan jikinta yabata ba aman Abdurrahim ba ne. Alheri kallan Abdurrahim ta yi da ta fito ta ce "Abdurrahim baka da lafiya ne naga amai a kitchen d'in ka? " " No, bani ba ne yarinyar nan ce. " Sai alokacin alheri ta tuno jiya Abdurrahim yakirata ta duba wata yarinya. Alheri kallan Abdurrahim ta yi ta ce "Ita ce tai aman?" Kinga idan bazaki goge ba zaki iya tafiya. " Alheri juyawa tayi ta shiga d'akin da ta duba Na'ima jiya. Zaune ta iske ta ta tusa kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka. "Keee,tashi ki je ki goge k'azantar da ki kai ma muta ne" Na'ima d'agowa tayi tana kallan alheri,sannan ta ce " Dama babu tsumma ne shiyasa bangoge ba"Tom yanzu ansamu tsumman tashi ki je ki goge" "Na'ima yi tayi kamar bazata tashi ba dan idan akwai abinda tatsana bai wuce arika mata magana ba cikin isa. Na'ima tashi tayi tabi bayan alheri,suna shiga kitchen d'in alheri ta mik'a mata mopper d'in. Amsa Na'ima tayi tafara aikin gyra kitchen d'in. Cikin kankanin lokaci Na'ima ta goge shi tass dan bawai aman da tayi ba kawai ta goge sai da tabi lungu da sak'o ta goge, alheri duk tana tsaye tana kallanta, kiran da akai matane awaya yasa ta tafiya, Abdurrahim ta kalla tace zanje gida amma zan dawo" kai Abdurrahim ya girgiza mata alamun karta dawo, sanin halin shi da alheri tayi yasa bata wani jaba tatafi. Wacece alheri? . Alheri ainuhin sunanta kenan ,karatu ne ya kawo su zama London kasan cewar ita 'yar gata ce awajan babanta, primary da secondry d'inta duk a Nigeria ta yi su. Bayan ta gama secondary ne suka dawo London inda taci gaba da karatu, atak'aice dai yanzu haka tana aiki ne a wata private asibiti da ke k'asar. Alheri sun had'u da Abdurrahim ne sanadiyar ciwan ulcer ya kaishi kwanciya a asibitinsu, kasan cewar Abdurrahim baya son kwanciyar asibiti yasa ya naimi abashi wanda zai rik'a zuwa gida yana duba shi, shine fa doctor ya had'a Abdurrahim da Alheri, tom daga nan ne fa Alheri tazama likitan shi, ahankali-ahankali shakuwa tafara shiga tsakanin su,inda yakasan ce Abdurrahim bashi da aminin da ya wuce kamar alheri. abotarsu ya sa Abdurrahim ko da lafiyar shi lau zai iya kiran Alheri tai mai wani abun ita kuma daga ya girata zatabar duk uzirinta taje. Sai dai ita alheri anata b'angaran so mai tsanani takema Abdurrahim, dan akwai lokacin da ta taba fada mai tana son shi, shi ko ce mata yayi iyayan shi bazasu bari ya auri christian ba.Wannan kenan haka dai sukaci gaba da ta rayya har izuwa yau Abdurrahim yak'i ba Alheri damar nuna mai kalar son da take mai,dan shi bata ita yake ba. Wannan kenan. Na'ima nagama mopping d'in kitchen d'in tazo ta wuce tagaban Abdurrahim, ba abinda yafi da mun Na' ima kamar zan manta ba d'ankwali agidan dan daga ita sai doguwar rigar dake jikin ta, kanta ba d'ankwali, d'ankwalin yacire ne alokacin da Abdurrahim yake ciku-cikun cire mata rigar ruwan da tasa,ga gashinta atsefe yake. Na'ima na nan zaune a d'akin da take , Abdurrahim yazo ya wuce ta ya shiga dakin shi, yunwa takeji sosai dan har cikinta yafara k'ugin yunwa , tashi tayi taje kitchen d'in bata ga ko mai ba Wanda zata sa acikinta gashi har wani yunk'urin amai takeji saboda yunwa, idonta ne ya haska mata wata leda da sauri ta k'arasa gurin ledar tana bud'ewa taci karo da farfesun kaza sai zuba uban k'amshi yake, zama Na'ima tagyara taci gaba da cin namanta. Shiko Abdurrahim wanka ya shiga yi yazo yaci ferfesun shi , sannan ya kalli wasan kwallo dan shi ma abocin kallon kwallo ne sosai, sai dai duk wasan kwallon da zai kalla bai zuwa ko ina ya kalla sai agidansa dan shi kamar mace yake daga dare yayi shikenan shida fita kuma sai gobe, ko dan ba mai abokai ba ne ohoho, bashi da k'awar da tawuce alheri dan har mommyn shima tasan da ita. Da saurin shi yafito cin namanshi dankarya huce, amma wazai gani, Na'ima zaune tana tand'e hannu dan har tagama cinye farfesun. kallanta Abdurrahim yake da mamki nuni yayi mata da hannu alamun ta zo, bamusu Na'ima taje dan talura bashi da mutunci inda yau kwanan ta biyu amma bai tab'a bata abinci ba saidai Wanda tagayarage take d'auka taci, so takema tace mai tana son taje gida amma takasa mai maganar, garashin kayan canzawa duk da dai tunda tazo ba tai wanka ba ne, dan ma farin mutum ba acika gane k'azantarshi ba ajiki. Zuk'unnawa Na'ima tayi nesa da shi. Abdurrahim yadad'e yana mata kallan wulak'anci abinda yake saurin tafasa Na'ima kenan tatsani kallan raini.Abdurrahim ko sai da ya gama mata kalllan raini acewarta sannan yace ahankali dan bawanima jin abinda yakecewa tayi ba" Ke wata irin bagidajiya ce, bakida hankali ne?, Abincin da nasa akaimin shine zaki zauna ki cinye min?" Abdurrahim harya k'ari maganarsa Na'ima batace komai ba, bare kuma tace yayi hakuri. Abdurrahim takaici ya isai daga tai mako. kallanta ya kuma yi ya ce " bargunnan " Na'ima yau gaba d'aya ita kanta kyankyamin kanta takeji so take tai wanka amma bata san kayan da zata Saba, inda bata da kaya, haka take wuni kullum ba d'ankwali akanta gashi yau har kwananta hud'u agidan bawanka, kai inda dai mutum min nan bada wuri yake da wowa ba mai zai hana inyi wanka da ganan in wanke rigata, tom wana zani zan d'aura? Take tambayar kanta, yauwa basai in d'akko rigassa ba wadda nake rufawa in benan inzanyi sallah insa kafin rigata ta bushe, yauwa aiko haka zanyi bari in rufe gidan kar inje yadawo, duk da rufe ni ya keyi tom nima bari in rufe ta ciki. " Rufe gidan Na'ima tayi, sannan ta dawo ta cire rigarta ta wanke ta sa ta Abdurrahim,sannan ta shiga wanka, tana cikin wankanne tarika jin buka k'ofa da k'arfi, bak'aramin razana Na'ima ta yi ba , dan tasan ba kowa bane sai mai gidan, kai aiko bazan bud'e ba inda rigata bata bushe ba, kuma inyaganni da rigassa korata zaiyi kuma bansan kowa ba, haka d'inma Nagoge masa taimakona da ya yi, saidai fatan Allah ya kawo yadda zan bar kasar" Shiko Abdurrahim wasu takaddun kayan da zasu d'auka ya manta yazo sauka gashi jiran shi akeyi, tunyana tunanin ko bacci takeyi harya bara tunanin anya lafiya, cigaba da buga k'ofar yayi amma ba alamun za abude. " Na'ima ko kasa k'arasa wankanma tayi saidai ta watsa ruwan kawai, koda ta tab'a rigarta kamarma yanzu ta shanyata, jin bugun k'ofar yayi yawa Na'ima ta yanke shawarar taje tace mai ta wanke kayanta ne tayi wanka, gudin kar yaji shiru ya koreta in ta bud'e kuma. Shawarar zuciyara tabi, cikin tsoro da addu'ar da duk tazo bakinta tak'arasa jikin k'ofar.Sai dai ko da taje kusa da k'ofar kasa magana tayi tarasa abinda zatace , ringing d'in wayar shi da taji ne yasa ta saurara danjin abinda zaice, ji tai yana cewa"Kayi hauri nad'an samu matsala ne agidan amma yanzu zan kawo in aha Allah. " Na'ima ko jin haka ta ce"Uhmm dan Allah ka basu hak'uri n...." Abdurrahim bai bari tak'arasa abinda take son cewa ba ya ya ce, "Keee,bud'e k'ofar mana"Ka yi hak'uri bazai yuwaba ne shiyasa. " Abdurrahim mamaki yasa yama kasa cewa komai,ga bak'incikin fad'an da ogan shi zai mai.Shi da gidanshi daga taimakon magidajiyar yarinyar nan tana naiman jaza mai aiki, jin wayar shi na ringing yasa ya ce, "Kee ,dan uwarki gidan ubanki ne da zaki kulle ki hanani shigowa?" "Ka yi hak'uri nawanke kayanane kuma ba kaya jikina shiyasa" Ita ko Na'ima bala in tsoran Abdurrahim yaganta da rigassa ne yasa tak'i bud'e mai k'ofar . "Keee, ki bude k'ofar nan nace!!" Abdurrahim ya fad'a cikin tsawa. "Ka yi hak'uri bakaya ne jikina shiyasa. "Ki bud'e naceeee!!!" Na'ima shiru tayi,dan ita gani take sai yafi hukunta ta in ya ganta da rigarsa ajikinta. Abdurrahim ko jin Na'ima shiru babu alamun zata bud'e k'ofar ya ce, "Shikenan bari in kira aballe min k'ofar inda ba zaki bud'e ba............. ๐Ÿ›ฅ๏ธ ABDURRAHIM ๐Ÿ›ฅ๏ธ MATUK'IN JIRGIN RUWA NE.(RENEW) ๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ…™๏ธŽ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‚๐—บ๐—ฎ๐—ถ ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐—ฟ๐—ถ๐˜๐—ฒ๐—ฟ๐˜€ ๐Ÿ…๏ธŽ๐˜€๐˜€๐—ผ๐—ฐ๐—ถ๐—ฎ๐˜๐—ฒ๐—ฑ๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ–Š Na Fadila Sani Bakori Marubuciyar๐Ÿ‘‡๐Ÿป 1 SO NE SILA 2 IN DA RAI 3 RAYUWAR HAIDAR 4 OGA HABIB 5 DAGA ALLAH KO D'AURA MA KAI 6 MENALLYN DADDY 7 ABDURRSHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE Page 12 & 13 Abdurrahim ko jin Na'ima shiru babu alamun zata bud'e k'ofar ya ce "Shikenan bari in Kira ab'alle min k'ofar inda bazakaki bud'e ba". Na'ima jin Abduurahim yace zai Kira a b'alle mai k'ofar,yasa ta fara zare ido tana tunanin yadda zatai tana cikin tunanin ne taji Abdurrahim yana waya yana Kiran aturomai mai b'alle k'ofar,yasa Na'ima jikinta narawa ta bud'e k'ofar. Gefe guda ta rakub'e tana zazzare ido tana jiran hukunci. Abdurrahim ko da yake sauri yake kallan Na'ima kawai yayi ya girgiza kai ya shige ciki batare da ya ma lura da jallabiyarshi da ke jikinta ba.Cikin sauri ya d'akko takaddun ya juya zai fita. Sai dai Kiran da ya shigo wayarshi ne na manager ya d'auka da sauri yana mai cewa"Ga shinan na d'akko ina...."Manager da katar da shi yayi ta hanyar cewa" Abdurrahim gashi nan sabo da sakacinka kajamana asarar milyoyin kud'i dan haka mun da katar da kai aiki na wata uku" Abdurrahim watsarar da takaddun hannunshi ya yi yana jan tsaki sobo da buk'atar takaddun da akace anayi yasa ko karyawa betsayayi ba ya fita tsabar sauri ne ma yasa ya manta takaddun,sai kuma Na'ima da ta dad'e bata bud'e mai k'ofa ba. Na'ima ko tsabar tsoran da take ji ne yasa takasa tashi daga inda take,tana nan zuk'unne taji abu na d'iga akanta dubawar da za tai jini ne ke d'iga awajan da ta bige lokacin da Abdurrahim ya turo k'ofar da k'arfi ta bigeta. Na'ima cigaba da zama tayi agun ga yunwa da take ji inda yau beyi abin kari ba (breakfast) balalle tasamu in yarage taci, gawani basifaffan ciwan kai da kanta ke mata, kukan ma dak'ar takeyin sa, gakan nata jinin yaki daina zuba, tashi tayi ahankali tana daddafa bango saboda jirin da takeji yana nai man kadata. Abdurrahim ne yafito zai shiga kitchen dan nai man abin da zaici, ko kallan inda Na'ima take beyi ba, ita ko Na'ima Ahankali- Ahankali ta shiga d'akin da yazama kamar nata takwanta. Tea Abdurrahim yahad'a makanshi, zama yayi falon amma duk inda idon shi ya kalla jini yake gani d'igo-d'igo agun, tashi yayi yana bin duk inda jinin ya d'iga da kallo, hankalinshi ya ji yafaratashi dube-dube yafarayi yana nai man inda zaiga Na'ima amma bai ganta afalon ba da sauri ya nufi d'akin da ya ke tunanin zai ganta acan. Kwance ya hango ta takawa yayi ya k'arasa inda take ya Kira ta da "Kee"amma Na'ima shiru dan azuwa yanzu yunwa take ji sosai. Hannu Abdurrahin yasa ya d'agota, rik'e take da cikinta ga inda ta kwanta duk ya b'ace da jini sakamakon buguwar da tayi da k'ofar lokacin da ya turo. Cikin rud'ewa Abdurrahim gake kallanta ya ce "Kee baki da lafiya ne?" Na'ima dai shiru ba amsa,Abdurrahim jin Na'ima tayi shiru ya ciro waya yakira alheri. Kira d'aya ta d'aga tana d'agawa ya sanar da ita tazo gidanshi yanzu. Cikin mintinan da basu wace goma ba alheri tazo gidan, ko da taga yadda jikin Na'imar ya yi lokaci guda cema Abduurahim tayi sai dai suje asibiti da ita. Abdurrahim kallan alheri yayi ya ce " ki dubata anan mana" badan alheri ta so ba ta koma ta d'akko duk wani abu da zata buk'ata ta ta dawo. Bandage tasa mata a inda ta buge dan buguwar sosai ce.Maganar ciki ko da take ta rik'ewa ko da ta aunata ba abin da ke damunta wanda ya wuce ulcer . Alheri kallan Abdurrahim tayi ta ce"Abdurrahim wai zaman me yarinyar nan take agidan nan ne ,me yasa baza ka barta ta koma gidansu ba ? " Abdurrahim shiru yayi Kamar ba zai ba alheri amsa ba sannan ya ce"cemiki akai ni na rik'eta? ni ma da zata tafi da nafi son haka"Tom shikenan yanzu dai serious ulcer ke damunta, amma gaskiya Abdurrahim ka kuri yarinyar nan karta jawoma wata wahalar gashi yanzu ma sai jama muta ne wahala take"Okay" Abdurrahim yace. Alheri zama tayi tana kallan Abdurrahim sannan zuwa can ta ce "Abdurrahim wai ya managanar aurenmu ne Ka yi shiru ko kana nufin har yanzu kana kan bakar iyayanka bazasu bari ka auri christian ba ne?". "Alheri nariga nafa'da maki daddyna ko zai bari in aure ki tom k'ila sai in nayi aure, kinga ni kuma yanzu bantashi yin aure ba ma. " Fuuuu alheri ta d'auki jakar ta tab'ar gidan tsabar b'acin ran maganar da Abdurrahim ya fad'amata. Na'ima ko bacin ta ta shi daga baccin wahalar ciwan da taji tana tashi yunwa ma tace gatanan,Na'ima tashi tayi ahankali ta nufi falon. Zaune ta iske Abdurrahim da waya yana chart da mommyn sa Na'ima ta shigo falon kallo d'aya za kai mata zaka fahimci halinda take ciki na yunwa. Na'ima kallan Abdurrahim ta yi ta ce "Ummm dan Allah bakarage abinci ba"tana rike da ciki take maganar, kitchen ya nuna mata da hannu alamun taje can akwai. Na'ima ko da taje kitchen d'in bataga komai ba, dan haka dawowa falon tayi dak'ar take magana sakamakon rikewar da cikinta yayi ta ce" Dan Allah ka tai makamin yunwa na ke ji zan mutuuuu... "Na'ima ta fad'i maganar da k'arfi sakamakon aman da takeji yana tasomata. Kallan ta Abdurrahim yayi sai yaji ta bashi tausayi dan shima yasan yadda ulcer take rike ma mutum ciki. Abdurrahim tashi yayi yaje kitchen d'in ya had'o mata tea mai kauri, inda yabarta azuk'unne anan yasame ta. Abdurrahim mik'amata tea d'in yayi tana sha cikinta ya k'ulle Abdurrahim duk yana nan zaune yana kallan Na'ima da dake juyi tana faman rike cikinta tana cewa "Dan Allah ka taimamin Wayyo cikina da marata " Abin da Na'ima bata fahimta ba ba wai cikin ne kad'ai ke mata ciwo ba hadda mararta lokacin period d'in ta yayi sai ya had'e da ciwan cikin' duk watan nuniya haka Na'ima keshan wuya. Cigaba da malele kuwa tayi agun dan ko tea d'in ma kad'an tasha. Abdurrahim da yarasa yadda zai yi da Na'ima alheri yakira amma wa yatta akashe. Abdurrahim kallan Na'ima kawai yake yamarasa taimakon da zai bata,magungunanshi na ulcer ya kwaso mata ya bata ya ce" Ki tashi ki sha ga magani nan" Na'ima ko kallanshi batayi ba tsabar azabar da take ji,jin yadda mararta ke mata yasa tafara tunanin abin da ke damunta. "Ki tashi kisha maganin" Abdurrahim ya sake mai-mai ta mata. Na'ima da ta fahimci abin da ke damunta cikin cije baki ta ce "Bazan sha ba ba cikina kemin ciwo ba ai. "Tom me ke mi ki zuwo? "cewar Abdurrahim. Na'ima kamar zatai kuka ta ce "Ni dai ka taimakamin"Abdurrahim da ranshi ya fara b'acewa cikin d'aga murya ya ce"Ke da'allacan da me zan taimake ki ,indai bazaki magana ba Wallahi zan rabu da ke ?" Na'ima sotake tacema Abdurrahim ya siyo mata panties da always da kuma maganin ciwan mara amma kuma tana jin kunyar fad'a mai " Abdurrahim da yaga bata da niyar magana tashi yayi yabatta agun. Na'ima har dare tana gun zaune takasa tashi kuma har yanzu bata da niyyar tashi dan ciwan yanzu ne ma yake cinta sosai. Na'ima jin azaba tayi azaba dan gaba d'aya tama rasa wana yanayi take jin yadda marar kaba d'aya ta k'ulle mata tashi tayi ta nufi d'akin da Abdurrahim yake,tana zuwa ta fara bubbuga k'ofar tana nishin wahala tana cewa............ ๐Ÿ›ฅ๏ธ ABDURRAHIM ๐Ÿ›ฅ๏ธ MATUK'IN JIRGIN RUWA NE.(RENEW) ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION๐Ÿ“š* Na Fadila Sani Bakori. Page 14 & 15 Na'ima jin azaba ta yi azaba dan gaba d'aya tama rasa wana yanayi take jin yadda marar gaba d'aya ta k'ulle mata ,tashi ta yi ta nufi d'akin da Abdurrahim yake.Tana zuwa ta fara bubbuga k'ofar tana nishin wahala tana cewa"Wayyo cikina ka taimakamin zan mutu Wayyo Allah na, haka Na'ima tai ta maimaitawa tana cikiga ba da bubbuga k'ofar, abin ne yayi mata yawa gaciwan cikin ulcer, ga kuma na mara na period. Abdurrahim cikin barci ya jiyo bugun k'ofar da Na'ima ke yi, tashi yayi da sauri ya fito daga d'akin kasan cewar be san jikin k'ofar Na'ima take ba da k'arfi ya tura k'ofar ya nayin shi kamar arud'e ya fito.Wata irin k'ara N'aima tayi dan ba kad'an ba k'ofar ta buge mata kai ba, dafe kan ta yi tana jijjuya yashi, wajan da alheri tasamata bandage ya famamata turo k'ofar da yayi da k'arfi. Da sauri Abdurrahim ya k'arasa inda Na'ima ta ke hannu d'aya dafe da kan d'aya kuma dafe da marar.Abdurrahim ya d'an da d'e atsaye yana kallan Na'ima sannan ya ce"Ke wai me ke damunki ne?". Na'ima tsabar azabar da kanta da marar ta kemata yasa ko amsa bata iya ba Abdurrahim. zuk'unnawa ya yi kusa da ita ya d'an ruk'ota kad'an kamar mai kyamar tab'ata ya ce"Yanzu me ke mi ki ciwo?"Na'ima kanta ta nuna ma Abdurrahim da mararta da ta k'ulle mata. Hannu Abdurrahim ya kai wajan kan na ta, zafi rau ya ji kan."Sai me kuma?" ya sake tambayar ta. Na'ima mararta ta sake nuna mai. Abdurrahim kallanta yayi ya ce "cikinki ke ciwo?". kai Na'ima ta girgiza mai alamun a'a, shiru ya yi sannan ya tashi daga zuk'unnan da yake kusa da ita, waya ya d'akko ya kira alheri ,cikin barci alheri ta ji wayarta na ringing, kamar karta d'auka ganin Abdurrahim be tab'a kiranta ba kamar wannan lokacin yasa ta d'auka. Abdurrahim naji alheri ta d'aga ya ce" Hello Alheri ulcer dama tana sa ciwan mara ne? "dan shi duk a tunin shi ulcer ce tasata ciwan mara,gashi shima bai da ciwo sai ulcer amma bai san tanasa ciwan mara ba. Alheri cikin muryar bacci ta ce"A'a gaskiya ulcer ba ta sa ciwan mara sai dai ko in lokacin period d'inta ne ya yi" Period" Abdurrahim ya mai-mai ta." Eh menstruation ba"Shiru Abdurrahim yayi sannan ya ce " Tom me ye maganin shi? " Tom ka ga dai yanzu dare yayi, amma first aid d'in da zaka ba idan akwai suga kasamata a tea dayawa tasha zai rage mata kafin safiya. Yadda alheri tace ma Abdurrahim haka yayi, kitchen ya je ya d'aura mata tea d'in sannan ya zuba ma ta suga mai yawa a tea d'in kamar yadda alheri tace, bayan ya gama had'a mata tea d'in ya kai ma Na'ima yace"Ga tea d'in tashi ki sha "Tofa anzo wajan dan Na'ima intana ciwo bata son cin abinci. "Wayyo cikina ni bazan iya sha ba "Cewar Na'ima."ke Wallahi biki'isa ba daga taimako ki zo ki zamanmin wahala ked'in banza, ina barcina kin tadani natashi na kuma had'amiki tea ance zai miki magani dan kin maidani wani sakarai ki ce min ba za ki sha ba, tom wallahi bazan iya ba yazam dole ki b'ar min gida" Duk b'ab'atun nan da Abdurrahim ke yi Na'ima najin shi sai dai ahalin da take ciki ta ciwanta take yi dan Allah ne ka d'ai yasan yadda take ji. Abdurrahim jin Na'ima shiru bata amshi tea d'in ba zuk'unnawa yayi kusa da ita ya jawota da k'arfi dan har sai da tayi 'yar k'ara hannunta ya rik'o ya dank'a mata kofin ahannu ya ce" Da Allah malama amshi ki sha" Na'ima cikin cije baki ta amshi kofin tea d'in ta d'aga ta shanye duka. Abdurrahim kallan Na'ima yayi ya ce"Ki tashi ki je ki kwanta"Dan shi ji yake duk ta zamar mai wani kaya. Na'ima tashi ta yi tana rik'e ciki ta k'arasa kan babbar katifar ta mai kamar gado wadda wasu ke Kira da gado huta. Ahankali-ahankali Na'ima ta ji ciwan marar nalafamata ahaka har barci b'arawo ya kwashe ta. Can b'angaran Abdurrahim ko yana ganin Na'ima ta tafi ya koma ya kwanta, yana kwanciya barci ya kwashe shi. Washe gari Na'ima kasa tashi tayi dan tana jin kunyar Abdurrahim yaga halin da take ciki, dan zanin gadon yab'aci sosai da jini, sai dai Alhamdullh ta ji sauk'i sai dai ciwan da kanta yake mata kad'an-kad'an marar ko Allah ya taimake ta kwana d'aya take mata tana ciwo dama. Kasan cewar Abdurrahim hutu yake na dakatar da shi aiki da akayi hakan yasa be tashi da wuri .Lokacin

Chapter 3 of 8