Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 8
tashi."ai hak'uri za ki yi gwaggo ta inda aka hau ta nan ake sauka dan haka dole da ke zamu ayi ma mahaifiyar yarinyar nan bayani" Gwaggo ba dan ta so ba sai dan ba ta da yarda zata yi.Haka suka d'unguma a motar hajiya Rahina suka nufi sabon yalwa gidan su Na'ima. Na'ima kuka ka wai take yi dan ita kanta batasan da idanun da zata kalli mahaifiyarta ba, Na'ima na cikin tunane-tuna nanta sai dai ta ji hajiya Rahina na cewa "mu je ko Na'ima, sannan ki goge hawayan nan na ki" Mahaifiyar Na'ima na d'aura ma yaro manja da yake itace sana'arta yanzu tun jalin da mijin hajiya Rahina ya bata ta saro manja da su kuma alhamdullilah sana'ar ta amsheta, dan tana ciniki sosai kuma da ita suke ci da sha da k'annan Na'ima.Mahaifiyar Na'ima da fara'arta ta shimfid'a ma su gwaggo tabarmar Na'ima ta kalla ta k'ara kallo ta ce"gwoggo wa na ke gani kamar Na'imata? "Ita ce Mariya ba gizo ta ke miki ba ita ce wallahi" Cewar gwaggo. Na'ima rugume Mahaifiyarta tayi tana kuka, Allah sarki ita ma mahaifiyar Na'ima kukan ta ke, saida suka gaji suka yi shiru dan kansu ba wanda ya hanasu daga gwaggo har hajiya Rahina, ita mahaifiyar Na'ima sun san na murnar dawowar 'yarta ce, ita ko Na'ima sun san kan zancan kukan na ta. Mahaifiyar Na'ima zaunar da Na'ima ta yi ita ma ta zauna tana mai cewa"Ku yi hak'uri hajiya ban baku ruwa ba mun tasaku gaba muna muku kuka" Murmushi hajiya Rahina ta yi ta ce"Wallahi hajiya banga laifinki ba"Mahaifiyar Na'ima tashi tayi tasamu yaro awaje ta ba shi kud'i ya siyo musu pure water. Bayan angaisane ansake gaisawa hajiya Rahina ta kalli mahaifiyar Na'ima ta ce"Maman Na'ima kin ga ikon Allah ko ya dawo mi ki da Na'ima alokacin da kin riga kin hak'ura da ita, haka ake so duk abin da yasamu bawa yayi hak'uri ya fawwala ma Allah, Allah na san bawansa mai yadda da k'adddara ko wata iri ce shi ne cikakkan musulmi. Kin ga da ki ka bar ma Allah ko mai duk da dai mun zaci Na'im ta mutu ne sai Allah yadawo da ita alokacin da ba muyi zato ba ,ashe Na'ima ba mutuwa ta yi ba duk da tace Wanda yatsince ta bai fad'a mata yadda akai ya tsinceta ba, tom Na'ima gatanan dai agabanki bata mutu ba, wani bawan Allah ne yatsinceta yakaita gidan shi yaci ga ba da riketa har izuwa lokacin da Allah yanufa ya biyamata kud'in jirgi ta dawo garemu.Maman Na'ima kin san duk indai namiji da mace suka kad'aita shaid'an ne yake zama cikon na ukun su, tom Cikin k'adddarorin da Allah ya rubuta mi ki ke da Na'ima gashi nan Allah nata nuna mi ki su d'aya bayan d'aya dan ko auran Na'ima da gali kin san k'adddara ne amma sai kuka nuna bazaku amshesa ba, tom haka Allah ke ikonsa da Na'ima ta nuna bazata amshi k'addarar auran gali ba sai Allah ya musanya mata da ciki yaga ita zata amshe ta Ko ko itama zata butulce mai ne.Maman Na'ima atak'aice dai ina so ince mi ki yarinyarki Na'ima na d'auke da ciki"Wata uwar k'ara Mahaifiyar Na'ima ta yi wadda saida ta rud'a su hajiya Rahina, balle kuma uwa uba Na'ima, dan ita take ta fasa kuka. Mahaifiyar Na'ima ta shi tayi ta shi ga d'akinta da gudu kamar sabuwar mahaukaciya ta d'akko tab'arya tayo kan Na'ima da ita da sauri hajiya Rahina su ka rirrik'e Mahaifiyar Na'ima.Mahaifiyar Na'ima kuma cikin b'acin rai ta ce "Hajiya ki sake ni ina jin kunyarki!"Ki yi hak'uri maman Na'ima na san da ciwo ,amma dan Allah ki yi duba da hankalinki kin san wacece Na'ima in ba k'addara ba kin san halin yarinyarki" Ina Mahaifiyar Na'ima bata saurari maganar hajiya Rahina ba,sai dai duk yadda mahaifiyar Na'ima ta so sub'arta ta bugu Na'ima abin yaci turo, ganin baza su saketa ba ya sa Mahaifiyar Na'ima cikin b'acin rai ta ce" Hajiya k'un k'i saki na ko? Tom shikenan gaku ga Na'ima nan dan Wallahi Na'ima sai saidai tasan inda zata zauna ba dai gidan nan ba, kuma in dai ni ce mahaifiyar Na'ima tom na cireta aciki 'ya'yana da nahaifa bani babu Na'ima,ki fita in bar ganinki wallahi kafin in mi ki baki, dama abin da ki ke son yi kenan shi yasa kika ce kar afad'a min zaki tafi ,Shikenan ki fitarnin agida na ce ko!, hajiya dan Allah ku fita baki d'aya ku fita bana son ganinku dukkanku abin da ku kai min Allah ya sa kamin kun had'a kai kun kai min yarinya ammata ciki dole za ku zo ku yi min dad'in baki ku fita dan Allah !!" Cikin wata irin razananniyar tsawa Mahaifiyar Na'ima tai maganar. Allah sarki Na'ima ko ta had'a kai da gwiywa sai kuka take, Hajiya Rahina jawo hannun Na'ima tayi tasa ta mota ta shiga suka tafi. har suka je gida Na'ima batayi shiru ba. Bayan sun shiga falon hajiya Rahina ne sun zazzauna, gwaggo ta ce"Hajiya yanzu ya za ai da Na'ima da cikin jikin ta? "Tom Na'ima dai sanadiyata wannan k'addarar ta fad'a mata ,dan haka za ta ciga ba da zama wajena, ciki kuma k'addararta ce dan haka zata raini abin ta"Wayyo ni dan Allah ku tai ma ka min azubar k'il in aka zubar ita ma mamana tayi hak'uri dan Allah ku tai ma ka min " Allah sarki da yake hajiya Rahina macece mai tsananin tausai jawo Na'ima tayi ajikinta ta ce"ki yi hak'uri Na'ima zubba ciki laifine babba, shi musulmi ana so duk k'adddarar da tasamai ya amsheta hannu bibbiyu ya gode ma Allah, sai ki ga Allah ya kawo mai mafita cikin sauk'i sabo da Wanda Allah ya nufa da alkairinsa shi ne yake jarabta, in ma yaran ne ko yarinyar in ki ka haifa ni nayi alk'awari zan rik'eta" Nan dai hajiya Rahina tai ta lallashin Na'ima, dak'ar Na'ima tayi shiru sannan hajiya Rahina ta kawo ma Na'ima abinci, Na'ima k'in ci ta yi hajiya Rahina matsama Na'ima tayi akan dole taci abinci,Na'ima cikin kuka ta ce " bana iya cin komai sai tea " Tea d'in Hajiya Rahina ta had'o ma Na'ima mai kaurin gaske, nan dai suka yi sallama da gwaggo bayan taci abinci ta tafi. Duk wata kulawa da ake ba mai ciki hajiya Rahina ta na ba Na'ima ita, game da mahaifiyar Na'ima ko hajiya Rahina tace ma Na'ima tambari sai ta haihu sunje su sa ke samunta dan har yanzu tana cikin takaicin cikin. BAYAN WATA TAKWAS: Cikin Na'ima har yafito dan a lissafin su koda yaushe Na'ima za ta iya haihuwa. Yau Na'ima ta ta shi da wani irin ciwan mara, Allah yasa hajiya Rahina ta na gidan, amma kuma tana ta shirin zuwa airport d'auko d'anta da ya gama karatu dan yama kirata suna gaf da sauka, zata tafi kenan d'akko shi ta shiga tai ma Na'ima sallama ta isketa cikin halin da ta ke ciki. Hajiya Rahina cikin rud'ewa ta shiga d'akin tana kamo Na'ima tana mata sannu,waya hajiya Rahina ta d'akko zata kira wata likita sai dai ganin yadda Na'ima ta zama lokaci guda yasa hajiya Rahina ta kasa kiran. Cikin kin ikon Allah da taimakon hajiya Rahina Na'ima ta haihu,dai dai lokacin ne kuna yaron hajiya Rahina ya shigo gidan yana mamakin jin kukan jinjiri agidan nasu, har zai shiga d'akin da ya ke jin kukan sai kuma yafasa ya zauna falon ya na jiran fitowar mommyn shi. Gajiya yayi da zama ya tashi ya shiga ciki ya watsa ruwa ya sakko k'asa samama kan shi abin da zai ci, karo su ka yi da hajiya Rahina da cup cike da tea ahannunta ,hajiya Rahina rik'e baki tayi ta ce"Kai-kai son afuwa Allah saura kad'an in manta da kai" mommy lafiya dai ko? Ina kuma ki ka samo b'aki ? Dan naji kukan jariri ina shigowa" "kai dai ka bari in mik'a mata tea d'in nan inzo in baka abinci da labari"Tom hajiyata afito lafiya"Hajiya Rahina tea ta ba Na'ima ta ce " yi ma za ki sha yanzu nan yarona ya dawo" murmushin K'arfin hali Na'ima ta yi dan bata jin dad'in jikinta gabad'aya. Hajiya Rahina falon ta dawo ta ce"Ayyah my son fushi bai ma kyau ba,gara kayi murmushinka ya fi ma kyau" Haba mommy tun d'azu nazo ba ta ni ki ke ba ta wata can ki ke wadda ban san ina ki ka samota ba"Dariya hajiya Rahina ta yi ta ce"ina yarinyar nan dana ta b'a baka labari wadda aka je d'akko mun kaya da ita lokacin da Jirgin kayanmu yayi accident na ce maka ta mutu?" Eh na tuna mommy"Tom wallahi ashe ba ta mutu ba wanda ya tsince ta ne kuma yayi mata ciki kasan mutane, mahaifiyar yarinyar kuma tace bazata rike ta ba shi ne fa ni na ke rik'onta,,,," kukan babyn da Hajiya Rahina tajine ta ce"ka ji ko yarinyar na kuka ina zuwa na bar mai haihuwa ita kad'ai"Hajiya Rahina ko da ta shiga Na'ima na gefe d'aya rik'e da mara saimalele kuwa take babyn kuma sai kuka take, Hajiya Rahina batabi ta babyn ba ruwa mai sanyi tasamo ta yayyanka allbasa taba Na'ima tace taci zai mata sauk'in ciwan marar, ganin tarasa yadda zatayi dasu ga Na'ima sai malele kuwa take tak'i shan maganin ga kuma babyn itama sai kuka take, babyn hajiya Rahina ta d'auka ta fita da ita ta ce"son dan Allah jijjiga min yarinyar nan inji da uwarta" Amsar yarinyar yayi yana jijjigawa, ita kuma ta koma ta d'au maganin da kanta ta ba Na'ima abaki . Shi ko sai jijjiga yake ita ko baby ta dake sai kukanta ta ke. Hajiya Rahina jin yarinyar tak'i shiru ganin ciwan Na'imar ya lafa ta ce "Son kawo min ita" Da sallamar shi ya shi ga sai dai kasa idasa salkamar yayi yana nuna Na'ima itama Na'ima ba ta san san da ta ta shi ba daga kwancan da take tace "Hafizzzzz kai ne?"Wanda Na'ima ta Kira da Hafiz shi ma cikin mamaki ya nuna Na'ima ya ce "Aunty Amarya ke ce!?" Hajiya Rahina kallan su ta ke yi ganin irin kallan da su kema juna na sani, gabantane yafad'i kardai ace Hafiz shi ya yi ma Na'ima ciki tunowar da tayi Hafiz ba a England ya ke karatu ba yasa hankalinta yad'an kwanta,ta kalli Hafiz ta ce "Hafiz kasan Na'ima ne dama?" Mommy matar brother Abdurrahim ce,,,,,,,,, ABDURRAHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE daga nan free pages ya k'are 'yaruwa ki na buk'ar ci ga ba ? Dan samun ci gaban Abdurrahim matuk'in jirgin ruwa ne cikin sauki za ki transfer ta account d'in nan Account number 2111619333 Account name Fadila Sani Bank name zenith Bank za ki yi transfer 500 Kacal ko katin MTN number 08063830828 idan kuma biyu ki ke so ABDURRAHIM MATUK'IN JIRGIN RUWA NE da MEENALLYN DADDY za ki transfer 900 only 👌🏻 ko katin MTN ta number nan 08063830828 Dan nai man k'arin bayani za ki iya magana da marubuciyar kai tsaye ta number nan 08063830828 . Dan Allah idan ba siye za ki ba kar mu b'ata ma juna lokaci🙏🏻🙏🏻🙏🏻 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 8 of 8