Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
yad'an harareshi dan shi atunaninshi jawo rainine hakan na kod'ata d'in da yayi. Sai zuwa can Abdurrahim ya ce dan katse Hafiz d'in "Tom malam idan kagama zub'ar sai katashi karakani inyoma cefane aimaka wani abun kaci"Kai broz nagaji fa, kawai taimin simple food ya'isa" kafad'a Abdurrahim ya d'aga irin ko ajikin shi, kallan Na'ima yayi yace" Tom kinji ki mai abu mai sauk'i kwai" Na'ima bata amsaba ta juya ta shiga kitchen d'in ,rasa abin da za tai mai tayi. Abdurrahim ko sanin hakan zata iya faruwa yasa yabiyo Na'ima kitchen d'in, tsaye yasa meta tayi tagumi daga gani tayi nisa aduniyar tunani, table d'in dake kusa da ita ya d'an buga, ya ce" Dafa mai ruwan zafi yasha tea sai ki soya mai k'wai kawai" Na'ima kai ta d'ama Abdurrahim,Abdurrahim harararta yayi ya ce "Ki natsu bawai kirik'a abu kina duk'ar da kai ba kamar wadda asirinta yatonu tayi gulma ba" kai Na'ima ta kuma d'aga mai alamun tom.Abdurrahim kuma juyawa ya yi yabar kitchen d'in. Cikin minti goma Na'ima ta gama had'a mai tea d'in ta soya mai kwai ta ta d'ora a plate ta kai mai. yauwa sannu da aiki Auntyna, murmushi Na'ima tayi mai ta ce"kai sai kace wani aiki mai yawa"Wow broz kai mai sa'ane voice d'in mai kwantaccan sanyi irin yadda kake so,Allah da gaske nake broz ina kamun k'afar k'anwarta dan karma arigani"Ita dai Na'ima murmushi ta yi dan taji dad'in yabata d'in da Hafiz ya yi gashi yana bata dariya. Abdurrahim ko hararar shi yayi bai tanka mai ba. Bayan Hafiz ya gama shanye tea d'insa ne, Abdurrahim yaja shi suka fita su kai sallah daga nan suka shiga gari duk da Abdurrahim bawani mai yawan dare bane basu suka dawo gidan ba sai 11:20 pm alokacin Na'ima ta dad'e da yin barci,rashin sanin inda zata kwanta yasa ta kwanta a falon inda gidan 2 bedroom ne . Hafiz ko da suka shigo yaga Na'ima kwamce a falo ya ce " kai! Kai!! Kai!!! broz yau ka yi laifi fa? "Abdurrahim cikin rashim fahimtar Hafiz ya ce"Laifin me? "Hafiz Na'ima ya nuna ma Abdurrahim da ke kwance tana bacci abin ta dan daga ganin barcin kasan tayi nisan kiwo. "Broz kalli inda amarya ta kwanta fa daga gani kai take jira ,ni karka jamin tabar ban abinci kafin in wuce"Banza Abdurrahim yayi da shi dan shi dama baya iya ma surutun Hafiz, kallan shi Abdurrahim yayi ya ce"Inkagama zubar sai kazo innunama inda zaka kwanta"A'a broz kyau kafara kai Auntyta taci tukun" Kai Abdurrahim ya sosa ya ce"Kai bataso in ta yi barci atadata barta anan kawai in ta tashi ta shiga ta kwanta" Haba broz daga gani fa zaman jiran mu take gaskiya ya kamata katadata taga dawowarka dan k'ilama da fushinka tayi barci"Kai bana son shirme kazo mu je ka kwanta". Hafiz da yake irin mutanan nan ne masu naci sai cewa yayi "Broz gaskiya bazataji dad'i ba ta tashi ta ganta a falo kwance zataka kamar danni ne ka juya mata baya kuma kaga laifina zata gani kasa tabar banu abinci"Hafiz ya k'arasa maganar da barkwancinsa. Abdurrahim gaba ya yi yana mai cewa"Inkashirya kwanciya ka kashigo ka kwanta ni nayi nan inda kai naga alamar bakajin barci magana kake jin yi"Hafiz bin Andurrahim yayi yana dariyar maganar Abdurrahim d'in. Inda Na'ima ke kwanciya Abdurrahim ya kai Hafiz ya kwanta. Washegari Na'ima koda ta ta shi fuska kawai ta wanke kasan cewar ba sallah take ba, Kitchen ta shiga tana tunanin abin da zatayi ma bak'onsu, nan dai tayanke shawarar d'ora ruwan zafi ta had'a mai tea inda bawani abu su ke da shi ba sai ya siyo kamar yadda taji yace jiya. Na'ima bayan ta kammala ne ta koma Falon ta gyara bayan ta gama gyara falonne ta koma kitchen d'in shima tana gyarawa,tana cikin aikin ne Abdurrahim ya leko ya ce"Sannu da aiki"Yauwa" Na'ima tace cikin girmamawa dan Na'ima akwai ladabi daganin mutumcin Wanda yake sama da ita. Hafiz ko da yatashi sai da yayi wankanshi sanna yafito falon alokacin Na'ima na zaune tana shan tea, shi kuma uban gayyar yana zaune nesa da ita yana danna waya. "Good morning Auntyna " cewar Hafiz yana murmushi. Na'im ma murmushin tayi mai sauti sannan ta ce"Barka da safiya, ka tashi lafiya, ya gajiyar tafiya?" Lafiya klau Auntyna, ina'iya zama?"Sosai ma kuwa"Na'ima ta ce tana mai murmushi. Zama Hafiz yayi d'an nesa da Na'ima. Banyan sun gama karyawa ne dan har Abdurrahim sai da yasha tea d'in dan yalura da yarinyar batada k'azanta sannan ya ce" tom kai sai ka ta shi mu je asiyo abubuwan buk'ata na dafawa, na sanka sarkin jin yunwa ne kai" Dariya Hafiz yayi sannan ya tashi suka fita. Na'ima na ganin fitarsu ta tashi ta shiga toilet d'in da ta saba shiga tayi wanka tasa d'aya daga cikin dogayan rigunan da Abdurrahim ya ba alheri ta siyo mata. Na'ima na gama shiryawa yayi daidai da da dawowarsu Hafiz. Hafiz cikin tsokana yake Kiran Na'ima ya ce "Auntyn gashi angonki yace yau ki yi girkin da yafi na kullum dad'i"Na'ima fitowa tayi tana murmushi ta amshi cefanan da sukayi ta shiga kitchen d'in. Tare da Hafiz suka shi ga kitchen d'in hatta aikin tare sukayi tun Na'ima na d'arid'ari da Hafiz har tasaki jiki suna aikinsu tare suna hira dan tafahimci Hafiz mutum ne mai sauk'in kai bakamar yayan shi ba. Abdurrahim ko dama suna dawowa cefanan ya tafi wajan aiki bashi ya dawo gidan ba sai dare. Hafiz ko ganin yadda Abdurrahim ya dad'e ya ce"Auntna wai dama haka broz yake da d'ewa?" Shiru Na'ima tayi dan yaune yayi haka,sai zuwa can ta ce" Gaskiya yana dawowa da wuri k'ila wani abunne yarik'e"Hafiz numa Na'ima agogon hannunshi yayi ya ce kalla 9pm fa? " Shiru Na'ima tayi dan itama tafara tunanin ba lafiya ba dan aiya zamanta da Abdurrahim ta lura shi ba irin mazannan bane masu firar dare awaje. Hafiz ko jin Na'ima tayi shiru ya ce "Aunty Amarya kin yi shiru?" Nima na fara tunanin k'ila ba lafiy,,,, " Turo k'ofar da akayi ne ya hanata k'arasa abin da tayi niyyar cewa. Abdurrahim zama yayi kusa da Hafiz ya ce" kaji na dad'e ko? "Kai Hafiz ya d'aga mai alamun Eh. " Kabari kawai wallahi bansan me ya faru ba yanzu ake yawan samun accidents d'in jirgin ruwa ba 'yan kwanan nan, kwanan nan fa ba afi wata d'aya ba akayi wani akarasa ran mutum da dama amma ikon Allah kaga yau aka sake yin wani" Wai gaskiya broz kuna aikin gan-ganci, ni me yajani in rasa abun da zanyi sai tukin jirgin ruwa wai!,sannunku" murmushi Abdurrahim yayi yace "Badamuwa ai tawani b'angaran aikin taimako ne, haka kwanaki fa na tsinci wata yarinya igiyar ruwa ta jawo acikin ruwa ,sai dai nayi parking cikin ruwa na d'akkota "Na'ima da sauri ta kalli Abdurrahim dan ta ji ajikinta bawata bace ita ce dagaji, aiko zata gwada tambayarshi taji itace" Hafiz cikin al'ajabi ya ce"Amma broz ta mutu?"A'a bata mutu ba"Abdurrahim ya kauda maganar da cewa" Kai nagaji sosai" Hafiz kallan shi yayi ya ce "Broz asama abinci ko?"No nak'oshi, sai da naci abinci na k'oshi sannan nadawo" Abdurrahim tashi yayi ya shiga ciki dan bak'ad'an ya gajiba, ya yi ma Hafiz saida safe ya shige ciki yabar Na'ima da Hafiz agun. Hafiz kallan Na'ima yayi yace"Auntna Allah bakyakulawa da broz sosai fa amma ki tsaya yanga wata ta kwace broz, duk da naga shima kamar irinki ne,ko dai dan kunganni ne?, amma idan har kina ganin kamar auran tausayi yayi dake yasa kikakasa bashi kulawa gaskiya shawara nake baki ki canza ki kula da mijinki da kyau kafin wata ta rigaki" Shiru Na'ima tayi tana sauraran Hafizs ji tai kamar ta fad'amai gaskiya ita ba matar Abdurrahim bace, amma tana jin tsoran kar Abdurrahim ya koreta gidan kuma batasan inda zata ba. Hafiz ko ganin Na'ima ta shiga tunani ya ce" yanzu dai duk ba wannan ba" ki ta shi ki je ki kula da mijinki" Na'ima cikin inda-inda ta ce "Gaskiya ni nan zan kwana" Haba Auntyna me ya sa ki ke yin haka ne mijinki ne fa!" Na'ima ba ta jin dad'i in taji yace wai Abdurrahim mijinta ne. Hafiz ko haka ya tasa Na'ima da naci da magiya sai da ya turata d'akin Abdurrahim. Na'ima ba dan taso ba sai dai ta rasa yadda zata zillema Hafiz haka ta hak'ura ta shiga d'akin da sand'a dan kar Abdurrahim yaji zuwanta,inda Allah ya taimaketa Abdurrahim yayi barci dan ya gaji sosai kamar yadda yace. Na'ima daddumar sallarshi ta d'akko ta shimfid'a ta kwanta ak'asa , sai dai kasa bacci tayi sabo da sanyin k'asan haka taita juye-juye ,asubar fari talallab'a kafin Abdurrahim ya tashi tai saurin barin d'akin. Yau satin Hafiz d'aya da zuwa kenan,shak'uwace sosai ta shiga tsakanin Hafiz da Na'ima kuma har yanzu Hafiz bai san Na'ima ba matar Abdurrahim bace, kullum Na'ima tare da Abdurrahim suke kwana d'aki d'aya sai dai Abdurrahim bai tab'a sanin Na'ima d'akin shi take kwana ba, sabo da ba ta shiga d'akin sai yayi barci haka zataitajan Hafiz da fira dan Abdurrahim yayi barci kafin ta shiga ,bata yadda ya tashi ya ganta zatayi sammakon barin d'akin. Dan Hafiz ba ya yadda ya kwanta sai yaga shigar Na'ima sannan. Yauma kamar kullmum Hafiz Ya ce" Auntna yau kije ki kwanta da wuri dannima barci nakeji" Na'ima k'in tashi tayi haka taita jan Hafiz da hira har sai ta ta tabbatar Abdurrahim yayi barci sannan tayima Hafiz sallama ta tashi ta shiga cikin sand'a kamar yadda ta saba, saidai me tana shiga taga Abdurrahim.............. Ayi hak'uri da wrong typing๐Ÿ‘๐Ÿป Masu naiman Abdurrahim matuk'in jirgin ruwa daga farko basu samu ba zasu iya magana ta numbar nan 08063830828 ๐Ÿ›ฅ๏ธABDURRAHIM๐Ÿ›ฅ๏ธ MATUK'IN JIRGIN RUWA NE. ๐Ÿ””๐Ÿ“š *JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION๐Ÿ“š* Na Fadila Sani Bakori. Afuwa kwana biyu shiru๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป Page 20 & 21 Zaune Na'ima ta iske Abdurrahim yana daddan na wayarshi,bak'aramin shock ta ji ba gashi yaganta bare ta koma dan saida ya d'ago kai ya kalleta sannan ya yacigaba da danna wayar. Tsayuwa Na'ima tacigaba dayi abakin k'ofar dan takasa k'arasawa.Abdurrahim bai tankamataba cigaba da danna wayarshi yayi ita kuma da alama bata gaji da tsayuwar ba. "Lafiya? "Abdurrahim ya tambayi Na'ima. "dama Hafiz ne yadaman saidai in zo nan in kwanta" Inda ki ke kwana fa?" Shiru Na'ima tayi tana najarin abin da za ta ce ma Abdurrahim inda dai duk kwanan da ta ke yi d'akinshi bai sani ba. Na'ima cikin rashin sanin mafita ta ce "tom kullum haka yake min ai sai ya rako ni dole"Abdurrahim da bai gane maganar Na'ima ba ya ce "Ina ki ke kwana na ce? "A nan!" Na'ima taba Abdurrahim amsa kai tsaye. "Anan kuma?"Abdurrahim ya mai-mai ta, kai Na'ima ta d'aga mai ,Abdurrahim da mamaki ya bar abin da ya keyi ya tsaya yana kallan Na'ima ya ce "Wato sai nayi bacci ki ke lallab'owa ki shigomin d'aki ko? "Na'ima kanta ak'asa tana wasa da yatsun hannunta ta ce"Hafiz ne ke takuramin amma bada son raina ba" Banzan Abdurrahim ya yi da ita yagama danne-dannan wayarshi ya kwanta yana jiran yaga ina take kwanciya in ta shigo. Na'ima ko ci gaba da tsayuwa tayi sai da ta kintati lokacin da take tunanin Abdurrahim yayi bacci sannan ta lallab'a ta hau gadon ta d'akko addumar sallarshi ta shimfid'a ta kwanta ak'asa, saidai Na'ima batasan duk abin da take ba da ido d'aya๐Ÿ‘๏ธ Abdurrahim ke kallanta,Abdurrahim ko yana nan yana tunanin yadda zai b'illoma Hafiz akan haka har bacci kwashe shi. Kamar yadda Na'ima tasa ba tashi haka ta tashi ta shiga kitchen ta had'amasu abin kari suka karya kamar yadda suka saba. Bayan wata d'aya. Wata irin shak'uwa ce ta shiga tsakanin Hafiz da Na'ima yanzu haka yau satin shi hud'u kenan a k'asar.Duk lokacin da Na'ima zasu zauna suna fira da Hafiz sai taji kamar ta fad'a mai ita ba matar Abdurrahim ba ce ko Allah zai sa ya tausayamata ya mai da ta k'asarta, saidai daga ta tuno da auran gali dake kanta sai taji kwata-kwata bata sha'awar komawa k'asarta, lokuta dadama tunanin mamarta da k'annanta na damunta gashi yanzu hattayi wata d'aya da sati biyu kenan ak'asar . Na'ima na nan zaune tana ta tunane-tunananta Hafiz ya yazo bata sani ba,Hafiz ganin haka ya ce"Amaryar big bro lafiya kuwa? Tunanin wa ki ke haka ne?" Murmushi Na'ima tayi ta ce" Hafiz kenan tunanin wa zanyi Wanda yawuce na....." Kafin Na'ima ta idasa Hafiz ya rigata da cewa"Na Yayana ko?" . Dariya Na'ima tayi tace"kusan haka"Aunty Amarya yafa kamata yau mu je ki kaini inga gari tun da nazo sau biyu fa ki na gani mijinki ya fita dani" itama Na'ima dama ta gaji da zaman gidan dan haka da saurinta ta tashi ta ce"aiko tashi mu je kaga dama ni ma ina sha'awar fitar"Na'ima d'an kwalin rigar dake jikinta ta yafa suka fita a motar Abdurrahim. Yau da wuri Abdurrahim ya dawo gida, sai dai Yana tura k'ofar rufe yajita gam, tunani yafara tom ina suka je lallai Hafiz rawar kanka ta kai, da yagaji da jira number Hafiz d'in yakira gashi tana ringing amma ba ad'auka ba, yakira yafi ak'irga amma ank'iyin picking call d'in, hankalin shine yafara tashi yace karfa inje yarinyar nan fa ta fad'ama Hafiz gaskiyar lamarin yadda nake da ita.Abdurrahim yana nan tsaye bakalar tunanin da bai yi ba, yana nan tsaye sai ganin motarsu yayi tayi parking . Kallo d'aya zakaima Abdurrahim kasan rashin ab'ace yake. Hafiz da sauri ya k'araso wajanshi ya ce"Yi hakuri brother mun ma laifi, Wallahi kaga wadda tasanan muketa yawo"Hafiz yanuna Abdurrahim Na'ima yana mai ci gaba da cewa "gashi abin haushi ma tasa na manta...." tasssss! Ka ke ji Abdurrahim ya d'auke Hafiz da mari ya ce" Da Allah rufe min baki dama na lura baka da hankali kwata-kwata waya baka izinin fita da ita?" Zuk'unnar da kai Hafiz yayi yana dafe da gun da Abdurrahim ya maraishi. Abdurrahim ko yaci gaba da cewa" tom daga yau har kabar k'asar nan nahanaka magana da ita baki d'aya kaji ko?" Kai Hafiz ya d'agama Abdurrahim yana tunanin tsafin rai irinna Abdurrahim d'in. Shiko Abdurrahim bakomai yasa yayanke tarayyarsu ba sai tsoran kada Na'ima ta tona mai asiri danyaga shak'uwarsu kamar wa inda suka dad'e da sanin juna ne. Abdurrahim mai da kallanshi ga Na'ima yayi ya ce" daga yau kar insake ganin ku tare Ke ma zamanki na d'an lokacine ki kiyaye "yana kaiwa nan ya fusge key d'in dake hannun Na'ima ya bud'e gidan ya shiga yabar su agun a tsaye. "Mu je "Hafiz ya ce ma Na'ima, shiga su kai suna shiga Hafiz yayi hanyar bedroom d'in shi Na'ima tace"abinci fa?" kai Hafiz girgiza mata yawuce ciki. Ba wanda yaci abinci ya kwanta dan gidan kowa ranshi abace yake ,shi Hafiz bawai marin da Abdurrahim ya yi mai bane yab'ata mai rai a'a cewar yahanasu magana da Na'ima shine abin ya bashi haushi, itama b'angaran Na'ima hakane maganar d'aya ce hanasu Magana da Abdurrahim yayi ne yab'ata mata rai. B'angaran uban gayyar ko ko ajikinshi dan shi dad'in ma haka yaji dan dama kullum tunanin shi kar Na'ima tayi gigin fad'ama Hafiz gaskiya. Na'ima kwanciyarta tayi a falon ganin Hafiz ya shige ciki dama shike takura mata taje d'akin Abdurrahim ta kwana. Hafiz ko wayarshi ya manta hannun Na'ima yazo amsa yasan zatayi tunanin aje mai a falon,sai dai sai yana zuwa yaga Na'imar kwance a falon, Hafiz hannun kujerar da take kwance ya bubbuga bud'e idonta tayi tana kallanshi Hafiz ya ce "Haba Aunty amarya ba dai sabo da kina fushi da Yayana ba ne yasa kika gudo nan ki ka kwanta? Dan Allah tashi kawai ki shiga ki kwanta" Na'ima sanin nacin Hafiz da tayi ne yasa ba tai mai gaddama ba taje ta kwanta. shigo Abdurrahim alokacin yayi nisan tafiya a duniyar bacci. Cikin dare Na'ima tafarka da matsanan cin ciwan mara dama tunda wata yazo k'arshe kullum cikin fargaba take, juyi takeyi a d'akin gaba d'aya tafita hayya cinta, wayyoo Allah na zan mutu, wani irin nishi takeyi na wahala cikin bacci Abdurrahim yajiyo nishin Na'ima.Abdurrahiim tashi yayi da saurin shi ya kalli inda ta ke ta malele kuwa ak'asar tana rik'e k'asan cikinta,tana cewa "wayyo Allah na" haka Na'ima ke ta maimai tawa dakyar-dakyar. Abdurrahim sakko wa yayi daga kangadon da sauri yayo kanta dan bak'aramin tsoro ta bashi ba ganin yadda takeyi, jawota yayi yana girgizata ya ce " ke me ke damunki ne ? "Yayi mata tambayar da alamun tsoran ganin halin da take ciki . Na'ima cikin cije baki ta ce mai"Marata ke ciwo" irin na rannan?"Abdurrahim ya tamayeta."Eh irin shi ne"Abdurrahim sakinta yayi yafita yahad'omata tea da suga dayawa kamar yadda alheri tace mai wancan karan yayi mata. Cikin mintina k'alilan Abdurrahim ya had'o tea d'in yaji suga sosai yakawoma Na'ima, sai dai ko kallan shi batayi ba ta ci gaba da juyinta tsakar d'akin tana mai k'ara tamke marartata. Abdurrahim kusa da ita ya matsa ya tadota ya d'an jinginata da jikinshi irin yadda akema yara, sannan ya d'akko cup d'in tea d'in ya kai shi bakinta, Na'ima hannu tasa ta ture cup d'in dan ji take bazata iya shaba , turewar da za tai ko tea d'in ya kusa barema Abdurrahim ajiki,hakan yasa Abdurrahim ya tunkod'eta da saurinsa ya ce "ke ki ka sani kuma daga wannan watan bazakisake min wannan ciwan agida ba daga Hafiz yatafi kema za ki san inda dare yayi Maki ke ma, dan kin samu ma tsabar samun guri zaki ture cup d'in ki zubar da shi a k'asa ina jin bacin na kaucema da ajikina za ki zuba min ke ki ka sani" Yana kai wanan yabar mata d'akin ya koma falo ya kwanta, sai dai ko da ya kwanta sai yaji duk ba dad'i abin da yayi mata,azuciyarshi ya ce Allah ya baki lafiya ki samu ki bacci inda kin zubar da maganin.Duk yadda Abdurrahim yaso bacci ya kwasheshi kasawa yayi sabo da tunanin halin da Na'ima take, dan gaba d'aya tunanin halin da Na'ima take ya hanashi sukuni gashi ya kasa zuwa dubata tsabar haushin zubar da tea d'in da tayi. Abdurrahim Sai da yayi sallar a suba sannan ya shiga d'akin dan ganin halin da Na'ima take ciki, Masha Allah bakamar jiya ba sai dai abin da be sani ba yanzu abin yafi na jiya dan yanzu ko juyin ma yagagareta , takure take guri d'aya ga rigarta duk ta b'aci da jini. Abdurrahim matsawa yayi kusa da Na'ima ya kirata ahankali amma Na'ima shiru bata amsa ba kuma tanajin shi motsin ne bata son yi,Abdurrahim ko jin tayi shiru matsawa yayi kusa da ita da sauri ya sa hannu ya ya d'an bubbugata yana mai cewa"Kee"Abdurrahim jin Na'ima shiru ga idonta arufe yake sai yaji kamar d'ayar take jan numfashi ma d'agota yayi sai yaga kad'an-kad'an take fidda shi tsabar tagama galabaita. Abdurrahim tunanin kaita asibiti yayi karta mace mai anan, saidai koda ya duba duk ta b'ata rigar jikinta da jini, batare da tunanin komai ba yakama rigarta zai cire, cikin d'an sauran k'arfin da yaragema Na'ima ta rik'e hannun shi,Abdurrahim ko cikin tausaya mata ya ce"Ki yi hak'uri taimakonki zanyi riga zan canza miki in kaiki asibiti" Abdurrahim na fad'in haka ya kama rigar ya zare mata ita ajikinta, sannan ya je inda yake tunanin kayanta ne ya d'akko mata wata rigar zaisamata sai asannan idon shi ya kai ga halitarta,rin tse ido Abdurrahim yayi yana mai son sa mata rigar kuma kasan cewar idonshi arufe yake ya kasa,dan gaba d'aya wani irin kasala da sanyi ya rufe shi,haka dai ya daure cikin sanyi jiki da mutuwar gab'b'ai ya zura mata rigar sanna ya shiga d'akin Hafiz.Zaune ya iske Hafiz d'in alamun bai da d'e da idar da Sallah ba, Abdurrahim kallan Hafiz yayi ya ce"Hafiz zan kai yarinyar nan asibiti batada lafiya" "Subhallah me ke da munta?" Wai lokacin menstruation d'inta ne yayi tom tana shan wahala. Hafiz kallan Abdurrahim yayi ya ce"Brother kamanta aikina kenan abin da nake karanta kenan? bari da akwai magungunan da zan rubuta ma ka amso mata zata samu sauk'i insha Allah dama wasu haka yake musu"Hafiz rubuta ma Abdurrahim magungunan ya yi. Abdurrahim na amsawa yaje ya siyo mata. Cikin ikon Allah Na'ima na shan maganin ciwan yalafa ma ta bacci yayi awan gaba da ita. Ko da Na'ima tatashi jitai kamar anzare mata ciwan baki d'aya. Na'ima koda ta fito Hafiz ya jiki kawai yayi mata yayi shiru inda Abdurrahim ya hanasu magana, in kaga Na'ima suna magana da Hafiz tom Abdurrahim baya nan daga yadawo shikanan ,hakan sai yasa Hafiz yaji jaman duk ba dad'i ya isheshi. Ranar da Hafiz yacika sati shida da zuwa ranar ya shirya tafiya kamar yadda yafad'ama Abdurrahim, saidai ita Na'ima bata san da maganar tafiyar Hafiz d'in ba saidai ta gan shi da kaya, sallama Hafiz yayi ma Na'ima sannan yabata number shi ko da Abdurrahim ya sai mata waya acewarshi. Na'ima bataji da'in tafiyar Hafiz ba ko kad'an dan bak'aramin sabo tayi da shi ba, bayan Hafiz yatafine taji gidan duk ba dad'i cire kayanta ta shiga wanka ko zataji dad'i.Bayan Na'ima tafito wankane tana cikin shiryawa Abdurrahim ya shigo d'akin , k'ara Na'ima tasaki tai sauri tajawo rigar da ta cire ta d'akko ta kare kirjinta da ita .Inda Na'im take tsaye Abdurrahim yanufa, Na'ima kai take girgizama Abdurrahim alamun karya k'araso inda take amma shikan shi Abdurrahim besan dalilin k'arasawar ba umarnin zuciyarshi kawai ya ke bi da gangar jikinshi,yana kaiwa kusa da Na'ima y........... Ayi hak'uri da wrong typing๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป ๐Ÿ›ฅ๏ธ ABDURRAHIM๐Ÿ›ฅ๏ธ MATUK'IN JIRGIN RUW NE ๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ…™๏ธŽ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‚๐—บ๐—ฎ๐—ถ ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐—ฟ๐—ถ๐˜๐—ฒ๐—ฟ๐˜€ ๐Ÿ…๏ธŽ๐˜€๐˜€๐—ผ๐—ฐ๐—ถ๐—ฎ๐˜๐—ฒ๐—ฑ๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ–Š Na Fadila Sani Bakori Page 22 & 23. Kai Na'ima ke girgiza ma Abdurrahim tana cewa"dan Allah karka k'araso inda nake" amma ina Abdurrahim bai fasa ba yana zuwa yasa hannu ya jawota jikinshi "Wayyoo Allah na dan girman Allah ka sake ni" cewar Na'ima da duk ta furgice."Sheeet" Abdurrahim yace ya ce mata "Uban wa ya ki tsaya min gida ahaka?, nan gidan kune?" Kai Na'ima ta girgiza ta ce"Wanka nayi Wallahi yanzu haka kaya ma zansa ka gama kayan nan na ciro " duk cikin furgici Na'ima take fad'in duk abin da take fad'a. "Tom d'akko kayan kisa"cewar Abdurrahim har yanzu yana rik'e da ita ba wai ya saketa bane, "tom ka sakeni dan Allah"sakinta Abdurrahim yayi yana maimamakin kanshi da abin da ya aikata, Na'ima ko na ganin Abdurrahim yasaketa tai saurin d'akko rigar da tacire tamaidata ,tana gama sawa tayi saurin juyawa zata fita d'akin, hannunta Abdurrahim ya jawo ya ce" Ina kuma zaki?"Dan Allah ni gidanmu nake son komawa" cewar Na'ima da duk tagama furgita da Abdurrahim dan ita da kallan mutunin kirki take mai shiyasa tasaki jiki tai zamanta agidan. Shiru Abdurrahim yayi sannan ya ce"Gida kuma?" Kai Na'ima ta d'aga mai alamun Eh. Shiru Abdurrahim yayi yana mai rik'e da hannun Na'ima har yanzu ,kamar yana tunani sai zuwa can ya ce" Me ya sa ki ke son zuwa gidan? " Na'ima kanta ak'asa ta ce "Sabo da bana son abin da kayimin yanzu ya sake faruwa"Abdurrahim kallan Na'ima yayi ya tab'e baki ya ce"ina ne gidan naku ?" kaduna sabon yalwa "Na'ima ta bashi amsa." ki na da kud'in jirgi ne?" Abdurrahim ya tambayi Na'ima. kai Na'ima ta girgiza mai alamun

Chapter 5 of 8