da ya tashi ko da ya fito daga d'akin shi kallan inda Na'ima take kwance yayi na 'yan seconds Kafin ya juya ya shiga kitchen ya had'a ma kan shi abin kari, bayan ya kammala Karin ne, yaciro wayar shi ya ci gaba da chart da friend's d'in shi.
Na'ima ko tarasa yadda zatayi ta tashi sabo da rigar ta duk tab'aci da jini,dama kuma idan menstruation d'in mutum ya zo ya sha tea ko kunu da suga da yawa haka yake zubar jini sosai.
Na'ima da tarasa yadda zatayi komawa tayi taci gaba da kwanciyarta tana nan kwance Abdurrahim har ya dawo ya shiga d'akin shi yayi wanka ya fito, da alama fita zai yi da Na'ima ta tabbatar in bata cire kunya ba taima Abdurrahim magana ya tafi batasan ya zata yi ba.Naima kallan Abdurrahim ta yi ta ce "Ina kwana"Lafiya,ya jikin naki?"Abdurrahim ya fad'a ba tare da ya kalle ta ba."Na ji sauk'i dan Allah ka taimakamin da pants da always"Abdurrahim be amsa ma Na'ima ba yaci gaba da tafiyar shi gidan alheri ya je ya bata ATM card na shi ya ce"Ga shi ki siyo min kayan mata na sawa da duk wani abu da mace ke amfani da shi"Alheri kallan Abdurrahim tayi ta ce"Nasan yarinyar nan zaka sai mawa ta gidanka ko? "Kai Abdurrahim ya d'aga mata alamun eh, tun da na ke da kai baka tab'a min kara ba ka sai min wani abu, haka da birthday d'ina baka ban ko mai ba duk ban damu ba amma gaskiya yanzu na damu.
Alheri kallan Abdurrahim ta yi ta ce "Abdurrahim ya ka ke da yarinyar nan,ka fad'amin gaskiya?"Bansanta ba na ce miki" Tom shikenan, bakasanta ba ka ce ko? "Alheri ta ce.
Kai Abdurrahim ya d'aga mata alamun eh, shikenan bari inje in suyo mata ka jirani ina zuwa.
Alheri bacin ta suyoma Na'ima duk wani abu daya kamata, takama hanyar zuwa gidan Abdurrahim, dan ace warta sai ta tanbayi yarinyar taji ta bakinta akan alk'arta da Abdurrahim d'in.
Na'ima ko tana ganin Abdurrahim ya fita ta tashi ta cire rigar da ke jikin ta ta d'akko ta Abdurrahim da ta tab'a sawa tasa inda ita duk atunanin ta ya tafi aiki ne.
Na'ima zaune take tana shan sauran tea d'in da yarage dakyar ma take shan tea d'in sabo da ya huce.
Alheri ko da ya ke tana da key d'in gidan Abdurrahim yasa tana zuwa ta bud'e ta shiga zaune ta iske Na'ima tana shan tea abin ta. "Keee alheri ta kira sunanta da gurb'atacciyar hausar ta ta ce"Wayasaka kasa wannan rigar? " Shiru Na'ima ta yi dan ba ta san amsar da zata ba ta ba.
Alheri jin Na'ima tayi shiru ta kuma cewa"Kai na ce ubanwa ya saka kasa wannan rigar? " Na'ima da duk ta gama daburcewa sai cewa tayi"Shima ya ganni da ita rannan bai ce ko mai ba kuma d...... " Marin da alheri ta wankama Na'ima ne ya hanata k'asara abin da tayi niyyar fad'a cikin tsantsar b'acin rai Na'ima ta ta shi rik'e da kunci ta ce"Bai war Allah mai ne miki zaki maran ko shima mairigar da ya ganni da ita ai bai cimin komai ba" Na mare ka dan ubanka" cewar alheri.
Na'ima ko cikin jin zafin zagin mahaifinta da akayi ta ce" ka da ki sake zagar min ubana yana kabari" Uban ka na ce na ce ubanka-ubanka" wani uban kukan kura Na'ima ta yi ta afka ma alheri, da ya ke alheri irin manyamanyan matan nan ce Wanda zaka gansu ga tsawo ga k'iba yasa ta rik'e Na'ima tai ta duka ,da taga abin bai ma ta ba shak'eta ta yi ta ce"Dan ubanka ya ka ke da Abdurrahim?"Ba dai ubana ba" cewar Na'ima.
Janta alheri ta ci gaba dayi ta ce"Inda bazaka fad'amin yadda kake da Abdurrahim ba, tom yanzun nan zakabar gidan nan dan ubanka" janta alheri tai ta yi har zuwa hanyar fita falon, Na'ima kuma sai cijewa take da d'an k'aramin k'arfin ta.Alheri ta ce"Dan ubanka gidan na ubanka ne Da bazaka fita ba? " ke ma gidan ai ba na ubanki ba ne"Ai alheri jin Na'ima ta zageta itama rud'ewa tayi tai ta bugun Na'ima tun k'arfin ta.
Abdurrahim ko yana can gidan alheri yana jiranta ta dawo, da ya ji shirun yayi yawa kiranta yayi awaya amma bata d'auka ba,rufe mata gidan ta ya yi Shikuma ya yo gida. Tun kafin ya gama parking motar sa yake jin hayaniya da saurinsa ya k'araso cikin gidan alheri ya iske tana tura Na'ima waje had'e da kai mata duka, tana sai ta fita inda gidan bana ubanta bane, ita kuma tana cijewa tana cewa bazata fita ba inda gidan banata ba ne.
Wata uwar tsawa Abdurrahim ya bugama alheri ya ce"Wa ya saki? " Alheri ko da ranta ya b'ace jin abin da Abdurrahim yace mata ta ce" Haka zaka cemin ko wayasani ,tom na rantse da d'unbun son da na ke ma yau sai ta b'ar gidan nan ,waya ce ma yasa ma ka riga" da ya ke haka take hausarta namiji ta mai dashi mace mace ta mai da ta namiji, itako Na'ima ta rakub'e gefe bak'inciki yasa sai kuka take yi, alheri kuma nuna Na'ima tayi da ke kuka ta ce"Kab'ar gidan nan nace" Allah sarki Na'ima ko kallanta batayi ba taci gaba da kukan ta, tun kud'ata alheri tayi tun karfinta Na'ima sai da ta bugu da get d'in dake gidan sannan tatafi taga-taga kamar zata fad'i wani k'arfe da ke kusa da Na'ima Na'ima ta d'auka ta yi kan alheri da shi alheri da taga bata da wani abu da zata kare kanta rugawa tayi sai dai duk inda tayi Na'ima binta take yi da gudunta ita ala dole sai ta bugamata alheri shi. ihu alheri ke yi Na'ima ko bata fasa bin ta ba. Abdurrahim da yaga indai ya kyalesu Na'ima zatai ma alheri rauni indai ta bugamata ,dai-dai ko Abdurrahim zai amse k'arfan Allah yaba Na'ima sa'a ta bugama alheri shi, dan ma Allah yasa ahannu ta same ta ba akai ba, wata uwar k'ara alheri ta yi ta zuk'unna agun tana rirrik'e hannun ta re da alkawarin sai taci uban Na'ima.
Da kyar Abdurrahim ya lallabi alheri ta tafi gida, ita kuma Na'ima tana ganin wucewar alheri ta kama hanya zata koma gidan hannu Abdurrahim yad'aga mata ya ce"Kar ki sa ke ki koma min gida" ya na kai wa nan ya shige ya b'arta agun.
Waiwaiye adon tafiya inji Hausawa,can kaduna ko gwaggo jerawa su kai da Mariya mahaifiyar Na'ima har'gidan da Na'ima take aiki kasan cewar me gadin ya gane gwaggo yasa ya barsu suka shiga kai tsaye, alokacin Hajiya Rahina tana waya da k'awarta Hajiya Suwaiba matar da gwaggo ke aiki a gidan ta,Hajiya Rahina ganin su gwaggo najiranta yasa ta katse wayar ta cema Hajiya suwaiba zata kirata anjima tayi bak'i ,sannan ta juya tana kallan su gwaggo ta ce " sannun ku da zuwa gwaggo" nan dai suka gama gaggaisawa, sannan gwaggo ta kalli Hajiya Rahina ta ce"Hajiya wannan da kike gani ita ce mahaifiyar Na'ima, na kawota ne in fad'amata yadda mukayi da Na'ima agabanki dan kar'ta zargan da cin amanar yarinyar ta" gwaggo ta ci gaba da cewa"Mariya bayan kin zo kinsanar da kina son Na'ima ta dawo gida sabo da auran da aka d'aura mata, tabbas agabanki Na'ima bata nuna komai ba, tom ammafa bayan kin tafi ga Hajiya nan itace sheda, Na'ima ta zauna sai rusamana kuka take tana rokan Hajiya akan dan Allah kasar da za'a d'akko ma Hajiya kaya za ai tafiyar dogon zango ta roki hajiya aje da ita wai kafin lokacin k'ila asamu mafita dan ita bazata auri mutumin da mahaifinta yabar wasiyar kar ta aura ba, hajiya tace ma Na'ima ita bazata d'auketa ba ta kai ta doguwar tafiya batare da amincewar ko wa na ta ba, sai dai ta fad'a ma mahaifiyar ta in ta amince, Mariya in tak'aicemiki magana Na'ima tazo tasamin kuka akan sai dai in amince aitafiyar da ita. Tom Allah yasani tausayin Na'ima yasani amincewa ,kin ji yadda akayi wallahi"
Kiran da akaima Hajiya Rahina ne awaya yahana mahaifiyar Na'ima magana, cikin furgici Hajiya Rahina ta tashi tsaye ta ce"Accident , kana nufin jirgin ruwan da ya d'akko kayan mu yayi accident?" Banji me akacemata ba daga can b'angaran naji tana cewa"Innalillahi'wa ina ilaihirraj'un, kana nufin ba aga Na'ima ba?" kashe wayar Hajiya Rahina tayi ta dafe kai tana karanto duk addu'ar da tazo bakinta.
Tun kafin Hajiya Rahina tayi masu gwaggo k'arin bayani suka fahimci duk abinda yafaru.
Kuka mahaifiyar Na'ima takeyi sosai tana fad'in "Allah sarki Na'ima ashe haduwar da mukayi itace ganawar mu tak'arshe"
Dukkansu Sunyi kukan su san rai dan bamai ba wani hak'uri, sai da mijin Hajiya Rahina ya dawo yayi masu nasiha akan shi komai da kuka gani muk'addarine daga Allah tunrar gini tunrar zane, nan dai alhaji yayi ta masu nasiha har Allah yasa jikinsu duka yayi sanyi bakamar maman Na'ima ba, saidai ita kad'ai tasan irin rad'adin da takeji acan k'asan zuciyar ta, Alhaji da kan shi yad'auki mama amotar sa shida Hajiya Rahina da gwaggo suka rakata har gida, bayan sun isa ne Alhaji yak'arayima ma mahaifiyar Na'ima nasiha sosai, sannan yaciro kud'i masu yawa yabata.
Kafin kace me mutuwar Na'ima takauraye duka sabon yalwa, koda labarin mutuwar ya isa kunnan dan gin baban ta, har gida su ka je sukacima mama mutumci sannan suka ce mata sunanan suna jiran dawowar Na'ima duk inda ta kaita," k'aryar banza in mutuwa ta yi dagaske kamar yadda ki ka ce ina gawar ta? " Cewar jimmai mahaifiyar gali Wanda aka d'aura auran sa da Na'ima.
Can b'angaran Na'ima ko tana ganin Abdurrahim yayi shigewar sa cikin gidansa ta na kuka ta fita daga gidan..........
🛥️ ABDURRAHIM🛥️
MATUK'IN JIRGIN RUWA NE.
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚*
Na
Fadila Sani Bakori.
Wannan shafin gaba d'ayanshi na sadaukar da shi ga 'yar'uwata barrister Hassana Sani,Allah ya taimakeki yabada sa'ar jarabawa🙏🏻🙏🏻
Page 16 & 17.
Na'ima ko da ta fita daga gidan ja tai ta tsaya tana kuka dan bata san inda zata ba gashi duk inda zata waiga masu ja-ja yan kunne kawai take gani suma jefi-jefi turawa kenan.
Na'ima na nanan tsaye sai ga wani bak'in kare yana kewaye unguwar yana zaro harshe, duk dare Wannan karan shike gadin unguwar, Na'ima ganin karan nan na tunkarota yasa tafara ja da baya ganin karan da gaske gunta ya yo yasa ta juya ta shige gidan Abdurrahim da gudunta, tana shiga taja k'ofar ta rufe, amma duk da haka jikinta be dai na rawa ba dan ta matuk'ar tsorata da karan, cikin tsoro Na'ima ta samu can gefe agidan ta rakub'e tana mai addu'ar da duk tazo bakinta. Na'ima na nan zaune agun har wani wahalallan bacci ya kwasheta.
Can b'angaran Abdurrahim ko sai bayan ya shiga gida ya ke jin abin da yayi ma Na'ima bai kyauta ba dan dagagani yarinyar batasan inda zata ba, "Tom ai garama da yayi mata haka dan yarinyar tana bashi haushi gashi tak'i fad'a mai dalilin zuwanta garin "Tofa in ban da abin ka Abdurrahim ba sai ka tambaye ta zata fad'ama ba"inji wani tunanin nashi kenan.
Abdurrahim tunawa da yayi be rufe gida ba ne yasa ya tashi ya nufi wajan get d'in dan rufe gidan, torch light d'in wayarshi ya haska ya rufe gidan dan shi daga dare yayi Yake kashe hasken gidan.Bayan ya rufe gidan ne ya juyo sai ya ga abu kamar mutum ya k'udindine awaje d'aya kusan mutuk'an jirgin ruwa basu da tsoro k'arasawa wajan yayi amma abin mamaki Na'ima ya gani kwance agun ta k'udindine jikinta tana barci abun ta.
Bak'aramin tausai Na'ima ta ba Abdurrahim ba ji ya yi tausayinta gaba d'aya ya cika zuciyarshi.
Abdurrahim ya dad'e atsaye akan Na'ima sannan ya lallab'a yadda ba zata tashi ba ya d'akko ta kamar k'aramar baby ya yi cikin gidan da ita, d'akinta ya kwantar da ita ya ja blanket ya rufe ta sannan ya je d'akin shi shi ma ya kwanta.
Abin mamaki washegari Abdurrahim har ya yi abin da zaiyi na karyawa (breakfast) amma Na'ima bata tashi ba, har ya gama danne-dannan wayarshi ya je ya watsa ruwa,sannan jin shirun yayi yawa ya je ya k'ara dubata, still bata tashi ba, tunani ya farayi anya ko lafiya dan yau satinta uku ke nan agidan amma bata tab'a kai haka tana barci ba.
Abdurrahim shiryawa yayi ya fita gidan dan zuwa ganin yadda alheri ta kwana ya duba hannun ta da Na'ima ta ji mata ciwo kafin tai mai k'orafi.
Na'ima kamar jira ta ke Abdurrahim ya fita yana fita ta tashi, kallan d'akin ta farayi tana tunanin ya akai ta dawo nan,"Kai sai dai in dawo da ni akai" Na'ima ta dad'e tana tunanin yadda akai ta dawo d'akin amma bata samo ba, daga k'arshe tai tunanin k'ila bacci ne ya kwasheta shikuma da yazo rufe gida yatadata ta shigo, kai amma wani irin nauyin barci garan haka, tom amma in haka ne yayi min hak'uri ne inda yakoran daga gidan, nan dai takasa gano amsar ya yi mata ha'kuri ko kuwa daga k'arshe ta tashi ta shiga toilet tai wanka ta cire rigar Abdurrahim dake jikinta ta mai da tata data wanke, tom nan fa yunwa tace itama gatanan zuwa.
falon Na'ima ta koma, tananan zaune yunwa nak'aracinta Abdurrahim ya dawo gidan, Na'ima tashi tayi daga kwancen da take da sauri ta ce "Ina kwana" Lafiya ya jikinnaki ?"Abdurrahim ya fad'i maganar yana kallanta da kulawa." Na ji sauk'i sai dai,,,,,,,, "shiru Na'ima tayi takasa k'arasawa.
Abdurrahim kallan Na'ima yayi jin tayi shiru,kamar yayi banza ya rabu da ita sai kuma yaji bazai iya ba dan ahalin yanzu yarinyar tausai take ba shi.Abdurrahim kallan Na'ima yayi ya ce "Sai dai me?"
Na'ima cikin jin nauyi ta ce "Dan Allah in karage abinci ina jin yunwa"Meyasa bik,,,,," banko k'ofar da alheri tayi ne yahana Abdurrahim k'arasa abin da yayi niyya kallan shi alheri tayi sannan tace"Abdurrahim kana ganin abin da yarinyar nan tayi min jiya amma bazakazo dubani ba ko?" Ke da Allah malama nazo dubaki kin tafi yawanki"
Shiru alheri tayi dan tabbas bad a gida take ba.Alheri kallan Na'ima tayi da ke tsaye da alamun magana suke da Abdurrahim ,alheri ta ce" Tom shikenan, amma jiya ai naji kace kakori yarinyar nan ya akai ta dawo?"Abdurrahim batare da ya kalli alheri ba ya ce" Sabo da bata da inda zata shiyasa ta dawo "
Shiru alheri tayi sannan zuwa can ta ce " Yanzu kana nufin ta dawo nan dazama kenan? " Abdurrahim da yagaji da tambayoyin alheri banza yayi da ita .
Alheri ko jin Abdurrahim yayi banza da ita ga kishin zaman shi da Na'ima da ke damunta sai cewa tayi"Shikenan ni ma yau-yau d'innan zan dawo nan gidan da zama, dan banyarda da zamanka da wannan yarinyar ba"Abdurrahim batare da yana mai ci gaba da danna wayar shi ya ce batare da ya kalli alheri ba" Amma dai kinsan ba ni da d'aki ko?"Sai muyi manage hakanan" cewar alheri. Abdurrahim shiru yayi yana tuna alherorin da alheri taimai ,hakan yasa yakasa hanata amma acikin zuciyar shi bayason zamanta gidan.
Alheri ko bata saurari amsar Abdurrahim ba ta ce " Bari inje in kwaso abubuwan amfanina" Abdurrahim ko kai kawai ya iya d'agama alheri.
Bayan fitar alheri ne Na'ima da ke nan tsaye har yanzu ta kalli Abdurraahim ta ce" Dan Allah in karage abinci ka taimakamin"dan zuwa lokacin Na'ima yunwa take ji sosai.
Abdurrahim d'aga kai yayi ya kalleta ya ce "banrageba,amma ki je kitchen akwai komai sai ki had'a ko tea ne ma " Ai ban iya kunna abun da kuke girkin bane" Muje in gwada "
Abdurrahim nuna ma Na'ima yayi yadda ake amfanin da duk kayan
Wutan sannan yace mata duk lokacin da take da buk'atar abinci ta dafa duk abinda zata iyaci. godiya sosai Na'ima tayi mai amma bai tankamata ba yawuce abinsa.
Kamar yadda alheri tace haka ko akayi dan duk wani Abu na amfaninta tadawo dashi gidan, d'akin dayazaman na Na'ima nan alheri takai kayanta ta jera, koda Na'ima taga haka gudun rigima kayan da Abdurrahim yabata Wanda alheri tasiyo kwaso kayan tayi daga d'akin duk da basu wani burgetaba dan duk k'ananun kaya ne sai dogayan ruguna guda uku sune ma masu dama-dama akayan,a falo Na'ima ta dawo da kayanta.
Shiko Abdurrahim tun da yafita sai dare ya dawo gidan, dan juwan alheri gidan sai yaji abun duk ba dad'i.
Ko da ya dawo a falon yaga Na'ima kwance, bece komai ba dan yasan alheri ce zatasata tadawo nan, ko inda alheri take be kallaba yawuce ciki abinsa, alheri tashi tayi tabi bayan shi har izuwa bedroom d'insa, kusa dashi ta zauna ta mai d'aura kanta akafad'ar shi ta ce"Abdurrahim kamar baka murna dawota kusa da kai ,Shine kazo koma ka kallan kai wucewarka ko? " Banlura da ke ba ne,amma meyasa kika kori yarinyar can ta koma falo bayan kuma ita kika iske awajan?"Alheri cikin jin haushin abin da Abdurrahim yace ta ce "Sabo da nafita iko da komai nagidan nan shiyasa , i swaer Abdurrahim indai kak'ara nunamin yarainyar nan kamar tafi matsayi awajanka ranar sai ta bar gidan nan ko kuma in b'atar da ita baki d'aya" Alheri na kawai nan ta tashi cijin jin zafi tabar wajan.
Washegari ranar ne yakasan ce Abdurrahim zai koma wajan aiki, yanagama shirinsa yafito zai fita kenan ya iske alheri itama ta shirya zata fita, tare suka fita, Na'ima najin duk wani motsun su tashi ne kawai da batayi ba tana jin fitar su ta ta shi ta gyara gidan duk wani abu mai k'ura saida ta goge shi sannan ta d'ora makanta abin kari.
Na'ima na nan zaune tana karyawa alheri ta shigo da kukan ta, ko inda Na'ima take bata kallaba tai gaba cikin mintina kad'an sai gata ta fito da jakar kayanta, kallanta Na'ima takeyi damamaki ba damar tambaya dan abun da take tunani Abdurrahim ne ya koreta agidan.
Kamar yadda Abdurrahim yasaba dawowa haka yadawo, zaune ya iske Na'ima a falon yana zama wayar shi nayin ringing, da mamaki ya bi number da kallo ganin number k'anin shi ,cikin mamaki ya d'aga kiran damamki ya d'auka dan sunfi magana ta WhatsApp basu cika waya ba.Abdurrahim,da mamaki ya ce jin abin da mai Kiran wayar yace ya ce" Inzo in bud'e maka gida kuma" cikin rud'ewa da mamaki yayi maganar, kallan Na'ima yayi itama shi take kallo yace mata" k'aninane yazo yanzu yazanyi idan ya ganki kuma inajin zai dad'e betafi ba dan yadad'e yana son zuwa"Wani kiran ne yak'ara shigowa wayarshi da sauri ya tashi yafita Na'ma ta bi shi da kallo.
"Kai broz ai na yi tunanin bazaka fito ba ne? " kai Abdurrahim ya d'an sosa alamun rashin gaskiya ya ce"Ina can inama k'anwarka fad'a batayi girki ba" k'anwata kuma?"
Cewar Hafiz da mamaki.Abdurrahim cikin tabbatarwa ya ce "K'nwarka kuwa, ai nayi aure bada sanin ku ba, tom dole ce tasa haka dai yarinyar marainiya ce"Hafiz da tsatsanin mamaki ya kuma cewa "Aure kuma broz? "Eh aure ka ga na huta da surutun su mommy ko, sannan kuma nayi surprise d'inku" Hakane" cewar Hafiz dan shi yayarda da maganar yayan nashi.
Itako Na'ima kafin su shigo tabar falon dan ta lura b'ako yayi kuma bayason yaganta shiyasa tayi shigewarta ciki bayan sun shigone Abdurrahim yace ma Hafiz yana zuwa , d'akin da Na'ima ta shiga ya shiga zaune ya isketa tayi ta gumi, kallanta Abdurrahim yayi nad'an lokaci haka nan sai yaji yanajin nauyin fad'amata abin da ya ko son fad'a,sannan dai ya daure ya ce" kee ya sunan ki? " Na'ima kallan Abdurrahim tayi sannan ta ce" Na'ima" Yauwa to nayi bak'o k'aninane yazo uwarmu d'aya ubanmu d'aya, tom akwai damuwa yaganmu tare kuma ke baki da inda zaki, ko kinada inda zaji?" kai Na'im ta girgiza mai alabun bata da shi.Abdurrahim yaci gaba da cewa " Tom nace mai ke matata ce, dan haka sai kirik'a behavioural kamar matata kingane ko...........
Ayi hak'uri da wrong typing 👏
🛥️ ABDURRAHIM 🛥️
MATUK'IN JIRGIN RUWA NE.
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S A SSOCIATION📚*
Na
Fadila sani Bakori
Page 18 & 19
Shiru Na'ima tayi tsabar al'ajabin maganar Abdurrahim,Abdurrahim kuma jin Na'ima tayi shiru ya kuma cewa "Wai bi ki ji ba ne? Nace kirik'a behavioural kamar matata idan ba haka ba da akwai damuwa idan Hafiz yaje gida ya sanar ina zaune da mace kin ga dole zasuyi wani zargin da bahaka ba ne ".Kai Na'ima ta d'agama Abdurrahim alamun ta gane.
Shiru Abdirrahim yayi sannan ya ce"Yauwa kin iya girki ko? Kinga munyi bak'o kuma yanada buk'atar abinci"Nan ma dai Na'ima kai ta d'aga ma Abdurrahim alamun Eh."Oh"Abdurrahim Yace ya ce " Kirik'a amsamin da bakinki mana" Tom"Na'im tace ahankali. "Yauwa tom yanzu bari in koma falon kar ya jini shiru"
'Hafiz mutanan England" cewar Abdurrahim da fitowar shi falon kenan.
Hafiza da fara'arshi ya ce dan shi mai fara'a ne"Broz Allah maganar auran nan taka ta d'aure min kai, dama zaka iyayin aure ba da saninsu mommy ba? "Kabari kawai Hafiz yarinyar auran tausayi nayi da ita bawai so ba ne, yanzu haka sonake Idan nagama shirina in kaita mahaifarsu"Hafiz da mamaki ya kalli Abdurrahim ya ce "Mahaifarsu kuma? Tom auran fa? " Tom Hafiz ina tsoran karsu mommy su k'i aminta da auran ,gara idan nai musu bayani suka aminta sai inje garinsu in kaita nan wajansu" Shiru Hafiz yayi yana kallan Abdurrahim bai ce komai ba,Abdurrahim kuma yaci gaba da cewa"Nasan kanada surutu saura inji maganar auran nan bakin mommy dan nafi so in sanar da ita da kaina, kaji dai abin da nacema ko? "Insha Allah broz bazataji ba,inda baka son ta sani abakina"
Nan dai kowa yayi shiru da tunanin da yake ,sai zuwa can Hafiz ya kalli Abdurrahim ya ce " Tom ita Auntyn ta wa bazata zo mu gaisaba ne? " Kai Abdurrahim ya sosa ya ce"Bari inje in fito da'ita"
Na'ima na kwance tanajin motsin alamun shigowa tai sauri ta ta shi ko inda take Abdurrahim be kallaba ya ce" So ki ke ki ruguzamin plan ko? Tom rugujewar plan d'in nan dai-dai yake da barinki gidan nan duk inda zaki kije babu ruwana, yanzu in kiga dama ki zo ku gaisa"Abdurrahim na kai wa nan yafita abinsa.
Bayan shi Na'ima tabi da k'ak'aro murmushin dole na tarbar bak'o tana zuwa falon ta ce"Snnu da zuwa"Tana fad'i maganar tana mai zuk'unnar da kai kamar wadda tayi k'arya asirinta yatonu.
kallanta Hafiz yayi mai makon ya amsa gaisuwarta sai cewa"Wow broz your wife she is very very beautiful, gaskiya ka'iya zab'e" Sannan ya maida kallan shi ga Na'ima ya ce " Auntyna kin ganki kuwa? kamar ke kikayi kanki, dan Allah ki na da k'anwa ina rik'o" Da ya ke Hafiz irin mutanan nan ne masu b'arkwanci. Abdurrahim kallan Hafiz yayi