Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 9
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 💦 AKWAI SILA💦 BY AMANARCOOL YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION/ YOTA ID/O21 Godiyata ba za ta gushe a gare ki ba Aysharcool. A matsayin ki na uwa a gare ni a Duniyar marubuta, kuma ƴar uwa amintacciyata, na tsinci kaina cikin wani gata da ba kowa ke samu ba. Kin riƙe mini hannu da gaskiya da amana, kina faɗa min abin da ban sani ba cikin natsuwa da kulawa. Duk irin hasken da zan samu a harkar rubutu ki ce sila, akwai gudummawarki, akwai tausayi da jajircewarki. Ina alfahari da ke, kuma ina yi miki godiya mai yawa wadda baki ba zai iya faɗa ba. Allah ya saka miki da alkhair, ya ƙaro miki ɗinbin nasarori a rayuwarki. Ina mika godiya ta musamman ga shuwagabannin ƙungiyarmu, musamman Aunty Sarauta da Aunty Zee Kumurya, bisa irin kulawa, gyara da shawarwari masu daraja da kuke bani a kan rubutuna. Goyon bayan da kuke bani ya ƙara mini kuzari da ƙarfin gwiwa sosai. Allah ya saka da alkhairi, ya ci gaba da ɗaukaka ku a duk inda kuka dosa. بسم الله الر حمن الر حيم PAGE 1-2 Misalin ƙarfe goma na dare, daren ya yi duhu sosai irin duhun nan da yake cinye inuwa ya bar zuciya. Garin ya yi tsit ba ka jin motsin komai, cikin tashin hankali da kaɗuwa take tsala gudu na fitar hayyaci, gudu take irin gudun da ba a iya sarrafa shi, gudun da ba ƙafa ke yi ba, tsoro ne ke tura ta gaba kamar an ɗaure ta da iska. Idonta na kallon gaba amma zuciyarta ta maƙale a baya. Jin sawun ƙartin mazan nan masu kama da samudawa na binta cikin kaifin mugunta. Zuciyarta na bugawa tamkar za ta yi tsalle ta fito daga ƙirjinta. Kowanne mataki da take ɗagawa yana yi mata nauyi saboda tsananin firgici, sai dai duk da haka ƙafafunta ba su tsaya ba, sai ƙara hanzari suke yi. A bayanta take jin ƙarar takun takalmin waɗancan ƙartin nan suna biye da ita kalmomi masu ban tsoro kamar hadari na fita daga bakinsu, “Ki tsaya mana, ba zamu cutar da ke ba”. Sai dai muryarsu ta nuna akasin haka, tana ɗauke da ƙiyayya da mugunta. Can kuma jin ɗaya ya ce “Idan ta kuɓuce mana wallahi za mu gamu da bala'i”. Dim! ƙirjinta ya ƙara ba da wani sauti mai nauyi, ta ƙara ƙarfin gudunta, hawayen tsoro na taruwa a idonta. Ta juya gabas sai ta tarar da duhu, ta nufe arewa sai ta ga daji mai ban tsoro. Ta rasa inda hanyar da ke gaban ta take, gudu kawai take yi jikinta na rawa sai ta ji ƙasa ta canja a ƙarƙashin tafin ƙafarta kamar ba ita ce hanyar da ta saba gani ba. Wata iska mai sanyi ta daki fuskarta, a take gashin jikinta ya miƙe tsaye. Ta kalli gaba sai ta ga wata hanya siririya, tamkar ba za ta kaita ko’ina ba, sai dai ba ta da zaɓi ta shige cikin hanyar da gudu. A daidai lokacin da take son tsallake wani ƙaramin dutse, ƙafarta ta zame. Ta ji ƙasa ta yanke kamar wani abu ya huda sararin Duniya a ƙarƙashinta. Ba ta yi aune ba ta afka cikin wani guri mai zurfi da faɗi, ihu ta yi wanda sai da ya karaɗe gurin gabaɗaya har sautin ya doki kunnen ƙartin mazan dake bin ta. ............... Ƙaramar yarinya ce, da ba za ta wuce shekaru goma ba. A hankali aka ji saukar takunta daga saman bene, ƙafafuwa masu sanyi, kamar wadda zuciyarta ke kiranta, ƙasa ta sauko ta bayyana a falon da murmushin kuka a muryarta ta ce “Sorry Dady, na fito” Dady ya ɗaga kai yana kallon ta murmushi mai cike da soyayya ya bayyana a fuskarsa. “Haba shalelena, ki daina ba ni haƙuri ai ko kin yi tsawon awa ba zan ji haushinki ba. Kin yi wa Momy sallama?”. Ta girgiza kai cikin ɗan wasa. Ya riƙe hannunta suka nufi harabar motoci. Ita ce ta zaɓi motar da zasu shiga. Ya buɗe mata ta shiga, sannan ya zagaya shiga ya ja motar da kansa suka bar gidan. Wani matashi ne da ba zai wuce shekaru sha takwas ba. Zaune yake a cikin bola tamkar wanda Duniya ta manta da shi. Busasshen biredi yake taunawa, ya haɗa uban gumi saboda rana. Wani lokaci yana wasa da hannayensa, wani lokacin yana zabura kamar wanda tsoro ya taso masa daga ciki, daga ƙarshe ya miƙe ya fara wata irin rawa mara kan gado, rawar da ba ta da wata ma’ana face irin ta mutanen da hankali ya rikice musu, sai da ya haɗa gumi, ya koma ya zauna yana tsinkar tarkacen datti yana ci. Sai kuma ya yi shiru. Ya fashe da kuka mai tashin hankali, ya kwanta yana birgima kamar yaro ƙarami da aka tsane shi da ciwo. A hanya kuwa Joriyya da Dadyn ta na hira cikin nishaɗi babu wanda ya kai Joriyya ƙima a zuciyar Dady. Ita ce autar gidansa, kuma ita ce abar son zuciyarsa. Duk abin da zai faranta mata rai zai yi. Suna wucewa kusa da gurin mahaukacin, ta sauko da gilas ɗin motar. Idonta ya tsinci matashin nan da yake birgima cikin datti yana kuka a cikin zafi. “Dady” “Na’am shalelena?.” “Duba can ga wani yana kuka a rana”. Ya ɗan kalli bangaren ya ce “Eh na gani rabu da shi, ai mahaukaci ne” “Mahaukaci kuma?” Ta tambaya idonta cike da tausayin da ba ta ko tunanin na mene ne. “Eh. Ina yawan ganin shi. Wani lokaci dariya yake, wani lokaci kuka.” Joriyya ta ja numfashi, ta ce “Dady mu koma gurin shi.” Ya kalleta da mamakin shagwaɓarta “Shalele me za mu yi masa?” “Wataƙila yunwa yake ji. A siya masa abinci Dady mu koma don Allah” Ya yi shiru sannan ya ce “To ina ruwanki da shi?” Ta zumɓura baki ta juya kai ta yi shiru. Nan Dady ya gane ta yi fushin, sai ya yi dariya. “To shikenan bari mu juya” ta saki murmushi mai cike da jin daɗi. Suka koma inda matashin yake. Dady ya fita, ita ma ta fito. A can gefe ya hango wata mata mai saida abinci, suka nufe ta. Dady isa gurin da sallama ya ce “Dan Allah abinci mai yawa nake son ki bawa wancan mahaukacin ki kai masa”. Ta firfita “Alhaji? Kai masa? Gaskiya bazan iya zuwa ba in dai kai zaka je ka karɓa, gaskiya ni bana shiga inda yake D duka yake”. Wani saurayi can gefe ya ce “Kai ka ji mugunta ke ba za ki kai masa ba saboda kina gudun duka, amma shi ki ke so ya je?”. Ta harare shi ta ce “Ni mace ce, shi kuma namiji ne ai ya fi ƙarfin irin abin da zan yi” Dady ya tambayi mai abincin “Duka yake?.” “Ƙwarai kuwa, babu wanda ke zuwa kusa da gurinsa” Ya ɗan yi shiru sannan ya ce “To zuba min kawai” ta zuba ya biya suka ɗauki ruwa da lemo, Joriyya ta nufi mahaukacin, sai Dady ya ja ta baya ya ce “Shalele ki tsaya, ki bari zan kai masa”. Ta girgiza kai “A’a Dady ni zan ba shi”. Mahaukacin ya zauna yana kallon su. Idonsa jawur, fuskarsa cike da gumi, sai ya miƙo hannu kamar yaro mai roƙo, kafin Dady ya yi magana, tuni Joriyya ta miƙa masa abincin idonta ƙur akansa tana kallonsa da tausayin da ta kasa ɓoyewa. ya karɓa sannan suka juya za suka wuce, sai mahaukacin ya ɗaga ƙafa ya hankaɗe Dady, taga-taga ya yi zai faɗi Allah ya tsare bai faɗi ba. Ya ce “Kin gani ko Shalele wannan nake gujewa, yanzu da ya karya ni fa?”. Ya ja hannunta da ɗan zafi suka shiga mota. Joriyya ta yi shiru har suka yi zagaye da yawa. Duk da ta ga yadda ya kusa cutar da Dady, hakan bai rage tausayin da take ji masa ba. Sun daɗe suna zagaya gari Dady dauriya ce kawai yake yi, saboda ƙafarsa tana yi masa ciwo sosai, ya yi mata siyayyar kayan ciye-ciye da yawa. A gajiye suka koma gida. Nan suka tarar da Junior ya zo gidan, cikin farin cikin dawowarsu ya gaishe da Dady, Momy ma sannu da zuwa ta yi musu, Dady ya zauna a nan falon, Joriyya kuwa ganin Junior yasa ta yi kicin-kicin da fuska. Yana yi mata magana ta yi kamar ba ta ji shi ba, ta fara ƙoƙarin hawa sama. Momy ta ce "Auta ba ki ji Yayanki na yi miki magana ba?". "Momy bacci nake ji ne" daga haka ta yi haye sama, Momy za ta kuma yi mata magana, Dady ya ɗaga mata hannu alamar ta yi shiru. "Haba Dadynsu wannan yarinyar na rasa me yake damunta ne? Ni lamarinta mamaki yake ba ni, yarinya ƙarama da ita sai shegen girmankan tsinya, kwata-kwata ta raina Jiniyo ba ta ganin girmansa ko kaɗan, indai ya zo gidan nan haka take yi masa wannan iskanci kuma ta san saboda ita yake zuwa gidan, tunda na haifeta yake matuƙar sonta da ba ta kulawa amma ita ba ta gani, ai ko tana yarinya ta san mai sonta da kuma kyautata mata" Momy ta shiga masifa Dady ya yi mata shiru daga ƙarshe shima tashi ya yi ya haye sama ɗin.vMomy ta ce "Jiniyo yi haƙuri ƙyaleta ka ji, kaima ka daina damuwa da ita, tunda ba ta san harkar arziki ba" . Ya ce "Ai babu komai Momy, Joriyya yarinya ce sai ana haƙuri da ita, ni banji hsushinta ba, kinga ai a gajiye take". "Duk da haka Junio Joriyya akwai raini a cikin lamarinta, kusan shekara goma ka bata amma take yi maka wannan rashin kunyar, son da kake nuna mata ko yayunta basu nuna mata shi" shi dai Jiniyo ya shiga bawa Momy haƙuri, akan ta daina yi wa Joriyya faɗa ƙuruciyya ce ke damunta. Ya daɗe a gidan kafin ya yi wa Momy sallama ya bar gidan. Tashi Momy ta yi ta shiga ɗakin Joriyya a zaune ta tarar da ita saman gado ta baje kayan ciye-ciyen da Dady ya siya mata tana ci tana game a wayarta. Zama Momy ta yi tana kallonta ta ce “Auta halin da kike yi wa Jiniyo ba daidai bane. Tun kina jaririya yake miki gata amma kin raina shi da yawa”. Shiru ta yi, sai can ta ce “Momy kin san wani abu kuwa?”. “A’a sai kin faɗa”. “Mun ga wani yana kuka a cikin datti yau sai da na sa Dady ya siya masa abinci. Amma bayan mun kai masa sai ya hankaɗe Dady”. Momy ta firfita “Subhanallah! Dadynku kuwa? Me ya kaiku can?”. “Ni ce na takura”. Momy ta riƙe haɓa ta ce “Auta ki daina irin wannan halin. Ko da kina tausayi, ki kula da kanki”. Daga haka Momy ta bar ɗakin tana girgiza kai. Momy ta fito daga ɗakin Joriyya kai tsaye ɗakin mijinta ta nufa. A hankali ta tura ƙofar ɗakin, Dady na zaune gefen gadonsa yana shafe ƙafarsa da ruwan sanyi, fuskar nan tasa mai ɗauke da girman kai da alfahari da dukiya tana cike da gajiya da ɗacin ciwo. Bai ɗago ba har sai da ta ƙaraso ta tsaya gabansa. Ta ce da siririyar murya mai cike da damuwa “Alhaji na ji abin da ya faru yau”. Ya ɗaga kai a hankali ya dube ta ya ce “Kin ji komai kenan?”. “Eh Joriyya ta faɗa min, yadda mahaukacin nan ya hankaɗe ka to me ya kai ku gurin mahaukaci?”. Dady ya yi ƙasa da murya “Kin san halin yarinyar nan. Idan ta saka abu a ranta ba ta da sauƙi, ni ma ba son raina na je gurinsa ba, sai don gudun rigimarta, kuma kin san ba zan iya jure kukanta ba". Momy ta zauna kusa da shi tana kallon fuskarsa. “Amma Alhaji mahaukaci fa? Ka san haɗari ne da shi. Babu wanda ke shiga inda yake, kai kuma ka je, ka san ba mu da hulɗa da irin waɗannan mutanen. Sun fi jawo bala’i fiye da alheri”. Dady ya ɗan yi murmushi mai ɗaci, ya ce “Shi ne fa dalilin da ya sa ban son su. Ni ba ruwana da talakawa, Shafa babu abin da ya haɗa mu da su. Su na kawo bala’i da nauyi. Ina kuka da su? Amma ita Shalele.." sai ya yi shiru, ya shafa gemunsa. "Wannan yarinya tana da zuciya mai tauri, ai dole na biye mata, amma ba zan kuma kuskuren bari ta kusanci wannan mutumin ba”. Momy ta ce “Ka yi a hankali, ai ya kusa cutar da kai yau, wannan rigima ta Auta daga ganin mutum baki san asalinsa ba ki ce sai an siya masa abinci”. Ta miƙe tsaye ta ce “Allah ya tsare ya tsare gaba zan je in duba maka abincinka”. Jiniyo na zaune a harabar gidansu yana sosa kai kamar mai jiran hukunci. Fuskar nan tasa ta matashi mai ƙananun shekaru ta nuna alamun damuwa fiye da shekarunsa, mahaifiyarsa Hajiya Munira ce ta fito, wadda ta kasance ƙanwar Momy ta ce “Hamma me yake damunka haka yau? Tun da ka dawo daga gidansu Aunty Shafa kake ta kai kawo kamar wanda aka faɗa masa mugun labari?”. Ya sauke numfashi mai nauyi ya ce “Mama Joriyya ce”. Ta ɗan yi dariya ta zauna kusa da shi, ta ce “To ita kuma wane sabon abin da ta yi maka yau?”. Ya ɗaga kai da murya mai sanyi ya ce “Mama ban san me ya sa ba amma tun da na balaga zuciyata ta tsaya a kanta. Amma ita ko kallona ba ta son yi . Da nayi magana sai ta yi kamar ba ni bane, kuma idan na je gidan su, sai in ji kamar ina ɗaure zuciyarta kamar ba ita nake so ba”. Mahaifiyar tasa ta girgiza kai ta kuma cewa “Hamma ka san wannan gidan dukiya ce kawai da girman kai ke ɗawainiya da su. Ita Joriyya ta taso tsakanin gata da shagwaɓa ne. Ka yi hankali kada ka cutar da kanka akanta”. Ya ce “Ni dai ban iya daina tunanin ta. Kuma Mama tun tana ƙarama nake jin kamar ita ce matata”. Murmushi ta yi cikin murya tausayi ta ce “Allahu ya kyauta. Amma ka riƙe kanka, kada ka nuna wa kowa" ya yi shiru, zuciyarsa na tafasa da soyayyarsa marar gata, mara amsa. Da daddare Joriyya na kwance saman gadonta, kayan wasa da kayan marmari a warwatse, amma hankalinta bai kan su. Idonta a lumshe, tana sake hasko hoton fuskar mahaukacin da ta gani yau, ta tuna jajayen idanuwansa, da birgimarsa cikin ƙura, yadda ya riƙe abincin da ta miƙa masa kamar wanda bai taɓa riƙe komai ba a rayuwa. A hankali ta ce "Shi ma wani ne ya haife shi, me ya kawo shi haka? Wai me ya sa ya fashe da kuka kamar yaro? Me ya sa babu wanda ya kula da shi? Ya ci abincin kuwa bayan mun tafi?". Nan take ranta ya soma nauyi.Ta zaro numfashi, zuciyarta na cike da wani sabon abu na tausayin da bata san dalili ba. Har kwanciyarta ta kasa nishaɗi tunani ya rufe mata ido gabaɗaya. By Amanarcool ✍️ 08163516796 💦 AKWAI SILA 💦 BY AMANARCOOL YOTA ID/O21 *SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*. PAGE 3-4 Washegari tun kafin gari ya fara yin haske Joriyya ta farka da wani irin ɗaci a zuciya. Tunanin mahaukacin ya rufe mata ido kamar mafarkin da yaƙi ɓacewa. Ta tashi ta wanke fuska, ko breakfast ba ta jira ba ta nufi kitchen. Mai aikin gidan Lami ta taso da mamakin ganin Joriyya ta shigo kitchen cikin sauri fuskarta ɗauke da damuwa. “Lami” ta faɗa da ƙaramar murya mai nuna umarni “ki girka min tuwon semo da miyar taushe. Ki tabbatar kin saka nama da kayan ciki sosai”. Lami ta kalle ta da mamaki ta ce “Amma Auta ke ba ki cika cin irin wannan ba, ko dai Dady ne ya buƙata?”. “Ba don mu za ki yi ba” ta amsa tana haɗe hannuwanta, ta kuma cewa “Wani mutum ne wanda muka kai wa abinci jiya ina so a ƙara kai masa yau. Yunwa yake ji”. Lami ta tsaya cak, ta ji duk jikinta ya yi wani irin sanyi. “Auta wancan mahaukacin da na ji Hajiya na magana akansa? Ko ni ba zan iya tsayawa kusa da shi balle ke, ko nesa da shi ba zan iya tsayawa ba”. “Ba ke za ki je ba” Joriyya ta katse ta “ni zan kai amma tare da Dady zamu je”. Daga haka ta juya ta fita da sauri kamar wata walƙiya. Ɗakinta ta kuma ta shirya, bayan kamar awa ɗaya ta fito. A falo ta ga Momy zaune tana shan tea, Dady na gefenta yana duba wasu takardu. Joriyya ta sauko a hanzarce tana takowa kamar mai son sanar da wani abin gaggawa, ta ce “Dady” ta tsaya gabansu, idonta ya cika da wani irin abu mai kama da kuka. “Dady don Allah mu je wajen mutumin jiya. Lami ta girka masa abinci”. Dady ya ɗaga kai a hankali, ya ɗan yamutsa fuska, ya ce “Auta ban shirya shiga bala’in wancan mutumin ba yau. Ƙafar nan tawa har yanzu tana yi mini zafi”. Momy ma ta ɗaga gira ta ce “Joriyya wannan wannan wace irin rigimar ce kike ƙoƙarin jawo mana? Bayan abin da ya yi wa Dadynki jiya?”. Ranta ya soma ɓaci, ta fara tattare leɓe, numfashinta na ƙaruwa, ta ce “In kun ce ba zamu je ba to zan yi kuka. Zan yi kuka sosai Momy, kuma kun san idan na yi kuka ciwon ƙirjina yana tashi, kuma bana so in yi kuka” Da sauri Momy ta kalli Dady ta ce “Alhaji ka ga abin da nake faɗa kuwa? Yanzu tana fara kukan nan amai yake zuwar mata, numfashinta ya rikice. Ka tafi kawai, don Allah ka barta ta samu natsuwa.” Dady ya yi shiru. Wani abu cikin zuciyarsa ya yi masa nauyi, ya ce “To shikenan zamu je ɗin”. Joriyya ta yi tsalle cikin farin ciki, ta manta duk fushin da ta yi ɗazu. Ta nufe sama cikin sauri. Momy ta kalli mijinta tana girgiza kai, “Ga abin da nake gudu nan ya fara bayyana, wannan yarinya tana son sa mu a cikin walagigi saboda wani mahaukacin da ba mu ma san asalinsa ba”. Jiniyo yana ta faman buga ball ɗin hannunsa, idonsa a kan ƙofar gidansu Joriyya da ya ga get ɗin gidan a buɗe, da yake unguwa ɗaya suke, shima mahaifinsa mai kuɗi ne amma ba kamar gidansu Joriyya ba. Jiniyo yana ƙoƙarin zama cikin tarbiyya da nutsuwa, amma soyayyar Joriyya ta yi wa zuciyarsa kulle. Ya hango su Joriyya na fitowa da flask a hannunta da sauri tana bin bayan Dadynta, an buɗe musu mota sun shiga direba ya ja suka bar gidan. Ya yi murmushi mai cike da soyayya. “Allah ya bani ikon samun ki Joriyya ya mallaka mini ke” ya furta a hankali Wajan da suka zo jiya mai ƙura, datti, da zafin bola nan suka ƙaraso. Mutanen gari suna wucewa suna ƙoƙarin kaucewa matsugunin mahaukacin. Yau yana zaune luf ciki yana ɗora tsakuwa saman tsakuwa. Dady ya tsaya daga nesa yana kallon yanayin gurin kamar wanda aka tilasta masa shiga kasuwar ƴan daba. “Ga shi can” ya ce da ɗacin rai. “Ki tsaya baya, kada ya kusance ki” Joriyya tuni ta taka gaba da ƙafafunta tana tafiya a hankali kamar wata mai tsoron karya abu. Mahaukacin ya ɗaga kai da sauri kamar mai jin motsin ruwa a cikin rijiya. Idanuwansa jajaye, gumi na gangarowa daga goshinsa. Da ya hango flask a hannun Joriyya ya tsaya cak, idonsa ya lumshe, Dady na dakatar da ita, ita kuma sai ƙara kusantarsa take, ta ƙarasa gurinsa ta tsugunna, a hankali ta buɗe flask ta zuba miyar a cikin leda mai kauri ta miƙa masa. Dady ya ƙaraso gurin da sauri yana zaro ido. Wannan karon bai yi ihu ba, ya miƙa hannunsa ya karɓi abincin a nutsuwa, yana kallonsu kamar jaririn da aka ba hanci ya fara sha. Idanun mutane suka fara bibiyar su, suna mamakin Alhaji Sulaiman a tsaye cikin bola saboda mahaukaci. Wani dattijo dake zaune a can gefen titi ya ce “Wannan fa sabon abu ne, Alhaji Sulaiman wanda ko talaka ba ya saurare, yau ya tsaya ga mahaukaci?” Wasu suka tsaya suna kallonsu da mamaki, wasu suka yi dariya, wasu murmushin mamaki da ganin ikon Allah suke yi. Dady ya so nuna rashin amincewa da zaman Joriyya a gurin, amma sai ta kama hannunsa ta ce da siririyar murya “Mu bari ya gama Dady” ta yi maganar cikin murya mai karya zuciya, hakan ya saka shi yin shiru. Mahaukacin ya zauna da abincin ya fara ci a hankali kamar wanda yake jin tsoron abincin ya ɓace kafin ya ɗan ɗanɗana shi. Ya ɗauki lokaci yana ci, yana kallon Joriyya lokaci zuwa lokaci, kamar yana tantance wani abu cikin zuciyarsa. Yana gama cin abincin ya miƙa musu flaks ɗin ya yi ƙasa da kai kamar yana miƙa godiya da harshen da ba shi da kalma. Jama’a suna kallo. Joriyya ta ɗauki flask ɗin suka juya. Dady bai yi magana ba har suka shiga mota, sai lokacin ya ce da ita cikin taushin da bai saba da shi ba “Shalele ki bar wannan abu. Ba

Chapter 1 of 9