Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 9
ɗai suka san ma'anarsa. Joriyya na zaune a class tare da ƙawarta Safina, Malam Musa na yi musu darasi amma ba ta fasa surutun da take yi ba, kallon sa take tana dariya ƙasa-ƙasa ganin yadda yake yi musu bayani kamar baya jin daɗin jikinsa, cikin ƙasa da murya ta ce "Safina kin ga Musa yau kamar wanda aka hana shi shayin safe, sai layi yake yana lumshe ido kamar yadda Indiyawa ke yi a film". Safina ta girgiza kai ta ce "Ke dai ba za ki daina surutu ba? Joriyya ka da ki jawo muna duka fa". "Surutu fa yanzu na fara, Safina kin san bashi da lafiya hannunsa ke ciwo" . Joriyya ta ce tana lumshe ido Safina za ta yi magana kenan suka ga Malam Musa na kallon su dole ta yi shiru. Da aka tashi daga school ɗin, direba ya zo ɗaukar Joriyya, kai tsaye gida ya nufa, babu za to ya ji Joriyya ta ce masa "Tsaya ba wannan hanyar zamu bi ba, ka wuce ta can baya nake son mu bi". Ya ce "Amma Shalele ga hanyar..." "Don Allah kabi inda na buƙata, zan ɗan tsaya ne wani guri" ta katseshi Direban bai sake magana ba, ya juya akalar motar zuwa inda ta buƙata, tun daga nesa ta hango shi zaune a cikin bolar, rana na dukansa. karensa na gefensa, hannunsa ya ƙara kumbura, fuskarsa ta yi duhu, idanunsa sun zurma sosai, bakinsa ya bushe, sai hamma yake yi alamar yunwa yake ji, tasa direba ya tsaya daidai bakin bolar. A firgice ta fito daga cikin motar tana faɗin "Subhanallah". Ta matsa kusa da shi hawaye har sun fara zuba a fuskarta ta ce "Me ya ƙara kumburar maka da hannu haka? Me yasa ba wanda yake taimaka maka ne? Yanzu dama haka kake fama da hannun? Da gani ma yunwa kake ji?". Mahaukacin ya ɗago da kai a wahale, ya kalle ta da idanunsa da suka yi zurfi, bai ce komai ba. Hawaye suka ƙara zubu mata, ta rufe fuskarta da tafin hannunta tana kuka. "Ba haka ya kamata rayuwar mutum ta kasance ba" ta faɗa cikin muryar kuka. Direban ya tsaya daga nesa yana kallon ta, zuciyarsa cike da fargaba. Amanarcool 08163516796 💦 AKWAI SILA 💦 BY AMANARCOOL YOTA ID/021 *SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*. PAGE 19-20 Tana durƙushe a gabansa, ba tare da tunanin komai ba, ta buɗe jakar makarantar ta ta ɗauko kwalbar ruwa da biskit ta miƙa masa hannunta na rawa ta ce "Karɓi ka ci don Allah". Ya kalli ruwan a hankali ya karɓa ya sha kaɗan ya ajiye, da ƙyar yake iya motsa hannunsa, Joriyya ta buɗe masa biskit ɗin ta miƙa masa ya amsa. Direba ya matso kusa yana cewa "Shalele mu tafi, wallahi ina cikin matsala idan aka gan ki a nan fa". Cike da tsiwa ta juya tana kallonsa ta ce "Bazan tafi ba, taya zan tafi na bar shi a haka? Ka jira ya gama ci sai mu tafi". Karɓar biskit ɗin ta yi ta fara karya masa shi ƙananu tana bashi, amsa ya yi yana ci a hankali, idanunsa na kallon ta ko ƙiftawa baya yi. "Baka da suna ne?" ta tambaya murya a sanyaye Shiru ya yi mata, ta kuma cewa "Ko ka manta da sunan naka ne?". Ya girgiza kai kaɗan, ya buɗe baki kamar zai yi magana sai ya fasa, yana jin yadda hannunsa ke yi masa raɗaɗi, ya ɗaga shi sama yana huci. Joriyya ta kalle hannun hawaye na ci gaba da zubo mata ta ce "Wannan hannu ciwo yake maka sosai ko? Zan sa Dady ya kai ka asibiti". Da jin kalmar asibiti ya janye hannunsa da sauri, tsoro ya bayyana a fuskarsa, ya fara girgiza kai yana ja da baya. "Baka son asibiti ne? To ba za a je da kai ba, za a siyo maka magani kasha ka ji dama". Ta faɗa tana matsowa kusa da shi.Kallon ta yake yi sosai, idanuwansa sun yi ja, hawaye sun taru a ciki, bakinsa ya fara motsi a hankali "Ki tafi..." Bai ƙarasa ba ya yi shiru. Ta tsaya cak, zuciyarta na bugu da sauri ta ce "Kana magana da ni ne?" Direba ya dafe kansa ya ce "Wannan yarinya ƴar bala'i ce, ko tsoron ya shaƙeta ba ta yi". Wata tsohuwa ta zo wucewa ta tsaya tana kallonsu, ta ce "Ke yarinya kin san ko waye shi kuwa?". Joriyya ta ɗago ido cike da hawaye ta ce "Ba na san shi ba, sai dai bai kamata ya kasance haka ba, dubi hannunsa babu wanda ya taimaka masa, kuma jama'a na kiran sa da mahaukaci". Tsohuwar ta girgiza kai ta ce "Shi ba mahaukaci ba ne, abin da ya same shi ne ya fi hauka muni". "Me ya same shi?" Joriyya ta tambaya da sauri Tsohuwar ta yi murmushi ta ce "Yariya tashi ki wuce gida kin ji". Kafin Joriyya ta sake yin wata maganar direba ya ce "Shalele wallahi lokaci yana tafiya, ki taso muje ka da ki saka ni a matsala". Ta kalli mahaukacin ta ce "Ka yi haƙuri zan dawo, za a baka maganin wannan ciwon". A hankali yake tuƙin zuciyarsa a cunkushe. Idanunsa sai shawagi suke yi a titi, motar da ya gani a gefen titi kusa da bola ya sa zuciyarsa ta buga da ƙarfi. Ya rage gudu yana kallon motar sosai "Joriyya?" ya furta a ransa, taka birki ya yi, ya fito daga motarsa ya tsaya can nesa, ji ya yi zuciyarsa na harbawa da sauri, idanunsa suka sauka a kan Joriyya dake durƙushe a gabansa tana kuka, mutumin da kowa ke gudu, wanda Duniya take kira da mahaukaci, shi ne yarinyar da yake yi wa kallon uwar ƴaƴansa take yin wannan abin a gabansa? Take ransa ya ƙara ɓaci ya ce "Haba Joriyya, me kike nema a gurinsa ne? Me yasa kike kusantar shi haka?" ya tambayi kansa cikin ɓacin rai. "Ba zan bari wannan abin ya ci gaba da faruwa ba". Yana kallo Joriyya ta miƙe ta shiga mota direba ya ja suka bar gurin. Shiga tashi motar ya yi, zuciyarsa cike da baƙin ciki ya rufa musu baya. Suna isa gida ta fito da sauri ta shiga ciki zuciyarta cike da damuwar halin da ta baro shi a ciki, tana shiga falo ba ta ma lura da Momy ba ta fara ƙoƙarin hawa saman bene. "Auta" Momy ta kira ta "Ina kuka tsaya tun ɗazu? Me ya faru kika dawo cikin wannan yanayin?". "Momy shi ne fa" kafin Momy ta yi magana Jiniyo ya shigo falon fuskarsa a murtuƙe, idanuwansa sunyi jajur. "Jiniyo?" Momy ta furta da mamaki "Lafiya ka shigo haka kamar wanda aka je fo?". Bai ba ta amsa ba, kai tsaye ya nufi Joriyya da ta tsaya cak a tsakiyar falon "Me kika je yi gurinsa?" ya tambaye ta cikin fushi. Joriyya ta kalle shi ta ce "Shi wa?" "Karki raina mini hankali Joriyya! Na ganki da idona, na ganki gurin mahaukaci nan, kina durƙushe a cikin bola kamar wata mara galihu". Momy ta ce "Subhanallah! Jiniyo me kake nufi? Ba dai gurin wannan mahaukacin ka ganta ba" . "Can na ganta Momy, baki ga a yadda na ganta ba. Momy Joriyya na son zubar da mutuncin gidan nan". Joriyya ta ɗaga kai tana kallonsa idanunta cike da hawaye, cike da rawar murya ta ce "Ba mahaukaci ba ne, ka da ka sake kiransa da wannan sunan!". "Me kika ce?" Ya tambaya cikin fushi da zafin kishin da yake jin yana nuƙurƙusar sa a zuciya. "Na ce ba mahaukaci ba ne, mutum ne kamar kowa, kawai an manta da shi ne" ta faɗa da ƙarfi, ƙara har zuƙa ya yi ya ce "Ke Joriyya ki shiga taitayin ki, wannan mahaukaci ne, kin san irin hatsarin da kike jefa kanki a ciki kuwa? Bana son damuwar nan da kike yi akan sa, wannan ai hauka ne". Ya ƙarasa maganar cikin hargagi "Idan tausayin sa ne da nake ji ya zama hauka, na ji ɗin ni mahaukaciya ce" Joriyya ta maida masa da martani. Mutuwar tsaye Momy ta yi, ganin abin na shirin zama rigima a tsakaninsu ya sa ta ce "Ya isa haka, ku daina wannan rikicin ba na so. Auta wuce ki bani guri kafin in saɓa miki". "To Momy zan wuce" ta dubi Jiniyo ta ce "Ka da ka sake shiga harka ta, kuma ka daina kiransa da mahaukaci, idan aka bibiya ya ma fika hankali". Jiniyo ya girgiza kai cikin takaici ya ce "Na yi tunanin kina da hankali ashe ba haka ba ne, yau kin karya mini zuciya Joriyya". "A'a bayanka na karya ba zuciya ba, ina naga zuciyar taka da zan karyata? Bana son sharri kuma ka daina shiga harka ta". Tana gama faɗar haka ta haye sama da sauri. Cike da baƙin ciki Jiniyo ya juya ya fita ransa a matuƙar ɓace, yana ƙara jin ƙiyayyar mahaukacin nan mai tsanani a zuciyarsa, take ya sha alwashin sai ya kuma ɗaukar hukunci mai tsanina a kansa, sai dai komai zai faru ya faru. Momy ta zauna a falon idanunta sun canza launi "Wannan wace irin masifa ce? Yarinya gabaɗaya ta rikice, anya ba malami zamu samu ya yi mata addu'a akan wannan lamari ba?" Tana tsaka da tunani ta ji ana kiran wayarta ko da ta duba Na'ima ce, ɗauka ta yi jiki a sanyaye "Hello Momyna" "Na'am Na'ima ya kuke?". "Alhamdulillah Momy ya gida? Ya Dady da kuma rigimamiyar ku?". "Kowa yana nan lafiya, Auta yanzu ta dawo daga school, ina Ummie ne tana lafiya?". Na'ima ta ce "Ummie yanzu ta fita da Dadyn ta. Momy ina fatan dai Auta ta daina rigimar da take yi ɗin?". Momy ta nisa ta ce "Tsakanin jiya da yau kafin ta je school ta yi sauƙi duk da abin na ranta, amma daga fitar ta makaranta kinga yanzu ta dawo a rikice, ashe da aka tashe su daga school sai da ta biya gurinsa kafin ta dawo gida, baki ga rigimar da suka gama yi da Jiniyo ba da ya ganta a gurin. Na'ima al'amarin nan ya fara isa ta, na fara tunanin ko malamai za mu sa suyi mata addu'a. Yanzu fa hadda faɗin take yi wai ha mahaukaci ba ne, an manta da shi ne, ban san me take nufi da wannan maganar ba. Yaro kamar ba mutum ba gabaɗaya yarinya ta rikice akansa, kuma fa sai kin ganshi ba wani babba ba ne, matashi ne kamar Jiniyo". Na'ima ta ce "To Momy ya aka yi ta je gurin sa? Ba tare take da direba ba?". "Na'ima sai ka ce baki san halin Auta ba, tare take da direba kin san dai halin tsiwarta idan ta tashi, ina tunanin tursasa masa ta yi, dole ba yadda ya iya ya je ɗin". "Duk da haka Momy bai kamata suna biye mata ba, tunda sun san ba ku son hakan da take yi, sannan Momy na ce idan kunga da matsala ta dawo gurina da zama mana, ina ga idan aka nisanta ta da shi ai za ta haƙura". "Ina ga hakan za a yi, duk da ta ce ba za ta je gurinki ba, amma dai yanzu bari Alhaji ya dawo na ji yadda zamu yi da shi, a fara saka malamai su yi mata addu'a tukuna mu ga abin da hali yayi, idan ba ta daina ba dole za ta bar ƙasar nan". Na'ima ta ce "To shikenan Momy, duk yadda ake ciki ki sanar dani, ai ba dole sai ta yarda ba" ci gaba da tattauna matsalar suka yi daga ƙarshe suka yi ajiye wayar. Joriyya na shiga ɗaki ta zauna idanuwanta cike da hawaye, zuciyarta na bugawa da sauri, ta yi shiru tana tunanin yadda taga hannunsa ya ƙara kumbura "Dole ne nasa Dady ya siya maka magani, ba na son ganin wannan ciwon a hannunka" ta ƙarasa maganar tana matsar ƙwallah. Da yamma sosai Dady ya dawo gida, bayan ya yi wanka ya ci abinci. Momy ta ce "Alhaji Auta fa ta koma gurin mahaukacin nan yau". "Kamar ya? Ban gane ba? Ba yau school ta je ba? Taya aka yi har ta fita ta je gurin sa?" Ya yi maganar yana tsare Momy da ido. "Alhaji daga school ɗin ta wuce gurinsa, bayan an tashe su". "What! Taya aka yi ta je can ɗin? Ina direba ne ko ba aje ɗaukar ta ba ne?" "Tare fa da direba take, tare suka je gurin" Momy ta faɗa tana kallonsa. Cikin tsanin fushi Dady ya miƙe tsaye zai fita, da sauri Momy ta ce ''Alhaji ina za ka je ne?" . "Zan je in ji dalilin daya sa zai kai mini yarinya gurin wannan banzan" . Momy ta ce "Haba Alhaji kafa san halin Auta, ni yanzu ba zanga laifinsa ba, ina da yaƙinin takura masa ta yi, ka yi haƙuri ka da je yanzu, idan ma magana za ka yi masa ka bari sai gobe. Alhaji lamarin nan ya fara ɗaure mini da kai, yau dalilin zuwanta gurin nan sai da na shiga tsakaninta da Jiniyo, baka ga rashin kunyar da ta yi masa daga ya yi mata maganar ta daina zuwa inda yake, ka yi haƙuri koma ka zauna ina da shawara". Komawa ya yi ya zauna yana jin zuciyarsa na yi masa zafi sosai "Duk da haka Shafa bai kamata ya biye wa Shalele ba" ka yi haƙuri Alhaji, yanzu dai ina da shawara, ni a ganina mu saka malamai su fara yi mata addu'a, saboda ina tunanin kamar yaron nan ba mutum ba ne, yarinya gabaɗaya ta rikice". Shiru ya yi yana nazarin maganarta kafin ya ce "Kin kawo shawara, zan yi wa Malam Nura magana ya riƙa zuwa yana yi mata addu'a ko Allah zai sa a dace". Kafin Momy ta yi magana, kamar daga sama suka ji Joriyya ta ce "Dady nima aljanu ne dani irin na Anty Teema ta makarantarmu? Ruƙiyya za a fara yi mini? Dady bari na kwanta na fara birgima irin yadda Anty Teema ke yi sai a kira Malam ya yi mini ruƙiyya". Amanarcool 0816351679 💦 AKWAI SILA 💦 BY AMANARCOOL YOTA ID/021 SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143. PAGE 21-22 Baki buɗe Momy ke bin Dady da kallon, Dady kuma na kallon Joriyya dake ƙoƙarin kwanciya a ƙasa. "Shalele" ya faɗa da ƙarfi, fasa kwanciyar ta yi, ta ɗago da kanta ta kalle shi ta ce "Na'am Dady". "Me kike ƙoƙarin yi ne?" "Dady birgima zanyi irin yadda Anty Teema ke yi idan..." "Shalele!" Ya daka mata tsawa "Ke daina wannan wasan ba na so, ka da na sake ganin kin kwatanta yin irin haka". Shiru ta yi ta ɓata fuska kafin ta ce "To Dady addu'ar me za'a yi mini? Ko don in daina jin tausayin mutane ne? Dady kasan wani abu? Jin zafi nake idan na ga mutum yana wahala". Sai a lokacin Momy ta yi magana "Auta wai ke bakinki ba zai taɓa yin shiru ba ne?". Joriyya ba ta ce ƙala ba, ta bar falon ta haura sama, tana shiga ɗaki ta kulle ƙofa, zama ta yi a gefen gadonta, hawaye na taruwa a idonta "Me ya sa mutane ba sa ganin abin da nake gani ne? Bana son ganin mutum a cikin damuwa". Ta faɗa tana duƙar da kanta tsakanin ciniyoyinta. Bayan tafiyar Joriyya Momy ta kalle Dady ta ce "Oh ni Shafa'atu ina ganin abin da yafi ƙarfina, ji mini wata lukutar masifa da take ƙoƙarin gayyato ma kanta. Alhaji bori fa take wasan yi". Dady kasa magana ya yi yana jin yadda gabansa ke faɗuwa, wani irin tsoro da fargaba na ƙara shigarsa, ya miƙe a hankali ya nufi ɗakinsa zuciyarsa cike da tunani iri-iri. Jiniyo ne kwance a ɗakin abokinsa, idonsa a rufe, wani tuƙuƙin baƙin ciki yake jin yana taso masa tun daga tafin ƙafarsa zuwa cikin ƙirjinsa, zuciyarsa na yi masa zafi mara misaltuwa, buɗe idonsa ya yi yana furzar da isaka mai zafi, ya kalle abokansa Salim da Yasir ya ce "Gayu wallahi ni ne zanyi ajalin wancan wawan mahaukacin, wai har ni Jory za ta kalla ta ce wancan banzan yafi ni hankali? Ni? Ni Jiniyo? Impossible, sai na ƙara koya masa hankali, idan ma da sauran hankali a tattare da shi sai na yi sanadiyar da zai rasa shi gabaɗayaa. Zanyi masa abin da zai ƙara zama silar ɓarkewar haukarsa!" Ya ƙarasa maganar cikin ƙunar rai. Salim ya ce "Jiniyo this is sad and frustrating for us, taya za'a yi mahaukaci ya riƙa baka matsala irin haka? This is embarrassing for us". Cike da jin haushi Yasir ya ce "I'm not happy about that, tabbas wannan abin kunya ne a gare mu, dole ne mu ɗauki matakin da ya dace akan wannan lamarin, kamar mu za a zo wa da wannan rainin hankali?". Jiniyo ya dube su da idanunsa da suka canza launi ya ce "Me ya kamata muyi masa wanda zai sa jikinsa ya gaya masa?". Salim ya yi wuff ya ce "Kamata ya yi an jima da isha mu same shi muyi masa ɗan banzan dukan da sai ya kasa tashi, mu canza masa kamanni ta yadda idan ta gan shi ba za ta yi marmarin sake ganinsa ba". Yasir ya ce "Good job Salim, that’s a suggestion this is how we should handle him." Cike da gamsuwa suka yi na'am da wannan shawarar. Bayan sallar isha da ƙyar ya tashi daga cikin bolar ya koma kangon nan ya kwanta yana fitar da numfashin da ƙyar saboda azabar da yake ji a hannunsa. Karensa ya fita, nesa da gurin suka yi parking ɗin motarsu, a hankali suka ƙarasu gurin cikin sanɗa, yana kwance sai gani ya yi an haske shi da fitar wayar dake hannunsu. Ya sa hannunsa mai lafiya yana kare fuskarsa. Jiniyo ya ƙarasa inda yake suna ci gaba da haske masa fuska da fitilar waya, duƙawa ya yi ya cusa masa wani abu mai raɗaɗi a cikin bakinsa, ya sa salatif ya liƙe masa baki. Shure-shure ya fara yi yana jin raɗaɗi da azaba na ratsa masa baki kamar ana yanka shi da reza. Cike da rashin imani Salim ya duƙa yana ɗauke sa da mari tare da matse hannunsa mai ciwon. Zabura ya yi ya fara ƙoƙarin tashi zaune, cikin ƙita da mugunta Jiniyo ya mayar da shi kwance yana ƙara matse hannun daya kumbura yana walƙiya. Mimmiƙewa ya fara yi yana kakari, Jiniyo ya ce "Ai baka ga komai ba tukuna, sai na yi ajalinka" Ya faɗa yana miƙewa tsaye, babu imani balle tausayi suka fara dukan shi da sandunan da suka zo da su, duk inda suka samu a jikinsa duka suke yi. Wani bugu da Jiniyo ya yi masa a ido sai da ya miƙe zaune da ƙarfi, da ƙafa Yasir ya mayar da shi kwance. Sai da suka tabbatar da sunyi masa duka ba na wasa ba, kafin suka ƙyale shi, Jiniyo ya fito da sabuwar reza a cikin aljihunsa, ya damƙi hannunsa mai ciwon ya yi masa yanka uku manya, sannan ya miƙe. Nan take numfashinsa ya ɗauke gabaɗaya, ganin ya daina numfashi ya sa suka fice gurin da gudu, motarsu suka shiga tare da janta da ƙarfi. Jiniyo ya lumshe idonsa yana jin zafin zuciyarsa na raguwa. Bayan kamar minti goma da tafiyarsu Karensa ya dawo bakinsa ɗauke da ledar abinci, gabansa ya zo ya ajiye ledar, sai dai duk da duhun da ya mamaye gurin ya lura da rashin motsin sa, zagaye shi ya fara yi yana kuka. Sai dai shiru bai motsa ba, da ya gaji da kukan ya zo kusa da shi ya kwanta. Hasken ranar da ya fara fitowa ne ya dake kumburariyar fuskarsa, a hankali ya fara motsa jikinsa da yake a kumbure, hannunsa mai ciwo ya ƙara kumbura ga busashen jinin da ya bushe ya ƙara mannewa da fatar gurin, idonsa ɗaya ya kumbura sosai. Ciwon da ke ratsa jikinsa ba zai iya bayyana shi da baki ba, ajiyar zuciya yake saukewa kaɗan, idanunsa suka fara buɗewa a hankali. Ji ya yi kamar ƙwayar idonsa ɗaya za fito tsabar azabar daya ji a gurin, ƙoƙarin motsa bakinsa yake son yi ya kasa saboda salatif ɗin dake manne a gurin, cikin azaba ya saka hannunsa mai lafiyar wanda shima ciwo yake masa a yanzu sakamakon dukan da a ka yi masa, cire salatif ɗin ya yi daga bakinsa yana zubar da yawo, abin da suka tura masa a baki tuni ya narke masa a ciki. Iska ya furzar mai zafi yana nishi da ƙyar, cikin ƙarfin hali da jarumta ya tashi zaune yana jingina jikinsa da ruɓaɓɓen ginin dake gurin. Kallon hannunsa ya yi yaga yadda hannun ya ƙara hawa, ga yanka a cikinsa, ya runtse idonsa hawaye masu zafi na zuba a gefen fuskarsa. Dubawa ya yi baiga karensa ba, ya miƙe da ƙyar yana tangaɗi, fuskarsa a kumbure ya fita waje yana jan ƙafarsa dake yi masa ciwo sosai, bakin bolar nan ya je ya zauna ya tsurawa hanyar da motar su Joriyya ke biyo wa. Misalin ƙarfe tara Dady ya je har gida ya samu Malam Nura. A ƙofar gida ya same shi zaune yana karatun da ya saba a nutse, cikin tsafta da kamala. Dady ya fito daga motar shi ya nufe shi. Malam Nura ya saki fuska ganin Dady, da sallama ya isa gurin, Malam Nura ya amsa yana miƙa masa hannu suka yi musabaha suna gaisawa cikin mutunci, Dady ya zauna akan tabarmar dake shimfiɗe a gurin. Malam Nura ya ce "Alhaji yau kai ne da kanka a ƙofar gidana?". Dady ya dubi shi cikin yanayi na damuwa ya ce "Na zo ne akan batun yarinyata ne, kwana biyu bamu gane ma kanta, shi ne muke tunanin ko akwai matsalar shafuwar aljanu a tare da ita, akwai wani mahaukaci da tunda ta fara ganinsa gabaɗaya ta rikice, da farko mun ɗauka tausayinsa ne take ji, daga baya sai muka ga abin ya fara wuce gona da iri. Shi ne nake son ka taimaka mana da addu'a. Saboda ina zargin mahaukacin nan kamar ba mutum bane aljani ne, kullum bata da batu sai na shi, gabaɗaya ta bi ta susuce akan shi". Malam Nura ya jinjina kai ya ce "Babu damuwa in sha Allah zamu yi abin da ya kamata, gidan zan je ko kuma nan za ka zo da ita?". Dady ya ce "Idan babu damuwa ina son mu je yanzu, idan kuma kana da wani uzuri ne sai mu bari zuwa anjima da yamma sai na aiko a ɗauke ka" Malam Nura ya ce "A'a muje yanzu, anjima da yamma akwai in da zani". Dady ya yi murna sosai da hakan, Malam Nura ya naɗe tabarma ya kai cikin gida sannan ya fito, mota suka shiga direba ya ja motar suka wuce. A rantsatstsen falon saukar baƙin Dady aka sauke Malam Nura, nan aka kawo masa lemu da ruwa. Dady ya wuce ciki, bai ɗauki lokaci ba ya dawo falon hannunsa riƙe dana Joriyya. Da sallama ya shigo, Malam ya ɗan bi ta da kallo yana nazartarta. Risinawa ta yi cikin sanyin murya ta gaida Malam, ya amsa mata cikin sakin fuska, Dady ya dubi shi cikin yanayin damuwa ya ce "Gata nan Malam, lokaci ɗaya muka kasa gane ma kanta, gabaɗaya ta birkice, don Allah a

Chapter 6 of 9