ɗan duba mana ita ko da wata matsalar" Malam Nura ya jinjina kai sannan ya fara yi mata karatu tare da karanta addu'oi. Ya ɗauki dogon lokaci yana karatun, ita dai Joriyya kanta a ƙasa tana sauraren ikon Allah, zuwa can Malam Nura ya kalle ta na ɗan lokaci kafin ya girgiza kai ya dubi Dady ya ce "Alhaji yarinyar nan bata da komai, babu wani shafar aljanu da yake damunta, wataƙila ta sakawa ranta tsananin tausayin shi ne shi ya sa take yin haka, sai dai akwai al'amari mai girma a tare da wannan ƴar taka wanda na kasa fahimtar ko mene ne, amma in sha Allah nan kusa ko mene ne zai fara bayyana".
Dady ya girgiza kai cike da damuwa yana dafe kai ya ce "To yanzu babu wani taimakon da za ka iya bamu ne? Saboda tana yawan ambaton shi, tana yawan magana akan shi, tun hakalinmu baya tashi har abun ya fara ɗaga mana hankali. Sai ta riƙa ce mana wai shi ba mahaukaci bane, ta san shi, mantawa aka yi da shi, sannan kuma tana yawan ɗaga hankalinta akan shi, dalilin haka ya sa muke zargin ba mutum bane aljani ne yake zuwar mata a suffar mutane".
Malam Nura ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ba aljani bane, tabbas mutum ne, kawai dai akwai wani al'amari mai girma tsakanin wannan bawan Allah da Joriyya, amma na kasa fahimtar komai, kuma ina son ku kwantar da hankalinku, ku sani lafiyar ƴarku ƙalau, sai dai akwai wani abu da yake fizgarta zuwa gare shi".
Joriyya ta kyaɓe fuska tana ƙoƙarin yin kuka ta ce "Yawwa Malam gaya musu dai ba aljani ba ne mutum ne kamar kowa, kuma ba mahaukaci ba ne mantawa aka yi da shi".
"Ka ji ko Malam, kaga irin wannan surutun ne bana son tana yi" Dady ya faɗa yana nuna Joriyya. Malam Nura ya ce "Yi haƙuri Alhaji in sha Allah za ta daina, idan na koma gida zanyi mata wani rubutu sai ka aiko a karɓa mata" Dady ya jinjina kai yana yi masa godiya, sannan ya yi masa alkhairi, bai so karɓa ya tilasta masa ya karɓa dole. Suka fito harabar gidan Dady ya sa a mayar da shi gida. Sannan ya kama hannun Joriyya suka koma ciki, suna shiga falon ta zame hannunta daga na Dady ta dafe ƙirjinta, Dady ya ce "Shalele lafiya dai?".
"Dady"
"Na'am Shalelena"
"Mu je mu duba shi, bashi da lafiya, Dady yunwa yake ji bai ci abinci ba!".
"Yi mini shiru babu in da za muje, kuma kika sake zancensa sai na kai gurin Na'ima in nisanta ki da ƙasar nan kowa ma ya huta" yana gama faɗar haka ya wuce da sauri ya bar ta a gurin. Yana ƙoƙarin haurawa sama ne ya ji ƙarar faɗuwar abu, juyowar da zai yi yaga Joriyya zube a ƙasa numfashinta na fita da sauri.
Amanarcool
08163516796
💦 AKWAI SILA 💦
BY AMANARCOOL
YOTA ID/021
*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*.
PAGE 23-24
Dady ya tsaya cak ganin Joriyya kwance a ƙasa tana shure-shure. Da gudu ya ƙaraso kusa da ita yana ɗaga kanta ya ɗora a cinyarsa. "Shalele Shalele ki buɗe idonki ki kalle ni" Ya faɗa cikin rawar murya. Momy ta fito da sauri tana faɗin "Subhanallah meya same ta kuma?" .
"Faɗuwa ne ta yi daga cewar ba za ta je gurin wancan yaron ba".
Momy ta buɗe baki za ta kira sunanta, suka ga Joriyya ta girgiza jikinta da ƙarfi, ta buɗe idanunta dake cike da hawaye, ta miƙar da hannunta sama kamar tana neman taimako "Dady.... Don Allah mu je mu duba shi, mu kai masa abinci" ta faɗa muryarta a sanyaye idonta na sake rufewa.
Daga Dady har Momy shiru suka yi, suna kallonta, zuciyoyinsu cike da ƙunci. Momy ta ce "Alhaji wai me Malam ya ce ne akan wannan matsalar?" "Ba abin da ke damunta, kuma ya tabbatar mini da cewar yaron nan mutum". Dady ya ba ta amsa.
"To amma Alhaji me ya sa take yin waɗannan abubuwan akansa?" Kafin Dady ya yi magana Joriyya ta sake buɗe idanunta, hawaye na zubowa a gefen fuskarta. Ta kama rigar Dady da ƙarfi "Don Allah Dady mu je yanzu, idan bamu je ba zai iya mutuwa" Ta faɗa tare da fashewa da wani irin kuka mai taɓa zuciya. Dady ya kasa magana. Abin da Malam Nura ya faɗa masa ne yake dawo masa ɗaya bayan ɗaya "Akwai wani abu da yake fizgarta zuwa gare shi". Shiru ya yi yana nazarin me yake fizgar Shalele zuwa ga wannan yaron da bashi da saiti a ƙwaƙwalwarsa.
Ƙara riƙe rigar Dady ta yi tana kuka, Momy ta ce "Alhaji me ya kamata muyi? Wannan kukan da take yi ina tsoron kar ciwonta ya tashi".
"Stop crying Shalele, na ji zan sa a je a duba shi, kuma za a kai masa abinci, ki yi shiru..." kafin ya ƙarasa ta katse shi da cewar "A'a Dady tare dani nake son a je in duba hannunsa idan ya warke".
"Ya salam!" Dady ya faɗa yana dafe kansa, sannan ya ce "Na ji tashi ki shirya mu je, shikenan hakan ya yi miki?" Ya yi maganar yana kallon Joriyya, miƙewa ta yi tsaye da sauri tana murmushi ta ce "Eh Dady, bari na canza kaya" tana gama faɗar haka ta nufi ɗakinta da gudu. Dady ya dubi Momy ya ce "Shafa ina ga dole ne Joriyya ta bar ƙasar nan, saboda banga alamar za ta daina nuna damuwarta akan wannan yaron ba, ba zan yarda da girmana da mutuncina a garin nan ba a riƙa ganina a gurin wani ƙasƙastaccen talaka ba, talakan ma mahaukaci". Momy ta ce "Alhaji nima na goyi da bayan ta bar ƙasar ko hankalin mu zai kwanta daga mu har ita". Ba a ɗauki dogon lokaci ba Joriyya ta fito cikin ƙananun kaya riga da wando, ta ce "Momy zuba masa abin a flaks mu kai masa" da sauri Dady ya ce "A'a bari idan mu je can sai a siya masa" fita suka yi zuwa harabar gidan Dady ya sa aka fito da ɗaya daga cikin motocinsa, suka shiga tare da rakiyar security biyu direba ya ja suka bar gidan.
Jiniyo ne kwance a ɗakin Salim, juya wa ya yi a hankali yana murmushi, abin da ya faru daren jiya na dawo masa daki-daki irin yadda mahaukacin ya riƙa kakari yana son yin ihu babu hali. Da yadda ya daina motsi, lumshe idonsa ya yi na ɗan lokaci kafin ya buɗe su ya ce "Shegen kaya ai yanzu mun koya masa hankali". Ya miƙe zaune ya dubi Salim da Yasir "Gayu Allah jiya wawan can fa ya daku ba ƙarya" ya ƙarasa maganar yana dariyar mugunta.
Salim ma dariyar yake yi ya ce "Ya daku dan uwarsa, har yanzu ina tuna yadda yake shure-shure, ya ji dukan manya, yanzu ai zai san bakin rijiya ba gurin wasan makaho ba ne". Yasir ya ɓarka uwar dariya suna tafa hannu da Salim.Ya ce "Ƙila ma ya mutu". Jiniyo ya yi dariya cike da shaƙiyanci "Ai bai mutu ba, zafin duka ne ya ji, irinsu ba sa mutuwa da wuri, azaba ce ta yi masa yawa ya suma". Dariya suka kwashe da ita, dariya irin ta samari masu cike da shaƙiyanci, babu alamar nadamar abin da suka aikata a tare da su.
Yana kwance a cikin bolar rana na dukansa, karensa na zaune a gefensa sai zuga yake yi yana fitar da harshe waje, zafin ciwo da azabar da yake ji ba za su misaltu ba, idonsa ɗaya ya ƙara kumbura sosai, cikin ƙarfin hali da jarumta ya samu da ƙyar ya tashi zaune, kallon hannunsa yake yi, daga jiya zuwa yau hannun ya ƙara canza kamanni, fatar gurin ta fara ɗayewa, ga wata uwar tsokar da ta zazzago tana na rawa kamar an yanko ta da wuƙa, yana jin zafin ciwo sosai, zuciyarsa ba ƙaramin ɗaci take yi masa ba. Wani abu mai kamar tsinin wuta yake jin yana ratsa hannunsa zuwa ƙirjinsa. Ya runtse idanu yana jan dogon numfashi mai azaba. Buɗe ɗayan idonsa ya yi hasken rana ya doki ƙwayar idon, da sauri ya rufe idon, gurin ya yi shiru baka jin motsin komai sai na iskar da take kaɗawa, ya ɗaura hannunsa mara ciwon a kan ƙirjinsa kamar yana tantama ko zuciyar da ke bugawa a ciki tasa ce, ko kuma wata irin halitta ce da ta tsaya masa a ciki. A hankali kamar wanda ya manta yadda ake magana, ya furta kalmomin da ba shi kaɗai yake fahimtar su. Ji ya yi kamar ana kiransa daga nesa, kamar wata ƙaramar murya na yi masa amsa kuwa a ƙasan zuciyarsa, bai san me yasa ba. Bai san me yake nema ba. Bai san wa yake nema ba. Amma yana jin sautin wannan kiran da ya kasa fahimtar daga ina ne? Ya sunkuyar da kansa, yana lumshe idonsa, yana jin kamar wani abu yana ja masa rai zuwa wani guri, guri da bai san shi ba amma yana jin shi daga cikin jini da tsokarsa, kamar ya haɗu da wani ɓangare nasa da ya daɗe da ɓacewa. Jama'a na wuce suna kallonsa babu wanda ya yi tunanin ya tsaya, balle ya yi yunƙurin taimaka masa akan halin da yake ciki.
Motar ta tsaya nesa da gurin bolar nan kaɗan. Dady na jin kamar zai yi bindiga saboda takaici, kamar shi ace yana zuwa wannan ƙasƙantaccen gurin, bolar cike take da tarkace, warin ƙazanta na tashi yana zunkuɗar zuciya, motar na tsayi Joriyya ta buɗe ƙofa ta fito a firgice. Fitowa Dady ya yi, ya tsaya yana kallon bolar yana yamutsa fuska, zuciyarsa na tashi, yana jin wani zafi a ƙirjinsa, bai taɓa tunanin ƴarsa za ta ja shi zuwa irin wannan guri ba.
Kafin ya anka tuni Joriyya ta ƙarasa in da yake, da sauri security suka bi bayanta. Dady ya taka a hankali ya ƙarasa gurin, yana zuwa ya ce "Shalele ki yi a hankali mana, idan ya ji miki ciwo fa".
Cikin kuka Joriyya ta ce "Dady dubi yadda hannunsa ya koma, don Allah Dady a sai ya masa magani, shi ma fa mutum ne kamar kowa". Sai a lokacin mahaukacin ya ɗago da idonsa, ya kalli Joriyya, sannan ya mayar da kallonsa ga Dady. A mugun firgitace ta miƙe tsaye tana ja da baya ta ce "Dady kalli fuskarsa, me ya same shi haka ne? Dubi jikinsa, idonsa ɗaya baya buɗewa Dady". Ta ƙarasa maganar jikinta na tsuma tsabar kaɗuwa da ta yi. Shi kansa Dady sai da ya ji tsoron ganin fuskar mahaukacin, lokacin ɗaya ya fahimci cewar doka ne aka yi masa ba na wasa ba. Ganin yadda Joriyya ke gunjin kuka tana tambayarsa me ya same shi? Ya ce "Shalele dukansa ne aka yi, kuma duka ba na wasa ba".
Cak ta tsaya, ta daina kukan da ta yi, ta kalli Dady sannan ta mai da duban ta ga gare shi, cikin sarƙewar murya ta ce "Dady duka kuma? Waye zai dake shi haka? Me ya yi masa? Wanda ko magana baya iyayi?".
Dady ya nisa ya ce "Shalele kin san fa mahaukaci ne bashi da hankali, wataƙila ya yi yunƙurin cutar dani wani ne ya sa aka yi masa wannan dukan, shi ya sa nake ƙoƙarin ankarar dake hatsarin dake tattare da wannan mahaukacin amma kin ƙi ki fahimta, yanzu dai ai kinga irinta, ya je zai cutar da wani ya jawowa kansa duka".
Cikin ihu ta ce "Dady wallahi ba haukaci ba ne, mantawa ne aka yi da shi, wannan zaluntar sa ne aka yi. Dady don Allah ka sa a kama wanda ya dake shi a rama masa, ji yadda idonsa ya yi" . "Shalele ki yi shiru da wannan kukan da kike yi, taya zan sa a kama wanda ya yi masa wannan dukan bayan ban san ko waye ba. Duk yadda aka yi wanda ya dake shi ɗin nan ya yi yunƙurin cutar da shi ne ya sa ya kare kansa". Tsalle ta yi ta fara ihu a gurin, hankalin jama'a ya fara dawowa kansu, baƙin ciki ne ya ƙara turniƙe zuciyar Dady. Cike da ƙunar rai ya daka mata tsawa "Shalele ki rufe mini baki kafin na ɓarar dake a gurin nan". "Dady don Allah..." "Ba za ki yi mini shiru ba ne!" Ya sake daka mata tsawa, idonsa sun kaɗa sunyi jajur. Ya dubi ɗayan security ɗin ya bashi umarni da ya siyo masa abinci, babu ɓata lokaci ya karɓo masa abincin ya kawo tare da ruwa ya ajiye a gaban mahaukacin. Dady ya ja hannun Joriyya da ƙarfi ya tura mota, tana ihun kuka, security suka shiga motar direba ya ja motar da ƙarfi suka bar gurin. Tsohon nan da yana tsaye a gefe ya yi dariya tare da jinjina kai ya wuce.
Har suka ƙarasa gida kuka take yi, Momy ta fito daga kitchen taga sun shigo gidan Joriyya na rusa uban kuka, ta ce "Alhaji me kuma ya faru ne?".
Ran Dady ya gama ɓaci, tun a hanya ya yanke shawar dole ne gobe ya bar ƙasar nan da ita.
"Alhaji magana nake yi ka yi mini shiru"
Dady ya shaƙi iska ya fitar da ƙarfi ya ce
"Na gaji da wannan abin, yau tura ta kai bango, ba zan bari Shalele ta ci gaba da tozarta ni a gaban jama'a ba, dole ne ta bar ƙasar nan". Ya juya ya kalli Joriyya
"Ki shirya gobe jirginmu zai tashi zuwa Dubai, za kai can gurin Na'ima ki zauna ko da na tsawon wata biyu ne, wataƙila rashin ganinku a gari ɗaya zai sa zuciyarki ta samu nutsuwa hankalinki ya kwanta, kuma na gama magana kada in ji kin ce ƙala". Dim! Ƙirjinta ya buga da ƙarfi ta ce
"Daddy Dubai? Ni ɗin?".
"Ke ɗin!" Ya ce cikin tsawa "Ba zan barki ki lalata rayuwarki ba, ba zan bari ki sake kusantar wancan yaron ba, ba za ki zubar mini da mutunci ba. Dubi yadda kika tara mini jama'a yau, kowa ne banza ya tsaya sai kallon mu yake yi". Lumshe ido ta yi, zuciyarta na tsananta bugawa, kalmar raba ta da ƙasarta ta dake ta sosai. Raɓa su ta yi ta haye sama tana jin zafi sosai a ranta.
Tun da motarsu ta bar gurin ya yi shiru yana bin hanyar da motar tabi da kallo, numfashinsa na fita a hankali, yana jin ɗaci a zuciyarsa. Idonsa na yi masa zafi sosai, yunwar da ya ji ta addabe sa ne kamar hanjin jikinsa za su fito ya sa ya jawo ledar abincin da ƙyar ya fara ci, bakinsa ne ya soma karkarwa cikin wata irin murya ya ce "Kar ki tafi…" Sai kuma ya ji zuciyarsa na buɗewa, wani abu daya rasa gane ko meye na shigarsa da ƙarfi. Lokaci ɗaya tunaninsa ya sake hargitsewa.
Littafen akwai sila na kuɗi ne, saura pages biyu free page ya ƙare, ga mai buƙatar cigaba zai biya 500 kacal ta wannan account ɗin 1019533255 Nafisa Muhammad UBA, sai a tura mini shaidar biya. Ka da ku bari a yi tafiyar nan ba da ku ba.
Amanarcool
08163516796
💦 AKWAI SILA 💦
BY AMANARCOOL
YOTA/021
*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*.
PAGE 25-26
Bayan shigar Joriyya ɗakinta, shiryawa Dady ya yi ya wuce gurin aikinsa ransa a jagule, gidan ya yi shiru. Momy ta zauna tana saƙe-saƙe a zuciyarta. Lamarin nan ya wuce duk yadda suke tunani, a hankali ta ɗauki wayarta ta kira Zainab, bayan sun gaisa ta ce "Zainab abin da ba so dai shi ne zai faru".
Zainab ta ce "Subhanallah Momy me ya faru kuma?".
Nisawa ta yi, sannan ta ce "Auta dai dole za ta bar ƙasar nan, abin da take yi ya yawa. Yau har ta tunzura mahaifinku babu shiri ya ce gobe zai bar ƙasar nan da ita. Zainab zuciyar Auta ta ƙeƙashe akan yaron nan, tana yin abubuwan da ba mu taɓa tunanin ba".
Zainab ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ce "Tafiya kuma Momy? Da dai an ƙara haƙuri a gani, duk da Joriyya ba ta iya saka abu a rai ba, amma ni ba na son ta yi nesa damu".
Momy ta share hawayen da suka zubo mata, tana kokawa da zuciyarta, kar kukun da take riƙe wa ya kufce mata, ta ce "Zainab kin san halin Dadyn ku magana ɗaya yake yi, tunda ya zartar da wannan hukuncin babu wanda zai hana shi, ni kaina ban so tafiyar nan ba, wallahi Zainab yau ba zan iya bacci ba. Autata rashinta a gida nan zai ɓata min rai sosai".
"Ki yi haƙuri Momy, na sani, in sha Allah wannan tafiyar za ta kawo ƙarshen wannan damuwar, muci gaba da yi mata addu'a. Ina da tabbacin Anty Na'ima za ta ba ta duk wata kulawar da ta dace".
Momy ta jinjina kai kamar tana ganin ta, ta ce "Shikenan Allah ya shiga lamarin Auta ya yaye mata komai" Zainab ta amsa da amin tana ƙara bawa Momy haƙuri tare da kwantar mata da hankali, daga ƙarshe suka yi sallama.
Daddy na zaune tare da abokansa Alhaji Fahad, da Alhaji Hamza a ofishin sa suna tattaunawa akan abin da ya shafi kasuwansu. Sai dai babu annuri a fuskar Dady saboda abin da ya faru kafin ya baro gida, sun lura da yanayinsa Alhaji Hamza ya ce "Sulaiman lafiya kuwa naga yanayin ka ya canza kalmar akwai abin da ke damunka?". Dady ya nisa tare da furzar da iska mai zafi ya ce "Ina tunanin rabuwar da zanyi da Shalele ne, in Allah ya nufa gobe zamu yi tafiya da ita, zan kai ta can Dubai gurin Na'ima ta zauna na ɗan wani lokaci".
Ya ce "Dubai kuma? Akan me za ka kai ta can ta zauna?" Dady bai ɓoye musu komai ba ya faɗa musu abin da ke faruwa. Alhaji Fahad ya ce "Danƙari, wata sabuwa in ji ƴan caca, to lallai gara ka rabata da ƙasar nan gabaɗaya, idan ba haka ba mutuncinka ne zai zube a idon Duniya, a riƙa yamaɗiɗi da kai a gari, ana cewa duk izzarka da taƙamar ka yarinyarka ta ƙare akan talaka, talakan ma wulaƙantacce wanda bai san inda Duniya ta sama gaba ba, sannan ka daina wannan damuwar da kake saboda banga abin da damuwa ba, karka manta gurin yayarta za ta je".
Cikin damuwa ya ce "Ba tafiyar ce ke damuna sosai ba, ina jin kamar akwai wani abu da ke shirin tasowa a can ɗin, wanda na rasa fahimtar ko meye, ban san me zai faruwa ba amma zuciyata tana faɗa min wannan tafiyar kamar akwai abin da zai faru da ba zai yi mini daɗi ba".
Alhaji Fahad ya dafa kafaɗarsa ya ce "Abokina kar ka damu in sha Allah babu abin da zai faru, zamanta a nan zai sa ta ƙara samun rikicewar zuciya. Idan kuka bari ta ci gaba da zama kusa da wannan mahaukaci zaku ga abin da ba zai yi muku daɗi ba".
Dady ya lumshe ido, ƙirjinsa na yi masa nauyi, gefe ɗaya yana jin tsoron bayyanar sirrin daya daɗe a ɓoye, wanda bayyanar zai iya haifar da abubuwa da yawa.
Tunda Joriyya ta shiga ɗakinta kwance take ƙasa akan tayis ta ƙurawa guri ɗaya. Wani irin zafi take a ƙirjinta wanda bai kamata a ce yarinya mai ƙananun shekaru na ji ba. Zuciyarta zafi take yi mata kamar an ɗora mata garwashin wuta. Idanunta sun yi ja sosai saboda kukan da ta yi, tun da Dady ya sanar da ita cewar gobe jirginsu zai ɗaga zuwa Dubai take jin wani sabon al'amari na shigarta, tsoro da fargaba suka ɗarsu a zuciyarta. A hankali ta ɗakko wayarta ta turawa Safina saƙo kafin ta a jiye wayar tana lumshe idanunta.
Wajan ƙarfe ɗaya na rana Jiniyo ya shigo, babu kowa a falo kai tsaye ya wuce ɗakinsa. Wanka ya yi ya sauya kaya sannan ya fito ya nufi ɗakin Abbansa. Yana isa ƙofar ɗakin ya ji Abbansa na waya, tsayawa ya yi a bakin ƙofar yana zaro ido waje, gabansa ne ya yi mummunar faɗuwa jin irin kalaman da suke fitowa daga bakin Abbansa. Nan take jikinsa ya ɗauki rawa, zufa ta fara tsatsafo wa a goshinsa. Ji ya yi kamar za a buɗe ƙofar a fito da sauri ya juya zai bar gurin. "Jiniyo" ya ji an kira sunan sa da ƙarfi, babu shiri ya juyo jikinsa na ɓari yana zaro ido kamar wanda ya yi wa sarki ƙarya. Abba ya ce "Alamunka sun nuna ka ji wayar da na yi, to ina son ka buɗe kunnuwanka da kyau ka saurare ni, wallahi wallahi wallahi ka ji na yi rantsuwa sau uku ko? Jiniyo idan ka sake na ji maganar nan a wani guri, kai ko da a wajan Mamanka ne saina kashe ka, ka bar ganin kai ne ɗa ɗaya tilo dana mallaka a Duniya zan iya kashe ba tare da nayi nadamar yin hakan ba". Jiki na karkarwa Jiniyo ya ce "Wallahi Abba ban ji komai b...." "Yi mini shiru" Abba ya faɗa yana daka masa tsawa, ya ce "Ni za ka cewa ba ka ji komai ba? Wannan gargaɗi ne na yi maka idan kunne ya ji jiki ya tsira". Daga haka ya buɗe ƙofa ya koma ciki. A guje Jiniyo ya bar gurin, yana isa falo Mama ta fito daga kitchen ɗauke da tire a hannunta Jiniyo ya bangaje ta ba tare da ya lura da ita ba, tiren ya faɗi ƙasa kofunan gilas ɗin dake kai suka fashe. Jiniyo bai tsaya ba ya shiga ɗakinsa da gudu ya rufe ƙofa, saman gadonsa ya haye ya rufe da bargo yana jin wani zazzafan zazzaɓi na rufe sa. Bayan sa Mama ta biyo ko da ta zo ya kulle ƙofa, bugun Duniya ta yi bai buɗe ba dole ta juya, falo ta koma tana zuwa taga Abba ya fito yana baza babbar rigarsa, zai fita, ta ce "Alhaji ina zuwa naga baka daɗe da shigowa ba?"
Ya ce "Wani uzuri ne ya kamani yanzu" daga haka ya buɗe ƙofa ya fice abinsa. Shiru ta yi daga baya ta shige ɗakinta.
Safina na zauna riƙe da wayarta ta gama duba saƙon da Joriyya ta turo mata. Idonta ya cika da ƙwalla, jikinta ya yi sanyi. Umman ta ce "Lafiya dai Safina? Naga kin tsurawa wayarki ido kina ƙoƙarin yin kuka?". Cikin shagwaɓa ta ce "Umma wai Joriyya ce za a tafi da ita Dubai gobe, kuma a can za ta zauna" ta ƙarasa maganar hawaye na zubowa akan fuskarta.
Umma ta ce "Ki yi haƙuri mana, tunda dai za ta dawo ba can za ta zauna ba". cikin kuka ta ce "Umma Joriyya ba ta son tafiyar nan dole aka yi mata, ya zan yi?".
Umma ta yi shiru saboda ta san irin shaƙuwar dake tsakanin su, ta ce "Duk da haka dai ki yi haƙuri, wataƙila akwai dalilin daya sa za ta tafi can ɗin" kuka sosai Safina ke yi. Umma ta shiga rarrashinta da kwantar mata da hankali akan cewar za ta dawo.
*******
Alhaji Kabir na zaune tare da