Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 9
ce "Umar ka zaɓe mutane uku daga cikin manyan ma"aikatana, ku ɗauki ɗaya daga cikin sabbin motocin da aka kawo mini satin da ya wuce, sai ku haɗa da biyu daga cikin motocina tsohi ku shirya yanzu. Abuja nake so ku je yau ɗin nan, ina son ku ziyarci ƙananun asibiti ku duba masu neman taimako sai a taimaka musu, daga nan ku wuce har asibitin mahaukata ku yi bincike sosai idan akwai masu taɓin hankali waɗanda akwai yiyuwar za su iya warkewa sai ku sanar da ni kai tsaye, za a biya ko nawa ne domin ganin sun samu lafiya. Idan ta kama a fitar da su ƙasar waje don magani ba damuwa zan ɗauki nauyin komai". Umar ya jinjina kai, zuciyarsa cike da mamakin irin ƙudurin da Alhaji ya ɗauka na taimakon da yake yi "To Alhaji in sha Allah yanzu zamu shirya yanzu kamar yadda ka buƙata, nan da awa ɗaya mun ɗauki hanyar Abuja" ya faɗa cikin girmamawa. Alhaji ya jinjina masa kai kamar yana ganinsa "Allah ya kai ku lafiya sai na jiku" daga haka ya kashe wayar. Cikin minti talatin su Umar suka shirya tsaf kamar za su je rangadin gwamnati. Umar da sauran ma'aikatan suka kama hanyar Abuja tare da rakiyar security ɗin gidan Alhaji Kabiru. Basu ɗauki dogon lokaci ba suka iso Abuja kasancewar lafiyayyun motoci ne, motocin sun yi tsaf-tsaf cikin titin Maitama, a hankali suke tafiya, shawara suka yanke a kan su fara zuwa asibitin mahaukata, suka nufe hanyar asibitin. A daidai bolar da mahaukacin nan ke zama motocin suka zo wucewa, ya na kwance gefe ɗaya, jikinsa a takure, ƙafafunsa sunyi kaca-kaca da ƙazanta, hannunsa na ajiye a gefe yana fitar da wasu kalar ruwa haɗe da jini babu kyan gani. Karensa na gefensa a kwance, can Karen ya hange wata leda a tsakiyar titi mai masƙi ya miƙe da sauri zai je ya ɗakko, ya kai tsakiyar titin kenan motocin yaran Alhaji Kabiru suka zo cikin sauri ba tare da sun lura da karen ba suka hau ta kansa da mota sai da ya yi wata ƙara mai sauti da ban tsoro, kafin ya yi shiru gabaɗaya alamar ya mutu. Duk da halin da yake ciki jin ƙarar da karensa ya yi ya sa ya ɗago da sauri ya dubi in da ya ji ƙarar karen, zaro idonsa ya yi waje, zafin da yake ji a hannunsa da idonsa ya ƙara tsananta, hakan ya sa shi tashi da ƙyar yana jin kamar an jona masa wutar lantarki a ƙirji. Ya ɗaga kai da sauri. Ya ga karensa a ƙasa ya murɗe guri ɗaya jini na fita ta kansa, wata uwar ƙara ya saki mai cike da raɗaɗi, ɓacin rai, da ciwo, ƙarar da ba ta yi kama da ta ɗan adam ba, kuma ba ta yi kama da ta dabba ba. Wata irin murya ce da za ta iya sa zuciya ta yi tsalle saboda firgici, ya ƙarasa gurin karen yana gunjin kuka. Motocin suka tsaya cak. Umar da sauran ma'aikatan suka fito da sauri. Dukan su tsaya wa suka yi cak, suna bin sa da kallo ganinsa da yadda hannunsa da idonsa ya kumbura, ya yi muni yana fitar da ruwa, ga jikinsa da ƙazanta babu kyan gani, hakan ya tabbatar musu da cewar mahaukaci ne, suka mayar da duban su ga karen da ya daɗe da mutuwa sai da Umar ya dafe kansa ya ce "Ya Allah!". Ɗaya daga cikin security ya matsa kusa da shi ya ce "Oga Umar wannan fa na cikin mawuyacin hali" ya faɗa yana gyara riƙon bindigarsa. Umar ya ce "Ku kama shi a hankali, kar ku yi abin da zai sa ya ƙara jin ciwo a hannun". Suka yi ƙoƙari da ƙyar da wahala suka miƙar da shi tsaye yana turjewa tare da nuna musu karensa yana kuka, riƙe hannunsa suka yi cikin kulawa suka saka shi a mota. Yana son yin magana ya kasa sai huci yake yi, idonsa cike da hawaye saboda karensa. Jama'a sunyi cirko-cirko suna kallo wasu sun ji tausayinsa wasu kuma dariya kawai suke yi masa. Cikin hanzari suka shigar motar direba ya ja, kai tsaye asibitin mahaukata suka nufa. Littafen akwai sila na kuɗi ne, daga wannan free page ya ƙare, ga mai buƙatar cigaba zai biya 500 kacal ta wannan account ɗin 1019533255 Nafisa Muhammad UBA, sai a tura mini shaidar biya. Ka da ku bari a yi tafiyar nan ba da ku ba. Amanarcool✍️ 08163516796 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9