Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 9
baka mance wannan ciwon ba har abada" Mahaukacin ƙoƙarin tashi yake yi ya kasa, cike da raunin murya ya ce "Ka bar ni" Jiniyo ya yi dariya mai cike da mugunta. "Kai ba ni da niyyar barinka, ai tunda ka bari Joriyya ta fifita ka a kaina ba zan taɓa barinka ba". Tsayawa ya yi yana kallon hannunsa da ya kumbura sosai, cikin rashin tausayi ya sa ƙafarsa ya taka hannun iya ƙarfinsa. Mahaukacin ya sake wata irin ƙara, ƙarar da ta karaɗe gurin, daga nan kuma ya yi shiru saboda numfashinsa da ya ɗauke, Jiniyo ya kuma kai masa harbi ga ciki sannan ya bar gurin cike da rashin imani, yana isa bakin ƙofar fita ya yi turus yana ƙwalalo idanu waje, jikunsa ne ya ɗauki rawa, lokaci ɗaya tsoro da firgici suka bayyana, ja da baya ya fara yi yana girgiza kansa cike da kaɗuwa. Amanarcool 08163516796 💦AKWAI SILA💦 BY AMANARCOOL YOTA ID/021 *SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*. PAGE 15-16 Sake buɗe idanunsa ya yi, jikinsa na ɓari, fitsari na ƙoƙarin zubo masa, ko a mafarki bai taɓa ganin wannan tashin hankalin ba balle kuma a zahiri, mutum biyu ne tsaye a bakin ƙofar kangon kamar an dasa su, idanunsu a buɗe suna kallonsa ko ƙiftawa ba su yi, fuskarsu kamar an shafa mata karmatako, ko ina a jikinsu raunuka ne. Ɗayan riƙe da sarƙa a hannunsa, ɗayan kuma yana ɗauke da wani ƙaton tabo a goshinsa. Cikin ruɗa ni Jiniyo ya buɗe baki zai yi magana sai muryarsa ta ƙi fita, numfashinsa ya ɗauke. Ɗayan ya ɗaga hannu ya nuna Jiniyo da yatsa, nan take numfashinsa ya dawo, ya miƙe tsaye da sauri, gani ya yi idanunsu na fitar da wuta haɗe da wata ƙara da ya rasa sanin daga ina take fitowa, nan ya ji kamar wani abu ya lauye ƙafafunsa, kasa tsayuwa ya yi ya faɗi ƙasa. Lokacin da ya sake ɗaga kansa da zumar kallon su, ya ga gurin ya koma shiru, kamar babu abin da ya faru, da sauri ya miƙe tsaye, ya juya ya ga har yanzu mahaukacin na nan a kwance ba ya motsi. Jikinsa na rawa. A guje ya fice daga gurin, zuciyarsa na bugu da ƙarfi, tsoro da ruɗani na ƙara shigar sa. Su Dady na ƙarasa wa guda kafin security su buɗe masa ƙofa har ya fito, fuskarsa ɗauke da tashin hankali, idanuwansa sun sauya kala. Kamar wanda aka jefo ya shiga falon gidan. Momy na zaune ganin yadda ya shigo ɗin ta miƙe da sauri "Alhaji lafiya? Me ya faru?" Ta yi tambayar tana tsare shi da ido. Bai ba ta amsa ba ya haura sama kai tsaye, zuciyarsa na tsananta bugawa, ɗakin Joriya ya shiga tana kwance saman gadonta. "Shalele" ya kira sunanta a hankali. Tashi zaune ta yi tana kallonsa ta ce "Dady". Ya zauna a gefen gadon yana kallonta kamar zai ce wani abu, sai kuma ya yi shiru, ya san ko da ya yi mata maganar ba za ta fuskanci kalmomin ba, da kuma inda suka dosa ba, lumshe ido ya yi, yana tuna takardar da aka bashi, kalmomin da ke ciki na yi masa yawo a zuciya. "Shalele ki faɗa mini gaskiya" ya yi maganar ƙasa-ƙasa "Idan kika ga wancan mahaukacin me kike ji?". Joriyya ta kalle shi "Dady wallahi ban sani ba, amma dai ina jin tausayinsa, Dady a ko zamu je mu sake dubawa ko hannunsa ya warke?". Dady ya lumshe ido wannan ne abin da ya fi tsorata shi akan lamarin ƴar tasa, abin da take yi ya wuce tausayi. "Ya Allah" ya furta a hankali sannan ya dubi Joriyya ya ce "Koma ki kwanta" "Dady ba za muje mu duba shi ba?" "Zamu je amma ba yanzu ba" daga haka ya bar ɗakin, a bakin ƙofa ya ce karo da Momy, raɓa ta ya yi ya nufi ɗakinsa, Momy ta leƙa ɗakin Joriyya ta ganta a zaune ta ɗakko wayarta tana dannawa, ba ta ce mata ƙala ba ta juya ta nufi ɗakin Dady. A zaune ta tarar da shi ya duƙar da kansa ƙasa, zama ta yi kusa da shi ta dafa kafaɗarsa ta ce "Alhaji lafiya? Me yake damunka ne?". Cike da sanyin jiki ya ɗago da kansa yana kallon ta, "Babu komai bana jin daɗi ne, gashi yau na yi aiki na gaji". Shiru Momy ta yi tana kallon sa, ba dan ta gamsu da babu komai ba ɗin "To ka samu ka yi wanka ko za ka ji daɗin jikin ka mana" ta faɗa tana ƙara tsare shi da ido. Miƙewa ya yi a hankali ya cire kayan jikinsa ya shiga toilet saboda baya son ta yi tunanin wani abu. Ganin ya shiga toilet ɗin ya sa Momy tashi ta fita domin ta haɗa masa abinci. A ruɗe Jiniyo isa gida, kamar guguwa haka ya wuce Mama da Abbansa dake zaune a falon gidan, wanda dawowarsa kenan daga tafiyar da ya yi, bai ma lura da Abban nasa dake zanune ba, ɗakinsa ya je yana shiga ya saka wa ƙofar key, ya haye gadonsa, ya rufe kansa da bargo ban da rawar sanyi ba abin da yake yi. "Ba ka tsira ba" ya ji an faɗa da murya mai firgitarwa, buɗe ido ya yi a firgici ya tashi zaune, gumi na tsatstsafo masa a goshinsa. Ya duba gefensa, babu kowa, riƙe kansa ya yi yana girgiza wa. "Me yake shirin faruwa da ni ne? Wai waye wannan mahaukacin? Daga ina ya fito? Lallai ta tabbata ba mutum ba ne, in ma mutum ne tabbas akwai wani zafi da yake yi, ko wani abu da ba daidai ba a tare da shi, ya zama wajibi na ƙara nisanta Joriyya da shi". ya ƙarasa maganar yana sake kwanciya ya ƙudundune a bargon, zuciyarsa na ƙara gaya masa abin da ya gani ba wasa ba ne. Duk da wannan hali na firgici da yake ciki, bai fasa jin tsanar mahaukacin ba da kuma sake shan alwashi akansa. Iyayen Jiniyo ganin yadda ɗan nasu ya wuce ba tare da ya kalli inda suke ba suka san cewar ba lafiya ba, ko da Mama ta biyo bayansa ta ji ko lafiya? Ta tarar daya rufe ƙofar ta buga ƙofar tare da yi masa magana ta ji shiru, jin an fara kiran sallar magariba ya sa ta juya ta bar gurin. Bayan sallan isha su Momy na zaune a falo tare da Joriyya, game take yi a wayarta tana murmushi, Momy ta kalle ta cike da jin daɗin ganin yau ta sake jiki tana walwala ba kamar kullum ba, ta ce "Auta ko ke fa, hakan yafi ai, ki riƙa sakin jikin ki, kina wasa da dariya kamar yadda kika saba, ki cire damuwar komai da tunanin komai a ranki" . Hankalin Joriyya na kan game ɗin da take yi ta ce "To Momy na daina, daga yanzu ba zan sake ba" . Daɗi ne ya cika zuciyar Momy ta kalle Dady da hankalinsa baya kansu, yana can Duniyar tunani ta ce "Alhaji kana jin abin da Auta ke faɗa?" Sai a lokacin ya mayar da hankalinsa kansu ya ce "Me ta ce?" "Au baka ji abin da ta faɗa ba? Alhaji kamar akwai abin da ke damunka, tunda ka dawo daga gurin aiki na lura da yanayin ka ya canza, don Allah idan akwai abin da ke damun ka ka gaya mini?". Kafin Dady ya yi magana suka ji Joriyya ta ce "Dady wai nima yaushe za a yi mini aure in haifi yara? Anty Na'ima tana da ƴarta Ummie, Anty Zainab tana da Fahat, nima ina son in haihu a riƙa ce mini Momy da Dady kamar yadda nake kiran ku" ta ƙarasa maganar tana dariya tare da ajiye wayarta ta sake duban iyayen nata ta kuma cewa "Momy wai yanzu shima wancan mutumin haifarsa aka yi ne ko kuma daga sama ya faɗo? Bashi da iyaye ne? Naga kullum shi kaɗai yake zama a cikin datti, Allah Sarki Dady gobe zamu je mu sake duba shi ko? Hannunsa na yi masa ciwo sosai, Dady shin wai...." "Auta ki yi shiru haka nan" Momy ta katsita, kafin ta ce "Ba yanzu kika gama ce mini kin daina zance sa ba? Auta ki raba kanki da zancen yaron nan idan ba haka ba Dubai zamu tura ki can gurin Na'ima kowa ma ya huta". "Momy ba zanje ba" "To ka da na sake jin kin yi maganarsa, idan ba haka ba Dadyn ki zai kai ki gurinta". "Dady da gaske za ka iya kai ni can ku daina ganina?" ta yi maganar tana tsare Dady da ido. "Eh mana Shalele idan baki son zuwa to ki daina nuna damuwar nan da kike yi akan wanda baki san daga ina yake ba, ba a san asalinsa ba, kuma gashi yana fama da matsalar ƙwaƙwalwa". "Dady shi ma fa mutum ne, kenan in ba a san asalinsa ba daga sama ya faɗo ko?". Dariyar takaici ce ta suɓuce musu gabaɗaya, suka kasa ba ta amsa, a wannan daren haka Joriyya ta shiga zuba musu shirme kamar ba ita ba, wani abin ya basu dariya wani kuma haushi suke ji. Sai da dare ya yi sosai sannan Momy ta raka ta ɗakinta ta kwanta, suma suka wuce nasu ɗakin. Haushin karensa ne ya farfaɗo da shi daga suman da ya yi, a hankali ya buɗe idonsa sai dai duhun dare ya sa baya iya ganin komai, cikinsa na ƙugi alamar yunwa yake jiki sosai, ga azabar da hannunsa ke yi masa wanda a yanzu ko motsa shi baya iya yi, ya yi iya yinsa ya tashi zaune ya kasa, gefen cikinsa na yi masa ciwo. A haka ya ƙara komawa ya kwanta tare da rufe idonsa hawaye masu raɗaɗi na zubo masa. Karensa sai kuka yake yana zagaye shi. A haka bacci ya kuma ɗaukar sa, washe gari, cike da ƙarfin hali da jarumta ya samu da ƙyar ya tashi zaune, ya jingina bayansa da jikin ruɓaɓɓen tsohon ginin dake cikin kangon, zuciyarsa ba ƙaramin ɗaci take yi masa ba. Wata irin suka yake jin tana ratsa hannunsa zuwa ƙirjinsa. Ya runtse idanu yana jan dogon numfashi mai azaba. Buɗe idanuwansa ya yi hasken rana ya doki ƙwayar idonsa da sauri ya rufe su, gurin ya yi shiru baka jin motsin komai sai na iskar da take kaɗawa, ya ɗaura hannunsa mara ciwon a kan ƙirjinsa kamar yana tantama ko zuciyar da ke bugawa a ciki tasa ce, ko kuma wata irin halitta ce da ta tsaya masa a ciki. A hankali kamar wanda ya manta yadda ake magana, ya furta kalmomin da shikaɗai yasan abin da yake faɗa. Ji ya yi kamar ana kiransa daga nesa, kiran da ya kasa fahimtar daga ina ne? Ya jingina kansa da bango, idanu a lumshe, yana jin kamar ana jansa zuwa wani guri, guri da bai san shi ba. Karensa ne ya shigo masa da ledar abinci ya ajiye a gabansa, da sauri ya ɗauki ledar abincin da hannunsa mai lafiyar ya fara ci yana zaro ido waje. Bayan ya cinye abincin duka, ya samu da ƙyar ya miƙe tsaye ya fita daga cikin kangon a hankali yake tafiya har ya isa cikin bolar da yake zama ya zauna. Yana kallon jama'ar dake wuce. ***** "Yaya gaskiya ya kamata ka ƙara aure, ka dubi irin arzikin da Allah ya azzurta familyn mu da shi. Sannan a cikin familyn ma kafi kowa arziki mai yawan gaske, amma a ce ka zauna da mace ɗaya? Yaya ka dubi sauran ƴan uwa da basu kai ba, daga mai mata biyu sai mai uku. Haba ai ko dan ka samu yaran da za su iya tallafa maka a nan gaba ka ƙara aure, tunda ita wannan ba haihuwar take yi ba, tunda ta haifi Nihal shekara goma kenan ba ta sake yin ko da ɓari ba ne balle a saka ran sake samun wani rabon daga gare ta". Shiru ya yi yana kallon ta sai da ta gama faɗar abin da ke ranta kafin ya gyara zamansa ya ce "Kina ji ko Mariya? Ni Alhaji Kabiru Umar mai nera, bani da ra'ayin zama da mata biyu, matata ta ishe ni, komai nake so shi take yi mini, ba ta rage ni da komai ba, sannan maganar yara da kike magana idan da rai da rabo zamu iya koma samun wasu yaran, idan ma bamu samu ba Alhamdulillah Nihal ta ishe ni, babu wata mace da zan iya tsayawa da ita balle har in ce mata ina sonta, bani da wannan tunanin a raina, don haka ki daina wannan maganar ba na so, ba don ke ce kika zo mini da zancen nan ba da sai na yi mugun saɓa ma ko waye ba". "Yaya ni gaskiya ba zan haƙura ba, dole ne ka ƙara aure, ni ka bar ni zan nemo maka matar da za ka aur...." "Ke Mariya" ya katseta a tsawace ya ce "Ba na ce ka da in sake jin wannan maganar ba? Zan yi mugun saɓa miki, maza tashi wuce ki bani guri". "Yaya yau ni kake kora saboda kawai na ce ka ƙara aure? Yanzu kafin son farin cikin matarka akan ni ƙanwarka da muke ciki ɗaya? Yaya ni ce fa Mariyarka" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin zubar da ƙwalla. Sai kuma jikinsa ya yi sanyi, ya sassauta murya ya ce "Kina jina Mariya, ba wai bana son farin cikin ki ba ne, ba ni da ra'ayin ƙara aure ne, ki yi haƙuri kin ji". "Ni gaskiya da sake, matar nan ba za ta zauna ita ɗaya a cikin gidan nan ba". Daga haka ta miƙe tsaye ta ɗauki jakarta ta fita daga gidan tana ƙunƙuni. Alhaji ya girgiza kansa, yana mamakin riguma irin ta ƙanwar tasa, yanzu saboda kawai ta ɗaga masa hankali da wannan maganar ya sa ta yi sammakon zuwa gidansa, tashi ya yi nufi ɗakin Maryam da ya ji ta shiru ba ta fito ba. ***** Tun jiya da Jiniyo ya kulle kansa a ɗaki bai fito ba sai yanzu, iyayensa sunyi bugun ƙofar bai fito ba, har sun fara tsorata idan ba wani abu ne ya same sa ba, falo ya fito ya tarar da babu kowa, kai tsaye ya wuce ɗakin Mama. Amanarcool 08163516796 💦 AKWAI SILA 💦 BY AMANARCOOL YOTA ID/021 *SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*. PAGE 17-18 Ya isa ƙofar ɗakin Mama, har zai yi noking sai ya fasa "Me zan ce mata idan na shiga? Taya zan yi mata bayanin abin da na gani jiya?" Ya tambayi kansa, juya wa ya yi ya koma falo ya zauna, dafe kansa da ya yi, yana jin zuciyarsa na yi masa zafi, ƙoƙarin kawar da abin da ya faru jiya yake yi, sai dai tunanin ya ƙi barin zuciyarsa. Mama ta fito falon, ganin Jiniyo zaune a gurin ya sa ta ƙaraso da sauri ta ce "Jiniyo lafiya kuwa? Me yake damunka ne tun jiya ka kulle kanka a ɗaki? Ni da mahaifinka har mun fara tsorata". Ɗago kai ya yi ya kalle ta, ya ce "Mama kin taɓa ganin hallitar mutum gashi dai siffar mutum ce amma zuciyarki ta kasa yarda da cewar mutum ɗin ne?". Kallon sa ta yi da mamaki ta ce "Kamar ya? Ban fahimci hausarka ba?". Shiru ya yi ya kasa ce mata komai, don bai san ta yadda zai yi mata bayani ba. "Jiniyo kodai mafarki ka yi ne?". Ya girgiza kai "Ba mafarki ba ne Mama". "To me yake damunka? Ka yi mini bayani mana". Ya ce "Babu komai Mama kaina ne ke ciwo" Kallonsa ta yi da kyau, tasan akwai abin da yake damunsa ba ciwon kai ba ne, ta ce "To yanzu ka tashi ka je ka watsa ruwa, ka zo ka ci abinci kafin Abbanka ya dawo, bai daɗe da fita ba wani uzuri ne ya fitar da shi. Bai musa mata ba ya miƙe ya nufi ɗakinsa, Mama ta bishi da kallo tana girgiza kai. Tun jiya Dady ya kasa samun nutsuwa, duƙe yake a ɗakinsa hannunsa riƙe da wata tsohuwar takarda da ya ɗauko a ƙasan drawer, rubutun dake ciki ya fara disashewa, kallon takardar yake, kalmomin dake ciki suna suna ƙunar masa zuciya. A hankali ya ce "Ba zan bari tarihi ya maimaita kansa ba, ko da hakan yana nufin zan zama azzalumi a idon ƴata". Mayar da takardar ya yi inda ya ɗakko ta, ya koma saman gadonsa ya zauna. Momy ta shigo ɗakin tun daga bakin ƙofa take kallosa, ƙarasowa ta yi ta zauna "Alhaji me yake damunka ne? Ina lura da kai tun jiya walwalar ka ta ragu, kamar akwai abin da ke damunka". Murmushi ya yi ya ce "Babu komai Hajiya, abubuwa ne suka yi mini yawa, ina Shalele ta tashi ne? Ina fatan dai ta wuce school?". "Alhaji kenan, mu bar zancen tunda baka son in sani. Auta tunda safe ta tashi, yau sai 11 za ta je school". Dady ya gyaɗa kai ya ce "Bari na shirya ina son fita da wuri ne, yau ina da baƙi". Ta ce "To shikenan" tashi ya yi ya fara shiri, Momy sai kallosa take yi, tasan akwai abin da ke damunsa amma ya ce mata babu komai, to kodai lamarin Auta ne ke damunsa haka? Haka dai ta shiga saƙe-saƙe a ranta daga ƙarshe tashi ta yi ta fita zuwa na ta ɗakin. Tana shiga ɗakinta a kwance ta tarar da Joriyya, ta ce "Auta yau kuma ke ce a ɗakin nawa? Hira kika zo yi mini ne? Naga kin kwana biyu baki shigo kin kwanta irin haka ba". Dariya ta yi ta ce "Eh Momy hira zan yi miki". "To shikenan ina sauraren ki". "Momy idan mutum bashi da iyaye, bashi da Momy kenan shi ya haifi kansa ko?" "To za ki fara ko?" Momy ta ce tana kallon ta Joriyya ta kuma cewa "Momy to shi wai ina iyayensa suke ne? Nifa ji nake kamar na san shi" kafin Momy ta yi magana Dady ya shigo ɗakin cikin shirinsa. Ta ce "Yawwa Dady zo ka ji" isa ya yi ya zanuna, ta ce "Dady idan zuciyar mutum nada kyau ana gani? Sannan ana yi mata kwalliya ko? Kuma ana shafa mata mai?". Dady ya nisa yana murmushi ya ce "Shalele idan mutum nada kyakyawar zuciya ana sani, amma taya za a shafa wa zuciya mai?" . Tsaki Momy ta yi ta ce "Idan ka biye mata sai ta ɓata maka lokaci da wannan shirmen nata. "Dady in sha Allah sai na yi karatu mai yawa, kasan wani abu Dady wallahi ba mahaukaci ba ne, kawai an manta da shi ne". "Shalele ki daina yin surutan nan mana, ki yi shiru". "To na yi shirun, amma Dady kaga yadda hannunsa ya yi? Me aka yi masa? Don Allah a siya masa magani, sannan mu tambaye shi ina ne gidan su". Cikin fusata Momy ta ce "Wai ke bakin ki baya yin shiru ne? Alhaji ka tashi ka yi tafiyarka idan ka biye mata makara za ka yi". Joriyya ta ce "Ni dai tambaya ce kawai na yi, amma sai na yi karatu na zama likita in warkar da shi, ko in zama malama in koya masa karatu da yin magana, ko kuma in zama Momynsa in riƙa bashi abinci kullum". Tashi Dady ya yi, tare da yi wa Momy sallama ya fita. Joriyya ta ci gaba da zuba wa Momy surutu kamar wata suda, idan ta saki wata maganar sai Momy ta razana, ita har tana murna daga jiya zuwa yau ƴarta ta fara samun nutsuwa ta rage damuwar nan, amma ta lura abin na nan a ranta har yanzu. ***** "Madam ya dai na jiki shiru tunda kika shigo baki sake fitowa ba?" "Alhaji baku guri na yi ka gana da ƴar uwarka, ka ga ban san abin da yake tafe da ita ba". Tsura mata ido ya yi yana kallon ta, ta ce "Abbin Nihal wannan kallon fa?". "Na so da ƙaunarki ne ƴammatana" ya yi maganar yana jan kumatunta. Dariya ta yi ta ce "Ƴammata kuma? A'a sai dai uwar ƴammata". Ya ce "In ji wa? Ni Alhaji Kabiru Umar mai nera har yanzu kamar ƴammata kike a gurina, gaki nan shar dake, komai naki a kintse, kullum zam-zam nake jinki kamar..." Da sauri ta rufe masa baki tana faɗin "Haba dai ka yi shiru, mu fa ba yara ba ne yanzu da zaka saki baki kafara ɓarin zance, tunda nake da Nihal ai na wuce zama ƴammata" ta ƙarasa maganar da tana dariya. "Waya faɗa miki mu ba yara ba ne? Ai ni a yadda nake jina nafi wani sabon angon more wa" ya faɗa yana rugumota jikinsa. Dariya take yi sosai, tasan halin mijin nata idan abin ya motsa masa komawa yake yi kamar wani yaro, ba ta yi aune ba taga ya kashe wutar ɗakin tare da rufe su da bargo. ****** Jiniyo wanka ya yi, ya shirya jikinsa tsaf ya sake fitowa falo, nan ya tarar da Abbansa zaune, tun daga nesa ya ƙurawa Jiniyo ado kamar yana karantar abin da ke zuciyarsa. "Jiniyo" ya kira sunan sa "Tun jiya kake kulle a ɗaki lafiya dai? Baka san na dawo ba ne?". Murmushin ya ƙe ya yi ya ce "Abba ba na jin daɗi ne, shi ya sa na manta cewar jiya za ka dawo". Mama ta ce "Ƙarya yake yi akwai abin da yake ɓoye wa" . Abba ya ce "Idan ma akwai abin da zai damuwar yarona nasan akan ƴar yayarki ba ce, da ina da ikon da zan cire masa son yarinyar nan da na yi". "Haba Abban Jiniyo ƴar uwarsa ce fa, taya za ka hana shi ya so ta?" . "Yi mini shiru Munira, tun da aka haifi yarinyar nan yake nuna mata so da kulawa, amma da ta buɗa ido ta fara wayo babu wanda take hantara kamar shi, ina kiyaye da ita ko gidan nan ta zo da Mamanta ba ta kula shi, akan me zan so yarona ya fara shiga damuwa akan yarinyar da ba ta san yanayi ba?". Tsam Jiniyo miƙe ya fita daga falon gabaɗaya, ya ja motarsa ya bar gidan. Mama ta ce "Abban Jiniyo bai kamata kana wannan maganar ba, Joriyya fa kamar ƴa take a gurink..." "Bana son jin komai daga bakin ki, ai ba za ki bari a yi magana ba" . Ya katse ta yana gama faɗar hakan tashi ya yi ya ba ta guri. Dady ne tare da baƙin sa suna tattaunawa akan harkar kasuwanci su da tsare-tsaren shigo da kaya daga waje, ɗaya daga cikin su ya ce "Alhaji wannan sabuwar yarjejeniyar da muka ƙulla da su za ta amfane mu sosai". Dady ya gyara zamansa ya ce "Ina so komai ya tafi bisa tsari, ba zan yarda da asara ba, mun sha darasi a baya, yanzu ba zan lamunci a sake maimaita abin da aka yi mana a baya ba". "In sha Allah babu wata matsala da za ta kuma faruwa a yanzu, da mun san akwai matsala ba za mu koma gayyato ka cikin tafiyar ba" Dady ya yi na'am da maganar sosai, suka ƙarasa tattaunawar sannan suka yi masa sallama tare da barin ofis ɗin. Suna fita suka kalli juna suka yi murmushin da suka

Chapter 5 of 9