Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 9
gurin da ya dace da ke ba ne”. Ta lumshe ido ta ce “Shi ma fa mutum ne Dady” Sai zuciyar Dady ta yi wani irin kakkarwa, bai san dalili ba. Motarsu na tsayawa a harabar gida Joriyya ta nufi ciki da flask ɗin zuciyarta cike da wata irin natsuwar da ta kasa bayyana. Dady ya rufe ƙofar mota da ƙarfi, alamar ransa a ɓace yake, ya kasa ɓoye damuwarsa. Momy na tsaye a tsakiyar falo tana jiran dawowarsu, tana ganinsu ta miƙe tana ɗan zaro ido ta ce “Kun kai masa? Da har zan tura yaranka su bi bayanku”. Dady ya ture hularsa gefe ya zauna “Mun kai” ya faɗa a gajiye “ sai dai ni wannan abin ya fara fitowa daga da'irar da za a iya sabawa da shi”. Ta kalle shi da damuwa. “Alhaji ya ake ciki ne? Yarinyar nan ta fara nuna halin da ban taɓa gani ba. Zan sanar da ƴan uwanta, wannan ba ƙaramin abu bane”. “Gara ki sanar da su yafi” Dady ya furta yana lumshe idanu, ciwon ƙafarsa na sake motsawa. Ana haka sai ga Anty Zainab ta kira, ƴar Momy wadda ke aure nan cikin Abuja ɗayar kuma babbar ƴarsu tana can ƙasar waje take da zama tare da mijinta. Momy ta ɗaga wayar tana faɗin “Yanzu nake shirin kiranki” Zainab ta gaishe da Momy tare da tambayar Dady sannan ta ce ”Momy ina rigimammiyarki? Kwana biyu ba ta zo mini ba”. Momy ta ce “Tana nan, yanzu wata sabuwar rigima ce ta ɗakko, abin nata sai gaba yake yi, narasa ya zanyi, wannan yarinya da nake ganin abin da take yi a matsayin shirme, yau ga shi ta fara wani abu da ban yarda da shi ba”. “Wane abu kuma Momy?” Aunty Zainab ta tambaya. Tsaki ta yi ta ce “Jiya ne ta fita da Dadyn ku ta ga wani mahaukaci, shikenan Auta ta saka masa rigimar sai ya siya masa abinci, garin kai masa abincin ya yi ƙoƙarin illata Dadyn ku ɗin, yau ma ta a za rigimar sai an kuma kai masa abinci, har take cewa idan ba a je ba za ta yi kuka, ƙirjinta zai yi mata ciwo, ciwon ta zai tashi, tausayinsa take ji”. Aunty Zainab ta lumshe ido “Wallahi akwai matsala. Wannan ba tausayi ba ne kawai, kamar dai akwai wani abin, anya Momy ƴar nan taki lafiyarta ƙalau?”. Momy ta ce “Shi ya sa na ce zan kira ku domin Joriyya tana buƙatar a kula da ita sosai. Kar fa mu yi sakaci”. Zainab ta ce ”Bari Momy wannan maganar ba ta waya ba ce in sha Allah zan zo gida sai musan abin yi, wannan ai zubar da mutunci ne” suka yi sallama Zainab sai mita take yi. Momy sukaci gaba da tattauna matsalar, Joriyya ko haka ta yini a ɗaki da tunanin wannan mutumin, komai take sai ya faɗo mata a rai. Washegari kasancewar Monday ce ya sa da wuri Joriyya ta shirya aka kai ta school, Joriyya ba ta kula kowa a makarantar sai mutum ɗaya da kusan halinsu ya zo ɗaya wato Safina, tunda ta je take bawa Safina labarin mahaukacin nan har sai da Safina ta fara jin haushinta, yanzu ma zancensa take yi mata “Safina wallahi abincin jiya ya yi masa daɗi. Kin ga yadda yake cin abinci cikin nutsuwa kuwa? Yafi wani mai hankali iya cin abin fa”. Safina ta runtse ido “Don Allah ki saurara mini haka Joriyya, na ji zancen ya fi a ƙirga, tun safe kike yin abu ɗaya, ki barni na huta mana, ko so kike ki cika mini kunnuwa ne? Ki daina ka da a jiki a ce yara damu muna zance maza”. “A’a wallahi ki bari in gama faɗa” Joriyya ta ce tana motsa hannuwanta da annashuwa. “Kin ga yadda yake yi wa idonsa kamar mutum mai jin bacci? Safina ni fa nake ji kamar yana jin...” “Joriyya” Malam Musa ya daka mata tsawa. “A mai da hankali ga karatu” Sai ta yi shiru, amma zuciyarta na ci gaba da tunani, tsawon zaman da ta yi a makaranta ba ta yi komai ba face tunanin shi har aka tashi, ko da ta fito daga class an zo ɗaukarta. Tana shiga gida ko kayan jikinta ba ta cire ba ta kira mai aikin gidan. “Lami kina ji? Ki shirya wani semo na gobe. Gobe ma zamu kai masa”. Lami ta ce “Auta kin ga dai wannan abin…” “Ki yi abin da nace” Joriyya ta katse ta tana haurawa sama. Yau tun daga ma'aikatan gidan har su Momy kowa ya fahimce cewar Joriyya rigima take ji sosai, yanzu ma fitowa ta yi harabar gidan ta tsaya tana kallon kowa. Can ta ce “Kai Baba Sale” daga yanzu idan zan fita kar ka sake tsaya mini a hanya. Na isa na fita na je duk inda nake son zuwa”. Baba Sale ya ƙurawa Joriyya ido kamar zai yi kuka. “Auta ni aikin nan fa…” “Ka bar wannan maganar” ta katse shi, sannan ta kuma ga mai wankin motoci ta ce “Kada ka taɓa flask ɗina dake cikin motar nan saboda yana da muhimmanci”. Haka tabi ma'aikatan gidan ɗaya bayan ɗaya kowa da abin da za ta ce masa. Tunda ya ci abincin jiya, zuciyarsa ta fara motsi da wani sabon abu da bai iya tunawa da shi ba, tun ɗazu yake dubin hanyar da motarsu Joriyya ke bi. Idan yaro ya zo wucewa sai ya watsa mishi tsakuwa ya kau da kai. Wasu yara suka fara tunzura shi “Mahaukaci, mahaukaci mai kwana a bola”. Sai dai ya juya ya kalle su amma ba zai bi su ba. Zuciyarsa ta fara yin wani abu mai kama da tunawa. Ya tsurawa karensa ido, karen da kullum yake kwana kusa da shi. A yau ma karen ya kwanta yana lumshe ido, mahaukacin ya sunkuya ya shafa kansa, ya tsaya cak. Lumshe ido ya yi, numfashinsa ya tsaya na ɗan lokacin. Wani ƙamshi ya ratsa shi. Ƙamshin miyar taushe wadda ta yi masa kama da wata miyar da ya taɓa ci kafin rayuwa ta juya masa baya. Bai tuna lokacin ba, bai tuno wace rayuwa ba ce, amma zuciyarsa ta yi wani irin lugude kamar ana buɗe ƙofa daga ciki. By Amanarcool ✍️ 08163516796 💦 AKWAI SILA 💦 BY AMANARCOOL YOTA ID/O21 *SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*. PAGE 5-6 Ya sake lumshe idanunsa, ƙamshin miyar taushe na ratsa masa hanci kamar ƙamshin wani wuri da ya taɓa rayuwa a ciki. Numfashinsa ya ɗan tsaya, ya doke shi da wani irin firgicin da bai fahimta ba. Hannunsa ya ɗora a ƙirji, zuciyarsa na lugude kamar ana buɗe ƙofa daga duhun da ya daɗe a kulle. Sai ga wasu hotuna kamar inuwa, sautin dariya, ƙamshin girki, murya mai taushi, duk suna ƙoƙarin fitowa, amma suna ɓacewa kafin ya kama su. Ya buɗe idanu da sauri, jijiyoyin kansa na matsewa kamar ana jawo su. Karensa ya matsa daf da shi, yana lumshe ido kamar shima ya fahimci wani abu ya faru. Zuciyar Joriyya ta fara tayar da wata guguwa ta daban, ta fara ɗagawa kowa hankali. A falo ta tsaya tana huci kamar wadda aka ci amanarta. Momy ta ce “Auta ki zo nan” Joriyya ta ce “Momy ku dai ku bar ni ku bar ni kawai!”. Dady ya sauko daga sama a hankali kukan takaici yana barazanar ƙwace masa “Shalele” ya kira ta da murya mai nauyi “Ni fa ba zan yarda ki ɓata mana suna saboda wani mahaukacin da ba mu ma san asalinsa ba, kina ƙaramar yarinya dake da ƙananun shekarunki za ki ɗaga mana hankali!”. Ta juya masa baya ta ce “Dady ba ku gane shi bane! Shi mutum ne kamar kowa!” Wannan kalma ce ta huda ransa. Zuciyarsa ta tashi duka. Ya ɗaga murya fiye da yau da kullum. “Ni ki ke faɗawa haka? Ni? Ni na raine ki ne da wannan dabi'ar? Na koya miki ƙaunar kowa ne? Abin da na sani shi ne ban koya miki mugunta ba, wannan abin da kike yi ƙasƙanci ne na fi ƙarfin wannan zancen da kike jawowa!”. Joriyya ta tsaya cak. Muryarta ta soma rawa. “Kai ka ce ƙasƙanci? Don ina jin tausayin mutum? Don ina son… don ina son…” Numfashinta ya fara birkicewa. Idonta ya cika da hawaye, hannunta ya fara rawa, Momy ta ruga da sauri “Auta ki yi shiru, ki daina” amma hawayen sun zubo. Ciwon ya motsa a ƙirjinta wanda duk gidan ke tsoro, numfashinta ya ɗauke na ɗan lokaci. Dady ya ruɗe. “Ke Hajiya riƙe ta, bari na ɗakko ruwa!” Sai ta zauna a ƙasa tana haki kamar za ta faɗi, da ƙyar suka samu abin ya lafa mata, gashi dare ya fara yi idan ba'a yi sa'a ba sai ciwon ya hanawa kowa bacci a gidan. Washegari. Joriyya ba ta je school ba saboda yanayin jikinta, misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe Anty Zainab ta iso gidan cikin hargagi kamar wadda aka kira ta don kashe gobara, Dady na ƙoƙarin fita suka gaisa, ganin Zainab ta zo ya sa shi komawa ya zauna, zama ta yi bayan sun gaisa ne ta ce “Dady, Momy tun jiya da kika gaya mini maganar nan hankalina ya tashi, wannan ba abin wasa ba ne. Yarinyar nan tana da neman magana, wannan ai zubewar mutunci ne”. Ta yi maganar tana kiran “Joriyya zo nan Joriyya” Fitowa ta yi ta zauna ba walwala. Anty Zainab ta ce “Joriyya dubi yadda kika fara fita hayyacin ki saboda wani mahaukaci da ko sutura ma bai iya sakawa ba, wane irin rashin hankalin ne da ke? Wannan wane irin abu ne kika ɗaukar wa kanki?”. Joriyya ta miƙe da sauri kamar an hura ta, ta ce “Ki daina zolayarsa, ki daina faɗin mummunan abu akansa bana so, bana son ana yi masa haka!”. Anty Zainab ta yi dariya mai ciwo ta ce “Shi fa mahaukaci ne Joriyya, mahau....” Bata gama ba Joriyya ta katse ta da murya mai kaifi “Ki yi shiru, ba zan bar ki ki zage shi ba, ni fa ban taɓa jin kunya ba kamar yanzu da kuke faɗar hakan, ku duka ba ku gane shi bane wai?" Ta yi maganar jikinta na tsuma tamkar za ta fita hayyacinta. Falon ya yi shiru. Idanun Momy sun cika da hawaye. Anty Zainab ta ce “Ke Joriyya, ni kike mayar wa magana haka? Mu gane shi a ina? Waye shi ɗin? Ni anya Joriyya ba iskokai ne suka shige ki ba kuwa? Ko dai ba mutum ba ne mahaukacin?”. Zuru ta yi musu da manyan idanunta, tare da rasa abin da za ta gaya musu, domin su fahimce ta. Fuu ta bar musu falon gaba ɗaya, su duka suka bita da ido har ta haura sama, Dady ya maida kallonsa ga Anty Zainab ya ce “Kin ga dai yadda muke fama da ita, gabaɗaya ta rikice, ita ba abin a yi mata magana ba wannan ciwon nata ya tashi, da haryanzu shi ma ba a san kansa ba, sai lalube kawai da ake yi a dubu. Anty Zainab ta ce “Lallai Dady wannan abin babba ne dole a san matakin da ya kamata a ɗauka, kafin abubuwa su rikice fiye da haka, Momy kin gaya wa Anty Na'ima ne?”. Girgiza kai Momy ta yi ta kasa magana saboda ta fara tsorata da lamarin yarinyarta ta, Dady ya miƙe ya yi musu sallama ya fita, ranar a gida Zainab ta yini su na tattauna lamarin Joriyya, sai bayan la'asar ta bar gidan. Da yamma Jiniyo ya zo gidan da nufin ganin Joriyya kamar yadda ya saba yi da ƙaunar da ta wuce misali, yau saboda halin da Momy ke ciki ya sa ba ta tsaya sunyi hira da shi ba, Joriyya na jin maganar Jiniyo ta fito da sauri, ba don shi ba sai don tana son yi masa zancen mutumin nan, babu sallama ba komai ta ce “Jiniyo” tana tsaye hannaye a ƙugu, “akwai wani mahaukacin wanda nasa muka kai masa abinci jiya ni da Dady, ka ga yadda yake cin abinci? Ka ga yadda idanunsa suka yi?” Da farko Jiniyo ya yi dariya da tunanin soyayya ce kawai. Sai ya gane ba soyayyarsa take faɗa ba, sautin wani mutum daban take faɗa. Nan take ƙirjinsa ya buga da ƙarfi, zuciyarsa ta yi masa nauyi mai girman gaske, ya ce “Ke kina jin zancen da kike yi? Kin manta kina da ni?”. Cikin ko in kula ta ce “Ka yi haƙuri Jiniyo ban da lokacin hakan yanzu”. Wannan kalmar ba ƙaramin ɓata ransa ta yi ba, ya juya cikin fushi ya bar gidan, zuciyarsa na tafasa da kishin wanda bai san ma asalinsa ba. Yau ma kamar kullum Joriyya ta je makaranta, sai dai gabaɗaya yanzu ba ta mai da hankalinta wajan karatu, idan aka zo tambaya game da karatun da aka yi musu sai ta yi shiru tana tunani kamar wadda ta yi nisa da Duniya. Malam Musa ya ce “Joriyya me ke damunki?” Bata ba shi amsa ba ta sunkuyar da kai ta ci gaba da jan biro tana zana layi ba tare da ma’ana ba. Momy ce ke video call, da yarta da take zaune a can Dubai, cikin damuwa ta ce “Na'ima kina jina Joriyya ta shiga wani hali. Wani mahaukaci ne ya shige mata rai, ni ban ma san wace irin alaƙa ce tsakaninsu ba, ni na fara zargin ko dai aljani ne ya fito a suffar mahaukaci, yake son shafarta. Na'ima ta yi shiru na ɗan lokaci cikin jimami ta ce, “Babbar magana, Momy kuna zaman me? Wannan ba abin wasa bane, lamari ne da yakamata a ɗauki matakin gaggawa tun da wuri, kafin al'amarin ya wuce tunani. Amma abin da tsoro a ce rana tsaka kawai ta haɗu da mahaukaci a ce tana shiga shirginsa kamar ta san shi" "Wallahi Na'ima na rasa abin yi, da na ɗauki abin nata wasa, amma yanzu na fuskanci da gaske akwai matsalar da take buƙatar matakin gaggawa" Na’ima ta yi ajiyar zuciya ta ce "Amma Momy ku faɗa min gaskiya wane irin mahaukaci ne haka? Me ya haɗa ta da shi? Waye shi? Ya aka ? Yaya ma take jin shi?”. Momy ta jingina da kujera, hannunta ɗaya na riƙe da wayar, ɗayan kuma tana goge zufa duk da sanyin AC dake ɗakin, muryarta ta yi ƙasa-ƙasa kamar wadda aka sare wa zuciya ta ce "Wallahi Na’ima tun jiya hankalina bai tsaya ba. Joriyya ta canza, ina jin tsoron kada ta faɗa cikin wani abu da ba zan iya fitar da ita ba” "Kin san mai zai faru, zan duba idan da yiwuwar ki bani ita ta dawo nan gurina mu gani" Momy ɗan waro ido ta ce ta ce “ Kina nufin ta koma wajanki da zama?”. “Eh Momy idan har ba ku samu mafita ba, ina ga a nesan ta da shi, nesantawa sosai yadda za ta daina ganinsa gaba ɗaya mu ga abin da hali zai yi ”. "Mummy gaba ɗaya wannan ba abu ne da za a jira dogon lokaci, ana nazari ko tunanin mafita ba, Joriyya yarinya ce ƙarama, babu yadda za a yi a ce rana tsaka ta tsiri alaƙa da mutum mahaukaci da ba a san daga inda yake ba, idan ya cutar da ita fa?" Momy ta katse ta cikin ruɗewa, “Na’ima ki yi mini shiru! Kar ki kara tsoratar da ni, don tuni tsoro ya ƙara cika zuciyata”. Na’ima ta yi ajiyar zuciya. “To Momy ki nutsu. Mu za mu nemo mafita. Ina da ra’ayi ɗaya kuma ina jin shi ne zai iya tsayar da wannan abu”. Momy ta ɗaga kai duk da ba ta ganinta ta ce “Me ne?” “Ki bar Joriyya ta zo nan wurina. Ki turo min ita Dubai. Ta yi zamanta a nan, sai taci gaba da karatu a nan. A nisanta ta da wannan mutumin kafin lamarin ya yi nisa”. Kalmar ta fito a hankali amma ta huda zuciyar Momy kamar ƙusa mai zafi. Hawaye suka cicciko a idonta. “Na’ima ke kina magana kamar sauƙi ne a raba uwa da yarinya. Yaya zan hana ta ganin iyayenta? Yaya zan bari ta tashi daga nan ta tafi tsakiyar wata ƙasa saboda wani mutum da ba mu san ko waye ba?”. Na’ima ta ɗan yi murmushi mara annuri. “Momy mafita fa ake nema, kada ki manta ba gurin wasu bare za ta zauna ba a gurina ne. Momy ba fatana nake ba yau idan babu ke a Duniya nice zan zama uwa a gare ta, zamanta zai dawo a gurina”. Momy ta kasa magana. Wani abu kamar ƙwallon dutse ya maƙale mata a maƙogwaro. Na’ima ta ci gaba da cewa, “Ki saurare ni Momy wannan yaron da kuke kira mahaukaci ban san waye shi ba, amma wani abu a jikinsa yana jawo hankalin Joriyya fiye da misali. Idan ba ku yanke wannan abin yanzu ba, zai iya kai ta ga wani hali da ya fi wannan nisan”. Momy ta dafe goshinta. Ta tuna yadda Joriyya ta yi kuka har ciwonta ya so tashi, yadda ta mayar wa Zainab magana, yadda idan ta ambaci wannan mahaukacin sai idonta ya cika da wani haske da ba a saba gani ba. Ta runtse idanu, hawaye suka sauka a kumatunta. “Na’ima zan yi tunani. Amma zuciyata na tsoro. Yarinya kamar Joriyya an fara ɓata ta. Ina jin wani abu zai faru da ita, amma ban san me ba”. Cikin tausayi Na’ima ta ce “Momy ki kwantar da hankalinki. Idan Nazir ya dawo zan gaya masa komai, idan kun amince sai mu ɗakkota, ba don mu raba ta da ku ba sai don a ceci hankalinta”ci gaba da tattaunawa suka yi. Suna gama magana Momy ta kashe wayar tana mai jin idonta ya ɗauki nauyi. Ta jingina da kujera ta saki wani huci mara ƙarfin rai, zuciyarta na bugawa a hankali kamar na mace mai jiran hukunci. Joriyya na zaune a gefen gado ta takure kanta cikin hannaye. Idonta ya kafe gilas ɗin tagar da ke kallon ƙofar gidan su. Tun da suka dawo daga makaranta zuciyarta ke faɗaɗa da wani zafi mara suna, wannan murya, wannan fuska mai datti, wannan idanu da ke rikita mata tunani duk sun mamaye ta, ta yi wani lumshe idanu mai zurfi. Gabanta na faɗuwa kamar tana jin shi a wajan. “Me yasa nake jin shi kamar na san shi?” ta furta cikin ƙasa-ƙasa da murya kamar wadda zuciyarta ke ƙoƙarin tuna abu mai nisa. Momy na jin ƙarar shigowar motar Dady daga waje zuciyarta ta ƙara harzuƙa da sabon tashin hankali. Ta san dole ta yi masa bayani. Dole su zauna su yanke hukunci. Zuciyarta ta yi nauyi, saboda duk hanyar da take gani duk akwai ciwo. Sai ta dafe ƙirjinta ta furta a hankali “Ya Allah Ka tsare Auta.” Amanarcool ✍️ 08163516796 https://chat.whatsapp.com/FQae3SgaQbTKcN3EMxobzQ?mode=wwt 💦 AKWAI SILA 💦 BY AMANARCOOL YOTA ID/021 *SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*. PAGE 7-8 Momy ta ƙara gyara zamanta a gefen gado, zuciyarta na bugu da sauri kamar za ta fito daga ƙirjinta. Tunanin tura Joriyya ƙasar waje ya kasance abu ne da ba ta taɓa hango shi ba, balle kuma a irin wannan lokaci, a irin wannan yanayi da yarinyar ta shiga. Da sallama Dady ya shigo ɗakin ya tsaya a bakin ƙofa yana kallonta, fuskarsa ɗauke da damuwa, sai dai yana ƙoƙarin ɓoye ta saboda jarumtaka irin ta namiji. Cikin sanyi murya ya ce "Kin yi waya da Na’ima ko?". Ta duƙar da kai ƙasa "Eh na yi" ta faɗa tare da yi masa sannu da zuwa. Zama ya yi a gefen gado, yana amsa sannun da zuwan da ta yi masa, kafin ya ce "To me ta ce miki? Shafa lamarin Shalele ya fara bani tsoro, an ya mahaukacin nan mutum ne?". Momy ta ja numfashi a hankali ta ce, "Haka Na'ima ta faɗa, sannan ta ce idan har ba mu samu mafita ba a tura Joriyya can gurinta ta zauna, ta yi karatunta a can, ta samu nisan da zai raba ta da wannan mutumin". Dady ya lumshe idanu, muryarsa ta sauya, ta yi sanyi ba kamar yadda yake ihu da hargagi akan lamarin ba. "Wato a ce mun kasa magance matsalar ƴar mu har sai mun tura ta wani gari?". Momy ta ce "Alhaji ka dubi Joriyya yanzu kamar ba ita ce yarinyar da muka raina ba. Tana cikin yanayin da bamu san inda ta dosa ba, bamu san me ye maƙasudin sa ba". Shiru ya yi ƙijinsa na yi masa zafi. "Kana ganin jiya yadda ta soma numfashi. Idonta ya rufe, ta soma irin wannan hucin na ciwo, kar ka manta likita ya ce mana damuwarta tana iya tayar mata da wannan ciwon, ciwon da muka kasa gane kansa". Dady ya saki ajiyar zuciya "To me kike so ayi?" Ta ce "A tura ta ta yi karatun ta a can har ta gama, nasan a lokacin komai zai fita daga zuciyarta, sannan mun raba ta da wannan mutumin da ba mu san ko waye shi ba cikin ruwan sanyi". Dady ya yi shiru, ya jin gina da bango, ya daɗe jingine da bango zuciyarsa na bugu, kafin ya ce "Zanyi tunani a kai" daga haka ya juya ya bar ɗakin. Bayan sallar isah Joriyya na kwance a falo tana kallon labulaye taga dake motsi a hankali saboda iskar dake kaɗawa. Sai dai ba labulen take gani ba inuwa take gani, murya take ji, wata ƙaramar dariya tana taso mata kamar ta wani da ta sani amma bata san ko a ina ta san dariyar ba. Abin da ya fi tayar mata da hankali shi ne idanun mutumin nan, ta rufe idonta a zuciyarta take "Me yasa nake jin kamar na taɓa ganinsa? Me yasa nake jin baƙin ciki idan na tuna halin da yake ciki?". Shiru ta yi ta kasa samun amsar tambayarta, lokaci ɗaya ta ji tana son zuwa ta duba wannan mahaukacin "Ko a wane hali yake? Ko ya ci abinci? Wata ƙila ma yunwa yake ji" ji ta yi Dady ya kira ta "Shalele ki zo mana". Tashi zaune ta yi, ta tsaya tana kallonsu shi da Momy kamar wadda aka yi wa hukunci ba tare da ta san laifinta ba. Momy ta yi gyaran murya zuciyarta cike da fargaba ta ce "Auta magana za mu yi". Ta ɗan yi murmushi mai "Wace managa Momy?". Dady ya yi ƙasa da murya "Kin san abin da ya faru jiya? Kin ga yadda jikinki ya koma? Ba za mu iya bari ki ci gaba da shiga cikin wannan yanayin ba da ƙananun shekarunki". Momy ta ɗora da faɗin "Auta Na’ima ce ta buƙa ci mu tura ki can Dubai ki zauna tare da ita. Ki yi karatunki a can tare da ƴarta Ummie, idan kika gama karatunki sai ki dawo, ai dai kina son ki yi karatu mai zurfi ko?". Wani abu ne ya yi tsalle cikin zuciyar Joriyya, idonta ya ƙanƙan ce, hannuwata suka fara rawa. "Ni? In tafi? In tafi saboda shi? Don kawai kun ga na damu da shi?". Momy ta ce "Auta ki fahimce mu" "Ba zan tafi ba!" Ta faɗa cikin hanzari Dady ya ɗaga murya. "Ke ba zaki zauna ki saurare mu ba? Wannan abin da kike ji, abin da ya shige miki rai shi muke son nemo miki maganinsa". Idonta ya cika da hawaye, hawayen ɓacin rai da tsoro, kamar wata babba "Dady ku duka baku gane shi bane. Baku gane shi bane!" Ta faɗi maganar da murya mai tsuma zuciya. Dady ya kasa daurewa da

Chapter 2 of 9