Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 9
matarsa shi Maryam, ƴarsa Nihal na zaune a gefen sa, sai hira suke yi cike da farin ciki da annashuwa, knocking ɗin ƙofar da a ka yi ne ya sa suka mayar da hankalinsu a gurin. Mariya ce ƙanwar sa ta shigo tare da wata zanƙaɗediyar mata fara doguwa, ma sha Allah da ita son kowa ƙin wanda yarasa, matar sai karairaya take tana wata rangwaɗa kamar ƴar tsana, kallon wulaƙanci Mariya ta yi wa Hajiya Maryam sannan ta zauna tana gaishe da Yayanta, da ido Maryam tabi ta da kallo kafin ta ce "Mariya ya kike? Ya gida? Ya yara?" amsa mata ta yi a wulaƙance, sannan ta dubi Nihal ta ce "Ke baki iya gaisuwa ba ne? Ko uwar taki ba ta nuna miki muhimmancina ba ne?" Nihal ta ce "Sannu da zuwa Anty" ƙin amsawa ta yi ta maida duban ta ga matar da suka shigo tare ta ce "A'a Anisa ki zauna mana, ya kika yi tsaye? Ki saki jikinki fa". Zama ta yi tana gaishe da Alhaji da Maryam, amsa wa ya yi, a hankali ya kai idonsa ga Anisa kallo ɗaya ya yi mata da sauri ya ɗauke idonsa. Murmushi Mariya ta yi ta ce "Yaya ya gida? Ya harkoki?". "Alhamdulillah Mariya ina zuwa haka kuma?" Ya tambaya yana kallonta. Dariya ta yi ta ce "Gurin bikin wata ƙawar mu ne zamu je, sai hanya ta biyo da mu, da har zamu wuce sai ƙawar nan tawa mai hankali ta ce ai gara mu shigo a sada zumunci". Ya ce "Kun kyauta Allah ya ba da lada" ya yi maganar yana ƙoƙarin miƙewa tsaye ya ce "Mariya bari na shiga ciki ba na jin daɗin jikina ne". Mariya ba haka ta so ba, tana gani ya ja hannun Nihal suka bar falon, haushe ne ya ƙara kama Mariya ta dubi Maryam ta ce ''Wato kinga na shigo da zankaɗeɗiyar mace shi ne kika ɓata fuska ko? Kika yi masa alama da ya bar gurin, to bari ki ji komi baƙin cikin da za ki yi sai wata ta shigo cikin gidan nan, kuma wannan da kike gani in sha Allah ita ce amaryar gidan nan, wadda za ta zo ta haifa mana santalasantalan yara ba kamar ki ba juyar banz...." Ba ta ƙarasa ba Maryam ta tashi ta ba ta gurin. Tsaki Mariya ta yi ta ce "Munafuka da ki tsaya" ta ce "Anisa tashi mu tafi zuwa gidan nan ne yanzu muka fara shi". Fita suka yi daga gidan zuciyar Anisa cike da burin son shigowa gidan. **** Cikin dare Momy ta je ɗakin Joriyya ta same ta a kwance tana kuka, jikinta ya yi sanyi, idonta a kumbure. Momy ta zauna a gefen gado ta dafa kanta ta ce "Autata ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki ba daɗe wa za ki ba za ki dawo, munyi hakan ne don nema miki mafita". Joriyya ta gyaɗa mata kai hawaye na zuba a idonta kamar ruwa ta ce "Momy shi fa? Wane hali zai kasance a ciki? Wa zai kula da shi? Shi baya da kowa? Babu mai sonsa ne?". Momy ta runtse ido, ta ce "Allah zai kula da shi. Kin yi abin da duk wata zuciya mai tausayi za ta yi. Amma yanzu ki kwantar da hankalinki. In sha Allah komai zai tafi daidai, zamu kula da shi mu riƙa bashi abinci" Joriyya ba ta kuma magana ba. Momy ta miƙe a hankali ta koma bakin ƙofa, tsayawa ta yi tana kallon Joriyya da har yanzu jikinta a mace yake, sai shasshekar kuka take yi. "Allah ya tsare mini ke Autata" ta furta kafin ta bar ɗakin. Ɗakin Dady ta wuce da sallama ta tsaya a bakin ƙofa. Amsawa ya yi, ya ce "Shigo" Shiga ta yi Dady na zaune a gefen gado hannunsa riƙe da kansa, tun da ya dawo daga ofis baya cikin nutsuwarsa, abubuwa da yawa na damunsa, ga matsalar Joriyya, ga wani abu mai girma da yake ɓoye a cikin ransa wanda baya fatan fitowarsa. Momy ta sauke ajiyar zuciya. "Alhaji yanzu shikenan gobe Auta za ta yi nesa dani? Gabaɗaya Auta ba ta cikin nutsuwarta, ina jin zafin rabuwar da zanyi da ita". "Na sani Shafa, amma dole ne mu yi wannan tafiyar, ɗazu ma nake sanar da Na'ima batun zuwan mu" ya faɗa yana fitar da iska mai zafi. Sannan ya kuma cewa "Sai dai ina jin kamar akwai abin da zai faru a can wanda ba zai yi mana daɗi ba" Momy ta ce "Alhaji ban fahimce ka ba?". Kafin ya yi magana dim! Ya ji ƙirjinsa ya buga da ƙarfi, nan take ya dafe ƙirji yana fitar da numfashi da sauri. Hankali Momy tashi ya yi ta dafa kafaɗarsa tana kiran sunansa. Amanarcool 08163516796 💦 AKWAI SILA 💦 BY AMANARCOOL YOTA/021 *SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*. PAGE 27-28 Hankali Momy ya tashi sosai, ta riƙe Dady da ƙarfi tana kiran sunansa cikin firgici. "Alhaji me yake faruwa ne? Me kake ji a ƙirjin naka?" Bai yi magana ba, hannunsa na rawa, numfashinsa na fita da ƙyar, gumi na keto masa a goshi. Momy ta fashe da kuka tana jijjigar sa. Da ƙyar ya furta "Shafa ƙirjina" muryarsa na fita a wahale "Alhaji me kake ji a ƙirjin naka? Ko dai in kira direba mu tafi asibiti yanzu?" A hankali ya buɗe idanunsa, ya kalli Momy, laɓɓansa na rawa, ya kama hannunta ya matse da ƙarfi ya ce "Shafa ki kula da kanki da Auta, kar ki yarda da kowa". "Ban gane ba, me kake nufi da wannan maganar?". Numfashi ne ya fara daidaita, ya ce "Babu komai kawai ina faɗa miki ne saboda halin rayuwa" ya faɗa a nutse, ganin ya fara samun nutsuwa ya sa Momy ta ɗakko masa ruwa masu sanyi ya sha. Jingina bayansa ya yi da jikin gadon yana lumshe idonsa. Ta zauna a gefensa tana yi masa sannu. Dare ya fara yi sosai, Mama na zaune a falo kamar mayya, tana riƙe da wayarta sai kiran layin Abba take yi baya shiga, idanunta a kan ƙofar shigowa tana jiran dawowar Abba da tun da ya fita da rana bai dawo ba, zuciyarta ta kasa samun natsuwa saboda bai saba kai dare a waje ba. Ta sauke ajiyar zuciya, ta kalli agogo 12:30 ta sake kallon ƙofar falon "Ya Allah ka dawo min da shi lafiya" ta furta cike da sanyin jiki, ta maida kallonta ga hanyar ɗakin Jiniyo da tun ɗazu da ya shiga bai fito ba, ta yi kiran sa har ta gaji ya yi mata shiru, tunanin abin da ke damunsa take yi da har za ta yi masa magana ya yi banza da ita bayan tana jin motsin sa a ɗakin. Jiniyo kuwa zaune yake saman gadonsa ya jingina da jikin gadon, duhu ya mamaye ɗakin saboda wutar ɗakin da take a kashe, idanunsa a buɗe. Abin da ya ji a bakin Abbansa na yi masa amsa kuwa a kunne, barazanar da ya yi masa tana yawo a zuciyarsa tare hargitsa masa ƙwaƙwalwarsa. Kunna wutar ɗakin ya yi ya miƙe a hankali, ya buɗe ƙofa ya leƙa waje. Mama ya hango zaune a falo ita kaɗai fuskar ta ɗauke da damuwa, ƙarasawa ya yi inda take ya zauna a gefen ta ya ce "Mama lafiya na ganki zaune a nan ke kaɗai a irin wannan lokaci?". Ta ɗago ta kalle shi, ta ce "Abbanka ne bai dawo gida ba har yanzu, gashi sai kiran wayarsa nake yi ba ta shiga, shi ne duk hankalina ya tashi, kasan baya kai dare a waje. Duk in da yake ana idar da sallan isha yake dawowa gida, amma yau gashi har sha biyu ta wuce bai dawo ba". Sai da gabansa ya faɗi, jikinsa ya ɗan soma rawa, yanayinsa ya canza, ya aro jarumta ya ce "To Mama bai gaya miki in da zai je ba?". "Bai sanar dani ba" ta faɗa tana kallon sa, ta lura da rawar da jikinsa ke yi, da yadda fuskarsa ta sauya. "Jiniyo lafiya kuwa? Tukuna ma meyafaru ɗazu naga ka fito daga ɗakin Abbanka hankalinka a tashe?". Ya haɗiye yawu masu ɗaci ya ce "Ba komai Mama, bana jin daɗi ne" sai dai a yadda ya yi maganar za ka san cewar ƙarya ya faɗa. Alamun tsayuwar mota suka ji a waje. Mama ta miƙe tsaye da sauri. Jiniyo ma jikinsa ya ɗauki rawa, buɗe ƙofar falon aka yi da ƙarfi Abba ya shigo, fuskarsa babu walwala, bai kalli kowa ba kai tsaye ya nufi ɗakinsa. "Abban Jiniyo" Mama ta kira shi, tsayawa ya yi cak ba tare daya juyowa ba, ya ce "A gajiye nake, koma meye ki bari sai da safe" yana gama faɗar haka ya shige ɗakinsa ya rufe ƙofa. Mama ta yi tsaye zuciyarta cike da tambayoyi. Ta kalli Jiniyo ta ce "Me yake faruwa ne? Me ke damunsa?". Jiniyo ya ce "Mama nima ban san abin da yake damunsa ba" . "Allah ya kyuta" ta ce tare da barin falon. Jiniyo ma jiki a sanyaye ya koma ɗakinsa. Washe gari kwance yake a cikin kangon yana cikin mawuyacin hali na azaba da rashin jin daɗin rayuwa. Hannunsa ya ƙara canza kamanni, fatar ta ƙara kwarewa, tsokar nan ta ƙara zazzagowa. Idonsa ɗaya ya kumbura sosai kamar zai fashe, nishi yake fitar wa cike da zafin ciwo. Yana ƙoƙarin motsa hannunsa ya kasa saboda zafin da yake ji, zuciyarsa na bugu da sauri, kowane motsi da zai yi ƙara masa azaba yake yi. Ko ina na jikinsa rawa yake yana jin raɗaɗin da bai taɓa jin irinsa ba, ƙunci yake ji mai tsanani a cikin ransa. Ya runtse idonsa yana jan dogon numfashi mai azaba. Ji ya yi kamar ana kiran sa daga nesa, wani sauti ne mai ƙarar gaske yake ji, ji ya yi kamar an riƙe hannunsa ana jan sa zuwa wani guri da bai san ko ina ba ne. A hakikani ya ɗaga idonsa ɗaya mai lafiyar ya kalli ranar da ta fara shigowa ta cikin kangon, lokaci ɗaya ya ji gabansa ya yi mummunar faɗuwa, ya sa hannunsa da ƙyar ya dafe saitin zuciyarsa yana lumshe idonsa. Misalin ƙarfe goma na safe, Joriyya ta kwana da tunanin tafiyar da za su yi, wata irin kewa take ji a ranta, "Yanzu shikenan ba zan sake ganin sa ba? Yau zamu bar ƙasar nan ba tare da na gansa ba? Ina wallahi sai na je yanzu na gan shi kafin mu bar ƙasar sai dai a yanka ni idan na dawo" ta faɗa tana saukowa daga kan gadonta ta fito, babu kowa a falo hakan ya sa da sauri ta fita waje kai tsaye get ta nufa, yau ma kamar kullum security suka fara ƙoƙarin hana ta fita. Nan ta fara yi musu ihu da kukan da ta saba yi a duk lokacin da suka yi ƙoƙarin hanata fita. "Yi haƙuri ki koma ciki, kinga oga baya son fitar nan da kike yi". Tsayawa ta yi a gabansu tana kuka "Ina ruwanku dani? Wallahi idan baku matsa mini ba duk sai na sa Dady ya kore ku, ku matsa mini na wuce, ba zaku takura mini ba ni da gidan ubana!" ta ɗaga musu murya da ƙarfi. Da sauri Dady ya ƙara so gurin yana faɗin "Shalele! Me yasa kike yin haka ne? Ina za ki je ne?" Da sauri ta ƙarasa gareshi tana kuka kamar ranta zai fita ta ce "Dady don Allah zan je in duba shi kafin mu tafi" Dady ya furzar da iska mai zafi, ya lumshe ido yana jin kamar ya yi ihu "Shalele ba inda za ki je, jirgin mu nan da awa ɗaya zai tashi, ina son ki manta shi gabaɗaya". "In manta shi? Dady ya zan manta shi?" Ta rushe da kuka tana girgiza kai. "Dady me yasa ni kaɗai ce nake jin tausayinsa? Ni ce kawai nake zuwa gurinsa ina taimaka masa, don Allah ka bari muyi bankwana" . Momy ta fito da sauri ta tsaya gefe tana kallon ikon Allah, cikin jin haushi ta ce "Za ki zo mu wuce ko sai na tattaka ki a gurin? Mara jin maganar yarinya". Dady ya jata da ƙarfi ya yi ciki da ita, yana jin komai zai zo ƙarshe tun da yau za su bar ƙasar. Ɗakinta ya kai ta ya zaunar da ita yana rarrashin ta, shiru ta yi kamar ta haƙura, ya ce "Kishirya kar mu makara, kinga 11 ne tafiyar mu" ta jinjina masa kai sannan ya bar ɗakin. Momy na ɗaki tana shirya mata kayanta, Joriyya ta fito daga ɗakinta, sulalewa ta yi kamar iska ta fita, cikin sa'a babu wanda ya kula da ita, mai gadi ya shiga ɗaki ya ɗakko rediyonsa, ta fice a gidan kamar walƙiya, gudu ta fara yi kamar wancan karon cikin ƙanƙanin lokaci ta isa gurin, ba ta gan shi a bolar ba ta nufi cikin kangon. Ganin ta ya yi kamar daga sama, ya tsura mata ido yana kallonta, Kuka take yi sosai ganin halin da ya ƙara shiga" ta duƙa nesa da shi kaɗan ta ce "Haka ciwon ya dawo maka?" Bai ce mata komai ba sai idanu da yake binta da su. Ta ce "Kaga suna son raba ni da kai saboda sunga ina jin tausayin ka, yau za su bar ƙasar nan dani, shi ne na zo in ganka kafin su bar ƙasar dani" ta faɗa kukan ta na ƙara tsananta, durƙusa wa ta yi a gabansa. "Yi haƙuri yi haƙuri, ba da don raina ne zan tafi na barka ba, ina jin tausayin ka, yanzu idan na tafi wa zai riƙa baka abinci?". Babu za to taga ya saki wani irin kuka mai firgitarwa da taɓa zuciya, kuka ne ba irin na hauka ba, kuka ne mai cike da ƙunci, kafin ta yi magana ta ga motocin gidansu sun tsaya a bakin titi. Dady ne shi da security ɗinsa da Momy. Dady ya fito cikin hargowa, ya nufi kangon zuciyarsa cike da jin haushi da baƙin ciki. "Shalele!" ya faɗa da ƙarfi. Miƙewa ta yi ta fara kuka tana riƙe ƙoƙarin faɗawa jikin mahaukacin. "Dady ka bar ni da shi don Allah, ka da ku raba mu, ku duba halin da yake ciki, don Allah Dady ka yi haƙur...." Kukan kura Dady ya yi ya damƙe ta saboda ya ga tana ƙoƙarin faɗawa jikin mahaukacin. Momy ta ɗora hannunta akai ta ce "Yau na shiga uku. Auta kina da hankali kuwa?" . Mahaukacin ya miƙa hannunsa yana nishi da ƙyar, idonsa ya cike da wata irin kewa ya ce "Kar ki tafi ki…" ya kasa ƙarasawa saboda kukan da ya kufce masa. Dady ya yi wuf ya ƙara rungume Joriyya yana janta zuwa cikin mota sai waiwayen baya take yi, ya ce "Ki daina kallon baya Shalele ki wuce mu tafi" Momy ta ƙaraso tana kuka, ta kama hannun Joriyya. "Autata ki yi haƙuri ki zo mu tafi ki zo kafin ya cutar dake". "Ni fa taimakonsa nake son yi. Momy Momy kada ku bar shi haka don Allah" Dady ya ɗaga Joriyya sama ya jefa ta cikin mota da hanzari. Ta riƙe gambun motar tana ihu "Kar ku raba mu! Dady don Allah ka bar ni in duba shi, ka bar ni!" Suka shiga motar da sauri driver ya tashi motar ta yi tsalle tana barin kusurwar kangon, Joriyya ta jingina da glas tana bugawa da hannunta tana kuka mai sosa rai. "Dady ya isa, ka tsaya, ka dawo Dady ba haka ake yi ba, ka dawo mu taimaka masa!" Babu wanda ya kuma kulata a motar. Dady na jin zafin zuciyarsa na ƙaruwa. Kai tsaye airport suka nufa. Duk zafin ciwon da yake ji haka ya durƙushe a gurin yana kuka kamar ransa zai fita, karensa ma kuka yake yi yana zagaye shi. Filin jirgin saman Abuja cike yake da hayaniyar jama'a, sai dai a kunnuwan Joriyya ba ta jin wannan hayaniyar sai sautin kukansa da take ji, zuciyarta na duka kamar ana buga gangar yaƙi a cikinta. Tun lokacin da suka bar kangon har zuwa yanzu bakinta bai daina kuka ba. Idanunta sun kumbura, hancinta ya yi ja, muryarta ta dushe saboda kuka, duk da haka ba ta daina gunjin kukan da take yi ba, kalma ɗaya take maimaitawa a ranta "Kar ku raba mu, kar ku raba mu". Dady na riƙe da hannunta yana ja a hankali, sai janye hannun take yi tana turjewa kamar wadda ake ƙoƙarin jefa ta wuta. Dady na jin nauyin da bai taɓa jin makamancin sa ba a zuciyarsa. Ya ci gaba da jan ta cikin nutsuwa da ƙarfin hali. Ta tsaya cak, ta waiwaya tana kallon waje kamar za ta hango shi, shi ɗin da ba ta san sunan shi ba, shi ɗin da ya buɗe mata wani ɓangare a zuciyarta da ta kasa fahimtar komai a kan hakan.Ta dafe ƙirji tana fitar da numfashi mai zafi kamar mara lafiya. "Dady" ta kira cikin raunin da ya karyar zuciya "Me ya sa kuka bar shi haka? Me ya sa kuka ce na tafi yanzu? Dady ba zan iya barin shi a cikin halin ciwo ba, ba zan iya barin shi cikin ƙunci ba, kuna ganin yadda yake kukan neman taimako". Dady ya tsaya, yana kallon ta, ƙoƙarin riƙe kalmomin da ke cunkushe a ƙirjinsa yake yi ka da su fito waje. Ya ce "Shalele na yi alƙawali zan aiko a duba shi. Zan sa a kai shi asibiti, ki kwantar da hankalinki". Ƙara sautin kukanta ta yi, cike da rashin amincewa ta ce "Haka kuka ce jiya. Dady yau har jini na zuba daga hannunsa fa, kuna ganin yadda yake kuka kamar zai mutu. Dady ya kira ni, ya kira ni ya ce kar in tafi..." Ta ƙarasa maganar saboda kukan daya ci ƙarfin ta. Momy ta durƙusa ta rungume "Autata ki daina yin kukan nan haka kada ki jawowa kanki wata matsalar, ki yi haƙuri, ki bar komai a hannun Allah kin ji? Ba daɗe wa za ki yi a can ba, ki yi shiru kinga sai kallon ki ake yi kina kuka. Allah ya tsare mini ke, share hawayen kin ji Auta ta" Joriyya ta kasa daina kukan, ji take kamar an raba ta da babban ɓangare na jikinta. A haka Dady ya ja ta suka shiga cikin jirgin, lokacin da jirginsu ya ɗaga a sararin samaniya. Momy ta tsaya tana kallon sararin da jirgin ya ɓuya a ciki, ta kai hannunta ta rufe bakinta ji take kamar ta zunduma ihu "Ya Allah" ta furta cikin sanyin murya "Allah ka tsare min Autata. Ka sauƙaƙa mata abin da take ji a zuciyarta. Security ya tsaya kusa da ita yana jiran ta, ta girgiza kai cikin rashin kuzari ta ce "Mu tafi, tana jin wani ƙunci a zuciyarta" buɗe mata motar ya yi ta shiga suka bar airport ɗin. Suna isa gida Momy ta ga gidan ya yi mata girma, gabaɗaya ranta a jagule yake, wayarta ta ɗauka ta kira Maman Jiniyo Munira, ɗaga wa ta yi tana faɗin "Anty barka da wannan lokacin, ya kike ya gida? Ina ƴata?". Momy ta nisa cikin rashin jin daɗi ta ce "Alhamdulillah Munira ƴarki ba ta nan ta yi tafiya, ya Jiniyo?". Munira ta ce "Ana school kenan Joriyya sarkin rigima, ina fatan dai rigamar ta ta da sauƙi yanzu?". "Ina fa sauƙi Munira, ba fa school ta je ba, Dadynta ne ya yi tafiya da ita zai kai ta Dubai can gurin ƴar ta zauna, ko za a samu sauƙin wannan hali da ta tsinci kanta a ciki". "Kamar ya Dubai? Ban fahimta ba Anty, yanzu abin har ya kai a bar ƙasar nan da ita ban sani ba? Me ya sa kika ɓoye mini Anty?". Momy ta ce "Ki yi haƙuri Munira a rikice nake, kuma tafiyar ce ta zo a bazata". Maganar ta daki Munira sosai ta ce "To Allah ya sauwwaƙe ya kawo mafita, ya sa hakan shi ne mafita a gare ta". Momy ta amsa da amin, suka ɗan taɓa hira sannan suka yi sallama. Suna ajiye wayar sai ga Jiniyo ya shigo ɗakin Mama, kallonta ya yi ya ce "Mama lafiya naga yanayinki ya canza?" Ya tambaya yana tare da zama a bakin gadon, sanar da shi abin da ke faruwa ta yi. Dim! Ya ji ƙirjinsa ya buga da ƙarfi, kalmar an tafi da Joriyya Dubai ta sa zuciyarsa ta ƙara shiga cikin ƙunci da damuwa, wani irin duhun kishi da baƙin ciki yake jin yana taso masa, wanda ya sa jikinsa ya fara rawa. Tashi ya yi ya bar ɗakin ya koma falo ya tsaya yana kallo ƙasa, ya ce "Yanzu kenan an bar ƙasar nan da ita saboda shi ne? Zan daina ganin ta saboda mahaukaci talaka marar gata?" Ya gyaɗa kai "Wallahi ba zai yiwu ba, ba zai yiwu ba!" Ya maimaita cikin hargagi zuciyarsa na tafarfasa, wani abu da bai saba ji ba ya fara tasowa a ƙirjinsa, sabuwar ƙiyayya da mugunta suka ƙara bijiro masa a zuciya. "Idan ba ni ba to babu wani wallahi" ya furta yana lumshe ido tare da yin murmushi, murmushin da ba shi da alamar alkhairi. Yana kwance a in da ya faɗi yana birgima bayan tashin motar, jikinsa ya yi butu-butu da ƙura, hannunsa ya fashi yana fitar da jini. yara na zagaye da shi suna kallon sa, wasu daga ciki na tsokanar sa hadda jifansa suke yi, bai kulasu ba, yunƙurawa ya yi ya tashi zaune da ƙyar, a hankali ya kalli in da motar tabi, sauke ajiyar zuciya ya yi, wani yaro ne ya jifo masa ƙaton dutse saura kaɗan ya daki idonsa mai ciwon sai Allah ya tsare dutsen ya faɗi a gefe. Miƙewa ya yi tsaye da ƙyar, yana tashi yaran suka fara gudu, bai bi ta kansu ba ya ja jikinsa cike da rashin kuzari ya koma bakin bolar nan ya zauna, raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa yafi na ciwon dake jikinsa nesa ba kusa ba. Ya rufe idonsa da ƙarfi jin yadda cikinsa ke juya masa tsabar yunwar da yake ji. Karensa ne ya zo ya kwanta a gefensa shima kamar ba shi da lafiya. Tsohon nan ya zo ya tsaya nesa da shi, ya ƙare masa kallo, murmushi ya yi ya ce "Kai kam abin ya zo maka da tsanani mai girma, wannan ba komai ba ne" ya ƙarasa maganar da dariya mai ciwo "Shi kuma yana ganin ya yi dabara daya bar ƙasar da ƴarsa, uhum Alhaji Sulaiman kenan ai mutum ba zai taɓa gujewa ƙaddararsa ba, dole ne cin kasuwa da maƙiyi" ya faɗa yana ɓarkewa da wata dariya mai ɗauke da ma'ano ni masu yawa, ya yi gaba yana ci gaba da dariyar. ****** Alhaji Kabiru ya shiga tunani bai san dalilin da ya sa zuciyarsa ta kafe a kan wannan sabon aikin taimako ba. A Duk lokacin da ya tuna da marasa lafiya musamman masu fama da taɓin hankali sai ya ji wani raɗaɗi na musamman a ƙirjinsa, ya kan tuna da amininsa da ya rasu sanadiyyar matsalar taɓin ƙwaƙwalwa. Ya kan ji zuciyarsa na yi masa zafi, kuma tana ƙara jansa zuwa ga aikata duk wani aikin taimakon da ba ya yi farko, ya rasa dalilin hakan, wani lokacin ya kanyi tunanin ko nasihar da Maryam ce ke yi masa ta fara karyar masa da zuciya? Sai dai bai san cewa wannan al'amari na da nasaba da wani abu da ya riga ya faru shekaru aru-aru da suka wuce tsakanin iyalinsa da wani familyn ba. Ya sauke ajiyar zuciya tare da ɗakko wayarsa ya kira Umar PA ɗinsa mutum ne mai amana, wanda ya shafe shekaru goma yana yi masa hidima ba tare da kuskure ba. Bayan sun gaisa, Alhaji Kabiru ya

Chapter 8 of 9