Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 9
TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*. PAGE 11-12 Gudu yake yi da motar kamar zai tashi sama a haka ya ƙarasa gida yana jin zafin zuciyarsa na raguwa, duk da ba iya haka ya so yi masa ba, ko salla babu ya shiga falon gidansu, Mama na zaune taga Jiniyo ya shigo kamar wanda aka tunkoɗo, bai yi mata magana ba ya wuce ɗakinsa, yana shiga ya zauna akan kujera, yana jin me ya sa ma ya gudu bai tsaya ya karya masa ƙafa ba? Tsaki ya yi yana jin tsanar mahaukacin mai tsanani a zuciyarsa. Joriyya na zaune a kan gadonta, tana jin zuciyarta kamar an ɗora mata wani abu mai nauyi, a duk lokacin da ta rufe idanunta sai ta hango yadda mahaukacin ya faɗi, da lokacin da ya miƙa mata hannu, da ajiyar zuciyar da ya sauke. A hankali ta ce "Ya zan tafi? Ya zan bar shi haka? Ya zan tafi ba tare da na san ko zai ci abinci ba?". Kuka ne ya kuma ƙwace mata, kwanciya ta yi ta ci gaba da kukan. Tunda Jiniyo ya bar gurin, yake zaune riƙe da hannunsa da ya fara kumbura, wasu ƙananun jijiyoyi sun fito, fatar hannun ta yi ja sosai. Ya kalli hannun kamar ba nasa ba, ya tsaya yana rawar sanyi da raɗaɗin da ya ke yanka masa tun daga yatsunsa har zuwa kafaɗarsa. Ƙoƙarin tashi yake amma gwiwoyinsa sun kasa ɗaukar nauyinsa, sake buɗe idonsa ya yi kamar wanda ya ga wani abun tsoro. A hankali yake motsa hannun yana ƙoƙarin danne raɗaɗin da yake ji, wata ƙara ce ta suɓuce masa. Ya kalli ƙofar kangon, yana jiran ko zai ga wadda kullum ke zuwar masa da abinci ko murmushi. Sai dai ya ga wayam babu komai sai iskar da ke shigowa tana shigar masa hancinsa tare da tunatar da shi cewa yau shi kaɗai yake cikin Duniyar da bata da suna. Karensa na tsaye sai zagaye shi yake yi yana fitar da harshe. Momy na falo ta ji shirun Joriyya ya yi yawa tunda ta shiga ɗaki ba ta fito ba, tashi ta yi ta shiga ɗakin, kwance ta tarar da ita numfashinta na fita sama-sama, da sauri ta ƙarasa inda take "Auta lafiya? Ina fatan dai ba jikin ba ne?". Cikin fizgar numfashi ta ce "Momy ƙirjina, zuciyata, zan mut..." Ba ta ƙarasa ba jikinta ya fara girgiza idanunta suka birkice nan take jini ya fara zuba ta kunnenta da hancinta, fashewa da kuka Momy ta yi, ta fara jijjigata "Auta Auta ciwon ne ya tashi? Don Allah kar ki mutu Auta, kin ga abin da muke yi miki gudu ko? Shi ya sa ba ma son kina shiga damuwa". Momy ta rikice sosai ganin wannan karon hadda jini ke fita a jikin ƴar ta ta. Wani irin yunƙuri Joriyya ta yi, ta ja numfashi mai haɗe da gurnani daga haka ta yi ɗif. Ihu Momy ta yi ta sauka daga kan gadon ta yi waje da sauri, ɗakinta ta je ta ɗauki wayarta cikin ruɗani ta fara kiran Dady, sai dai wayar ba ta shiga, nan ta ƙara shiga ruɗa ni ta koma ɗakin Joriyya da sauri, tana shiga ɗakin, turus ta yi ta ƙame a bakin ƙofa tana kallon abin mamaki da al'ajabi. Joriyya ta gani zaune kamar babu abin da ya faru da ita, ta yi shiru tana kallon gefe. Cikin sarƙewar murya ta ce "Auta" Ɗago da kai ta yi ta kalli Momy ba ta ce ƙala ba "Auta babu abin da ke damunki ne?" Momy ta yi maganar tana zama kusa da Joriyyar. "Momy" "Na'am Auta" "Ka da ku kai ni gurin Anty Na'ima ba na so, idan kuka kai ni can mutuwa zanyi". "To Auta ki kwantar da hankalinki in sha Allah ba za ki je ba, amma da sharaɗi ɗaya, sai in za ki daina shiga harkar wancan mahaukacin?". Shiru ta yi ba ta amsa ba, daga ƙarshe ta yi kwanciyarta, ganin haka ya sa Momy tashi ta bar ɗakin don ta san ba kulata za ta kuma yi ba. Wasa-wasa mahaukacin nan ya kasa iya tashi. Hannunsa ya kumburi sosai har ya fara sauya launi. Ya matse yatsunsa, yana jin wani irin raɗaɗi mai zafi, ya cusa hannun a ƙirjinsa yana neman sauƙi da sassauci akan zafin ciwon yake ji. Ya jingina da bango yana fitar da numfashi mai zafi kamar mai ciwon daji. A hankali ya fara furta wasu kalaman da shikaɗai ya san me yake faɗa, ya lumshe idanuwa yana jin zuciyarsa na yi masa nauyi fiye da kowane lokaci, hanjin cikinsa sai ƙugi suke yi alamar babu komai a cikin nasa. Sake buɗe ido ya yi ya kalli ƙofar kangon ya sake rufe idonsa, yana son tashi ya je bolar da yake zama amma babu hali. A haka ya koma kada kai ya kwanta cikin mawuyacin hali. Yau lamarin Joriyya ya ƙara tsorata Momy, ya ba ta mamaki matuƙa, ta fara gasgata cewar akwai abin da basu gane ba akan Auta, yarinyar da idan ciwon nan ya tasar mata da ƙyar yake lafawa, sai gashi yau ya kwanta cikin ƙanƙanin lokaci, sannan ya zo da wani sabon salo. Ko da Dady ya dawo ta gaya masa abin da ya faru shima ya tsorata matuƙa. Cikin dare suka je ɗakin Joriyya a kwance suka same ta tana kuka, jikinta ya yi sanyi, idonta a kumbure. Momy ta zauna a gefen gadon ta dafa kanta ta ce "Autata ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, ai na ce miki ba za ki je ko ina ba kina nan tare da mu, dama munyi hakan ne don nema miki mafita amma tunda baki so Shikenan, sai dai idan baki daina wannan damuwar ba, da shiga harkar mutumen can, dole ne ki bar ƙasar nan". Joriyya ta gyaɗa mata kai, hawaye na zuba a idonta kamar ruwa, ta ce "Momy shi fa? Wane hali zai kasance a ciki? Wa zai kula da shi? Shi baya da kowa? Babu mai sonsa ne?". Momy ta runtse ido ta ce "Allah zai kula da shi. Kin yi abin da duk wata zuciya mai tausayi za ta yi. Amma yanzu ki kwantar da hankalinki. In sha Allah komai zai tafi daidai, zamu sa a riƙa kula da shi a bashi abinci ba tare da kin je gurinsa ba". Shiru ta yi ba ta kuma magana ba, ta zubawa Dady ido tana kallonsa. "Dady" "Na'am Shalele" "Mu je yanzu mu kai masa abinci yunwa yake ji". Dim! Ƙirjin Dady ya yi, ya runtse kafin ya ce "Shalele kwanta ki yi bacci da safe sai mu je". Daga haka ya buɗe ƙofa ya bar ɗakin. Momy tasa hannu tana rufe bakinta jin kuka na ƙoƙarin ƙwace mata, ta miƙe a hankali ta koma bakin ƙofa, tsayawa ta yi cak, ta juya ta kalli Joriyya "Allah ya tsareki Autata" ta furta cikin rauni. Ɗakin Dady ta wuce da sallama cikin murya mai raunu ta tsaya a bakin ƙofa Amsawa ya yi ya ce "Shigo" Shiga ta yi yana zaune a gefen gado hannunsa riƙe da kansa, tun da ya dawo daga ofis baya cikin nutsuwarsa, abubuwa da yawa na damunsa, ga matsalar Joriyya, ga wani abu mai girma da yake ɓoye a cikin ransa wanda baya fatan fitowarsa. Momy ta sauke ajiyar zuciya. "Alhaji Joriyya ba ta cikin hayyacinta fa, wannan lamarin ya dame ta sosai". Dady ya lumshe ido, ya ɗauki lokaci kafin ya buɗe su. "Na sani Shafa, amma dole ne mu yi wannan tafiyar matuƙar naga abin yana neman fin ƙarfinmu, wane irin al'amari ne haka? Lokaci ɗaya yarinya ta rikice akan mutumin da kowa ke gudu". "Alhaji kamar akwai abin da ke damunka bayan wannan?" "Ina ma akwai, bari mu gama da wannan matsalar tukuna, shi ne abin da ya fi muhimmanci a yanzu".Ta yi shiru tana kallonsa, yanayin sa ya nuna cewar akwai wani abu mai girma da yake tsoro fiye da komai. A haka shiru ya shiga tsakanin su, haka suka kwanta ko wanne zuciyarsa a cunkushe. Washegari kafin kowa ya fito Joriyya ta fita harabar gidan cikin sauri, idanunta a kumbura, ta kusanci get ɗin gidan security biyu suka taso da hanzari ɗayan ya ce "Baby Joriyya ina zuwa haka?" "Fita zanyi" ta bashi amsa "Ba za ki fita ba, ki yi haƙuri umarni ne daga oga". Ta tsaya gabansu tana rawar sanyi da kuka "Ku matsa ku matsa na wuce!" Ta ɗaga musu muryarta cikin tsiwa da hargagi "Ba za ku takura mini ba, zan je duk inda nake so, ku matsa mini!" Mamaki ne ya cika su, ƙaramar yarinya da ita amma muryarta ta cika da hargowa da tsanani kamar wata babba. "Haba Shalele don Allah ki koma ciki…" "Ku ƙyale ni" ta katse su tana fashewa da kuka, ta fara ture su da ƙaramin jikinta, ta hau ihun da ya karaɗe ko'ina, "Kada ku hana ni, don Allah ku bar ni na gan shi, ba daɗewa zan yi ba yanzu zan dawo". Hankalin security ya tashi sosai. Da sauri ɗayan security ya nufi cikin gidan a bakin ƙofa ya ce karo da Dady ya fito da sauri jin ihun Joriyya, ƙarasawa ya yi yana faɗin "Me ke faruwa ne?" Ganin Joriyya ya yi a tsaye idonta cike da ƙwalla tana neman ɗaukewar numfashi "Shalele" ya kira ta cikin murya mai rauni "Me yasa ki ka fito yanzu? Ina zaki je ne?". Da sauri ta ƙarasa gareshi, ta kama rigarsa tana kuka kamar za ta suma. "Dady don Allah zan je in duba shi, zai mutu da yunwa idan ban je ba!". Dady ya furzar da iska mai zafi, ya lumshe ido "Shalele na ce ba za ki je gurin wancan mutumin ba, ki manta da shi!" "In manta da shi? Dady ya zan manta da shi?" Ta rushe da kuka tana girgiza kai. "Dady shi baya da kowa, ni ce kawai nake zuwa gurinsa ina taimaka masa" Momy da ta fito a guje ta tsaya zuciyarta na yi mata zafi, tana jin kalmomin ƴarta na ƙona mata rai, hana mata fita Dady ya yi ya jata zuwa ciki ya zaunar da ita a ɗakinsa cikin damuwa da rashin sanin abin yi. Yana zaune a kangon nan kamar jiya. Ƙura ta lulluɓe shi, hannunsa ya ƙara kumbura har fatar ta fara tsagewa a gefe, karensa na zagaye da shi yana yi masa kuka da wata irin murya da ba a saba ji ba.Ya ɗaga hannun yana kallonsa kamar an canza masa shi. Hawaye ya gangaro gefen idonsa, ya jingina kansa a kan dutse yana jin zafin ciwon na ratsa shi. Da ƙyar ya iya miƙewa tsaye ya fito ya zauna a cikin bolar da ya saba zama, mutane na wucewa suna kallonsa, sun ga halin da yake ciki amma ba wanda ya tsaya, ba wanda ya yi tunanin me ya samu wannan mahaukacin a hannu? Ba wanda ya damu da ciwon sa. Wasu yara ma jefa masa tsakuwa suka fara yi suna ihu da dariya, wani ƙaton dutse da aka jefo masa ne a hannun ya sa shi sakin ƙara yana ɓoye hannun nasa a baya. Karensa ne ya zo da sauri bakinsa riƙe da leda baƙa, ya ajiye a gaban mahaukacin, da ƙyar ya sa hannunsa mai lafiya ya buɗa ledar wani abinci ne da ya fara lalacewa, cikin rawar jiki ya fara tura wa cikinsa abinci, yana gama ci ya leda a gefensa da kingin ruwa a ciki ya ɗauka ya shanye, nan take cikinsa ya ƙulle ya fara murƙusu a gurin. Joriyya na zaune a falo ta yi shiru kamar wadda ta amince da duka umarnin da aka gindaya mata, sai dai shirun na rigima ne, sulalewa ta yi kamar iska ta fita daga falon ta ɓoye cikin fulawowi, sai da ta fake idon security, mai gadi ya shiga banɗaki tabi ta ƙaramar ƙofa ta bar gidan. Ta fara gudu saman titi kamar za ta tashi sama. Jikinta sai rawa yake yi, duk nisan tafiyar nan Joriya ba ta ganta ba cikin ƙanƙanin lokaci kamar walƙiya ta isa bakin bolar, jin motsi ya sa shi ɗagowa. Joriyya ya gani tsaye tana kuka tana magana "Na zo, na zo, gani na zo, me ya sa meka a hannu?" ta durƙusa gabansa ta kama hannunsa, ta ji da zafi kamar wuta, ta yi ajiyar zuciya mai tsami, cikin kuka ta ce "Yi haƙuri yi haƙuri, me ya sa meka a hannu? Garin yaya ka ji ciwo haka?" ta faɗa hawaye na bin fuskarta. Ya saki wani irin kuka na manya, ba irin na hauka ba, kuka ne mai cike da ƙunci yaron da ya rasa komai, kafin ta yi magana ta ga motocin gidansu sun tsaya a bakin titin. Dady ne shi da security ɗinsa, Dady ya fito cikin hargowa, ya nufi gurin zuciyarsa cike da jin haushi da baƙin ciki. "Shalele!" Miƙewa ta yi ta fara kuka "Dady ka bar ni da shi don Allah ka bar ni ka duba hannunsa!" Mahaukacin ya ja baya yana kuka yana ɗaga hannunsa da ya kumbura sosai. Dady ya kama Joriyya ya cireta da ƙarfi daga gurin "Shalele ki tsaya, ta ya ya ki ka fito daga cikin gidan nan?" Ta riƙe rigarsa tana kuka tana girgiza kai. "Dady kada ka tafi da ni don Allah kada ku raba ni da shi!" Amanarcool ✍️ 08163516796 💦 AKWAI SILA 💦 BY AMANARCOOL YOTA ID/021 *SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*. PAGE 13-14 "Dady kada ka tafi da ni don Allah, kada ku raba ni da shi!" Ta yi maganar cikin gunjin kuka kamar wadda ake ƙoƙarin raba ta da rayuwarta "Dady dubi hannunsa, duba ka gani bai ci abinci ba, Dady a siya masa abinci ya ci kafin mu tafi". Dady ya sauke numfashi mai zafi, zuciyarsa na yi masa zafi kamar an yi masa duka a ƙirji. Ya rasa kalmomin da zai yi amfani da su, gani yake kamar zai fashe idan ya ƙara kallon yadda yarinyarsa ke riƙe shi take yi masa kuka mai tsanani saboda mahaukaci. "Shalele ki tsaya, ki nutsu zan sa a kawo masa abinci yanzu, ki daina yin kukan nan kin san ba lafiya ce dake ba" ta girgiza kai kamar za ta karya wuyanta "Dady ka duba hannunsa, zai mutu, ni ce kaɗai nake zuwa wajensa, ba shi da kowa sai ni" kukan da take yi ya tsananta, ya cika gurin da sautin da ya yi kama da wani abu mai tarwatse zukata. Jama'a suka fara tsaya wa da mamaki, suna kallon ikon Allah, wani dattijo dake gefe ya yi murmushi yana jinjina kansa ya ce "Farawa ce, yanzu ma kuka fara ganin irin wannan abin, saura ɗayan". Mahaukacin yana kallon su cike da tsoro. Ya ja baya yana ƙara riƙe hannunsa, idonsa jajir tamkar mai neman mafita ta ƙarshe. Yana kuka, irin kukan da mutum ke yi idan ya ga zai rasa wani abu na ƙarshe da ya rage masa a Duniya, security biyu suka ƙaraso da sauri suka kama Joriyya a hankali ganin halin da take ciki. "Shalele ki yi haƙuri don Allah ki kwantar da hankali…" "Ku ƙyale ni ku ƙyale ni!" Ta fara ture su, sai dai ƙarfinsu ya rinjaye nata. Dady ya fizgeta daga hannun mahaukacin da ƙarfi. Wata irin ƙara ta yi "Dady don Allah kada ku bar shi haka, ku duba hannunsa, ka duba yadda yake kuka, ku bashi abinci ya ci!" Da hannu ya yi wa yaransa alama da su karɓo masa abinci, da azama ya tsallaka titi ya isa gurin matar nan mai siyar da abinci ya karɓo da ruwa ya kawo masa. Dady ya ce "Kin gani an kawo masa abincin? To zo mu je gida" ya faɗa yana janta zuwa mota, shiga suka yi aka ja motar da ƙarfi suka bar wajan. Joriyya ta jingina kanta da gilas ɗin motar tana kuka mai sosa rai. "Dady ya isa, ka tsaya, ka dawo Dady ba haka ake yi ba, ka dawo mu taimaka masa". Babu wanda ya kuma kulata a motar, Dady na jin zuciyarsa na yi masa zafi da ɗaci, har suka ƙarasa gida kuka take yi, Dady ya fito da ita ya riƙe hannunta zuwa ciki, Momy na zaune a falo hankalinta a tashe. Dady ya shigo riƙe da Joriyya a hannunsa, zaunar da ita ya yi kusa da Momy sai shashekar kuka take yi, "Hajiya ki kula da ita sosai, ka da ki bari ko harabar gida ta kuma fita, ni zan wuce gurin aiki". "In sha Allah zan kula Alhaji, Allah ya kiyaye a dawo lafiya" fita Dady ya yi, Momy ta mayar da hankalinta ga Joriyya ta ce "Auta, ina so ki nutsu, ki gane cewar bai kamata kina bibiyar wannan mutumin ba, ba girmanki ba ne, hakan da kike yi kina zubar mana da mutunc..." ba ta ƙarasa ba Joriyya ta tashi da sauri ta haye sama tana ƙunƙuni. Zauna yake bayan tafiyarsu ya zuba wa hannunsa ido, da ƙyar yake jan numfashinsa, idonsa sun ƙara yin ja saboda azabar ciwo, karensa sai kuka yake yi yana zagaye shi, ya ɗaga kansa ya kai hannunsa zai shafa kan karen ya kasa, saboda ciwon da yake ji. Karen ya matso ya kwanta a gefensa, shiru ya yi kamar mai tunanin wani abu, yara sai tsokanarsa suke yi, babu wanda ya kula a cikinsu. Abincin da aka siyo masa yana ajiye bai taɓa shi, duƙar da kai ƙasa ya yi, yana jin yadda hannunsa ke ci gaba da yi masa zogi da azaba. A hankali ya yunƙura da ƙyar ya nufi cikin kangon da yake zama, kwanciya ya yi a ciki yana fitar da numfashin a wahale. **** Houses no 18 GRA Kano. Katafaren gidane mai tsanani kyau da tsari irin na zamani, harabarsa na da faɗi sosai a ƙalla zai iya daukar motoci sama da goma. Kallo ɗaya za ka yi wa gidan ka gane cewar mai gidan ba ƙaramin mutum ba ne. Alhaji Kabiru Umar mai nera, ɗaya daga cikin manyan attajiran da Kano ta sani kuma take alfahari da shi saboda taimakonsa ga al'umma. Mutum ne wanda kalmarsa ke da ƙima, duk inda sunansa ya shiga ana ja da baya saboda girmansa da kuɗinsa. Kasuwancinsa ya bazu daga cikin Najeriya zuwa ƙasashen waje, yana da masana'antu, gidajen haya, kamfanoni, da kadarori fiye da tunani jama'a. Matarsa ɗaya Hajiya Maryam, mace ce mai kunya, nutsuwa, da tarbiyya, wadda ke da mutunci a idon jama'a da dama. A duk faɗin birnin Kano, idan ka ambaci familyn Alhaji Kabiru, to ka ambaci iyali ne da babu wanda ya san ƙarshen arzikin su. Sai dai duk da wannan yalwar arziki akwai wani abu da ba daidai ba a gidan, abin da tarin dukiyarsu bai isa ya warware musu shi ba. A falon gidan wanda yake ƙyalli, fitillun falon na fitar da wani kalan haske mai ɗaukar hankali. Hajiya Maryam na zaune riƙe da wayarta ta tsura mata ido da alama abu ne mai muhimmanci take kallo a wayar, ta sauke numfashi a hankali "Ya Allah" ta faɗa cikin sanyi murya. Alhaji Kabiru ya shigo cikin falon fuskarsa cike da damuwa, zuciyarsa cunkushe da wani irin tunani mai girma, idan ka duba shi ba za ka iya gane cewar akwai wani abu dake damunsa ba. A waje mutane na yi masa kallon mutum mai cikakkiyar natsuwa, sai dai a cikin zuciyarsa akwai rauni ɗaya da ya gagara warkewa. "Hajiya lafiya dai?" Ya tambaye ta yana ƙoƙarin karɓar wayar hannunta, da sauri ta yi baya da wayar saboda ba ta son ya ga abin da take kallo a wayar, ta ce "Alhaji wai wannan karon wane gari za'a je yin taimakon kamar yadda aka saba?" Ya nisa sannan ya ce "Wannan karon ina son tura wasu daga cikin yarana su je asibitin mahaukata dake garin Abuja da ma sauran wasu asibitocin, idan akwai waƴanda zasu iya warkewa daga matsalar dake damun ƙwaƙwalwarsu, da marasa lafiyar da ke buƙatar taimako duk zan ɗauki nauyin kula da komai har Allah ya basu lafiya daga nan idan ta kama a fita dasu waje ne duk zan yi" Hajiya Maryam ta ce "Ma sha Allah, Allah ya taimaka ya yi jagora, na ji daɗin wannan abin, Allah ya ƙara tsare mini kai Alhajina". Ya amsa da Amin tare da rumgumota jikinsa yana shafa ta "Alhaji a falo muke fa, ka da Nihal ta tarar damu a haka, kasan wayo ne da ita" . Dariya ya yi yana laƙace mata hanci kafin ya miƙar da ita tsaye ya ja ta zuwa bedroom ɗinsa. ***** Dady tunda ya je ofis zaune ya kasa aikin komai, tunani da damuwar halin da Joriyya ke ciki sun hana shi suku ni a zuciyarsa, noking ɗin ƙofa ya ji, sai da ya ɗauki lokaci kafin ya ba da izinin a shigo, ɗaya daga cikin ma'aikatan sa ne, "Sir saƙo ne aka ce in ba ka" ya faɗa tare da miƙa masa wata ƙaramar takarda, har ya juya zai fita Dady ya ce "Waya baka saƙon ka kawo mini?" "Sir ban san shi ba" da hannu Dady ya yi masa alama da ya tafi. A jiye takardar ya yi ba tare da ya duba ta ba, ya ciro wayarsa yana dubawa bayan ya gama duba wayar ne, ya ɗakko takardar ya buɗa, idonsa ya sauka a kan rubutun dake ciki, wata irin zabura ya yi da ƙarfi ya miƙe tsaye, jikinsa ya soma rawa, ya ƙwalalo idanu waje yana sake kallon rubutun. Duk da sanyin Ac dake cikin ofishin bai hana zufa ya fara fira fita daga cikinsa ba, komawa ya yi ya zauna daɓas, yana sauke numfashi, tare da lumshe idanunsa. A hankali ya furta "Ya Allah, waye wannan ɗin? Me yake nufi da wannan takardar?" . Ji ya yi ba zai iya zama a ofis ɗin ba ya miƙe da sauri bai tsaya duba komai a ofis ɗin ba ya ɗauki wayarsa ya fita, ma'aikata sai gaishe shi suke yi, bai kula su ba, tun daga nesa security suka ganshi ya fito kamar baya cikin nutsuwarsa, kafin ya ƙaraso suka buɗe masa mota ya shiga, cikin ba da umarni ya ce "Ku yi sauri ina son in ganni a gida yanzu". Ta motar suka yi kamar walƙiya suka bar kamfanin. Kwance yake a takure cikin kangon, da ƙyar yake fitar da numfashi saboda raɗaɗi da azabar da yake ji, sai juyi yake yana yunƙurin tashi ya kasa saboda ciwo da hannun ke yi masa. Hawaye masu zafi na bin gefen fuskarsa, ya ƙara ɗaga hannun kaɗan ya ɗan juya sai ya ga karensa baya gurin. Joyawar da zai yi sai ya ga mutum tsaye a gurin. Ƙuri ya yi da ido yana kallon Jiniyo da idanunsa suka yi ja, fuskar nan tasa babu alamar imani balle tausayi, kallo ɗaya za ka yi masa kasan tsantasar mugunta da rashin imani ne kwance a kan fuskarsa "Ka ga abin da ka jawo mini ko? A kan ake ƙoƙarin nisanta ni da Joriyya, yadda ka hana mini jin daɗi kai ma ba za ka ji daɗin ba, sannan kai da Joriyya har abada". Ya ƙarasa maganar cike da ihu da hargagi, cikin rashin imani ya sa ƙafarsa ya take masa yatsun ƙafa, wata ƙarar azaba ya saki yana so ya tashi zaune ya kasa, "Ai wallahi baka ga komai ba, ba kai mahaukaci ba ne yanzu zan koya maka hankali. Ka ga yadda hannunka ya fara yi ki? Zan tabbatar

Chapter 4 of 9