Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 9
ƙarfi ya ce "To waye shi? Me kike gani wanda ba mu gani? Wace alaƙa kike tunanin kina da ita da shi?". Ta gyaɗa kai a hankali, idonta cike da hawaye masu tsananin zafi. Cikin rawar murya ta ce "Na san shi ban san dalili ba, amma na san shi. Idan nayi nesa da shi kamar na rasa wani abu mai muhimmanci nake ji". Sai hawayenta suka gangaro. Momy ta rufe baki saboda firgici, Dady ya zaro ido kamar an jefa masa da wuta. "Shalele kina jin abin da kike faɗa? Kina ji kuwa?" Dady ya ce, ba ta tsaya ba ta juya da sauri zuwa sama tana kuka mai ƙarfi tana kuka. A ɗaki ta kwanta tana haki "Me yasa nake jin haka? Me yasa idanuwansa suke biyoni har cikin bacci? Me yasa yake min kama da wani wanda ya....?" Sai kuma ta yi shiru, ta rufe kanta da filo tana dariya mai ciwo hawaye na cigaba da gangaro mata. Momy ta zauna ta ce "Alhaji wannan abu ya wuce hankali, abubuwan da yarinyar nan ke yi bai kamata ace mai shekaru irin nata na yi ba, gabaɗaya ta sauya kamar ba Joriyyata ba". A sanyaye Dady ya ce "Zan san abin da ya kamata muyi, dole ne ta bar ƙasar nan". Jiniyo tunda ya bar gidansu Joriyya zuciyarsa ta koma kamar kwalbar guguwar da ba komai sai hazo, zafi yake ji sosai a cikin ransa, ya kasa zama a gida, ya kasa cin abinci, ya kasa kallon wayarsa. Ya dinga yawo a harabar gida yana jijjiga ƙafafunsa kamar zararre. "Ni Jiniyo niɗin nan ni da tunda aka haifeta nake sonta, na ba ta dukkan wata kulawata duk da rashin kulawar da take nuna mini ban gaza wajan ƙoƙarin ganin na faranta mata ba, shi ne yau za ta soma yi mini maganar wani? Wanin ma mahaukaci? Wannan wawan da ba a san ko sunansa ba, balle asalinsa". Ya ju ya tsaya gaban ƙofa yana huci. Zaune yake a cikin bola kamar kullum, karensa na kwance a gefensa, idanuwansa sun kumbura, yana yawo dasu a hankali kamar yana bin wata murya da shi kaɗai yake jinta, magana ya yi kaɗan muryarsa ba ta fitowa balle a ji me yake faɗa. Sai ya yi murmushin da ya fi kuka taɓa zuciya. Ya lumshe idanu yana shafa kan karensa "Ka gani ko? Duk Duniya bata da armashi sai idanunta, idanunta da suka ce min…" Ya tsaya, yana maimaita kalmomi da ba su fitowa a fili, kamar ba mahaukaci ba. Da sanyi safiya Joriyya ta fito da rigar bacci tana riƙe da hijabi, idonta sunyi ja saboda kuka da rashin bacci, ta samu Momy da Dady a zaune suna shan tea. Kafin su yi magana ta fara yi kai tsaye kamar mai ba da umarni "Ina so a kai masa abinci. Ba zan bari yunwa ta kashe shi ba". Dady ya ɗaga kai da sauri. "Waye kuma kike magana a kansa da safe ko karyawa ba ki yi ba?" "Dady ku daina yi min kamar bani da hankali. Ku daina". Momy ta ɗan matsa kusa da ita ta ce "Auta ki nutsu mana. Yau ba mu da lokacin wannan batun" "Ina da lokaci, ku dai ku bar ni kawai na kai masa". Dady ya daki teburin da hannunsa. "Ba zaki je ba, babu wanda zai sake kaiwa mahaukaci abinci a cikin wannan gida!" Ta tsaya cak, idonta ya kaɗa, zuciyarta ta yi wani irin bugawa. "Zai iya mutuwa idan kuka hana ni kai masa fa, kai wallahi sai na kai masa" tsabar takaici ya sa Dady miƙewa ya haura sama Momy ta maramasa baya suka bar Joriyya tsaye a gurin kamar wata dusa. Da gudu ta wuce kitchen ta ɗauki flask ta fara zuba abinci tana zubawa da sauri. Jikinta sai rawa yake yi. Ta fito da flaks ɗin a hannunta ta yi waje, security na zaune suka ga ta nufi get za ta fita. "Ke Baby Joriyya ina za ki je yanzu? Kuma kin san ba a barin ki fita ke kaɗai". Ɗaya daga cikin su ya yi maganar yana nufarta. Ta ɗaga murya cikin huci ta ce "Ku matsa wallahi sai na fita" Ja baya ya yi saboda sun san muguntar fushin ta. Ta kalli direba tana huci. "Mallam ka ɗakko mota mu tafi" Ya kalle ta yana mamaki, ya tashi jiki ba ƙwari ya fito da mota ya buɗe mata ta shiga sannan ya kunna motar suka bar gidan. Ƙarar tashin motar ta jawo hankalin Dady wanda ke ɗaki.Fitowa ya yi zuwa harabar gidan ya ce "Wace mota ce ta fita yanzu?". Cikin rawar murya mai gadi ya ce "Ranka daɗe Shalele ce ta ce…" "Ta ce me?" Dady ya katse shi yana zazzaro ido. Cikin ladabi mai gadin ya kuma cewa "Ta ce a fito da mota fita za ta yi, da aka yi ƙoƙarin hanata sai ta yi fushi tace dole sai ta fita". Dady ya balbale su da masifa kamar ana zuba masa wuta. "Akan me zaku barta ta fita ba tare da izinina ba? Me ye amfaninku kuma da zaku barta ta fita daga ita sai direba?" Ya yi maganar yana tsare security da ido, haƙuri suka shiga bashi bai tsaya sauraronsu ba ya juya a fusace ya koma ciki. Jiniyo na tsaye a bakin get ɗin gidansu yana shirin fita ya ga motar gidansu Joriyya ta wuce, Dim! Ya ji zuciyarsa ta yi "Me take nema a waje haka da safe? Kuma me yasa aka fito da wannan gudu haka?" Ganin bai da amsa ya sa ba tare da tunani komai ba ya juya cikin sauri ya shiga gida, ya ciro makullin motarsa daga aljihunsa ya shiga ya fi gi motar ya fita kamar iska ya bi bayan su yana jin bugun zuciyarsa kamar ƙarar harbi. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso bolar da mahaukacin ke zama, gurin ya yi shiru iska mai sanyi tana kaɗawa, yana kwance a takure karensa na gefensa. Joriyya ta fito daga mota hannunta riƙe da abinci, yana daga kwance idonsa a rufe kamar an mitsine shi ya buɗe idonsa karaf suka sauka a kanta, tashi ya yi a hankali yana kallonta da murmushi mai ciwo. Ƙarasowa ta yi ta durƙusa a gabansa tana miƙa masa abincin zuciyarta na rawa. Cikin zafin nama Jiniyo ya fito daga motarsa ya ƙaraso inda suke da sauri, ya daka mata tsawa cikin muryar da shi kansa bai san yana da ita ba "Dama tunda naji zuciyata ta buga akan ki na san cewar gurin wannan banzan za ki zo, me za ki cinta a gurin wannan ɗin? Mutum min da ba zai iya banbance fari da baƙi ba, wallahi yau zaki gane kin yi kuskure Joriyya". Yana gama faɗar hakan ya fizge abincin ya wurgar da shi gefe. Abincin ya watse ƙasa. Joriyya ta miƙe da sauri idonta ya canza launi saboda ɓacin rai ta ce "Me ya kawo ka nan? Me ya sa ka biyo ni? A kan me za ka zubar masa da abinci?". Jiniyo ya matsa kusa da ita, jikinsa na rawa saboda kishi da baƙin ciki, ya ce "Ke zan tambaya Joriyya, me yake damunki da kike ƙoƙarin halaka kanki? Ke fa yarinya ce, shekarunki sun yi ƙanƙanta da ki fara bibiyar namiji har inda yake, namijin ma mahaukaci wanda bai san inda ya dosa ba gabaɗaya, wanda ba'a san asalin sa ba balle tushe". Da ƙarfi ta ce "Kada ka sake aibata shi, ina ruwanka da rayuwata ne? Bari ka ji Jiniyo na ji duk da ƙarancin shekaruna ina da hankali, nasan abin da nake yi, kuma wannan da kake gani nafi ganin ƙimarsa a kanka". A gigice mahaukacin ya tashi ya fara yawo yana faɗin wasu kalmomi marasa ma'ana. Karensa ya soma yin ihu yana fitar da harshe waje, Jiniyo ya kalli mahaukacin yana huci ya ce "Ka da ka kuskura ka taɓa ta nafi ka hauka". Mahaukacin ya ƙaraso kusa, ya yi taga-taga kamar zai faɗi, Jiniyo bai tsaya tunanin komai ba ya ɗaga hannu ɗauke sa da wani mugun mari yana faɗin "Wawa kawai". Joriyya ta zaro ido tana kallon abin kamar ba gaskiya ba, gabansa ta je tana huci kamar wata babbar mace ta yi wani irin tsalle ta ɗauke Jiniyo da mari. A firgice ya riƙe kunce yana kallonta yadda take huci kamar wata zakanya, can ya ɗaga hannu zai kai mata duka, da sauri direbanta ya iso gurin ya riƙe Jiniyo. Jiniyo ya ture direban ya ce "Ka barni wallahi ita da wannan banza mahaukacin duk sai na yi maganinsu!". Joriyya ta kuma matsowa tana kuka mai zafi ta ce "Kai ne banza! Kai ne marar hankali! Kuma ka sani wannan yafiye mini kai nesa ba kusa ba". Mahaukacin ya tsaya yana kallonta, idanuwansa suna cike da wani irin haske mai ban tsoro da ba kowa ke iya fassara shi ba. Jiniyo ya yi shiru. Idonsa ya rufe, zuciyarsa ta buga. Yarinyar da ya ɗauka tasa ce, ashe ba tasa ba ce. Amanarcool ✍️ 08163516796 https://chat.whatsapp.com/FQae3SgaQbTKcN3EMxobzQ?mode=wwt 💦 AKWAI SILA 💦 BY AMANARCOOL YOTA ID/021 *SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA 08081012143*. PAGE 9-10 Gurin ya yi shiru na ɗan lokaci, Jiniyo da Joriyya sai huci suke. Jiniyo ya fara ƙoƙarin ƙwace jikinsa ya daki Joriyya direban ya ƙara riƙe shi yana faɗin, "Jiniyo kayi haƙuri, kada ka fara wannan ganganci ka sa ƙaramin abu ya koma babba, duk da tana ƴar uwarka taɓa ta ba zai haifar da ɗa mai ido a tsakaninku ba". Jiniyo ba ya gane abin da ake faɗa saboda zuciyarsa ta rufe, idanunsa sun yi jajir tsabar ɓacin rai. Ya nuna Joriyya da yatsa cikin rawar murya ya ce "Ke Joriyya ke ni kika yi wa haka a matsayina na ɗan uwanki? Ni kika zubar wa da mutunci a gaban wannan dabba? Kika mari ne saboda shi Joriyya?". Matsowa ta yi gabansa kamar wata cikakkiyar budurwar da take jin ta isa daidai take da kowa, cike da raunin murya ta ce "Na mare ka ne saboda ka taɓa shi. Na mare ka ne saboda ka zubar da abincin da na kawo masa. Na mare ka ne saboda na fahimci kana son ganin kukana fiye da farin ciki" Ta ƙarasa maganar cikin hargagi da ɗaga murya kamar wata babbar mace. Jiniyo ya zaro ido "Ni? Ni ke son ganin kina kuka? Joriyya anya baki samu shafuwar aljanu ba kuwa? Anya ke ce? Kalamanki sun girmi shekarunki". Joriyya ta girgiza kai, hawaye suna sauka "Eh kai ɗin, akan me za ka takurawa rayuwata? Kar ka manta ni ba mallakinka bace, ni ba abin da ka ƙirƙiro bane, kana iƙirarin cewar kana son farin cikina, sai gashi yau ka yi mini abin da bazan taɓa mantawa da shi ba, ka bani mamakin da ban taɓa tunani ba". Ta juya tana kallon mahaukacin da ke tsaye gefe yana ɗan karkarwa.Yana kallonta tamkar yaron da aka ɗauke wa abincinsa. Idanuwansa sun cika da ƙura, sai dai duk da haka akwai haske a ciki, haske mai kama da fargaba da wani guntun farin ciki. Jiniyo ya kalle shi da idon ƙiyayya ya ce "Wallahi ka sake matsowa inda take zan…" Kafin ya ƙare maganar, mahaukacin ya yi gaba kamar zai faɗi a gabansu, hannunsa na rawa, babu kalma, babu magana, amma idonsa ya tsaya a kan Joriyya kamar yana son faɗin abu, kamar yana tuna wani abu mai zurfi. Sai kawai ya miƙa mata hannu a hankali tamkar jariri. Jiniyo ya yi tsalle ya ce "Kada ki kuskura ki taɓa hannun sa, Joriyya kada ki taɓa hannun wannan mutumen yana ƙoƙarin shiga tsakaninsu". Kafin ya ƙaraso Joriyya ta riƙe hannun mahaukacin, ji ta yi kamar an jona mata wutar lantarki, shi kuma ya sauke wata ajiyar zuciya mai tsayi, mai zafi, mai kama da kuka da murmushi a lokaci ɗaya, zame hannun shi ya yi a nata ya zube ƙasa, dafe zuciyarsa ya yi yana jin wani nauyi na raguwa a zuciyarsa na tsawon shekaru. Joriyya ta rusuna tana girgiza shi "Ka tashi mana, kayi min magana, kayi min magana"Ta faɗa cikin kuka. Jiniyo ya ƙaraso cikin sauri yana faɗin "Ki matsa gefe, ki matsa ki bar shi". Miƙewa mahaukacin ya yi da ƙyar, ya ja numfashi, ya kalle Jiniyo da idonsa da suka canza launi, muryarsa na fita ƙasa-ƙasa kamar sabuwar murya ya ce "Ka bar ta". Dukkan su suka tsaya. Jiniyo ya ɗan ja da baya, Joriyya ta rufe baki cikin tsoro, karensa kuwa ya soma ihu yana zagaye su tamkar yana kare wani sirri da ba su sani ba. Mahaukacin ya ɗan ɗaga yatsarsa yana kallon Joriyya, idonsa sun rikice, muryarsa ta fara fitowa da wahala yana faɗin "Kar ki tafi…" Kafin ya ƙarasa ya faɗi gurin a some Ihu Joriyya ta kurma "Ku taimaka mana, ku taimaka mana". Direba ya zo da sauri da robar ruwa a hannunsa, ya yayyafa masa a fuska nan take ya sauke a jiyar zuciya yana buɗe idonsa a hankali. Joriyya ta ce wa direban "Ɗaga shi zaune" zaro ido ya yi ya ce "Shalele duka fa yake yi, naje garin ɗaga shi ya shaƙe ni? Shalele ki tashi mu koma gida tunda dai ya tashi". Baƙin ciki da zafin kishi ne suka sa Jiniyo ya tsaya cak babu baki, babu ƙarfi sai kalmar da mahaukacin ya faɗa take dawo masa a kunne "Kar ki tafi…" Ji yake ƙirjinsa ya yi masa wani irin nauyi, mai fushi da tsoro da wata sabuwar fargabar da bai taɓa jin irinta ba suka yi masa dirar mikiya a zuciyarsa. A hankali mahaukacin ya tashi zaune kamar babu abin da ya faru, ya fara wasa da kayan dake baje a gurin da yake tarawa, nan hankalin Joriyya ya kwanta, ganin Jiniyo ya ɓarar da abincin da ta zo masa da shi ne, tasa direba ya tsallaka bakin titi ya karɓo masa biredi. Jiniyo ji ya yi idan ya ce gaba da tsayi a gurin komai zai iya faruwa cikin ƙunar zuciya ya bar wajan, sai dai ya ƙullaci wannan mahaukacin a ransa, mugunta ce take zuwar masa kala-kala da zai yi masa domin huce haushin abin da Joriyya ta yi masa akansa. Direba ya karɓo masa biredin ta miƙa masa ya karɓa cikin rawar jiki ya fara turawa bakinsa kamar wanda ya shekara bai saka komai a cikinsa ba, sai yanzu ta ji natsuwarta ta dawo, ta miƙe a hankali ta ɗauki flask ɗinta ta bar gurin, buɗe mata mota direba ya yi ta shiga, sannan ya shiga ya ja motar suka nufi hanyar komawa gida. A hanya direba sai sauke ajiye zuciya yake yi yana kallon Joriyya a madubi bai ce uffan ba, sai dai yana tunanin kamar yarinyar tana buƙatar addu'a domin abin da take yi ya wuce haddi. Ita kuwa kanta a jingine yake da kujera, idonta a rufe, zuciyarta ɗauke da nauyin abubuwa uku, mahaukacin, Jiniyo, da marin da ta yi masa. Da isar su gida kafin ma direba ya tsaya, aka buɗe ƙofar falon da zai sada ka da cikin gidan da ƙarfi, Daddy ne idanunsa sun rine, ya fito da sauri kamar wanda ya ji labarin an yi masa kisan kai. "Shalele zo nan yanzu". Ta fito daga mota a hankali, jiki a sanyaye kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Momy ta biyo bayan Daddy fuskarta a ɗaure ta ce "Na faɗa maka tun farko Auta yarinya ce mai zafin zuciya, ba kowa ne lokaci ya kamata a riƙa yi mata wasa da dariya ba, damar da aka bata ne ya sa take yin abin da taga dama. Ka ga abin da muke tsoro yana shirin faruwa yanzu, tunda har ta san ta fita da kanta zuwa gurin wancan mahaukacin". Daddy ya tsare Joriyya da idanuwansa masu kaifi "Ina kika je? Waye ya baki izinin fita? Gurin wancan mahaukaci kika je ko? Kin san abin da kika aikata kuwa?". Ta buɗe baki za ta yi magana sai hawayen da ta maƙale suka fara sauka.Ta durƙusa da sauri. "Daddy kayi haƙuri, ban je gurin sharri ba, ban yi abu da nufin cuta ba". Momy ta ɗagota tana jijjigarta kamar za ta ɓallata "Ke kin haukace ne? Gurin mahaukacin ne ba gurin sharri ba? Muna tunanin ke yarinya ce mai hankali sai ga shi…" Sai ta kasa ƙarasa maganar ta juya ga Daddy cikin ƙunar rai ta ce "Abubuwan nan sun yi yawa. Tunda ta kamu da sha’awar tausayin wannan yaron gabaɗaya ta sauya, kamar ba Joriyyata ba, tana yin abubuwan da bai kamata ace mai ƙananun shekaru kamar ta na yi ba". Daddy ya shaƙi iska ya fitar da ƙarfi. "Ba zan bari ta lalace a idona ba, ba zan zuba ido na ga tarbiyyar da muka fara ɗora ta akai na zubewa ba" Ya juya ya kalli Joriyya."Ki yi ƙoƙari ki dawo kan hanyar da ta dace. Ina son ganin hankalinki ya kwanta, zuciyarki ta samu nutsuwa. Dole ne na tashi tsaye akan wannan lamarin, dole ne in yi ƙoƙari wajan ganin na raba ki da zuwa gurin mahaukacin nan". Zuciyarta na yi mata zafi ta ce "Daddy ni ɗin?". "Ke ɗin" ya ce cikin tsawa "Ba zan barki ki lalata rayuwarki ba, ba zan bari ki sake kusantar wancan yaron ba, ba za ki zubar mini da mutunci ba". Ta lumshe ido, zuciyarta na buɗewa, kalmar wancan yaron ta dake ta fiye da komai. Raɓa su ta yi ta shige ciki tana jin zafi sosai a ranta Jiniyo ya shiga falon gidansu ran shi a matuƙar ɓace. Mahaifiyarsa na zaune kallo ɗaya ta yi masa ta san cewa ran shi a ɓace yake. "Lafiya kuwa Jiniyo? Naga ranka a ɓace haka?". Ya tsaya ya kalleta da idon da suka haɗa zafi da ciwo ya ce "Mama Joriyya ta yi mini wulaƙanci, ta tozarta ni saboda wani tangaran da ban san ko ɗan uban waye ba, mahaukacin banza". Hajiya Munira ta ce "Wani kuma? Shi ne ya sa kake ɓacin rai haka kamar wanda ubansa ya mutu?" Jiniyo ya zaro ido zuciyarsa na bugawa kamar ana kaɗa gangar salla "Joriyya ce ta mare ni a kan wani mahaukacin, ta kai masa abinci, ta tsaya masa, ta riƙe hannunsa!". Hajiya Munira ta dafe ƙirjinta tare da jinjina kai a hankali, zuciyarta cike da mamaki da tashin hankali "Subhanallah! Yarinyar nan akwai abin mamaki" ta ce cikin rawar muryar da takaici. Ta kalli ɗan nata gabaɗaya fuska a kumbure ta yi ja saboda marin da ya sha."Jiniyo mari fa? Kana mi ƙaramar yarinyar za ta mare ka? Me ya haɗa ku da har za ta iya ɗaga hannu ta kwaɗa maka mari haka?". Jiniyo ya yi shiru, idanuwansa sun gama bayyana ɓacin ran da yake ciki, zafin marin ba wai a fuska yake ba a zuciya yake, a mutunci "Na rantse Mama" ya ce cikin muryar da ta shaƙu da zafi da fushi, "kamar zuciyata ta fashe lokacin da ta taɓa shi gaba, ta riƙe hannunsa, ta dube ni kamar ban da wani ƙima a idonta rangaɗa mini mari kamar wani ɗanta". Hajiya Munira ta ɗaga kai ta dubi shi cikin murya mai ɗauke da ɓacin rai ta ce "To gaskiya dole a je a tattauna wannan abin Joriyya ta fara shiga wata hanya da ba ta dace da ita ba. Wannan abu bai kamata ba, tun yanzu ne ya kamata a hana ta yin wannan kasadar, yarinya sai ka ce mai shafuwar aljanu?" Ta miƙe tsaye cikin zafin rai, ta ɗauki mayafinta "Mu tafi gidan nasu, ai ni ban san da haka ba sai yanzu, Anty ba ta faɗa mini ba, yarinya ƙarama tana neman tsokanowa mutane rigima". Ta yi maganar tana fita daga falon Jiniyo ya rufa mata baya. Momy na zaune idanunta sun kumbura saboda rashin bacci da tashin hankali. Sallamar ƙanwarta ta ji Hajiya Munira sai Jiniyo dake bayanta fuska a ɗaure kamar matashi da ya sha ƙunci a kasuwa. Momy ta ce "Munira ke ce da safiyar nan? Allah ya sa dai lafiya? Sannu da zuwa". Munira ta zauna fuskarta ɗauke da damuwa suka gaisa kafin ta ce "Na zo ne saboda Joriyya. Akwai abin da ya faru yau tsakaninta da ɗan uwanta kuma abin ya yi girma da yawa". Momy ta lumshe ido, kamar ta san me za a ce. Munira ta kalli Momy kai tsaye ta ce "An samu rashin fahimta tsakanin Joriyya da ɗan uwanta, inda ta kai ga har ta ɗaga hannu ta mare shi, abin bai yi mini daɗi ba sam, a matsayin su na ƴan uwa ban so suka fara samun saɓa ni har haka ba, da na tambaye shi me ya haɗa su? Shi ne yake gaya mini akan wani mahaukaci ne ta mare shi". Momy ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihim raji'un wallahi abin nan ya isheni Munira, yanzu Joriyya ce ta mare Jiniyo?" Ta maida duban ta ga Jiniyon ta ce "Kana zaman me da har za ka bari ta mare ka?" Shiru ya yi ya kasa magana, ta kuma cewa "Ka yi haƙuri Jiniyo, in sha Allah komai zai daidai, ku yi ta addu'a Allah ya raba ta da wannan masifar". "Amma na yi mamaki da jin wannan zance, kuma shi ne baki sanar da ni ba?". Momy ta ce "Ki yi haƙuri a ruɗe nake shi ya sa, tana yin abubuwan da ba ta taɓa yi ba ne, kamar wata mai shafar aljanu. Tausayin wannan mahaukacin ya rikita ta, Na'ima ta ce idan da yiyuwar ta koma gurin ta da zama sai a tura can ɗin, ko Allah zai sa rashin ganinsa ya sa ta daina jin abin da take ji". Jiniyo ya runtse ido yana ɓoye zafin da yake ji, kenan rabuwa zai yi da Joriyya? Nan take ya ji zuciyarsa kamar an ɗaure ta da sarƙa. Bai so ya nuna ba, amma fuskarsa ta riga ta tona asiri halin da yake ciki, nan ya ji ya ƙara tsanar mahaukacin nan tare da alwashin sai ya azabtar da shi tunda shi ne ya yi sanadiyar da Joriyya za ta iya barin ƙasar nan. A mugun hasale Jiniyo ya fita zuciyarsa na zafi kamar wutar da aka kunna ana zuba mata fetur. Matsala ɗaya ce ke damunsa mahaukacin nan da ya ƙwace masa Joriyya, kai tsaye ya nufi gurin mahaukacin da wani irin duhun fushi da muguntar da yake jin sun shige shi lokaci ɗaya, bai tarar da shi a cikin bolar ba, ya tsaya yana waige-waige sai can ya hange shi cikin wani kango dake kusa da bolar. Ya ƙarasa da sauri cikin kangon idonsa sun yi duhu sosai, tsayawa ya yi akansa ya ce "Wai kai ne kake son ɓata mini farin cikina ko?". Mahaukacin ya ɗago kai a hankali, idonsa sunyi haske, muryarsa na fita da wahala ya ce "Kar ki tafi...." Jiniyo ya ji kalmar ta ƙara masa zafin zuciya. Ya yi wani irin tsalle ya ture shi da ƙarfin da bai taɓa zatar yana da shi ba, Mahaukacin ya faɗi hannun sa ya bugu da dutse.Ya saki ƙara kamar ƙaramin yaro. "Idan ka sake ko da kallonta ne sai na ƙwaƙule maka ido, wawan banza daƙiƙi kawai". Ya ƙarasa maganar cikin ihu da hargagi. A hankali mahaukacin ya ɗago da idonsa yana kallon Jiniyo, da ƙyar ya ɗaga hannunsa da ya bugu wanda alamu ke nuna kamar ya yi targaɗe a hannun, ya dafe kansa ya fara ihu, Jiniyo ya tsaya, tsoro ya daki zuciyarsa na ɗan lokaci, cikin mugunta da rashin imani ya kuma sa ƙafarsa ya harbi mahaukacin tare da taka masa hannun da ya bugu, mahaukacin ya saki ƙara mai ƙarfin gaske. Karensa ne ya shigo gurin da gudu ya nufi Jiniyo, cikin zafin nama Jiniyo ya bar gurin, karen ya rufa masa baya, bai yi nasar cimma sa ba ya faɗa motsarsa ya ja ta da gudu ya bar gurin. Amanarcool ✍️ 08163516796 💦 AKWAI SILA 💦 BY AMANARCOOL YOTA ID/021 *SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA

Chapter 3 of 9