Share this page
da ransa baiso hakan ba amma haka ta nace mai tacemai yaje gida wajen matarsa ya huta intanada bukatar sa zata kirashi awaya. Duk ma'aikatan ta na gidan ta basu hutun bacci cos she wanted to be alone kwata kwata bata son hayaniya, dan ganin yadda suke nuna damuwa da itan ma kara mata wani damuwar yakeyi aranta sai tanajin kamar duk wanda ya rabeta sai ta jefashi cikin baqinciki da damuwa. Cikin kankanin lokaci ta tarkata komi da komi daya dangance zach hotunansa da kaya da kyautuka. Valuable items kamar su tsadaddun agogo turarruka da manyan gwalgwalai duk tay parkaging dinsu a box ta rubuta sako ajiki ta aje a dakin uztaz, akan inya dawo yaje ya siyar dasu akasuwa ko nawa ya samu ya raba musu kudin shida su malam liman ko suyi sadaka dashi dan tasan suna da son yin sadaka wa mutane marasa karfii acewar su addininsu ne ya tanadar. She is alwys proud of masu mata aiki agidanta shiyasa take dada ganin su da daraja dan kuwa har murmushi takanyi inta tuno da cewa Allah ya riga ya zaɓa mata nitsatsun mutane masu Addinini ya kewayeta dasu a matsayin ma'aikata. Malam liman duk ya fi uztaz ilimin Addini dan haka yake koyar dashi qur'ani da wasu littafai kowani lokaci inbasu da aikin yi zaka ga sunata bitar karatu. Mai kula da security system dinta kuma christian ne amma shima akwaishi da rike nashi addinin snn mahaifyarsa itace rayuwarsa sam babu ruwansa da neme nemen mata. Its been years suna zamansu a haka agidan wani bin haka kawai zata fito ta zauna tanajin daddadar sautin kirar sallah da malam liman yakeyi a kofar gidanta dan sosai hakan yake sanyaya mata zuciya. She Admire them in All aspect, koda ma ace akwai saɓanin dayake kiftawa a tsakanin su nayau da kullum duk dai baifi a kirga ba. Gidan yadau shiru dake safiyace sosai. Halisa bata dawo back yard inta inda ta tarkata kayan ba harsaida ta hadawa kanta coffe sann ta taho da gallon din kerosine da Lighter ta dawo ta tsaya agaban kayan zuciyarta na bugawa, bata kulashi ba saida ta gama tuttula keron akan kayan tanajin kamar zach din gabaki daya zata kona ba kayan ba. Nannauyar ajiyar zuciyane ya kufce mata snn ta kunna lighter ta jefashi acikin kayan ya kama fuuuuuuuuuu ya fara ci sosai. Haka kawai taji wani abu mai nauyi na zamewa mata daga kan kirji kamar ana narkashi. Hawaye masu sanyi ne suka shiga sauko mata nan ta dauki cup din coffee dinta tana sha ahankli tanata kallon wutar dakeci bal bal ji take aranta kamar zach din ne aciki yake konewa. Waje ta nema jikinta a sanyaye ta zauna akasa tare da matse kanta a tsakanin cinyoyinta cikin wani yanayi na rauni, Addua takeyi da dukkan zuciyarta tana rokon Allah ya cire mata digon soyayyarsa aranta dan burbudinsa dama mata zucyarta yake har yanzu. Tana cikin wann yanayin Taji saukar wani hannu mai bala'in sanyi ya dafata ta baya, a firgit ta dago Da tsananin mamaki suka hade ido da babban kawarta na modelling wato _jasmine tacha_ Da wani irin rauni jasmine ta jawo ta akasa suka rungume juna sosai dukansu sunamasu fashewa da kuka. She was out of the country, modelling for french designers in germany saiga mummunan labarin abunda ya faru da halisa ya isketa. Hakan ya girgiza jasmine tacha bana wasa ba sabida bayan kawayenta biyar din nan banajin akwai wanda take kaunar halisa da gaskiya da kuma amana kamar jasmine dan sun bala'in tsayawa juna ayayin da suka fara career dinsu ta modeling Atare, dan a modeling schl din suka soma cin karo da juna. Duk dama iyayen jasmine billionaires ne amma sosai take daukar halisa mansa kamar yar uwan jini.. They have alot of memories together Suna fahimtar emotions din junansu sosai. Rungume da juna suka sha kukansu har saida ya ishesu snn suka sassauto. Jasmine tafara share ma halisa hawayenta da suke sauka kan fuskarta muryanta a dishe take cewa "queen, my halsy.. are u okay?taja kumanta tace Awnn queens dont cry...cmn wipe ur tears. Halisa tafara murmushi kadan kadan. Jasmine Ta kalle wutar dake cin tay murmushi tace good that u burn that bastard... Kallon juna sukayi halisa tana murmushin jin dadi ganinta,cikin sanyin mura tace tacha, you came for me? Dada goge mata hawaye jasmine tay tace "i have to"..Halsy tace thank u jasmine, ya kike..ya aikin yake tafiya Jasmine bata amsa ba ta jawota gefe tana cewa forget about all that halsy...ni ba tambayarki abunda gayen nan ya miki zanyi ba..just let me deal with him please, i am sure i can make him pay..wallh lokci guda zan ci ubansa. Halisa ta riko hannunta da sauri sanin how dangerous jasmine can be for men, hankli tashe tace noooo..Dan Allah jasmine kar kice zaki masa wani abu..na rokeki kiyi hakuri. Jasmine ta mike tsaye a masife tana cewa cmn halisa, dats crab... akan me baza aci ubansa ba, dont tell me you still love him after all the embrassment and pain he caused you? Shi asuwa tsinken goge tsuliya? Mtswwww. Halisa tace no jasmine, ni walhhi bana son ma nasakejin sunansa akaina, Banason na sake bawa lamarinsa wani attention dina..i just want to forget him Like totally..totally. but inkuka ce zaku daukar min fansa he will surely knw and he wll keep coming after me to destroy my peace. Karki manta izuwa yanzu wata tsinannayar dabba mahaukaciya ta je ta juye masa sirrikan dake boye arayuwata..duk wani digon kazantar dake cikin rayuwata saida yasani. Shiru jasmine tay in shock najin haka sai batace komi sabida sosai ta soma fahimtar inda halisa ta dosa.. Ajiyar zuciya tay ahankli ta dube halisan tanata karantar yanayinta ,ta lura kamar Aranta so takema ta mance da shi a sigar da zai zamo kamar basu taɓa sanin junansu ba. Can ta riko hannayenta cikin nata tace "What ever happen..knw that im alwys with u halisa. cikin sauke nakasashen murmushi halisar ta gyada mata kai ahankli tana sauke ajiyar zuciya mai sanyi Jasmine tace why are u alone.. ina uztaz? Tace.. ya gajine jasmine nacemai yaje gida kawai ya huta..he was with me the whole time kuma fa yanada mata agida. Jasmine Tace its okay Yanzu ki tashi muje gidana cos u cant be alone,zama ke kadai shine sai saki tunani ..see..i wont let u suck urself up in depression ki tashi kawai muje gidana Halisa tanaki tanaso haka jasmine ta jata suka shiga motarta suka wuce gidanta dake cikin anguwar lekki ta layin da manyan mansion din nigerian celebrities dake lagos yake. Its a cool sleeky duplex mai kyaun gaske, kana ganinsa kasan is just one of her past time houses bawai tana rayuwa aciki bane dan tanada gidaje akasashe daban daban Masu kyan gaske. Suna shiga cikin gidan halisa ta nemi waje akan Kujera ta zauna, tacha ta dau wayarta tay odering musu breakfast a online Chicken wings,burgers da salads da mashed potatoes da drinks dan ta riga tasan halissa robert mansa batashan giya da duk wani abu mai bugarwa arayuwarta dan komin baqin cikin dake damunta bata amfani dashi. In 35 minutes Abincin safen su zai iya isowa Halisa tanata danne dannen remote tama rasa wani channel zata kamamusu tsabar bata saba zama haka idle tana kallon tv ba. Jasmine kam tuntuda giyarta na herrnesy xo mai uban tsada tay a wine glass, ta kurba ta kora baqin cikin zach daya cika mata kirji, snn ta fidda tabar marlboro ta kunna tsinke biyu ta miƙawa halisa guda. Da Kamar bazata amsa ba sai can ta karba ta saka abakinta tafara zuka tana fetsar da hayakinshi ahankli. Rabonta da tasha taɓar shima bakaramin jimawa yay ba, but akan data sha giyar ta gwammaci ta sha tabar kawai. Kan kace wani abu wajen ya kaure da hayaki, jasmine ta taho ta zauna agefenta suka fara hira kada kadan suna busa hayaki atare. Tambayoyi take ma halisa akan wanda take zargi game da asirinta datace an tonashi awajen zach. Halisa was still insisting cewa hala matar kawunta ne ko kawuntan ma dakansa. Duk wani bayanin da halisa take mata jinshi kawai takeyi da kunnen basira da kuma nisan tunani.. Batace komi ba har aka kawo musu Abincin suka zauna suna ci,sosai ta cusawa halisa ra'ayin cin abincin sosai hardai tay nasaran sakata taci sosai ta koshi zufa duk ya fetso mata akanta. Bayan sun gama ne jasmine ta kunna musu cool music na shyne ward ta jawota tsakiya suna slow dance a tare, lokacin sosai halisa ta saki ranta tanata dariya mai tsafta bamai tattare da burbushin damuwa ko tunani ba saidai Kallon da Jasmine din take mata shine sam ta kasa ganewa sai chan ta kwace hannunta daga nata taje ta kashe music din ta jawo jasmine dake adan buge dan tasha giyar sosai, tace Hey hey jasmine,..a cikin layi jasmine tace what? Ido ta zuba mata tace why are u looking at me dat way?..meye... Jasmine tay dariya sai can ta sauke ajiyar zuciya tace halisa kina son na fadi miki gaskiya? Gaban Halisa yay mummunan faduwa Tace inaso mana why not .please tell me.. Gyara zama Jasmine tay kafin nan ta dada daukar giyarta ta kurba tace are u sure...cos folks say that when they dont mean it. Halisa tay murmushi mai cike da fargaba batace komiba danta lura kamar da akwai wani abu acikin zuciyar tacha saidai batasan meye ba wanda shine yake sakamata jin faduwar gaba sosai Shiru ne ya ratsa tsakaninsu,banda karar Ac babu abunda ake ji. Agefe kuma Banda kurban giya babu abunda Jasmine takeyi After around like 10 minutes ta sauke ajiyar zuciya ta juyo tana kallon kwayar idanun halisa dake cike da fargaba. Cike da seriousness ayanayin muryanta tafarayi ma halisa tambayoyi gameda kawayenta daya bayan daya kamar wata kwarariyar CID yar bincike. Kan halisa sosai ya kulle tarasa ina jasmine ta dosa da wayannan tambayoyin nata amma nitsuwa yasata kwantar da hanklinta sosai tana amsata dan tanason taji ina zasuje da karshen zancen. Bayan jasmine tagama tambayarta tabita sauke ajiyar xuciya dan zarginta bai kai kan kowa ba sai kan SHEMA'U DA MEENAL.. Dalilinta na farko shine kowa yasan shemau irin munafukan lawyoyin nan ne dat are so ambitous kuma jasmine tasan shema'u da son rayuwar karya ga baqin ciki tun a camp na nysc da sukayi team daya A kaduna. Acewarta hala baqinciki yasaka shemau already ta binciko dark secrets na past din halisa dan ta rabata da samun arzikin zach dan kowa yasan kalar hankli da kudin da gayen yake dashi. Ata bangaren Meenal kuwa cewa tay meenal tafi kowa yin shisshigi wa zach dan ko baison hira haka take janshi da surutai, jasmine tace it is obvious dat agarin hirar makircinta ne ta zazzage masa labarinki dan ta baqantaki tunda itakam kowa yasan tasan komi akanki halisa. Nacewa da jasmine tayi dacewa tafi zargin meenal din ma shiyafi saka ran halisa ya dan baci ta miƙe tsaye tana cewa "ohhh god...ya isa haka jasmine just shut up..nifa nasan kawai dan jininku bai hadu da meenal bane yasaka kikeson lallai ki laka mata wann maganan. Jasmine taki sam, ta cigaba da fidda mata dalilai manya manya da yasa zarginta yafi karfi akan meenal amma sam halisa taki amincewa. A musu musu fada fada suka aje maganan. Jasmine cikin nanata mata tace nide na gaya maki wallahi..kifara bincikar munafukarki acikin kawayenki..if not dat sly shema'u, then its Definately that "BITCH AMINA ALI TALBA". Dan banyarda da wayann mutane biyun nan ba. tsaki halisa taja tana jin saukar maganan wani rambatsau acikin kunnenta da zcyarta. Aranta cewa take It cant be true cos Her best friends will never ever betray her like dat, barin ma meenal..kai No way.. Jasmine bata karace mata komi ba har suka rufe chapter maganan Sede sosai ta bar halisa cikin rikicewar tunani. After a while tajawota sukeje swimming pool suka danyi games masu saka nishadi tanata bata labarin abunda ke faruwa a fashion and modeling industries yanzu. Hakan ya saka halisa samun nishadi wasu labaran abun dariya wasu na abun mamaki Ba karya she had a good time with jasmine, kafin chan sai ga uztaz ya zo. Jasmine acikin kudi ta taso kasancewar babanta billonaire amma sam bata da girman kai Tana ganin uztaz tafara masa murmushi..tace halsy To fa your guiding angel harya biyoki.. Dariya halisa tay. Uztaz Ya gaishe u a ladabce yanamai sanar da ita cewa shemau da meenal duk sunzo nemanta agida yau da safe har sau uku basu same ta ba shine yace bari yazo ya duba musu ita. Jin hakan yasaka suka kalle juna ita da tacha dariyane ya kufcewa halisar me dan uban karfi jin yadda jasmine take cewa ohhh ohh my suspects gang..kode mayu ne suna jina inata miki huduba akansu..to wallh nikam nafi karfinsu Halisa na dariyarta tace Uztaz jirani acan ina zuwa. Yay murmushi yace yess maam snn ya fita. Ajiyar zuciya haliisa tayi Tace ma jasmine See girl i gat to go karsu fara tunanin wani abunebya sameni sufara daga hanklinsu. tana fadin haka ta fito a ruwan ta jawo towel ta rufe jikinta dashi bayan tay drying kanta ta bushe tass snn ta mikawa tacha hannu itama ta fito suka koma can sama cikin luxurious closet dinta tana daga tsaye halisa ta zabi Wani doguwar riga mai kyau aciki, bakine highneck mai three qtr lenght amma very simple babu design ko kadan jikinshi. Sosai ya amsheta ya mata kyau jasmine tay mata kwalliyar dole tana ta mata dariyar ganin har ta dan zube. Bayan sun gama komi Har bakin motar da uztaz yazo dashi jasmine ta rakota suna hira mai ban dariya suna dariyar hauka mai cike da nishadi aciki.. Murmushin uztaz har kasa boyuwa yake ganin Yadda miss jasmine tacha tay kkri a bugu daya ta fuxgo halisa acikin yanayin damuwar datake ciki. Dede zasu rabu suka dan Rungume junansu sosai, akunne cikin sanyin murya halisa tace mata thank u soo much jasmine i love u soo much, ure more than a friend.. kwalla ya cika idanun jasmine ayayin da kwace jikinta anata ahnkli tanata kallon idanunta tace "i love u halsy..the queen of all the Alpha ladies in the world, halisa ta fashe da dariya..itama dariyar tay snn tace and please dnt forget what i told u okay?..Alwys rember that the cruelest betrayal will neva come from ur enemy but a freind.. Halisa batace komi ba ta gyada kanta ahankli tace thank u..i will take care!! Daganan sukayi sallama uztaz ya bude mata gidan baya ta zauna acikin hadadden Rolce royce nata Yabi ya kunna mata Ac tare da kunna mata sautin music me dadi "unstoppable by ava max,Tunda ta suka fara tafiya ta jinginar da kanta akan chair babu abunda take juyawa aranta face maganganun jasmine akan shemau da meenal wani zuciyar na zugata tay wa meenal din wasu yan tambayoyi amma wani zuciyar kuma yana ce mata is better tay shiru sabida zargi zai iya kawo rashin yadda da rikici atsakaninsu. Har sunyi nisa ta bude lumsashun idonta ta dubi uztaz tace." Kiramin meenal awayrka naji inda take saika kaini wajenta. Uztaz yace okay,baiyi wata wata ba ya kirata haka wayar yaci ringing ganin nmbrsa ne yasa meenal taki dauƙa, haka yay ringin kmar me da kyar ta dauka tana jan tsaki,a walkance tace and who is this? Why have u called me kasame halisan ne? Sai ya rasa me zaice kawai ya mikawa halisa wayar tana murmushi tace hello meenal Nice fa nake kiranki. Jin muryan halisa yasa ta mike tsaye ta sake muryanta tanamai cewa oh my god halsy...Wher have u been...i mean wher are u, "are u okay?...cikin yanayin nuna damuwa da ita ta fada. Halisa tace dont worry am fine...am on my way, kina inane nazo na sameki naji ance kunzo gidana keda shema ko? Tace eh..kizo office kawai ina nan zan jiraki.. Halisa tace okay snn ta katse wayar ta mikawa uztaz tare da umartan sa akan yakaita talba grop of companies. Daga ta dayan bangaren kuwa cikin wani private hospital fadilace tazauna akan kujera kirjinta na bugawa sosai tana jiran likita ya fito ya gaya mata sakamakon gwaje gwajen dataje tay dan ta tabbatar da lafiyar kanta kafin ta tsunduma cikin sabuwar rayuwar data zabar makanta nan gaba Dan tunda tay tunani me zurfi akan maganganun da halisa ta gaya mata snn likita ya fahimtar da ita komi ta gane cewa bata bukatar meenal a rayuwarta. Yankewa tay akan is better ta bar aikin ta neme wata rayuwar awani waje inyaso daga baya zataje ta nemi mahaifyarta yafiya. An riga an mata jinyar vagina dinta da hjy zee ta coccokala mata shi da fartsu,amma duk da haka saida tay wasu yan kwaje kwaje sabida tsorata da bayanin da likita ya mata akan cuttutukar da ake kamuwa dasu ta hanyar saduwa barkate batare da kwaroron rubber ba. Izuwa yanzun dai tasan ta kwana da important client dinsu sunfi su 30 dats wanda sukayi asalin sex da ita,wanda suke jin tsoron ciwo suka sata ta shassha musu gabansu kam ma bazata iya kirgasu ba,lesbianism kuma first time dinta kenan da hjy zee. Yaune likitan yace mata ta dawo dan jiya ya riga ya kirata a sabon layinta ya mata nasiha mai shiga jiki akan qarban qaddara da hakuri da halin rayuwa. Zuciyarta kamar zai fashe take zauna harji take kamar numfashinta yana raguwa ta ciki tsabar fargaban abunda zatazo tagani a takardan sakamakon gwajin dan duk wata cuta dat is sexually related saida aka mata gwajinshi. After like 10 min likita ya aika aka kirawota ta shigo cikin office ya nuna mata waje ta zauna tana kallonshi. Calmy shima yake kallonta har saida yaga ta dan nitsu snn ya soma mata nasiha yanamai bata hakuri har saida kalamansa yasata fara hawaye sosai. Ji take Kanta ya mugun daurewa kanta na bugawa sosai amma dai ta daure ganin ya ciro takardan kwajin yana kallo.. Girgiza kansa yayi ahankli snn ya mika mata sakamakon hannunta na rawa ta karba, takai minti uku cikin tsoro jikinta na rawa rawa ta bude takardan ahankli tafara karantawa da dan karfi. Acikin cutuka biyar manya manya da ake kamuwa dasu ta hanyar jiima'i kwata kwata guda biyune kacal babu ajikinta.. wanda take dasu din ta kafe da idanunta dake fidda ruwa sosai yana sauka akan takardan tuni har ya jikashi. babban abunda ya fi tada mata hankli shine dataga wai ta kamu da cuta mai karya garkuwan jiki wato HIV. Sam fadila Batasan sadda takardan ya sulale a hannunta ya fadi kasa ji tayi ta kasa daurewa ta dora hannunta akanta tay wani irin ihu mai tattare da birkitaccen kuka akasa ta fado rigijib cikin rikicewar tunani duk ta rasa inda zata saka kanta nan danan likitar ya sauko ya dauketa aka kaita counselling room shida dayan colleaque dinsa macen sunata danne ta suna bata baki....THIS IS A LONG PAGE 14 readmores, so I HOPE IS ENUF FOR u guys, SAI MUN SAKE HADUWA AND PLEASE AMIN SHARING AGROPS _08060712446_ *SURAYYAHMS* [1/24, 9:13 AM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB...*_ _(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_ #ROMANCE #FICTION #ADULTHOOD #SEXADDICTS #WOMENPOWER BY _SURAYYAHMS_ _08060712446_ Hp palace ⏯️1️⃣2️⃣ Daga cikin private room na HIV counselling unit Wani irin kuka mai karfi fadila takeyi tamkar zata cire ranta doctocin biyu duka sun taru akanta suna rirriketa jikinta yay wani irin zafi sai jujjuya kanta gefe takeyi cikin rikicewar tunani tabi ta runtse idanunta gam gam dasuke fidda dumbin ruwan hawaye masu zafi tay tsamm da jiki jin Wai yau itace take dauke da cutar kanjamau? hakan datake nanatawa aranta yasata saki wani irin kakkarfan numfashi mai tattrre da firgici tabita dora hannu akai idonta a rufe cikin rudani tanamai cewa wayyo Allah na nashiga uku wayyo Kun cuceni kun cuceni Allah ya isa wayyo Allah na shiga uku. Bakaramin tausayi tabawa likitocin ba ganin irin firgicewa da rudewar datayi tanata kuka. Doctor sai Cewa yake malama Fadila kidena cewa kin shiga uku pls kiyi Addua ki furta innalillahi wa inna ilaihi rajiun kidena cewa kin shiga uku babu kyau. Bama jinshi take ba tana cikin yanayin firgici daya gama nakasata aranta tana jin ina ma ace mata mummuman mafarki takeyi ba agaske ba. Izuwa yanzu takai k'ololuwa wjn tashin hankali da firgici, bacin kakkarwa bbu abinda jikinta keyi. Da kyar suka lallameta tay dan shiru, snn dayan docton tahau mata bayanin yadda za'a mata wasu kwaje kwajen co-infections kamar su tuberculosis da wasu kananan infections kmr su oral cancers snn a soma dorata akan maganin HIV na ARV (Anti retro-viral Drugs). Bisaga kwajin da aka mata Viral load dinta ya nuna cewa Da alama cutar ya dan jima ajikinta kimanin tsakanin wata 8 ko shekara daya ganewa ne kawai ba ayi da wuri ba. A kasa kan bare floor Fadila ta zauna dabas kamar wacce ta samu tabin kwakwalwa sai hawaye dake sauko mata yuuu sam yaki daukewa, har iyanzu jin kanta take kamar a mafarki tana ta Allah Allah ta bude idanunta ace mata kawai mafarki take amma ina da alama qaddara ya riga ya riga fata. Sunci kusan mintina sha biyar ahaka suna famar tausasar zuciyarta tare da bata karfin gwiwar amsar rayuwarta ahaka kafin nan da kyar fadila ta iya miƙewa tsaye, tace musu ta gode snn ta kama hanya ta fice a office din tanatafiya ahankli sosai kmr wacce ruwa ya kwasota tana share hawayenta da hannunta dan yadda kasan mutuwa aka mata haka yanayinta ya dawo. Ita kanta Batasan yadda akayi ta isa bakin motar ta ba tsabar batacikin hayyacinta kafafuwanta taji suna rawa dakansu ta dafe jikin motar ta tsaya gabobin jikinta a mugun ragwabe, saida tay tsayuwar mintina biyu masu kyau tana sauke ajiyan zuciya kafin nan ta bude motar ahankli hannunta na rawa ta shiga ta zauna aciki cikin yanayin jimami. Rife motar tay kriff snn ta kunna Ac takai shi can koluluwar karshe sanyi ya shiga busota duk dama batajin wani sassauci ajikinta, Kuka mai karfine ya sake kufce mata ta haɗa kanta kirif da steering motar tanayin kuka a zafafe jin kamar jijijiyoyin zuciyarta zasu tsinke a lkci guda. Tsananin Duhun Baqin ciki tare da radadin ciwon da zucyarta yake mata yasaka ta rasa waye ma zata fara dorawa lefin wannn abun??? Shin Meenal talba ce ,ko ko mahaifiyarta ko ita kanta datayi wa meenal din makahuwar biyayya akan saɓon Allah daya jawo mata wann musibar da bazai taɓa rabuwa da rayuwarta ba. This enuf, is a lifelong mental trauma..Hiv fa, Hiv?hiv of all sicknesses, shin Dukkan wayann tantiran karuwan da sauran mutane da sukeyin karuwanci da son ransu basu kamu da cutar kanjamau ba sai ita da ake tursasata takeyin shi na dole kuma ma bakoyaushe ba? Cewa take ita Metayi wa Allah ..Da karfi taja wani kakkarfan numfashi hummmmm tanajin tsananin zafi na tsaga mata zuciyarta sosai. Wann wata iriyar musiba ce take bbiyar rayuwrsu, shin mutuwar da mahaifinta yay a yayinda yake aikata zina da matar makwbcinsu bai isheta abun kunya a fuskar duniya ba sai kuma ace gata da cutar kanjamau?...ta kara fashewa da kukan sosai tana cewa na shiga uku...na lalace wayyo Allahna pls How is dis fair to me...? Ita Dama can ba wani ilimin Addinin tay ba iyakacinta na sallahne dan ko datazo birni hajy nadia bata kula ta sakata a wani islamiya ba ilimi kawai aka bata na iya handling business sabida ta rika bautawa yarta meenal har iyakar karshen rayuwarta,. Fadila sam bata gama sanin waye Allah ba bare ta gane babin karban qaddara mai kyau ko mara kyau bare har kuma taayi imani dashi,wanda hakan yasata ta fara tunanin hala Allah baiyima rayuwarta hukunci bisa adalci bane ayau da ya jarrabeta da wann cutar. she was soo angry and furious da qaddarar da Allah ya dora mata tanajin kamar ta kashe kanta ta rabu da duniyan nan me gabaki daya.. Kukan fitan rai take tana ganin lallai Ubangijinta baya sonta,iyayenta da meenal kuma sun tsaneta gaba daya sun zalunce rayuwarta da suka sakata ta kamu da wann kazantacen cutar mai cike da kalubale na tsangwama da zubewar mutunci aciki. Tasan inba dan son kudi irinna mahaifyrta ba da bazama ta san meenal ba bare hartakai wann matsayin datake ciki ayanzu. Wani zuciyace ta debeta ta fixge motar a 360 tabar harabar asibitin aguje tahau kan titi tana tukin tanata kuka at same time kwakwalta na buga mata lissafin inda zata soma juye fushin dake kwarara asaman zucyarta.. Direct hanyar talba grop of companies ta nufa zuciyarta na tafasa dan harga Allah bata san mema zataje ta gayawa meenal din ba amma aynxu tafijin tsanarta fiye da komi arayuwarta. Ta shararo tafiya kenan tana daf ta iso motarta ya fara alarming yanamai nuna mata cewa man ta ya kusa ya dauke, a dan dole yasata tay slow down ta lallaba motar ahankli

Chapter 14 of 44