Share this page
tay wani irin karamin kwalliya wanda ya wani irin sauya mata kamanni daga na wanda take cikin damuwa. Wani irin bone straight wig cap mai dan karan tsada ta ciroshi a park dinsa black colour ta kima akanta ta wani irin gyarashi da coiling gels ya zauna mata cif cif ya mata kyau kamar nata ne. Closet dinta data jima bata bude shi ba ta nufa ta dauko wata arniyar cool grey colour palazo da white coller shirt na steve meden me gutun hannu ta saka su ajikinta sann ta bi kan rigar dede kan hadadden kugunta ta dora masa bakin belt na gucci wani irin kyau na daban tayi. Bakin takalmi me tsini da karamin jakarsa na kamfanin gucci ta dauko snn ta feshe jikinta da turaren yara da lattafa masu azaban sanyi ta dauki littafin Dr asim din ta saka ajakarta sann ta fito ta samu uztaz yanakan amsa waya haryanzu bai gama ba. Suna hade ido yace maam we are late doctor nan ne yaketa kira tun dazu.. Agaggauce Tace am here lets go mana. Jakarta ya amsa ya mata jagora har sukakai waje. Daga ganinsu kasan uztaz yana balain ji da halisa a duniyarsa dan kallon yar uwansa na jini yake mata ba ogarsa ba Hadadden jeep wrangler dinta baki daya dace da hadadden shigar datay ya dauko tare da bude mata kofar ta shiga ciki.. Tana zama tace masa Nayi ma meenal alkwarin zanje na sameta idan mun fito daga asibitin wajenta zata kaini. Bai mata musu ba Yace okay maam Horn yay malam liman yazo da gudu ya bude musu motar yanamai daga mata hannu daga windon ta leko snn ta masa murmushi me sanyi. Yana rufe gate din tun basu kara da gaba ba wata farar lexus ta sha gabansu adede hanyar mafitar anguwarsu tun daga cikin motar uztaz ya gane cewa doc khalid ne dan Shide harga Allah bawani burgesa likitan yakeyi ba dan aransa yaga alaman kamar shidinma shishigewa halisan kawai yakeso yay. Juyowa yay ya kalleta snn yace maam I think is the Doctor. Tace okay. Kaje kaji me yake tafe dashi bazan iya sauka kasa dominshi ba Dr khalid ya sauko da rawan jikinshi saiga uztaz nan ya sauko shima atake ya sauya fuska suka gaisa sama sama. Yace I came to check on ur boss you knw she is now my responsibility too. Uztaz yace ahanyar zuwa asibitin muke yanxu sai kaje ka jirata acan. yake dr khalid yay masa gashi babu halin ya rainashi ganinsa fes fes acikin tsadadden suit kamar wani presidentual escort, mimmika wuyarsa yake da wayo wai koda halisan zata dan hangosa ta fito amma uztaz yay masa babakere ya hanasa sakat. Ganin bazai samu shiga ba yace its okay..cant i speak with her? Uztaz baice mai uffan ba ya zura hannunsa a aljihu Wayarsa ya ciro agabansa ya kira layin halisar bugu daya ta dauka tace what wai meya kawosa? Ahankli yace He said he want to talk! Tace badamuwa its okay ina zuwa. Tana fadin hakan ya katse wayar baice masa komi ba harsaida halisan ta gama jan minti biyar dinta snn sauko ta iso. Tun da ta bude motar ya dan hango ta yaji gabaki daya ya rude.. Tsabar maitar mata jikinsa har rawa yakeyi ta ciki duk ya kasa tsayuwa akan kafafunsa idanunsa kamar zasu fadi kasa wajen kallon halittar halisa musmmn ma yau dayaga ta danyi kwalliyar daya fito sosai.. yay nan yay nan dakansa sekace kadangare, sai hangame baki yake yana sauke wasu kananan giggleskamar wanda ake sosamai ramin tsuliya. Tana karasowa uztaz yaja baya ahankli tana dan murmushinta mai aji gamida tafiyarwa tace Hi doctor ??? Kusan a rude Yace khalid..my name is Dr khalid.. Da murmushi ayanayinta tace yes i remember you... ina fatan babu wata matsala Cikin dedeta nitsuwarsa yace no bawani matsala Naga bakizo ba and i was passing by nace bari na dubaki.. Tace dats totful of u amma next time idan zakazo gidana u can call my personal assistant for permission is dat okay? Yace sure. So shall we???nace In ba damuwa i will love to drive with u tunda yau munyi latti se mufara tattaunawar mu tun ahanya ko. Da kamar bazata amince ba daga bisani tace okay yeah Why not..Ji yay kamar zai tashi can sama dan murna duk bakinsa yakasa rufuwa. Da ido tay ma uztaz alaman ya bisu abaya Doc khalidi nata saurin yaje ya bude mata gaban motarsa uztaz yay sauri ya rigashi kafin tazo har ya bude mata motar. Kasa kasa yay ma uztaz din wani irin kallo uztaz ya bishi da harara a bayyane har sede ya make sure halisa ta zauna snn ya rufe mata motar ya zago yace masa" sir,...doc khalid ya juyo wani irin stern look yagani afuskarsa yace masa "Be careful while u Drive.. Adan tsorace dr khalid Yace okay. Uztaz bai kulashi ba ya koma mota abunsa ya fara binsu abaya. Suna fara tafiya kamr wanda yake jira akan uztaz din ya soma janta cikin hira yace that guy is tooo hot oo baya wasa da alaman yanada zafi...So is he ur bodygurd.? Atakaice Tace masa no. Ya kuma mata wani tambayar yaga kamar bata da lkcin jan hira dashi dan dolensa ya dawo da maganan bisa abunda ya shafe lafyarta. Nan ya fara tambayarta akan book din..Tafara gaya masa cewa ta fara karantawa. Hira kawai yake mata kala kala kamar irin sun jima da sanin juna din nan. Yace Kinsan nima naso na rubuta book irin wann amma Doc asim bashine ya koyardani ba soo only his student are allowed to featured in his editions. Tace really?.. Yace yess oo ai dana rubuta wani kalma aciki da bazaki jima ba zaki warke sosai. Tace hmm but dis is one also is good...i like it. yace yeah yeah kananan likitoci akwai rawan kai so its obvious u will like it. Cike da jan aji Tace wow kananan likitoci ne ma, so Who wrote chapter seven then, ai na dauka ma kaine? Da mamaki aransa Yace har kin kai chapter seven? .. Tace no na tsallake nayi naje wajen..cos the begining is soo boring yace okay its one unprofessional therapist haka a hospital namu inata kkrin ma kar asakashi a case naki. Yana fadin hakan kawai se mind dinta ya tuno mata da ranar data jiyo sa yana magana akan Dr khaleel kawai saita share zancen bata kara tambayarsa akai ba dan batason ma taji ance shine bare ta tsane book din shiyasa har suka iso cikin asibitin bata kara tambayarsa komi akan book dinba Suna sauka a harabar tafara dube dube dan Mamaki tasha da bataga uztaz abayan su ba, har saida dr khalid ya sauko ya sameta snn saigashin nan ya shigo. As usual yana bayansu har suka kai office din after like 40 min suka kammala tattaunawa da Dr khalid akan sauran abubuwan daya rage basu kammala jiya ba. Yaukam Tasha tambayoyi game da rayuwarta amma hakan nan dai ta daure ta boye abubuwa dayawa acikinta dan amincewa da dan Adam akan sirrin rayuwarta yana neman yay mata wuya ynxu. Shawo kanta da Dr khalid yake tunanin zai masa sauki sai gashi yana neman yay masa wuya sosai dan sai ya kwaso wani tambayar dayasan zai mata ciwo ya raunata ta sai ta shanye aranta snn ta juya zancen ta bidashi wani ma'ana na daban. Gashi next session dinsu sai next week kuma practical sesseion ne baison suyishi a asibitin shiyasa yau din ya gwada zuwa gidanta direct koda zai samu sakin fuska daga gareta, yin excise din yadda yake so a asibitin bazai masa dadi ba dan yasan alkciin khaleel yana nan zai iya tsoma masa baki gashi ya tsanesa sosai. Yauma har waje ya rakata dan yanata cusa mata kai yanason su dawo abokan dole sede har sukayi sallama yau din bai wani gane hanklinta ba dake yanayin uztaz kawai take dubawa. He look very alert and suspicious akan asibitin Har Allah Allah take su shiga mota ta dan tambayesa ko lafiya Tana shiga kuwa taga ya dau hanyar anguwar lekki Da ita gashi gudu sukeyi Ba kakkautawa gani tay suna ta tafiya ciki cikin anguwar harma bata gane ina suka dosa ba. Abun ya dameta aranta tun tana shiru taji bazata iya ba Tace uztaz kamanta abunda nace maka ne ..i said zaka kaini wajen meenal wani hanyane kuma wann Yace i know maam i just want to confirm sumting.. Nervously tace Something like what? Bai amsata ba ya waina kan motar yasha wata kwana da ita tun kan tay magana sai ganan wasu motoci dasuka sha bakakeken tintted har biyu abaynsu daf daf sun wuce su fewwwww sun wuce caannn gaba harsaida taji ta mugun tsorata da su . Kashe motar yay snn yace mata maam someone is following us tun daga asibitin nan amma nasan inda suke buya anan anguwarne 'A mamakance Tace really? So How did u know about it. Bai jira ba ya ciro wayarsa ya mika mata pictures din daya dauka na garajin bata gane komi saida tay zoming hoton sosai ajikin badge din rigarsu taga logon kamfanin zach wani irin sarawa kanta yayi. Tace "Ka tabbata sune suke bibiyata?..yace eh na tabbata jiya har nan na biyosu yauma kinga sune suke binmu ahanyar asibiti shiyasa na tsaya ina marking dinsu. Dafe kanta tay jin yana sarawa mata da karfi snn tace "I know them. Yace who are they Adan rude cikin yanayin rashin jin dadin jikinta tacemai mubar nan wajen kawai uztaz just take me to the jasmine. Batare da bata lokaci ba ya juyakan motar basu tsaya ko ina ba sai gidan kawarta jasmine. Sauka tay a rude tun bai zo ya bude mata ta kama hanya zata nufi ciki Yace shud i wait for u Tace nooo kaje ka dada bincikamin masu wann motar and make sure they belong to this logo Idan ka gama ka kirani awaya. Yace yes maam . but are u okay? Ahankli tacemai i will be. Da sauri ta shige cikin gidan ta same jasmine na zaune akan kujera ta kunna slow music tana video call da saurayinta tana kuma shan shisha. Yanayin da halisar ta shigo yasaka ta kashe wayar ta miƙe tsaye Tace"Babe..whats wrong ya naganki ahaka Hawayenta datake dannewa suka sauko kasa yarrrrrrrrrr. Cos she is emotionally weak. A rude jasmine tace meyafaru halisa??? Karamin Kukan gajiya da ryuwar nan ne ya kufce mata tace jasmine..the devil is really working againts me.. im never going to have any peace of mind Jasmine Tace how? What happen..meye Ahankli ta goge hawayen snn tace Ive met my doctor.. yafara min treatment har yau din nan nafara jin sauki sauki nafara kkrin yin tunani akan rayuwata. Then kawai saiga wasu motoci suna bina and gues wat??? A tsorace Jasmine tace "what? Bakinta harna rawa tace its zach.. Take jasmine ta hade rai tare da zare karar tabar dake bakinta tace what? Halisa tace wallhy shine jasmine..zach is after me. See, I knw all his secret logos shiya nunamin. his boys are following me..im just scared.. what if he came to destroy my life what if he want to come back to me for a secnd chance jasmine am soo scared zuciyata baida wani karfi kuma banason na sake komawa cikin halin da nashiga ciki akansa da ko warkewa banyi ba. Da sauri Jasmine ta rikota suka zauna ta debo ruwa mai sanyi a cup ta bata tasha ahankli tana rarrashinta hartay shiru... Sai can snn Tace halisa Kinsan inde zach ne ya dawo bazai bi wani kwana kwana ba direct zaizo ya gaya maki feeling dinsa ko?.. Ahankli Ta gyada kai tace eh na san da haka Tace toh Sede in an gaya masa wani abu akanki Or..maybe yana son ya tabbatar da cewa baki tare da wani or he saw u with sumone else and he thinks u have replace him dis quickly. Halisa tace and so what? Ba rabuwa dani yayi ba Nide tsoro nakeji kinsan yanzu fa yasan komi akan past dina i dont want my present life to get ruined by my past Ayanayin lallami jasmine ta riko hannunta tace haba halisa babu abunda zai iyamiki daibJust calm down kiyi tunani a inane suke bibiyarkin? Tace uztaz yace min tuna asibiti ne. Dan shiru jasmine tay snn Tace okay here is what we will do dan musan asalin gaskiyar shi.. Is dat ur doctor friendly with u? Tace yeah.. Jasmine tace perfect Toh ai dashine zamuyi amfani wajen warware wann lamarin. Dan Inde akan soyayya zach ya dawo he will follow u more often idan kika soma kulla kawance da Dr dinki...amma idan dan wani abu ne we wll act ahead of him..ina uztax yanakan bibiyarsu? Did u tell ur friend hadiza...zata iya sawa a temaka mana da wasu bayanai. Shiru halisa tay acikin tunani bata amsata ba tukuna...... SHARE TO UR GROPS [2/11, 9:58 PM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB*_ _BY SURAYYAHMS_ 30. Duk yawan Daƙikanin lokutan da halisa ta dauka acikin shiru bashi yahana jasmine tsura mata idanuwanta ba. Ajiyar zuciyane ya kufce mata tace "Hey Halsy i am asking u a question kin min shiru, nace kin gayawa hadiza maitama kuwa?...Juyowa halisan tay ta kalleta Ahnkli snn ta sauke ajiyan xuciya fuskarta kamar na wacce bata cikin hanklinta tace.."No...bangayawa kowa ba. jasmine batace komi ba ta kura mata ido tanata kallon mood dinta daya sauya gabaki daya yadawo na damuwa. nauyin idanun jasmine dake yawo akanta shiyasata lumshe idonta ahnkli snn ta juyo ta fuskanceta tace... "Jasmine look,..nifa bana son nagayama kowa maganan nan ne, atleast kedin ma kawai ya isa..ni de kawai banason tashin hankaline. Atake jasmine tace but why not?Akan meye sauran bazasu san me kike ciki ba cos dis is pretty serious ba abun wasa bane..zach yana miki kwantan bauna ne halisa, kafin kizo ki hankara zai kamaki a inda bakiyi tsammani ba so, we all have to think fast.. Idanunta ta lumshe muryanta na rawa rawa nervously tace ..."Im thinking jasmine...i am seriously thinking..kawai de...kasa cigaba da maganan tay dan dede nan taji wani baqon rauni ya rufeta atake kalma ya dauke akan harshenta cak tanajin kamr ta fashe ma jasmine din da kuka. wani irin yanayi mai gajiyarwa taji yana kkrin shigarta, idanunta a lumshe sosai cikin yanayi mai kashe jiki ta cusa hannayenta can cikin suman kanta tana calming kanta ahnkli kasar makoshinta tace "ohh jesus christ, i am sooo done..wayyo Allahna na shiga uku na! Da sauri Jasmine ta riko hannunta sigar lallami tace baki shiga uku ba halisa,i am with u..kawai ki kira hadiza yanxu kuyi magana dan ita kadaice take da cikakken hanyar da zata binciko mana moves din boys din zach acikin kankanin lokci. Kekanki kinsan mijinta yana da iko da security system na garin nan, it wont take them a minute to figure those guys out. Agajiye halisa ta bude lumsashun idanun nata da suka jike da ruwa aciki ta kalle jasmine da sacewar jiki tace " ..Jasmine i knw.. Amma wann fa ba mafita bane ki yarda dani.. Dan dukan kawayena bazasu tsaya su fahimce komi ba dan suna balain jin haushin zach, sun asalin tsanarsa wallh idan na gayawa hadiza ka ita daima she will make sure tamasa wani abu mummuna, snn koda hadizar batay ba shemau da meenal fa? They dont have chill..sunajin cewa zach ya dawo kaina wallh komi zai lalace karshe kuma nice a tsakiyansu dan asirina ne zai dinga tonuwa duk duniya sai ansan past dina wanda shine dama abunda mutane dayawa suke jira akaina ayanxu. Kafadunta jasmine ta dafa da sanyin jiki snn tace toh yanxu ido zamu zuba masa kome? Shiru tadanyi kafin nan tace "mafitar dayane shine ta hanyar amfani da wann doctor da kika gayamin amma ai kinsan bazan iya deceiving din feelings din kowa ba, kar nazo na dan sakemai fuskane ya fara tunanin ko inasonshi ne bcos i will neva...i don't even find him atrractive..yana da banzan hali he is too boastful yana son yaba kansa da son bata sunan wasu. Jasmine tace cmon halisa aike ba ajinsa bane ma amma ai bada son ranki bane zaki kulashi and is just for a while...abokantaka fa bazai taba zama cutarwa ba. Da sauri muryanta kasa kasa ahanki tace jasmine nifa bana bukatan wani abokantaka...araina bana tunanin zan sake iya kula ko son wani ɗa namiji aynxu,and with zach being around me i dont even knw whats gonna happen to me, raina zaina baci inna gansa a inda nake,ni bana son mu dedeta i dont even want him to apologise to me"...Adede nan hawaye masu zafi suka soma zubowa a idanunta tabi ta sunkuyar dakanta can kasa tanata kallon kasa hawayen nata na diga ahnkli. Shiru ne ya ratsa awajen jikin jasmine yay sanyi tanami shako sheshkarta dake kkrin danneshi da karfi. Da kyar kafin ta iya fidda kalma abkinta, muryanta na rawa ahnkli tace."i just want to move on with my life jasmine..bani da wani gata, sai wanda nake nema nabawa kaina a duniyan nan. Idan har ƙimata da mutunci ya zube kasa zai xamo kamar rayuwata ne ya kare. nide banason kwata kwata na koma cikin rayuwar zach har abada wallh banason shi yariga yafice min araina.."why is he back for me for god sake ??????? Jas baki san ya nakeji bane.. nikadai na san wahalar da nasha da zach ya rabu dani saboda nasoshi na kaunaceshi da imani na, na bashi zuciyata da dukkan yaddata, Da kyar na iya cireshi araina ynxu haka ko gama warkewa banyi ba. Jin numfashinta na neman sauyawa yasaka tay shiru hawayenta nata saukowa ahnkli tafi minti biyar tana hawaye mai sanyi batare da tasake cewa uffan ba. Jiki a muce jasmine ta jawota jikinta tabita rungumeta sosai acikin sigar lallashi,kukan taji ya ballo mata ta kwanta jikin hasmine tanayinshi harsaida tay kukan yawuce mata aranta kafin nan tasaketa ahankli tanamai kallon idanuwanra da sanyin murya mai cikeda tausayawa. hannunta jasmine ta riko snn tace calm ur self Halsy i know how u feel. Kidena tunanin ko ban fahince abunda kikeji ba..,Zach is going to distract u and u dont need to allow that..I totally get it..amma kiyi hkri kinji. Karki bari hakan ya taɓa maka ranki In Allah ya yarda zaki kufcewa duk wani mummn shirinsa akanki. gyada kai Halisan tay ahnkli Batare da tace mata komi ba tay shiruuu cikin nazari sai can bayanta dedeta nitsuwarta snn tace" iya mafitar kenan frndshp dina da doctor dinnan amma zanje nayi tunani akai sabida gaskiya bana son na cutar da zucyarsa da yaudara, Banason na zama kamar zach i just cant destroy anyones life with love or friendships. Dafa kafadunta Jasmine tay ahnkli snn tace Kiyi tunani akai din dai...ur life matters alot too. And Selfish ppl live longer just try dis once. Batace komi ba ta share hawayenta duka snn ta dauki ruwan sanyi a bootle tasha tace bani cigarattes din chan..mika mata jasmine tay ta dauka ta kunna tafara sha ahankli tana buso da hayakin waje cikin jan ajiyan zuciya har saida yafara distracting mind dinta daga tsoron datake ji aranta na fuskantar abunda zatay anan gaba. Anan ta karace zamanta bata wani jima ba bacci ya dauketa, har uztaz ya kammala bincikensa ya kira wayarta, lkcin tana bacci, jasmine ne ta dauki wayan sukayi magana ta gaya masa abunda suke ciki daga nan ya wuce office ita kuma ta cigaba da abunda yake gabanta. Ata dayan bangaren kuwa Koda engr mahmud ya tashi daga baccin huce gajiyar jiya it was late aroud 7:45am in the morning..gani yayi kamar shema'un batama shigo dubasa ba, nan ya mike daga kan gadon ya shiga bathrum don ya kimtsa ya samu ya fito dubata. yana shiga ya kunna ruwan shower akansa,blkcin babu abunda yakeji aransa face quilty consience na auren mai aikinsu hafsa da yaje yay abayan idanun matarsa dan gani kawai yake kamar bai kyauta ma shemau ba daya dauko hanyan yaudararta da karya.. Kafin ya kammala ya fito ya shirya It was already past 8am. Daga gaban mirroe yay tsaye Yana kammala taje suman kanshi da hadadden gemunsa Agurguje ya shafa ma jikinshi mai snn ya dauko jallabiyar sa ta muharramain mai kyau daya siyo a makka kalarsa brown kalar kasa Ya zura ajikinshi ya fetsa turaren mousuf wardi yabi ya shafa oil perf na baccarat rouge 550 snn ya nufo hanyar dakin shema'u. Tafiya yake yanata tunanin yadda zai je ya sameta abunka da wanda baisaba karya ba gabaki daya sai yakejin kansa daban. Dede bakin main room nata ya tsaya kafin nan ya danna lock press yanajin shi a kulle ya kirata awaya nan ma ba a daga ba. Yakai 15 min yana tsaye yana knocking tanajinshi taciki bata amsa shi ba bandama tulin hararar datake bin kofar dashi. Agogonsa ya kara dubawa ganin takwas ta wuce yasan tabbas ta farka abarci, sede Ganin kamar bazata amshi ba yasaka ya hakura ya wuce babban palonsu ya zauna tare da daukar remote ya kunne tv just for a while ya saka channel din labarai. Ana neman 9:20 lkcin shema'un ta riga ta gama shirin ta yau kam Riga da skirt tasa mai tsada irin na silk material din nan matured rusty olive and black colour na kamfanin christian Dior. skirt din straight ne baki wuluk rigar kuma olive mai shegen tsantsi tare da Doguwar hannunsa mai adon black swvroski stonea ajiki.. nan ma ta sauke straight malaysian wig din data saka bisa kanta side by side suka zubo mata harkan kafadunta wanda ya dada bada kim kardashian white colour na fatar jikinta wata fitinanniyar classy look. wani kalar kyau na ban mamaki yau tay dan babu wani abu waishi sanya acikin lamarinta dan haka ta rigada ta soma bida kanta inda zata samu cikar burinta na samun wani mijin mai narkakken kudi irinna kawarta hadiza ba ire iren normal millonaires kamar mijinta engr mahmud ba. Karamin Jakarta da Takalminta na miu miu kalar rigar ta sakalasu a jikinta designs dinsu badai daukar ido ba, tsabar tsinin takalmin da igiyoyinsa aka daureshi wanda yasaka take bida takunta ahnkli kamr wata sarauniya.. Yau Ko mayafi ta kasa yafawa ajikinta da kyau don dama chan ganin darajar auren mahmud akanta yakesa in zata yi irin wannan shiga wani bin saita rike veil a hannu wani lokaci kuma tayi rolling kawai amma yanxu batama son kwata kwata dressing din da zata komoyi yay kama da na wancce take da auren wani akanta dan kar hakan yaje ya kashe mata kasuwa. A hankali ta ke saukowa cikin catwalk mai daukar hankali sai dai cikin ranta a cunksuhe yake da haushin ganin mahmud a zaune a falo da safen nan ya kunna tv kenan yana dan kallon chanel news. Wani irin tamke fuskarta tay snn ta cigaba da takun ta tana saukowa ahnkli qamshin turarenta na mousuf sexy shine ya soma sauyawa iskar wajen launi da dadinsa. she knew mijinta bai da hayaniya sosai so zata dan daure ta gaishesa badan kallon haushi dayake ata aranta ba. If not for the Adalcin da mahmud yake mata na bata duk wani abu datake so a duniya da tuni ta gayamasa cewa she is suffocating in his wife..infact ji take kamr tana cikin halin dan danasanin aurensa datayi a rayuwa. Tun da qamshin turarensa ta bugesa ya ya dade da maida kallon sa kanta karasowa take kamr bazata taka kasa ba, Da kyar batare da ta kalleshi ba cikin shan qamshi mai tattare da azaban rigima, muryanta ciki ciki tace "ohh kaine anan? Toh sannu! Gaisuwar datay masa kamr ansakata dole shikuwa Dressing din nata yaketa kalla a mamakance, humbly and calmy yace good mrning my wife and where did u think ure going dressing like this?.. Sama da kasa ta kalleshi cikin shan qamshi ta jefa kanta cannnnn batama kallonshi, kasar wuya tace" ina kuwa zance inba Aiki ba !!.. Shiru yy bai amsa ta ba Da idanunsa masu cike da kwarjini kawai ya kureta har saida ta soma duban kanta da kanta a dan sace, karamin tsakine ya kufce mata tace "wai meyene, ehen? me ya same dressing dina kuma mahmud kakemin irin wann kallon kauyanci? Ohh please kabarni fa na sha iska!! Ajiyar xuciyane ya kufce masa jin hanklinsa na neman ya tashi yace shemau badai ahakaan zaki fice ba ko?..Fuskarta a dore tace ahaka kamar yaya? tsirara na fito ne ko ya... Ban gane maka ba what is wrong with u ? Yace Hmmm babu komai"nothing is wrong with me... kishinta yasaka ya dan kau da kansa ya cigaba da maganansa a nitse yana cewa mrs slay stylish of the 21st century kuna sanin cewa dai da aure akanku kuma Allah zai tambaye ku irin shigar da kukeyi awaje. "Tsaki ne ya kufce ma ta cikin jin haushin maganan ahankli tace its enough dan Allah kar mifara da

Chapter 35 of 44