ta rokesa daya aje maganan sirri atsakaninsu gobe inta tashi daga aiki zata dawo sukarasa maganan a nitse.
Tsabar tausayin data bashi Har motarta ya rakata yanamai mata adduar Allah ya shiga lamarinta dan yasha mamakin irin hakuri da amanan datayi ma mijinta wanda yasan acikin mata dayawa bazasu iya hakuri da mijin da baiya basu nitsuwar da gamsuwar aure ba.
Ayayinda shemau ta dukafa wajen shirye shiryen zuwa hidimar manya da za'ayi abuja sati na gaba mahmud yaga tijara wajenta kala kala dan kuwa zaman doya da manja kawai takeyi dashi acikin gida while shikuma yanata tunanin cewa hala dan bai mata suprises irinna hadizar bane yasaka ta fara walakntashi.
Ya shiga tashin hankli da rashin samun nutsuwa musammn akan yanayin suturar data dawo sakawa da bakaken maganan datake gaya masa a duk sanda yazo kusa da ita.
Wasu Contract din ya shiga nema gadan gadan koda zai warware masa matsalarsa da shemau, atleast koda bai mata irinna hadiza ba koda kadan ya samu hala hanklinta zai dan kwanta.
Ata Kowanne bangare kowa jira yake satin nan ya kare domin yay abun da zai iya sauya masa rayuwarsa.
Musamman ma ata bangaren hafsa datake kan farfadowa cikin hayyacinta da kadan kadan dan kullum ta kwanta saitayi tunani me zurfi gameda kalamomin da mahmud ya gaya mata. And she thinks is high time to make up her mind to chase that dream and make her parents so proud.
Snn Aranta ta aje cewa bazata taba kunyatar da wayann mutanen da suka taimakawa rayuwarta dana ummnta ba.
Satin nata gabadaya a makoki tare da nazarin rayuwarta na gaba takare..
Hakama halisa datake tunanin cewa a satin nan mexuwa zata kare dukkan wani wasan dake tsakaninta da mazaje biyun nan dan already ta gaji sosai da kasancewa inuwa daya da khalid daurewa kawai takeyi.
While ata fanninsa shima gani yake wann satin da zasu shige ciki shine satin da zai samu damar shigewa jikin halisa da sexual attachemnt harya siyo fake engagemnt ring nasa don so yake ya aiwatar da tsarinsa akan lkci.
Yau asabar da yamma Halisa ta fito sanye da wani light gown na shan iska da simple flat shoe akafarta ta saukar da duka sumanta na asali bisa kafadarta da hat dinta a hannu.
Yau batajin sha'awar kasancewa a koina sai abakin ruwa,a anguwar da suke din akwai babban beach Mai suna Tarkwa Bay Beach which is Accessible by boat from Victoria Island ko ta can cikin anguwar ikoyi.
As usual tare da uztaz suke je wajen ya saka simple casual dress da face cap suka boading booth yakaita wajen domin ta samu hutu cos
Tarkwa Bay beach offers a serene environment and water sports wajen akwai nishadi da dadin zama sosai sabida iska mai sanyi dake hurawa
Suna isa ya nemi waje ya zauna daga kan wani chair can nesa yanamai kulawa da motsinta at same time yana dannne danne akan tap din aikinsa sabida mutanen da suke son suzo office din ganinta ranar monday jin dasukayi ance zata fara fitowa.
Water sports halisa tafarayi tanamai tuka water bike harsaida ta gaji sann ta dawo ta zauna akan mat tay shiru sosai tanamai sauraran karar ruwa dayake saka mata kwanciyar hankli..
Lumshe idanunta tay sosai tanamai tunowa da rayuwarta ahnkli saidai batajin wann tsananin baqin cikin datake yawan jin idan tana tunawa abaya. Wanda hakan alama ne dake nuna cewa hanklinta ya soma dawowa jikinta.
Tana cikin wann yanayin taji wani hannu mai sanyi sosai ya dan dafa ta...
Wani qamshin turare na daban taji wanda bata taba sanin irinshi ba.
Bude idanuwanta tay ahankli tare da dago kanta sama tana juyowa suka hade ido, tsananin mamaki ya hanata budan baki....
#Surayyahms
08060712446
SAURA SHAFI DAYA MUGAMA BOOK 1 PLEASE.
[2/19, 8:40 PM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB...*_
_(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_
#ROMANCE
#FICTION
#ADULTHOOD
#SEXADDICTS
#WOMENPOWER
BY
_SURAYYAHMS_
_08060712446_
*FINAL EPISODE BOOK 1.*
Tsananin Mamakine ya turnuke zcyar Halisa data hade ido da warce ta dafa mata kafadunta a hankali ganin fadilah ce daga tsaye sanye da wasu kayan sanyi dark cobalt colour riga da wando masu kauri ta dan rufe fuskarta da hular hoodie din rigar da alaman batason aganeta a asarari.
Cikin sauri uztaz ya taso daga zaunen dayake zaiyo wajen da suke hannunsa na dama dafe da bakin aljihunsa dan already ya gama yin readyn fitowa da bindigarsa dake boye adede wajen Seidei tun kafin ya isosu halisa tamasa ido akan ya dakata kawai bakomi
Gyada kai kawai yay amma Duk da haka idanunsa na kan fadilar dake tsaye yanamai lura da duk wani motsinta dake ta bayanta yake kallo bata gaba ba baima san itace tazo wajen ba.
kallo daya halisa ta mata snn ta dan dauke kai tay murmushi me sanyi acikin nitsuwa sosai tace
"Fadila right???.
Ahnkli fadila tace yes ma'am.
Cikin wata sassnyr muryavme tafe da aji tareda dauke kai tace
"..What a surprise?
Fargaba da bugun zuciya mai yawa shi ya turnuke fadilar kalmomin bakinta suka dauke mata cak rauni yasaka idanuwanta suka kuma tara ruwa sosai dan batasan me zata kuma cewa ba..
Jikinta a sanyaye ta tsuguna agaban halisan a ladabce muryanta na dan rawa rawa snn tace Good evening ma'am i am soo sorry i have to bother u. Pls forgive me, dawani irin desperation a muryanta tace "its just dat i really really want to talk to u..maam pl...
Cikin datsar numfashinta halisa tace "U're here to talk to me? Fadila ta gyada kanta da sauri, fuskarta ba wani sake ba tace .."talk!.. karki batamin lokaci na.
Ajiyar zuciya ta sauke cikin dedetu makanta nitsuwarta ganin yadda halisar ta kame ajinta sosai tabi tazuba mata sanyayyun idanuwanta mai cike da kwarjini acikin nitsuwa wanda yake bayyana tsantsar Aji da ilimi daya gama ratsa mata gangan jiki.
Bazaka taɓa iya tantance saukin kan halisa a bugu daya ba face harsai ka xauna da ita a inuwa daya.
She is indeed the most matured and soft heartd person sede a fili gani ake kamar tafi sauran kawayen nata girman kai da rashin sake fuska duk dama ba'a taɓa lissafata acikin masu izgili da walakanta jama'a kamr Barister shema'u usman marafa Da hajya meenal Ali talba ba.
Alot of ppl do mistake shiru shirun halisa a matsayin girman kai shiyasa mutane da dama suke kkrin son suji wani aibunta dan a samu nacewa akanta a kullum.
Hawaye taf suka ciko idanun fadila tarasa yadda zata fidda kalmomin bakinta data kwana tana memetasu dan karta mantasu da suke neman yimata nauyi a akan harshenta yanxu.
She have no idea how halisa manage to pull herself out of that pain and heartbreak dan Ganin halisan zaune a bakin ruwa cikin kwanciyar hankli ya tabbatar mata da cewa tafara samun nitsuwane ynxu sosai.
Tayaya kenan zatazo ta lalata mata wann nitsuwar data same shi da kyar.???
Wani sabuwar yanayi ta shiga najin karayar zuciya tareda dana sanin zuwa nan wajen da quddirinta data riko acikin zuciyarta na daukar fansa akan meenal talba...
Satan kallon halisan tay aranta tanamai cewa bazai kyautu tay amfani da macen data nemi ta taimake rayuwarta alkcin da hatta uwarta data haifeta ta gujeta ba.
Hawayen dake kkrin sauko mata ta hadiye cikin dedeta nitsuwarta tay murmushi batare da tasan me zatace mata ba kuma.
Fadila i am waiting for u to talk.
Jin halsyn ta fadi hakan yasata sauke nannauyar Ajiyar zuciya snn tace "uhmm uhmmm...dama dama. Sai tabi ta sunkuyar da kanta can kasa alaman batason ma su hade ido bare tasan karya take mata.
Tace ammm miss halisa dama Inaso ne ki bani aron kudi...ma'am i promise i will pay u back, dan Allah kitaimaka min i have no wherelse to stay and i really really want to start sumting da zai taimaka ma rayuwata.
Yanayin yadda tay maganan da i i na tare da barin baki yasaka halisa kasa gane gaskiyar lamarinta gabaki daya.
U want to start a business bayan anata nemanki awajen aikin ki fadila? So why wont u go back to talba grp of companies?
Wani irin Shiru mai tattare da sakonni fadila tay batare da ta dago kanta ta bata amsa ba kawai sai tafara sauke ma halisan hawaye masu sanyi sosai.
Halisa dake kallonta cikin kyabe baki tace
"hmm fadila kenan..
i knw bani da wani iko akan rayuwarki..baki sanni ban sanki ba ur life is actually none of my business. But look at you ure young yanxu kike cin zamaninki..,ure a woman in struggle and dats what make us the same. Inhar kina so na taimaka miki you have to tell me what is wrong with u, kifada min gaskiya meye shiga tsakaninki da meenal talba kuma Meyasa take cewa kin bar aikinki ne domin kibibiya maza?
Dan shiruuu tay snn ta dafa kafadun fadilar ahankli in a comforting way dayasaka zuciyarta karyewa sosai.
Muryanta kasa kasa tace ki fahimce ni,Bawai dan kin tambayeni aron kudi yasaka nake so sainaji matsalar rayuwarki ba. Ki kalleni dakyau I worked soo hard to make my own money batare da neman temakon iyayena ko yan uwana ba.
Dats why I value my money alot, Bana son na dauki kudina na baki dan ki temaki kanki snn daga baya inji cewa labarin biye biyen mazan da akeyi akanki gaskiya ne..
wani irin takurarren kuka mai cinrai fadilar tafashe dashi tun kafin halisan ta gama rufe bakinta
tanamai jan shesheka mai zafi alaman kukan ya rike mata kirjinta sosai.
Cikin wnn yanayin tace wallahi wallahi karya akemin ni ko saurayi bani dashi bare inje wajensa. Tambayoyin da halisar ta mata sai taji kamar dawo mata da ciwon abubuwan daya faru da ita akayi baya.
Tsabar ɓarin da jikinta yakeyi gabaaki daya wta kasa iya dago kanta sama bare ta kalle halisar cikin ido ayayin da zata gaya mata mugayen abubuwan data bata sani ba akan aminiyarta .
Dan tasan halisa is going to get hurt and shocked and also angry...
Kuma tafi kowa sanin amana da kaunar yan uwan jini da suke nuna ma junansu tunda dai tazauna dasu tun tana karama. Abu mai wuya kwakwalar halisa ya iya daukar wann sabuwar labari musmmn akan aminiyarta meenal dan zai iya mata rauni fiyeda kowa a duniyan nan.
Aragwabe ta kuma fashe mata da kuka mai sanyi da kuma karsashi.
Tasan inhar tagaya ma halisa cewa har cutar HIV ta samu a sanadiyar muguntar meenal tamkar karamin yaki kawai zata hadasu.
Tausayi yasaka halisan tariko hannunta in a comforting way tare da kura mata idanuwanta dats full of emphaty and understanding.
Haka kawai take ji ajikinta cewa fadila nacikin matsalane me girma and she honestly wish that zata gaya mata danta taimaka mata dan ta riga tasan zafin rashi, Dana talauci da zafin walaknci da kaskanci, ta kuma san na yaudara da zafin rasa masoyi wanda shiyasa take ji aranta kamar ko da maqiyinta ne agabanta bazata so ace ya dandane irin zafin da takeji anata rayuwar ba.
Tace Fadila u need to calm down and talk to me okay
Fadila ta lumshe ido sosai cikin sassanyar kuka ta rike hannayen halsy anata cikin tunanin abunda zata gaya mata me dan dama dama.
She just cant hurt her feelings, she cant tell her who meenal is. batason sanadiyarta ace sun rabu da junansu bayan tasan irin amanar dake tsakaninsu tun na yaranta.
Hawayenta ta shiga sharewa ahankli muryanta asanyeye snn tace arayuwa akwai wasu abubuwan da Allah ne kawai zaka bar masa ya daukar ma fansa.
Ma'am am sorry pls Kiyi hakuri..da akwai wasu abubuwan da bazan iya gaya maki. Amma ina so ki fahimceni. barin aiki a talba grp of companies abune mai matukar wuya agareni nikaina bada son raina na barwajen ba sabida sune sukaban ilimi da rayuwar danake tunkaho dashi yanxu. Ci, da sha da sutura tareda kulawa da ummana da yan uwana..they basically owed me evrything, i worked, i slaved...but i just can't do it anymore sabida aikin danake yi anan din ya cutar Da rayuwana ata hanyar da bazan taɓa iya gyarashi ba.
Sabbin hawayenta da suka sauko masu dumi akan hannayen halisa data riko take kallo cikin sheshehka.
Jikin halisa yay sanyi sosai tanata kallonta in a comptely broken state..
Kanta na cann kasa hawayenta na diddiga akan hnnun halisar tace
Anty halisa inason nayi miki wata tambaya
Sihirtaccen ajiyar xucya ya kufce ma halisa tace go ahead inajinki.
Akaro na farko data dago jajayen idanunta ta zubasu acikin na halisa suka kalle juna.
Wasu sabbin ruwan hawayene suka kumaa zuba mata tace Anty halisa kisaka kanki a matsayina nasan zaki iyayin komi ma waya da suka taimaka ma rayuwarki dana iyayenki..
Amma zaki iya sadaukar musu da rayuwrki ta duniya da lahira duka????
Nakasshen murmushi halisa tay snn tace tabbas zan iya sadaukar musu da lokaci da dukiya akansu amma bazan iya sadaukar da rayuwana da lahirana akansu ba.
Fadila Ta dada riko hannun halisa tace mutuncinki da lafyrki fa?..
Ahnkli Halisa tace what?
"No way..wayann ai sune arzikinki da Allah ya baki.
No one' is worth it. See,.. I left many jobs, many roles na fashion show, many huge business contract dan na kare mutuncin kaina da lafiyata kuma naga amfanin hakan sosai.
Cikin lumshe ido da budewa ahnkli fadila tace i lost mine sabida inason nay cikakken biyayyawa wanda suka ceto rayuwana dana familyna..Lokaci na, da Mutunci na, da lafiyata duk na zubashi akansu.
wani tsammmm tay tanaji aranta kamar ta fada ma halisa komi kawai tahuta maranta sai can kuma ta fasa acikin sassanyr kuka painfully tace Mrs meenal talba is asking for too much frm me. I did evrything for her but She dont have ruined my life like this..nasan tarihin mahaifina bamai kyau bane,yes he is quilty of duk abunda kikaji ana zarginsa dashi, anty halisa we cnt choose who we come frm. Ni babu abunda ya hadani da irin wann rayuwar tasa amma dukkan abunda yay ma yayan wasu nima ya shafi rayuwata.. Nayi kkri na nema aiki awasu wajejen amma duk tabi ta gaya musu karya akaina da familyna. She've just ruined my life. Tanakaiwa kukan yaci karfinta.
Cikin yanayin rarrashi Halisa tace kuka bazai ficceki ba, cos no one can ruin ur life except u fadila. Sabida kece kadai zaki iya zabar makanki abunda zakiyi da abunda bazakiyi ba babu me tursasaki..nasan kuma bazaki iya zabar irin baqar maganan da za'a gaya maki ba, but the power to ignore them is totally in ur hands...abu mai matukar wuyane ka rabu da wasu abubuwan duniya na arxiki da ake nunamaka domin akarbi mutunci ka amma danaki yanxu fa??? Bai zanca komi daga arzikin dake jirana ba...i worked hard with my mutunci sann ina da kudina nakaina.. So u alwys have a choice okay. Blaming urself ko mahaifinki ko meenal bazai sauya miki komo ba...Ko ki koma aiki wajen amina tareda kare mutunciki da lafyarki,Ko kuma ki barshi ki nemarwa kanki mafita me dorewa..
amma fa kisani duk wani abunda zaki jefa kanki aciki da duk wani shawarar da zaki yanke akn rayuwarki daga karshe inhar tay kyau cigaban na kowane, amma idan tay muni matsalarki ce ke kadai. And the first person that will stigmatize u is urself.
Nannauyar ajiyar zuciya ya kufce ma fadila tare da kwace hannunta ana halisan tafara share hawayen dake fuskata ahankli.
Iya Tunanin me zatayi da rayuwartane ya soma yawo acikin kwakwarta jin maganganun halisan ya shige jikinta sosai ya sanyayatta taciki. dan Harga Allah tazo neman hanyar daukar fansa akan meenal ne kawai ya kawota, ata wani fannin kuma aranta tasan itama akwai kuskurenta aciki sosai. Har kasar zucyarta tasan da can bata amincewa meenal ba da hala bazatana tursasa mata shiga harkan karuwanci da xubda mutunci ba.
Hausawa suka ce sai bango ya tsage kafin kadangare yake iya tsagawa ciki...her biggest and foremost mistake shine rashin tsayawa da kafarta wajen kare mutuncinta agaban meenal talba.
Hadiye maganan tay aranta jin halisa na tambayarta menene shawararta ayanxu?
Juyowa tay ta kalle Halisar cikin sauke ajiyar zuciya snn tace mata
I want to focus on myself..Kaina kawai nakeso na taimakawa. Dan Inaga Bazan taɓa iya komawa aiki a talba grop of companies ba.
Ruwan Hawaye suka ciko idonta a karo na babu adadi tanamai dubn idanun halisa aragwabe
tace anty halisa ke kadai ce zaki iya temakamin..
ure the only one that can save my life from crumbling, ban isa na tunkare mahaifyata aynxu ba babu tantama saita tsinemin albarka
,nasan tanemeni harta gaji duk dama nasan itade damuwarta kudine ba mutuncina ko lafyata ba bada son raina na rabu dasu ba, ynxu ma na fitone sabida na samu wani abu wanda zan cigaba da tura musu kudi komi kashinsa dan su na ci suna sha da shi. Yarane dayawa agaban mamana, they all depend on me wallh bansan inda zanje na fadi damuwana a saurareni batare da anyagamin mutunci na ba.
Cikin yanayin tausayawa
Halisa tace its okay fadila,bakomi..But do u want a business or a job???
Tace duk wanda na samu
Maam, Inde har zai taimakawa rayuwata zanyi shi, sedei zanfi son business din sabida banason sanadiyata wani abu ya shiga tsakaninki da anty Amina.
Cikin kyabe baki Halisa tace dont worry abt that zan duba naga wanda yafi dacewa dake. You will be fine okay???
Godiya sosai fadila tamata sai batace komi ba tay ma uztaz hannu ya karaso..shikansa ya sha mamakin ganin fadilar musmmn ma dayaga yadda fuskarta ya dan haura tsabar kukan dataci.
Baice mata komi ba ya dube halisa yace yes maam.
Tace ummm uztaz.
Kabata private email ina, she will submit her curriculum vitae(CV)
Zan duba nagani duk abunda ake ciki sai ka gaya mata.
Aladabce yace yes ma
Ta juya ta kalle fadilar dake famar gode mata tace "follow him saiku karasa..and make sure u are ready anytime okay.
Tare da rusunawa har kasa cikin tsansan nuna godiya da girmamawa tace thank u ma. Tana hawaye Tay mata wasu yan adduoi,Kafin nan tabi bayan uztaz sukaja can gefe inda ya amshi sabon numbarta,ta amshi nashi da email din halisan..sann ya je motarsu ya bude ya dauko bunch din five hundred naira notes ya bata 30 thousand naira aciki kyauta.
It means alot to her abunda suka mata ayau.
Tunda tabar wajen hawaye take tana tafiya ahnkli kwakwalrta cike da mamkin yadda rayuwa yake a murde wata rana mutanen da kake sadaukar da komi akansu sune da zasu tozartaka su walakanta ka wasu kuma acan da basu san ka ba sune zasu rufa maka asiri.
Dama can da 20k ta tsira wanda rabi ya karene a biyan kudin hotel da cin abinci. Karshe ma da kudin nata ya kare wanke wanke take a hotel din ana bata abinci wanda ya dada sawa taji aranta dolene ta dau fansa akan meenal talba kota halin kakane. Saidai Ta nemi aiki ako ina amma anki daukarta sabida gulmace gulmace da sharrin da meenal ta dinga bazawa akanta na karuwanci da na batun mutuwar baban ta agidin mace.
sosai ta zubar mata da mutuncinta a idanun mutane dayasaka babu wanda yakeso ma yay tarayya da ita.
Koda ta koma matsuguninta tunanin rayuwarta kawai ta dingayi..duk dama maganganun halisa yay tasiri a zuciyarta amma in her heart tana da wann babban buri na nunawa meenal talba cewa ita ba komi bane arayuwa...
Tana burin kaskantar da meenal tareda koya mata hankli acikin ruwan sanyi
Sauka tay daga kan gadonta ta bude jakarta ta ciro wasu files data lullume su acikin wani jaka tare da flash drive aciki. Akoyaushe inta kalle wayann abubuwan jitake aranta kamar rayuwar meenal din ne duka a hannunta. But no body will begin to knw why harsai ta cimma burinta akanta.
Ata dayan fannin kuwa wkends din nan gabaki daya shemau tayi planning tayi spending dinsa ne tareda Meenal talba tunda vicky tace musu batajin dadin jikinta already kuma sunsan halisa tana shirin komawa office bazata samu lokcinsu ba.
Ba wani abu zasuyi a wkend din ba face holewa suji dadi, sun gama shiryawa zuwa body shop, exclusive spa da shopping na kayan kyale kyale. Washe gari sunday kuma zasuje gym ne sudan motsa jiki.
meenal tanason ta huce dumbin stress tare da haushin datakeji akan koma bayar da business dinta ya somayi.
While shema'u kuwa so take ranar monday ta fito tana baza kyalli sabida ranar ne zasu je abuja wajen babban taro.
Mijinta engr Mahmud na can yanata presentations ba dare ba rana yana kkrin neman babban contract da zai samar mai kudi danya kashe mata kamar yadda takeso dan tun ranar data fara masa walaknci da gori bai sake samun kwanciyar hankli da nitsuwa aransa ba
Tun ran juma'a da ya fita agidan bai dawo ba kuma bata nemesa ba. yanacan ana fafatawa dashi acikin manyan enginiyoyi Da kyar da wuya ya samu aka jefashi acikin consulting team ahaka ma an bukaci yay final presentation na proposal plans dinsa on monday mrng.
Lokcin kansa baida shi dan kkri kawai yake yaga yashirya komi ta inda baza'a samu wata matsala ba. Ya kammala meeting dinsa kenan zai dawo gida yaji wayarsa tay kara alaman sako ya shiga ciki.
Cirowa yay daga aljuhnsa with a deep sight of relive dayaga lambar shemau akan screen ta turo masa sako.
Murmushi yay batare da yasani ba cos it means alot to him dayaga sakonta gabaki daya ya dauka cewa dan bata gansa tun jiya bane yasaka take nemansa ynzu.
Da murmushi ayanayin sa yashige cikin hadadden farar motarsa harsaida ya zauna sann ya bude sakon.
Ba wani gaisuwa bakomi durus ya tsaya da idanunshi akan few words dinta dat look soo mean and comanding
Ta rubuta "mahmud kudi nake so zanjeni shoping da spa. Do Send it right now im going out with my friend amina and pls u can't embrass me with the amount kasamin abunda zai isheni basai na cikaba....
Ajiyar zucya ne ya kufce masa dan Baisan ma ya akayi mood dinsa gabaki daya ya sauya daya karanta sakon ba.
Nevertheless, he shake it off. Cikin nitsuwa ya dauko dayan wayarsa kirar samsung ya bude
Ya shiga mobile app ya saka 8million naira ya turo matashi akan lokci
Yau asabar Wajajen karfe 10.am na safe Lkcin shemaun tana zaune akan vanity chair tana
Kwalkwale fuskarta da make up sai ganan sakon mahmud din ya shigo..tunda ta leka taga alert ne sai ta cigaba da abunda takeyi. Har saida ta gama zana girarta yay masifar kyau kafin nan ta dau wayar da saibin jiki tana jan tsaki ta bude alert din taga 8 million
Rau da idanunta tay ta zuba wani takuraren tsaki
Yanxu fa da ire iren mijin su hadiza ne wann saidai abata na siyen pants ko ice cream da saidai aga miliyon kmr talatin ko ma fiye but her husband is here giving both spa and shoping money a million takwas mtscheww.
Tanajan tsaki ta bude sako tahau rubuta masa
With details explanation of amount din datake so
Mahmud na fama da traffic ahanya sakon nata ya shigo ..babu godiya da masifa ma ta tareshi
Whats is the meaning of what u sent me..wann wani irin rainin hankline dan kudin shopping din ma dana tambayeka saika walkantani akai.
My spa service alone is six million, 2 million din daya rage kuma ko jaka bazai siyamin ba..nide kawai kasan yadda zakayi idan ba hakaba ka dawo kawai muyi magana inbazaka iya kulawa dani bane ka sakeni inkama gabana ana dolene?
Yana kammala karanta sakon nata instantly yaji zuciyarsa ta dau zafi..
Duk da haka bai dau lkci ba yay hakuri ya kara mata wani 8 million din akai. But ques what? Tun da ya tura mata bata kirasa ba, baiga wani sakon godia ba. Sai ma gututturen tsaki data ja.
Haka ya dawo gidan nasa agajiye, zuciyarsa bata masa dadi ko kadan ga yunwa datake damun sa sosai still bai samu shema'u agidan ba.
Already meenal talba tazo harta dauketa sun fita izuwa inda zasuje holewarsu.
Ata fannin Vicky kuwa wkends din nata gabaki daya a zuwa church kawai yakare karfe 10 na safe take fita taje ayi sevice ayi komi da ita bayan angama saitana samun tattaunawa da pastorn ta akan matsalar aureta da femi.
Gani take abunda kkrinta bazai iya bata ba Allah ne zai magance matashi.
Tana da kudi dan haka ake bata kyakkwan tarba church din.
Nan da nan aka hada mata prayer session
Har daren asabar din tana cikin church inda
Aka hada manyan prayer warriors suka zagayeta suka mata adduoin deliverance to ward off any evil spirit and energy thats destroying her marital life with femi.
Daya daga cikin sisters dince dake tana da baiwa sosai bayan angama adduar tajata gefe tanamai bata shawara akan cewa ta kawo mijinta church dinsun for deliverance sabida taga wahayin cewa shine yake da babban matsala a rayuwarsa ba ita ba.
Duk dama Victoria tasan matsalar bazai wuce na rashin haihuwa bane amma yanayin da matar ta fada mata acikin nuna tsauyawa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 40 Chapter of 44