Share this page
da halisa agidanta tun safe. Dan Tun bayan musayar yawu da suka danyi sa halisa akn farida a office dinta ranar sai basu kara samun daman yin wani doguwar hira tsakaninsu ba. Gashi ta gama tara makirci aranta duk ta rasa wanda zata kawo masa kukan mijinta a wajenshi ya goyi bayanta inba halisar ba. Ana kammala shiryata ta dauki clutch purse dinta a hannu ta fito nan da nan driverta ya kamo hanyar gidan hadiza da ita almost the same time suka taso da shemau marafa dake tahowa ata daya bangaren ********** Kafin nan Dagata dayan bangaren engr mahmud kuwa yana sharo kwanan gidan mahaifyarsa ko shigewa cikin mansion din bai gama yi ba wayarsa ya fara kara,bai dauka ba har saida ya kammala parking motarsa acikin gidan sann ya dauki wayar yana ganin abokinsa ne dake can jigawa dayabar masa amanan case din hafsat saida yaji kirjinshi ta dan buga da fargaba, cikin basar da hakan ya dauki kirar muryansa ba yabo ba fallasa yace salam alaikum Alhaj aliyu barka dai.. Dagata dayan bangaren aka amsashi da fara'a bayan sun gaisa yace mishi "mahmud gani nan na iso asibitin zan duba masu jiki..da mamaki engr mahmud yay murmushi yace ahhn da wahala haka aliyu??.yace bakomi ai ɗa na kowa ne jiya dakaban labarin yarinyar nan naji tausayinsu sosai nace tunda nayi tanan ai gara muzo muma musamu ladar nan da kuke samu. Murmushi yy yace toh let me call the doctor sai ashigar dakai ciki and pls inkaje saika kirani awaya ka hadani da ita yarinyar ..yace toh ba matsala. Daga nan suka katse wayar alhj aliyun ya sauko ya shiga ciki. Yana daga reception ko wani minti biyar baiyi ba aka zo aka masa jagora har izuwa dakin da su hafsan suke duk dama batasan shi ba amma bakaramin girmamashi tayi ba Tausayi ta bashi ganin ta yar yarinya karama amma babu kowa nasu agangan dasu, banda zare ido babu abunda takeyi duk ta kasa saka abinci abaki duba da lkcin anata kkrin shirya mahaifyrta izuwa dakin theater ne. Likitan ne yakema alhaj aliyun bayani na cewa agwaje gwajen da suka mata sun gano cewa harda appendix acikinta sann cutar typhoid ya riga da ya kusa tsinka mata hanji dolene su fedeta su san yadda zasu ceto ranta cikin gaggawa. Shi yay ma hafsa jagora ta saka hannu akan takardan operation din tanata kuka dan akauyen su cemusu akeyi insun saka hannu akan takardan asibiti ai tamkar da sun sayar da rayukan iyayensu ne abanza. Sosai hafsa ta tsorata ta rude gabaki daya sai da alhj aliyun ya fahimtar da ita muhimmncin yin aikin kafin nan ta nitsu. Tun da aka shigar da mahaifyarta ciki bata samu ta zauna ba tana tsaye da dumbin fargaba aranta. Bayan kamar minti goma sha biyar dakaita ciki can saiga kawunta mudi ya iso faca faca da wata tsofaffiyar malum malum dinsa jikinsa duk datti. Halinka da bakauye Ko gaisheda alhaj aliyun baiyi ba ya doka ma hafst din kira ta waigo tun daga can ya mata hannu ta karaso inda yake Da mamakin ganinsa ta tsuguna har kasa tana mai cewa kawu mudi ina kwana sannu da zuwa Kallon banza ya bita dashi daga sama har kasa batare da ya amsata ba a masife yace ina mayyar uwarkin nan take da ita zanyi badake ba...yabi asibitin da kallo "waida da kudin uban wa kuka zo nan asibitin, wato rubutun da ake karba wajen malam gardi bai isheki ba... ja ira mummuna saida kika kawota wajen macutan nn da suke lashe kudin jama'a kamar jinin maita. Jikinta a sanyaye tace kawu bani na kawota ba kuma An riga an shiga da ita dakin theaater... Cikin datsar nunfashinta da Baki bude yace sallallahu sanyi kalau wato haihuwa ma zatayi shiyasa kika gudo da ita cikin gari asibitin kudi dan karda asirinku ya tonu Ashe abun kunyar nata har yakai hakane to Waye mijin data aura bamusani ba ko karuwancin data saka agabane yau zai hallakata. araunnace hafsa tace umma na bata da wani miji ciwon afendis akace na damunta shine za'a cire mata shi aciki. Tare da banka mata wata uwar harara Yace ke kikasan wann karyan makira munafiki mai baqar jini meye kuma Afendiris? ..yo waye baisan taɓarancinta ba, inba dan shegen satar data koya miki a binni ba yaushe zan ɓata lkci nazo inda take bari na damu daku bayan kowa yasan itace mayyar data cinye mana dan uwa yo inta mutu ma bamu da asara,...can ta matse muku... kaikayi dama dolene ya koma kan mashekiya... Kuka mai sanyi hafsa ta fashe masa dashi batacemai uffan ba dan tasan wani alheri bazai taɓa kawosa inda suke ba saicin mutunci da cutarwa. Ganin hafsa na hawaye sosai yasa Alhaj aliyu ya matso ta inda suke yace ma mudi malam kai kuma daga ina haka? Mudi yakarewa alh aliyun kallo daga sama har kasa ganinsa babban mutum yasaka ya dawo da muryansa dede misali agidadance yace ni Sunana mudi, ni kawun hansatu ne nine nake bin ubanta kaikuma wayene. Alhaj aliyu yace toh sannu malam mudi Amma saika bita ahnkli ai yarinyace tana cikin tashin hankline yanxu. Bai amsashi ba ya dauke kansa yana kukkuni cikin wuyarsa yana cewa wamu ne za gaya wa hankli? Ai babban rashin hankli bai wuce ku dakukay amannna da wann wajen domin neman waraka ba bayan Allah ya riga da ta zuba mana magunguna awajen almajirai mtsww. Duk kukkuni dayay alhaj najinsa baice dashi komi ba ya kama hanya yahe waje ya zauna yana jiran afito da ita ta zantar da abunda ta kawosa snn ya kara da gaba dan rabonsa da rike dubu biyu nakansa ma bazai iya tunawa ba bare dubu goma ji yake ko kashe ta akace yay akan dubu goman nan zai iya Ata fannin vicky tana isa gidanta wanka ta faɗa sharp sharp ta fito tay kwalliya ta gyara suman kanta yay kyau sosai tabi ta dauko wata figigiyar party dress dinta white colour sharara mai fallen neck ta saka ajikinta da farin purse da jaka sai wani tsiririn abun wuyan red diamond ta saka a wuyarta. Bata dauki wani driver ba ta dauki farar motarta a inda suke parkesu, kirar RR mai aji ta ja kanta izuwa gidan hadiza daga kasa har sama all white tay bakaramin kyau shigar ya mata ba. Kusan lkci guda shemau da meenal suka isa gidan hadiza inda suka samu har angama decorating babban garden din gidan da abinci kala kala da kayan shakatawa na zamani acan ta baya inda bbu wani hayaniya wajen yay wani irin kyau kamar wani babban hidima zasuyi....TO BE CONTINUED SHARE PLEASE [2/3, 9:05 PM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB...*_ _(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_ #ROMANCE #FICTION #ADULTHOOD #SEXADDICTS #WOMENPOWER BY _SURAYYAHMS_ _08060712446_ ⏯️2️⃣7️⃣ 3:pm na yamma hadiza maitama ta kammala shiryawanta ta taho waje a inda kawayentan suke nan a zazzaune. wani irin nishadi yau takeji acikin ranta, musmmn inta tuna yanayin yadda rayuwa ya ke neman sauya mata acikin dan kankanin lkci. Dan Ko a mafarki batay tsammanin cewa hidimar su da hjya ramatu zai iya juya al'amari harya sauya mata wani bangarena mugayen halayyar mijin nata ba,yaudin tasha kyakkwan mamaki da alhaj kyari ya zage tare da nuna mata cewa ya girgiza sosai da lamarin da ramatu tazomasa dashi na tsafi da yaudara wanda hakanne yasaka yafaraji aransa cewa lallai hadizarce mace na asali datake kaunarsa tsakani da Allah badon abun hannunsa ba. All the love and care she was looking for azaman aure wanda bata samu ba adacan saida yau ta sameshi awajensa tasha tarairaya da rarrashi snn ya tsaya ya saurareta yaji dukkan wata matsalarta snn yay mata alkwarin gyarawa. Yaune karo nafarko da ya barta agida ya wuce business trip dinsa acikin dadin rai sann yana isa S.A din ya kirata ya sanar da ita cewa ya isa. Duk wani abun duniya da ya damka mata jiyan a sanadin rarrashi bashine damuwarta ba bare har ya sakata acikin wnn farinciki datakeji yanxu,.. iya wann sauyawar nasa izuwa namiji me kulawa da matarsa yafiye mata komi wanda shine ya saka ta kira gaggan kawayenta na amana dansu zo sutayata farincikin da ita kadai ta barwa kanta sirrinsa acikin zuciyarta dan hatta shemau datake iya gayawa komi tay bata fetsa mata zancen cewa alhaj yana neman sauya musu rayuwar aurensu ba. kwalliya aka tsantsarawa kyakkwar fuskarta na kece raini,tay masifar kyau gameda wata sassanyar nishadi dake kwance akan fuskarta yanamai karama kyaun fuskarnata annuri mai ratsawa hartacikin zuciya da gangan jiki.. Tahowa take ahnkli tana murmushi designer dress data saka ajikinta irin Draped gown din nan ne marar nauyi na kamfanin jeager le coulture red in colour da swavroski stones work ajiki ,rigar me fallen neck ne amma jelarsa har kasa yake binta yana bazuwa tana tahowa dei dei kamar wata hamshakiyar sarauniya hannunta da wuyanta sai wal wal sukeyi da tsadaddun gwalagwalai. Lkcin da ta isko kawayen nata ata inda suka shirya hidimar tasu gani tayi babu abunda yake tashi atsakninsu face musu da surutayya na mata nayau da kullum. faffadar murmushin datake sakewa acikin ranta shine ya fito fili dan ganin su datayi ahakan cikin nishadi yasata karajin wani sabuwar farinciki marar misaltuwa acikin ranta. tun xuwarsu meenal da shema'u gidan halisa take tare dasu..,vicky na karaso kuwa suka cika dedei and since then it has been Banters here and der ana ta tsokanar juna ana kankaro hira na nishadi wanda zaka iya rantsewa sun jimane basuga junansu ba. Tsayawa cak hadiza tay daga dan nesa tanata kallon irin soyayya da aminantaka tare da nishadin dake wanxuwa atsakaninsu ayayinda suke hira mai ban dariya. Yadda suke bawa bukatun junansu na rayuwa muhimmanci yasaka duk suka aje abubuwan dake gabansu sukaci kwalliyar kure adaka kowa tay kyau tazo gidan domin amsar kirar hadiza duk dama basusan dalilin wann karamar shanawa da ta haɗa musu ba. They All look soo beautiful meenal talba acikin peach colour jumpsuit dinta tun zuwanta ta makale kusa da babban aminiyarta halisa mansa data saka wata hadaddiyar black color cascade mini gown na versace dabai kai kan gwiwarta bama tun da suka zauna tambayar halisan kawai takeyi gameda batun lafyarta duk tabi ta damu, wani bin har tausayinta halisan takeji dan yadda take nuna ta damu da ita sosai zaka iya rantsewa cewa babu wata wanda take sonta da amana kamar meenal arayuwa. shema'u marafa data saka hadadden golden colour valentino garavani dress dinta up and down riga da wando wanda ya fidda hour glass shape din manyan duwaiwakan ta,tun da tazo bata zauna ba dan ayadda takeji da hadadden dirin jikinta wanda tamkar itace kim kardashian wajen shape. Tsaye tay agabansu tanakan basu labarin dalilin dayasaka bazata taɓa yadda ta haihu da mijinta engr mahmud ayanxu ba. Acewarta haihuwa da shayarwa suna lalata siffar mace dan haka batason dirin da Allah ya bata take murzawa ya lalace da wuri bare mijnta yazo ya fara reinata dan tun da aka haifeta tazo duniya kallon matar manya kawai take ma kanta. vicky dake tsaye agefenta sam bata amince da wann ra'ayi nata ba, dan haka suka ta rusa musu atsakanin su.. dake ita haihuwar ne ma yake shiga tsakanin ta da uwar mijinta cewa take itakam koda siffarta zai lalace ta dawo mei shape din Amoeba ne inhar Allah ya kawo mata haihuwa zata amsheshi da hannu bibbiyu sabida ƴaya albarka ne na musammn daga wajen ubangiji. Kamar yadda Meenal ke bin bayan ra'ayin shema'u akan haihuwa kai da kafa haka halisa ma take bin bayan ra'ayin vicky sosai sabida halisa sosai take son yara duba da taso ne itakadai bata da wani dan uwan jini. wanda musun nasu ne ya jawo surutayya mai yawa wanda har baka iya jin muryan kowa awajen. saidai hirar tasu ce gwanin ban Dariya,dan a sigar hira ayi nishadi kawai sukeyinshi kowacce Acikinsu na fadin ra'ayinta ne kawai batare da wani manufa ba. As usual meenal na shiga cikin maganan ne amma sam bata iya fitowa fili ta fadi dalilin bin bayan ra'ayin shemau marafa datake yi saboda aranta ta riga tasan cewa ita da mahaifyarta sunyi agreement akan bazata haihu da mijinta Dr khaleel ba sabida batason taxo ta mutu khaleel din ya gaje arxikinta adalilin abunda zata haifa snn ya auro wata macen su more arzikinta tare. Ji take da ace ta mutu khaleel ya mallake dukiyarta gara shi din ya fara mutuwa yabarta a duniya inyaso ita ta mallake harda nashi arzikin.. Shema'u kuwa har da yaran ma ta tsana, gani take kamar a child is a burden, haihuwa ai takura kaine kawai,..ko gaisuwa taje daga an mika mata jinjira sai kaji tana cewa "no please babies are messy"hardly kaga shema'u ta dauki dan wani ta rike a hannunta wanda shiyasa sam batasan darajar yaran da ake kawowa dan suke mata aiki ba. Ana cikin surutun nan halisa ta hango hadiza acan ta makale a hanya da hawayen farinciki taf a idanunta at same time tanata murmushi... shirya mini girls to girls date iya yasu yasu kusan dadaddiyar Al'adace data zame musu jiki a tafiyar click din nasu sau tarin yawa sukan shirya ire iren karamin meeting haka domin su baja kolin damuwarsu ko su tattauna wani labari na farinciki kona cigaba ko kawai dan hutawa ko a tattauna wani abu mai muhimmanci daya shafe kawancensun musmn ayanzu da suke kallon kansu kamr yan uwan juna. Miƙewa halisa tay tana murmushi taje ta jawo hannunta ahankli suka karaso cikin filin dayagaji da hadadden gyara, nan da nan hanklin sauran kawayen ya dawo kanta suka mimmike tsaye suna murmushi har saida halisa ta karaso tsakiyarsu tare da ita snn ta saketa Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke a tsakiyarsu sann tace you look amazing girls..duka suka amsa da murmushi vicky tanamai cewa we cant wait to hear the good news dan harsashe takey a mind dinta ko ciki hadizan take dashi!!.. Shemau tay kamar bata san komi ba. Murmushi hadizar takeyi snn ta umarce maids suka kawo kala kalan drinks a dump waiter dan kowacce ta dauki kalar abunda take sha. Shemaun ce ta saka hannu ta dauki glass din Mojito mai sanyi ta fara sha,hadizar ta dauki na margrita, piña colada halisa ta rike snnn ta zuba blocks din kankara aciki, snn meenal talba ta dauki chilled manhattan and lastly vicky ta dauki glass of martini duka suka zubawa hadiza idanu suna masu sauraran abunda zai fito daga bakinta ganin she looks really happy nevours and emotional at same time. Cikin lumshe ido da budewa tace okay guys Abu biyu nake son na sanar da ku..na farko marar dadinji ne, na biyun kuma sabanin haka.. Kallon juna sukayi duka Kirjinsu na dan bugawa banda shemau data dan ja baya tanata shan drink dinta ahankli. Halisa ce tay gyaran murya kadan snn tace toh da me dadinjin zamu fara ko?... Vicky tace noo halsy. Negative befor positive dai..whats up hadiza whats bad?.. Meenal da shemau basu ce komi ba. Ahnkli meenal din takai drink dinta baki a kwakwarta tanata nazarin shin wani abun baqin ciki kenan da har hadiza zata kirasu duka ta gaya musu while she is still smiling ita da tasan hadiza da rauni da kuma saurin karaya??? Saidai Ko kammala lissafin nata a mind dinta batayi ba cikin sauke ajiyar zuciya Hadiza ta dubesu su ukun snn tace Vicky,meenal, halsy mijina ne yay aure jiya kuma.....Tunma bata karasa idda kalaman ba Abazata meenal tay Wani tufffff da qarfi ta fetso da drink din data kurba waje tare da dago kanta sama in shock tanamai kallon bakin hadizar looking confused kamar bataji abinda tace da kyau ba.. Hannun vicky harna rawa ta matso kusa da hadizar a sigar i dont quiet get you well,suna hade ido da halisa kusan atare dukansu uku suka ce .. "Hadiza kkce mijinki ya miki kishiya? Shemau dake tsaye bata motsa ba Kamar zatay dariyar tune din da suka furta hakan dashi amma ta fuske jin Hadiza Tace 'yes..wani irin nunfashi meenal taja snn tace tabdi jam...Juyowa hdzar tay ta kalli shemau snn tace shemau is aware of it cos i called her.. ..banason na daga muku hankli ne shiyasa.. Cikin katseta da masifa vicky tace"..No hadiza. Wann ba magana bace i mean Matsalarki ai matsalar mu ce akan me zakice haka??? Kishiya gatsau haka sai kace wani almara? Halisa ta tsaya in silence batace komi ba danji tay kamr kanta na juyawa. haka kawai ta tsani taji duk wani mummunan labari da zaina daga mata hankli ko ya saka mata damuwa dan muddin tafarajin hakan to atake ciwon depressiin dinta yake dawowa mata kamar sabo a brain dinta sai taji hanklinta yana tashi sai kuma tafarajin kmr batajin dadin komi. Kacokam meenal ta aje drink dinta akan table jin tarasa taste din bakinta gabaki daya dan arayuwarta gani take kamar cikin kawayenta duka babu wacce bata fi karfin ayi mata kishiya ba bare kuma ita. Yo me namiji zai nema awaje inhar ya aure daya daga cikinsu? Gani tay Suna da kyau, ga diri, kudi, suna da kuma muhibba acikin sauran mata. cikin sassarfa ta karaso ta dafa kafadun hadiza datakeji kamar ta mata kuka snn tace babe wai wacce shegiyarce ta shigo gidanki kuma yaushe aka shirya wann abun da bamu sani ba, this is an insult to all of us ..to wabillahillazi sai munyi waje road da ita dan gidanki ba gidan zamanta bane . Hadiza zatay magana cikin katseta shemau tace guys calm down mana aii ni zan muku bayani, but first mu zazzauna tukuna. A mugun sanyaye su ukun suka zauna dan lkci lkci guda annurin dake yawo akan fuskokinsu ya dauke cak kamar an walkiya an dauke. Cike da salon lauyanta magana shemau ta kirkiro part din datake son sujin tahau gaya musu shi acikin sauki Dede wajen da ramatu ta tonawa kanta asiri tare da saki uku da alhaj ya dankara mata a daren farkonta iyashi kawai ta gaggaya musu shi. Sauran zancen kuma duk bata gaya musu ba dan batason suduka su san cewa itace takai hadiza gidan malami sukayi wani abu Na tsafi sai kawai ta nuna musu cewa asirin ramatun ne kawai ya tonu sabida hadiza bata da haqqinsu wanda Kasancewarta kwararriyar lawyer shiya dada sakawa lkci guda kowa acikinsu ta amince da zancen nata batare da wani tantama ba... Tunda maganan ya fito fili wani sabuwar surutu ya kaure awajen kowa na fadar ra'ayinta as usual shema'u da meenal sune masu nuna cewa sun mugun tsanar kushiya dan haka su sukafi kowa zage zage da dariyar mugunta. Hadiza na basu sauran labarin yadda abun ya wakana da aka cicciro kayayykin tsafi ajakar ramatu Abun al ajabi amma dariyar mugunta su biyun sukadingayi suna shewa suna tafawa. Vicky was busy wajen tausar zciyar hadizan tare da dada bata haquri da kalamai masu sanyi ayayinda zancen ya rikikita ma halisa hankli duk tunaninta shine yadda ramatu ta shirya wnn mugunta kamr bazata mutu ba sai taji ta kara tsorata da lamarin duniyar gabaki daya "Hmmmm Hadiza tay kkri fa.. Ai randa mahmud ya kuskura yace zaimin kishiya wallh rabuwa dashi zanyi inje cahn in nemi mijina tun ma kafin ta shigo gidan dan banason rainin wayo wann ai raini ne... Shemau ta fadi hakan cikin nuna isa tana jujjuya kai cikin bunkasa da kadadi . Cikin kyabe baki Meenal tace Tab di jam..ke shema wani wargin ma waje yake samu. Duk fitinan uwar mijina akan cewa batasona ai kinga bata isa ta kawo masa mace tace ya aura ba bayan ina nan ba bare shi kuma..ai Inkinga khaleel yay aure to ni Amina ali talba na nabar masa duniyar ne amma muddin ina raye wallh bai isa ya auro wata macen ba. Vicky dake rike da hadiza tace u guys pls banda cika baki dai kar azo ana amai ana lashewa. Halisa batace komi ba ta dauki taɓarta ta kunna ta zuka ahankli dan gani take kamar har ta mutu hala bazata san dadin soyayya bama bare tasan me akeji in mijinka zai kara aure. Cikin share zancen vickyn, Meenal tace guys This actually calls for a celebration...wallh naso ace ina nan akayi draman nan badan komi sai dan inga shegiyar tana hauka.. Shemau tace abeg her chapter is closed... "good riddance...Vicky ce ta karasa mata da cewa "to bad rubbish!!! hahahah suka fashe da dariya mai karfi. Sautin wakar hadiza yar gidan malamai shemau ta saka music player dake wajen suka jawo hadixar tsakiyarsu suka zagayeta suna rawa da jikinsu suna mai mata wakar suna tafi suna balain zugata aciki.. Kai mata! A rike darajar aure da kyau, A bar hushi da ikon Allah, Dan ikon Allah ya wuce hushi. Lale Hadiza lale lale Hadiza yan malamai Kun ga Hadiza ta burge ni, Ina cikin yawo na, na ga Hadiza ta burge ni Kun ga Hadiza ta burge ni, Yara suna kiranta amare mata suna kiranta amare, Ni ina cikin yawo Na ga Hadiza ta burge ni Na aure diya ta amare Lale Hadiza lale lale,Hadiza yar malamai Kun ga Hadiza ta burge ni,Ko wa taba Rakumi shi ga hauka, Jaki bai kula da bugu ba, Ko wa taba Rakumi shi ga hauka Jaki bai kula da bugu ba Lale Hadiza lale lale Gyara gida Hadiza Duk naki ne Gyara wuri Hadiza Duk naki ne Gyara mujinki Hadiza Duk naki ne Toh ladabi biyayya Duk naki ne Ba ni ruwa Hadiza Sai ta durkusa Ba ni hura Hadiza Sai ta durkusa Ba ni tuwo Hadiza Sai ta durkusa Ruwan wanka Hadiza Sai ta durkusa Gyara gida Hadiza Duk naki ne..... Lokcin da suke rera mata wakar suna zagayeta Zuciyan ta tarr... Wani nishadi ne ya mamaye ta Ganin yadda kawayen nata sukayi spicing din wakar dan har kasa meenal da vicky suke kaiwa wajen rausayawa Shemau tana rausaya kanta na kaduwa kamar tsohowar kadangariya Chan halisa ta dada kunna hayakin tsadadden tabar marlboronta ta hadashi da shisha pot ta bula masa wuta tana busa shi yana fadada hayaki dan ita bata wani fiye son hayaniya sosai ba. Wajen gabaki daya ya dau zafi da nishadi sautin wakar tana wani irin buguwa a speaker da sunan hadiza evrywher is giving all the vibes na big babes celebrations. Bayan nan Aka bude shafukan ciye ciye, an sarrafa namar kaza dana tolo tolo ga shawarma da sinasir, sushi, salad da small chops, ana ci ana babbaka dariya akan lamarin hajy ramatu da kusan ince aynxu ta zama tarihi a hannunsu. Meenal was extremly proud of yadda hadiza ta zama sanadiyar kawo karshen gagarumar matsafiyar can badan komi ba saidan hakan zai karawa wa clique dinsu daraja a idanun manyan mata bana wasa ba. Duk wata hamshiyar yar iska irinta idan taji labarin cewa clique din sune suka kawo karshen ramatu dolene a basu darajawa ta musammn acikin taro. To make the date very meaningful yasaka hadiza ta kawo wani karamin words games inda kowa zata bada random advice and motivational quotes. Bayan sun kammala cin abinci sun koshi Akan wani shirgegen turkish capert awajen haka suka zazzauna vicky ce zata ta rubuta sunan kowa ajikin paper sai ta watsashi akasa wanda ya riga bude nashi zai kira sunan wanda yake ciki sai yazo tskiya ya bashi word of advice ko motivation. Karon farko ana wurgawa akan uwar gayyar ya fado,hadiza tana bude nata papern taga sunan shema'u ne aciki. Vicky ta kalli shemau tace ki zo tsakiya ki gayama hadiza one Word of advice or motivation Babu tantama shemau ta taso ta iso tsakiya tana fuskarta hadiza datake zaune.. Alokacin babu abunda yake yawo a akwarwlta face kishi da kuma kaico. Dan bansan yadda zan fassara muku radadin yadda takeji aranta kamar qaddararta ne hadiza ta sace mata a duniyan nan ba. Lumshe ido tay sann ta bude tace "Dear hadiza, i will give a word of advice: "Hadiza tana murnushi tace am all ears. Sihirtaccen ajiyar zuciya shemau ta sauke snn tace "Cin amana baya taɓa zuwa daga wajen makiyi sai masoyi. Cos Friendship's demise, is a tale of shifting tides."but alwys rembr dat Betrayal is an inherent part of love!!!. Tafi wajen ya kaure da shi jin kalaman shemaun ya burgesu.... banda hadizar data tsaya shiru cikin sakin murmushi a mind dinta tanamai kkrin fahimtar sakon da shemaun ta jefa mata acikin maganan nata dan magana ce a dunkule wanda yake nuna alamar cewa da akwai sauran rina akaba. Murmushin dole kawai takeyi tana cewa thank u amma badan ta fahimce komi ba dan Har shemau ta koma wajen zaman ta zauna hadiza bata dena nazarin kalamanta ba..,tsoro takeji Kode shema'un tasan wani abu akan mijinta ne and she is hiding it from her ko kuma hala kawai shawara take son bata akan ta kula da zuciyarta sosai musmmn wajen trusting mutane. Ana sake juyawa game din sai takardan ya

Chapter 30 of 44