Share this page
da ita. mafi kyawun abin da ke tattare da Mutuwa shi ne cigaba da rayuwa tare da ubangiji da tawakkali. Dan haka ki miƙa damuwarki zuwa ga shi snn kiyi murmushi kice ma zuciyarki cewa zaki iya jurewa. Leave upto the expectations of ur God zaki samu nutsuwa a zuciyarki sosai, dan duk abin dakikaga kin samu a duniya ki tabbata rabonki ne, duk abinda baki samuba to haƙiƙa ba rabonki bane, ke dai ki jijirce wajen ganin cewa iyayenki da suke can suna alfahari dake ynxu. Jin maganan nasa ya dan shigeta yasaka ta sauke sihirtaccen ajiyar zuciya batace mai uffan ba. Wajen zamansa ya koma ya zauna snn ya dauko wani karamin littafi ya mika mata gabansa an rubuta some powerful pyschology tricks by Dr asim khan, snn yace Try and read this book akai akai duk lokcin da kikazo kwanciya da kuma in kin farka daga bacci...lets bet... u will find ur parents talking to u inside of this book. Batace mai komi ba Ta masa kallon irin really? Tare da kureta da idanu yace Its a bet ki gwada, Ur foremost cognitive behavioural trigger is the thought of loosing ur parent wanda shine yake kitsa miki duk wani rauni da feeling na jin tsoron fuskantar rayuwa ko kin shiga rudani..and muddin kika bani hadin kai muka kawar da wann tunanin to in sha Allah cikin kankankin lkci zamu iya goge dukkan wasu maladaptive negative beliefs dasuke damun brain din ki. Kallon littafin tay tayi karamin smirks snn tace okay thanks.. i will go find my parents words in it.. Kallonta ya dingayi snn yay murmushi yace shikenan ki gwada yin hakan sai gobe ki sanar dani yadda kikaji cos Ders need for us to see tmrw sabida mu cigaba da yan tattaunawa akan wasu abubuwa masu muhimmci. Batare da ta kallesa ba Tace ba matsala.. Cikin sauke ajiyar zuciya yace inbabu wata tambaya zamuyi zaki iua tafiya gobe by this time zamu sake haduwa inba komi. Tace okay, thank u! Tunkan ta tashi Ya miƙe da sauri yana cewa i wll walk u out. Tay karamin murmushi..tunda ta suka kamo hanyar fitowa yake ta mata tambayoyi game da alakarta da tsoron idanun mutane datakeji inta fito waje, wanda yake sawa tanajin kamar duk duniya babu wanda yakaisa saukin kai da tausayi. Har waje gaban motarsu ya rakata ganin yadda aketa kallonta yasashi dada kara kaimi wajen shigar dakansa wajenta da kalamai masu sanyi.. Cikin lallami Ya dingq cewa idan bazaki iya zuwa nan asibiti ba ni zan zo har inda kike and I will arrange a more safer session for ur mental health aikina ne in tabbatar da lfyarki. Tace nagode doctor idan nayi tunani akan haka my sctary will call u... Yana murmushi yace ba matsala sukayi sallam. Daga nan har ta juya ta barshi a tsaye bai iya dauke idanunsa akanta ba... Aransa ya aje tambayoyi masu zafi wanda Bai son yay garajen furta matasu tun ayau amma ganin yanayinta na me saukin kai yasa yaji zai iya furta matasu a gobe. Tun da ta fita tunanin kalmominsan kawai takeyi Batace ma uztaz uffan ba har saida suka bar harabar asibitin gabaki daya Wata bakar motace take bibiyar bayansu ita batama lura ba amma hanklin uztaz gabaki daya naga kan motarne yanamai lura dashi ta glass din motarsun batare da yace mata komi akaiba. Kwalin taɓar ta ciro ta kunna tafara zuƙa ahnkli meenal ce ta fara fado mata har ta dauki waya da niyyar kirarta awaya dan ta tambayeta ko ansame fadila sai kuma tafasa yin hakn taji kawai gara ta tambayeya baki da baki. jin kmr bata sha'awar komawa gidanta yasata tace ma uztaz yabi da ita gidan hadiza kawai ta dubata tunda duk a anguwa dayane da asibitin bawani nisa... Yana juya kan motar wani katoton jeeep baki kirin rufe da tintend yayo kansu da mugun gudu kamar zai ci karo dasu.. A mugun razane halisa ta dago kai ayayinda uztaz yay saurin taka burki a tsakiyar titi, motar tazo ta wuce fewwwwwwww kamar zata turesu ta sha wani coner da mugun gudu acikin unguwar. Tsaki uztaz ya ja yana kkrin ya fitowa da sauri dan ya dauki numbar motar yasa akama musu maishi amma inaaa kafin ya karasa sauka har sun masa nisa iya coner da suka shiga din kawai ya iya gani. Bindigar dake gaban motar ya zare ya saka a cikin aljihunsa zai juya kan motar cikin katseshi da sauri halisa tace pls let it go uztaz...kabarsu kawai zai iya kasancewa barayine lets just move kawai... Hanklinsa adan tashe Yace but maam tun dazu na lura kamar wani mota yana bbibiyar mu..ni inaganin kamar atare suke da wann din we have to knw who they are for secruty reasons. Nervously Tace wani mota na bibiyarmu ne dama? Kafin ya amsa cikin basar da zancen tace am sure they are just thiefs mutafi kawai. Karka kulasu..pls lets go. Ganin ta matsa su tafin yasaka bai kara cewa komi ba ya kunna motar suka kama hanyar gidan hadiza dan aransa already ji yake kamr ya riga daya samu wata kwakkwaran sheda akan mai bibiyarsun dan tun daga asibitin mind dinsa yaketa bashi cewa kamar Body qurds din zach ne snn yasani cewa anan unguwar gidan zach din yake...shan kwanan da sukayi acikin unguwar ya dada sawa yaji cewa kamar hunch dinsa is probably true... zai iya yuwa shine yasaka mutanensa suke bibiyar masa rayuwar halisa a boye. Lissafin daya dingayi aransa kenan har suka isa gaban gate din gidan hadiza maitama. Lokacin har halisa ta kirata waya suna kan magana dan ta sanar da zuwanta, shiyasa isowarsu gaban gate din batare da wani bata lkci ba aka bude musu suka shigo ciki.. Uztaz na kammala parking aharabar gidan saiga nan hadizan ta fito daga cikin main building dinta fuskarta dauke da wani irin nishadi da fara'a tasaka wani kankarrren leshi daya mata azaban kyau ajikinta tay kwalliya tanata murmushin jin dadi kamr ba ita ba. halisa tana saukowa kasa daga cikin motar suka wani rungume juna sosai... cike da farinciki hadiza tace mata I'm sooo happy ure here halisa dama yanxu nake shirin inkira ki awaya dan kece baki online dazu. Jin dadin ganin hadizan hakan yasaka halosa sakewa, . cikin jin sanyi aranta tanata murmushi tace meya faru hadiza whats the gist gayamin mana. Sounding excited Tace..munacan group chat muna shirya party mana. Halisa tace what? Party?.. Shine ban shirya ba nazo aaahhhh bazai yuwa ba, uztaz lets go home naje nima na shirya na cancare buuu so kike the party scatter shemau marafa tazo ta fini kyau suyimin dariya ...Dariya sosai hadiza ta fashe dashi. Halisa bana son shirme, ke aiko bakiyi kwalliya ba kina kyau so lets go in sai gaya miki komi inyaso zaki shirya aciki u knw i have all the brand of cloth u need. Gabaki daya harabar gidan saida ya kaure da dariyarsu hadi da surutunsu.. Hadiza ta jawo hannunta Kenan uztaz yay gyaran murya duka suka juyo suka kallesa Yace "ma'am. Cikin katseshi hadiza tace pls dont talk to her about work she is here to relax,..yau hutawa kawai zamuyi... nan ta juyo ta kalle halisa a shagwabe tace halisa just give him a day off plessse...yau fa babu inda zakije kina gidan nan tare da ni har dare. Halisa tana murmushi ta kallesa tace toh kaji dai my queen has spoken ..just go and enjoy uslf idan nagama i will let u knw... A ladabce Yace yess maam. Suna juyawa yay sauri ya shiga motarsun tareda ficewa acikin gidan agaggauce, wani hanya na daban ya dauka ta inda yaga motocin dazun nan sunbi dan aransa so yake lallai sai ya tabbatar da abunda zucyrsa take zargi gameda zach..... SHARE...[1/31, 8:44 PM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB...*_ _(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_ #ROMANCE #FICTION #ADULTHOOD #SEXADDICTS #WOMENPOWER BY _SURAYYAHMS_ _08060712446_ ⏯️2️⃣6️⃣ Gudu uztaz yake shararawa acikin anguwar har saida ya cimma kwanan da motocin nan da suka kusa bugesu suka shige dazu,yana shiga kwanan yaga wata mikakkar hanyace tarwal agabansa wanda baisan iyakarta ba sai manyan manyan gidajen masu kudin gaske dake nan ajere lane by lane wanda komin kaifin nazarinsa yasan bazai iya fahimtar inda motocin nan suka shiga ba. Hakan bashi yasaka ya rusuna ba dan safetyn halisa ya fi masa komi aynzu,... Atunaninsa inma zach ne ya saka ake bibiyarta to awani dalili kenan zai saka a bibiye rayuwar halisa bayan shine ya soma walakantata. Tafiya ya dingayi akan titin anguwar har saida ya kusa kurewa sann ya nemi wani inuwa ya dan tsaya yana lura ganin har yaci minti goma amma babu wani mahalukin da yazo ya gifta ta wajen dayake. Zuciyarsa sosai ta fara karaya da samun wata mafita Sai can ya hango wata katotowar thatched house agabansa mai kama da babban garejin gyaran motoci tunani yay halako masu garejin zasu iya bashi wani information game da motocin dayake nema dedekun mutane yagani agaban wajen sun fito daga ciki suna tsaye suna magana da junan su kusan kaya iri dayane ma ajikinsu kamar wani uniform. Sauka yay acikin motar da bindigrsa ajikinsa sabida tsaro. Wajensu ya dosa batare da ya bari sun hangosa akan lkci ba.. Yana daf da zai karyo hanyar ta inda suke sai caraf idanuwansa suka sauka akan wani kakkarfan mutumi daya gansa dazu acikin mutanen da ya lura dasu a harabar asbitin da sukaje dazu. Da sauri ya koma baya ya mannu da bangon wajen yana lekosu ahankli dan kar a ganesa, duk sauran yan mazajen da suke tsaye awajen bai ganesu ba amma kuma sosai ya gane wann mutumin dake tsaye. Magana sukeyi awaya amma baiji me suke cewa ba sabida sun dan masa nisa sosai. Yana tsaye awajen har suka kammala maganan nasu snn dayan gayen ya nufi garajin ya budeta gabaki daya,nan danan uztaz ya leƙo wuyarsa ciki tundaga nesa yanata kallon kala kalan motocin dake garejin wanda sunkai guda goma sha biyar a ciki harda motocin da suketa bibiyarsu dazu,Ahankli ya ciro Wayarsa yay videon wajen gabaki daya snn ya maida shi aljihunsa cikin sanɗa ya bar wajen ya je tacan ta bakin titi ya tsaya ajikin wani bango yay kamar fitsari ne ya tsayar dashi awajen har gayun suka zo suka wuceshi acikin wata mota na daban batare da sun lura dashi ba. Tsabar naciya jiyake kmar yabisu yagata inda zasuje wani zuciyar kuma nace masa kar yaje sabida zasu iya gane motarsa inya bibiye bayansu. Karshe haka ya hakura ya kyalesu har suka dan yi nisa sosai snn ya dawo motarsa ya kama hanya ya nufi office domin ya dan duba wasu ayyukan da yau suke dashi... 11:30 am victoria ta kammala lectures ta fito kenan tana sauri zata wuce gaban motarta dan tatafi gida tashirya zuwa wajen casu a gidan hadiza wanda har yanxu basu san dalilinsa ba. they just woke up and saw hadiza in a very happy mood. Altho shemau na sane da duk wani dalilin daya jafe hadiza acikin farincikin da take ciki ynxu amma koda suke chatting din nuna wa vicky tay kamar batasan komi ba. Vicky na fitowa daga aji wani malami ya nemi ya tsareta,acikin sauri yake bibiyarta yana cewa "Excuse me, Mrs femi.... mrs femi... Ahankli ta juyo ta kallesa ganin dattijo ne sosai wanda tunda tazo schl din ire irensu ne basa iya mata magana ta fatar baki.. kai tun tana saukar dakanta kasa tana gaishesu sunakin amsata har tagaji ta dena kulasu gabaki daya. Wani irin haushinta talura sunaji aransu naganin bata shigewa harkan kowa snn kusan babu wani dalibi a makarntan da baisan da zamnta ba. a nitse ta tsaya fuskarta babu yabo ba fallasa snn tace "yess mr Adetunji is evrything okay?.. Wani daure fuska yyi yana kakkauda kai cikin shan kamshi, dattijiyar muryansa ciki ciki Yace yes dama shugaban makaranta ne yake son ganinki for just few minutes if u can spare him. Agogonta ta daga ta dan duba lkci..yanata lura da ita aransa yana Allah Allah tace masa bazata je ba yaje ya haɗa mata manyan sharruka wajen provost din dan abata query snn ahanata hawa kan matsayin special level advisor da ake son abata ynxu inyaso shi ya je ya ƙarba. Mr adetunji haifaffen bayarben ogbomosho ne mai bala'in son kanshi.. Yana da babban matsayi a makarntan amma aransa baiki a karbi wanda za'a bawa vickyn akara masa ba badon komi ba saidan yana son yanasamun extra penny acikin aljihunsa awajen yaran masu kudiin nan. Shide haryau gani yke kamar hukumomin makarntan tsoron vicky sukeji sabida mijinta yana da kudi da politcal connection sosai. Hukumar Makarntar sun zabi bata matsayin SLA ne sabida sunsan kudaden su baya gabanta dan tana dashi mijinta ma yana dashi, dan haka sukeda yaqinin cewa zata iya deliveriing role dinta sosai wajen kula musu da sabbin yaran da za'a kawo makarntar batare da wani scam alert ba. Cikin katsemai tunani tace its okay..i will be der in few scnds. Haushin amsar data bayar din yaji ya juya ko amsata baiyi ba ya nufi office din shugaban makarantar. Batare da ta kulashi ba ta bude motar ta aje jakarta akan seat aranta tanata tunanin dalilin dayasa shugaban makntar ke nemanta dan koma yayane tasan bazata iya cancelling din hidimarta da kawayenta domin ta musu wani extra work a schl din ba. Wani babban office mai dauke da hotunan shugaban kasar nigeria mr adetunji ya shiga wanda basai an gayama ba kasan offishin shugaban makarntar ce. Shugaban makarntar ne zaune a kujerarsa sanye da wata tsaddaiyar suit yana duba wasu files sai wata dattajiyar mata bakar fata a zaune da jakarta a gefe tana mai kallon Mr adetunji daya shigo ciki yanxu.. Yana zama ta matso kusa tana kallonsa sigar son jin gulma da yarensu na yorubunci tacemai how far ina victorian take?... Cikin kyabe baki ya kalle shugaban makarntar snn ya kalleta yace Ahhhh toh tace tana zuwa amma ni banga alaman haka agareta ba dan gaban motar ta nufa,and it seems like she is in a hurry to attend to her businesss. Matar tace ehhn since she is not coming muyi abunda ke gaban mu mana.. Mr adetunji yace ohhhooo ai na fada tuntuni anki jina ne, Dat woman has no business with schl activities, beside she is only doing this lecturing business for fun ko an koreta amkrntar nan ma bazai dameta ba, da an bani aikin nan kawai, me i can manage it. Shugaban makarnta dake famar rubuce rubuce batareda ya kallesu ba yace musu calm down lets give her five more minutes since she says she is coming karmu yanke mata hukunci. Daga nan shiru sukayi basu karacemai komi ba dan babu yadda basuyi dashi ya basu ragamar yaran ba amma sam yaqi.. After like 3 minutes saiga victorian ta iso wajen da dan karamin sallama abakinta ta shigo har cikin office din mr adetunji da matar suka bita da wani irin kallon tsana. Fuskata bbu yabo ba fallasa tace musu Gud morning fellows .. Ciki ciki suka amsata ta wuce gaba ta gaishe da shugaban makarntan aladabce wanda da fara'a a fuskarsa shikan ya amsata. Yana murmushi yace Please have a seat mrs femi. Da takunta na manyan mata ta wuce gabansu ta zauna calmy in a classy way snnn Tace thank u sir,formally ta kalleshi tace i heard u wanted to see me. Yace yess. snn ya turo mata file gabanta mai dauke da sunayen wasu dalibai aciki kusan su ashirin. Daukawa tayi tana dubawa dan daga cikinsu Babu wanda bata gane matsayin ubansa awajen ba dan Daga yaran multi millionaires ne sai na billionaires and all of them transfer students izuwa wann makarntar tasu. Ma'ana an tattaro sune daga wasu makarntun aka dawo dasu izuwa wann inda zasu cigaba da karatunsu cikin sauki. Wasu kuma laifi suka aikata ta karya dokar kasa wanda yasaka karatunsu na kasashen waje ya samu tangarda aka dawo dasu gida dan su cigaba.. Provost yace mrs femi wayann yara dakike gani duka zasu dawo under ur watch daga ynxu, dan already sunyi lattin zuwa wann session din so dolene asamu mai musu jagora da zai sakasu su kamo yan uwansu da suka musu nisa a karatu.. Wayann file din nasu ne zaki iya duba level da information nasu snn saiki shirya ire iren educational programs da kike ganin zai kawo musu cigaba. Ure also incharge of deir welcoming orientation and acadamic perfomance. Har ya kammala magana vcky batace masa komi ba tanata kallon sunayen yaran wanda acikinsu baifi mutane biyar ne ba yan aji biyar ba 12 maza 8 din duk mata ne Mr adetunji da dayan matan sunata Allah Allah tace bazata iya ba su amshe aikin daga hannunta... Duk dama aranta bata kawo tunanin amsar wann aikin ba amma dake tana girmama shugaban makantarn yasaka bata dizgashi agaban wayann mutanen ba, tana dan murmushi tace mishi ba matsala amma zataje da file din gida izuwa gobe zasu tattauna akai sosai. Yaji dadin hakan datace sukayi sallama ta fice ta kyalesu awajen tanaji suna bibiyarta da tsaki. Tana kaiwa car dinta ta dumping din file din abayan seat dinta ta dauki hanyar gidanta tana tuki acikin sauri... tunani take haryaushe hanklinta zai samu daman kwanciyar da zata kula musu da yan makarnta ga business dinta ma yana neman attention dinta sosai.. Ga kuma Sakonnin email da ake ta turo mata da unknwn number wanda yasaka take tunanin ko zarginta femi yake kanyi yasa boye kansa yake neman gwada gaskiyarta wanda hakan bakaramin cusa mata haushi da baqin ciki aranta yakeyi ba. Tunda ta amsa sakon a farko sai bata kara amsashi ba, daga sakon yashigo saidai ta bude ta karanta tabarshi gashi bakaramin kalamai masu ratsa zuciya yake rubuto mata ba, dan son da kayden yake mata irin tsaftaceccn son nan ne wanda shaukinsu yake fitowa tun daga can kasar zuciya. A bangaren kayden din kuwa ji yake kamar ma yanxune ya fara bibiyar rayuwar vicky duk dama yaga haikan bata amsa sakonsa dagangan.. Bayajin dadin hakan aransa Sede Iya budewar datakeyi ta karanta shi yake basa karfin giwar cigaba da kokartawa. Kwana biyu baije ko ina ba yana kwance a room dinsa sabida mura daya kamashi sosai gashi yana da ciwon Asthma mai ƙarfi duk dama bai fiye tashi masa ba sai inya cusa abu aransa sosai yaje yana taɓamai hanyar fitar numfashi. Kowani rana boyayyar soyayyar dayake ma vicky karuwa yake yi a zuciyarsa ayayinda rashin ta yake kkrin haifar masa da cuta mai radadi acikin zuciya.... Tun daya farka yau bai sauko kasa ba har saida yayansa henry yazo dakin ya lallabeshi tare da sanar dashi cewa gobe ne zai fara zuwa makaranta... Tun daga wann lkcin ya dingajin farinciki aransa dan yasan koda vicky bata amsa sakonsa ba zaina ganinta kowani rana a maknrta. Shikansa henry bai san mesa kayden ya cusa son zuwa makarantar aransa ba gani kawai yake kamar yaranta ne yake damunsa at age 23 kam baisan meyake masa ciwo ba. Ana neman wajajen karfe 12 da rabi na rana kafin nan shemau ta kammala shirinta ta sauko kasa izuwa babban falonta fuskarta a mugun daure tawani sha wata uwar kwalliya kusan komi yaji a fuskarta like a real diva tana taku akan dogon heels nata na kamfanin valentino kwas kwas kakeji harta sauko kasa cikin babban falonta. Wasu yankunannun mata ne da talauci tagana yiwa illa azaune akan carpet a falon nata suna jiran karasowarta. Sautin karar takalminta yasa suka miƙe tsaye cikin faɗanci suka rusuna kai har kasa suna cewa sannu da saukowa hajiya. Kallo basu ishe ta ba bare ta amsasu.. cak ta tsaya a gabansu tana watsa musu kallon kyamata dana rainin wayo. Tsiririn tsaki taja snn tace Wacece magajiya acikin ku? Nan wata mata datay sa'ar uwarta ta dago kai atsorace tana cewa gani nan hajiya. Da kallon raini ta bita dashi..snn tace .ohhh mtsww. Inadai fatan angayamiki abunda yasaka na kiraki nan Tace eh angamun hajy dan Allah... Cikin katseta Tace dan Allag mene ya isa haka.. bari na kara memeta miki, Yarinyar dakika kawomin baqar mayyace kuma munafukace dan haka nake so ki kira uwarta kija musu kunne kice bana bukatar sake ganin yarta agidana dan wallh ta yadda yarta ta dawo gidan nan aiki saidai tazo ta dau gawanta.. with comanding voice tace "yanxu nake so Ki kira uwartan ki mata kashedi agabana in bazaki iya ba ki kira ki haɗani da uwartan ni ai bakina baya haila. Kasa cewa komi sukayi suka fara bata hakuri ko kulasu batay ba kafin nan magajiya ta hau kirar layin mamn hafsat din amma netwk yasaka baije ba. Sunyi sunyi amma baya shiga sammmm Shema'u kuwa sai masifa take rusawa tana cewa Kuna ɓatamin lokacina bata da yan uwane ku kirasu nide banaso ne ta dawomin gidana Sai can dayan matan tace da akwai lambr kawunta bari mu gwada kira hajiya ayii hakuri A tsawace Shema tace toh me kuke jira nikumin sauri. Dama kunada lambar sa kuka tsaya batamin lkci sabda bakusan darajar lokci ba? Jikinsu na rawa suka kira mudi bugu daya ya dauka da hangamammen baki yana cewa magajiya yau an tunani kenan yau kuma da wanne kukazo. Cikin katsesa Tace kai mudi hajiya ce take son magana dakai game da maganan hansatu, .. Sigar rashin mutunci yace wacece hansatu? Tace yar gidan dan uwanka mana hansatu Yace au hansatun tana raye ne, hahahaha to meya faru kuma..cikin shege tay ko haihuwa tayi a ikkon? Magajiya tace hmmm mudi bari kawai yarinya kam ashe barauniyace tazo binni ta ishesu da sata gashi tana neman ta tona min asiri awajen hajyar data dauketa ynxu hakama neman lambar uwarta takeyi zatace mata kar asake turo mata ita. Dariyar mugunta ya bushe da ita snn yace yo ai dama nagaya miki babu kashin arziki ajikin hansatu amma kika kiji na kika dauketa kika kaita ikko dan jarabar son neman kudi. To ni me zan muku yanxu Tace dama so nake ka temaka ka isar mana da sakon hajiya kunnen uwarta ace musu kar su sake hafsa ta dawo mata gida idan ba haka ba bazu kwashe ta dadi ba. Yace to naji amma nawane nawa kason aciki dan ba abnza zan tashi naje har gidan su hansatu ba, kuma wann karon bazan karbi dari uku saga wajenki ba inma na daure ne in amshi dari biyar me kikace magajiya A Dede nan shemau ta fauce wayar tace kai bakauye saurareni nan... Zan baka dubu goma amma ka tabbata da cewa yanxun nan zakaje ka isar da sakona kunnen uwar yarinyar kace musu karda su yadda ta dawomun gidana.. Na kiraku ne sabida mijina ya riga ya furta min cewa yana son ya dawo da ita aiki agidana nikuma banaso sabida natsaneta dan haka nakeson ko an zone manta yin aiki ta wajenku kuhanashi idan kuma kunkiji bazaku ki gani ba Bakin mudi harna rawa yace toh hajiya angama wann ai duk me saukine bari naje yanzu.. Cike da masa barazana Tace banason wasa dan muddin kamin shirme har kauyenku zan turo da yan sanda suzo su kamaka Yace ahh hajya baza a mayi haka ba..inma taki jina basai na karbe yarinyar ta dawo wajena da zama ba, ai hansatu yar yayana ne mu muke da iko akanta ba uwarta ba Shemau tace to dakyau. Snn ta katse wayar ta jefa musu shi kasa Nan Ta ciro kudi dubu talatin ta miƙa musu a walaknce tace gashi saiKu bashi dubu goma kudin aikinsa sauran kuma kuyi amfani dashi kufara nemo min wata mai aikin acikin gagggawa haka suka dauki kudin suna mata godiya wanda ko amsasu batay ba. Tamkar sarauniya haka take takawa dagwas dagwas kamar wacce takejin tausayin kasa, dukan su english wears suka yanke cewa zasu saka, dan haka riga da wandone golden colour ajikinta na kamfanin valentino garavani dat is so fucking classy and hot irin silk matareial mai tsantsi din nan ne mai adon shararan net ajiki duk inda ta wulga sai ka shaqa tsabar kyaun datayi ga wani dadddar qamshi bisa qamshi da ke tafa da ita. har sanda ta kai gaban babban jeep dinta snn ta tsaya driver yazo ya bude mata mota ta zauna a owners coner tabi ta toshe idanunwarta da katoton classes tare da maida hanklinta bisa kan wayarta tana daddanawa cikin kwanciyar hankli A tunaninta yanxu tagama da batun hafsa from the root koda mahmud ya aika ta dawo wann bakauyen kawun nata bazai bari hakan yayuwa ba dan dagajin yadda suke amsata atsorace tasan bazasu ketare magananta ba. Daga office meenal ta wuce wani hadadden gidan kwalliya for good one hour tana cikin VIP spa room ana shiryata after that ta ta fito tass sanye da wani light peach colour jump suit na tsadadden chiffon material dayabi dirin jikinta ya mata kyau sosai. Allah Allah take taje ta samesu sabida ji datay hadiza tace mata suna tare

Chapter 29 of 44