Share this page
tace wowww... soooo, zazzafar sauke ajiyar zuciya da vicky tay tana cewa thank u jesus, shiya katseta., rai a mugun bace vickyn tace abeg abeg girl, call that bastard up now sena tsage masa rashin mutunci dan iska kawai.. Meenal ta dubesu tace calm down girl i will right away tunda abunda ya fito dani kenan,..harta fara dialing sai ta bari ta dube vicky tace "wait, vicky, pls can you join them inside..halisa is silently crying wallh,we need to comfort her, when is dis waiting gonna end for god sake. Shema'u ta runtse ido tace "crying kuma? Vicky tace Yo ai dole tay kuka, irin wann tozarci dame yay kama? Shema'u tace "lahaula wa la kuwwa illa billah...Allah ya tsine ma wasu mazan. Vicky ta girgiza kai cikin tsananin takaici da bacin rai daya soma nunawa boro boro akan fuskrta sai batace musu uffan ba ta juya ta koma cikin church din cikin gaggawa tayi wajensu hadiza da suke zaune cikin kakalar murmushin dole ma mutane, basu ce ma juna komi ba,nitsuwa sukayi suma suna jin abunda akeyi. Pastor johnson ne yaketa wa'azi yana dan cracking jokes just so that kar mutane su fara hatsala da jirar da suka kwasa dan wasu tun takwas suka iso gashi an doshi sha biyu na rana. Tafiyar vicky keda wuya shema'u ta sako meenal agaba suka dialing number sukaga ashema international number ne wanda bugu biyu kawai yay aka dauka. Meenal tace hello. Muryan wata baturiyace suka tsinkayo tana cewa "Hello this is zach and zach industries how can i help u maam? Meenal tace oh yes, I want to speak to ur boss, tell him is urgent. Secrtary tace im sorry maam but all urgent calls are directed to his hotline. Shema'u ta fauce wayar very rudely tace 'What do u mean by that u little succumb..hand it over. Calmy Sctary Tace am sorry maam but Sir isnt available on calls at the moment. Cikin sauribMeenal ta katse shemau tace i know, so where is he now.. Sectary tace im sorry ma'am, i cant share his personal informations. Shema'u ta fauce wayar again ta duba taga location london abun se ya daure mata kai sosai. Da kwakwalarta tayi amfani snn tace "fine, is about his contract with finland construction company Abuja in nigeria, one of the files he submitted to us is missing and his multi million naira contract with us might be terminated in few hrs if he dont call us urgently, so if u like don't give us his personal information hold it at the expense of the multi million contract. She make sure ta jadadda "multi million din "sann ta karashe da idiot.. tana fadin hakan sai ta katse wayar taja tsaki a mugun masife. Duk wann be darata ba A Brain dinta tunani ne take tana lissafin wai zach is in london But how? ...when? Kallonta meenal takeyi ganin yadda ta zafafa cikin tunani can ta ja tsaki mtsss snn tace haba shema dan Allah kina rage zafin zuciya mana ita sectaryn meye nata aciki being polite wont eva hurt u kiga yadda kika masifeta kamar itace zach din Shema ta harareta tace dama mekike expecting inyi mata ne meenal inhau peting sectry din zach like she is a queen elizabeth of london kome, meenal are u on kolos? I dont even get how zach get to be in london?..kinsan da cewa a london yake ne.. Menaal batace komi ba ta kyabe baki, Sai Can tace yazanyi in sani toh ai gashi kin masife ta halama su kama wann layin ma su kashe mana bazamu san meya faru yake london aranar aurensa ba. shemau tace seee, i knw what im doing. They will call us back immiditely trust me. Hnm kawai Meenal ta furta aranta tana tunanin taya hakan zai faru. Ko gama kammala tunaninta batayi ba saiga kirarsu na biyo baya ware ido meenal tay cikin mamaki snn ta kalle wayar ta kuma juyo ta dube shemau tay murmushi tace shegiya kawata ure a witch.. Shema tay rolling ido cikin wani irin jiji da dakanta snn tace "i told u" ninasan maganin shegu... daf meenal zata dau wayar tay sauri wajen rike hannunta tare da cewa ke allow them to call us "thrice"..have some classs jare. Meenal tace why? Tace lets make them wait. Suma sujira mu mana..ana ukun ma sai inyakusa yankewa saiki dauka muji me zasu ce. Aikuwa hakanan ya faru a kira na ukun yana daf yankewa meenal ta dauka ta saka a hands free. Basuce komi ba face gyaran murya da shemau tay cikin jan aji dan asan suna bisa layi Wann karon muryanshi zach din suka tsinkayo Da husky and Coarse voice nashi mai cike da professionalism yace "Good evening maam Ure speaking with zach wellington..i heard... Tun Bai gama rife baki ba shema'u tace "ur english is as terrible as ur sense of maturity mr zach or what eva u call urself ..so, How dare you? Wani irin Shiru yay ya runtse idonsa cikin tsananin jin bugun zuciya. A karsashe Shema'u tace zach kaifa ba karamin yaro bane U left the country on ur weding day as per what? What sort of evil is this..u shud have call off the weding by throwing ur stupid engagement ring on her face yestade rather than humiliating her to this extent.....u fucking imbecile. Kasa katse wayar yay musammn daya tsinkayo yadda muryan shema yake aman wuta kiris ya rage ta dura mai ashar amma rashin son taja attention din mutane kansu shiya mugun cetorshi datay masa maganan da murya kasa kasa bamai karfi ba. Meenal ce ta fauce wayar jikinta na rawa zucyarta na bugu da fargaba, itakam ma tsoro takeji aranta karde ace maganan data gayamai ya jiyan ne ya haddasa wann fitar,dake bata son kowa ma yasan metayi dan haka nan da nan ta cireshi a handsfree snn taja can gefe inda shemaun bazataji me zatace ba snn sukayi magana da zach din cikin wasu yan mintina kadan da baifi biyar ba ta dawo jikinta a mugun sanyaye tana hawaye sosai. Cikin ziriya ta samu shemau ranta ya baci ya hautsine, A zafafe ta juyo idonta na fidda ruwan tsananin bacin rai ta yo kan meenal dib kamar kububuwa zata fauce wayar cikin masifa tana cewa "ke da Allah ban wayar nan in zazzageshi dan iska kawai shege makiri azzalumi jaki kawai Arnen banza jahili. She is bcoming unctrollabe meenal ta rirriketa suka koma ta baya inda babu mutane dan ɓari kawai take tana jan zuciya da karfi, suna isa ta bayan church dib shemau ta fixge jikinta tareda tureta cikin masifa mai tsanani har tana kumfar baki meenal What the hell is this. He is in london... Zach is in london really? And On his weding day "What about halisa? Kaiwa nan jikinta ya sace da tsananin tausayin halisar daya lullube mata zuciya sai jajjan zuciya takeyi mai zafi,"muryanta a karye tace "What has she done to dersev this humiliation on her best day? Metayi masa da zafi haka? Kiji yadda yake business dinsa hankli kwance kamar babu abunda yake faruwa anan ehhhhh? Ranta na dada harzuka ta cije baki babu abunda take tunawa aranta face wahalhalun da halisa tasha da rayuwa hakan yasaka zuciyarta dada karyewa..kukan tausayi ne ya kufce mata...tace i cant belive this..why will bad things happen to good ppl, Chaiiiiii..This guy is overly wicked. Jikin Meenal rawa yake tama kasa nitsuwa sai memeta innalillahi wa inna ilaihi rajiun takeyi aranta,ciwo da karsashi biyu ke dawainiya da ita, tunanin yadda halisarta zataji da kuma tunanin abubuwan da zach ya gama gaya mata. "Bazai iya auren mace mai cike da kazanta ba "Bazai iya rayuwa da macen da tay rayuwa irin na halisa ba.. He loved halisa amma he just cant grace d weding dan baison yaransa suyi gadon irin qaddarar mahaifyarsu. Wani irin jiri takeji dan tasani cewa da son gulma da makirici bai tunzirata ta bude masa labarin kazantar dake cikin rayuwar halisa na baya ba da bazai taɓa sanin haka ba.. sulalewa tay kan kafarta batare da shiri ba dan tasan dolene halisa ta iya shiga wani hali, nan ta durkushe kasa kan gwiwarta tana kuka sabida sosai abubuwa suka taru suka cunkushe mata azuciya ayanzu tsoro mai tsanani ma takeji dan batasan mezata furta musu ba inta bude bakinta wajen yi musu bayani... Hade da abunda take ji na tausayin kawarta halisa awani bangaren zuciryata yanzu ne take da tabbacin cewa itace tay sanadiyar abunda ya faru da halisa na baqin ciki da tozarci ayau ranar aurenta... Kuka meenal takeyi kamar wanda zata cire ranta a durkushe awajen ta bayan church din inda suka boye har abun nata ya soma damun shemau dake tsaye cikin ziriyar bacin rai tana kallonta da mamaki mai yawa aranta. Tasan dai meenal da halisa sun mugun shakuwa da juna sun zama tamkar yan uwan jini tunda dai agidan su halisar tay rayuwarta tun suna yan mata kafin ta tsaya da kafafunta. Kasa cewa meenal din komi tay ganin irin kukan rikicewa da gigicewar datakeyi ayanxu. Tunani kala kala ke rikita kwakwalar meenal yana saka mata tsananin fargaba.. Shin ta fito fili ne ta gaya musu gaskiyar cewa itace tayo silar faruwar kome daya tarwatsa aure tsakanin halisa da zach ayau koko ta boye musu dan karda tsakaninta da halisan ya dawo babu yafiya sai gaba na har abada, kuma tasan itace zataji kunya, hala wann lamari kuma ya kawo karshen kawancen su mai dadi ko ya kawo rabuwar kai atsakanin grp dinsu sanadiyarta. Tuna hakan kawai take tanata kuka wayarta ne yay ringing cikin katseta ,ganin wacce take kira yasaka ta mike agaggauce ta koma gefe domin ta amsata... A tsaye shemau ta tsaya kanta a mugun dore tana mai binta da idanu cikin kasa tantance me take ciki.. Anayi ana sharing cikin grops dan Allah For my posting grp chat 08060712446 [1/24, 9:13 AM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB...*_ _(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_ #ROMANCE #FICTION #ADULTHOOD #SEXADDICTS #WOMENPOWER BY _SURAYYAHMS_ _Watsap only 08060712446_ ⏯️3️⃣ Gefe meenal ta koma dan tsabar kukan dataci har tana jan hancinta hawaye masu yawa da dumi sam suka ki tsayawa acikin kwayar idanunta sai zubowa bisa kan kyakyawar fuskarta sukeyi yuu kamar an kunnasu, hannunta na rawa sosai ta kara wayar a kunnenta muryanta mai cike da shessheka ta dada sauke shi can kasa kasa snn tace "Hello, mumy.."? Daga dayan bangaren mahaifyarta ne mai suna hajiya nadiya talba da bugu daya ta shako sautin kuka a muryan yartata hankli tashe tace "Amina.. Amina lfya kuwa kike kuka wai meke faruwa ne naji muryanki haka? Hows the weding going hope dai ba wani matsala bace?.. Kamar jira Meenal take hajya ta gama rufe baki nan ta sake wasu sabbin hawaye masu yawan da dumi ta runtse idonta tanamai cewa wayyo Allah na mumy na shiga uku.. Hajy tace Kin shiga uku kuma?..shiru meenal tay bata amsata ba banda boyayar sheshekarta datakeyi ahankli bakajin sautin komi, Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, hajya nadiyar tace Sann ta dora dacewa "toh meya faru? Wani abune ya sameki ko halisan? Meenal na kuka a hankli tace "A'a...sann ta kuma cewa eh. Mum kaina a kulle yake nide nayi abunda ya dameni. Da sauri cikin katseta Hajya tace menene. Wai Me kikayi? Kuka marar sauti sosai meenal takeyi hjya na jinta ayayinda hanklinta ke dada tashi sai batace mata komi ba. Da kyar meenal din ta iya tsagaitawa bayan dedeta nitsuwarta ta danyi shiru cikin sauke sarkafaffen ajiyar zuciya ta soma cewa "Mummy wallh wata yar matsala akasa mu, auren halisa is not holding anymore..zach yaki zuwa yace wai ya fasa aurenta wai bazai iya auren mace irinta ba. Cike da tsananin mamaki hajya nadiya ta dafe kirji tanamai cewa..what? Meenal Me kikace?..wai wata halisar, kina nufin auren da kuka zuba milliyoyin kudi kuka shiryashi shine akafasa din?hmmmm Lallai tab di jam,toh akan wani dalili. Hawaye fall idon Meenal tace mummy ki tsaya kiji. Nan ta hau bata labarin yadda akayi batare da ta tsakuro mata nata kalar fargaban ba tukuna. Hajia nagama jin bayanin ta tace toh Hmm Allah ya kyauta cikin sauke ajiyar zuciya take famar jinjinawa.. Shiru meenal tay a brain dinta tana kan tunanin yadda zata soma bullowa mahaifyarta da maganan da sukayi da zach. Ita kuwa hajy nadia ta cika fam dan Aynzu janjan zcya da meenal kekanyi shiyake ɓata mata ranta sosai dan Bakaramin son yarta takeyi ba. Irin mummunar soyayyar nan ne takema yarta meenal wanda da bata iya kallon aibunta. Hausawa nacewa ɗa na kowa ne amma banda wajen hajya nadiya, iyanzu kukan da meenal takeyi shine babban damuwarta cos she dont really give a shit akan matsalar kowacce yarinya. Ajiyar xuciya ta sauke tuna cewa inbadan son ran aminan bama da hala bazata taba amsar halisa ta zauna gidanta dachan harta rayu alakarsu takai haka girma ba, dan aranta gani kawai take kamar halisa is unlucky in her life, mummunar qaddarori ne kawai ke tafe da kaskantacen rayuwarta tun tana yar karama,. Wani tukikin tsaki taja acikim ranta Sai can Snn ta kuma cewa a masife "toh ke amina wai meye naki aciki ne da kiketa wann uban kukar sai kace an miki mutuwa eeehh,... Ynxu Ciwon xuciya zaki dorawa kanki dan kawai yaron nan zach yace bazai aure halisa ba? Meenal tace haba mummy zach fa bai kyauta ma halisa ba. On her wedding day, Is This fair?muntara mutane na alfarma mun kashe kudi mun bata lkcin mu, yanzu da wani irin ido halisa zata kallesu bare har ta samu gwarin gwaiwar gaya musu cewa zach yace ya fasa aurenta? Karamin Tsaki hajy nadiya taja snn tace hmmm,..But Things like that are bound to happen this way meenal. yo ai qaddararta kenan. ni dama jikina tuntuni yabani wallh auren nan da wuyane yayu. Masu kudin nan basu fiye auren yaran da basuda asali ba..i mean, halisa's life and standard is nothing to write home about ke kanki kinsan yanayin kazantar data tashi aciki. She was a street girl har rawar kan karfen nan na karuwai tay a club danta ci abinci, snn ke zaki iya tantance mazan da suka taɓa kwana da itane? har ciki ma kawunta ta tay kikacemin..to wani hamshakin me kudin ne da iyayensa sukace masa jeka zaka gani zai aureta? Ku kun fiye tsawwalawa. Baki bude Meenal ta tsaya sam takasa cewa komi saijin hajiya nadiya take datake famar rero bayanai.. Tace masu kudi suna neman mace ce mai kyaun asali koda batada kyan fuska sai kiga ta auru awajensu,wacce dai batayi rayuwa irin nasu halisa ba..kyabe baki tay, hnmmm"toh tunda wnn abu yafaru ai hakuri zakuyi ku rungumi na Annabi... kuyi masa adalci shima just imagine him bcming a presidential aspirant one day yo ai iya past din matarsa ma kadai ya isa ya jawo masa wata musibar arayuwarsa. Meenal ta jinjina kai tare da sauke ajiyar zuciya jin yadda mum dinta take maganar babu dandanin tausayi babu tausasawa ayanayinta sam sam. Idonta a lumshe cikin ragwabewar murya tace "Mumy ta ina lefin halisa ya fito acikin wann lamarin..she' have never even choose this life for herself..bataso amma kamawa dole yayi..mum kiyi tunani nima dana taso cikin gata da daula inda ace Allah yaga dama zai iya daukeku duka kamar yadda ya dauke iyayen halisa, nima kuma zan iya fadawa cikin rayuwar kazantar dayafi nata muni. Cikin katseta da sauri a hayayyake hajya tace ke Dakata min Amina,wann maganan ya isa haka Allah ma ya tsagaita mana irin wannan mummunar qaddarar, "tuff da baqin yawu, kar inkuma jin kinyi makanki wann mummunan fata shashasha kawai!..ke Allah ya rufa miki asiri ashe kinan nan kinata neman wa kanki fitina.. Meenal tace mumy toh ai gaskiya ne. Kofa tausayi halisa bata baki ba, sai famar kushe komi kike as if her feelings is not valid a wann yanayin data tsinci kanta aciki. Hajya nadia tace Hmm Toh tunda kince haka shikenan.. zach bai kyauta ba..amma shin kinsan dalilinsa nayin mata haka..naji kince min dake kukayi magana menene asalin dalilin dayasa yace miki ya fasa auren nasan dai da wani abu akasa ruwa ai baya tsami banza. Meenal nataro hawayenta jikinta a sanyaye tace Mummmy, dats why am telling u is not alwys halisa's fault at all dan zach baisan komi game da rayuwarta na baya ba. hajya tace Toh dama akan rayuwarta na bayan kenan ya fasa aurenta? Wani Shiru Meenal' tay saida tadan sace juya baya kadan data lura da kamar hanklin shemau nakan wayarta saita sauke ajiyar zuciya, sann tace "Eh mummy akan hakan ne..amma fa mani kawai ya fada sabida dani muka yi magana irin haka dashi kwanan nan. Hajya tace ban fahimceki ba.. Wani ajiyar zcyar meenal ta sauke snn tace mum Dama ranar ne muna dan hirar virginity a office dinsa da mukaje tare da halisan then she left us alone for some minutes inata tsokananshi akan yabi kawata ahankli, shine sai yace min shi ai bai taba aikata premarital sex ba, he is a virgin..sede ince halisa ce zata bishi a slow ..so, daga nan dai sai nafara masa hira, and i told him about halisa past life. Hajiya tace kamar me da me kenan kika gaya masa har haka ? Shiru meenal tay tana dan dube dube duk tsoro yabi ya cikata dan gani take kamar hala shemau zata iya jiyota ga hjya ta matsu tanason itama taji Da kyar ta iya budan baki tay magana kasa kasa dan saida hjya ta kasa kunne sosai kafun nan tasoma jiyota da kyau Tace "Mum kawai de na gaya masa komi da komi ne..like..saitayi shiru alaman tanajin nauyin maganan abaknta.. Hajya tace ehn ehen inajinki meenalin mama Dada kankance muryanta tay tace nide na faffada masa cewa tay talla tun tana karama kuma maza suka budata, kawunta ma yasha kwana da ita, kuma har yamata ciki ta xubar. Sai naga zach yaji tausayinta sosai,shine na kara gaya masa cewa ai da halisa tazo lagos club club take bi tana kwana kuma tana musu aikin goge goge dan abata na cin abinci kuma ba irin mazan da basu kwana da ita ba, cos u knw Dats how she pays her schl fees kafin nan ta dawo zama a gidanmu. I also told him dat.. Cikin katseta Hajiya ta dafe kai tace wow, Dat was soo foolish of you Amina. Gaskya baki kyauta ba..Ke Me yakaiki gaya masa haka ina ruwanki da sirrikan ta Amina? Abunda Allah ya riga ya lullube kece zaki ce sai kin bankado fili anan kam Kinyi ganganci wallhi!! Irin wann sirrin ba a gaya ma namiji sede in mugunta kikayi niyyar mata. Ahankli Tace mum kawai nayi tunanin ai yakamata ace yasani ne. Ta turo baki gaba" Ko ba haka ba? I tot it wasnt a big deal ai..bansan zai dau abun da zafi haka ba.. tafadi maganan ba har cikin ranta ba. Cikin sauke ajiyar zuciya mai nauyi hajiya tace Subhanllah amina kice ke dai kikayi kutunkutun kika hana yuwar auren kawarki da zach kuma nasan kina da dalilin yin mata hakan wallah sede inki boyemin. Cike da yanayin damuwa a muryanta tace mum nide abinda ya faru ya riga ya faru ders no going back ni damuwata shinene yanzu me zanyi..am soo scared wallah, Ni Kaina duk ya kulle banason guilt yasani na gayawa halisa gaskiya ynxu zata iyacewa naci amanarta sauran kawayen ma zasu iya ganin lefina suce nice munafuka. Mumy am soo scared dan Allah ya zanyi. Ko de in je in fada musu kawai ince musu i tot it wudnt be a big a deal hala zasu fahimce ni. Cikin katseta da sauri hjy nadia tace hmm Amina lallai kanki na rawa..toh Ahirrrrr dinki da fadin mata, Are u really that mad? Kina tunanin zasu taɓa fahimtar ki acikin ruwan sanyi ne..this is gonna be a war girl cos u didnt just break a marrige you broke a whole beautiful relship. Yarinyar nan halisa tun da ta fara neman nakanta bata taɓa bude zucyarta tay soyayya da kowa ba se zach din na Ke kanki nasan tsantsar soyayyar da suke yawan nunawa junansu agaban duniya na taɓa maki zuciya. Mata da hassada da kishi hmm? Tunda burinki ya cika...toh wallh Kada ki kuskura ki fada musu, shinkina hauka ne amina, to ki kame bakinki kiyi gum kamar kin binne gawa a kogi,yo kika sani ko zucya ya debeta ma ta kasheki u think u can fool anyone with ur silly excuse ko mtsww,..irin wann maganar ai tamkar wutar daji ce,inya kama bishiya daya to tabbass sauran bishiyoyin duk sai sun hadu sun kone, karda kisoma kunna wutar fitinar da bakisan inda zai tsaya ba,kinaji na ko? Gyada kai kawai meenal takeyi bata iya cewa komi ba sai sauke ajiyan zuciya datake faman yi jin maganar mahaifyrtan na dada bata gwarin gwiwar sanin yadda zata bullowa abun. Shiru tyi Tanajin Hajya nakan mata magana cikin jadaddawa "Amina kada kice komi kuma kar ki aikata kome Just wait for my arrival inna dawo daga dubai zamu san ya za'ayi da wann maganan kinji auta na. Jiki a sanyaye tace toh mumy. Nagode..harkin sa hanklina ya kwanta ure the best muaah i love u. Murmushi hajiya ta sake najin dadi snnn tace yawwa Toh maza jeki karma suga kin jima kina waya su tuhumeki tunda bawai kin fada ma shemaun abunda kuka tattauna da zach din bane sai Kinemi wani abuna na daban ki gaya musu amma banda gaskiyar kinji . Meenal Tace toh mumy. Nan da nan suka datse wayar ,Meenal saida taci minti biyar cikin neman makanta nitsuwa da dedetuwar hankli kafin nan ta saka himman karasowa wajen shema'u. Ahankli Meenal take takowa hawayen dake fuskarta sundan rage sauka sakamakon kiyasi da lissafe lissafe dake gudana a brain dinta na tunanin karyan da zatayi domin ta rufawa kanta asiri, dan saidai mum dinta ta fayyace mata hakan snn itama ta gane cewa fadar gaskiya iyanzu bazai ficce ta ba sabida kowa acikinsu ransa a harzuke yake itakanta amarya halisa already bata cikin hayyacinta bare ta fahimce wani abu, dan haka fadin gaskiyar sam bazai haifar musu da ɗa mai ido a yanzu ba. Tahowa take ahankli kamar bata da laka tana dan sarrafa maganganun da zata fada musu a kwakwalrta, ayayinda take daf da cimma shema'u tana daga idanuwanta sama caraf sai ga hadiza ta faso a rikice,abayanta vicky ce itama ta taho cikin sauri har kafafunta na hardewa. Kusan dada rudewa tayi ganin dukansu sun hallara a rikice da alaman shemau har ta tura musu text ta gaya musu abunda ake ciki Isowarsu wajen shemau yay dede da karasowar meenal din dake kkrin dedeta komi aranta cikin gaggautawa da sauri dan kar gaskiyarta yay saurin bayyana. Hadiza na tsayawa hawaye masu zafi suka tsinko mata akan fuskrta jikinta na wani irin kyarma na bacin rai. Cike da dauriya Vicky tacewa shemau da meenal muna bukatar bayani meye ke faruwa please what is going on girls..shema'u ban fahimce sakonki ba meyasa kikace auren nan bazai yu ba..what is goin on.. meenal talba? Shemau marafa. Both of u shud answer us now!!! A dan hatsale hadiza tace u guys shud just say it out loud mana...i knw He cant make it, he is london right..?i saw his location in dat email. Vicky ce batasan komi ba jin hakan ya fito daga bakin hadiza yasa ta juyo a hujajan ta dube hadizar a tsananin mamaknce tanamai cewa "what did u say?..kikace bayama kasar ko kunnena ne ya dena jin magana dakyau Shema'u tace yes vick..zach yana london..he dumped halisa in the church waiting for him, while he is over der doing business... off couse. Cikin sauri Meenal tace haba mana ya isa haka shema'u ,Karda ki gaya musu maganan nan ata wani siga dazai kara hatsala su mana. Muryan kuka ta saka, snn tace We are all in pain right now.. amma yakamata muyi amfani da hankalin mu wajen neman mafita.. we need to find a way of taking halisa out of this place...away from this messy weding nightmare dat zach created for her.. Hadiza dats soo hurt and emotional, dama tafi kowa rauni acikinsu abu dan kadan ne ke daga mata hanklinta sosai, nan ta kara fashewa da kuka mai ciwo dan wani irin tausayin halisa taji har cikn ranta yana tsagawa, atake shemau ta rungumeta sosai tana rarrashinta. Vicky ta tsaya cak hawayenta na zubowa ta cije bakinta acikin yanayin baqin ciki silently take kuke batayi yunkurin tarewa ba. Banda saka kanta a matsayin halisa babu abunda takeyi acikin kwakwalta dan kuwa tasan bakowane zai iya daukar irin qaddarar rayuwar halisa a zcyarsa ba. Meenal yakamata ki gaya mana abunda bastard din can yace..shema'u ta tuhumeta. Vicky dake tsaye waje guda bacin rai yasaka duk jikinta yadau ɓari

Chapter 3 of 44