Share this page
1 / 9
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 🥹GAMO MUKA YI🥹 Chapter 1 True Life Story😱🙆‍♀️ By Queen Jiddah....✍️ Zaune muke kamar koda yaushe a cikin 'dakin mu, da misalin karfe goma na dare tare da Kanwa ta, dukan mu waya ce a hannun mu sai dai ita indian film take kallo sa'banin ni da nake yin Chat da wani class mate 'dina mai suna Kokanii ! Shine nick name din da muke kiran sa a school. Film din take kallo tana dariya, yayi dana juyo ina tambayar ta me take ma dariya, sai tace min na daina damun ta idan bazan kalla ba na kyale ta, sai nayi murmushi na cigaba da chat 'dina ba tare da na tankata ba. "Assalamu Alaikum". Naji wata murya mai amo da 'karaji tayi sallama, ban saka komai a raina ba na kar'bi sallamar tare da waigawa domin ganin meyin sallamar, kasan cewar a uwar 'daka muke amma daga inda muke zaka iya hangar kofar falon mu, gashi kuma kwan lantarkin mu na falo ya lalace shiyasa baka iya ganin falon sosai sai dai kana iya hangar waje dai dai kofar falon. Koda na juyo nayi GAMO da abinda ya gigita tinani na, nan take na fara karkarwa jiki na na bari na sake kallon kofar. Wata mata ce tsaye a bakin kofar sanye da farin hijabi zanen jikin ta iya guiwa yayin da take 'dauke da ,kafa daya tal👌 kuma tayi tsaye, ga zanin ta a yaye ballan nata nace ko ido nane, gashi bana iya ganin fuskar ta, farin watan daya haska waje ne ma ya bani damar ganin siffar ta. Da sauri na waigo kusa da kanwata dake zaune tana kallon, da yake ba wata tazara ce mai yawa tsakani na da ita ba, domin shekara daya da watanni na bata, sai na kalle ta cikin firgici ba tare da nace komai, domin tsoro nake ji kar aje nikadai ce ke ganin matar ganin kanwata bata tsorata ba, murmushi Maryam tayi ka na cikin kwanciyar hankali tace min, "baby ki kwantar da hankalin ki duk abinda kika gani nima na ganshi" sai muka sake tsinkayi muryar matar tana fa'din. "Maman ku ta dawo daga Tudun Wada?". Sai nayi karfin halin ce mata " A a bata dawo ba, duk da kuwa nasan maman mu bata je can ba, domin can din gidan kakar mu ce kuma yau a can muka wuni, dawowar mu kenan ma saita shigo ta same mu. "To daman sa'ko ne nazo na bata, saboda haka idan ta dawo ku gaya maya na dawo ban tarar da ita ba" ta sake fa'da cikin murya mai amo tana kallon mu. Yayin da na 'dan sake juyowa 'kirjina yana harbawa na sake kallon kafar ta still dai Kafar 'daya ce har yanzu, cikin karfin hali na ce mata. "To shi kenan idan ta dawo insha Allah za'a gaya mata". Daga budar bakin ta saita ce min. " To idan maman taku ta dawo wa zaku ce tazo tana neman ta?". Sai nace mata "to wa za'a ce mata?" Kuma jiki na har yanzu bai dena karkarwa ba, yayin da ita kuma Maryam duk wannan musayar zancen da nake da wannan matar wacce na kasa gane shin mayya ce ko Aljana, bata tanka mu ba, kuma bata tashi daga kwancen da take ba saima shiru da tayi tana sauraron mu. Sai naji muryar ta ta 'kara girma da amo ta sake ce mana. "Kuzo na baku sa'ko idan ta dawo sai ku bata!". Na 'dago da sauri na kalle ta, zuciya ta na tsananta bugawa, domin idan harba gizo ido na kemin ba tabbas babu komai a hannun ta kuma sannnan hannayen ta zube suke a cikin hijabi ko ganin su ba ma yi, to wane sa'ko zata bamu? Sai na aro duk wata jarumta na sanyawa kaina, ka na nace mata. " A a gaskiya ba sai munzo ba, kawai ki fa'di sa'kon ki inyaso idan ta dawo sai mu gaya mata". Sai tace min. "Me kike nufi kenan ba zaku zo ba ko?". Nace mata "Eh mukam ba zamu zo ba"🥹 jiki na a matukar sanyaye. "To shi kenan tinda ba zaku zo ba, ni bari nazo na kawo muku!" Ta fa'da tana tunkaro mu....✍️ Idan kuna so na saka maku cigaba da wuri, to kuyi sharing kuma kumin react👌🤓. Kuyi following wannan channel din domin samun cigaba daga zarar na 'daura👇👇. https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H Daga Al'kalamin👑 Queen Jiddah....✍️ [11/20, 11:45 AM] null: 🥹GAMO MUKA YI🥹 Chapter 2 True Life Story🙆‍♀️😱 By Queen Jiddah....✍️ "To idan ba zaku zo ba ni bari nazo na kawo muku!?" Ta fa'da tana tunkaro mu. Na waiga da kyau naga da gaske fa zuwa zata yi, ai ban san lokacin da na buga tsalle na koma can 'karshen gado ba na 'kan'kame Kanwata maryam, wacce tayi shiru bata ce komai ba kuma bata da alamun yin magana, na 'kan'kame ta sosai na fara karanta duk addu'ar data zo baki na. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un! La ilaha illa antas subhanaka inni kuntu minaz zalamin" na Fa'da ina waigen kofar falon. Yayin da na rufe ido na tamau ina kwarara ihu na rinka kiran sunan wata aunty fati, wacce kenan cikin gidan mu, da yake kofar ta tana dan nesa da tamu sai dai duk a gida 'daya muke. Haka wannan fatar ta iskomu har uwar 'daka kusa da gadon da muke zaune, sai dai wannan karon bluen hijab ne sanye a jikin ta, kuma tana da jiki ba kamar 'dazu ba, wanda nake saka ran a falon mu ta riki'de ta dawo mutum kafin ta 'karaso uwar 'daka, saboda kwan lantarkin mu na falo ya lalace shiyasa bamu ga shigowar ta ba, kawai ganin ta muka yi a kusa damu, kuma yanzun har tufafi ne a jikin ta ba kamar 'dazu ba. Har ta 'karaso kusa damu ban yarda na bu'de ido na ba, sai dai ita Maryam tana nan zaunen ta kuma tayi shiru bata ce komai ba, wanda hakan ne ya sake rikita ni. "Kee! Dan Allah kuyi wa mutane shiro, to idan ni muguwa ce wannan ihun da kike shine zaisa bazan cutar daku ba?". Da sauri da bu'de idanuwa na sakamakon jin abinda ta furta, sai kuma na 'ka'kalo murmushin 'karfin hali, ganin itama Maryam din Murmushi take yi, amma ko da wasa ban yarda na kalle ta ba, sai dai na fahinci ita din bamai tsayi bace ka na kuma leben bakin ta jah ne kamar wacce ta shafa janbaki, sai dai bakin nata ne ahaka ba wani jan baki data shafa. " Dan Allah kumin shiru shirmammi kawai" ta fa'da tana murmushin mugunta domin ita kanta tasan mun firgita. Nan take ce mana wai daman daga nan bayan gidan mu take taje ta siyo itace ne nayin girki, ta fa'da tana nuna mana hannayen ta nan ta ke saiga itace sun bayyana a hannun ta har 'dauri biyu a kowane hannu! Bayan koda ta shigo cikin 'Dakin babu itace a hannun ta, nan na sake firgicewa a raina nace siyo ice karfe goma na dare sai kace dole? Nan ta katsiye ni tana fa'din. Dama tazo ta gayawa maman mune cewar ta gayawa kakan mu wacce ke Tudun Wada wai an sallamo dan uwanta na 'kauye daga asibiti!. Sai ga 'kanwar mu ta shigo dakin tana tambayar mu wai me mukewa ihu haka?. Sai wannan Aljanar tace mata. "Kinga kyale su kiyi tafiyar ki basu da hankali" tana gama fa'dar hakan tayi waje, a a wajen tayi kicibis da Aunty Fati itama zata shigo domin taji ihun mu, sai take ce mata. "Baiwar Allah lafiya? Meya faru nake jin ihun su Baby?" Tayi tambayar tana yi mata kallon tuhuma. Yayin da ita kuma wannan Aljanar tayi murmushi tana mai tinkaro wajen da Aunty fati take tsaye......✍️ Yawan like da sharing din ku yawan page din da zaku dinga samu na Littafin GAMO MUKA YI🤓 Kuyi following channel din mu domin samun cigaban labarin GAMO MUKA YI daga zarar mun 'daura👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H Daga Al'kalamin 👑Queen Jiddah......🥹 [11/20, 8:40 PM] null: 🥹GAMO MUKA YI🥹 Chapter 3 True Life Story😱🙆‍♀️ By Queen Jiddah.....✍️ Yayin da ita kuma wannan Aljanar tayi murmushi tana mai tinkaro wajen da Aunty fati take tsaye. Aunty fati kuwa tayi tsaye tana kallon ta, bu'dar bakin wannan Aljanar sai tace mata. "Daman Nazo ne wurin Salame na gaya mata sa'ko saina tarar bata nan, nace suzo saina basu sa'kon shine fa suka saka ihu, wallahi ni kaina saida suka firgita ni" Aljanar ta 'karashe maganar murmushi 'dauke a fuskar ta tana kallon mu. Sai Aunty fati tace "haba Baby! Yanzu fisabilillah kan wannan dan abin ne kuke ihu har kuna neman tayar min da hankali? Wannan ai shirme ne, kina matsayin babba amma bazaki natsu ki fahinci abu ba" ta 'karashe maganar cikin 'bacin rai tana kallo na. Yayin da ni kuma na sunkuyar da kaina ba tare da nace komai ba, domin harga Allah makircin wannan Aljanar ya bani mamaki😩. "A a ke kuwa karkiga laifinta, kinsan mutane ba abin yarda bane yanzu, shiyasa ta tsorata" Aljanar ta fa'di hakan tana nufar kofar fita ri'ke da itacen ta data siyo. Tana fita nayi wuff na ri'ke Aunty fati idona yana ciko da kwalla nace🥹. "Wallahi Aunty fati karya take yi, ba mutum bace, Allah Aljana ce" na fa'da ina hawaye tare da bata labarin abin da muka gani nida maryam jiki na sai rawa yake. Shiru tayi tana 'dan nazari dik da itama ta firgita sai dai bata bari mun fahimta ba, sai kawai ta juya tana fa'din. "Allah dai ya shiga tsakanin ku da ita" tare da nufar kofa zata koma bangaren ta. Nayi wuff na sake ri'ke ta ina fa'din. "A a Aunty fati dan Allah jira ni" na fa'da ina hawaye tare da wuce wa uwar 'daka na dauko waya ta harda hand bag dita nace ni binta zanyi, tace to mu rufe kofar tamu muje can kofar ta kamin maman mu ta dawo. Haka kuwa akayi muka je can kofar ta, lokacin da muka isa mijin ta yana nan, sai yake tambayar meye ya faru muke ihu, nan nace masa wallahi Aljana muka gani, na basa labarin yanda muka ganta. Jikin sa yayi sanyi sai yake cewa ai yaga lokacin da ta shigo ri'ke da itace a hannun ta lokacin shi yana kofar gida, kuma ma matar fa a unguwar mu take can bayan gidan mu, sai dai jama'a suna jita jita akan mugunya ce kuma tana da iskokai. Nayi sauri nace " eh wallahi yaya kuma Aljana ce da 'kafa 'daya muka ganta" na fa'da ina kuka tamkar karamar yarinya. Maryam tace eh yaya gaskiya ta fa'da nima na gani. Aunty fati tace " gaskiya ku dage da addu'a tinda har kuka ganta a siffarta ta ainahi ni nasan ba zata kyale ku ba". Yaya kuwa shiru yayi na dan wani lokaci, ka na yace. "Koma menene Allah ya maida mata manufar ta akanta🤲 ku kuma ku shiga ciki kafin maman taku ta dawo". Bayan Mama ta dawo da kyar na iya fita waje tare da kannena biyu maryam da Nana muka tarar da ita a uwar 'daka, da sauri ta tambaye mu me yake faruwa ganin ina hawaye. Ai da sauri na fa'da jikin ta ina kuka nace wallahi mama aljana tazo gidan nan da 'kafa 'daya,na fa'da ina kuka. Nan Maryam ta bata labarin abin da muka gani da abinda Aljanar ta fa'da harta biyomu a uwar 'daka. Murmushi mama tayi tace. " Amma baby kinyi girman banza, yanzu akan wannan kike kuka? Duba fa kiga ko kannenki gasu nan basu kai ki tsorata ba, keda ya kamata ki karfafa masu guiwa amma ke ki ke kuka saboda sakarci". Nace "wallahi mama Aljana ce kuma ta tsorata ni, kuma ga maryam nan ai lokacin da ta shigo ni kadaice ke mata magana ita Maryam batace komai ba sai kallon mu da take, shiyasa na 'kara firgita". " Hmm naji ku tashi kuje zuwa sabgar gabanku, insha Allah idan gari ya waye zanje har gidan matar tare da officer naji menene dalilin da yasa zata zo ta firgita min yara". Kasan cewar shi officer din ma'kocin mu ce, kuma Aunty fati ta gaya mata wai yaya yace matar anan bayan gidan mu take. Maryam dai wayarta ta janyo ta cigaba da kallon indian film din ta, nikam tawa wayar a hannun karamar kanwar mu Nana take, nida bana bayar da aron waya, sai gashi Nana ta samu yau a free sai kallon ta take, yayin da ni kuma na 'kudundune a bargo sai shar'bar kuka nake jiki na yana famar karkarwa, yayin da duk wata tsiga ta jiki na ke mi'kewa. Da muka zo kwanciya ma ma'kal'kale maryam nayi, nida bana yarda ko ka'dan na kwana tare da wani saboda bana so ana ta'bani sai gashi nice a yau Ma'kal'kale da maryam, ina tsiyayarda hawaye, a cikin dare 'daya dik na fita a hayyaci na, ko 'bera ne yayi motsi saina firgita saboda tsabagen tsoro, daga karshe dai bacci yayi awon gaba dani😴. Cikin bacci naga wata mata, wacce a unguwar mu kowa yana zargin cewar mayyace, sai gashi naga ta biyoni a guje ri'ke da wu'ka ni kuma sai faman gudu nake a cikin jeji tana biye dani......✍️ Hmm laifin da'di 'karewa🙆‍♀️. Kuyi sharing like react da kuma comment domin samun cigaba da wuri🤓. Kuyi following wannan channel din domin samun cigaban labarin nan daga zarar ni Queen Jiddah na 'daura👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H Daga Al'kalamin Queen Jiddah....✍️ [11/21, 7:45 PM] null: 🥹GAMO MUKA YI🥹 Chapter 4 True Life Story😱🙆‍♀️ By Queen Jiddah...✍️ Free page is about to pinish🔔🤓🙋‍♀️ Idan kana bu'katar ka cigaba da karatun Littafin GAMO MUKA YI to ka hanzarta turo da ₦500 ta wannan bankin👇 0686693377 GT Bank HAUWA'U MUSA YELDU. Shedar Biya ta wannan layin👇 08145999600 A Chapter 6 free Page zai kare, idan har na kammala free page baka turo da kudin ka ba, Tofa zasu dawo ₦1000🤧 saboda haka saiku hanzar ta🤓. Wanda ya biya ya turomin da screenshot ta numbern dana saka, saina saka sa a paid group💃💃💃 Chapter 4 Haka naga wannan mayyar a mafarki tana biye dani, da wu'ka a hannun ta. Koda gari ya waye kowa ban gayawa ba naja baki na nayi gum kar kuma ace karya nake😔. Kuma maman mu taje gidan matar da sassafe ita da officer sai dai lokacin da suka je matar tariga da ta fita, haka mama ta dawo ta bamu labari, nidai bance komai ba, bayan mun karya kumallo haka mama ta shirya ta wuce gidan aikin ta, Nana ma tayi makaranta muka rage nida maryam a gidan. Duk inda maryam tayi haka nake binta a baya, domin kuwa har yanzu a tsorace nake🤧, ita kuwa sabgar gabanta kawai take yi babu alamun tsoro ko ka'dan a tare da ita. Bayan mun kammala aikin gida muka 'daura girki, maryam tace zata je ta siyo kayam miya, nace mata muje na rakata saboda bazan iya zama nika'dai ba. Haka muka tafi tare sai mita take min ni kuma nayi banza da ita, domin Allah ka'dai yasan halin da nake ciki, saboda dama can ni matsoraciya ce abu ka idan ke razana ni. Dawowar mu gidan siyan kayan miyan kenan muka nufi hanyar gida, ai kuwa muka yi kicibis da wannan mayyar da nayi mafarki jiya🙆‍♀️ domin ganin ta kawai muka yi a gaban mu, ni kuma sai na'ki yarda na kalle ta cikin karfin hali na raku'ba ta gefen ta na shige gida itama Maryam tabiyo ni a baya. "Malika! Malika!" Maryam ta kira ainahin suna na tana karasa shigowa cikin gidan namu. Kallon ta nayi nace. "Menene Maryam?". " hmm wai Malika kin kuwa ga Matar nan, wallahi ke take kallo har kika shege gida idonta yana kan ki". "Hmm na sauke nannauyar ajiyar zuciya sa'annan nace, wallahi Maryam na gani, kuma jiya har mafarkin ta nayi wai ta biyo ni da wu'ka, shiyasa ma yanzu ban yarda na kalleta ba, kinsan bamu ci abinci ba kuma ance maye yana saurin kama mutum musamman idan ya fita bai saka komai a cikin sa ba". " Hmm Malika kenan, Allah dai ya kare ki daga sharrin ta saboda ni wannan abin ya fara 'daure min kai, ace daga wannan sai wancan". Nace mata "Maryam kenan, to fisabilillah ita wannan mayyar ta rawa wa zata biyo saini, yo ina ma laifin ta biyo ki tinda ke kinada jikin ki tubarikalla, ni kuwa kamar a busa na fa'di, idan ba jaraba ba me maye zaici a jiki na😩". Maryam kuwa Ranta baci yayi cikin masifa tacemin. " Wallahi Malika mugun fatanki ya tsaya akan ki, a hakan dai da nake tu'bul tu'bul 'dina a haka zasu kyale ni, kuje can ku 'karata ai ke suka gani suka ce kinyi musu" a haka dai tayi ta masifa ni kuma na zuba mata idanu, tinda dai ba dakuwa zanyi a wurin ta ba. Bayan kwana biyu, muna zaune tare da Maman mu da kuma Maryam, sai nake cewa Mama. "Maman Mu nidai inason mussa( Mage ) dan Allah ki bari na kar'bo ta gidan Aunty Jamila wallahi ta kira ni ta gayamin wai Magen ta ta haihu nazo ta bani 'daya"😁. Daga Bu'dar bakin ta saita cemin. " Wai Malika lafiyar ki Kalau kuwa?". Sai nace "me nayi Maman mu?"🥹. " ok baki ma san me kika yi ba kenan? To idan baki sani ba bari na gaya miki, kinji na rantse wallahi babu mai kawomin Mage a gidan nan! Sanin kan ki ne sarai Nana tsoron mage take yi, shine saboda tsabagen son kai irin naki zaki ce ki kawo mana mage, to ba'a gidan nan ba, sai dai ko idan zaki je can Tudun Wada sai kije can ki zaune tare da magen". Ta fa'da tana huce kamar zata fashe, wai duk akan nace inason mage, harda cewa naje gidan kakar mu ta Tudun Wada, sai nace mata. "A a maman mu Dan Allah kiyi hakuri, na fasa bazan 'dauko magen ba". Saita mi'ke tsaye tana cemin " oho idan ma Zaki 'dauko to ba a gidan nan ba" ta 'karashe maganar tana shigewa bedroom din mu. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un!". Muka jiyo maman mu tana salallami a 'daki, ai kuwa da gudu muka shiga 'dakin nida Maryam. " Maman mu! Menene?" Muka fa'da nida maryam a tare. Hannu ta 'daura a ha'ba tana fa'din. "Amma wallahi 'berayen nan basu da mutunci, yanzu fisabilillah ku duba fa kuga, Kifin nan dana ajiye zanyi wa Jamila miyan cuwaka na Jego, shine dan banzan beran nan ya cinye" ta fa'da cikin takaici tana kallon mu. Ni kuwa dariya na 'barke da ita ina fa'din. "To Maman mu ba shine nace miki ki bari na 'dauko Mussa (Mage) a gidan Mama Jamila ba, amma kika 'ki, to aiga ranar Magen nan tazo" na 'karashe Maganar ina sake kecewa da wata dariyar. Da sauri na ruga aguje ganin Maman mu ta tinkaro ni, kwafa tayi tana cewa. "Ai da ki tsaya kiga idan jikin ki bai gaya miki ba, kuma mage dai ba a gidan nan ba, Maryam zoki je ki siyomin wani Kifin a kasuwa" ta fa'da tana bu'de jakar ta. Bayan isha'i ma haka muka shinfi'da yakusasshiyar katifar mu nida maryam muka kwanta, saboda har yanzu tsoro bai sake ni ba shiyasaban fara kwana ni ka'dai ba. Washe gari kuwa haka naji Maryam tana kwalamin Kira. "Malika! Malika!". Na tashi cikin masiba ina tambayar Lafiya Dan ubanki kike kwalamin wannan kiran? Ko bashin ki naci?". " la'ilaha illalahu muhammadur rasulullahi (s.a.w) Malika aida ni kika zaga tinda ni nace ta tayar dake" Maman mu ta fa'da tana matsar kwalla wai ala dole nayi mata rashin kunya🙄. Ba yanda na iya haka nace mata" maman mu dan Allah kiyi hakuri wallahi ban zata kece ba". "Hmm Naji meya kawo Mage a kusa dake?". " Mage kuma Maman mu?" Na fa'da ina waigen kusa dani. Kyakkyawar mage ce kuwa Light broun Mai dan girma kwance a kusa dani sai Sharara bacci take. "Na shiga Uku Malika wai nikam yaushe zaki barni na huta a gidan nan?" Maman mu ta fa'da tana kuka. Yayin da ni kuma na 'kurawa wannan magen ido ina Murmushi domin harga Allah inson Mage.....✍️ Hmm wata sabuwa inji 'yan caca💁‍♀️ da alama dai Malikan nan ba haka kawai take ba🤔 koya kuka ce?. Tau kardai ku manta yawan like share da kuma comment yawan page din da zanyi maku💃💃💃 Mu ha'du daku a chapter 5 domin yanzu aka fara🥳🥳🥳 Channel link anan zaku dinga samu daga zarar na 'daura👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H Daga Al'kalamin👑 Queen Jiddah....✍️. [11/27, 9:05 PM] Queen Jiddah: 🥹GAMO MUKA YI 🥹 Chapter 05 True Life Story 🙆‍♀️😱 By Queen Jiddah...✍️ Free page is about to finish🧏 Saboda haka ku hanzarta ku biya kudin ku ₦500 kacal🤌 Domin cigaba da Karatun Littafin🤓 idan na kammala shi zan sayar da document ₦1000. Akwai group na musamman, ga masu bukatar littafin GAMO MUKA YI na karatu🤓. 0686693377 GT Bank Hauwa'u Musa Yeldu Shedar biya ta wannan layin👇 08145999600. Wannan shine YouTube channel Dina, ana zaku dinga samun Na saurare insha Allah. https://youtube.com/@queenjiddahnovels?si=mX_BU1my5mNkYrsX Akwai VIP group ₦1000 Normal group ₦400 Na tanadesa ne domin wa'yanda ba zasu iya zuwa YouTube su 'dauko na saurare ba, acan zan dinga Saka maku dashi, amma fa Littafin GAMO MUKA YI kawai🤓👌 A VIP group zan dinga Saka litattafaina na saurare duka💃💃 0686693377 GT Bank Hauwa'u Musa Yeldu Shedar biya ta wannan layin 👇 08145999600 Allah ya Baku iKon biya🤓🤲. Chapter 05 Ni Kuma ban furta komai ba, face cigaba da kallon Magen da nayi Ina murmushi, domin harga Allah inason Mage, shiyasa nayi farat Daya ta shigemin arai. Jikin Maman mu a matukar sanyaye ta 'dau hijabinta ta Saka domin wucewa gidan aikinta, domin harga Allah itadai hankalinta Bai kwanta da Magen nan ba. Maryam kuwa ko a jikinta, domin sabgogin gabanta kawai take yi, Daman ita ba Mai shiga abinda Bai shafe ta bace. Ni kuwa a wannan ranar cikin farin ciki na fara aikace aikacen gidan, Kai harda na Maryam na ha'da duk nayi, Mage ta kuwa duk inda nayi haka take bina a baya, tana ma'kal'kaleni, farin ciki duk ya isheni, yau Gani ga Mage. Bayan kammala aikin gidan MUKA zo MUKA zauna nida Maryam domin karya kumallo, itama

Chapter 1 of 9