Share this page
2 / 9
magen tawa haka tazo a kusa Dani ta zauna tana kallon mu, abinda ya 'kara burger ni da ita shine , ita ko iron yanda Mage keyi idan suka ga abinci suzo suna shinshinar sa sam bata YI, kawai lafewa tayi a jiki na, ni Kuma na dinga shafa jikin ta. "Malika gaskiya sai dai ki Nemo waje ki 'debi naki abinci, domin ba zai yiyu ki shafa mana gashin mage a abinci ba" Maryam ta fa'da tana wani kumbura fuska. Murmushi nayi nace "Haba Maryam, yanzu fisabilillah ita magen I tace abin kyama? Karfa ki manta acikin sahabban manzon Allah (s.a.w) akwai Wanda har Abu Huraira ake ce masa, saboda yanda yake tsananin son Mage "na fa'da Ina sake shafa jikin Magen, murmushi 'dauke a fuska ta. "To naji, aike ba Kya cikin sahabban nasa, saboda haka koki daina ko wallahi a raba abincin " ta fa'da cikin tijara tana kallona. Daina shafa magen nayi na Sanya hannu na a cikin kwanon abincin, na joloup din Taliya wace taji kayan ha'di sai kamshi take yi, na 'debi kadan na sanyawa Mage ta, ai kuwa ta fara cin abincin cikin kwanciyar hankali, nayi shiru Ina kallon ta, can dai nayi Bismillah sa'annan na Sanya hannu tare da fara cin abincin nima. GABA 'Daya yinin ranar a haka MUKA wuni, lokacin da Nana ta dawo daga makaranta, bata wani tsorata ba da taga magen, saboda magen ko Ina bata zuwa, idan har kaga taje wani wurin , to nice naje ita Kuma ta bini abaya. Da daddare ma bayan Mama ta dawo bata sake magana akan magen ba, Gani da tayi nana bata tsorata ba kamar yanda ta saba. Da muka zo kwanciya, daga ni sai Mage ta kadai muka kwanta a katifa, saboda Maryam cewa tayi ita wallahi ba Zata kwanta da mage ba wai saboda yanda mage keda son jiki, nace mata kanta ake ji, haka ta tattara inata da nata ta koma wajen Nana suka kwanta a tare, ni Kuma na kwanta a kusa da mage ta muka rungume juna. Da misalin karfe 2:30 na dare na dinga Jin Mage ta tanata yakushi na, idan na tashi saita daina idan Kuma na koma na kwanta saita cigaba. Da naga ba Zata daina ba, haka yasa dole na tashi na fita waje ita Kuma tamin rakiya, ban'daki na shiga na fito madaidaicin tsakar gidan mu nayi alwala kana na koma 'daki na shimfi'da dadduma na tayar da sallah, ita Kuma magen tawa tayi kwanciyar ta akan dadduma kusa Dani. Raka'a biyu nayi, tare da tasbihi sa'annan na shafe addu'a na lankafe sallayar ka na nakoma saman yakusasshiyar katifa ta na kwanta, Mage na biye Dani abaya, itama ta kwanta nan take bacci yayi awon gaba damu. Washe gari ma haka MUKA sake tashi, Ina lure da maman mu tana fushi dani amma nayi kamar ban Gani ba, zamu karya kumallo Maryam ta 'debi fatefaten Kanzon da muka yi Wanda yasha alayyahu a cikin sa, ta sanyawa Mage ta a gaban ta, amma ko ka'dan magen bata Kalli wannan abincin ba ballantana taci. Maryam tace "Malika anya kuwa magen nan taki lafiya kalau take?". Nace "Me kika Gani halan?". Tace "duba fa kiga na Saka MATA abinci, amma ko kallon sa ba tayi ba". Nace "iKon Allah, to bari na gwada Saka mata muga ko zata ci" na sanya hannu tare da 'dibar kadan na Saka mata, ai kuwa ta matso da sauri ta fara ci. Nayi murmushi nace "to Kinga dai ni dana Saka mata taci, Ina tinanin bata son abincin hannun kowa saina Mai ita" na fa'da Ina murmushi. Maryam kuwa cewa tayi" Amma fa wallahi Magen nan taki munafuka ce, aikuwa zanga wanda zai bata abinci a gidan nan idan bakya nan" ta fa'da tana kumbura fuska wai ita ala dole ranta ya baci. Maman mu dai komai bata ce ba, saima murmushi da tayi tana Mai jinjina kanta, wanda ita kadai tasan manufar hakan. Tun daga wannan lokacin Koda ace fita nayi, tofa mage ta ba zata ci abinci ba harsai na dawo, idan na dawo haka za kuga ta she'ko a guje ta tarbeni tana min oyoyo, idan Kuma naje wani wajen nayi kwana 'daya ko biyu, tofa idan na dawo bata kulani, Kuma a haka zata zauna bataci komai ba, wai ita ala dole fushi take yi. Dana lura da hakan saina dinga fita tare da ita, domin ko bakin shago zani, Bina take a baya, idan Maman mu ta aikeni, ma tare da ita nake zuwa shiyasa na dena cewa Maryam tamin rakiya kwata kwata saboda daman, idan na nemi rakiyarta ta dinga min mita kenan, yanzu kuwa na samu 'yar rakiya wace bata gajiya Dani. Har a unguwar mu ma cemin ake YI Malika Mai Mage, ni kuwa sam hakan baya damu na, saima dadin hakan dana keji. Ranar wata Juma'ah, a haka na shirya nacewa Maman mu zanje Tudun Wada, gidan kakarmu, so nake nayi kwana biyu a can, saboda akwai shakuwa sosai tsakani na da ita. Tace min saina dawo, na shirya cikin farin ciki, itama Magena na shirya mata. Domin har Karamar jaka na saya mata, wace nake saka mata madarar ta da kuma sauran abubuwan ta. Shukrah! Shukrah! Na ambata Ina kallon kofar falon mu, saiga mage ta, ta she'ko aguje ta tsaya kusa Dani, na rataya jakata na sunkuya na 'dauki Mage ta shukrah, nacewa Maman mu. "Maman mu mun tafi sai mun dawo". "Allah ya tsare " tace min ta cigaba da sabgar gaban ta. Ni Kuma nayi murmushi Ina yiwa Maryam da Nana bye bye na wuce nida Shukrah zuwa waje. Ina fita na tari adaidaita na hau, kasancewar gidan mu akan titi yake. Bai tsaya Dani ko Ina ba sai Tudun Wada gidan kakarmu, na sauko tare da Daukar jakata na rataya, ka na na'dauki shukrah na runguma a jiki na, shi Kuna na biyasa ha'kkinsa.....✍️ Hmm masu karatu, ku biyo ni a Kashi na gaba din ganin irin rawar da shukrah Mage zata taka a gidan kaka tare da Malika, karku bari a Baku labari🤓. Kuyi sharing like da Kuma comment domin samun update da wuri👌. DAGA AL'KALAMIN👑 QUEEN JIDDAH.....✍️ [11/30, 9:16 PM] Queen Jiddah: The Pen Of 👑Queen Jiddah.....✍️ Channel Link https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H Update group Link https://chat.whatsapp.com/LZtufHUnlqUFvnBvvoUWs3?mode=hqrt3 YouTube channel Link https://youtube.com/@queenjiddahhausanovelschannel?si=NajxqyDlNBtjeOPh Arewa Book channel https://arewapen.com/u/hauwaumusa06 Facebook page Link https://www.facebook.com/profile.php?id=61580403014165 Facebook group Link https://facebook.com/groups/559415480283144/ 🥹GAMO MUKA YI🥹 True Life Story By QUEEN JIDDAH Chapter 6 Da sallama na shiga gidan kaka ta, A farfajiyar gida na tarar da ita, tare da Matan cousins dina , ko wanen su ya zubamin Ido yana kallon na, da yake family house ne gidan, shiyasa ko yaushe bai rabo da jama'a. Ban damu da kallon 'kurillan da suka bini dashi ba, na nufi wajen Kaka ta Ina murmushi, saboda idan da sabo mun saba, nida su, musamman daya zamanto cewar inada sha'kuwa da mazajen su, to ko wace a cikin saita 'dauki Karan tsana ta 'daura a kaina, ni kuwa ko a jiki na, domin nasan Babu komai tsakani na da mazajen su. "Kaka! Oyoyo, nayi kewar ki" na fa'da tare da rungume ta. Shiru nayi Ina kallon ta Ganin Bata rungume ni ba, kamar yanda ta saba, sai nayi sororo Ina kallon ta. Da sauri ta ja, hannu na ba tare da tace komai ba, muka nufi falon ta. Bamu zame a ko Ina ba, sai uwar 'daka, ta zauna gefen gado, sai nima na zauna a kusa da ita Ina Mai fuskantar ta. Mage ta kuwa ta callara 'kara, sakamakon yanda na matse ta, na sake ta da sauri Ina fa'din. "Ayya Shukrah sannu, na matse ki ko?". "Malika!". Na 'dago da sauri sakamakon Jinda nayi kaka ta ambaci suna na, Ina fa'din "Na'am kaka". "Malika Daman da gaske ne, cewar kina yawo da magen da, Babu Wanda yasan inda ta fito?" Kaka ta fa'da a tausashe tana kallon na. Kasa amsa mata nayi, face shiru da nayi kaina a kasa Ina wasa da 'yan yatsun hannu na. "Malika ya zama dole ki jefar da magen nan!". Da sauri na 'dago, sakamakon jin furucin da kaka tayi, zuciya ta na tsananta bugawa. "Kwarai kuwa, dole ki rabu da ita, domin inaji Ina Gani ba yanda za'ayi, na ganki a masifa ba tare Dana fitar dake ba, bayan inada yanda iKon hakan". "Masifa fa kika ce Kaka?" Na fa'da Idona na ciko da kwalla. "Tabbas kuwa Malika, domin wannan Masifa ce, Malika kin ta'ba ganin inda Aljani ya shiga cikin jikin mutum yayi shekara da shekaru a jikin sa,ba tare daya cutar dashi ba?". "A a kaka" na fa'da jiki na a matukar sanyaye. "To inaso ki sani, shifa wannan a 'boye ne yake cutar da bil'adama, ba tare da sanin kowa ba, ina kuwa ke da kike yawo dashi a Koda yaushe, ka na ki kwanta ki tashi duk a tare dashi, Kuma a bayyane mutane suna ganin sa a siffar wata Dabba wai mage!". Dum! 'kirji na yayi, mummunar fa'duwa, yayin da gumi ya keto min, na fara ganin dishi dishi, Gani na yana barazanar 'daukewa!. Ni Malika, nida a rayuwa ta, Babu abinda nafi tsoro kamar Aljani, Amma nice nake rayuwa a tare dashi?. Na tashi da sauri, na fa'da jikin Kaka, tare da fashewa da matsanancin kuka, har numfashi na yana shu'dewa. "Kaka Meyasa? Meyasa nake ha'duwa da irin wa'yan nan 'kaddarori a rayuwa ta ?, meyasa ni ka'dai? Shin wane kalar zunubi na aikata a rayuwa ta, da har ubangiji yake jarabta ta, da haka....". "Akul din ki Malika!" Kaka ta fa'da tare da Sanya hannu ta toshemin Baki na. "Malika karki sake na sake jin irin wannan furucin ya fito daga bakin ki, ki sani duk wani abu da ubangiji ya zartar a rayuwar bawan sa, tabbas Mai kyau ne". "Tau Amma kaka! Meyasa nake yin GAMO a Koda yaushe? Meyasa ba zan zauna lafiya ba tamkar ko wane 'dan Adam?". "'Kaddara Malika! Tabbas 'kaddarar kice a haka, sai dai idan kika yi hakuri zaki samu nasara, domin inaji ajiki na, kyakkyawar 'Kaddara ce ke 'dawainiya da rayuwar ki Malika" kaka ta fa'da tare da Sanya hannu ta goge mini hawayen fuska ta. Da sauri na tashi daga jikin Kaka Ina Mai Sanya hannu, na 'karasa goge hawaye na, na fara waigen gefe da gefe na. "Kaka Ina Mage ta? A nan fa na sake ta, Kuma Bata fita ko Ina sai tare Dani". "Hmm Malika kenan, Magen ki fa ta Riga da ta tafi, tafiya ta har abadah! Ki kula da kanki Kuma ki dage da addu'a, domin Ina iya han'go 'kalubali tafe a rayuwar ki nan gaba! Sai dai fa ki sani zaki ji da'di nan bada jimawa ba insha Allah, wannan tabbacin ne nake baki, Koda bayan Raina ki tuna da wannan" kaka ta fa'da murmushi 'dauke a fuskar ta tana kallon na. Na 'dago na kalle ta Ina tsiyayar da hawaye, ita Kuma ta jinjina min kanta alamun tabbatarwa. A haka na cigaba da rayuwa a gidan kaka, ko waje bana fita, kullum Ina 'daki, motsi ka'dan idan naji zan waiga, domin har yanzu, Dana cika kwanaki biyu a gidan kaka, ban cire Rai da dawowar Shukrah ba, domin kuwa Ina matukar kewar ta, kamar yadda Babu shakka Ina tsananin tsoron ta!. Jiki na a mace na tashi, na shiga ban'dakin kaka, tare da 'dauro alwala na fito, sakamakon kiraye kirayen azahar da na fara jiyowa a masallatai. Kaka ce ta shigo 'dakin da sallama, lokacin harma idarda sallah Ina Jan carbi, kular abincin ta ajiye min ta fita, wai zasu je ma'kota barka, nace saita dawo Allah ya tsare. Bayan ta fita na bu'de kular kamar ba zanci ba, Amma ganin abincin kalar Wanda nafi sone yasa na fara ci, joulop 'din macaroni ce wace taji carbej aciki, na kuwa ci abincin sosai, na bu'de fridge 'din 'dakin na kwarara kunun Aya Mai sanyi a Dan madaidaicin Kofi nasha, ka na, na tattara kayan na fita dasu waje, na dawo na Nemi lafiyar katifa na kwanta, saboda bala'o'en baccin daya tasomin. manyan motoci ne a kalla guda goma, Nevy blue ne , saita tsakiyar su wacce I tace fara kall, wace ke tsananin she'ki da 'daukar Ido take. Gudu suke shararawa a saman kalta, sai kace dansu akayi titin. Gudu nake sosai a tsakiyar jeji, yayin da wani bijimin kare ke Bina a baya, sai haushi yake tamkar zaici Babu, ni kuwa gudu nake ko takalmi Babu a 'kafa ta, gashin kaina a hargitse, yayin da kaina ke tsiyayar da jini, sakamakon fa'duwar da nayi kaina ya bugi dutse. Gudu nake Ina waigen baya na, yayin da wannan Bijimin Karen ke Bina tamkar zai kama ni, Wanda yayi dai dai da lokacin da na samu nasarar fita daga jejin Ina, Mai hayowa kan kwalta. Hakan kuwa yayi dai dai da isowar wa'yan nan manyan motocin, ni kuwa na kawo a huje, ji kake bam!. Wannan motar ta farko ta ka'de ni, da sauri gaba 'daya motocin suka tsaya a tare, yayin da wani daga cikin yaron motar ya fito da sauri ya nufi wannan motar ta tsakiyar, wacce, ogan su ke ciki yana Mai bu'de masa kofa. Ya sanyo dogayen 'kafafuwan sa waje, cikin shigar 'kananan kaya, ya fito , yayin da wani daga cikin yaran nasa ya fito da lema yana Mai zuwa bayan sa, ya rufa masa ita. Shi kuwa sauri sauri yake tafiya cikin zafin nama harya 'karaso wajen da nake kwance a kan kwalta, jini na tsiyaya ajiki na, ya Sanya hannu ya tallafo ni tare da 'dauka ta kacokan zuwa mota, ni Kuma na bu'de lumsasshin idanuwa na cikin azaba, na 'daurasu a kansa, da sauri na sake ware Idona sakamakon tozali da nayi da kyakkyawan ba'indiye, Wanda ko makaho ya shafa yasan shi 'din ba jinin Hausawa bane, to wa ne ne shi?. Ban samu amsar ba, sakamakon idanuwa na da suka rufe ruf, ta yanda ni kaina bansan a inda nake ba. "Malika! Malika!" Nayi firgigit na tashi daga mafarkin da nake, Ina waige waige, yayin da gumi duk ya ji'ka ni. "Lafiya kuwa Malika? Gumin me kike yi haka, gashinan duk kinyi wani iri" kaka ta fa'da tana tsure ni da Ido. "Babu komai kaka, har Kun dawo ne?" Na fa'da 'kirji na yana harbawa, Ina kallon ta. "Eh mana, tin 'dazu Muka dawo ai, sanda na shigo kina barci shine ban tashe ki ba, Murjanatu Kam ai ta haifi santalelen yaro sak mahaifin sa" kaka ta fa'da tana murmushi. Murmushi nima nayi, sa'annan nace. "To kaka, Allah ya rayar suwa akan Sunna, bari na 'dauro alwala naji kamar Kiran sallar la'asar akeyi" na 'karashe maganar Ina shiga ban'dakin na Kaka. Yayin da ita Kuma ta tashi ta nufi farfajiyar gidan, jin kamar hatsaniya na tashi.....✍️ Hmm masu karatu, ha'ki'ka rayuwar Malika tana dauke da kalubali, sar'ka'kiya, da Kuma boyayyiyar 'kaddara, sannu a hanlaki zaku fahimta. Kardai ku manta, yawan sharing da comment din ku, yawan update din Queen Jiddah 🤓. DAGA AL'KALAMIN QUEEN JIDDAH....✍️ [12/4, 6:36 PM] Queen Jiddah: The Pen Of 👑Queen Jiddah.....✍️ Channel Link https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H Update group Link https://chat.whatsapp.com/LZtufHUnlqUFvnBvvoUWs3?mode=hqrt3 YouTube channel Link https://youtube.com/@queenjiddahhausanovelschannel?si=NajxqyDlNBtjeOPh Arewa Book channel https://arewapen.com/u/hauwaumusa06 Facebook page Link https://www.facebook.com/profile.php?id=61580403014165 Facebook group Link https://facebook.com/groups/559415480283144/ 🥹GAMO MUKA YI 🥹 Chapter 7 True Life Story By Queen Jiddah....✍️ Da fitowa ta banɗaki na fita waje da sauri, sakamakon matsananciyar hayaniyar da naji tana tashi a waje. Shiru nayi ina mai dakatawa daga wajen da nake tsaye, jiki na a matuƙar sanyaye. "Ke munafukar Allah! Maza ki ƙaraso nan, don wallahi yau, mai hana ki daku a waje na sai Allah". Yaya Hansatu ta faɗa, tana cika tana batsewa, ita ɗin ta kasance matar Cousin ɗina ce Muzbahu. Dum! Kirji na yayi mummunan bugawa, nayi tsaye baki sake ina kallon Hansatu, wacce tazo ta cimin kwalar riga tana jijjiga. "Akul Ɗinki Hansatu! Karki kuskura hannu ki ya taɓa jikin ta, idan ba haka ba wallahi kinji na rantse yau a gidan ku zaki kwana!" Yaya Muzbahu ya faɗa ransa a ɓace. Ni kuwa shiru nayi, da naga ta sakarmin riga ta, na sauke nannauyar ajiyar zuciya hawaye suka fara gangara daga idanuwa na. "Ai dole kace zaka sake ni, saboda kaje ka Auro wannan figaggiyar kazar, mai kama da al'janu, da nace kana son yarinyar nan, cikin kayi ba gaskiya bane, kai me zaka yi da ita? Yanzu kuma shine kullum daina kama ka kana kallon hoton ta, sai kace wanda aka asirce, hakan duk bai maka ba harda, zuwa kaje kayi mata sayayyar kayayyaki masu tsada, wa'yanda ko Ni da nake matar ka baka siya min, to wallahi sai Allah ya bimin haƙƙi na, mugu kawai azzalumi" Hansatu tana gama faɗar hakan, ta kwasa a guje tayi ɗakin ta tana zubar da hawaye. Yayin da Ni kuma nayi sororo ina biyar ta da ido hatta ɓacewa gani na, shin hoton waye Yaya Muzbahu ke kalla a koda yaushe? Me zai sa yayi min siyayya? To me ma ya siyo min? Kardai zargin su Hansatu ya zama gaskiya, cewar mazajen su ni suke so! To ma saboda meye zasu so ni? Dududu fa a shekarar nan na cika shekara ashirin. Lallai kuwa barin gidan kaka ya cimmin, a yau ɗin nan ba sai gobe ba,domin kuwa ba ta yanda za'a yi ina ji ina gani, ayi mutuwar aure a gaban ido na, kuma ta sanadiyya ta. "Kaka! Dan Allah kiyi haƙuri, kar wannan shashancin na Hansatu ya dame ki". Yaya Muzbahu ya katsiyemin tunani, ta hanyar furta wa kaka hakan. Jiki na ne ya sake mutuwa, ganin yanda kaka ta washe baki tana faɗin. "A a Muzbahu, ko kusa wallahi Ni raina bai ɓaci ba, saboda idan dai Hansatu ce ai inda sabo mun saba, kuma ita bata isa ta lalata zumunci dake tsakanin ka da Malika ba, sam bata isa ba". Da sauri ya washe Baki yana miƙawa kaka ledar hannun sa, tare da faɗin. "Tau shi kenan kakar mu, godiya nake, gashi sai a bawa Malika, kuma ɗan Allah kaka ki sake lalla shin ta, kin san ƴar leler jikar taki halinta sai ita" ya ƙarashe faɗa yana yi mata saida safe, tare da shigewa ɗakin Hansatu. Ita kuwa ta karɓi ledar sai saka masa albarka take yi. Ni kuwa ina nan sai kallon ikon Allah nake, domin har yanzu Ban motsa daga wajen da nake ba, tambaya nake a cikin raina, to ita kaka Meya Kaita karɓar ledar yaya Muzbahu, bayan tasan duk saboda wannan ledar ce ake wannan hasumin, A iya sani na da kaka ba tadà kwaɗayi, ballantana nace saboda kwaɗayi ta karɓa, to kenan me ƙarɓar wannan ledar yake nufi? Ya zama dole na samo wannan amsar a wajen kaka. "Ke Malika! Tunanin me kike yi ne haka?". Kaka ta faɗa tana dafa kafaɗa ta, ban tankata ba saima idanu dana zuma mata ina kallon ta. "Zo muje daga ciki" ta faɗa tana jan hannu na zuwa cikin ɗakin ta. Yayin da sauran matan gidan dake tsai tsaye suna tsintse da tsegumi, ganin mun shige ciki sai kowacce a cikin su, ta kama sabgar gaban ta. Zaune nayi tamkar wata mutum butumi, a gaban kaka, ina biyar ta da kallo ita da ledar hannun ta. "Malika!". "Na'am kaka" na faɗa murya ta a raunace ina kallon ta. Murmushi tayi, tana mai girgiza kanta, sa'annan tace. "Wai Malika sai yaushe ne zaki ari rigar jarumta ki sanyawa kanki? Yanzu fisabilillah sai ki ka yi tsaye sororo, a gaban Hansatu ta wani cumuimuye ki, zata daka, sai kace wata dafaffiyar kaza?, haba Malika wannan sululhlun naki yayi yawa wallahi komai kuka? To har zuwa yaushe ne za'a daina tare miki faɗa?". "Wallahi nima ban sani ba kaka" na faɗa ina kuka tamkar raina zai fita. "Ji nake kawai ina kuka ba tare da nasan da zuwan sa ba, kaka Meyasa rayuwa ta zata kasance a haka? Meyasa duk wani mafari na shafin rayuwa ta baya kasancewa Alkhairy ne....". "Akul Ɗinki Malika! Wai ba na hana ki irin wannan zancen bane?" Kaka ta faɗa jikin ta a sanyaye tana kallo na. "Yi haƙuri kaka, bazan sake ba da yardar Ubangiji, amma kaka Meyasa kika karɓi ledar yaya Muzbahu?" Na faɗa ina tsure ta da idanu, hallau hawaye basu daina zuba daga idanu na ba. "Malika kenan, nasan zaki ji mamakin karɓar ledar Muzbahu da nayi, amma ina so ki sani koda ace Muzbahu shine kaɗai namijin da ya rage a duniyar nan, to Ni Kuwa bazan bari ki aure sa ba! Nasan kin san cewar matsayin ki ɗaya dashi a waje na, domin yanda ki ke jika ta, shima jika na ne. Daman na karɓi ledar ne kawai ko hakan zai sa waccen fitsararriyar matar tasa ta shiga taitayin ta, amma ko kusa bawai don na amince da muradin sa ne ba" kaka ta faɗa tana sakarmin da murmushi. Nannauyar ajiyar zuciya na sauke, ina mai hamdala ga Ubangiji, daya kasance zargi na bai zama gaskiya ba. Hannu kaka ta saka tana mai share min hawaye na, ka na ta rike min hannu tana kallo na, ba tare da tace komai ba. Da kuka sosai na fashe ina faɗin "Kaka!". "Na'am Malika" kaka ta faɗa tana kallo na,tare da ƙoƙarin ɓoyemin damuwar ta. "Kaka a koda yaushe ji nake tamkar Ni ba mace ɓace kamar sauran mata! Ji nake kamar na banbanta dasu, ina jina a takure musamman idan naga saurayi da budurwa suna taɗi, na kanji tamkar na zubda hawaye! Kaka sanin kanki ne, a yanzu haka inada shekaru Ashirin a duniyar nan, amma ban taɓa jin kalmar so ta fito daga bakin namiji ba! To me yasa kaka? Kodai niɗin bani da farin jini ne? Kamar yanda nake jin ƙawaye na suna faɗa, da yawa masu furta min kalmar so, zaki ga basu cancanta ba, mafi yawan su mutanen banza ne, wasunsu kuma ƴan gida ne, waƴanda alaƙata dasu bazai haifar da komai ba face taɓarɓarewar zumuncin mu, saboda da yawan su iyayen su sun tsane Ni" na ƙarashe maganar cikin kuka ina kifar da fuska ta a tafukan hannaye na. Shiru kaka tayi na ɗan wani lokaci, sa'annan ta matson kusa dani, tana mai bude fridge ɗinta ta kwararo ruwa a ƙaramin cup, tare da tofamin addu'a cikin su, ka na ta bani nasha. Ina shan ruwan kuwa na shiga sauke ajiyar zuciya ba ƙaƙƙautawa, ina jin wani nauyi na raguwa a zuciya ta. "Malika!". Kaka ta sake ambatan suna na, tana kallo na, ban amsa ta ba, saima ɗagowa da nayi ina kallon ta idanuwa na cike da ƙwalla. "Malika ina so ki sani, duk wani ɗan adam yana dauke da tashi zanen ƙaddara, wanda ke rubuce a cikin littafin lauhil Mahfouz, babu wani motsi da wani ɗan adam zai yi, face yana rubuce a cikin sa, a cikin sa aka rubuta arzikin ɗan Adam da kuma talaucin sa, Rayuwar sa da kuma mutuwar sa, ajalin sa da kuma sanadiyyar sa, shin ɗan wuta ne ko kuma ɗan aljanna ne. Saboda haka ina so ki saka a ranki Mijin ki yana rubuce a cikin wannan littafin, kuma tabbas zai bayyana, a jiki na nake ji Malika, ji nake tabbas mijin ki na musamman zai kasance, saboda haka mu cigaba da Addu'a, hakiƙa Allah baya bacci, kuma alhayyul Qayyum ne, wato rayayye kuma tsayayye, idan muka miƙa lamurran mu a hannun sa tabbas zai share mana hawaye, domin baya taɓa tozarta waƴanda suka dogara dashi" kaka ta Ƙarashe maganar cikin ƙwarin guiwa tana jinjina min kanta alamun tabbatarwa akan zancen nata. Ina murmushi na isa kusa da ita, tare da rungume ta ina sharar ƙwalla. "Kaka! Yanzu da gaske nima zan samu wanda zai soni har muyi Aure dashi?". "Tabbas kuwa Malika! Insha Allah ". Ƙara rungume ta nayi ina faɗin. "Nagode sosai Kaka! Aduk lokacin da na tsinci kaina a cikin duhu, ke kike haskamin fitila, ina alfaharin samun ki a matsayin kaka ta". Na faɗa ina sake fashewa da kuka. "Oh oh ni Kulu, Malika da alama daɗin kukan nan kike ji, saboda haka tashi Ni karki Karyawa ƴaƴana uwar su, ki kaisu ki baro" kaka ta faɗa tana dariya. Nima dariyar nayi, muka miƙe gaba dayan mu domin mu ɗauro alwala, saboda kiraye kirayen sallar magriba da muka fara jiyowa a masallatai.....✍️ Hmm muje zuwa fans of Queen Jiddah, yanzu aka fara insha Allah 🤗. Idan kun lura na ɗan jima banyi update ba, saboda bakwa yin sharing, saboda haka sai ku gyara, nima na gyara alkalami na🤓. Daga AL'KALAMIN QUEEN JIDDAH.....✍️. [12/5, 8:42 PM] Queen Jiddah: The Pen Of 👑Queen Jiddah.....✍️ Channel Link https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H Update group Link https://chat.whatsapp.com/LZtufHUnlqUFvnBvvoUWs3?mode=hqrt3 YouTube channel Link https://youtube.com/@queenjiddahhausanovelschannel?si=NajxqyDlNBtjeOPh Arewa Book channel https://arewapen.com/u/hauwaumusa06 Facebook page Link https://www.facebook.com/profile.php?id=61580403014165 Facebook group Link https://facebook.com/groups/559415480283144/ 🥹GAMO MUKA YI 🥹 Chapter 8 True Life Story By Queen Jiddah....✍️ Koda na sallame sallar Magriba, ban tashi daga wajen da nayi sallah ba, anan na zauna ina jan karbi har aka kira isha'i, bayan

Chapter 2 of 9