nayi sallar Isha ma ban tashi daga wajen ba, sai da nayi shafa'i da wuri, nakai kuka na wajen mai duka, na jima a wajen ina yabo da zikiri wajen Ubangiji, tukunna na tashi tare da lankafe sallayar da nayi sallah, na ajiye ta a muhallin ta, ka na naci abincin dare tare da kaka, sai fira muke muna nishaɗi har muka kammala, na kwashe kwanikan nakai waje tare da wanke hannu na, na dawo akan lafiyayyar katifar ta na kwanta, ai kuwa nan take, bacci yayi awon gaba Dani.
Ɓangaren Hansatu da Muzbahu.
Tun lokacin da ya dawo daga sallar Isha, ya tarar da ita tana harhaɗa kayanta, yayi sallama bata amsa mishi ba, yi yayi kamar bai gane fushi take yi ba, ya tambaye ta ina abincin sa, nan ma bata kula sa ba, saima
zuge marfin babbar bakkon ta da tayi, bayan ta kammala loda ƴan tsimokaran kayan ta ciki.
"Wai Hansatu wane irin iskanci ne ke samun ki? Tin ɗazu sai magana nake kinmin banza, sai kace da kurma nake magana".
Nanma bata tankasa ba, saima cicciɓar ƙatuwar bakkon ta da tayi tana ƙoƙarin fita daga ɗakin.
Da sauri ya sha gabanta, yana riƙe bakkon da iya ƙarfin sa.
"Haba Hansatu! Dan Allah ki daure ki amsa min mana, kin barni sai magana nake Ni kaɗai kamar tsohon mahaukaci, ina zaki je ne cikin daren nan? Harda ɗaukar kaya haka".
"Gidan uba na zanje!, nace gidan uba na zance Muzbahu Yanzu ai ka ji, nasan kasan da cewar Ni ba Shegiya ɓace, da uba na, don ba a bola ka tsinto Ni ba, saboda haka maza gafara ka bani waje na wuce" ta faɗa tana gallara masa harara, idanuwanta sunyi jajir.
"Haba Hansatu! Me yayi zafi har haka ɗan Allah?".
"Me yayi zafi? Tambaya ma kake kenan, Muzbahu Ni Hansatu zaka cewa idan har na saka hannu na daki Malika a gidan uba na zan kwana yau? Saboda bani da daraja a wajen ka? To ka kwantar da hankalin ka, Isha Allah yau ɗin nan a gidan uba na zan kwana, dai dai da second ɗaya bazan ƙara a gidan nan ba, kuma wallahi saina zubda cikin ka dake jiki na, domin bazan taɓa haɗa jini dakai ba!".
Tana gama faɗar hakan ta shige ta gaban sa zata wuce, yayi saurin sanya hannu ya ɗamƙo ta, jiyojin kansa na miƙewa gumi ya fara keto masa, domin duk duniyar nan idan da abinda Muzbahu ke so ya gani bai wuce gudan jinin sa ba, yana son yara, kuma yana so a haifa masa nasa, ita kanta Hansatun tasan da hakan shiyasa zata yi amfani da cikin dake jikin ta yanzu, a domin ta raba tsakanin sa da Malika! Kasancewar itama bata jima da gane tana ɗauke da cikin ba, a yau kuma idan dare yayi taso tayi masa albishir saiga wannan saɓanin ya gifta.
"Hansatu ke ce ke ɗauke da juna biyu? Tun tsawon yaushe? Meyasa baki gayamin ba?".
Ya jero mata tambayoyin a lokaci guda, yana mai sanya hannu ya dafa kafaɗar ta tare da fuskantar ta, fuskar sa na bayyanar da farin cikin da yake ciki.
"Koma tsawon yaushe ne watannin cikin bai shafe ka ba" ta faɗa tana tsiyayarda hawayen makirci.
"Bai shafe ka ba, Muzbahu tunda dai dani da kuma ɗana ba ka ƙaunar mu, har kake cewa zaka datse igiyoyin auren mu, duk akan kana so ka Auro Malika! Saboda haka wallahi saina zubar da cikin, ba zan taɓa haifar sa ba'....."
Tass kake ji, ya kwashe ta da lafiyayyar mari, ta ɗago da sauri hannun ta dafe da kuma tun ta.
"Wallahi Hansatu idan na sake jin kalmar zubda min da ciki a bakin ki, ranki zai yi mummunan ɓaci a wajen nan".
"Wallahi sai na zubar! Kamar yadda na ƙare zama a gidan ka daga yau ɗin nan, to shima wallahi ya gama rayuwa a ciki na" ta ƙarashe maganar cikin kuka tana shirin barin ɗakin, a wannan karon ma, ko bakkon Tata bata ɗauka ba.
"Inna lillahi wa inna lillahir raji'un".
Muzbahu ya faɗa yana mai dafe kansa da sauri, saboda yanda yayi mummunan daurawa, ka na ya miƙe da sauri yana isa wurin Hansatu, wacce ke ƙoƙarin fita daga ɗakin, dawo da ita yayi, yana mai zaunar da ita akan madaidaicin gadon su, ya sanya hannu tare da share mata hawaye, kana ya sauke nannauyar ajiyar zuciya Yana mai faɗin.
"Hansatu dan girman Allah kiyi haƙuri, wallahi wannan duk laifi nane, karki hukunta yaron da bashi da laifi, ki sani fa shi baima san wainar da ake toyawa ba".
"Amma ai shi ubansa ya sani, idan har shi bai sani ba" ta faɗa cikin kuka tana mai sanya gefen mayafin ta, tare da face majinar hancin ta.
"Yanzu Hansatu kina nufin zaki iya hukun ta jinin ki da hannun ki, akan laifin da uban sa ya aikata miki?".
"Idan ba kada abin faɗa ka cika ni" ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa tsaye.
"Dan Allah Hansatu kiyi haƙuri, idan har akan zancen Malika ne kike wannan hasumin, ki kwantar da hankalin ki, wallahi na janye magana ta, na fasa Auren nata".
Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke, tana mai sakin murmushin mugunta, ka na cikin tsantsar kissa da makirci tace.
"Ni wallahi ba zan yarda ba, domin ba zaka raina min da hankali ba, tana a zaune gidan nan ne zaka ce min ka fasa Auren ta?" Ta faɗa tana wurga masa harara.
"Yanzu kuma fisabilillah Hansatu me kike so nayi? Aure ne nace na fasa, to kuma Meta rage?" Ya faɗa cikin sanyin murya yana kallon ta.
"So nake tabar gidan nan, ta koma can gidan uban ta! Domin hankali na bazai taɓa kwanciya ba idan har ina ganin giftawar ta a cikin gidan nan".
"Hansatu kuwa anya lafiyan ki ƙalau? Malikar kike cewa tabar gidan nan? Bayan kin san yanda nake jika a cikin gidan nan, to itama jikar gidan nan ce, ke kan ki kin sani cewar kaka ba zata taɓa lamuntar haka ba"....
"To shi kenan, saita zauna a gidan, Ni kuwa saina je can gidan mu na zauna, kowa saiya zauna a gidan su" Hansatu ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa tsaye.
"Kinga shi kenan, naji zata bar gidan, amma kiyi haƙuri harda safe, in yaso saina Sami kaka nayi mata bayani, tinda yanzu dare ya riga yayi" ya faɗa cikin rauni yana kallon ta.
Ita kuwa sake fashewa da kukan makirci tayi, tana faɗin.
"Wallahi Muzbahu kaji na rantse idan har bata bar gidan nan a gobe ba, to wallahi a gidan uba na zan kwana ".
"Haba Hansatu! Insha Allah hakan ma bazai faru ba, yi haƙuri kin ji?".
Ya faɗa tare da janyo ta a jikin shi, ya sanya hannu ya cire mata katon hijabin da ta sanya, yana mai goge mata ruwan hawaye, ya shiga aikin lallashi, a haka dai suka kwanta babu yabo babu fallasa, sai kukan makirci take zabga masa .
Washe Gari.
Ni kuwa cikin farin ciki muka tashi da safe nida kaka, bamu san kalar waunar da ake toyawa ba,na fara haɗa mana abin karin kumallo, kunun koko da kosai, cikin ƙanƙanin lokaci na kammala, kosan kuwa yayi laushi kuma yayi kyau sai ƙamshi yake yi.
Madaidaicin flaks na ɗauko, na juye kunun a cikin sa, na sake ɗauko matsakaici yar kula na juye kosan shima, sannan na ɗauko na girke mana a falo, kaka ta fito sai santi take yi duk da bata ci ba, muka zauna muka fara Karyawa, sai firar mu muke yi cikin nishaɗi.
Muna cikin Karyawa saiga yaya Muzbahu yayi sallama, kaka ta bashi izinin shigowa, ya shigo ya zauna yana yi mata ina kwana, sai dai fuskar sa babu walwala kamar yanda ya saba, gaisar dashi nayi, ya amsa ba tare da ya kalli ko gefen da nake zaune ba, hakan kuwa yayi matuƙar bani mamaki, domin yaya Muzbahu ko ganina yayi ya dinga wasar haƙora kenan yana tsokana ta, harya siyamin kayan laƙumashe, kaka ce ta katsiye min tinani tana faɗin.
"Malika tashi kije ki kawowa yayanki abin karya kumallo, shima ya ɗanɗana girkin ƙanwar sa".
Na kalle sa, bai ce komai ba kuma kansa a sunkuye, jiki na a matuƙar sanyaye na kama hanyar kitchen, bawai saboda ina son sa ba, a a saboda kawai ban tsammaci hakan daga wajen sa ba.
"Muzbahu lafiya dai na ganka yau ba kamar yanda na saba ganin ka ba?" Kaka ta faɗa tana kallon sa.
Murmushin ƙarfin hali yayi yana mai ɗagowa ya kalle ta.
"Kaka Hansatu tana ɗauke da juna biyu!".
"Kai Masha Allah, ina taya ka murna Muzbahu, ashe abin nema ya samu?" Kaka ta faɗa cikin farin ciki sosai tana kallon sa.
Dakatar da dariyar Tata tayi tana mai faɗin.
"To amma lafiya naga baka farin ciki Muzbahu? Bayan abinda kake nema ne yau Allah ya kawo?".
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, yana mai faɗin.
"Ba Lafiya ba Kaka! Domin Hansatu tace zata zubar da cikin nan idan har Malika bata bar gidan nan ba! Kaka dan Allah kiyi haƙuri Malika ta koma gida kar Hansatu tayi min asarar cikin nan, wallahi ina so naga jini na a duniyar nan......."
"Kai dakata Muzbahu! Idan baka son Malika yanzu ni wannan duk ba damuwa ta ɓace, amma fa wallahi ka sani Malika ba zata bar gidan nan ba saboda wata can barer matar ka...."
"Kaka dan Allah...."
"Fita daga ɗakin nan Muzbahu tun kan Raina ya ɓaci, amma wallahi ka bani mamaki, Daman ashe zaka iya wulakanta ƴar uwar ka, saboda matar ka? To ba zubar da ciki ba, idan taso ma taje asibiti a cire mata gaba ɗaya mahaifar kowa ya huta" kaka ta faɗa cikin ɓacin rai tana kallon sa.
"A a Kaka! Ba za'ayi haka ba, ki barsa kawai Isha Allah zan koma gida yau ɗin nan" na faɗa daga bakin ƙofar da nake tsaye rike da faranti ina kallon su.
"Ba inda zaki je Malika, barsa kawai idan har asiri ke aiki a jikin sa, to Ni babu shi a jiki na, saboda haka zaman ki daram a gidan nan, babu wanda ya isa ya fisshe ki...."
"Kaka kin san halin Hansatu, ba hankali ya ishe ta ba, wallahi tunda hatta furta zata iya zubar da cikin nan...."
"Zanci abu ta kaza kazan ubanka Muzbahu! Ni zaka cewa bata da hankali? A a wiwi take sha!.
Kaka ta faɗa ranta a ɓace tana mike wa tsaye.......✍️.
Hmm tirƙashi, lallai hansatun nan ba ƙaramar makira ɓace, shi kuwa soloɓiyo ya biye mata, Allah ya zama gatan ki Malika🥹.
To kardai ku manta, yawan kike sharing din ku, shine zai saka nayi update gobe idan Allah ya kamu.
Daga Al'kalamin👑 Queen Jiddah......✍️
[12/11, 9:02 AM] Queen Jiddah: The Pen Of 👑Queen Jiddah.....✍️
Channel Link https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H
Update group Link
https://chat.whatsapp.com/LZtufHUnlqUFvnBvvoUWs3?mode=hqrt3
YouTube channel Link
https://youtube.com/@queenjiddahhausanovelschannel?si=NajxqyDlNBtjeOPh
Arewa Book channel
https://arewapen.com/u/hauwaumusa06
Facebook page Link
https://www.facebook.com/profile.php?id=61580403014165
Facebook group Link
https://facebook.com/groups/559415480283144/
🥹GAMO MUKA YI 🥹
True Life Story
By Queen Jiddah
Chapter 9
"A a Kaka! Dan girman Allah kiyi haƙuri ki ƙyale sa haka, kar kiga laifin sa, ƙaddarar Rayuwa ta ce a haka, haka Allah ya tsaramin.
"yaya Muzbahu kayi haƙuri, kuma ka bawa itama Aunty Hansatun haƙuri , Isha Allah zan tafi, domin bazan bari ta zubar da gudan jinin ta, a sanadiyya ta ba".
Na ƙarashe maganar cikin tsananin kuka, tare barin falon na shige uwar ɗaka, hankali na a tashe.
"Malika! Malika! Malika!".
Kaka ta faɗa tana miƙewa tsaye, yayin da nayi wucewa ta ba tare da na sauraren ta ba, cikin ɓacin rai ta dubi yaya Muzbahu wanda yayi shiru bai ce komai ba, domin yasan yanda kaka ke tsakanin ƙaunar Malika, amma bai zata abin zai rincaɓe kamar haka ba, ya zata ko yaya ne zata fahimce shi, musamman idan taji cewar za'a salwantar masa da jinin sa.
"Kai Muzbahu!".
Da sauri ya ɗago daga duniyar tunanin daya lula cikin fargaba ya kalli kaka.
"Muzbahu wallahi ka bani mamaki, ashe Daman kai banza ne! Shashasha! Bakin sakarai! Ban sani ba? Daman shiyasa ka rinƙa nuna kana son ta? Duk domin ka walaƙanta ta? Ina so ka sani a yau Ka samu damar walaƙanta Malika, sai dai ina jiye maka ranar da zaka yi gagarumar nadama, a lokacin da na damar ka bata da amfani".
"Kaka dan girman Allah kiyi haƙuri wallahi ban zata ranki zai ɓaci har haka ba"....
"Dakata! Sam ba haƙurin ka nake bukata ba Muzbahu, kayi maza kabar falon nan tin kan Raina ya ɓaci".
Ta faɗa tana wucewa uwar ɗaka ba tare da ta jira domin jin ta bakin sa ba.
"Inna lillahi wa inna lillahir raji'un!, me zan gani haka Malika?".
Kaka ta faɗa tana ƙarasowa kusa Dani, tare da ƙwace jakar hannu na, wacce nake sanya kayana a cikin ta.
"Malika wai da gaske haɗa kayan naki kike yi? Meyasa zaki ɗau maganar shashashan nan ne? Bashi fa da ikon hanaka zama a gidan nan, domin kinma fisa matsayi a waje na, domin shi ubansa na haifa, ke kuka uwar ki na haifa, wacce na shayar da kaina, Kinga kuwa shi yayi kaɗan yasa kibar gidan nan"...
"A a Kaka dan Allah ki barni na tafi, Ni Malika a Koda yaushe annoba nake zamewa mutum idan harna raɓesa! Na zata wasu ne nake zamewa hakan, ashe harda ku ahali n"...
Tass! kake ji, kaka ta ɗauke Malika da tagwayen maruka har biyu nata fitar da huci ta furta.
"Wai Malika ke wace irin mutum ce, acikin jerin ƴan adam? Meyasa ba zaki karɓi ƙaddarar ki da hannu bibbiyu ba, meyasa kike so ki butulcewa Ubangiji bayan duk yawan tarin ni'imomin da yayi miki? Ki sani fa ke mutum ce ƴar adam, musulma, wacce ta fito a cikin tsatso na ƙwarai, aka haife ki a halattacciyar ƴa ba shegiya ba! Duk waƴan nan ni'imomin dana lissafa miki basu isa ace kin godewa Ubangiji akan su ba? Haka Malika dan Allah ki natsu karka zama shashasha mana".
Kaka ta ƙarashe faɗin hakan tana mai ƙarasowa kusa Dani tare da zaunar Dani akan gado ta sanya hannu tana share min hawaye, tare da fara lallashi na.
Ni kuwa kasa furta komai nayi, sai kuka nake yi hawaye kuwa suna kwarara a fuska ta, yacce kasan an kunna fanfo, yaushe ne zan daina kuka a rayuwa na Ni Malika? Yaushe zan samu soyayya daga wajen dangi na? Yaushe ne rayuwa zata yimin adalci?....
"Malika!".
"Na'am" na faɗa tare da ɗago da fuska na, ina kallon kaka.
Kaka bata ce komai ba, sai shiru da tayi tana kallo na jikin ta a matukar sanyaye.
"Kaka dan Allah ki barni na tafi gida, wallahi koda ace zan cigaba da zama a gidan nan to hankali na, ba kwanciya zai yi ba, bazan kasance cikin farin ciki ba kaka" na ƙarashe maganar tare da sunkuyar da kaina ƙasa, hawaye na sulalowa daga ido na.
Nannauyar ajiyar zuciya kaka ta sauke, ka na tayi murmushi tare da riƙo hannu na.
"Malika kenan, ki kwantar da hankalin ki bazan hanaki tafiya ba kinji?" Ta faɗa tana kallo na, yayin da Ni kuma na jinjina mata kaina, ina mai sanya bayan hannu na, na goge hawaye na.
"Amma fa Malika ina so ki sani bazan ji daɗi ba idan har kika tafi, wallahi ba'a son raina ba Malika, sai dai Ni Kulu a shirye nake, aduk lokacin da kika buƙaci wani abu daga gare Ni, kizo kanki tsaye, karki ji komai a ranki, domin Ni Kakarki ce, wacce duk a cikin jikoki na, bani da wacce nake so kamar ki".
"Nagode Kaka! Na gode sosai, haƙiƙa ke kyauta ce a gare ni, daga wajen Ubangiji" na faɗa ina mai rungume ta tare da fashewa da kuka.
Tashi kaka tayi, tana mai janye jikin ta daga jiki na, tare da janyo jaka ta, ta cigaba da sanyamin kaya na a ciki.
"Hmm Malika Ni dai ban san meyasa kike jin daɗin kuka ba, saboda haka Ni kam ai bazan bari ki koyamin ba, ah to! Tsofai tsofai Dani aga Ina kuka ai abun bai kawo kallo ba" Kaka ta ƙarashe maganar tare da sanya goro a bakin ta, ta fara taunawa, Ni kuwa nayi murmushi ina mai sanya hannu na sake goge hawaye na tare da sakin murmushi.
A ɗaki na bar kaka tana ƙoƙarin shiga banɗaki, saboda nace ba sai tamin rakiya ba, koda na fito tsakar gidan kowa ban kallaba nayi wucewa ta, duk kuwa da yanda nake jin idanun matan gidan na yawo a kaina, wasun su harda faɗin.
"Dube ta fa dan Allah, sumui sumui sai kace mutuniyar kirki, anzo a ƙwace mana mazaje, to ba'a nan ba, sai dai a ƙara gaba" Yaya Zinaru ta faɗa tana hararan ƙeya ta, yayin da sauran matan suka sanya shewa, wasun su harda gwalo, wai nayi bungai babu mai so, shiyasa aka rasa mai kwasa yakai gidan sa.
Duk abinda suke faɗa inaji a kunne na, kuma harga Allah kalmar da suka faɗa a karshe ta ƙona min rai, sai dai hakan bai sanya na tankasu ba, domin idan kare yana haushi ai ba'a tankasa. Hannu na saka gefen fuska ta, sakamakon wani abu mai sanyi da naji yana gangaromin a fuska, koda na shafo sai naga ruwan hawaye, murmushi kawai nayi, domin idan da sabo na saba, kuka ba baƙon abu bane a wajen Malika, idan har mutum zai bada labarin hali na, to kuwa sai dai yace inada saurin kuka, saboda ko harara na kayi bazan tanka kaba, sai dai nayi hawaye na na share.
Ina fitowa na tari, adaidaita na shiga, tare da gaya masa ya kaini, bayan gidan sarki, shiyar fada, sunan unguwar mu kenan wacce ke cikin garin Birnin Kebbi.
Bai tsaya Dani ko ina ba, har saida yakai kofar gidan mu, na sauka tare da ciro ɗari biyar a jaka ta na bashi, sa'annan na ɗauki jakar kaya na, na shiga gidan mu, da sallama ɗauke a baki na, nayi kicibis da baban mu fitowar sa kenan zaije masallaci, har ƙasa na risina na gaishe shi.
"Baba Ina wuni".
"Lafiya kalau Malika, an dawo daga wajen kakar?".
"Eh baba yanzu na dawo".
"To shi kenan, ina fatar kin baro su lafiya?".
"Eh lafiya lau na baro su, sun ce ma, a gaishe ku" na faɗa ina murmushin yaƙe tare da ƙoƙarin ɓoye damuwa ta.
"Tau madalla, Ni bari na wuce masallaci naji kamar ma an tayar da Sallah".
"To Baba, a dawo lafiya" na faɗa tare da kaucewa na basa hanya ya wuce, shi kuwa ya amsamin da Amin, yana fita daga cikin gidan.
Ƙarasa shiga nayi cikin gidan, inda na tarar da Maryam a bakin fanfo tana wanke shinkafar da zata sanya a tukunya.
"Oyoyo Malika, Kai gaskiya munyi kewa a gidan nan" Maryam ta faɗa tana mai ƙarasowa kusa Dani ta rungume ni.
Ban ce komai ba nayi shiru ina sauraren duk abinda take cemin ban tanka ba, har dai itama ta lura da bana cikin walwala, saita sake ni ta dawo tana tambayar meke damu na.
"Lafiya Malika! Meya same ki? Ko wani abu aka miki a gidan kakar? Ina kuma Magen da kika je tare da ita? Naga kin dawo ke kadai, Meke faruwa ne?".
Maryam ta jeromin duka tambayoyin a jere tare da tsure ni da idanuwanta ta, domin idan wani abu ya same ni, itace ke fara ganewa, saboda yanda muke da shaƙuwa da ita.
Mama ce ta fito da sauri a cikin daki, sakamakon Jinda tayi Maryam na ambatar Malika, ai kuwa koda ta fito ina nan a tsaye bance komai ba, saima hawaye dana fara fitarwa ina shessheka.
Da sauri Mama taja hannu na zuwa ɗaki ba tare da ta furta komai ba, ashe Daman kaka ta kirata ta sanar da ita duk abinda ke faruwa harda irin yanda duk nabi na damu kaina akan hakan.
Ranar kuwa mama tasha kuka, domin tana matukar so na, duk wani abu dazai same ni, itake fara jin raɗaɗin a ranta.
Koda na baro gidan ma a yanzu saida suka yi waya da kaka, kaka ta sanarda ita duk yanda muka yi da ita, da nufin idan na dawo ta kwantar min da hankali, saboda kaka tasan nidai bazan faɗi abinda ya faru ba, koda kuwa me zai faru, sai dai damuwan ya kashe ni, amma bazan faɗawa kowa ba, domin ina da zurfin ciki, ba kowa kejin ciki na ba.......✍️.
Hmm yanzu aka fara mutanen Malika, kardai ku manta yawan sharing ɗin ku, shi zai sa nayi saurin yi muku update 🤓
Daga Alƙalamin👑 Queen Jiddah....✍️
[12/14, 9:26 PM] Queen Jiddah: The Pen Of 👑Queen Jiddah.....✍️
Channel Link https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H
Update group Link
https://chat.whatsapp.com/LZtufHUnlqUFvnBvvoUWs3?mode=hqrt3
YouTube channel Link
https://youtube.com/@queenjiddahhausanovelschannel?si=NajxqyDlNBtjeOPh
Arewa Book channel
https://arewapen.com/u/hauwaumusa06
Facebook page Link
https://www.facebook.com/profile.php?id=61580403014165
Facebook group Link
https://facebook.com/groups/559415480283144/
GAMO MUKA YI 🥹
True Life Story
By 👑 QUEEN JIDDAH....✍️
Chapter 10
Tun lokacin da muka shigo ɗakin, koda wasa ban ɗago na kalli maman mu ba, kaina a sunkuye yake ina wasa da ƴan yatsun hannu na, yayin da kuma ruwan hawaye ke sake gangarowa a gefen kumatu na, nayi sauri na goge ina kallon kasan ledar dake shimfiɗe a tsakiyar ɗakin mu.
"Malika!".
Maman mu ta kira suna na tana kallo na, jikin ta a sanyaye, ban tankaba saima ɗago da kaina , da nayi ina kallon ta hawaye taf a ido na.
"Malika wai meyasa kike jin nauyin sanar Dani damuwar ko ne? Ko kin manta cewar Ni ɗin nan Salame, nice wacce na haife ki, ka na duk wani wanda zai nuna miji soyayya a duniyar nan, to wallahi a baya na yake, domin soyayyar uwa da ɗanta ta daban ce, Allah ne da kansa yake sanya ta" maman mu ta faɗa cikin sanyin murya tana kallo na.
"Maman mu me ki ke so nace? Meyasa zan bayyanar da abinda ke damu na, bayan nasan ba samun abin zanyi ba, Maman mu so ki ke nace miki ƴarki Malika da baƙin jini ki ka haife ta, ko kuma so ki ke na rinƙa bayyana damuwa ta a gaban ki, har kema ki kamu da ciwon damuwa" na ƙarashe maganar cikin matsanancin kuka ina kallon ta.
Nannauyar ajiyar zuciya Maman mu ta sauke, ka na ta riƙo hannu na tana mai faɗin.
"Malika! Ina so ki sani, koda ace bani da maganin warakar damuwar dake damun ki, to hakan bashi ke nufin, bani da ikon nasan matsalar ki ba, domin ko ba komai zan taya ki da addu'a, Malika anya kuwa kin san yanda ƙarfin tasirin addu'a iyaye take akan ƴaƴan su" Maman mu ta ƙarashe maganar tana kallo na.
Ƙasa furta komai nayi, sakamakon yanda kuka yaci ƙarfi na, sai kawai na girgiza mata kai ina kallon ta.
"Ban sani ba Maman mu, wallahi ban sani ba, nidai kawai naji bana so na gaya miki wallah na ne, domin kar kema ki shiga damuwa".
Murmushi Maman mu tayi, tare da sanya hannayen ta biyu, ta tallafo fuska ta, tana mai girgiza min kanta, alamun nayi shiru.
"Kinga Malika! Naji kukan ya isa haka, gayamin ina sauraron ki, maza ki gayamin damuwar dake damun ki ƴa ta" Maman mu ta faɗa itama idanuwanta na ciko da kwalla.
"Maman mu!" na kira sunan Maman tare da sanya hannu na, na riƙo nata.
"Na'am Malika!" Maman mu ta faɗa tana dafa kafaɗata.
"Ki nutsu kimin bayani kinji, karki ji komai Malika, kwantar da hankalin ki".
"Maman mu! Ni kaina ban fahimci cewar ina da banbanci da sauran ƴan mata ba, sai a lokacin Auren Yaya Fatima, duk da cewar tun lokacin da na, taso na fara girma, tun daga primary har zuwa makarantar secondary, ina ganin abokanai na mata, suna fira da samari da sunan soyayya, a lokacin kokaɗan hakan baya burge ni, kuma ban ɗauki hakan a matsayin burge wa ba, duba da yanda ki ke mana faɗa nisa Maryam akan karmu kula maza da sunan wata alaƙa, sai dai zuwa lokacin da na shigo aji uku da secondary, lokacin ina da shekaru goma sha biyar, saina dinga jin wani abu dan gane da soyayya, na kanji ina ma, ina da wanda zamu yi soyayya, to meyasa Ni ba'a cewa ana sona, bayan gasu Mansura nan, a tare da samarin su, suna fira da komai irin na masoya, daga lokacin na fara jina daban a cikin su, sai naji na takura, musamman idan naji kowace su na bayar da labari akan saurayin ta, maman mu sai suka dinga min wani kallo suna tsangwama ta, wani lokacin har kuka nake yi, idan na zauna Ni kaɗai, cikin su Mansura ce kawai bata tsokana ta, takance min nayi haƙuri, wata rana sai labari.
Ana cikin haka Bikin Aunty Fatima ya tashi, yayar Mansura, ta gayyaci duka Class mate ɗin mu, lokacin ma har munyi graduation, Ni kuma ina da shekaru goma sha takwas.
Muka shirya a ranar wata Alhamis muka je Dina, tare muka je gabaɗayan mu, saboda akoda yaushe