Share this page
5 / 9
ki tsaya ki saurare ni, kin san haka kawai ba zance ba zanje ba, dole ina da dalili, idan kowa ya juya min baya, bai kamata ke ki kasa fahimta ta ba"..... "Enough Malika! Wace hujja ce ki ke da? Shin Malika ke ba musulma ɓace halan, dahar ba zaki amshi ƙaddarar ki ba, ko kuwa cewa akayi zaki tabbata a haka ne? Eye?" Ta ƙarashe faɗa cikin ƙaraji tana kallo na. Yayin da ni kuma na sunkuyar da kaina ƙasa, ba tare da nace komai ba, hawaye na gangarowa a kumatu na. Ganin hakan sai yasa jikin Mansura yayi sanyi, duk wata tijara Tata, saita kwanta, ta sanya hannu tana mai dafa kafaɗa ta tare da faɗin. "Wallahi Malika Ni inaji a jiki na, kamar wannan yanayin, ba zai jima ba zai wuce, ji nake kamar na ɗan Wani lokaci ne, idan muka yi haƙuri wallahi wata rana sai labari ki yarda Dani Malika" Mansura ta faɗa tana rungume ni tare da fara lallashi na. Na ɗago daga jikin ta, tare da sakin murmushi ina mai jinjina mata kaina, alamar na gamsu da zancen ta, ka na, na sake jiyowa gefen Maryam na kalle ta, wacce tayi shiru tana kallon mu, jikin ta a matuƙar sanyaye, domin har cikin ranta tayi dana sanin abinda ta faɗawa Mansura. "Yaya Malika dan Allah kiyi haƙuri, wallahi dana sani daban gaya mata haka ba, dana sani zan gaya mata cewar kawai baba ya hana ki zuwa, dan Allah ki yafe min". Ban ce mata komai ba, na tako da ƙafafuwa na, harna iso kusa da ita ina mai dafa kafaɗarta tare da sakar mata da murmushi, na furta. "Kinga Maryam, kwantar da hankalin ki dan Allah, ki nutsu, ai ba laifi ki ka min ba, kinyi abun kirki sosai, tunda har ki ka hana ni yin ƙarya, kinga kuwa kin sami lada".... "Amma Yaya Malika!"... "Ya isa Dan Allah Maryam! Nace miki ba komai ya wuce, Mansura bari na shirya sai mu wuce ko?" Na faɗa ina buɗar wedrobe ɗin tufafin mu. "Malika wankan fa?". "Wane wanka kuma Mansura? Ina ce da azahar ɗin nan nayi wanka, to fisabilillah wane wanka kuma zan sake yanzu?" Na faɗa ina ɓata fuska ta, tare da fitar da kayan da zan saka. "Oh oh Malika mayarda wuƙar, abin duk bai kai can ba, amma wallahi idan muka je aka ce ana jin bashi bashi a wurin ba rufa ki zan ba, ah to gaya musu zanyi kece baki yi wanka ba" Mansura ta fada tana kwashewa da dariya. Ni kuwa ban kula ta ba, na zaro jallabiya ta sabuwa fall, onion color na sanya, na janyo takalmi farare tare da jaka ta, itama fara na rataya, light make-up nayi, daga powder sai man leɓe, na shafa, humra mai sassanyan ƙamshi na murza, na kawo mayafin abaya ta na yafa tare da ɗaukar ƴar madaidaiciya waya ta, na riƙa Infinix Smart 10 sabuwa dall wacce Baban Mu ya siyamin Lokacin da nayi passing Exam ɗita ta Diploma A Waziri Umaru Federal Polytechnic Birnin Kebbi department of (Science Laboratory and Technology). Na juyo cikin yanga ina cewa. "Mansura tashi muje mana, ko kin manta Uncle Ammar yana waje yana jiran"..... Ban ƙarasa maganar ba nayi shiru sakamakon ganin maman mu ta shigo cikin ɗakin. Nan suka gaisa da Mansura har take tambayar ta ina mamar ta, tace tana nan lafiya. "Allah sarki Mansura, ki baiwa hajjo haƙuri, insha Allah anjima zan shigo akai amarya tare Dani" Maman mu ta faɗa tana murmushi. Murmushi itama Mansura tayi tana faɗin. "Lah babu komai wallahi mama, karki damu nasan zata fahimta". "Hmm Mansura kenan, Ni nasan nayi laifi ai, ko ba dan Malika ba ai zanje saboda maƙotaka, amma Kinga sai nayi biris na watsar banje ba, Ah ah ke kuma ina zaki je ne haka da wannan kwalliyar?" Maman mu ta faɗa tana kallo na. "Maman mu Walima zamu je". "Hmm Malika kenan, Daman nasan ai zaki je walimar shiyasa ɗazu da naga kina nema ki saka min ciwon kai, na saka miki ido ai" Maman mu ta ƙarashe maganar tana harara na. "Mama dan Allah ki gayawa baba, ba zamu dawo da wuri ba, saboda tare damu za'a kai amarya". "Tau shi kenan Mansura insha Allah zan sanar mai, amma kar kuyi dare, Malika Kinga dai faɗan da ki ka sha jiya ai, ah to"... Mama Faɗa akayi mata jiya"..... "Maman mu mun tafi sai mun dawo" na faɗa ina jan hannun Mansura muka bar ɗakin ba tare da ta ƙasara tambayar ƙwaƙwaf ɗinta ba. Koda muka fita, a waje muka samu motar Uncle Ammar, bamu ɓata lokaci ba muka nufi wurin walimar, ina ji yana yi mata mitar wai munshaya sa a waje, nidai ban kula su ba, na kunna waya ta, tare da shiga Whatsapp ɗina, nan take na shiga wani channel Mai suna QUEEN JIDDAH NOVELS CHANNEL wanda ake update na littafin MASARAUTAR ZAZZAU na wata Marubuci ya wai Queen Jiddah, babban abinda ya burge ni a labarin bai wuce yanda aka haɗa masarautoti har uku a cikin sa ba, ga kuma tsaface tsaface gami da Yaren larabci a cikin sa, da kuma rayuwar indiyawa, saboda nidai a rayuwa ta, ina son rayuwar India, komai nasu burge ni yake yi. Ina cikin karatun muka Isa wurin, ai kuwa na kashe Data na, tare da saka waya na cikin jaka na riƙe tamau, gudun kar amin salalar tsiya. Abdullahi Fodio Islamic center (A.F.I.C) Shine sunan hole ɗin walimar. Koda muka isa hole ɗin ma, Amarya Aunty Fatima da ƙawayen ta har sun jima da isowa, saboda lokacin har ƙarfe 6:20pm tayi, kasancewar bamu fito gida ba, saida muka yi sallar La'asar. Wani Malam ILiyasu ne, yazo yayi Nasiha a wajen walimar, shi ɗin ya kasance Malamin mu na islamiyya ne,( Madarasatul Nurul Huda) wacce ke cikin garin Birnin Kebbi. A nan wurin ma bamu zauna ba, domin nida Mansura aka hannun tawa rabon take away na wurin, da kayan savenious. Muka yi rabon har muka gama Banga Shamsiyya da Nadiya ba, da naso na share, sai kuma na tambayi Mansura, nan take cemin wai ba zasu zo ba sai idan za'a kai amarya, saboda suna da uzuri, nace to Allah ya kaimu, tace min Amin. Da muka tashi wajen walimar ma, uncle Ammar ne yazo ya ɗauke mu, saboda yace shi bai yarda Mansura ta hau adaidaita sahu ba. Kai tsaye gidan su Mansura ya ajiye mu, da nufin zai dawo anjima idan za'a kai amarya. Koda muka shiga gidan kuwa timƙim yake da mutane, Maman mu ma a can muka tarar da ita, tare da Maryam da Nana. Bayan mun gaisar da mutanen wurin muka nufi ɗakin Mansura kasancewar su suna da matsakaicin ƙarfi. Muna isa Mansura ta faɗa toilet, bata jima ba ta fito ɗaure da towel, nace. "Wai Mansura wanka ki ka yo ko me?". "Eh wanka nayo, kuma wallahi kema sai kinyi, ƙazama kawai" ta faɗa tana harara na. Ba don naso ba haka nima na shiga banɗakin nayo wanka, koda na fito harta shirya cikin wata tsadaddar atamfa, ɗinkin A_Sharp. Ina fitowa kuwa na shiga yaba kyan ɗinkin harma da atamfar, nan ta janyomin nawa ɗinkin, ashe wai anko tayi mana mu biyu komai iri ɗaya, harda ɗin kin. Abinci muka fara ci, ka na muka yi sallar isha'i, sannan muka yi make_up, fararen jaka da takalman mu muka sake saka wa, kasancewar atamfar tana da duhu, kuma tasha duwatsu farare sai sheƙi muke yi, ai kuwa muka ƙara fita ɗas ɗas damu. Sanda muka gama komai har masu ɗaukar amarya sun zo, wanda yayi dai dai da isowar Uncle Ammar, ai kuwa muka nufi motar sa, ba tare da munbi takan amarya da ƙawayen ta ba, saboda Daman ita Aunty Fatima da Mansura ba wani shiri suke yi ba, ga ƙawayen nata sai faman ji da kan tsiya. Zamu shiga motar muka tsinkayi Muryar Shamsiyya tana kiran mu, koda muka juyo kuwa muka saki ihu tare da rungume juna, saboda Daman bamu da riƙo, daga munyi faɗa muke shirya wa. Ihu muka saka muna tsalle saboda yanda muka yi bala'in haɗewa, ashe suma anko suka yi su biyu Nadiya da Shamsiyya. Mansura tace su zo muje a motar uncle Ammar, suka ce A a tare suke da abokanen ango, General Jamal Abbas, da kuma saurayin Shamsiyya. Cikin yanga da iyayi suka shige motocin su, mu kuwa muka shiga a motar uncle Ammar, tare da biyar bayan sauran motocin da amarya take ciki, su Aunty Fatima ansha kuka har an gaji, za'a rabu da gidan iyaye aje bautar aure, rabuwa da iyaye babu daɗi, amma hakan shine kowace macce ke fatan gani a rayuwar ta. Lokacin da muka ƙarasa ƙofar gidan, a lokacin na sauke nannauyar ajiyar zuciya ina mai fatar kamar yanda zamu shiga gidan nan lafiya, to Allah yasa mu fito cikin sa lafiya ba tare da wata hatsaniya ba, yayin da zuciya ta ke tsananta bugawa, ƙirji na yana harbawa, inaji na a matukar tsorace, akoda yaushe irin wannan yanayin nake tsintar kaina idan har zanje a wurin da ya kasance akwai Samari da ƴan mata , ji na nake yi a matukar takure, tamkar na ɗaura hannu na aka, in fasa ihu! Yayin da nasan ba zan samu wata kima ko darajar kallo a wajen su ba....✍️ Like share and comment fisabilillah 🙏 🙏 Daga Alƙalamin👑 Queen Jiddah....✍️ [12/21, 8:13 PM] null: The Pen Of 👑Queen Jiddah.....✍️ Channel Link https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H Update group Link https://chat.whatsapp.com/LZtufHUnlqUFvnBvvoUWs3?mode=hqrt3 YouTube channel Link https://youtube.com/@queenjiddahhausanovelschannel?si=NajxqyDlNBtjeOPh Arewa Book channel https://arewapen.com/u/hauwaumusa06 Facebook page Link https://www.facebook.com/profile.php?id=61580403014165 Facebook group Link https://facebook.com/groups/559415480283144/ 🥹 GAMO MUKA YI 🥹 True Life Story By Queen Jiddah 👑 Chapter 13 Koda muka isa gidan Masha Allah, wuri yayi kyau ba laifi, sai dai mu kaɗai muka shiga gidan ba tare da uncle Ammar ba, cewa yayi zai dawo anjima tare da abokanen ango. Mukam muka shiga cikin zumuɗi, muna biyar ko'ina da kallo, kasancewar gidan ba ƙaramin tsaruwa yayi ba, two bedroom ne da kuma one falor sai kitchen da dining tare da sauran abinda ba'a rasa ba. Shamsiyya da Nadiya ma acan muka tarar dasu, sun riga mu isa, maman mu da Maryam tare da Nana ma basu jima da wucewa ba, tare da kakannin Aunty Fatima da kuma ƙannen mahaifiyar ta. Wuri kawai muka nema muka zauna, bayan sallamar da muka yi, saboda ƙawayen Aunty Fatima shegen iyayin tsiya ne dasu, shiyasa bamu wani shige musu ba. Fira suke suna tsokanar ta, ita kuwa sai ƴan matan hawaye take yi, jikin ta duk yayi sanyi. Ana cikin haka muka jiyo hayanitar angwaye tafe, nan aka gyarawa Aunty Fatima lulluɓinta, tare da sake feshe ɗakin da tirare . Da shigowar su kuwa surutu ya ɓarke, aka fara ba'a da musayar zance irin na abokanen ango da ƙawayen amarya. Shamsiyya dai tana a gefen saurayin ta, sai Nadiya wacce ke gefen General Jamal Abbas, da kuma Mansura wacce ke kusa da uncle Ammar dan shima bai jima da shigowa ba. Sai kuma ƙawayen Aunty Fatima su uku, wato Lantana da Jamila sai kuma murja dukkan suma a wajen suka yi samari, cikin abokanen ango. Nidai ban shiga cikin su ba, kasancewar dama can bana son hayaniya, gefe na rakuɓe ina danna waya ta, ba tare da Ni kaina nasan irin halin da nake ciki ba. Bayan wasu abubuwa da kuma nasihohi da angwaye suka gabatar , aka sayi bakin amarya Naira dubu saba'in, kasancewar gaba ɗayan mu, ƴan matan Amarya mu bakwai ne,sai ko wanen mu ya tashi da dubu goma. Aka fara watsewa nida Mansura muka nufi motar uncle Ammar, Shamsiyya da Nadiya ma motar samarin su, suka shiga, sai sauran ƴan matan ko wace ta nufi motar sabon saurayin ta, don ya mayar da ita gidan su. Da yake unguwar da aka kai amarya a G.R.A NEFA ne shiyasa uncle Ammar ya tsaya da mu ta wajen MARACANA ya fita ya bar mu a mota, baifi mintuna biyar ba sai gashi ya dawo da ledoji guda uku. Yabaiwa mansura biyu, tare da ajiye ɗaya a gefen sa, kamar bata so ba ta amshi ledar tana yi masa godiya, tare da juyowa bayan sit ta miƙomin ɗaya ledar, kamar bazan karɓa ba sai kuma na amsa ina murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciyo, tare da yi masa godiya. Bamu fi mintina biyar ba muka isa unguwar mu, kasancewar daga MARACANA zuwa unguwar mu Bayan Gidan Sarki, ba wata tazara bace, face titina da suka zama tsakani. Ƙofar gidan mu ya fara tsayawa, lokacin har ƙarfe 10:20pm na dare, na buɗe murfin motar ina musu Saida safe, can na tsinkayi Muryar Mansura tana cewa, wai kar dai na manta gobe da safe idan Allah ya tashe mu lafiya akwai YININ AMARYA da za'a yi, saboda haka saina shirya da wuri. Kai kawai na jinjina mata, tare da ƙarasa rufe marfin motar na shiga cikin gidan mu, sallama ɗauke a baki na. Saida na fara jan ƙofar na rufe da sakata, sunan Allah ɗauke a baki na, saboda nasan kowa ya riga da ya shigo ni kaɗai ce ban shigo ba. Farfajiyar gidan namu shiru, ga duhu daya mamaye ko'ina, ai kuwa na susuɗa da sauri na shige ɗakin mu, abinka da mai tsoro, sai kace farar kura. Koda na shiga ɗakin namu, zaune na tarar da Maryam tana waya da saurayin ta, cikin sauri sauri na ajiye ledar hannu na tare da gyale na da jaka, nayi waje, saboda yanda fitsari ya cika min mara. Banɗaki na fara zuwa nayi fitsari tare da fitowa tsakar gidan mu ina wanke hannu na. "Malika! Kin dawo ne?" Na tsinkayi Muryar Maman mu tana faɗa. "Eh Maman mu, yanzun nan na shigo" na faɗa ina kallon ta. "To ina fatar kin rufe ƙofar gidan?". "Eh Maman mu na rufe". "Tau shi kenan saida safe" ta faɗa tana shigewa ɗakin Baban mu. Nace mata Allah ya tashe mu lafiya, sanda nake ƙarasa wanke hannu na tare da fuska, saboda na riga da nayi sallar isha'i tun a gidan su Mansura kafin muje kai amarya. Shiyasa hannu na kawai na wanke a yanzu Tare Da ɗauraye fuska na, na nufi cikin ɗakin mu. Maman mu mace ce, wacce bata iya barci har sai taga a inda muka kwanta, shiyasa duk inda naje nake sauri na dawo, saboda nasan Maman mu ma bata yi bacci ba. Koda na shiga ɗakin ina kyarma, saboda sanyi, don yanzu lokacin sanyi ne, ba'a jima da gama ruwan sama ba, Maryam kam harta buɗe ledar dana shigo da ita, tare da nemo faranti. Ai kuwa nima nazo na baje a wurin saboda yanda nake jin yunwa kamar naci babu. Muna ci muna santi, ashe Shawarma ce da kuma cips tare da ice_ cream ya saya mana. Ice_cream muka fara sha, sannan muka ci Shawarmar saboda shawarmar guda biyu ce, shiyasa muna ci muka ji cikin mu yayi bam. Cips ɗin kuwa muka baje shi a faranti, saboda yanda ake ƙarancin wuta a Birnin Kebbi shiyasa bamu saka shi a fridge ba. Nan Maryam ke tambaya na, wai ko Sabon saurayi nayi ne? Murmushi kawai nayi tare da ce mata, ai uncle Ammar ne ya siya mana, tare da Mansura, duk kuwa da yanda maganar tata ta daki ƙirji na. Tsakar gida muka sake fita muka wanko hannun mu, tare da shan ruwa, komai da muke yin sa, cikin taka tsantsan muke yi, kar maman mu taji, duk da mun san gobe ma akwai rikici, idan ta tarar da cips ɗin nan, saboda bata so muna karɓar komai a hannun namiji, amma wataƙil idan taji daga uncle Ammar ne, ta taƙaita faɗan nata. Koda muka dawo ɗakin ma, fira muke yi har bacci ya ɗauke mu. Da asuba ma, sallah kawai nayi na koma bacci, saboda yanda na kwaso gajiyar biki, shiyasa ko maman mu bata tashe ni ba, duk da cewar bata bari muna baccin safe. Ban tashi ba sai wajen ƙarfe 10:30am na safe, lokacin har Maryam ta gama aikace-aikacen gidan, ai kuwa na faɗa banɗaki tare da yin brush da wanka ka na, na fito. Koda na fito a ɗakin na tarar da Maman mu, nayi mata Barka da safiya, ta amsa cikin kulawa, sannan na fara shirya wa, saboda nasan yanzu haka idan Mansura ce tana hanya. Wani kyakkyawan leshi na, na saka Miyon goro, mai matsakaicin kuɗi, ɗinkin riga da sket, ni kaina nasan nayi kyau, ina cikin ɗaurin ɗankwali, maman mu ke tambaya na, ya muka kai amaryar jiya? Tana fatar Komai dai Lafiya. Nayi murmushi ina ɗaga mata kai, saboda Alhamdulillah babu wata matsala, lafiya ƙalau muka watse. Muna cikin haka saiga Maryam ta shigo, banbi ta, tata ba na fita tare da wucewa kitchen, na nemi waje na saka abinci, tare da dawowa ɗakin mu ina yamutsa fuska, saboda shinkafa da wake ne Maryam ta girka gashi ni Kuma bana son shinkafa da wake, idan har aka dafa shi sai dai nayi zaune na tsince waken tass sannan naci zallar shinkafar. To yanzun ma zaune nake ina tsince waken, maman mu tace. "Oh ni Salame! ni Kam Malika na kasa gane wannan ƙiyayyar taki da wake, shi mutum ace ba zai ci wake ba, bayan yana gina garkuwar jiki" ta ƙarashe maganar tana ɗaura hannun ta a haɓa. Nidai murmushi kawai nayi ina faɗin. "Wallahi Maman mu Ni dai waken nan ne kawai bana so" na faɗa ina langwaɓarda kaina. Maman mu tace. "wane wake ne bakya so Malika? Keda ko Doya muka dafa a gidan nan cewa kike bakya ci, bakya cin wake haka kuma bakya cin sakwara, kunun kokon nan idan har aka saka mishi sikari bakya sha". "Kinga Maman mu, Allah ki ƙyale ta, Ita da bata cin wake meyasa idan akayi kosai ko alala take ci" Maryam ta faɗa tana taɓe bakin ta. Nidai ban tankasu ba na fara cin abinci na, bayan na tsince waken duka. Ana cikin haka muka jiyo Muryar mansura tana yin sallama. Muka amsa mata, ta shigo ɗakin tare da rissaniwa ta gaida Maman mu, Maman mu ta amsa mata cikin sakin fuska tana tambayar ta, yaya hidimar biki, Mansura tace. " Alhamdulillah Mama sai godiya". "To Allah ya basu zaman lafiya ya nuna mana naku". Ameen Mansura ta sake faɗa tana sussunne fuska cikin jin kunya. Nace "Allah kinji daɗin addu'ar nan, ki daina ma wani munafurci". Mansura ta ɗago tana kallo na tare da ware idanuwanta tana faɗin. "Kai ta waje na, kin kuwa ga yanda kika yi masifar kyau!". Ban tanka ta ba, saima taɓe baki da nayi ina faɗin. "Kya ji dashi". "Allah Malika kin yi kyau, wannan wankan ai har gidan Dr. Nasir Idris kwauran gwandu, gwamnan mu na Jahar Kebbi sai muje" ta ƙarashe maganar tana juyar da dara daran idanuwanta. Ban kula ta ba, na tashi naje bakin panpo na wanke hannu na tare da kwanon da naci abinci, sa'annan na dawo ɗakin tare da ɗaukar mayafi na da jaka na rataya, na sanya takalmi, nace. "Mu je". Mansura ta tashi tana yiwa Maman mu sallama. A dawo lafiya Maman mu tace tana murmushi, yayinda muka fice muna amsa wa da Amin. A ƙofar gidan mu, muka tarar da motar uncle Ammar, muka yi sallama tare da shiga ciki. Ya ja motar muka fara tafiya, shi kanshi uncle Ammar yayi mamakin gani na cikin annashuwa kamar haka, saboda daman can Ni ban cika sake wa da mutane ba, sa'annan ban cika kwalliya ba, sai idan Mansura ta takura ni, sai gashi yanzu na caɓa ado, wanda ni kaina bansan dalilin yinsa ba. Bamu fi mintina goma ba, muka isa har ƙofar gidan Aunty Fatima, uncle Ammar ya sauke mu da zummar zuwa ƙarfe biyu zai dawo tare da abokanen ango. Mukam muka yi shigewar mu ciki, a can muka tarar da Shamsiyya da Nadiya, suma Masha Allah sunyi kyau abin su, muka kuwa zauna a nan falon Aunty Fatima muna shan firar mu. Ina jin su Murja ƙawayen Aunty Fatima suna magana akan zasu je nan maƙotan Aunty Fatima suyi girki, nidai ko kallon su banyi ba, amma a yanda na fahimta kamar angwaye sun jima da kawo kayan yin girkin tun kamin mu iso. Da yake idan za'a yinin Marya, ƙawayen ta ke yin girki na musamman tare da wasu soye soye, saboda angwaye su zo su ci, kuma su biya kuɗi, to wasu daga nan ne ma suke kulla soyayya har akai ga yin aure! Sai kaji ana faɗin ai wance da wane a auren wance suka haɗu, shi kenan fa. Nan dai suka sanya almajirai suka kwashi kayan girkin zuwa maƙotan Aunty Fatima, bayan sunje sunyi magana da matar gidan, ta ce su zo ba matsala, aka kwashi shinkafa, kabej, Magi, oil, da sauran Vegetables suka tafi. Mukam muna nan a zaune, muka yi kamar bamu gansu ba, tinda suma basu neme mu ba, ita kanta Aunty Fatiman bata ce muje ba, saboda tasan halin ƙawayen ta da shegen son girma, mu kuwa ba basu girman zamu yi ba. Mansura tamin raɗa a kunne tace. "Ke Malika! Banga fa sauran kazar amarya ba, bari na tambayi Aunty Fatima". Nace 'A a Mansura! Dan Allah ki ƙyale ta, kin san dai da akwai zata bamu, yanzu haka ba shakka wa'yannan kwaɗayayyin sun cinye".... Tun ban ƙarasa ba, Mansura ta kece da dariya tana faɗin. "Wallahi kuwa Malika da gaskiyar ki, dan da alama sammako suka buga". Nidai ban sake cewa komai ba, face murmushi da nayi, ina mayar da hankali kan game ɗin da nake bugawa a waya ta. A bisa al'adar mu idan har aka kai amarya to washe gari ƙawayen ta ke zuwa su cinye ragowar kazar amarcin ta, wanda da alama su murja sun jima da gamawa da ita. Har muka yi muka gama, ba wacce ta kula mu a tsakanin Shamsiyya da Nadiya, ko wacen su sabgar gaban ta take yi, mu ma kuwa sai muka cigaba da firar mu muna annashuwa. Can saiga wayar Mansura tayi ƙara, bata ɗaga ba sai ɗagowa da tayi muka haɗa idanu, tamin alama dana biyo ta sanda take shigewa bedroom ɗin Aunty Fatima. Na kuwa tashi sumui sumui kamar munafuka nabi bayan ta. A ɗakin Aunty Fatima na tarar da ita, tayi ashe ashe akan gadon . Na kuwa zaro ido ina dafe ƙirji tace. "Yanzu ke Mansura akan gadon amaryar kika kwanta?". Tsaki Mansura tayi tana dalla min harara tace. "Ke dan Allah bana son munafurci idan zaki zo ki zo muyi magana". Nace. "Amma fa kin san malamai sunce bakwai hawa shimfiɗar amarya hakan na nufin akwai zunubi kenan".... Ban kai ga ƙarasawa ba mansura ta janyoni da ƙarfi na zauna akan gadon, ta wani haɗiye fuska tana faɗin. "Wallahi Malika kin cika ƙorafe ƙorafe, to idan ƙonewa akeyi a gadon sai mu ƙone tare". "Ah haba dai Mansura Meya kai can? Allah ma ya tsare". "Oho miki dai" ta faɗa tana ɗauramin wayar ta a cinya ta. Koda na ɗau wayar, sai nayi sororo ina biyar fuskar dake ciki da kallo. Tare da mayar da hankali na wajen ta domin neman ƙarin bayani. Matsowa tayi kusa dani tana faɗin. "Kin gani ko Malika? Dama me nace miki? Ba nace dake komai zai wuce ba, Malika Allah baya barci kuma yana amsar roƙon bayin sa! Wannan da ki ke gani sunan sa Yaya kamal, abokin mijin Aunty Fatima ne, tun lokacin da aka fara hidimar bikin nan ya ganki, sai jiya da muka kawo Aunty Fatima yamin magana akan yana son ki! Ba yanda baiyi min magiya akan na bashi numbern ki ba, amma naƙi, kiran nan ma da ki ka ga anyi min shine yake kira na, wai so yake yaji Muryar ki, bawan Allah Ni wallahi harya bani tausayi, Amma nace dashi ya bari zuwa anjima idan suka zo saina hada ku, ku zauna kuyi magana ku fahimci juna, amma ke ya ki ka ce?" Mansura ta ƙarashe maganar tana kallo na, yayin da Ni Kuma nayi shiru, jiki na yayi matuƙar yin sanyi, na sunkuyar da kaina ina tsiyayar da kwalla domin abun ya zo min a bazata.....✍️ Mutanen arziki kuyi haƙuri saboda jinkirin da nayi banyi update ba, har nayi tapping word 1,600 na nemi page ɗin na rasa, saida na sake wani tapping ɗin🥹. Like share and comment fisabilillah 🙏 Daga Alƙalamin👑 Queen Jiddah .....✍️ The Pen Of 👑Queen Jiddah...✍️ Channel link https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H 🥹 GAMO MUKA YI 🥹 True Life Story By Queen Jiddah 👑 Chapter 14 "Malika dan Allah kar kice bakya son Yaya Kamal, wallahi a jiki na nake jin cewar shi mutumin kirki ne, duk da cewar ban wani sanshi ba, amma ba zan manta ba, akwai wani lokaci da mijin Aunty Fatima yazo fira wajen ta tare dashi, kamin suyi aure, lokacin ne Aunty Fatima ta dawo tana bamu labari, har take cewa wai shi ɗin ya kasance ɗa mafi soyuwa a wajen Ministan Shari'a na ƙasar nan!"

Chapter 5 of 9